Showing 6001 words to 9000 words out of 113545 words
Chapter 3 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
a wajen
yana ta mata kirarin da ba ta ma fahimta don a hargitse ta
ke.
***
Ga Ramlat kuwa, kasa sanarwa Hajiyarta ta yi akan abinda
ya faru a wurin aikinsu ta yi, ta dai sanarmata dalilin kiran
da Hisham ke mata.
"Toh kinga wannan ma kadai ya isa ki yiwa kanki faɗa ba
ruwanki da shiga harkarta ballantana har ta kaiku da
samun matsala. Àllah Ya rufa asiri dai."
Daga haka suka rufe zancen.
***
Hussein ya yi shiru ya kuma baza kunne yana sauraron
Hisham har ya kai aya, fuskarsa kadai ka kalla za ka ga
damuwa da ɓacin rai kwance.
"Kenan duk abinda nace ba ta ji ba?" Fadin Hussein a
kausashe.
"Ramlat ko wa?"
Hisham ya nemi sani. Girgiza kai kawai Hussein ya yi kafin
yace.
"Ka bata hakuri, ka kuma..."
"A'a Malam, wallahi na gaji. Nima fa ina da aikina ba
masinja ba ne. Haka kawai sai a takuran da kaiwa da
kawowa wurin faɗar saƙo. Toh na gaji fa, ana cin
lokacinmu nisa Princess. Haba, aure ko wata ba'a yi ba an
ban sabon aiki?"
Harɗe hannu Hussein ya yi a kirji yana dubansa fuska
dauke da murmushi, ya maida idanunsa sararin samaniya
yana ganin yanda ake zuba walkiya da kuma iska. Ba ta
"Give me her digits."
Ba Hisham ba da mamaki ya kusan kaiwa ƙasan gwuiwa,
hatta shi ɗin da ya nemi lambar sai da ya ji faɗuwar gaba,
ya nemi tsoro da fargabar abinda hakan zai haifar ya rasa,
ji yake kamar akwai abinda ke danneshi.
"What did you say?" Hisham ya faɗi kusan a birkice.
Maimakon ya amsa sai ya fiddo wayar ya ajiye saman
mota ya bude murfin zaman direba ya shiga ya soma
kokarin tayarwa. Ganin haka Hisham ya dauki wayar bayan
ya fiddo tasa wayar, hannunsa har rawa yake yana mai jin
wani farin ciki, fatansa yake so ya tabbata. Lambar Ramlat
na Mtn da Airtel duka sai da ya ɗuramasa, kowanne ya
ɗan danna kira amma sai ya kashe bai bari ya shiga ba,
so yake dai lambobin su fada cikin Log.
Ta cikin gilas ya miƙa masa wayar.
"Shegen sama, gashinan ba ruwana kuma idan Hajiya ta
gani, wallahi kar ma ka ambaci sunana. Ban yi saving ba,
idan ka ga dama ka sanya Rabe a kan sunan ko Talle Mai
Wanki."
Dariya sosai Hisham ya ba shi, suka hau yi can kuma ya
ɗan lumshe ido ya bude.
"Zan rama ɗaya bayan ɗaya wallahi, ka yimin duk abinda
ka ga dama yanzu. Sannan ni ba da wata manufa ma
nemi lambar ba kar ka yi zaton akwai wata bayan Zeenat,
wai don na ragemaka zirga-zirgar ce. That's it."
Hisham dai dariya ya yi bai ce uffan ba. Suka yi sallama
ya ja motar ya nufi Rijiyar Zaki.
***
Washegari direba ta sanya ya kai yara makaranta, ko
bakomai tana son yin baccin safe kadan sannan ta yi
shirin Ofis. Ga garin ya yi luf sakamakon ruwan da aka
samu a daren jiya. Wannan ne ya bata damar komawa
bacci mai dadi bayan tafiyarsu. Ba ita ta farka ba sai da
wayarta ta Soma ringing.
Duk yanda ta kai ta share hakan ya gagara don mai kiran
bai yi ɗaya ya haƙura ba. Da wani irin takaici ta mike ta ja
tsaki kafin ta duba sunan dake yawo sama screen. Hilal.
Ɗagawa ta yi da sallama.
"Ayya na tasheki a bacci kenan. Shikenan ma yi magana
anjima. A yi bacci lafiya."
Bai jira cewarta ba ya katse kiran, murmushi ta ɗan yi ta
kara maida kanta cike da kasala. Wayar dai ta ƙara ringing,
a dolenta ta miƙe zaune. Lambar Salisu na ofishinsu ke
yawo saman screen. Ta ɗaga da sauri.
"Ramlat, kina ina ne?"
"Haba Yallaɓai, ba sallama ba komai?"
Ƴar dariya ya yi sannan ya yi sallamar suka gaisa, ya ɗora.
"Kiyi hakuri, abin ne naga gwara na sanar da ke shiyasa
shaf na mance da wannan batun."
Cikin rashin nutsuwa ta zuro kafafunta ƙasa.
"Lafiya Salisu?"
"Ji nayi Oga Ɗalhatu na maganar an miki sauyin wurin aiki,
za ki koma ɓangaren Chairman, a matsayin secretary
ɗinsa."
Kirjinta ya bada dam! Koda ace ranta a ɓace yake jiya, ba
ta mance irin shu'umin kallon da Chairman Aliyu Dikko ke
watsamata ba. Ba ta son ta munana zato game da abinda
ba ta da tabbacinsa kamar yanda take ganin baƙin jama'ar
ma'aikatar da ke gulmar Chairman din da cewa ɗan iska
ne. Don haka sai ta kyautata zato.
"Ko kina da masaniya ne Ramlat? Naji ba ki ce komai ba?"
Dan murmushi mai sauti ta yi.
"Banda ka faɗi bani da labari Salisu. Yanzu ai zan shigo
ofishin In sha Allah. Sai na ƙaraso."
Daga haka suka yi sallama, shiru ta yi na ɗan lokaci, so
take ta gani ko za ta iya fahimtar manufar yin hakan, sai
dai duk iyakar tunaninta ba ta gane komai ba. Tasan dai
ko mene ba alheri ba ne tunda mutumin Hajiya ne.
Miƙewa ta yi ta shiga wanka, a gaggauce ta shirya cikin
doguwar rigarta na Atamfa, mai kawai ta shafa kafin ta
zura hijabinta dogo ta dauki duk abinda take ɓukata ta
fito. Sai a sannan ta tarar da missedcalls har uku duk
daga mutanen Department dinsu ne. Ba wanda ta bi, ta
karasa ta gaida Hajiya dake zaune suna hira da Ladidi.
"Yau dai babu niyya. Daga jin sanyin gari kin shantake."
Dariya ta ɗan yi.
"Wane sanyi? Ai da saura ruwan Hajiyarmu. Bai kankama
ba tukunna!"
"Allah Ya bamu damina mai albarka dai." Fadin Hajiya,
suka amsa. Ta gaidata karo na biyu kafin ta dubi Ladidi su
gaisa sannan ta karya a gaggauce ta fita. Ba ta iya ta
sanarwa Hajiya sauyin da aka yi mata ba, bar wa cikinta ta
yi har sai ta je ta ji asalin abinda ke wakana.
***
AKWAI WATA A ƘASA!.
KARFEN KAFA Chapter 43
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Gaban Notice Board ta soma tsayawa, shakka babu
dagaske Salisu yake, ajiyar zuciya ta sauke bayan
kammala karanta bayanin sauyin da ta samu. Sati mai
zuwa za ta fara sabon duty dinta.
"Allah Yasa hakan ya fi alheri." Ta fadi a fili sannan ta
karasa cikin ofis dinsu wanda kiris ya rage ta bar shi.
Bayan sun gaisa ta zauna.
"Za dai mu yi kewarki anan Ramlat, ko ba komai kin fi
wasu a nan."
Fadin Oga Ɗalhatu, aka ɗan dara idan ka cire Halima da
hassada da bakin ciki ya cikamata zuciya, yanda ta ke jin
tsanar Ramlat a yanzun har ya fi na baya. Ta jima tana
burin kasancewar mai aiki a ƙarƙashin Chairman duk kuwa
da cewa hakan bai rage ko ƙara albashinta ba, amma dai
tasan alhairan da ita za ta kwantar da kai ta samu wurin
Chairman, ba lallai ne ita Ramlat ta yi ba.
"Ki dai bi sannu don kinsan ko waye shi."
Cewar Halima tana yamutse fuska.
"Kedai ba ruwanki, zato zunubi. Kuma kin fi kowa sanin
Ramlat da halayyarta." Fadin Zuhra kenan.
Ramlat kallonta kawai ta yi ba tare da ta tanka ba, tsaf ta
gama gane wacece Halima da kuma irin takun saƙar da
take yi da ita wanda ita kam ba ta ga dalilinsa ba.
Da wannan damuwar ta dawo gida ta sanar da Hajiya
halin da ake ciki.
"Toh ke meye naki na damuwa? Sauyi ne fa kawai, idan
batun kamun kai ne ai na yarda da ke bana jinki a wannan
ɓangaren. Allah Yasa hakan ya zamemaki alheri."
Ta amsa da amin.
Bayan Magriba suna zaune tana koyawa yaranta
Homework, Maigadi ya yi sallama a bakin ƙofar suka
amsa. Jin saƙon wai ana sallama da Ramlat ya ba ta
mamaki, ta dubi Hajiya, itama kallonta take tana
murmushi.
"Ka ce tana zuwa."
Bayan tafiyarsa ta dubi Hajiya.
"Haba Hajiya, mutum da bansan ko waye ba, yanzun ai
ba'a irin haka, da ace ya san ni toh ba zai rasa lambar
wayata ba. Ta nan zai neme ni."
Harararta Hajiya ta yi.
"Kuma ya zama dole ki fita ba, naga alamar kin fi kaunar
zama a haka babu aure, toh ya isa. Nima kamar Babanki
Dakta, ba zan ƙara biyemaki ki kori masu zuwa wajenki
ba. Idan ma a baya an yi bai wuce na tausayawa
marayunnan ba. Tashi maza ki je."
Kamar ta yi kuka ta ce.
"To wa zai ƙarasa koyamusu?"
"Jeki, nasan duk daɗewa ba za ki wuce awa ɗaya ba. In
Sha Allahu ma ba su kai ga yin bacci ba. Tunda kin sallami
Affan ai da sauƙi."
Miƙewa ta yi ranta duk ba dadi, hijabi kawai ta zura ta
kama hanya su Ummi na kiran a dawo lafiya, a tahomusu
da alawa. Harara kawai ta watsamusu ta yi gaba ta bar
Hajiya da dariya.
Sai dai me? Wanda ta gani ya matuƙar shayar da ita
mamaki, sakin baki ta yi kafin kuma su yi dariya a tare.
"Kai Yaya Hilal, yaushe ka zama baƙo a gidannan? Kuma
fa ko Malam Bala bai fadamana wanda ke sallamar ba."
Dariya ya yi. Sanye yake cikin shaddarsa ruwan toka, ya
karya hularnan ta zannah Bukar ta zauna caras a kansa.
Yana daga cikin mota zaune a inda ya fiddo ƙafarsa ɗaya
waje.
"Ke din ce sai da hakan, farko na so kiran wayarki sai
kuma na fasa tunda nasan dai zai wahala ace a wannan
lokacin ba kya gida. Malam Bala kuma ni na roƙeshi akan
kar ya ce ni ne saboda yau zuwan naki ne ke ɗaya."
Ta ɗan sadda kai ta yi shiru, ta san tatsuniyar gizo ba ta
wuce na ƙoƙi. Abu ne da ba ta jin har abada za ta iya
aminta da shi.
"Ɗan zagayo mana ki zauna."
Ba tare da musu ba ta zagaya ta bude motar ta shiga,
kamar yanda ya bar ƙofa a buɗe, itama hakan ta yi.
Gaidashi ta soma tare da tambayar iyali da wajen
iyayensa. Ya amsa mata cike da annashuwa.
"Kin ɓuya da yawa, ta ko'ina gujemin kike kamar rai da
ajali. Na rasa hanyar ɓullomaki. Sai na kiraki ki share ki ƙi
ɗauka, daga baya na samu text dinki wai ba kya kusa ne
nayi hakuri. Anya kuwa?"
Kunya ta kamata, ashe dai ya gane. Ita kuwa dalilinta na
yin hakan a ganinta mai ƙarfi ne. Kokarin nesanta kanta
da shi ta ke yi ta kowace hanya don ba ta son jawowa
kanta magana.
"Ka yi hakuri."
"Na yi, amma ba duka ba. Ramlat, Maman Ummi, Ansar
da Affan. A karo na biyu ga Hilal nan, bai kuma zo da
niyyar yaudara ba. Aure ne ya kawoshi idan har kin
amince."
Ajiyar zuciya ta saki don dama ta san maganar kenan,
jikinta ya yi sanyi da irin wannan soyayyar ta Hilal gareta.
Ta dubeshi, shi dinma ita yake kallo babu ƙaƙƙautawa.
Ɗan kauda idanunta ta yi.
"Ko da can ma ba ka zo min da niyyar yaudara ba balle
kuma yanzu. Asalima ni ce na yaudareka. Ka yi hakuri
Yaya Hilal. Don Allah ka yi hakuri."
Ta ƙarashe a raunane, ita sam ba ta san ta
"Ka yi hakuri."
"Ba hakuri za ki bani ba, dalilinki na guduna za ki faɗamin.
Idan da wajen da na kuskuro na gyara."
Girgiza kai ta shiga yi, kwalla ta soma ciccikomata idanu.
Hilal wane irin mutum ne mai matukar sanyi da hakuri?
Wace irin soyayya yake mata da ya kasa ganin laifinta?
"Akwai abubuwa da dama da ya kyautu na gujeka
dominsu. Ba ka taɓa yimin laifi ba, ba zan iya kallon
danginka a karo na biyu ba a matsayin matarka. Bayan
abinda ya faru wa kake tunanin zai ƙara kallon Ramlat
matsayin matar kirki? Wallahi da kaina na faɗa, bani da
kirki, ban yi halin hakuri da dattako na iyayenmu ba. Ka yi
hakuri Hilal, mu ƙaddara ba'a rubuto aure tsaka.."
Ta kasa ƙarasawa saboda kunya da kuma irin hararar da
ya watsamata. Can kuma ya numfasa ya runtse ido. Da
ace ta san yanda yake jinta a rai da ba ta ce haka ba, a
gefe guda kuma bai mance irin kalaman da iyayensa suka
yi gareshi ba muddin ya ce zai aureta ko bayan ransu ne.
Kansa ya yi zafi da yawa.
"Ka yi hakuri."
Ta kara nanatawa, a wannan lokacin tuni hawayen sun
zubo. Ya bude idanunsa da suka kaɗa ya dubeta.
"Bana jin har abada zan manta da ke Ramlat, you are my
first love. Ki daina bani hakuri, da ace zan iya da tuni na
rarrashi zuciyata. Aurenki da Aliyu na dauki hakan
matsayin rubutaccen al'amari wanda ba makawa sai ya
faru. Albarkar auren gashinan mun gani (yana nufin
yaranta), don haka ni wallahi tuni na yafe abinda kika yi
gareni. Idan da naki a sannan, nima ai akwai nawa tunda
ni na naace akan sai na aurekin ko ba so. Kar ki saurin
yanke hukunci a kanmu, na baki nan zuwa sati kiyi tunani
mai kyau, koda ba ki kirani ba, da zarar lokaci ya cika zan
kawo kaina."
'Allah Sarki.' Ta furta a ƙasan ranta. Da wannan suka rabu
ya bata kayan maƙulashe na alawa da biskit da ya siyowa
yara. Ta karɓa gami da godiya suka yi sallama ta shige
ciki.
Hajiya zaune a falo ta a gyangyaɗi kaɗan-kaɗan, yaran
sun ƙurawa talabijin idanu su na kallon Angrybird.
"Waye ne ya zo?"
"Yaya Hilal ne."
Hajiya ta mike zaune.
"Yaronnan dai dagaske ya ke yi."
Ramlat ta zauna jikinta a sanyaye.
"Na rasa ya zan yi Hajiya, ya dage aurena ya ke son yi. Na
rasa hanyar ɓullomasa ya fahimci illolin da hakan zasu
haifarmin a danginsa da wurin matarsa."
"Nima bana goyon bayan aurenki da shi, sai dai bamu san
abinda Allah Ya ɓoye ba tunda har ya kasa hakuri ya dawo
karo na biyu. Shawara ki dage da addu'ar neman zaɓin
Allah, duk abinda Ya yi mai kyau ne."
Jinjina kai ta yi cike da gamsuwa.
***
A kwana a tashi ba wuya a wurin Mai Rahma, bikin Munir
ya taho. Ana gobe za'a yi ɗaurin aure ƙalilan daga
mutanen Daura suka iso don Hajiya ba ta yi gayyata ba
duba da cewar ba'a jima da bikin A'isha ba.
An daura aure lafiya, a daren aka yi shirin tafiya
dinnerparty. Ramlat da yayyunta mata har A'isha da
Amrah wacce basu daukarta bare cikinsu, ankonsu iri
daya na wani leshi peach colour. Kowannensu riga da skirt
ya zauna ɗas a jikinsa.
Motarta daga ita sai Amrah don Yaya Munir ya ce babu
yara. Suna tafe suna hira, anan take ba ta labarin sauyin
da aka yi mata wurin aiki, ta kara da fadin.
"Tsorona daya, rashin sanin taƙamaiman manufar wannan
Chairman ɗin. Ina tsoron ya kasance wani mugun abin ne."
Amrah tana taunar cingam din da ya zamemata ciki tun
tana laulayi har a yanzun da cikinta ya shiga watansa uku.
"Kar wannan ya dameki, ai kinsan kanki. Daidai
gwargwado kin san mutuncin kanki kina kuma karewa.
Addu'a za ki yi ta yi akan Allah Ya kareki daga sharrinsa.
Ba abinda zai faru amma shakka babu dai akwai wata a
ƙasa!"
Jinjina kai Ramlat ta yi.
"Wallahi ko ba ki faɗa ba Amrah, ni ban taɓa ganin mace
mai irin kishin na wannan matar ba."
Amrah ta ɗan muskuta.
"Af, kin ce za ki nunamin hotonsa."
Ta yi murmushi.
"Mu ƙarasa tukunna."
Daga nan suka faɗa wata hirar ta daban har ta ke
sanarmata da kiran da Baba Dakta ya yi mata. Amrah
banda dariya da hamdala ba abinda ta ke yi.
Wurin ya cika sosai, mafi yawa dangin Amarya Hunainah
ne.
"Ke me ya kawo waccan wurin nan?"
Cewar Amrah tana kallon Salma kanwar Bilkisu.
Idanun Ramlat ya kai gare ta. Taɓe baki ta yi.
"Au ke duk hirar da su Maman Twins suke yi ba ki ji ba?
Cewa fa aka yi itama Bilkin za ta zo. Ita gwanar kissa."
Suka yi dariya suka karasa ciki basu kara kallonta ba.
Salma ta bisu da harara ta ja dogon tsaki gami da fadin
"Munafukan banza!"
Koda sun ji basu tanka ba.
Sai da suka samu wuri suka zauna kafin Ramlat ta fiddo
wayarta ta lalubo hoton ƴan biyun da ta dauka ta miƙa wa
Amrah. Sakin baki da hanci ta yi tana kallonsu.
"Wow! Ke wai Twins ne? Toh ai banda gilashin da ke
idanun daya, ba za ka ganesu ba. Lallai wallahi ban ga
laifinta ba, dole ta yi kishi. Amma kika ce babba ce?"
Amrah ta ƙarashe fuskarta ɗauke da tsantsar mamaki.
Dariya ta ba Ramlat.
"Dattijuwa ma kuwa don idan ma ba ta yi sa'ar Hajiyarmu
ba, kadan ya yi mata saura ta yi. Ke kin gani kinsan wuff
ta yi da shi."
Suka yi dariya can kuma Amrah cike da tausayawa ta ce.
"Wallahi nidai sai naga kamar ba banza ta bar shi ba.
Wannan kyakkyawa ya tsaya a auren sa'ar uwarsa?
Gaskiya jikina na bani akwai wata a ƙasa Ramlat."
Ramlat ta gyara zama don ta sosamata inda ke mata
ƙaiƙaiyi.
"Ke kenan da ba ki ma ga matar ba. Ni banda duka
wannan kinsan cikin biyunnan na hoto ba wanda ban hadu
da shi ba?"
"Me kike nufi?" Amrah ta tambaya da rashin fahimta.
Ramlat ta bata labarin kaf haɗuwarta da Mutumin Mall
(AlHassan) da kuma Hussein da ma yanda aka yi ta ga
hotonnan.
"Tun ganin bayanin da ya rubuta kasan hoton na kara
tabbatar da zargina. A farko da na ganshi a shago na gane
ƴan biyu ne, tunanina sai ya ba ni ko su na tare ne da ya
zo Kanon jin daga baya ya ce shi Adamawa su ke.
Wannan ne ya kara sanyawa na dasa alamar tambaya ga
lamarinnan. Mai yiwuwa su na nemansa ne basu san ma
inda ya ke ba, mai yiwuwa kuwa mallakeshi Hajiyarnan ta
yi sun san inda ya ke amma ya ƙi sauraronsu."
.
"A'a haba dai, me kika ce ya rubuta? Allah Ya
bayyanamusu shi, kinga kuwa basu da masaniyar a inda
yake rayuwa ma kenan. Gaskiya Ramlat babban jihadi za
ki yi idan har kika zama silar saduwarsa da ƴan uwansa."
Jinjina kai Ramlat ta yi zuciyarta cike da tsantsar tausayin
Hussein da AlHassan.
"Ina fatan na yi hakan Amrah, sai dai abu ɗaya, ina tsoron
na ɗauki matakin da zai sa ya bar gari a rasa inda ya
shiga. Ma'ana, idan kai tsaye na cewa shi Abban Fatima
cewa nasan inda ɗan uwansa ya ke, idan ya zo ya ganshi
shi kuma ya ƙara sauya garin da za'a rasa ina ya ke, kinga
anan an yi ba'a yi ba, wannan ne dalilin da yasa zan fi
kaunar na soma sanin meke faruwa ko ya ya ne daga shi
na Kanon kafin a san abin yi. Wallahi tun sadda na ga
wannan hoton, Hussein ya shiga cikin jerin mutanen da
nake tayawa da addu'a. Tausayi ya ke ban, na kuma rasa
dalilin da yasa nake yawan tunanin lamarinsa."
Wani murmushi Amrah ta yi gami da dafa hannunta.
"Tunda kika ga haka, babban alheri ne haɗuwarki da
wadannan bayin Allahn. Ɗari bisa ɗari na goyi bayanki, ko
yaya ki samu ki soma tunkarar Hussein, sai dai ki sani,
idan har bai saba da ke ba, ba lallai ne ya ba ki damar da
za ki san wani abu dangane da shi ba. Ki nemi yardarsa
kafin ki nemi ko menene. Abu na biyu ki yi takatsantsan da
duk abinda zai sa matarsa ta ƙara ganinki tare da mijinta.
Na uku kuma wanda shi ne ma ya kasance na farkon fari,
ki haɗa da addu'a sosai, nima zan tayaki. Allah Yasa ta
dalilinki wannan bawa ya sadu da ɗan uwansa."
Murmushi sosai Ramlat ke yi har dimple dinta na fitowa
raɗau.
"Amin amin."
Ta amsa cike da jin dadi da kuma farin cikin samun
Aminiya kuma ƴar uwa ta gari.
Washegari aka kai Hunainah ɗakinta, Ramlat ba ta je ba
don ta san za ta hadu da dangin Hilal sosai a bangaren
Bilkisu. Ta dai ji irin salon Bilkisu wacce ba ta nuna komai
ba asalima nunawa ta yi ta karɓi Hunainah da hannu
bibbiyu za kuma su zauna da juna bisa amana. Da wannan
dangin Hunainah suka miƙata ɗakinta wasu na yabon
hakurin da Bilkisu ta yi yayinda wasu ke fadin ai ta ciki na
ciki.
***
Ranar Litinin ta soma aiki a matsayin sakatariyar
Chairman. Tana zaune a inda aka tanadar