Showing 72001 words to 75000 words out of 113545 words
Chapter 25 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
sa na yi
yunkurin kashe ki ba. Duniya aka kwaɗaitamin, ni kuma na
karɓa da gaggawa ba tare da tunanin abinda zai je ya
dawo ba. Ina neman gafararki. Ki yafemin domin Allah
Ramlat. Wallahi a yanzu haka na tsani kaina. Ba ni da
kwanciyar hankali daidai da kwayar zarra. Ki yafemin ko
zan samu ganin haske a rayuwata da kuma mafarkaina.
Na gode.*_
_*Halima Shehu.*_
Ajiyar zuciya ta saki sannan ta ninke takardar, a hankali ta
sanya bayan hannu ta share hawayen saman fuskarta. Ba
ta taɓa kawowa Hajiya Zeenatu ce ta sa Halima kasheta
ba. Sai dai tayar da zancen ta san ba shi da amfani, ta bar
wa Allah komai.
Ta ƙurawa takardar idanu sai kuma ta yi murmushin yaƙe
ganin cewar Halima ba ta da masaniyar ita ta jima da
yafemata ma. Gefen dirowar gadon ta buɗe ta cilla.
"Mami! Mami!"
Ansar ne ya shigo hannunsa riƙe da wayar Hajiya yana
game.
"Wai Hajiya ta ce ki zo, ga Baba Dakta ya zo."
Ta ji kirjinta ya buga. Ta amsa da toh sannan ta mike ta
yafa mayafin doguwar rigar da ke jikinta. Hajiya na zaune
ta sha lulluɓi su na ɗan taɓa hira. Ta karasa ta durkusa ta
gaidashi. Ya kalleta da fara'arsa. Ta mike ta koma kicin ta
kawomishi ruwa da lemu. Sannan bisa umarnin Hajiya, ta
ja yaran zuwa ciki don su yi magana.
Hankalinta ya kasa kwanciya a dakin, zirga-zirga kawai ta
shiga yi, ganin an kwashi mintuna yasa ta kasa hakuri sai
da ta ɗan kasa kunne. Ta ji Hajiya da na fadin.
"Ai wannan ba a bukatar jin ta bakina ko ita Ramlatun.
Ramlatu da Amrah duk daya ne. Dukkan hukuncin da ku ka
yanke a kanta nasan ba za ta taɓa yin da na sanin zaɓinku
ba in sha Allahu. Balle kuma dama akwai fahimtar juna
tsakanin yaran. Ni dama hankalina ya fi kwanciya da shi
tunda ko ba komai ba wannan ne aurensa na farko ba.
Allah Ya sanya alheri. Ya sa ayi muna raye."
Ramlat tuni ta ji wani gumi na tsastsafo mata, kirjinta ya
tsananta bugu, ta ji Baba Dakta na kara godiya da yiwa
Hajiyar addu'a. A karshe ma yake batun zai je takanas can
Yakasai ya ga su Kawu su yi magana. Gwuiwa a sake ta
juya ta koma saman gadon, Affan ya damu da kai ƙarar
Ummi ta ɗauki wayar Mamin, ba ta san sadda ta
dakamasa tsawar da dukkan yaran sai da suka tsorata ba.
Ta ja guntun tsaki ta riƙe kai, salati kawai ta ke yi da
addu'ar Allah Yasa hakan ya zamemata alheri. Ta dafe
saitin kirjinta, ba ta taɓa zaton lamarin aurenta da Baban
Hanif zai zo mata da yanayin ɓacin rai kwatankwacin na
Hilal ba sai yanzu. Sai dai wannan karon alƙawari ta yiwa
kanta, ko me zai je ya zo, za ta rungumi zaɓin iyayenta da
hannu bibbiyu.
"Ki godewa Allah da zaɓinSa. In sha Allah jikina yana bani
wannan aurennaki shi zai zama na dindindin duk kuwa da
cewar sai an yi hakuri kuma an kai zuciya nesa saboda
kananun maganganun da kan iya tasowa."
Wannan shi ne kadai abinda ta ji a bakin Hajiya, nan ta
tuna wayarta a safiyar yau da Baban Hanif, inda cike da
damuwa yake sanarmata irin tashin hankalin da yake
fuskanta daga iyayensa game da aurenta da ya yi niyyar yi.
Labari ya zo musu cewar ta taɓa yunkurin kisa a aurenta
na farko. Wannan ne dalilin da yasa gaba ɗaya a kwanakin
ta kasa gane inda ya nufa.
Ramlat ta dubi Hajiya karo na ba adadi tun zamanta a
falon, waya Hajiya ta shiga yi da Munir, ta kasa kunne
amma a karshe ma sai Hajiyar ta miƙe ta nufi ɗaki. Ranta
sai ya soma ɗan baci. Ko ba komai ba wannan ne aurenta
na farko ba, ya kamata ta san wa za ta aura ai. Hakan
kuma bai nufin jayayya za ta yi da su. Ko kadan, ta rantse
koma waye ta yarda kuma ta amince da aurenta da shi,
kawai dai tana son sanin waye. A gefe guda kuma jikinta
yana ba ta cewar ta yi BANKWANA DA HUSSEIN.
Bankwana na har abada.
"Mami! Wayarki."
Ta sa hannu ta karɓa a hannun Ummi. Baban Hanif din ne
kuwa ya kira don haka ba ta jira ya kara ba ta bi bayansa.
Sai da ta shiga daki ta rufe kafin ta amsa sallamarsa.
Bayan sun gaisa a gaggauce ta ce.
"Kun yi magana da Baba Dakta ne?"
"Eh ya kirani dazunnan da yamma, mun yi magana sosai
da shi. Labari ya zo maki kenan?"
Ta kasa magana kawai sai ta kashe wayar gaba daya, kai
ta dora saman gwuiwar ƙafafunta ta shiga rera kuka.
Kukan jin zafin Hussein da ya kasa kallonta matsayin
masoyiyarsa. Ta gasƙata cewa yanzun babu wani abu da
zai ƙara shiga tsakaninta yanzun. Ta ji kuma ta hakura da
zaɓin Allah. Dakyar ta iya miƙewa ta faɗa ɗakin yaranta,
kowannensu ta gyarawa gado don yanzun ta sauyamusu
da gado kanana na yara kowanne da na shi. Ta kakkaɓe,
ta ba su umarnin kwanciya. Kasancewar sun saba da
baccin wurin hakan yasa su na kwanciyar bayan ta sa sun
yi addua, bacci ya ɗauke su.
Ta yi shiru tana kallonsu bayan ta gama kwashe shirgin
kayan da suka zubar a ƙasa ta ninke kayan sif din da ya
lalace. Aliyunta ne ya faɗomata, zuciyarta ta ƙara karyewa,
nan ta shiga rera wani sabon kukan. A karshe don kanta ta
rarrashi zuciyarta ta share sannan ta fita ta ja musu ƙofar.
"Ashe AlHassan ya zo garinnan?"
Ta dubi Hajiyar da le tambayarta, robb ta ke faman
shafawa a ƙofofin hancinta.
"Ban sani ba wallahi. Yaushe?"
Murmushi Hajiya ta yi.
"Ai da Husseini muke waya, sai ya ba shi muka gaisa. Wai
jiya-jiyan nan. Amma ya cemin zuwa gobe zai shigo in sha
Allahu."
"Allah Ya nunamana."
Ta fadi a ɗan gaggauce don ji ta ke yi kamar ta fashe da
wani kukan.
Hajiya na lura da ita kuma abin na ba ta mamaki amma ba
ta ce uffan ba. Ta san dai idan ma da wani abu na daban
a zuciyar Ramlatun, dole yanzu ta yi kokarin kawar da shi
tunda dai bakin alƙalami ya riga da ya bushe.
***
Tun sadda Hajiya ta shaidamata cewar ana nemanta a
Yakasai, Kawunnanta, kirjinta ke bugu da sauri. Affan
wannan karon maƙalewa ya yi zai bi ta, dole ta shirya shi
suka fita tare. Adaidata Sahu suka hau kasancewar
motarta ta samu matsala.
A hanyar ma babu cikakkiyar nutsuwa tattare da ita
sakamakon tunanin abinda zai biyo baya da ta sa a rai.
Kiran ko kusa bai ba ta mamaki ba, ta san dama tunda
har aka ce an mata miji to komai ma za ta gani. Har dai
suka iso ba ta jin ta ba Affan kwakkwarar amsar
tambayoyinsa na shirme da ya ke mata. Karshe ma da ya
dameta cewa ta yi za ta bar shi a cikin Napep din dole ya
ja baki ya yi shiru.
Ɓangaren Baba Dije ta soma shiga. Bayan sun gaisa ta ce.
"Ina tayaki murna ƴarnan, kin yi goshi wannan karon ba
shakka. Allah Ya sanya alheri ya nunamana lokacin."
Ta rasa yanayin da ta shiga. Ta kasa amsawa hakanan ta
kasa cewa komai don haka kawai sai ta mike ta fita tana
murmushin yaƙe.
"Ayiririri!"
Guɗar da ta ji yasa ta waiga, Baba Hajara ce yayar
Hajiyarsu. Su uku ne kadai mata a wurin Hajjar, Baba
Hindu, Baba Hajara sai Hajiya. Mazan kuwa su uku, Kawu
Jamilu, Kawu Bello da Kawu Sunusi, su ne manyan maza
a ɗakin.
Jiki a sanyaye ta gaida ta kafin ta karasa ɗakin Hajja
itama Baba Hajara na daga bayanta.
Hajja ce zaune tana shan fura, tana ganin Ramlatun itama
ta saki fuska.
"Kishiyar ce a tafe kenan? Sannu da zuwa."
Ita dai ba ta ce uffan ba, Affan ya karasa a guje ga Hajja.
Zama ta yi gwuiwa a sake kafin ta maida hankali ga Baba
Hajara.
"Wai Baba lafiya?"
Baba Hajara ta zauna tana dariya, ba ta kai ga magana ba
Hajja ta katse ta.
"Na rabaki, idan ba so kike tarihi ya maimaita kansa ba. Ki
bari ta ji komai daga bakin Ubanninnata. Ai ba abinda
zamu ce ga Dakta (Baba Dakta) sai godiya da fatan alheri.
Allah Ya biyashi da aljanna. Yanda yake nunamaku kulawa
kamar ƴaƴan da ya haifa a cikinsa, Allah Yasa aljanna
makoma. Na ji ma ance ya kawomaku kayayyakin abincin
azumi, to nan ma haka ya aikomin. Wannan bawan Allah
sai fatan alheri da fatan Allah Ya jiƙan iyaye."
Baba Hajara ta amsa da amin, itama Ramlat ta amsa ta
hanyar motsa lebbanta amma dukkan wata gaɓɓa ta
jikinta ta yi sanyi. Can kuma sau ga shigowar saƙo.
Hussein ne. Ta bude hannunta har rawa ya ke don yanzu
ta kasa fahimtar komai.
_*"Ban yarda da dukkan wani so da za'a yi shi kafin aure
ba. Ban kuma yarda akwai kulawar da namiji zai yiwa
mace ba da za ta kere kulawar miji ga matarsa. So da
kauna na gaskiya ya fi ma'ana idan aka zama mallakin
juna. Ina taya junanmu murna."*_
"To wai me yake nufi?" Ta tambaya a fili bayan ta karanta
ya fi sau biyar amma ba ta gane komai ba.
"Wa kenan?" Hajja da Baba Hajara har suna haɗa baki
wajen tambaya. Ta ma kasa cewa uffan sai kai da ta
girgiza tana sharar gumi ga kwalla cike a idanunta.
"Idan ma za ki saka ranki a inuwa tun wuri gwara ki sanya
don wannan karon na tabbatar wanda za ki aura ba fetur
ba, Allah Yasa tankin mai gaba daya za ki zazzaga maku,
zai yarda ku mutu ƙurmus! Sawun giwa ya take na raƙumi!"
Hajja ke wannan sababin ta karashe da kurɓar furarta ta
bar Baba Hajara da dariya. Ita dai Ramlat ba ta ce komai
ba sai hawayen da ta shiga sharewa, gaba daya gaɓoɓin
jikinta sun yi sanyi, yanzun kuma abin haushi ya ke bata.
"Yaya Ramlatu ki zo inji Kawun Zaure."
Wato Kawu Jamilu kenan wanda shi hanyar shiga
sashinsa na daga wurin zauren gidan, ai ba ta ma jira
Hauwa diyar Kawu Sunusi ta karasa faɗin saƙon ba ta yin
zumbur ta miƙe tsaye har wayarta na faɗuwa amma ba ta
ko damu da ɗauka ba. Tana ji Hajja na fadin.
"Kuma yarinya ta dawomin daki da baki kamar gonar
auduga sai na yi ƙasa-ƙasa da ita. Maza Affan bani
wayarnan idan mijinnamu ya zo sai ya siyamata wani."
Tana jin dariyarsu amma babu wanda ta tanka asalima
baki ta turo ta ɗan ja guntun tsaki tsabar ɓacin rai. Haka
ta dinga tafiya har sashin Kawu Jamilu, duk a zatonta shi
kadai ne, sai ganin sauran Kawunnan da ta yi zaune ƙasan
bishiya suna taɓa hira. Ta karasa gami da durkusawa ta
kwashi gaisa. Suka amsa fuska a sake duk da cewar
kanta a ƙasa yake amma sautinsu ya nuna hakan. Sai da
aka gama gaisuwar da ɗan barkwanci kafin Kawu Jamilu
ya yi gyaran murya ya soma magana.
"Toh Ramlatu, abu na farko shi ne mu miƙa godiyarmu ga
Ubangiji domin Shi ya yi mana dukkan ni'ima. Ya kuma so
ki da dukkan rahma da mu ɗin gaba ɗaya. Alhamdulillah."
Ya ɗan ja numfashi gami da gyaran murya sannan ya ci
gaba.
"Kamar yanda ki ka ji daga bakin mutanen gida, abin alheri
ne ya sameki. Babanki Dakta ya yi maki zaɓi bisa damar
hakan da kika damƙa maki. Kar kuma hakan yasa ki yi
zaton cewa shi da kansa ya haɗa auren, aa, shi yaron ma
asali tun ana zancen aurenki da Dikko ya tunkari Baba
Daktan da batun aurenki sai dai Baba Daktan ya ba shi
hakuri ya kuma sanarmasa da batun Dikko, a karshe ya yi
mishi kwatancen gidannan ya ba shi lambar wayar
Kawunki Bello cewar yana iya zuwa nan wurinsa ya
faɗamasa ko Allah Zai sa a dace. Da yake shima yaron
nada hankali ya ce aa babu komai, ya yarda Allah bai
kaddara ke din rabonsa ba ce. Ba ya son ya yi nema cikin
nema. Wannan ne dalilinsa na janyewa bayan ya nemi
alfarmar su bar maganar tsakaninsu. Yanzun ma da kika ji,
magana ce ta kawo magana shiyasa ya faɗamana shi
Babannaki. Sai kuma cikin ikon Allah lamarin aurenki da
shi Dikko ya lalace, anan ne kuma bayan kin bar wuƙa da
nama a hannun Daktan, ya ba wancan yaron iznin turo
nashi magabatan bayan shawarar da ya yi da mu kuma
muka amince. Alhamdulillah, Ramlatu ke ba yarinya ba ce,
mun kuma sani, yanzun kin fi baya hankali. Kin kuma ƙara
hankaltar rayuwa. Mun sani, wannan karon ba za ki ba mu
kunya ba in sha Allahu."
Zufa sosai ta ke fitarwa, ta hadiyi miyau mai ɗaci, ba ta
bar ambaton Innalillahi a ƙasan ranta ba har zuwa sadda
Kawu Jamilu ya miƙomata damin kudi ƴan ɗari biya-biyar
a baƙar leda bayan ya warware ledar ya turo kudin
gabanta.
"Wannan ne kudin aurenki, dubu ɗari gashinan. Juma'a
mai zuwa cikin yardar Allah za'a ɗaura aurenki da
HUSSEINI MODIBBO. Ina ce haka sunan yake ko?"
Ya karashe yana duban yan uwansa da dariya, suka dara
lokaci guda.
"Hakayake Yaya." Kawu Sunusi ya bada amsa.
Ta rasa me za ta ce, ta kuma rasa me za ta yi, a zaune ta
ke amma jiri ta ke ji. Kanta ya yi wani irin sarawa, lokaci
guda ya shiga ciwo. Hawayen da ta tsayar a ɗazun, suka
ci gabada kwaranya su na ɗiga saman k
rafar ɗari biyar biyar din da Kawu ya ajiyemata. Wa ya
faɗamusu sonta yake?
KARFEN KAFA Chapter 68
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
'Me yake nufi da ni?' Ta jefawa zuciyarta tambayar da nan
da nan ta samo amsar da ta ji wani mugun ɗacinsa.
Hussein na nufin ra'ayinta ba komai ba ne, yana nufin
koda ba ta sonsa ta rayu da shi. Ko kuma dai daga saƙon
da ya turomata yana son ta fahimci ya gane tana sonsa
amma ya dinga basarwa. Nan da nan ta ji wani haushinsa
ya mamaye zuciyarta. Ta ci alwashin sai ta rama abinda
ya aikata gareta, ba za ta taɓa yin musu a aurensa ba,
amma ta rantse sai ya gane shayi ruwa ne.
"Allah Yasa hakan ya zamemin alheri." Ta ba Kawu amsa
a hankali, gaba daya suka amsa da amin cike da jin dadi.
Suka sanya mata albarka a karshe suka sallameta.
Mikewa ta yi bayan ta share hawayen yanda ba za su gani
ba, ba tare da ta ɗau kuɗin ba ta bar wajen. Kawu Sunusi
zai magana Kawu Jamilu ya katseshi da zummar za su
damƙawa Hajiya.
Ba ta wani jima cikin gidan ba ta yi musu sallama sai dai
ba su fahimci komai ba don ta ɗan saki fuska kamar ba
ita ba.
Koda ta koma gidan, ba abinda ta nunawa Hajiyarta.
Wannan ya kwantar da hankalin Hajiyar don dama tun fitar
Ramlatun ta ke cikin zullumin ta yanda za ta karɓi lamarin.
"Idan kin sauya kayan sai ki fito mu shiga kicin, na
fadamaki yau Hassan zai shigo a gaisa."
Maganar Hajiya ta katse yunkurinta na shigewa ɗaki da ta
yi niyya, ta juyo ta amsa da toh bayan ta haɗiyi miyau mai
ɗaci.
***
Hajiya Zeenatu ta shigo falonta gaba daya jiki a sanyaye,
likita ya duba ta amma ya ce bai gane komai ba, karshe
aka haɗata da tests kala-kala akan ta yi ta kawo
sakamako a gani. Ranta gaba daya a jagule ga wani jiri-jiri
da ke ɗibanta. Turus ta yi ganin mutum zaune a falon. Ta
daure ta shigo da fara'ar da bai kai zuci ba. Suka dubeta
gami da amsa sallamarta.
Hussein ne fuskarsa cike da wani farin ciki sai AlHassan
dake zaune yana amsa waya Madam dinsa Kausar,
ganinta yasa shi yin sallama da ita.
"Ah, ɗan uwanmu zuwa babu sanarwa?"
Ya yi murmushi, sai yanzun dai ya zo gidan dan uwannasa
don haka ba su hadu da Hajiya Zeenatun ba sai a yau,
amma a Hotel ya sauka tare da Kawunsu Adamu wanda
shi a yau da safe ya juya ya kama hanyar Adamawa.
"Hajjaju, Allah Ya huci zuciyarki. Nima zuwan ne ya
tasomin babu shiri. Aiki na zo yi daga kamfaninmu na
can. Ko shi Ogannaki haka ya gan ni babu zato ba
tsammani."
Ta yi dariyar yaƙe gami da satar kallon Hussein da ya ɗora
ƙafa ɗaya saman kujera hankalinsa ya koma kan waya
yana zabga murmushi.
"Hakan ma ai daidai ne. Dama kuwa ina da saƙon da zan
bayar a kaiwa Ɗiyata. Gwara da Allah Ya kawoka."
Ya yi dariya yana gyara zaman gilashinsa.
"Ba ki da matsala. Tana godiya."
Daga haka ta maida duba ga mijinta.
"Yallaɓai barka da hutawa."
Ta fadi da wani irin shagwaɓa wanda ya ba AlHassan
dariya, sai dai ya haɗiye kawai ya miƙe.
"Bari na ɗan amsa waya." Yana kaiwa nan ya fice zuwa
farfajiyar gidan, wannan ya ba Hajiya Zeenatu damar
ƙarasowa ta zauna gefen Hussein. Ya ɗan dubeta da
kulawa.
"Ya jikin naki?"
Cike da damuwa ta karya wuya.
"Likita ya duba ni, ya ce ba zai gane taƙamaiman
matsalar ba sai an yimin gwaje-gwaje. Yanzu dai haka ya
ban gwaji zuwa gobe zan koma mu gani. Amma na fi
kaunar na hakura idan mun je London sai a yimin magani
sosai."
Ya gyaɗa kai yana murmushin da ke ƙara tafiyar da imanin
Hajiya Zeenatu a kansa.
"Saurin me ki ke? Ita lafiya ta fi komai ai. Ki kwantar da
hankalinki. Tunda har kika ga na dakatar da aiki toh hakan
na nufin na shirya koyaushe ne ma mu bar ƙasar. Abinda
ya fi yanzu ki je goben ki yi gwaje-gwajen har a gano
matsalar a shawo kanta. Gwara ki ɗan samu sauki sai mu
wuce. Amma fa sai mun fara biyawa Adamawa kinga su
Dada kun gaisa."
Ko ɗarr ba ta ji ba, a wautarta gani ta ke har a sannan
babu wanda ya gane da hannunta a ɓatan Hussein.
"Yanda ka tsara hakan za'a yi Ranka ya daɗe."
Kauda kai kawai ya yi bai ce uffan ba, ta mike ta haye
sama. Ya bi bayanta da kallo, sai kuma ya yi murmushin
mugunta. Shi kadai ya san me ya bar wa zuciyarsa.
Tabbas sai Hajiya Zeenatu ta kusa haukacewa idan ta
gano taƙamaiman shirin da ya ke yi.
Wayarsa dake ringing ya duba. Hisham ne. Murmushi ya
yi don ya san labari ya isa kunnensa.
"Kai dan iska ne fa! Wai me nake ji daga bakin My
Princess? Dagaske kai ne ka kai kuɗin auren Ramlatu?"
Lumshe idanu ya yi, sunanta kaɗai idan ya ji sai tsigar
jikinsa ya tashi. A hankali ya shafi sumar kansa.
"Mamaki ka ke yi? Ba haka ka ke so ba?"
Dariya Hisham ya yi.
"Haka nake so, sai dai ka rainamin hankali fa. Zan rama
amma. Kar ka yi tunanin zan tayaka campaign."
Taɓe baki Hussein ya yi kamar yana kallonsa.
"Campaign after marriage? Ni zan yi abina dama."
Hisham ya ɗan dara don shi abin kam dadi ya yi mishi ba
kadan ba. Addu'a ya yi da fatan alheri. Hussein ya amsa
da amin kafin su yi sallama. Agogo ya kara dubawa, da
sauran mintuna a kira sallar Magriba. Ya ƙagu ya ganshi a
gidan su Ramlat. So ya ke ya sanyata a idanunsa. Bai zaci
za ta ga saƙonsa ta shareshi ba, abin ya ba shi mamaki.
Hakan yasa ya ke son zuwa ganinta da kansa.
***
Kawu Modibbo rai a ɓace ya ke amsa wayar ƙaninsa
Adamu.
"Me ya kawoka Kano? Wato Adamu har wuyanka ya yi
kaurin da za ka shigo inda nake ka kasa nemana? Idan
kuma aka yi magana sai ka nuna ka fi uban kowa riƙon
zumunci ko?"
Kawu Adamu da mamakin yanda Modibbo ya san da
zuwansa garin Kano ya ba da amsa ta wayar.
"Wa ya fadamaka na je Kano?"
"Ɗanka Yahaya muka yi waya ya cemin ka shigo Kano tare
da Hassan. Ko karya ya ke yi?"
Ganin yanaamsawa a zafafe ne yasa dole Kawu Adamu ya
sauko ya shiga bada hakuri da fadin.
"Wani ɗan uzuri ne ya shigo da