Showing 111001 words to 113545 words out of 113545 words
Chapter 38 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
sun je, ba abinda za su iya yi mata sai addu'ar.
***
Ramlat suna zuwa ko awa ɗaya cikakka ba ta yi ba ta
haifo ɗanta namiji, sai dai kafin Nos ta yi wani yunƙurin,
wata naƙudar ta kara zuwar ma Ramlatu, da mamaki
Metron da Nos suka ƙara yin kan Ramlat, wannan karon
sai da aka haɗamata da ruwan naƙuda, ba karamin
galabaita ta yi ba, Hussein kamar kansa zai tarwatse yana
daga waje, ga kukan jariri yana ji kuma ana fadin ai ba ta
kammala ba. Ga murna ga kuma tashin hankali da
tausayin matarsa. Kalmar mutuwar da ta ambata har
yanzu ba ta sakeshi ba, fargaba sosai ya ke ciki duk kuwa
da ya sani mutuwar ba a baki ta ke ba.
Kukan jaririn da ya kara ji, sai ya rude, ya rasa na farkon
ne ko na biyun, kawai sai ya cusa kai ba tare da neman
izni ba. Aikuwa wata jaririyar ce aka kara cirowa Ramlat.
Ita kuwa ta lumshe ido sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke
yi.
Dole ya fita yana murna, kafin a kammala gyarasu ya
shiga laluben waya don ya sanarwa Dada da ɗan uwansa
sai dai wayam. Hakanan ya hakura ya dinga murna da
farin cikinsa shi ɗaya. Gaba daya jariran aka kawomasa,
Metron na fadin sai fa ya ba ta goron albishir, dariya ya yi
yana ɗaukarsu.
"Ki biyoni bashi."
Itama dariyar ta yi ta miƙa masa tana fatan Allah Ya
rayamasa.
Kammanin Dada sak ko kuma yace kamanninsa yake
hangowa a fuskar yaran wadanda suma ke cike a kansu a
saman fuskarsu.
Sumbatar kowannensu ya yi yana mai jin taruwar kwalla a
idanunsa, ashe dai wataran mafarkinsa zai tabbata, zai ga
gudan jininsa? Ya soma yiwa namijin huɗuba a kunne
kafin ya juya ga macen.
Daga nan kuma ya yi zamansa yana ƙaremusu kallo, haka
har aka soma kiraye-kirayen Assalatu. Aka ba shi umarnin
ganin Ramlat, ya shiga ciki. Ta zubamusu do tana
kallonsu cike da kauna, yana karasowa ta yi murmushi.
"Alhamdulillah." Ta furta, ya ajiye yaran a gefe kusa da ita
ya sumbaci goshinta shima ya na hamdalar. Dakyar ya
samu ya wuce masallaci. Ana idar da sallah ba jimawa sai
ga AlHassan tare da su Dada.
Kowa ya ga ƴan biyunnan sai ya hau murna. Dada har da
hawayenta tunawa da ta yi da Yayanta kuma ɗan uwanta
Aminu.
Ranar dai Ramlatu ta sha baƙi dakyar aka fice aka bar ta
ita kadai ta samu bacci mai nauyi ya fisgeta. Jariran kuwa
su na hannu, wannan ya dauka wannan ya dauka har sai
da Hussein ya yi ta maza ya ce ya isa hakanan su ma a
bar su su huta. Duk shaƙiyancin da ake mishi ko a jikinsa.
Ya shimfidesu a kusa da uwar ya tsaya ya kuramusu idanu
yana kallo. Ya kalli Ramlatun ya kallesu. Tausayinta ya
kamashi, ba karamar wuya ta ci ba. A karshe dai ya fice
ya bar su. Sai da Dada ta lallaɓashi kafin ya koma gida ya
yi wanka ya sanya suturar arziki ya kuma biya shago ya
siyo kayan jarirai na mace don kusan rabin siyayyar duk na
namiji suka yi jin abinda scanning ya bayar.
KARFEN KAFA Chapter 80 Last
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
End! End!! End!!!
002
Kwanan Ramlatu biyu aka sallameta, sashin Dada ta koma
inda Baba Mariya ke wanketa tas ita kuwa Dada ke wanke
jarirai.
Hussein ko yana ofis ba ya rabo da waya. Ranar suna aka
sanyawa yara suna Amina da Aminu, farin cikin Dada ba
ya misaltuwa. Daidai da iyalan Kawu sai da suka zo suna
wannan karon har da Umma matar Baba Dakta, Hajiya ma
ta so zuwa sai dai makarantar yara ta sanya dole ta
hakura amma itama kam zuwa lokacin kewar diyarta take
ji. Abinda ya yiwa Ramlatu dadi bai wuce na zuwan
Muhibbat ba. Sosai ta yaba da wannan karar da ta yi mata,
abin mamaki kuma har saƙo ta samu na kayan jarirai daga
iyayen Hilal, matar Hilal ta kira ta mata barka ta kuma yi
mata fatan alheri. Koda ta ke ba su Rafee'ah da suka zo
suna labarin wayar, dariya suka yi.
"Ai ke yanzu wacce da kika sani a baya yanzu ba ita ba ce,
ko ma dai mene ai yanzu dole ta sauko tunda aure zai
ƙara kuma yanzu ko ba komai ta ga kin auri wanda ya
shanye mijinta a komai da komai na rayuwa.
Jinjina kai kawai ta yi tana murmushi a ƙasan ranta tana
mai hamdala da Ubangiji.
***
Rayuwa sosai ta ke yiwa Ramlat da mijinta dadi, zuwa
lokacin gininsa da yake ya kammala sai fenti da ake yi da
kuma zuba furnitures da ya yi saura. A wannan lokacin ne
kuma ba zato ya yi mata albishir da kai ziyara Kano. Dama
tun sadda ta yi kwanaki arba'in ta ke saka rai da hakan, ya
nuna ba yanzun ba. Har faɗa suka yi ta gama fushin ta
haƙura ta sauko. Haka ta dinga shirya tsaraba, Dada ma ta
haɗamata da nata.
Hajiya ba karamin farin ciki ta yi ba, abincin da Ramlatun
ta fi kauna shi ta girka mata, hakanan Umma itama ta
aikomata girki. Su Ummi kamar su haɗiye ƴan biyu
wadanda suka dauko hasken mahaifinsu kamar ka latsa
jini ya fito. Duk ganin da Ramlat ke yiwa Ummi tana da
gashi sadda tana ƙarama ashe ba komai bane idan aka
haɗa da na Meena. Kamar yanda suke kiran Amina don
Dada sam ta hana a ɓoye suna.
Hisham kuwa koda ya ga amininsa sai ya hau dariya da
zolayarsa ganin yanda ya ajiye naman wuya ya ƙara zama
wani fresh. Har gidan su Hisham din ya je ya gaida
mahaifiyarsa kafin ya koma masauki.
Washegari ya juya Adamawa ya bar Ramlat, sati biyu
kawai ya ba ta hakanan ta hakura don a son ranta ne ta yi
wata guda cif. Ai kuwa a sati biyun ta zage yan uwa da
abokan arziki, koda ta je gidan Yaya Munir ta kara shan
mamakin zamantakewar matansa wadanda tuni ya haɗe
su gida daya. Salma kanwar Bilkisu ita kanta ta sauya ta yi
sanyi. Anan suka hadu ta dinga ba ta hakurin abinda ya
faru a baya, banda murmushi ba ahinda Ramlatun ta yi
don har ga Allah ita kam yanzu dukkan kunci ko bakin
cikin da ta shaƙa a baya ta bar sanya damuwarsa a rai sai
dai ta tuno ta auna da yanzu ta godewa Allah.
Ana jibi zasu tafi ne ta fita tare da Amrah, daga gidan
Muhibbat suke kafin su karasa wani katafaren shago don
nemawa Kausar wani man jiki da ta addabeta a kansa.
Dama daga Kano ake aikamata, wacce kuma ta ke siya
wajenta, nata ya ƙare.
Sai da suka fito Amrah na kara yi mata bayanin wani
maganin mata da ta ba ta, ba zato ta ji an kirayi sunanta.
Juyawa suka yi a tare ita da Amrah, mamaki ya kama su
ganin Chairman da wasu ƴan matan yara da zasu kai
shekaru goma sha biyu zuwa goma, bayan yaran sun
gaishesu ya basu umarnin shiga shagon kafin ya zo. Ya
juyo ga su Ramlat, suka gaidashi fuska ba walwala. Sai da
ya soma da neman gafarar Ramlatun kafin ya dora.
"Kina da labarin rasuwar Hajiya Zeenatu ko?"
Kusan a firgice ita da Amrah suka ce.
"Hajiya Zeenatu?!"
Ya jinjina kai da mamakin rashin saninsu.
"Ta rasu yau wata hudu kenan, tun dai iftila'in gobara da
ya afkawa shagonta ta samu matsalar shanyewar ɓarin
jiki. Haka dai a sanadin jinya komai nata ya ƙare. Sau
ɗaya naje duba ta na kuma bada tallafin kuɗi domin a yi
mata abinda ya dace. Na isketa cikin mawuyacin halin da
har babu wani ko wata da ke tsaye a kanta domin jinya.
Nima saƙo ta bayar ta hanyar Ƙawarta Hajiya Batool akan
a faɗamin. Ta bar min wasiyya akan duk sadda na haɗu
da ke ko Hussein na nemamata gafararku. Ita kanta yanzu
Hajiya Batool din kokawa take da tata lafiyar, ciwon
Kansar Gaba take fama da shi. Abin dai babu dadi don
yanzu haka ɗanta ma ba ya ƙasar, ya juya da iyalinsa
ƙasar waje."
Chairman na kaiwa nan ya girgiza kai, kansa a ƙasa kafin
ya ɗago ya dubi su Ramlat wadanda tsoron Allah ya kuma
mamayesu. Wai Hajiya Zeenatu ta mutu. Lallai Allah abin
tsoro.
"Ki yafemin nima Ramlatu, ko aurenki da na je nema
banda soyayya har da sa hannun Hajiya Zeenatu."
Ya basu labarin komai, take Ramlat ta ce ta yafemishi,
aka rabu suka wuce shi kuma ya shige ciki.
"Allah Kenan! Kin ji yanda jikina ya yi sani Ramlat?"
Amrah ke zancen tana matsar kwallar tunanin rayuwa,
shakka babu DAN ADAM ba a bakin komai yake ba.
Ramlat ta sa hannu ta share nata hawayen.
"Bari kawai Amrah, duniya abin tsoro. Allah Ya
gafartamata. Ni dama ban riƙe ta ba, wadanda ta yiwa su
ne abin ji."
Amrah ta gyada kai.
"Allah Ya basu ikon yafemata."
Ramlat ta amsa da amin. Haka suka dinga maganar su na
kara roƙon Ubangiji akan cikawa da imani.
Washegari kuwa duk yanda ta so Hussein ya amincemata
da ziyarta Halima a gidan yari kamar yanda ta ƙudurta, sai
dai ina! Hussein ya ce bai lamunta ba. Dakyar da siɗin
goshi ta shawo kansa ya amince akan ta nemi Yusufa
ƙanin Halima ta isar da saƙo ta hannunsa. Hakan ba
yanda ta iya kuwa, ta aikata. Yusufa ya zo har gidansu
Ramlatun, bayan sun gaisa ta ke tambayarsa batun
Halima.
"Yaya Halima tana nan, wallahi wacce kika sani a baya
yanzu ba ita bace Anti. Ina nufin sauyi a ɓangaren ɗabi'u
da halayya, ta samu sake litattafai da dama na addininta.
Koyaushe idan na kai mata ziyara sai ta tambayeni ko ina
da labarinki. Amma in sha Allahu yanzu kam ina da labarai
kwando-kwando da zan kai mata har da na twins."
Ya fadi yana kara sumbayar goshin yaran, Ramlat ta yi
dariya. Basu rabu ba sai da ta ba shi kudi da nashi, da
kuma na siyayyar abin bukata da ta ce ya yiwa Halima. Ta
kara da fadin.
"Ka isarmata da saƙon gaisuwata sosai."
Yusufa da farin ciki ya sa kwalla taramasa, ya yi ta yiwa
Ramlat godiya, ita dai ta karbi yaranta ta yi cikin gida.
***
Koda suka koma Adamawa, ba ta ɓoyewa Hussein komai
ba, har faɗa ya dinga yi akan don me ta tsaya kula wani
ƙaton a waje. Dakyar ta lallaɓashi ta nemi gafara ya
hakura ya sauko. A karshe kuma ya ce bai son batun
Hajiya Zeenatu. Hakanan ta kyale zancen sai dai ta ci
ɗamarar ƙara yinta ko nan gaba ne. Ɓangaren Dada kuwa
koda ta ji murmushi ta yi.
"Babu sauran tabon matarnan a zuciyata, ni tuni na
mance da ita. Na kuma yafemata, Allah Ya gafartamata."
Ramlat ta amsa da amin cike da jin dadi. Hakanan
bangaren AlHassan shi dama mai sauki ne.
Satinsu biyu da dawowa Adamawa suka tattara suka tare
a sabon ginin gidansu. Gida ƙerarre flathouse mai shegen
kyau. Tsayawa fasaltawa ma ɓata lokaci ne. An ɗan yi
liyafa ƙarami wanda yan uwa da abokan arziki suka zo,
daman kafin nan sai da aka yi saukar Alkur'ani a gidan.
Kowa ya yaba ya kuma sanya albarka. Daga bisani aka
watse aka bar Hussein da iyalinsa.
***
BAYAN SHEKARA ƊAYA
Rayuwa mai tsari da kuma daɗi su ke gudanarwa, ƴan
biyu sun yi wayo sun yi ɓulɓul abinsu. Duk inda ka gansu
sau sun burgeka, Amina ta fi Aminunta ƙiba sosai, sai dai
duk ƙibarta idan rikici ya haɗasu yanzun zai kirɓeta. Ita
kuwa ta wangale baki da kuka, idan kuwa ka ce za ka ɗau
mataki akan Aminun, yanzun za ta hau taremishi tana
dukan wanda ke kokarin dukansa. Shiyasa iyayen basu
shiga rikicinsu.
Yau ma Ramlatu na zaune jiki duk babu kuzari, gaba daya
damuwa ta bayyana karara saman fuskarta, tun safe ta yi
test na ciki da pt-strip sakamako ya bata positive, tana jin
Aminu na kukan cizon da Amina ta narka mishi a gadon
baya, ya kuwa bi ta a guje ya shiga bugu, aikuwa da
Ramlat ta fusata ta yi kansu duka biyun ta zane tas. Suka
haɗa kai su na kuka ita kuwa ta shige ɗaki don takaicinsu.
A haka uban ya shigo ya iskesu. A rikice ya karasa su ma
suka faɗa jikinsa, ya rungumesu sosai.
"Ya isa my twins, wa ta taɓa ku?"
Suka hau nuna ɗaki.
"Mamiiii" Amina ta faɗi tana kuka da taɓe pink lips dinta.
Ya miƙe ransa a ɓace ya shiga ɗakin. Sai dai ganinta a
kwance tana hawaye ya sanyaya jikinsa, duban yaransa ya
yi ya kuma dubeta, bai ce komai ba kawai ya kama
hannunsu suka bar ɗakin. Sai da ya rarrashe su ya basu
kayan cakulet din da ya siyomusu ya ga sai washe baki
suke da dariya kafin ya sumbaci kowannensu ya mike
zuwa ɗakin.
Gadon ya hau ya shafi gefen fuskarta. Ta dubeshi don tuni
ta bar hawayen.
"Sannu da zuwa."
Cike da kulawa ya ce.
"Meke damunki? Kukan me kike?"
Ta mike zaune ta fada kirjinsa.
"Ciki ne da ni."
Ya yi murmushi.
"Shi ne ki ke kuka saboda ba kya son haihuwa da ni ko
me?"
Da sauri ta ɗago ta girgiza kai.
"Wallahi aa, kawai dai tausayin kaina naji, duka-duka
twins ko shekara biyu ba su cika ba."
Ya ɗaga rigarta ya sumbaci cikin kafin ya ɗago ya sumbaci
lips dinta yana murmushi.
"Shi ne me? Tun yaushe nake maki fatan samun cikin? Ina
ce har zargin ko kima shan maganin hana ɗaukar ciki nayi
maki? Ba halak za ki haifarmin ba? Ramlat ko yara goma
za ki haifamin akai-akai, wallahi ina son abina. Ashe dalilin
da yasa kika huce akam yarana kenan? To ki shirya
dagaske sai na rama musu."
Ta harareshi da wasa, ya ɗan ba ta mintsili kuwa a
kafaɗa. Ta rike tana kuka shagwaɓa gami da fadin wash.
Haka ya dinga lallaɓata kafin ya jawo ta jikinsa.
"Akwai goron albishir babba, yana nan tafe nan da wata
uku."
Ta yi farr da idanunta.
"Watan Azumi fa kenan."
Ya jinjina kai yana murmushi.
***
BAYAN WATANNI UKU..
Kamar yanda ya yi mata alƙawari sai ga shi ta sha
mamaki, ashe dama dalilin yi nata Passport kenan?
Tafiya ce Umarah za su yi, don murna ranar haka ta
rukunkumeshi tana kuka tana sumbatar duk inda bakinta
ya kai. Tare da Dada da su AlHassan da matarsa duka za
su wuce. A waya suka yi bankwana da mutan Kano da
zummar sai sun dawo za ta kai ziyara.
Azumi nada kwanaki goma sha biyar suka tafi. Sosai sun
yi ibada. Anan ne kuma Ramlat ta ƙara zuwar ma da
Hussein roƙo akan ya yafewa Hajiya Zeenatu, da
murmushi ya rungume matarsa ya sumbaci goshinta.
"Na yafemata, Allah Ya yafemata."
Ramlat ta rungumeshi itama da jin dadi.
Koda suka koma ɗaki, kasancewar ƴan biyu na tare da
Dada, wata ibadar suka shiga yi. Bayan komai ya kammala
ya zubamata idanu sadda ta fito wanka tana goge jiki,
garin na Makkah ya karɓe ta sosai, ga cikinta ya fito. Ta
kara mulmulewa ga kumatu da suka yi mata kyau.
Ƙarasawa ta yi ta yi amfani da jelar gashinta ta
watsamishi ruwa a fuska, ya kai hannu zai riƙota ta ja
baya. Girgiza kai ya yi gami da sauke numfashi.
"Wallahi ina sonki."
Yanda ya fadi sai da ya ratsa dukkan sassan jikinta, tsikar
jikinta ya mike. Ba ta san sadda ta taka zuwa gareshi ba
ya kuwa rungumeta sosai suka lumshe idanu. Ji suke
kamar su haɗiyi juna.
"Ina maka son a baki ba zai misalta ba My Hussein, Abban
Twins. Na soma sonka daga sadda na soma ganinka."
Ya ɗago ya haɗa fuskokinsu wuri guda, maimakon amsa,
sai ya haɗa bakunansu. Can kuma ya ɗago kai ya dubeta.
"Sai dai fa a sake sabon.."
Ba ta bari ya karasa ba ta rufemishi bakin da nata. Gaba
daya ta ruɗa shi. Ta sakeshi tana murmushi da maida
numfashi.
"Na shirya yin duk abinda zai farantamaka."
Daga haka ya sa hannu ya ƙara kashe fitilun ɗakin ta
hanyar amfani da makunnin dake gefen gadon. Salo ya
sauya.
ƘARSHE..
_*Alhamdulillah. Ina godiya ga Allah da Ya nunan kammala
littafin Karfen Kafa lafiya. Ina kuma godiya gareku masoya
masu karfafan gwuiwa da kuma hakuri da juriyar bibiyar
labarina duk da irin tsaikon da akan samu. Ina kara ba ku
hakuri bisa duk wani kuskure da ku ka ci karo da shi, dan
adam ajizi ne. Ina maraba da kofofin gyara ko shawara
amma don Allah ba ta hanyar cin fuska ba. Allah Ya kara
haɗamu a wani littafin nawa. Na gode kwarai. Son so
fisabilillah mutan Rof, Rof2, Karfen Kafa group, both
whatsapp & Wattpad fans duka ina godiya. Allah Ya bar
zumunci. *_
_*Godiya Ta Musamman gareki BARR FIRDAUSI KABIR,
wallahi ina maki son so fisabilillah. Kaunar da kike yimin ba
zan ce komai ba gareki tare da sister dinmu, FADILA
KABIR. Allah Ya bar zumunci. *_
_*Ummu Abdoul my editer, chairlady of Fikra. Allah Ya
saka da khairan, Sis Batool Mamman, Donutfairy da ma
dukkan masu bibiyar Karfen Kafa marubuta. Ina maku son
so. Allah Ya bar zumunci. Ameen. *_