Showing 27001 words to 30000 words out of 113545 words

Chapter 10 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

suka ba Ramlat. Ta dara kadan, ya
ƙaraso yana hararar A'isha. Daga bisani suka gaisa da
Ramlat.
"Kin ganta nan, girki ma yanzu ba ta fiye yi ba yayi dadi.
Wataran gishiri ya yi yawa, ko maggi ya yi yawa. Wai
dama haka ake laulayin da shegen tsawo da kuma wuya?"
Murmushi sosai Ramlat ta yi.
"Irin naku kenan sai hakuri."
Nan dai ya yi ta caccakar A'isha ita kuwa sai cika take da
batsewa. Dariya kawai Ramlat ke yi, ganin dagasken fita
yake son yi siyo abinci ta mike tsaye.
"Haba dai, wallahi ka barshi bari na girka tunda na zo."
Ya kuwa shiga godiya, ya ja hannun A'isha wai ta zo ta
kwanta ta huta ya mata tausa. Kunya ya kama Ramlat, ta
yi saurin faɗa wa kicin tana murmushi. A can ƙasan ranta
ƙara godewa Allah ta yi da baiwar da ya yiwa ƴan uwanta
na mazaje nagartattu masu sonsu. Tunanin Aliyu ya
faɗomata da yanda aka sha fama akan aurenta da shi da
kuma Hilal. Idanunta suka ciko da kwalla. Ta haɗiyesu
sakamakon Bingel da take tare da ita a kicin din.
Shinkafa da miya kawai ta girka, ganin suna da kayan
ganye sai ta yanka kabeji da su karas ta haɗa coleslow.
Ta shirya komai saman tebur kafin ta dawo falon ta
zauna tana danna waya. Muhibbat ta kira suka gaisa ganin
kwana biyu ba su yi magana ba. A karshe ta nemi Amrah a
waya suka hau hira. Har zuwa sadda A'isha ta fito.
Zama ta yi tana hamma, dagasken dai bacci ta yi don
idanunta da fuska sun nuna.
"Ya kike ji yanzun?"
Gyada kai ta yi.
"Da sauki sosai. Sai dai yunwa."
Murmushi Ramlat ta yi.
"Daukomin hijab sai ki je ga abincin can saman tebur."
Miƙewa Aishah ta yi ta koma daki, ca ta fito rike da Hijab
da darduma. Ramlat ta shimfida ta tayar da sallah, tana
cikin sallar Hisham ya fito yana amsa waya.
"Dagaske kake ko wasa?"
Can kuma ya ce.
"Ok ganinan zuwa."
A'isha ta dubeshi tana kokarin zuba abinci a plate. Kafin
ma ta tambaya ya amsa da dariya yana satar kallon
Ramlat.
"Wai kinsan kuwa Hussein ne ya zo yana waje? Bari na
shigo da shi."
Daga haka ya fita, har suka shigo tare ba ta idar ba. Jin
sallamarsa sai da gabanta ya fadi kafin ta yi istigfari a
zuciya ta maida hankali ga sallarta. Sai da ta idar ta shiga
addu'a hannun har yana rawa. Ya na zaune kujerar da ke
fuskantarta. Gaisawa suke da A'isha amma kusan
hankalin yana kanta. A'isha ta saci kallon Hisham ya
kashemata ido daya. Ta girgiza kai, ta san dama shi ya
haɗa hakan.
Ramlat ta kasa cire hijabin, ta mike ta ninke dardumar.
"Ina wuni." Ta gaidashi, ya amsa a hankali. Rabonsu da
juna tun wayar a suka yi kwanaki, ko a WhatsApp bai ƙara
kulata ba.
"Ku muje mu ci abinci, don wallahi Princess yunwa take
ji."
Fadin Hisham yana mai miƙewa.
"Na ƙoshi." Daga Hussein har Ramlat kusan a tare suka
furta, abin sai ya ba Hisham da A'isha dariya. Suka saci
kallon juna, kunya ta kama Ramlat ta kauda kai. Shi kuwa
Hussein murmushi ya yi.
"Toh duk sai kun ci wallahi."
Fadin Hisham.
A dole suka bi bayansa, Ramlat ta dage a falon za ta ci.
"Kai Sis." Fadin A'isha kamar ta yi kuka. Hussein ya ja
kujera ya zauna bai ce musu uffan ba. Wayarsa ta yi ƙara
ya mike cak ya fita gami da fadin.
"Ina zuwa."
Hajiya Zeenat ce, tambayar inda yake ta hau yi, ya dafe
goshi.
"Ina gidan Hisham, wani abu?"
"Shi ne ba za ka fadamin ba? Na dawo gida ban ganka
ba."
Ransa ya ɗan sosu.
"Da za ki fita yawon biki kin fadamin?"
"Ni kake faɗawa haka?" Fadin Hajiya Zeenatu cike da wani
irin firgici.
Ya lumshe idanu ya bude.
"Sai na dawo."
Daga haka ya katse kiran. Ya koma ciki.
Madadin ya ganta a tsakar falon, sai ya ganta zaune
kujerar gefen da ya tashi, ya karasa ya zauna.
"Hala Madam din ce ko sabuwar kamun da muka yi?"
Fadin Hisham yana ƴar dariya da satar kallon Ramlat.
Kirjin Ramlat ya buga, wani irin kishi ya turniƙeta. Ba ta
san Hisham na da zancen da hankali ba zai dauka ba,
zance marar kan gado ba, sai yanzun. Wani haushi ya
bata, abincin ma ya daina yi mata dadi, dama tun zaman
Hussein ƙamshin turarensa ya mamaye ilahirin jikinta ya
haifarmata da kasala. Yanzun jikinta ya idasa mutuwa.
"An fadamaka kowa irinka ne kenan."
Abinda Hussein ya ce kenan bai ƙara uffan ba ya bar
Hisham da dariya.
Tunda ya soma cin abincin wani dadi ke ratsa
kunnuwansa. Ya kasa ɗagowa har sai da ya yi nisa da
soma ci, can dai ya dubi Hisham.
"Nikam Princess dinka hala ta yi makarantar koyon girki
ne."
Haba! Ai daga Hisham din har A'isha da uwar gayyar
Ramlat, dariya suka ya basu. Ya dubesu yana dan yarfa
hannu, ya tsaida kallon kan Ramlat.
"Mene abin dariyar?" Ta sunkuyar da kai tana murmushi.
"Antinmu kinga karo na biyu wannan bawan Allahn na
buga santi akan girkinki. Gaskiya yau goron da zai ba da
kamata ya yi ya fi na rannan."
Ita dai ba ta ce komai ba, ta kasa ci gaba da kai lomar,
karshe ma miƙewa ta yi.
"Na ƙoshi."
Daga nan ta yi gaba da sauri ta koma cikin falon ta zauna
ta basu baya tana sauke ajiyar zuciya. Shima gogan bai
ƙara magana ba har ya kammala ci ya mike ya bar
Hisham da A'isha ma ƙusƙus.
Wuri ya samu ya zauna yana danne waya, sai dai rabin
hankalinsa a kanta yake. Tun yana satar kallo har ya koma
kallon sosai. Karshe ya maida hankali saman wayar,
whatsapp ya shiga. Ganinta online ya taɓota.
"Thank you."
Ta bude saƙon kafin ta saci kallonsa, murmushi yake
amma idanunsa na saman waya.
"Kallon fa? Kar ki mata kwace."
Jin bing na shigowar saƙo ta maida hankali ga wayar.
Abinda ta gani kenan, ta turo baki kadan ta kashe data
gami da jefa wayar cikin jaka.
Miƙewa ta yi ta dauki mayafinta ta nufi dakin baƙi. Hijab
din jikinta ta cire ga gyara zaman mayafin ta fito. Lokacin
su Hisham sun dawo falon.
"Ba dai tafiya ba?"
Fadin A'isha.
"Tafiya zan yi, Hajiya ta ce kar nayi dare."
"Kai kamar wata karamar yarinya. Ko hira fa bamu yi ba.
Prince ka yi mata magana."
Fadin A'isha a shagwaɓance. Sakin baki Ramlat ta yi don
ita abin ma na A'isha da Hisham mamaki yake bata.
Soyayyar dai kamar ana ƙaramata zuma.
"Ji, toh banda uzurin gabana da zan ƙare a gidanku?"
"A'a amma don Allah ki zauna, kinga fa yanzu shida, ga
hadari a gari..."
"Shiyasa ai zan tafi, kinsan ban fiye tuƙi idan ana ruwa
ba."
A'isha kuma ta rasa abin faɗi. Hisham dama bai ce ba, so
yake abokinsa ya ce!
Jakarta ta dauka cikin lallashi ta ce.
"Haba Autar Hajiya, In sha Allah za ki ganni kwanannan, ai
yanzun sai ana leƙowa ana dubaki. Yauwa Maman Twins
ma sun ce na fadamaki suna nan zuwa."
Jin haka yasa A'isha sakin ranta kaɗan.
"Toh ai shikenan. Allah Ya kaimu."
Ramlat ta amsa da amin tana murmushi.
Hussein ya mike yana duba agogo.
"Nima zan gudu."
"Kamar hadin baki?" Fadin Hisham.
Girgiza kai Hussein ya yi.
"Yamma ta yi ga hadari."
Gyada kai Hisham ya yi.
"Ai shikenan, don ma dai kai din baki da hanci ne. Ba nisa
sosai."
Hussein bai amsa ba ya bi bayan Ramlat da tuni ta fice.
Hisham na dariyar mugunta ya yiwa A'isha raɗa a kunne
ya bi bayansu.
"Innalillahi, garin yaya?" Fadin Ramlat a hankali tana jin
kamar ta yi kuka. Hussein ya juyo yana dubanta, iska na
faman ɗaga mayafin nata da ja mata rigar. Tayarta ya
gani a sace.
"Ya Salam, Antinmu garin yaya hakan ta faru?"
Fadin Hisham sadda ya karasa yana kyafkyafta idanu
ganin iska na neman yi mishi lahani. Kamar ta yi kuka ta
dubi Hisham.
"Wallahi nima bansani ba."
Ta furta cike da takaici.
A'isha ta danne dariyarta, game din dadi yake mata sosai.
Tuni Hussein ya bude motarsa ya shige ya ba ta wuta.
"Shigo na kaiki." Abinda ya ce kenan. Ta dubeshi ta maida
duba ga su Hisham.
"Je ki don wallahi hadarinnan yanda ya haɗe ba zan iya
fita ba. Sai dai ko ki kwana zuwa safe."
Ta haɗa daga shi har A'ishar ta watsawa harara.
"Gobe na ƙara zuwa gidanku."
Nan kuma suka hau aikin ban hakuri, ta karasa ta bude
gidan gaba ta zauna. Hussein ya dubi abokinsa.
"Sai mun yi waya."
Daga haka ya fice bayan Maigadi ya budemusu ƙyaure.
***
Tunda suka kama hanya yake murmushi, ya san ko mene
aikin Hisham ne. Amma hakan ba karamin dadi ya yi mishi
ba, ya juya ya kalleta. Ta takure kanta wuri guda, ta wani
rungumi jaka. Basu yi mintuna biyar da soma tafiya ba aka
soma ruwa dagasken gaske. Ganin irin karfin ruwan yasa
dole ya taka burki ya sauka ya gangara gefe. Wayarta ta yi
ringing ta duba, Hajiya ce.
Hakuri ta bayar gami da bata tabbacin ta taho. Hajiya na
faɗa akan ba ta ji dadin hakan ba suka yi sallama. Tasan a
zatonta ita ke jan motar, ba zata fadamata ga abinda akai
ba.
"A dalilinki na zo gidan Hisham."
Ya fadi kansa tsaye yana kallon yanda ake zuba walkiya
da ruwa kamar da bakin ƙwarya. Ta dubeshi da mamaki,
maimakon murmushi, wani kwantaccen damuwa ta gani
shimfide saman fuskarsa. Ya karkato yana dubanta, ta
kauda kai saboda nauyin da kwayar idanunsa suka yi
cikinnata.
KARFEN KAFA Chapter 52
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


"Kar fa ki fassara kalamaina."
Ta yamutse fuska kadan.
"Fassara ta me?"
Ya yi murmushi yana dubanta sannan ya maida kai ga
tuƙinsa.
"Akwai hoton da nake da buƙata a wurinki."
Ta saci kallonsa. Ba ta tanka ba ya ɗora.
"Wata little angel da na gani kwanakin baya kin ɗora
hotonku tare. Ita ba ƙatuwa ba kuma ba siririya ba. Fara
ƙal."
Da gaskiyar Bature da yace Blood is thicker than water.
Fati yake nufi.
Murmushin da ba ta san ta iya shi ba ta shiga yi kafin ta
saita kanta da tunaninta.
"Ka santa ne?"
Taɓe baki ya yi gami da girgiza kai.
"Ko daya, kawai dai yarinyar ta burgeni sannan ina jinta
kamar ƴar da ta fito daga jikina."
"Alhamdulillah." Tsabar ruɗu yasa ta furtawa a fili har ya
kai dubansa gareta.
"For?"
Ya nemi ba'asi. Murmushi kawai ta ke yi.
"Murmushin fa?
"Ba murmushi nake ba." Ya dubeta sai kuma ya yi dariya.
"Toh kuka kike yi." Ta shafi bakinta sai kuma ta sunkuyar
da kai tsabar kunya.
Ya sanya hannu ya kunna music. Wannan karon ma dai
muryar Nancy Ajram ke tashi. Abinda Ramlat ta fahimta,
Hussein ma'abocin jin waƙoƙin larabawa ne.
Shiru ya biyo baya har suka kai ƙofar gidan su Ramlat.
Kirjinta ne ya bada dam ganin Yayanta Munir tsaye a jikin
motarsa yana amsa waya. Tunda motar ta tsaya ya
ƙuramata idanu yana son ya shaida waye.
Hussein ya dubeshi sadda ya ke ƙoƙarin cire Seat Belt din
da ya sanya. Kamanninsa da Ramlat kawai ya gani da kuma
irin firgicin da ke saman fuakar Ramlat din, ya fahimci ko
waye. Bai cewa Ramlat komai ba ya fita, itama ganin haka
ta fito kirjinta na lugude. Yaya Munir da ganin Ramlat ya ba
shi mamaki, dakyar ya iya miƙawa Hussein hannu suka
gaisa. Ita kuwa Ramlat tana gaidashi wuf ta faɗa cikin gida.
"Ke kuma lafiyarki?" Tambayar da Hajiya ta watsomata
kenan ganin shigowar da ta yi a hargitse. Girgiza kai ta yi
ta zauna kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki.
"Ba komai."
"Hala kin haɗu da yayannaki a waje?"
Ta gyaɗa kai, ba ta kai ga bata amsa ba sai ga Munir din.
Abinda ta ke gudu ne ya kasance, faɗa sosai ya shiga yi
akan don me za ta shiga motar abokin Hisham. Hajiya dai
mamaki ƙarara don ba ta da labarin hakan.
"Ku yi hakuri, wallahi tayar ce ta sace. Ga Auta ba lafiya
shiyasa dole Hussein din ne zai kawoni. Kunsan yanayin
unguwarsu ba'a samun abin hawa cikin sauƙi."
Ta faɗi jiki a sanyaye. Harara Yaya Munir ya danƙara mata.
Hajiya kuwa jin Hussein ne yasa ba ta ƙara uffan ba.
Dakyar dai ta lallaɓashi ya tafi. Bayan fitarsa ta miƙe ta yi
ɗaki, sai bayan sallar isha'i sannan ta fito, ta ƙara wanka ta
sanya doguwar rigar bacci da ƴar hula.
"Gidan gaba ɗaya sai ya yi ba daɗi wallahi."
"Uhm, ni zan faɗi haka ba ke ba Ramlatu, nayi kewar
yarannan kamar na kira waya a maidomin su."
Murmushi Ramlat ta yi ta zauna.
"Hajiya kinsan wani ikon Allah? Yau da kansa ya tambayeni
hotin Fatima. Wai haka kawai yarinyar ta burgeshi, na
aikomasa hotunanta."
Hajiya ta ɗan yi shiru alamar nazari.
"Fatima wacce?"
"Ɗiyar baƙonmu na Adamawa."
"Ikon Allah, jini ba wasa ba. Allah Sarki."
"Ni kaina nayi mamaki."
"Allah Ya ci gaba da taimakonmu, in sha Allah za'a dace.
Wataran komai zai zama labari."
Cikin gamsuwa Ramlat ta jinjina kai tana murmushi, fuskar
Hussein na yawo cikin ƙwayoyin idanunta.
"In sha Allah." Ta maimaita.
***
Ranar litinin da tana kammala shiri ta fito, a gaggauce ta
karya ganin tana dab da makara. Haka ta fito titi don har
sannan Hisham bai ga damar maidomata motarta ba, ba
kuma ta ƙara kiransa ba tunda ta ji yana kiran shi ba shi da
kuɗin gyaran taya toh ta san da biyu ya ke yi.
Ta yi tafiya kaɗan kafin ta fito bakin titi ta samu abin
hawa. Zamanta keda wuya cikin Napep, wayarta ta ɗauki
ƙara. Halima ce. Kamar ba za ta ɗaga ba sai kuma ta
ɗauka.
"Ke kuwa Ramlat ba faɗa me ya kawo gaba? Shikenan don
kin bar Revenue an rabu?"
Yaƙe ta ɗan yi kamar a gabanta.
"Ayya Halima ba haka bane. Allah Ya huci zuciyarki. Fatan
kuna lafiya, Ya sauran mutanenmu?"
"Uhm, lafiya kalau, sai dai kin tafi kin bar baya da ƙura."
Da mamaki ta ce.
"Ban fahimta ba. Wani abu aka yi?"
"Eh, yanzu ba wanda bai san cewa Chairman yana sonki ba.
Idan ma kina tunanin bamu sani ba gwara ki san cewa ƙwai
ya fashe."
Wani ɓacin rai ya zo wa Ramlat wuya, ta danne komai.
"Shi ne me? Don yana sona mene a ciki Halima?"
"Aa ba komai bane, Allah Ya ba ki hakuri. Yanzun sai na
faɗi zancen da zai yimin sanadin wurin neman halal ɗina.
Dama shawara zan ba ki kawai don matar Chairman ba
kanwar lasa ba ce."
Don tsananin ɓacin rai ba ta san sadda wani wawan tsaki ya
suɓucemata ba.
"Daga ita har mijinta basu ɗaɗani da ƙasa ba, ke kinsan ni
kuma kin san halina. Bana kallon mutum irin Chairman
matsayin nagartaccen namiji da ya isheni kallo ballantana
har na ƙulla alaƙa ta dindindin da shi, wato aure. Ke dai da
ya tsolemaki ido har ki ka kasa haƙurin bar wa cikinki
gulmar sai ki je can ki ƙarata."
Daga haka ta katse wayar ta kasheta gaba ɗaya ma tsabar
takaici da ɓacin rai. Har suka isa ta sauka ba ta ji sassauci
a ranta ba. Ita ta soma zargin ma Halimar ce ta kwatantawa
Chairman din gidansu na Yakasai. Can kuma ta ja istigfari a
ƙasan ranta.
***
*
ADAMAWA*
AlHassan ke ta zuba sauri a hanyarsa ta komawa cikin
babban shagon siyar da kayayyaki na Alkhairat Mall adalilin
mantuwar da ya yi na wallet ɗinsa saman teburin Cashier.
Karo suka ci da wani matashi da kallo ɗaya za ka yi mishi
ka san ruwa biyu ne, kamar dai ɗan Sudan kamar kuma ɗan
Nijeriya.
"Sorry please." Faɗin AlHassan kenan yana dubansa a
fisge, Matashin ya zaro ido kafin ya saki ƴar dariya yana
nunashi da yatsa.
"Hussein!"
Daga haka ya rungumeshi yana dariyar farin ciki, AlHassan
ya tsaya cak! Ya kasa magana kwakkwara, can dai ya ɗago
ya dubeshi da kyau, kamar ya so sanin fuskar sai dai Allah
bai ba shi ikon tunawa ba.
Rasheed da ya lura da irin kallon da yake binsa da shi, sai
jikinsa ya ɗan yi sanyi. Daidai sadda wani ma'aikacin wurin
ya nufosu, duban AlHassan ya yi.
"Yallaɓai ai na fita ban iskeka ba mun yi saɓani, ga wallet
ɗinka ka manta."
Ya karɓa da godiya, Rasheed dai kallo yake sai kuma a
sannan tunaninsa ya ba shi anya kuwa wannan Hussein ɗin
da ya tako takanas daga ƙasarsa don ya gani ne? Nan da
nan jikinsa ya ba shi Twin brother ɗinsa ne wato AlHassan
Aminu.
"My name is Alhassan Aminu, Hussein's Twin Brother."
Rasheed ya shiga murmushi da gyaɗa kai, bai lura da
yanayin sauyawar fuskar Alhassan din ba, daga yanayin
farko zuwa wani yanayi na daban mai nuni da alhini da
kuma sosuwar rai.
Alhassan ya nemi su ɗan fito farfajiyar wurin. Ba musu
Rasheed ya bi bayansa. Ji yake kamar ya yi tsuntsuwa ya
je ga Abokinnasa, shekarun da suka gabata ya yi masifar
kewarsa. A hanyar ma su na tafe ƙorafi ya ke zubawa
AlHassan na yanda Hussein ya kasa cika alƙawarin kawo
mishi ziyara sai shi ne ya cika a karshe.
"Kusan satina ɗaya a garinnan na kasa gane gidanku, har
na fidda rai don har na yi komai na komawa garinmu sai yau
cikin ikon Allah muka haɗu da kai."
Duk yana maganar ne cikin harshen turanci, Alhassan ya ba
shi address din gidansu kafin su yi musanyen lambar waya
suka rabu. Rasheed dai ya yi mamakin dalilin da yasa bai
ba shi lambar Hussein ba, ya so tambaya kawai sai ha bar
wa cikinsa. Da wannan ɗokin ya nemi adaidaita ya koma
masaukinsa, siyayyar da bai yi ba kenan tsabar murnar
cimma abindanya kawoshi. Tun a hanya ya kira
mahaifiyarsa yake labarta mata haɗuwarsa da AlHassan da
yanda ya rungumeshi a zatonsa Hussein ne. Ta tayashi
murna sosai sannan suka yi sallama.
***
*KANO*
Tana zaune bayan kammala wasu aikace-aikace, ta tuna da
cewa wayarta a kashe ta bar ta gaba ɗaya yinin ranar, da
sauri ta jawota ta kunna. Mintuna ƙalilan da kunne Data,
saƙonni suka shiga faɗowa daga Whatsapp. Wanda ta ke
burin ta ga ya aikomata saƙo babu shi a ciki, har tana shirin
ajiye wayar sai ga text message ya faɗo, ta duba. Ba ta kai
ga buɗewa ba sai ga kira, duk daga mutum ɗaya wanda ta
daukeshi SPECIAL.
"Kashe mutum kike kokarin yi."
Ta ɗan dafe ƙirji kafin ta saita kanta tuna a inda ta ke,
lumshe ido ta ɗan yi tana murmushi. A baya zabta ƙaryata
idan wani ya ce za ta ko kalli wani ɗa namiji ta ji ya burgeta
balle ta kaunaceshi, a yanzun kuwa tana jin Hussein a
ranta. Da wani irin ƙauna mai sanyi, da wani irin so mai
cakuɗe da sinadarai masu ban mamaki.
"Tuba nake yi, me na yi?"
Ya sauke ajiyar zuciya wanda ya ratsa kunnuwanta.
"Kin kashe wayarki bayan kinsan na kamu da son Beautiful
Angel dinnan da kika ɗora a status."
Runtse idanu ta yi cikin son haɗiye abinda kunnuwanta su
ka yaudareta da son ji. Maimakon hakan sai ta ji abu daban,
cikin sarewa da sanyin jiki ta amsa.
"Ka yi hakuri, na ma manta cewa na kashe wayar. In sha
Allah yanzu zan turamaka."
"Ok! Na gode, ina jira."
"Toh."
"Naji muryarki ta sauya, hope komai lafiya?"
Ta ciji leɓbanta na ƙasa tsabar haushin kanta da ya kama
ta, toh mene dalilin da za ta ba shi damar fahimtar wani
abu?
"Lafiya kalau, ina wurin aiki ne."
Shiru ya biyo baya can kuma sai ya amsa.
"Ok ba damuwa. Idan kin koma gida kya turomin. Thanks."
Daga nan ya katse kiran.
"Ke kam dai naga alamar da wani gwanin naki kike waya."
Ta kai duba ga Hajiya Salma, darakta din department din da
ta ke. Kasancewarta mace mai raha da haba-haba yasa ake
sonta. Ga ba ta da wuyar sabo. Murmushi kawai ta yi ba ta
ce uffan ba. Ta faɗa whatsapp, Hussein din ma ba ya
online, haka ta turamasa duk hotunan Fatima da ke kan
wayarta har wanda Fatiman ke tare da Hafsat. Babu dai
nata ko ɗaya a ciki.
Karfe biyar da kusan rabi ta bar Ofis zuwa gida. Gaba daya
jikinta a sanyaye yake sakamakon soyayyar da ta ke yiwa
kanta shamaki da ita, amma kamar zuciyar ba ta jin
kashedinta. Ƙara cusa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login