Showing 93001 words to 96000 words out of 113545 words
Chapter 32 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
a nashi, ya
kara damƙewa yana dariya.
"Wallahi sai na ɗaga ki cak mu shiga har wajen Dada. Kin
san zan iya ko?"
Dole ta hakura ganin akwai ma'aikata a farfajiyar gidan ta
kuma tsorata don ta san halinsa dagasken yake.
Dada ta yi farin ciki matuƙa da ganinsu, ita kuwa Ramlat
wacce ta samu dakyar ya saki hannunta, kunya sosai ta ke
ji don ma Allah Ya taimaka baƙi duk sun watse, wasu yau
da Asuba suka wuce.
Anan wurin Dadar ya bar ta ya fice wurin AlHassan.
***
KANO...
* DA SAURAN RINA A KABA..! *
KARFEN KAFA Chapter 74
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Hajiya Batool ta zabga uban tagumi tana kallon
Aminiyarta, ba ta san ta inda za ta fara magance mata
matsalarta ba alhalin ita kanta yanzu cikinsa ta ke. Gaba
daya ɗanta ya kwashi matarsa sun bar garin sun koma
Abuja da zama. Waya ta kira sai ya ga dama yake ɗagawa
balle a kai ga aike. Komai na rayuwa ya sauyamata,
kasuwancin ya ja baya babu albarka ciki.
Hajiya Zeenatu wacce ta gama kai wa bango da shirun
Batool, ta kundumar ashar da faɗin.
"Wannan wane irin wulakanci ne Batool, na kawomaki
kukana ina neman mafita shi ne tsabar wulaƙanci ki ka
shareni ki ka maida ni wata banza?! Hussein ne fa, kin fi
kowa sanin yanda nake son Hussein amma har na gama
ba ki labarin cin kashin da ya yimin gaban yan uwansa ki
kasa jajantamin?!"
Tana maganar tana faɗa rai a ɓace. Hajiya Batool ta
sauke ajiyar zuciya.
"Me zan maki? Wane irin nusarwa ce ban maki ba don
Allah? Amma ke makahon son yaron nan ya sanya ba kya
ji ba kya gani, ai gashinan ya nunamaki shi na zamani ne!"
Hajiya Zeenatu ta yi kwafa, ba abinda ya faɗomata a rai
sai cin mutuncin da ya yi mata a farkon haɗuwarsu, da
gaskiyar Batool da ta ce makahon so ya rufe idanunta. Ta
sauke ajiyar zuciya.
"Naji, koma me ya faru, ina da hannu a ciki. Amma kuma
kin san ba zan zauna haka ba ko? Kin san sai na rama? Ki
tashi mu shirya mu leka wurin Gora. Mene a ciki? Zan
durkusa na ba shi hakurin laifin da na yi mishi idan ya so
ya samarmana mafita."
Hajiya Batool ta yi shiru, itama fa yanzun tana da bukatar
hanyar da za ta bi a karkato da hankalin ɗanta gareta, ta
kuma amince idan ya dawo ko wacece ya aura idan har
hakan zai yiwa Fa'iza ciwo. Abinda ma ta lura da shi,
itama kanta Fa'iza tama tsubbace-tsubbacenta shi ne
dalilin da yasa ta fi karfinta. Sauke ajiyar zuciya ta yi, ta
tuna kowacece Fa'iza, dama tun can ƴan gidansu ba
wata cikakkiyar tarbiyya ce da su ba, ganin irin arzikin da
ubanta ke da shi matsayinsa na tsohon minista ya sanya
tun ɗanta bai wani ba soyayyar da Fa'izar ke mishi
muhimmanci ba, har sai da ta yi yanda ta yi ta tursasashi.
Yanzun gashinan tana girbar abinda ta shuka.
"Na yarda muje. Idan ma bai sauraremu ba, za yiwa
Mariama waya mu wuce Nijar kawai. Na fi yarda da aikin
buzayennan ma."
Da wannan suka shirya suka fice wurin Gora.
***
ADAMAWA..
Dada ta dubi Ramlat cikin nutsuwa ta ce.
"Kinga abin Allah ko? Ba ya kyale azzalumi, shiyasa duk
abinda aka dage da kai kuka gareShi, watarana zai shuɗe
ya zama tarihi. Ba wanda ya fi ban mamaki a lamarin sai
ɗan uwana Modibbo, ban yi tsammanin ƙiyayyar ta kai har
haka ba, amma ina nan inda nake, shiru ma magana ce.
Allah ne zai maganinsa don nikam ban isa nayi ba. Ba na
jin wannan karon zan iya yafemishi wannan zaluncin da ya
yimin ni da yarana. Duk yanda zan so na ji alaƙarsa da
matarnan, zan jira har zuwa lokacin da zai kawo kansa
garemu."
Hafsat da ke zaune itama sai ta ji jikinta ya kara sanyi,
wayarta ta kara kalla, wani saƙon ne na Taheer ya kara
faɗowa, duka dai ban hakuri ne da nuni da yake mata
cewar laifin wani ba ya shafar wani. Kalaman soyayya
zafafa ya ke jifanta da su, ta yarda so ba karya ba ne, tana
son Taheer sosai, duk da son ta ke mishi bai kai wanda
shi ya ke mata ba, amma dole za ta sanyawa zuciyarta
dangana. Ta san babu ta yanda aurensu zai yiwu. A
hankali ta mike ta zame daga falon ta shige ɗaki, hawaye
ne ya tahomata sai dai dole ta haɗiyeshi. A yanda ta ke da
zafi, ba ta yi zaton soyayyar Taheer zai russunar da ita har
haka ba har ma ta ji inama ɗan wani gidan ne daban ba
gidan Kawun ba.
Ɓangaren Ramlat itama haka ta koma sashinta cike da
tunane-tunane, ta kara ganin girma da ƙimar uwar
mijinnata. Tabbas mahakurci mawadaci. Kai tsaye ta
shiga gyaran duk inda bai ba ta ba, sai da ta tabbatar
gidan ya kimtsu babu sauran dauɗa da kayan datti a kicin
sannan ta kara gyara jikinta ta shirya cikin doguwar riga
ƴar kanti milk mai adon duwatsu. Sam ba shi da nauyi. Ta
feshe ko'ina na jikinta da turare. Saman doguwar kujera ta
shimfide ta zurawa ƙaton enlargement na hoton mijinta
idanu. Murmushi sosai ta shiga yi tana tuna kalamansa da
ma saƙonni da dama waɗanda ya isarmata a daren jiya. A
hankali ta lumshe idanunta wani farin ciki na mamayeta,
wani lokacin ta kan ji kamar mafarki, wai yau ita ce a garin
masoyinta kuma matsayin matarsa. Ta jima cikin tunani
kafin wani bacci mai dadi ya kwasheta.
Ya jima da shigowa gidan, sai dai yana sashen Dada su na
tattauna. Koda ya karaso gidan, ya isketa tana bacci
murmushi kawai ya yi, ciki ya karasa ya rage suturar
jikinsa ya ɗan watsa ruwa don ba laifi garin ana ɗan zafi.
Gajeran wando three-quarter ya sanya da yar shirt marar
hannu, gaba daya ƙirarsa ta bayyana muraran. Koda ya
fito ya ci karo da Hafsat da ke faman sallama amma
gwanartasa ba ta ji ba. Kofar ya bude ya sanya yatsa a
bakinsa yana mata alamar ta yi shiru, murmushi kawai
Hafsat ta yi hango dalilin, Adda Amal ke bacci. Hanya ya
ba ta ta karasa kan tebur ta ajiye kwandon abincin ta juya
ta fice ya rufe ƙofar a hankali. Cikin falon ya dawo ya
zauna saman kujerar da ke fuskantarta, waya ya ke
amsawa da Hisham sai dai rabin hankalinnasa yana ga
Ramlatun yayinda ya ke kallon sauka da hawan
numfashinta. Harma da yanda rigar ta fiddo surarta fa yi
mata kyau. Wani lokacin kuma ya maida kai ga
ƙawatacciyar fuskarta da kallon ke sanya shi nishaɗi.
A jikinta ta ji ana kallonta, a hankali ta soma kikkifta idanu
kafin ta budesu kaɗan, ganinsa zaune yana kallonta ya sa
ta ware duka dara-daran idanun kafin ta mike zaune ba
shiri. Kunya ta sa ta mikewa sum-sum don ta shiga ɗaki ta
ƙara wanko bakinta, sai dai tana zuwa gefensa ya yi
azamar riƙota ta faɗo cinyarsa ta zaune ɗabas. Ta
sunkuyar da kai yayinda shi kuwa wayar yake amsawa
amma hannunsa guda ya kasa tsayuwa wuri guda, karshe
ma zancen kasa fita ya yi yanda ya dace sakamakon
fuskarsa da ya tura a ƙasan wuyanta yana shaƙar ƙamshin
jikinta. Hisham ko fahimta ya yi ko mene? Kawai sai ji ya
yi wayar ta ɗauke don haka ya kalli wayar sai kuma ya
ajiye a gefe yana murmushi, ita kuwa Ramlat da gaba
ɗaya ta rufe idanunta numfashinta na hawa da sauka da
sauri, ta kara yunkurin miƙewa. Ya riketa sosai.
"Wai ina za ki je? Ba ki yi missing ɗina ba."
Kai ta girgiza ta kasa magana. Ya bi bakin da kallo kafin ya
dubi idanu da ta bude a yanzun.
"Kin daina magana ko me? Wani abu ki ke ci?"
Ya maida dubansa ga bakin da take ƙara damtsewa.
Girgiza kai ta yi alamar aa, tana kokarin tashi sai ya ƙara
riketa ya yi murmushi.
"Oh na fahimta, wato daga bacci kika tashi ba kya son ki
yi magana naji wari ko?"
Kunya da takaicinsa ta ji har ba ta san sadda ta
watsamasa harara ba. Ya kara murmusawa.
"Na nawa kuma?"
Ta waro ido.
"Me kake nufi?"
Ba ta san sadda ta yi furucin ba sai kuma ta yi saurin rufe
bakin ta mike a guje ta yi daki ta bar Hussein da yi mata
dariya. Koda ta wanke baki da fuskar sai kunya ta hanata
fitowa falon, ta samu gefen gado ta zauna ta na mai jin
haushin kanta. Yanzu dariyar ma da ya yi watakila don ya
shaƙi warin bakinta ne. Tana nan zaune ya shigo, fuska ta
ɗan haɗe ita a dole kar ya yi mata dariya. Hannu ya
miƙamata yana murmushi. Ta kasa miƙamasa nata, sai shi
ne ya gaji ya ja kamo hannunta ya miƙar da ita ta faɗo
jikinsa har tana take masa kafafu da lausassun tafukan
kafafunta. Goshinsu haɗe wuri guda, ta kankame rigarsa
don ji ta ke kamar za su zube.
"Ko ba ki wanke ba ni ban ji komai ba."
"Uhmm."Abinda ta ce kenan, amma ita dai ta san ko yaya
mutum ya yi bacci to fa sai a hankali.
"Wai idan na riƙe ki me kike ji? Sai naga kina kanne
idanu."
Wayyo kunya, ta buɗe idanun tarr ta dubeshi da harara,
murmushi ya yi don dama kwayoyin idanun yake son gani.
"Kai ka ga haka."
Daga nan ta zame jikinta ta yi falon ya bi ta a baya.
Haushin kanta ma ta ji.
Tana zama ya zauna a gefenta, ta matsa, ya matso. Ta
dubeshi, ya sakarmata murmushi. Kafin ta yi yunkurin
mikewa ya kamata sosai, ya shiga aikamata da sakonni
daban-daban wanda dolenta ta russuna. Sai da ya gaji don
kansa ya matseta a jikinsa yana maida numfashi. Lalubo
kunnenta ya yi bayan ya zagayeshi da harshensa ya shiga
yi mata magana a tausashe.
"Na fi ki mance kaina idan muna tare. Na fi ki rawar jiki da
mazari. Kar ki damu da duk abinda Hussein ya fadi ko
kuma zai fada, haka nake, ina son tsokana ko don na yi
dariya. Ina sonki sosai, ina kaunarki."
Murmushi tayi kafin ta kara shigewa jikinsa, ya kuwa ba ta
kyakkyawan mazauni. Sun ɗan jima a haka kafin su mike
zaune.
"Yunwa fa nake ji." Ya fadi, ta mike, ita kanta yunwar ta ke
ji don tuni abincin safe ya narke.
Sai da ta soma zuba mishi, tana kokarin zuba wani ya
hanata.
"Ba fa na son muna raba plate. Ki fahimta please."
Ta gyada kai.
"Zan kiyaye."
Daga nan ta dauki cokali ta matsa suka soma ci. Bayan
sun kammala ta tattare komai ta kai inda ya dace. Koda ta
dawo shi tuni ya yi daki, alwalar sallar la'asar ya yi. Ya
dube ta.
"Bari na wuce masallaci."
Ta amsa da toh da yi mishi kyakkyawan addu'a sannan ya
fice ita kuma ta kara miƙe ƙafa don har sannan ba ta
samu tsarki ba. Ta sani sai a gobe za ta samu don ita
mutum ce mai ƙidaya kwanakin al'adarta. Hakan na
taimakawa kwarai wajen sanin lokacin farawa da
kammalawa na kowane wata. Wannan yasa a wayarta ta
ke da App mai suna FLO, tana lissafe da kwanakin farawa
da kammalawar period dinta.
Tana nan zaune ya shigo amma fuskarsa ba kamar yanda
ya fita ba, gaba daya a ɗaure. Ya karaso ya zauna bai ko
kalleta ba. Ta ji gabanta ya fadi.
"Sannu da dawowa."
Kai kawai ya gyadamata, hakan ya ba ta tabbacin ba lafiya
ba. Shi kuwa a hanyar dawowarsa ce ya biya wurin Dada,
Hafsat ya tarar kadai a falon tana amsa wayar Taheer har
tana ba shi shawarar ya gwada zuwa neman aurenta
hannun yayyunnata. Wannan ne ya fusatashi, ya kuma
kirata da marar zuciya da ba ta tausayin Dadarsu. Ya
kammala fatattakarta ya kwace wayar sannan ya shigo.
Ramlat gaba daya ta ji damuwa da sauyawarsa don haka
ta yi shahadar miƙewa ta karasa kusa da shi ta zauna. Ta
daure ta kamo hannunsa ba tare da ta yarda ta kalleshi ba
ta ce.
"Ka yi hakuri, ko me aka yi maka, ka zama mai hakuri don
Allah."
Shi kuwa kallonta ya ke kawai. A hankali yanayinsa ya
soma sauyawa, ɓacin ransa ya ragu sosai, ba abinda ya
ke ji sai matukar kaunar kasancewa da matarsa kuma
halaliyarsa. Ita kuwa dagaske bacin ransa ne ya taɓa ta,
ba ta kaunar ganinsa a yanayi irin hakan.
"Toh ya isa, ko su kike ki jefani yanayin da ba za ki iya
magancemin ba?"
Sai ta ji gaba daya ya ba ta kunya, ta dan harareshi da
wasa tana mai zame hannunta cikinnasa, ya yi murmushi
ya zauna sosai yana fuskantarta.
"Yarinyar ce naga alamun ba ta ji, ta yi zurfi a soyayya da
wancan yaron."
Ramlat duka ba ta fahimci me ya ke son cewa ba, ta
tsuramasa idanu cike da neman ƙarin bayani.
"Hafsat."
Ya fadi kai tsaye, nan ta fahimci komai, ta san da
soyayyar Taheer ɗan Modibbo da ita Hafsat din,
tausayinsu ya kamata, ta tabbatar laifin Babansa ya shafi
soyayyartasu.
"Ka yi hakuri."
Haka kawai ta iya cewa don ta tabbata idan ta fadi wata
kalmar bayan hakan, zai iya hucewa a kanta.
Da wannan ta samu suka share zancen inda ya shiga yi
mata bayanin ya soma neman aiki. Ta bishi da addua da
fatan alheri.
***
KANO
Taheer a fusace ya shiga sashin Hajja Fatouma
mahaifiyarsa. Tana kallon yanayin fuskarsa ta ji zuciyarta
ta taɓu, tun sadda ta fahimci irin son da ya ke yiwa ɗiyar
Dada ta san akwai matsala. Kaf cikin yaranta ta fi sonsa,
ko don kasancewarsa namiji na farko a ɗakinta? Ba ta da
masaniya, to haka ma daga bangaren Modibbo, duk wani
tsaurinsa yakan sassauta akan lamarin Taheer. A yanzun
da shi kansa Modibbo kunyar kansa da kansa ya ke ji, ya
kuma kasa samun sukuni ko ƙanƙani game da lamuran su
Hussein, ta tabbatar ba zai iya komai ba don su ba
mahaukata ba me da za su ɗauki ƴarsu su ba Taheer duk
da irin abinda ubansa ya shukamusu.
Maimakon Taheer ya zauna, sai ya durkusa ya kama
ƙafarta, ga mamakinta hawaye ya ke.
"Hajjata zan iya mutuwa wallahi, kirjina zafi kawai ya ke yi.
Ina son Hafsat, bana jin zan iya rayuwa idan babu ita. A
yau Hamma Hussein ya kira wayata ya yimin gargadi kan
na rabu da ita. Ba zan iya ba Hajjata, ba zan iya ba
mutuwa zan yi. Na kasa sukuni tun da muka yi waya da
shi, ji nake kamar na shirya gobe na wuce Adamawa."
Ta girgiza kai tana sharemasa hawaye da hannunta, ita
kanta nata idanun ne suka cicciko da kwalla.
"Karatun naka fa wanda saura kiris ka kammala? Kar ka
kara cewa za ka wuce Adamawa a yanayin nan a muke
ciki, ba za su taɓa kallonka ba. Ba za ka yi wata ƙima ko
daraja a wajensu ba saboda tun ran gini tun ran zane.
Mahaifinka ne silar komai, a yanzun da girmanmu ya
gama faɗuwa a gabansu gaba ɗaya, ba na jin ko karen
gidansu zai ragamaka idan ku ka ci karo."
Ya numfasa yana jin ciwon gaskiyar da Hajjarsa ke fadi,
don ɗacinsa har a maƙwagoro ya ke ji. Ya haɗiyi zazzafan
miyau ya dubeta da jajayen idanunsa.
"Idan har dagaske Abban ya yi nadama, meyasa ba zai
taka da kansa ya je ya samu Dada da su Hamma ya ba su
hakuri ba? Idan mutuwa ta daukeshi a wannan yanayin fa?
Shi ne silar lalacewar komai, don haka ya je ya gyara. Na
fadamaku, idan na rasa Hafsat ba zan rayu ba. Ita ce
numfashina."
Daga haka ya mike ya fice yana tangaɗi sakamakon jirin
da ke kwasarsa, bai kai ga ficewa daga ɗakin ba ya zube
warwas a bakin ƙofa. Wani ihu da salati Hajja Fatouma ta
yi a lokaci guda wanda ya jawo hankalin mutan gidan har
shi kansa Modibbo da ya samu zazzaɓi ya lafamasa ya
ɗan fara gyangyadi. Ba karamin gigicewa ya yi da ganin
shalelan nasa a yanayinnan ba, tuni ya nemi zazzabin ya
rasa balle ciwon kai, nan da nan aka kwashi Taheer sai
asibiti.
***
Tun zamansu a gabansa, ya haɗe fuska kamar bai taɓa
dariya ba. Ba abinda ke mishi yawo a idanu sai irin
cakumar da Hajiya Zeenatun ta yi mishi a haɗuwarsu ta
ƙarshe kafin wannan. Yanzun tsabar makirci ita ce
gabansa har tana kuka da neman gafararsa. Ya yi wani
shu'umin murmushi mai nuni da cewa sai ya rama.
Kwanaki can ya yi mata aikin da bai yi tsammanin za ta
warke da wuri har haka ba, don haka zai mata wanda kaf
dukiyar da ta ke taƙama da shi sai ya tarwatse.
"Shikenan, na ji ya wuce. Sai dai ina mai gargadinki akan
kar ki kara yin gangancin da ki ka yi gareni a baya."
Hajiya Zeenatu ta kalli Hajiya Batool suka sauke ajiyar
zuciya kusan a tare kafin su dubeshi da fara'a.
"Ranka ya dade Gora, ba zan kara ba ko giyar wake na
sha saboda na ga abinda na gani bayan na kaurace
maka."
'Kaɗan kika gani, yanzun za ki ga fiye da hakan. Gora ba
ya yafiya, ba ya mance sharri.' Abinda ya fadi kenan a
ƙasan ransa daga nan ya ɗan bubbuga ƙasa kamar gaske,
can ya dago ya dubi yanda duk suka kwalalo idanuwansa
da fatar duk ta tattare saboda girma ya ja, a ransa ya ce
tsoffin banza kawai. A fili kuwa ya yi wata arniyar dariya
wanda gaba daya hankalinsu ya kwanta.
"Ai wannan auren ba inda zai je, zan miki aikin da shi
yaron da kansa zai tattaro ya dawo wajenki, ita kuma
yarinyar zan mata aikin da za ta shiga bariki ya daina
ganinta da daraja. Hakan ya yi?"
Wata dariya Hajiya Zeenat suka sanya har da tafawa ita da
Hajiya Batool.
"Gora mai gayya mai aiki! Shiyasa duk inda naje sai na
dawo gareka nake ganin daidai a lamuran rayuwata (Allah
Ya ganar da masu hali irin naki). Hakan ya yimin daidai,
dama nafi tunanin kamun kan yarinyar ne ya rinjayi
Hussein ban da haka ban ga wani kyau a tattare da ita ba.
Na ba ka wuƙa da nama."
Ya yi dariya.
"Hajjaju kenan, sai dai wani hanzari ba gudu ba, aiki ne
mai tsauri domin sai na haɗa da tattaunawa da Sarkin
bakaƙen aljanu, kinga kenan sai an yi zubar jini na dabba
da jaririn mutum kafin a cimma yiwuwar aiki. Don haka
aikin zai kama miliyan biyar."
Hajiya Batool ta kalleshi a hargitse kafin ta dubi Hajiya
Zeenatu, ta ga alamar ko a jikinta. Asalima ba ta sani ba,
yanda Hajiya Zeenatu ke ji a yanzu ko don ta dauki fansa,
za ta iya kashe ko nawa ne domin hankalin Hussein ya
karkato gareta karo na biyu kuma wanda ta ke fatan ya
zama na mutu ka raba.
"Na shirya, na shirya ba da koda duk abinda na mallaka ne
muddin Hussein zai dawo gareni."
Gora ya ji kamar ya daka tsalle, shakka babu ya samu
kudaden nan zai gudu ne ya bar garin a nemeshi a rasa,
dama har yau shi kansa bai san asalinsa ba, daga
almajiranci ne ya zama gawurtaccen Bokan Mata. Zai
sauya ƙasar gaba ɗaya ya je ya kama wata sana'ar mai
kauri. A fili kuwa cikin dakiya ba tare da ya nunamata
komai ba ya amsa.
"Shikenan, sai na jiki."
Daga nan ya karkata ga Hajiya Batool, itama dai Miliyan
Biyu ya nema, nan da nan ta hau zufa sai dai shaiɗan
wanda ya kaɗamata ganga da kuma taimakon zigar Hajiya
Zeenatu ta yarda ta kuma amince za ya san abin yi. Da
wannan suka rabu akan nan da kwanaki uku za su dawo
su damƙa masa kudaden da ya bukata.
A ɓangaren Hajiya Zeenatu, ta yanke siyar da A&Z ga wani
hamshaƙin matashin ɗan kasuwa wanda ya jima yana
muradin wajen yana son ya ƙara ƙawatashi ya haɗa da
filinsa da ke a gefen wajen ya gina Park na wasan manya
da yara ma. Amma fir a lokacin ta ƙi yarda bisa shawarar
Hussein da ya ce ba