Showing 33001 words to 36000 words out of 113545 words

Chapter 12 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

haifarmasa da
sukuni da kwanciyar hankali? Sai dai kuma akwai wani
duhu da ya kasa nemo haske a cikinsa, watakila sai nan
gaba! Ya ayyana a ransa.
"Shikenan, zan tafi. Ki gaida su Mama."
Daga nan ya juya ya shige motarsa, iska da sanyin safiyar
na busata, ba ta fasa kallonsa ba har ya shiga motar.
Gilashin ya sauke yana kallonta, sakanni biyu zuwa uku
kafin ta farga, ta juya da sauri ta faɗa gida. Ya ja motar
kamar wanda kwai ya fashewa a ciki.
Allah Ya taimaka Hajiya ba ta falo, da sauri ta shige
dakinta ta rufe, a bakin ƙofar ta zame ta cure wuri guda,
kuka ko dariya za ta yi? Ba ta sani ba, ba ta da tabbacin
abinda kwakwalwarta ke kokarin hasasowa sai dai ta jera
Hussein a sahun mutanen da suka san ƙima da darajar
*Ɗ AN ADAM*. Ta sauke ajiyar numfashi tare da neman
tsari daga Ubangijinta akan sharrin zuciya da saƙe-
saƙenta.
***
"Daga ina kake?" Ta yi tambayar ba tare da ta bari ya
ƙarasa fitowa daga cikin motar ba, ya kalleta kallon tsaf.
Gabansa na faɗuwa sai dai akwai wani ƙwarin gwuiwa da
yake ji na iya kallon cikin idanun Hajiyar da ɗan ƙaramin
kuzari.
"Bai kamata ki fito haka ba."
Ya fadi a sanyaye ganin daga ita sai doguwar rigar bacci,
damtsen hannun duk a waje ga tumbi da ya ɗaga rigar.
Hajiya Zeenat idanunta a kaɗe, ji take kamar ta shaƙe
wuyan Hussein saboda wani irin kishi da ya mamayeta.
Tasan ƙarya ne a kowane yanayi mace ta ga Hussein ba ta
ƙyasa ba, ta kuma sani ba zai taɓa zuwa wajen kowace
mace ba musamman da safiyar fari. Amma tana son
tabbatar da inda ya je don ta samarwa zuciyarta hujjar da
za ta nutsu sosai.
Gaba ya yi zuwa cikin gidan, ta mara mishi baya. Yana
niyyar taka matattakala ta riƙe hannunsa. Ya runtse ido da
sauke ajiyar zuciya alamar gajiya, bai bari ta ƙara tambaya
ba ya tari numfashinta.
"Wasu takardu na kaiwa Hisham. Shikenan?"
Ta bishi da kallo tana mai sakin hannun, ya haye sama.
Ƙarya abu ne mafi muni cikin munanan ɗabi'u, ya shiga
istigfari a ƙasan zuciyarsa. A ɓangaren Hajiya Zeenat,
tasan waye Hussein, ƙarya ba ta daga cikin shirginsa, don
haka sai ta gasƙata amma ta soma jin tsanar Hisham a
ƙoƙon ranta. Yana neman shigemata hanci da ƙudundune.
Ta yi ƙwafa kawai ta bishi saman.
Kwanciya ya yi ya rufe har kansa da bargo saboda bai
shirya amsa wasu tambayoyin daga Hajiya Zeenat ba
bayan wancan. Murmushi ya tsinci kansa da yi, murmushi
sosai, Ramlat da firgicin dake kwance samam fuskarta shi
ya ƙayatar da shi a yanzun.
***
"Jimin ja'irar yarinya! To ba kya sonsa wa kika kawomana
za ki aura? Ko an faɗamaki akwai wani cikin iyayennaki da
za ki je wa da wannan magana su ɗauka?"
Dada ke wadannan kalaman sadda Ramlat ta kai mata
ziyara da kuma roƙonta akan a janye batun Chairman. Jin
abinda ta ce Ramlat ta ɓata fuska.
"Da ace kinsan waye shi da ke za ki zama farkon wacce
za ta ce aa."
Ta zayyanemata kaf labarin Chairman, tun Dada na faɗin
toh meye a ciki? Har ta yi shiru tana gyaɗa kai. Ramlat na
kaiwa aya ta dubeta.
"Toh yanzu ya dace ace kun bayar da jininku ga wannan
mutumin? A ma ɗauke duk wannan, bana sonsa. Ba shi da
kyawawan ɗabi'un da zan kaunaceshi dominsa. Bana son
na maimaita gidan jiya, abin nufi, ina gudun na saɓa
umarninku a karo na biyu naga ba daidai ba."
Murmushi Dada ta yi ba tare da ta furzar ba. Ta jinjina kai.
"Ai shikenan, zan yi magana da shi Bellon, ya dace su yi
bincike mai kyau a kansa, idan da hali ma gwara a tattara
a ajiye zancensa gefe. Sai dai kuma da sharaɗin ki fiddo
miji nan kusa. Da ƙananun shekarunki ba zamu zubamaki
ido ki yi ta zama haka ba aure ba kuma kina yawon wurin
aiki, babu ƙima da mutunci a hakan Ramlatu."
Ramlat ta gyaɗa kai cikin tausayawa kanta.
"Ki tayani addu'a Dada, Allah Ya zaɓamin nagari."
Dada ta amsa da amin. Ta ɗora da faɗin.
"Yaushe angwayen nawa zasu dawo ne?"
Murmushi Ramlat ta yi, tana gyara zaman mayafinta,
takanas ta biyo daga wurin aiki don ta roƙi alfarma wurin
Dadar.
"Ni kaina ina kewarsu, amma mun yi waya da Muhibbat ta
cemin za ta je ta ɗaukosu zuwa gidanta su yi kwana biyu
tukunna ta maidosu. "
"Allah Ya nunamana. Za ku je Daurar?"
Dada ta ƙarashe tana ɓallar goronta daidai sadda Ramlat
ta dauki jakarta.
"In sha Allah zamu je. Inace su Nusaiba ma duka za su
je?"
"In sha Allahu. Ai bikin na gida ne."
Fadin Dada, a karshe suka yi sallama ta fice ba ta ko yi
sallama da sauran jama'ar ba don tana jin haushinsu ganin
mafi yawa na goyon bayan Chairman. Ita mamakin ma irin
karɓuwar da Chairman ya yi a gidan ta yi don ko a
gidansu bai samu hakan ba.
***
Tsakaninta da Hussein sai gaisuwa, ta rasa dalilin
sauyawar alaƙarsu. Wani jzolaya da wasa duk ya daina.
Kamar wani kalma na sabo bai taɓa ratsawa tsakaninsu
ba. Wannan ya jefata damuwa, ga matsin lamba daga
Chairman wanda ba dare ba rana sai ya kira. sai dai har ya
kammala ringing ba ta ɗauka, idan ya dameta kuwa ta
latse wayar gaba ɗayanta.
Tafiyarsu Daura ta gabato har Hajiya zaa je wannan karon
sai Amarya Hunainah wacce ta saki jiki da su sosai ake
zumunci ba kamar Bilkisu ba wacce tun hayan auren
Munir ta haɗe danginsa kaf ta jerasu layin munafukai.
Wannan ne ya siyawa Hunainah daraja da ƙima ba kaɗan
ba a idanun su Ramlat. Gidanta ne dai har sannan Ramlat
ɗin ba ta taka ba, ba kuma don wani abin ba.
Ana gobe zasu wuce gaba daya su Rafee'ah har Hunainah
mai karamin ciki sun zo cikin gidan kwana, Aisha ma ta
na nan ta zo ayi sallama. Hira suke yi cike da nishaɗi ana
dariya, sallamar Munir ce ta katsesu. Suka amsa ya dubi
Ramlat.
"Ke wancan na wajen ne Chairman din naki?"
Nan da nan annashuwar Ramlat ta dauke.
"Zuwa ya yi?"
Ta fadi ranta a ɓace, tasan ya kira ta ƙi ɗagawa ya yi
mata text akan zai zo su gaisa ta maida masa martanin
ba ta buƙatar hakan.
"Nikam dai bari na leƙa naga waye wannan Chairman din."
Rafee'ah ke faɗi tana ƙoƙarin miƙewa.
"Shi auren a igiya kika ratayeshi? Ba ki da kai fa Rafee'ah
naga alama."
Munir ya fadi gami da harararta.
"Goɗai-goɗai da ke kina abinda ko Auta ba za ta yi ba. To
ki je ki ce masa me? Ki leƙa wuta ma ko?"
Dariya suka sa mata idan ka cire Ramlat da ta yi daki
ranta na ƙuna. Kamar ba za ta fita ba, sai kuma ta yanke
ta je kawai ta tunkare shi komai zai faru ya faru. Mayafin
rigar jikinta ta yafa. Koda ta fito lokacin Hajiya na zaune.
"Ke dama haka kike zuwa hirar fuska kamar baƙin
tukunya?"
Munir ya faɗi yana duban Ramlat da ta nufi Hajiya don
sanarmata.
"Yaya Munir nidai da ka roƙarmin alfarmar mutuminnan ya
bar zuwa gidannan. Na faɗamasa ya kyaleni bana sonsa
wallahi."
Taɓe baki Munir ya yi.
"Au, wato dai gidan jiya kike neman a maimaita? Ai yanzu
babu mai miki dole Ramlat, a baya ma ba'a iya anyi maki
ba sai yanzu? Ta inda aka hau ai ta nan ake sauka, ki
samu wadanda suka karɓi kuɗinsa."
Yanda gaban Ramlat ya buga da ƙarfi, haka fuskokin
Hajiya da su Zulaihat ya nuna razani da mamaki.
"Me kake nufi? Kuɗin auren Ramlatun su Yaya Bello suka
karɓa?"
Munir ya dubi Hajiya yana mai murmushin tambayarta.
"Haba Hajjaju, a karɓi kuɗin auren Ramlatu ba ki sani ba?
Kawai dai yana sakarmusu bakin aljihu ana bushasha."
Wani wahalallan ajiyar zuciya Ramlat ta sauke, cike da
bakin ciki ta kama hanyar ficewq daga falon. Maganar su
dinma sai suka bar ta anan adalilin Hunainah dake wurin,
ko ba komai suna buƙatar sirri.
***
"Girman kujerarki ce tasa na jure dukkan wata shanya da
kika yimin, sai dai koda na bushe ganinki ya maidani ruwa
tsundum."
Murmushi yake yana ci gaba da dubanta, jinsa yake
kamar wani saurayi mai shekaru talatin idan yana gabanta.
Ramlat ta dubeshi a ɗaure.
"Ina haɗaka da girman Allah da ManzonSa s.a.w ka fita
hanyata. Kaga mu ba yara bane da za mu tsaya muna
magana da maimaici. Ina za ka ji daɗin zaman aure da
wacce ba ta jinka a ranta? Wane kyautatawa ka ke tunanin
za ta yi gareka?"
Chairman ya yi wata ƴar dariya.
"Kina tunanin barazanar kisa a daren amarcinmu zai sa na
sake ki? Aa Hajjaju, wannan namiji ne ba muna maza ba.
Ba ki da abinda za ki faɗarmin da gaba har ya yi sanadin
rushewar alaƙarmu."
'Innalillahi..' Ta kai har ƙarshensa yayinda jiri ke neman
kwasarta. Dakyar ta samu ta daidaita tsayuwarta bayan ta
dafe Black Camry din Chairman. Wani yawu ta haɗiya.
"Me kake nufi?" Ta fadi cikin sarƙewar harshe. Chairman
ya yi dariya karo na biyu.
"Abun dariya, kunkuru ya yiwa busjiya ƙafa, banda abinki
Ramlatu ai maganar duniya ba ta ɓuya, kin ɗauka haka
kike zaune ana ganin ina neman aurenki ba'a kawomin
sukarki ba? Ai ba zai yiwu ba. Kedai ayi sha'ani kawai."
Shiru ya biyo baya ga idanunta sun cicciko da kwalla.
"Idan ka gama zancen zan koma ciki."
Chairman ya marairaice.
"Haba Ramlatu, me kike gujewa a auren mutum irina mai
muƙami da kuma rufin asiri? Kinsan adadin matan da ke
neman irina kuwa? Da za ki ga matan da ke bina za ki cika
da mamaki. Ramlatu sonki nake dagaske amma kin ƙi
fahimta. Da ace na biyewa Kawunnanki da tuni an daura
auren, yanzu ma abinda ya kawoni batun turowa ne suka
bn iznin nayi, shi ne na zo mu kara daidaitawa kafin
lokacin."
Kamar wacce aka harbawa mashi, haka ta ji wani radadi a
kirjinta. Daidai sadda ta ke share hawayen da ya zuba
saman kuncinta ta kalleshi.
"Me ka ce? Iznin ka turo fa suka yi maka?"
" Kwarai kuwa, kuma kinsan dama ce da ba zan taɓa bari
ta suɓucemin ba. Na zo ne don kawai na kwantar da
hankalinki, ki ƙara samun nutsuwa da ni don idan har ina
numfashi kina yi, babu wanda ya isa ya rabani da ke."
Ranta ya ɓaci ainun.
"Sai mu gani inda ake dole! Aure ne bana yi, ba zan
aureka ba. Ina mai tabbatarmaka ko ka turo babu inda
zancen zai ɗara."
Daga nan ba ta juya ba ta ko waigo ta ji dalilin kiran da ya
shiga kwalamata ba.
***
"Lafiya?"
Kusan lokaci guda suka jehomata tambayar ganin yanda
ya faɗomusu ɗakin. Ta kasa magana sai kallo, karshe ta
wuce ɗaki.
Ganin haka Munir ya mike ya fita waje, Chairman ya shige
abin hawa har ya fice. Ya dawo ciki ya sanar da su ya tafi.
Gaba daya suka bita dakin idan ka ɗauke Hajiya da Munir
da suka faɗa tattaunawa game da lamarin Ramlatun.
"Ai mafita fa a wajen su Kawu shi ne kawai ta nemo wani
ta kai musu. Yanzun bata da abinda zai kwace ta a
hannunsu. Su gani suke sun kama dami a akala. Rannan
ma na shiga gidan na tarar Malam (Kawu Rabe) yana ta
rubutu, wai mai neman auren Ramlatun yake rubutawa na
tsarin jiki. Kinga kuwa ba karamin kamu suka yi mishi ba,
fahimtar da su barin aurennan sai da taimakon Allah."
Hajiya ta yi salati. Tana mamakin ƴan uwannata, idan
kuma ta tuna wasu abubuwan da suka wanzu a baya na
irin rashin jituwarsu a wasu lokutan matsayinsu na ƴan
uba, sai ta ga fiye da hakan ma zai iya afkuwa. Haɗin kan
ma da yanzun ake yi da iyalinta tasan bai je koina ba.
Yaransu dai gashinan sun fi su hankali.
"Biri ya yi kama da mutum, Allah Ya kyauta."
Ta furta a fili ranta na zafi. Munir ya amsa da amin.
***
A bangaren Ramlat kuwa, daga Zulaihat har Rafee'ah
zagin Chairman suke su na ƙarawa. Hunainah dai tausayin
Ramlat ta ke ji sosai.
"Kema kin so hakan ta faru, ai kinsan babu yanda za'ayi a
zubamaki ido. Ruwan ido ne ko me? Don ba za ki ce ba ki
da manema ba. Korarsu kike kin ƙi ba kowa fuskar fitowa,
daga samarin har masu auren da dattijai. Ai gashinan ana
neman yi miki bita da ƙulli."
Fadin Rafee'ah dake jin kamar ta shaƙe Ramlat tsabar
takaici. Ta furzar da bacin ran ta hanyar dakawa ɗiyarta
Daddy tsawa ganin kokawar da suke da kanwarsa Afrah.
"Uhum, kema dai Rafee'ah kya faɗa. Ai tunda haka ta
zaɓa sai ta zauna a cuceta. Koda dai watakila za ta iya
tunda ba yau farau ba."
"Ba yau farau ba? Meyasa abinda ya wuce ba za ku bar
tayarwa ba? Meyasa ku ka riƙi abinda na aikata ku ka
kasa yimin uzurin kasancewata cikin ajizai kamar ku?"
Ramlat ta furta da duban Zulaihat. Su kansu ba wai da
wata niyyar abin ke tasomusu ba, sai dai a lokuta irin haka
idan ta ƙona ransu, takan motsa musu da abinda ya wuce
ɗin.
"Anti Hunainah ki zo inji Uncle."
Daddy wanda ya fita ya shigo yana faɗi iyakar ƙarfinsa.
Hunainah ta miƙe ta fita don yin sallama da mijinta.
"Har maganar ta kai ku kasa dannewa a gaban Hunainah?"
Cikin karyewar zuciya Ramlat ta furta.
"Hum ai shikenan. Allah Ya kyauta."
Rafee'ah ta faɗi tana mai miƙewa ta fice daga ɗakin.
Sosai Zulaihat ta fuskanci ƙanwarta.
"Ya kamata ki nutsu ki yiwa kanki faɗa Ramlat. Ke ba
yarinya ba ce, kin taɓa aure kin kuma hayayyafa, ba
girmanki bane a soma ƙirgamaki aure wannan ne yasa
gwara ki watsar da komai ki fuskanci rayuwa tun lokaci ya
ƙuremaki. Da ki yi auren jeka na yi ka, gwara ki dau dogon
lokaci ki auri wanda za ki zauna da shi har mutuwa ku
rayu. Idan har ba ki tsaida wani kin kawo matsayin miji ba,
kina ji kina gani za'a ɗaura aurenki da wanda ki ke gujewa.
Na fadamaki ki nutsu ki san me kike. Ki kuma haɗa da
addu'a, za mu tayaki."
Ramlat ta gyada kai tana jin wani sassauci na ratsa
zuciyarta. Zulaihat ta fita ta bar ta anan zaune. Shiru ta yi
tana mai ƙurawa hannunta da ya sha lalle idanu, mutuwa
mai tonon silili. Hakan ta ayyana yayinda hawaye nta suka
soma ɗiga.
***
Tafe yake cikin shiga ta alfarma, a gefensa Hajiya
Zeenatu ce tana zabga uban murmushi. Hannuwansu
sarƙe cikin juna.
"Husseini!" Ya ji wata murya ta kwalamasa kira, kusan
lokaci guda suka juya shi da Hajiya Zeenat. A fuskar
Hajiya Zeenatu, tashin hankali ne tsagwaronsa, idan ka
ɗauke Hussein wanda idanunsa suka kaɗa suka yi jazur.
Damƙe hannunsa da Hajiya Zeenatu ta ƙara ya sanyashi
dubanta a hargitse.
"Husseini kai ne?!" Ya juya ga matar da ke tsaye tana
dubansa dakyau.
KARFEN KAFA Chapter 55
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


_*Tafe yake cikin shiga ta alfarma, a gefensa Hajiya
Zeenatu ce tana zabga uban murmushi. Hannuwansu sarƙe
cikin juna. *_
_*"Husseini!" Ya ji wata murya ta kwalamasa kira, kusan
lokaci guda suka juya shi da Hajiya Zeenat. A fuskar Hajiya
Zeenatu, tashin hankali ne tsagwaronsa, idan ka ɗauke
Hussein wanda idanunsa suka kaɗa suka yi jazur. Damƙe
hannunsa da Hajiya Zeenatu ta ƙara ya sanyashi dubanta a
hargitse. *_
_*"Husseini kai ne?!" Ya juya ga matar da ke tsaye tana
dubansa dakyau. *_
_*"Kar ka je gareta! Zo mu tafi!" *_
_*Hajiya Zeenatu ta furta iyakar karfinta. Matar na jin haka
ta taho gadan-gadan da zummar nufar Hussein kai tsaye
tana fadin. *_
_*"Ni ce Husseini! Dadarka ce! Ka manta ni?" *_
_*Ba ta kai ga ƙarasawa ba ta ci uban tuntuɓe za ta faɗi.
Sai dai caraf aka riƙeta. Hussein ya dubi mai shi, mace ce
cikin fararen kaya. Daidai sadda Hajiya Zeenatu ta soma jan
hannunsa, hawaye yake fitarwa yana dubansu da wacce bai
san ko wacece ba. Caraf aka riƙe hannunsa, dole suka
tsaya cak. Fuskar Ramlat ya gani na wani haske da kyalli,
murmushi ta ke yi madadin kukan da Dada da kuma shi
suke yi, ta ɗago hannunsa ta sanya a cikin na Dada ta
matse su. *_
_*"Har abada babu wani ko wata da zai ƙara shiga
tsakaninku." *_
_*"Ƙarya kike!" Hajiya Zeenatu ta furta tana ihu. *_
***
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!"
Ya furta a fili yana maida numfashi kamar wanda ya yi
tsere, jikinsa gumi yake fitarwa duk kuwa da sanyin da ke
a ɗakin. Kirjinsa bugu yake da sauri-sauri. Ya kai duba ga
makwancin Hajiya Zeenatu. Bacci take ta lulluɓe har kai
da bargo. A hankali ya dauki wayarsa a gefen gado ya kalli
agogo, biyar saura mintuna, tabbacin Asuba ce. Don haka
ya mike yana juyayin mafarkinsa.
'Dada?' Ya maimaita a zuciyarsa yana juya sunan, yana da
wata mai suna Dada? Kuma a ina? Tunani ya yi mishi
yawa har ya ɗaura alwala ya fito, kansa wani irin sarawa
ya ke. Me mafarkinsa ke nufi? Ramlat ya gani, ihun kuma
da Zeenatu ta yi na menene?
Babu mai amsa masa, wannan tasa ya fice daga dakin
zuwa falo gami da shimfida darduma ya yi nafila. Bayan
idarwa ya yi addu'a. Masallaci zai fita, don haka sai ya
koma dakin ya tashi Hajiya Zeenat sannan ya fita. Ta bishi
da kallo har ya fice sannan ta ja tsaki tana miƙa, ta lura
da wani ustazanci da ya soma. Sallah a masallaci ya
daina wuce shi, ita dai tana jin tsoron ibadar da ya soma
maida hankali a kai. Ko ba komai ai ta sani wutsiyar
raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Ƙarfin ikon Allah da addu'a ya
shallake dukkan ƙarfin mai ƙarfi.
Jiki a sanyaye ta miƙe tana tunanin mafita.
'Ku bar ƙasar zuwa wata ƙasar kawai!'
Wani ɓangare na zuciyarta ya shawarceta. Sai dai tana
tunanin ta yanda za ta sa Hussein ya amince da wannan
shawarar da tun ba yau ba ta ke ƙoƙari a kai.
***
Misalin shida na safe, iyalan gidan Alhaji Khalid
Mu'azzam sun fito fess sun sha wanka har da yaransu
idan ka dauke Ramlat da nata yaran ke gidan Muhibbat.
Dalilin yaran ne Ramlat ta yi ƴan soye-soye na snacks da
zasu ci a hanya.
Ta sha adon doguwar rigar atamfa kalar ruwan toka da
sirkin ja da yellow an mata dinkin Bubu. Ta ɗora ƙaramin
mayafi kalar ja a samansa. Murmushi ta ke sai dai
iyakarsa leɓɓanta bai kai ga shiga zuciyar ba. Tunani
goma da ashirin take duk ita daya, rayuwar yaranta, auren
Chairman, soyayyar Hussein da ta ke ji kamar Son Maso
Wani ta ke yi kawai. Wannan ne yasa da safe ta tashi
idanun ƙozai-ƙozai shaidar bacci bai wadaceta ba.
Bayan sun ɗuru a motar da Munir yasa aka hayo musu ta
kasuwa, tana daga can baya tare da yara sai Hunainah a
ɗayan gefen. Ta bude whatsapp, ta gwada yiwa Hussein
sallama sannan ta sanarmasa da tafiyar da za ta yi zuwa
Daura. Daga nan ta sauka online ta kira Amrah suka ƙara
sallama. Ba ta son yi mishi text gudun kada ya faɗa
hannun Hajiya Zeenat.


'Koda shi ne abu na ƙarshe da zan maka, in sha Allah zan
yi Hussein. Zan sulhuntaka da ƴan uwanka.'
Abu na farko da ya faɗo ranta bayan wannan tunani, shi
ne Kawunsa da aka ce yana zama a Kano. Da dabara za
ta nemi cikakken sunansa a wurin Hafsat, sauƙinta ma
unguwarsu ɗaya da kakanninta (Hajja).
Ta toshe kunnuwanta da earpiece tana sauraron Suratul
Maryam tana bi a hankali idanunta a lumshe. Wakokin
soyayya ba ta da muradinsu a lokacin kasancewar ba
karamin ingiza zuciyarta suke yi ba akan Hussein.
Tafiya ta yi nisa, shiru na ƴan sakanni, karatun ya tsaya, ta
duba. Kira ne daga Hussein. Kirjinta ya bada dam! Ta ɗaga
ta yi sallama a hankali tana mai satar kallon su Hajiya,
hirarsu suke yi na dangi yayinda Hunainah ta rufe kanta da
mayafi alamun bacci ya ɗauketa ko zai ɗauka, ba ta da
tabbaci.
"Tafiya ba sallama? Ba ki faɗamin ba sai yau?"
Daga yanda ya yi furucin za ka fahimci ɓacin ransa.
Daƙyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login