Showing 57001 words to 60000 words out of 113545 words

Chapter 20 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

gami da yin nan nan da
AlHassan.
"Me ka fi so dan uwanmu, me za a girka maka?"
Ya yi murmushin da bai kai zuci ba.
"Ko me kika sa aka girka zan ci Hajjaju."
Ta yi dariya tana duban Hussein wanda ya dauke kai ya
maida hankali ga wayarsa.
"Shikenan an gama! Kai fa Mijin? Me ka ke da muradin
ci?"
Ba tare da ya dube ta ba ya amsa.
"Duk abinda ki ka sanya a girka."
"Shikenan. Ai yau da kaina zan shiga kicin, da hannuna
zan muku girki don yau ranar farin ciki ce gare mu. Rana
ce da ba za mu mance ba."
Anan ne Hussein ya ɗan kalleta ya yamutsa fuska. Ta
wuce sama da sauri da niyyar sauya kaya. Bayan tafiyarta
ya yi jifa da wayar ya riƙe kai zuciyarsa na zafi. Dakyar ya
iya kai zuciya nesa bai shaƙe wuyanta ba.
"Akwai wuya fa, dakyar na iya jure kallon fuskar matarnan
taka."
AlHassan ke maganar yana dubansa, ya dago ya ja guntun
tsaki.
"Ka daina haɗa ni da ita please."
Murmushi kawai AlHassan ya yi ya dubi agogo.
"Ya kamata mu yi haramar tafiya masallaci, daga nan ina
son wucewa asibiti na ga jikin Ƙanwata."
Shiru ya samu maimakon amsa daga bakin Hussein kawai
dai ya mike ya nufi bandakin dake falon, can ya fito. Ganin
alwalar ya yi shima ɗan uwan ya mike ya shiga toilet.
Daidai sadda Hajiya Zeenatu ta sauko cikin wata doguwar
riga ƴar kanti da ta matse ta, albarkatun tumbinta duk sun
fito sun yi layi-layi. Ya kauda kai yana ji kamar ya yi amai
da ya tuna tsawon lokacin da ya ɗauka yana haɗa jiki da
ita.
"A'a, ya na ga kun miƙe? Ina shi AlHassan din?"
Hussein ya ci gaba da ɗora agogonsa bai ce komai ba.
Don kanta ta ba kanta amsa.
"Oh, yana toilet kenan. Lallai kam don Magriba ta kusa.
Bari na leka kicin sai na koma na yi alwalar nima."
Murmushin gefen kumatu ya yi jin wani sabon salo, kiran
sallah da wutsir. Hajiya Zeenatu da batun ɗora alwala?
Jinjina kai kawai ya yi ta sauke ajiyar zuciya ta yi hanyar
kicin tana kwala wa John kira.
AlHassan na fitowa suka kama hanya. Daga masallaci,
suka dawo suka shiga motar Hussein din, a waya ya ke
sanarwa Hajiya Zeenatu fitarsu.
"Haba haba don Allah, girki fa zan muku yanzu."
Sai da ya daki sitayari gami da jan tsaki don wani irin
ɓacin rai da shagwaɓar Hajiya Zeenatu ta jawomasa. Yana
gani AlHassan na mishi hannu alamar ya nutsu. Ya daure
ya amsa.
"Kiyi hakuri Madam, yanzu za mu dawo, ba wani jimawa
za mu yi ba. Kayansa zan kai shi ya kwaso daga Hotel."
Bai bari ta karashe amsawar ba ya kashe wayar.
***
Yusufa wanda a kan idonsa mota ta fice daga gidan da
Halima ta mishi kwatance, ya bi motar da kallo, ganin
ba'a ganin na ciki ne yasa shi maido hankali ga Maigadin.
Da sauri ya karasa tun kafin ya karasa rufe ƙyauren.
"Sannu Baba."
Maigadin ya dube shi.
"Yauwa ɗan samari, lafiya dai?"
"Lafiya kalau. Don Allah nan ne gidan Hajiya Zeenatu?"
Gyada kai Baba Maigadin ya yi.
"Eh kwarai, nan ne."
Sauke ajiyar zuciya Yusufa ya yi.
"Alhamdulillah, don Allah wurinta na zo. Idan ba damuwa
ka yimin iso Baba. Ka ce mata Halima ce ta turo ni.
Sunana Yusufa."
"Toh banda abinka ɗan samari, Halima kawai babu wata
inkiya ko wani abun? Idan ta ce ba ta gane ba fa?"
Yusufa ya yi shiru, ya san ko sunan ubansu zai faɗa a
banza don ba lallai Hajiyar ta san ta da wannan sunan ba.
Don haka dabara ta faɗomasa.
"Yauwa, ka ce ƙanin Halima ne ma'aikaciyar Revenue.
Aikoni ta yi."
Kasancewar Baba Maigadi ba baya ba, daidai gwargwado
yana da ilimin boko yasa fadin sunan bai ba shi wuya ba.
Ya ce ya shigo ya tsaya daga bakin ƙyauren, Yusufa ya yi
godiya ya shigo. Ya dinga bin tamfatsetsan gidan da kallo
cike da jinjina irin dukiyar da ala narkar. Sai ya gan shi
wani ƙaramin alhaki kuma wani almajiri a gaban gidan.
Koda Baba Maigadi ya isar da saƙon ga Hajiya Zeenatu,
nan da nan ta daure fuska.
"Na ba ka damar barin ko wane kare da biri shigowa
gidana?!"
Baba Maigadi ya dan russuna a ladabce.
"Ki yi hakuri ranki ya daɗe, na dauka kinsan Halimar ne.
Amma.."
"Kai dalla yimim shiru hakanan! Ka koma ka ce mishi babu
wata Halima da na sani don haka ya gaggauta bar min
gida tun kafin ya yi maka sanadin aikinka."
Jin haka ai da sauri Baba Maigadi ya kara bada hakuri
tukunna ya kama hanya da sauri-sauri. Idan aka yi mishi
sanadin aiki kuma ina ya kama?
Yusufa na hango shi ya ƙuramishi idanu. Maimakon ya ji ta
ba shi damar ganawa da ita, sai ya ji akasin hakan. A
ƙarshe ma Baba Maigadi bude mishi kyaure ya yi yana mai
ba shi hakuri da roƙon ya tafi tun bai jazamishi ba. Haka
Yusufa ya fita jiki a matukar sanyaye. Ta tabbata dai
karshen Halima ne ya zo. Komai yanzun zai iya faruwa
gareta tunda har ta bari zuciyarta ta rinjaye ta wurin aikata
abin dana sani da kuma nadama.
***
A farfajiyar asibitin ya faka motar.
"Muje ko?" Cewar AlHassan ganin Hussein din ba shi da
niyyar fitowa.
"Ka fara shiga, ina nan zuwa. Akwai wayar da zan amsa
ne."
Bai takura mishi ba ya yi gaba zuwa ciki, Hussein ya
kwantar da kai saman kujera gami da lumshe idanu.
Hoton fuskar Chairman Aliyu Dikko ya kasa fice mishi. Ya
kasa mance ganin da ya yi mishi a wajen Ramlat.
Kwankwasa gilashin motar da aka yi ne ya maido shi
hayyacinsa, ya ɗago kai ya sauke gilashin. Ganin Hisham
ya ja guntun tsaki. Hisham ya dora hannu saman windon.
"Yanzu na ga Twin brother dinmu, ya cemin kana mota shi
ne nace bari na zo na ji abinda ha dakatar da kai daga
shiga."
Hussein bai ce uffan ba, hannu kawai ya sa ya ƙaro
volume na waƙar da ya ke ji.
Hisham ya zagayo ya bude mazaunin gaba ya shiga gami
da kashe waƙar gaba daya.
"Kana da tabbacin abinda ka ke yi zai haifarmaka da ɗa
mai ido? Kana da tabbacin wacce ka ke so za ta so ka a
wannan halin? Meyasa ka ke kokarin hana zuciyarka
abincinta a koyaushe? Meyasa ka ke hana idanuwanka
ganin irin sadaukarwar da Ramlat ta yi maka da gangan?"
Hussein bai ce uffan ba, bai kuma katse shi ba don haka
ya ci gaba.
"Anya Hussein ka san wace ce Ramlatu?"
"Mutum."
Ya amsa kai tsaye yana murmushi gami da kallonsa.
Hisham ya harareshi.
"Eh mutum ce, amma ta bambanta da irin mutanen da ka
ke mu'amala da su."
"Rabinta aljana ce?"
Ya ƙara watsamasa tambayar da ta ƙara kai Hisham
bango.
"Kana ƙin gaskiya da gangan, amma magana ta gaskiya,
Ramlat ba irin macen da namiji zai kyale ba ce."
"Ya aka yi ta rabu da uban ƴaƴanta?"
"Wai ban taɓa faɗamaka baban yaranta rasuwa ya yi ba?"
Hisham ya tambaya da mamaki. Hussein ya girgiza kai.
"Bana jin mun taɓa hirar, idan ma mun taɓa to na manta
kam. Allah Ya yi mishi rahma."
"Amin."Hisham sai ya karkace ya hau ba shi labarin
rayuwar Ramlat tun daga farko har zuwa rasuwar mijinta a
tsakiyar filin sallar juma'a kuma cikin watan azumi.
Hussein ya yi shiru bai katse shi ba har ya kammala.
"To meyasa yanzu ba za ta auri Yallaɓai ba? Ko ba komai
zai jiyar da ita farin cikin da za ta mance dukkan ƙuncin
rayuwa."
Hisham ya ji kamar ya shaƙe shi.
"Ba wannan nake nufi ba, kai nake so ka auri Ramlat ko
don irin son da ka ke mata. Wallahi ba ta dace da kowane
namiji ba sai kai."
"Na taɓa ce maka ina sonta?" Hussein ya fadi kansa tsaye
yana murmushi, wani irin murmushi tun daga ƙasan
zuciya. Hisham ya kara jin haushi da takaicinsa.
"Dan iska kawai, sai ka zauna kar ka aure ta din!"
Yana kai wa nan ya bude motar ya fice. Hussein ya tashi
motarsa ya yi ribas har ya kusa yin sama-sama da
Hisham banda Allah Ya sa ya matsa gefe. Murmushi ya ke
yi ganin yanda Hisham din ya fusata ya na surfa bala'i. Ya
juya kan motar ya fice daga asibiti zuciyarsa kamar an
narkar da ƙanƙara.
Awanni biyu zuwa uku, sai ga shi nan ya dawo niƙi-niƙi da
kayan dubiya ya bar su a cikin motar, sai da ya shiga
masallaci ya gabatar da sallar isha'i sannan ya karasa ciki.
Aka yi sa'a masu gadin Ramlat sun yi gaba bisa umarnin
da Chairman din ya bayar. Sai kuma goben za su ƙara
dawowa.
Kwankwasawa ya yi ya shiga da sallama, gaba daya
mutanen da ke dakin suka amsa. Ya karasa shiga bai ko
kalleta ba ya durkusa suka gaisa da Hajiya. Ta amsa da
fara'arta tana kara taya shi murnar haduwa da ɗan
uwansa. AlHassan na zaune yana cin abinci kai ka rantse
dama can wani irin mugun sabo aka yi da juna. A'isha ce
abokiyar hirar, ana ta dariya. Hisham wanda ya kauda
fuska bai ko kalleshi ba. Hussein ya mike ya nufi gefen
Ramlatu, tun shigowarsa kirjinta ke harbawa da sauri-
sauri.
"Sannu, ya jikin?"
Ya fadi ƙasa-ƙasa, hirar da su AlHassan ke yi ya hana
Hisham mai kasa kunne jin gulma.
A hankali ta dube shi., fuskarta ta yi fayau.
"Alhamdulillah da sauki."
"Allah Ya ƙara lafiya."
Ta amsa da amin ta kuma yi mishi godiya. Har zai juya ta
yi magana.
"Na tayaka murna, Allah Ya kara kiyayewa."
Ya juyo kansa ya dube ta. Ta kasa gane ma'anar kallon
don haka ta kauda kai.
"Na gode sosai."
Daga haka ya koma wurin su Hajiya. Nan Hajiya ta ba
Aisha umarnin ga zuba mishi abincin. Bai yi musu ba don
dama yana jin yunwar kadan kuma ba ya son ko loma
daya na abina Zeenatu ta girka ya shiga cikinsu shi da ɗan
uwansa. Kusa da Hisham ya zauna saman kujera
maimakon gefen AlHassan wanda ke zaune saman
darduma.
"Ka gama fushin?"
Ya fadi daidai saitin kunnen Hisham yana murmushi.
Murmushin shima Hisham ya yi. Ko ba komai zuciyarsa ta
yi tas ganin bai ba shi kunya ba ya shigo. Aka zuba mishi
abinci ya soma ci.
Ramlat gaba daya fa an kasa sakewa, ita ce ta ja mayafi
ta gyara sai kuma ta ja zani. Har dai garin juye-juyenta ta
fama ciwon aikuwa ta saki ƙaramin salati.
Ya ɗago idanu ya dube ta, ita din ma shi ta kalla. Sai ta
janye da sauri tana amsa tambayar Hajiya.
"Lafiya lau Hajiya, fami nayi kaɗan."
"Sannu, ki dinga bi a hankali."
Cewar AlHassan. Ita kuwa Aisha ta mike ta nufi wurinta
tana gyaramata zaman mayafin da ta ke ta fama da shi.
"Sis, wannan irin rashin sukuni? Ko duk a dalilin Hussein
ne?"
Ta fadi murya ƙasa-ƙasa yanda Aisha din ce kadai za ta ji.
Harara ta bi ta da shi ita kuwa Aisha ta yi ƴar dariya.
KARFEN KAFA Chapter 63
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


Shi kuwa gogan abincinsa kawai yake ciki fuskarsa cike da
wani irin nishaɗi. Ya kammala ya dire farantin.
"Hajiya muna godiya."
Murmushi Hajiya ta yi don tagwayen ba karamin burge ta
suke ba.
"Yaushe ne tafiyar taku Adamawa?"
AlHassan ya amsamata.
"Gobe da zarar an shiga kotu an fito za mu wuce."
"Allah Sarki, toh Allah Ya nunamana. Sai dai zan so na ji
taƙaimaiman tarihin abinda ya faru gareku a baya."
AlHassan ya murmusa.
"Kar ki samu damuwa Hajiyarmu, in sha Allah komai za ku
ji gaba dayansa."
Ta jinjina kai.
"Allah Ya nunamana lokacin."
Aka amsa da amin. Ramlat ta yi shiru, itama abinda ta ke
son ji kenan, tana son sanin yanda har Hajiya Zeenatu ta
yi nasara akan su.
Kwankwasa kofar da aka yi gami da sallama yasa duk
suka mayar da hankali. Nos Farida ce. Suka gaisa sannan
ta miƙawa Ramlat takarda. Cikin raɗa-raɗa ta ce.
"Gashinan, Khadija ta nemi da na ba ki."
Ta karɓa da mamaki ta kuma yi godiya. Daga nan Farida
ta juya ta fice. Ta ɗago ta dubi mutan dakin wadanda ita
suke kallo. Ta maida hankali ga takardar ta warware ta
shiga karantawa.
_*Assalamu alaikum, *_
_*Ramlat ina miki fatan alheri da kuma samun lafiya. Akwai
wani lamari da nake son sanarmaki. Wata mata ta yi
barazanar hallaka ni matukar ban aiwatar da aikin da ta
sanya ni ba, wato na kashe ki. Laifi ne da har abada bana
fatan na aikata koda a kan maƙiyina ne. Ina mai ba ki
shawara akan ki nar asibitin nan da gaggawa domin idan
ma ni na kasa aiwatarwa za ta iya siye wani da kudi ya
cikamata burinta. Taku mai kaunarku, Khadija Ashir. *_
Bakin Ramlat ya shiga rawa yayinda idanunta suka cicciko
da kwalla. Tsam! Ya miƙe ya ƙaraso wurinta ba zato ta ji
an zare takardar daga hannunta. Ta dubeshi, shima ita ya
ke kallo cike da zargi kafin ya maida hankali ga takardar.
"Meyafaru ne?"
Hajiya ta nemi sani. Ya miƙawa Hisham, Hisham ya
karanta a fili. Hussein ya sa kai ya fice daga ɗakin.
Su Hajiya suka sanya salati.
"Wai wace ce wannan matar mai neman ganin bayan
Ramlatu? Oh duniya ina za ki da mu? Nikam ko maganin
asibitin nan ban yarda a ƙara kawowa ki sha ba Ramlatu."
Maganar karshe na Hajiyar sai ya ba AlHassan dariya.
"Kar ki damu Hajiyarmu, ba abinda zai sami Ramlatu da
yardar Allah. Sai dai ya kamata a bi shawarar Khadija, a
ɗauke ta daga asibitin."
"Dama ai Likitan ya fadi, yanda take samun sauki zai iya
ba mu sallama gobe ko jibi. To ai kuwa gwara a yi komai."
Can wayar Hisham ta yi ringing, Hussein ne. Hisham ya
saurari bayaninsa sai ya yi murmushi ya katse kiran.
"Ga wanda ya fi mu can ma ya tafi nema maku sallama a
darennan."
Da mamaki Aisha da AlHassan har su na haɗa baki wurin
tambayar waye?
"Hussein." Aisha ta saci kallon Ramlat tana murmushi,
itama Hajiya murmushin ta yi kawai ba ta ce komai ba.
Kamar dai da wasa, haka Hussein a daren ya yiduk cuku-
cukun da zai yi har aka ba su Ramlat sallama a daren.
Suka haɗa komatsansu, Hajiya da Ramlat a motar
Hussein, shi kuwa Hisham da madam dinsa suna tare.
Amrah wacce har ta kamo hanya, sai waya suka yi mata
suka sanarmata da batun sallama. Ita kanta ta yi mamaki.
A hankali ta ɗago kai don tun shigar ta motar kan yana a
ƙasa. Caraf suka haɗa idanu ta cikin gilashin kasancewar
AlHassan ke tuƙin wannan karon. Ta sauke kanta, shi
kuwa ya samu damar ƙarewa fuskar kallo yanda duk ta
faɗa kamar wacce ta yi cutar wata guda.
A hankali ya kauda kai, suka yi ido hudu da AlHassan da
ke satar kallonsa, murmushi AlHassan ya yi mishi shi
kuwa ya gyara zama gami da ɗan ɗaure fuska kadan yana
shan ƙamshi.
Har gida suka kai su, Ummi da su Ansar duk suka fito a
guje suna mata oyoyo, za su fada jikinta Hussein ya yi
saurin riƙo Affan wanda ya fi kowa kusantarta, ita kuwa ta
dafe hannu tana kiran wash!
"Ba kwa ganin ciwonta?"
Ya faɗi a hankali, suka fasa rungumeta su na dariya. Ya
kama hannunsu zuwa wurin mota.
"Ku zo muje"
Ramlat ta bisu da idanu kafin ta juya ta bi sahun su Hajiya
zuwa ciki. Shi kuwa Hussein ledojin dubiyar da ya loda a
boot, shi ya ciromusu ya damƙa musu.
"Oya, maza ku je a kaiwa Mami sai ta ba ku."
Affan ya hau washe baki ganin Hussein ya fiddo alewa
daga aljihu ha bude ya sanya mishi a baki. Murmushi
sosai shima ya yi mishi ya bishi da kallo har ya ɓacewa
ganinsa.
Bayan Hussein sun koma gida, Hajiya Zeenat ta tarbe su
da fara'a tana mai danne takaicin da suka ɗuramata.
Hussein ya dan sakarmata.
"Ki yi hakuri, gidan Hisham muka ci abinci ba haka na so
ba."
Ganin yanda ya fadi cike da kulawa yasa nan da nan ta ji
zuciyarta ta sake. Ko ba komai hanyar lafiya a bita da
shekara. Yanzun dai kaffa-kaffa ta ke yi kar kwaɓarta ta yi
ruwa. Da haka ya nunawa AlHassan dakinsa kafin shima
ya shige nashi dakin. Hajiya Zeenatu ta yi mamakin da ya
bari ta kwana tare da shi duk da bai yi mata kama ko
hannunta ba, asalima baya ya juya da nufin bacci yake
ji.Ta so su yi batun tafiyarsu London ammata share, har
lokacin jikinta a sanyaye yake, burinta yanzu gari ya waye
ta shiga asibitin da Ramlatun take ta ga ko ta aiwatar da
aikinta.
"Gobe in sha Allah zan yi ƴar tafiya."
Hajiya Zeenatu ta tsinci maganar Hussein wanda ta yi
zaton bacci ya ke kamar daga sama, ta mike zaune gami
da kunna fitila. Har sannan ya bata baya. Ya yi crossinh
hannaye a kirji.
"Ina za ka je kuma?"
"Adamawa." Ya furta kai tsaye gami da juyowa ya kalli
tsaka idanunta. Duk sai ta ji ta rikice, hanjin cikinta sun
kaɗa. Ta haɗiyi miyau, Hussein zai je Adamawa?
Hannunta ya ɗan riƙe ba don ya so ba.
"Ya naga duk kin sauya? Ba kya son na je na ga ƴan
uwana?"
Ta yi murmushin yaƙe.
"Ko kusa aa, amma na ji haushi da ba ka shirya tafiya da
ni ba, da ace ka yi niyyar muje tare za ka sanar da ni akan
lokaci."
Ya yi ɗan murmushi.
'Makira.' Ya furta can ƙasan ransa. A fili kuwa ya shafi
gefen fuskarta.
"Ki yi hakuri, bansan yanda za su kalli lamarin aurenmu ba.
Gwara naje na yi musu bayanin komai a tsanake cewa
auren soyayya muka yi. Kinga hakan zai fi armashi."
Ta ji wani sanyi kamar kankara, tana so ta yi shakku akan
zancensa sai dai kuma ta kasa. Ta shiga gasƙata dukkan
kalamansa. Hussein ya ci gaba da yi mata daɗin baki har
sai da ta gasƙata da kanta cewar dagasken Hussein sonta
ya ke yi ba wasa a ciki. Da wannan ta ji salama amma duk
da haka tana tsoron a hana shi dawowa.
"Za ka dawo garinnan kuwa?"
Ya yi murmushi ya lumshe idanu.
"Wa zan bar wa ke?"
Ya fadi ba da manufa biyu, ta ji wani sanyi har sai da ta
dara cike da shauƙi. Da wannan suka kwanta bacci.
***
ƘARSHEN ALEWA..!
A ranar Talata sha biyu ga watan Maris, kotu ta yankewa
Halima da Gwaska hukuncin shekaru goma zuwa sha biyar
a gidan yari a dalilin yunkurin kisan kai.
Halima ta yi kukan nadama sosai, karshe ta nemi alfarma
wurin ƙaninta akan ya je ya nemar mata gafarar Ramlatu.
Yusufa na hawaye haka suka rabu da Yayarsa aka tsitsa
ƙeyarta suka bar kotun.
A can gida, Ramlat ta ji labarin komai a waya daga
Hisham, kuka sosai ta yi na tausayin Halima. Haka ta
dinga samun kira daga tsofaffin abokan aikinta na
ma'aikatar Revenue, da yawansu sai yanzu suka san
dalilin kamen da aka yiwa Halima. Sun jajantawa Ramlat
gami da yin Allah wadai da son abin duniya irin na Halima
wanda ya kai ta ya baro.
"Ai godiya za ki yiwa Allah don yau kam duka ranarki ce.
Ga shi dai an yankewa wadanda suka zalunceki hukunci,
ga Kawunki Jamuli ya karɓi kuɗi, ya kuma tabbatarmin da
kansa yau ba gobe ba, zai damƙawa Chairman kayansa. A
yi ta ta ƙare. Ke kuma ya ce idan kima kara warwarewa ki
je yana son ganinki.
Maimakon farin ciki sai ya ci gaba da hawaye jin kalaman
Hajiya, dama tun safe ta karbi Atm card din kuma ta fice
tare da Munir. Uwa daban ta ke, ita ta tsaya tsayin daka
tare da Hajja wurin karɓar mata ƴanci.
Sallamarsu ce ta katse dukkan tunaninta. Suka dube su.
Shaddar ba iri guda ba ce, sai dai kowannensu fari ƙal ya
sanya. AlHassan da hula a kansa, yayinda gogan ya fidda
nashi a mota, sai sumarsa kwance. Hajiya tun shigowarsu
take murmushi da yi musu adduar neman tsari da kariya a
ƙasan ranta.
Ita kuwa tun da ta kalle su ta sunkuyar da kai cikin sanyin
jiki. Suka karaso suka durkusa suka gaida Hajiya ta amsa
fuska a sake. Suka yi mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login