Showing 54001 words to 57000 words out of 113545 words

Chapter 19 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

hadu. Koda wasa
ban yarda ku bar wannan matar ta shiga dakin ba."
Ya jinjina kai cike da girmamawa ya karbi odar ya koma
motarsa. Motar Chairman ya wuce su kuma suka juya
zuwa asibitin.
***
Hussein ya yi shiru kawai yana kallon Halima wacce har
sannan ta ƙi faɗar gaskiya. Sai ka rantse hankalin a kanta
yake, amma ina! Zuciyarsa na wani ɓangaren, sai hura
hanci ya ke yana ƙara cin magani. Garin Kanon ta fita
ransa, so yake su juya tare da ɗan uwansa kawai. Sai dai
kafin nan yana son nunawa Hajiya Zeenatu kurenta. Yana
son maka ta a kotu yanda za ta fuskanci fushin hukuma,
duniya kuma ta san da abinda ta aikata.
Wayar AlHassan ta yi ringing, gani Dada sai ya yi
murmushi ya fita daga station din. Hisham ya ɗan daki
kafaɗar Hussein kaɗan, dubansa ya yi kawai ya
watsamasa harara ya kauda kai.
Dariya sosai Hisham ya yi.
"Ikon Allah, to ni kuma me na yi? Nasan fa me ke cin
ranka"
Hussein ya gyara tsayuwa gami da ɗan lumshe idanu bai
ce uffan ba.
"Kar ka yiwa kanka saki na dafe, tun kafin lokaci ya
ƙuremaka gwara ka faɗamata abinda ke ranka."
Ya dubi Hisham.
"Me kake nufi? Kuma wa kake nufi?"
Hisham ya bude baki zai magana ya ɗaga mishi hannu.
"Malam bana son shirme, yimin shiru. Kai a komai sai ka
sanya wasa da zolaya. To ka fita idona."
Dariya sosai ya ba Hisham. Daidai sadda AlHassan ya
dawo ya dubesu yana dariya.
"Lafiya dai? Tom and Jerry?"
Murmushi kawai Hussein ya yi.
"Dada ce?" Ya tambaya. Gyada kai AlHassan ya yi yana
murmushin shima.
"Yes, ita ce. Sai dai ban fadamata komai ba, na dai ce ina
tafe da wani babban albishir."
Jinjina kai Hussein ya yi.
"When? Nima na ƙagu na gan ta."
"Very soon in sha Allah."
"Maiduguri fa?"
Cewar Hussein kamar zai yi kuka.
Dariya AlHassan ya yi.
"Duk za mu je da yardar Allah. Saboda rashinka na ɗauke
ƙafa, ganina yana sa Hajjo kukan tunawa da kai. Wannan
ta sa tsakaninmu sai waya."
"Ina son hukunta ta." Hussein ya fadi zuciyarsa na zafi,
fuskar Hajiya Zeenatu ya ke haskowa da kuma cuɗanya
iri-iri da ya yi tare da ita.
"Muje daga waje please. Nan ba wurin tattauna wannan
zancen ba ne."
Suka dubi Hisham mai magana, su ka maida hankali ga
Halima da ta yi musu ƙuri da kumburarrun idanunta. Duk
hirar da ake yi tana ji, kalaman Hussein na ƙarshe ya sa
tsoro ya ƙara kamata. Kada dai ita yake nufin a hukunta?
Ita kam ta shiga uku. Ba ta mance shawarar da kaninta ya
ba ta ba da ya zo.
"Idan kinsan ba da gaske kike ba Yaya Halima, ki fito ki fadi
gaskiya kafin lokaci ya ƙuremaki. Nidai gaskiya ban yarda
da abinda kika faɗamin ba."
Ta share hawaye tana ci gaba da kokwanto a ƙasan ranta.
Ta faɗa ko kuma ta yi shiru? Ita kanta ta rasa wanne za ta
zaɓa. Har suka fice tana kallonsu. Ta bi wurin kwananta
da kallo, ta ja majina. Anya Hajiya Zeenatu dagaske ta ke
za ta cire ta a wannan taskun? Shiru ta yi, karshe ta yanke
shawara ta aika ƙaninta wurin Hajiya Zeenatu ya yi mata
bayanin halin da take ciki.
***
Ramlat ta yi shiru, ita kadai a dakin, su Rafee'ah sun
wuce, sai Hajiya dake bandaki ɗauro alwalar sallar Azahar.
Nos Khadija ta kwankwasa ta shigo tana jan kayan
dressing din ciwo a ɗan keke. Suka yiwa juna murmushi.
Ɗan zaman da ta yi a asibitin sun saba, mace ce mai kirki.
"Su kuma waɗannan ƴan sandan da aka zubamana a
bakin ƙofa fa? Da alama dai Angonnaki na baki kulawar da
ta dace."
Wannan ne karon farko da ta ji haushin Nos Khadija, sam
ba ta son abinda za'a haɗa ta da Chairman. Tun kafin su
Munir su tafi, suka zoda zummar tsareta bisa umarnin
ubangidansu. Har ta soma faɗa Munir ya ce ta rabu da shi
kawai. Shi ya sani. Taɓe baki ta yi ba ta ce komai ba.
Daidai sadda Hajiya ta fito, suka gaisa da Nos Khadija
gami da yin ƴar raha don mace ce mai tsokana da kuma
ja da wasa. Tana cire Bandage din kafadar suna ta hira
abinsu, bayan ta goge ta ƙara rufewa sannan ya dubi
Ramlat jin Hajiya na faɗan ba ta son cin abinci.
"Ki dinga cin abinci don Allah Ramlat, haba yar uwa, ina
yabonki? Ki ci yanda idan na ba ki magani ba zai sanyaki
jiri ba. Yanzu zan dawo."
Ta gyada kai ba don ta so ba, ita kawai komai ma ba dadi
ya ke mata.
***
Hajiya Zeenatu tunda ta doshi barandar ɗakin da Ramlatu
ta ke ta hangi wasu masu kayan ma'aikata tsaye a bakin
ƙofar ta yi turus. Wuƙar da ke cikin jakarta yasa ta kasa
ƙarasawa, juyawa ta yi tana tunanin ina mafita? Ta ya za
ta cimma burinta? Yanzun ta tabbatar Hussein ba zai kara
yi mata kallon mace mai daraja da ƙima ba a idanunsa,
amma tabbas idan ta bar Ramlat na yawo a doron ƙasa
tofa shakka babu, wataran za ta ji batun aurensu. Abinda
ba za ta taɓa ɗauka ba har abada. A kan idanunta, Nos
Khadija ta shiga, hakanan a kan idanunta ta fito. Wata
dabara ta faɗomata don haka koda Nos Khadija ta zo
wucewa ta wurinta ta saki fuska sosai suka gaisa.
"Nace don Allah idan babu damuwa, ina son ganinki."
Nos Khadija ta bita da kallo, a shekaru ta girme mata
sosai hakanan kuma ba ta yi mata kama da wacce ta fito
daga ƙaramin gida ba.
"Shikenan, ba ni minti biyu."
Hajiya Zeenatu na murmushi ta gyada kai. Ba jimawa
Khadija ta dawo suka ɗan fita waje.
Shiru Khadija ta yi tana jin bayanan Hajiya Zeenatu.
Kirjinta ya shiga dukan uku-uku.
"Ki sani, wallahi-wallahi duk wani jin dadi na rayuwa kin
sameshi kin gama matukar kika yimin aikin da na sanyaki.
Zan ba ki duniya iyakar ƙarfina. Za ki taka duk ƙasar da
kike so, za kuma ki shiga duk inda kike so a faɗin
garinnan ba wanda ya isa ya ce maki don me?"
Jikin Khadija ya ɗauki wani irin rawa. Tunda take a duniya,
tunda ta ke, ba ta taɓa jin lamari irin haka ba. Wani irin
tsoron da ba za ta iya misaltawa ba ya shige ta. Daga
yanayinta Hajiya Zeenatu ta gane babu nasara don haka
ta bude jaka ta fiddo bandiran kudi ƴan dari biyar guda
biyu ta miƙamata, Allah Ya taimaka babu jama'a a wurin,
ta ɗago mata lafiyayyar wuƙa sabuwa fil ta nunamata.
"Ki zaɓi ɗaya Hajiya Khadija, idan ba haka ba ni da kike
gani don na kasheki ba komai ba ne a wurina. Sai na ɓatar
da ke da ma ƴan gidanku. Don haka zaɓi ya rage naki, na
baki nan da awanni biyu, duk abinda kika yanke ki kira ki
sanarmin. Kar ki manta rayuwarki a tafin hannuna yake."
'Ƙarya kike, Allah ne Mai iko da rayuwakanmu.' Nos
Khadija ta fadi a fili don ba ta jin tana da kwarin gwuiwar
faɗa a zahiri. Ta gyada kai kawai a fili, ta karɓi kudin ba
don ta so ba ta zura a aljihun wandonta.
"Ina tsumayenki. Ga lambar wayata." Hajiya Zeenatu ta
fadi karo na biyu tana miƙamata karamin complimentary
card mai dauke da numbobin wayoyinta a jiki. Nan ma
Khadija gyada kai ta yi.
"Je ki." Ta ba ta umarni, ta juya da sauri ta shige ciki har
tana cin karo da wata mai tsohon ciki.
"Yi hakuri don Allah." Matar ta bita da kallo kawai gami da
jan tsaki irin na masifaffun masu ciki. Haka ta wuce ta a
mita.
Koda ta karasa dakin Nurses, ba ta tarar da kowa ba don
haka da sauri ta ciro kudaden hannu na rawa ta cusa a
jaka ta zuge zif. Bandaki ta shige ta soma watsawa
fuskarta ruwa tana salati a ƙasan ranta. Yau da wane
rashin sa'a ta fito daga gida? Kawai sai ta shiga hawaye,
nutsastsiyar fuskar Ramlatu da kuma na Hajiya mai cike
da dattako da kamala take tunawa. Ta ya ya? Ta wace
hanyar za ta iya kashe wannan baiwar Allahn? Duk da dai
idan ta so abu ne mafi sauki a aikinta, za ta iya kasheta
irin kisar da zai yi wuya kafin a gane ita ce silarsa. Amma
ina! Ba'a ba ta wannan tarbiyyar ba kuma ita ba
haɗamammiya ba ce akan abin duniya. Kaɗan ma da ta ke
samu ya wadatar da ita.
Sai da aka kwankwasa ƙofar sannan ta fito. Karo suka yi
da Nos Jamila. Ta bita da kallo.
"Dije, lafiya?"
Murmushin yaƙe ta yi ta hau murza idanu.
"Ba komai, abu ne ya faɗa idanuna."
"Aa Dije, faɗamin gaskiya."
Girgiza kai ta yi, ba za ta iya ba, tana tsoron abinda zai
sanadin rayuwarta.
"Ko haihuwar ki ka karɓa, don nasan halinki na tausayi."
Dariya ta ba ta.
"Oh na tuna, ashe fa ba duty naki bane yau." Cewar Nos
Jamila karo na biyu.
Ita dai Khadija ta sulale ta fice daga ɗakin. Maganin ma
kasa komawa ta ba Ramlat ta yi sai wata ta aika.
***
Hussein da AlHassan zaune a falon gidan Hisham suna
cin lafiyayyen girkin Aisha. Gogan ci yake kamar an mishi
dole.
"Wai Hussein lafiya? Ko kaima jinyar kake taya Ramlat?"
AlHassan ya fadi yana murmushi don tuni ya ɗago shi.
"Mene haɗina da ita? Kawai dai na damu da harbin ne, na
kuma rasa waye zai yi ƙarya da ni ya harbe ta. Shiyasa na
kasa fahimtar mai laifin, me ya sani tsakanina da ita da ya
zaɓi hanyar kasheta ta amfani da ni."
"Da mamaki kam, amma ko ma mene in sha Allah nan ba
da jimawa ba zai bayyana. Har wanda ake ɓoyemana."
Hisham ya furta yana kashe mishi io ɗaya, AlHassan ya yi
kamar bai gansu ba ya ci gaba da kai loma yana
murmushi. A yau jinsa yake kamar a duniyar gajimare
tsabar murnar ganinsa zaune tare da ɗan uwansa.
Hussein din ma banda harara bai cewa Hisham uffan ba,
saboda gudun zargin sai ya saki jiki ya ci abinci. Bayan
sun kammala ya mike.
"Ina zuwa?"
Fadin AlHassan don ba ya son ya ji Hussein din ya matsa
daga gareshi. Murmushi Hussein ya yi.
"Gidan Hajiya Zeenatu."
"Aa, bai kamata ka je kai kaɗai ba. Muje tare."
Jinjina kai Hussein ya yi cikin amincewa da zancen dan
uwannasa. Suka ɗunguma suka fita, Hisham ya takamusu
har ƙofa kafin ya dawo ciki. Kusan shima yau dai jinsa
yake sak. Babu sauran damuwa.
KARFEN KAFA Chapter 62
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


Tun daga farfajiyar gidan ma'aikata suka dinga al'ajabin
ganin ƴan biyunnan. Har dai Malam Bala mai guga ya ka
sa hakuri.
"Yallaɓai ashe ku ƴan biyu ne."
Hussein suka dubi juna da AlHassan, kauna ta jini na ƴan
uwantaka na ƙara ratsa zuƙatansu, banda kaddara me zai
raba su? Su da suka rayu tare a mahaifa guda.
"Eh Malam Bala, we are twins."
Fadin Hussein wanda ya ƙarashe da kallon su John. Nan
suka shiga washe hakora suna gaida AlHassan da fadin
abinda ya bambantasu, hakan ya ba ƴan biyun matasan
dariya. Hussein ya yi ciki yana murmushi, ya bar su da
AlHassan. Yasan matar gidan ba ta nan kamar yanda ya ji
daga masu gadin, don haka ya shiga bin ko'ina na falon
da kallo. Tafkeken hotonsu shi da ita ya ƙurawa idanu
kamar wani fulanin daji da bai san hoto ba.
"Ita ce. Makira."
AlHassan ya fadi a hankali, sai sannan Hussein ya juyo da
rinannun idanunsa ya dubeshi.
"Idan na ce maka ban san ta ya ya na aureta na za ka
yarda? Idan na ce maka ba da son raina..."
"Ba fa sai ka faɗi komai ba ɗan uwa, na maka farin sani
na kuma san kalar macen da ka ke so. Ko ka mance cewa
ka ban labarin haɗuwarku da tayin kaunar da ta yi maka?
Ban san dalilin da yasa na kasa tunawa da hakan ba, ban
kuma san dalilin da yasa na amince ka bar mu ne saboda
ka auri wacce ka ke so. Amma ban taɓa kawo wa ita ce
ba nasan dai babbar mace ce kamar yanda ka faɗi."
Sauke ajiyar zuciya Hussein ya yi gami da jinjina kai. Falon
suka koma suka zauna. Nan kuma AlHassan ya shiga ba
shi labarin abubuwan da suka faru a bayansa. Rasuwar
Baba Naziru mijin Dada da kuma rasuwar ƴar uwar
kakarsu da ta riƙe su kamar jikokinta da yaran cikinta suka
haifamata ba su Dada ba.
"Allah Yay musu rahma. Yasa aljanna makoma. Baba
Naziru ya rasu da bakin cikina."
Girgiza kai AlHassan ya yi.
"Kar ka ce haka. Wallahi har ya rasu kewar ka ya ke, ya
kuma faɗa ya ƙara, ba halinka ba ne."
Hussein ya jinjina kai.
"Yaushe za ku tafi?"
AlHassan ya tambaya.
"A satinnan. Ina neman alfarma a wurinka, koda kun haɗu
da ita kar ka nuna mata komai kamar yanda nima ba zan
nuna ba."
Hussein ya faɗi idanunsa cikin na ɗan uwan. Da mamaki
AlHassannya tambaya.
"Dalili?"
Hussein ya yi mishi bayanin duk abinda ya ke buƙatar yi, a
farko AlHassan ya ji abin kamar babu amfani, a karshe
kuma sai ya hau murmushi sosai.
"Good, hakan shi ne daidai."
Abinda ya ce kenan bayan gama sauraro. Hussein ya ɗan
ciji leɓɓansa gami da shafa sumar kai.
Daga farfajiyar gidan kuwa, Hajiya Zeenatu ce ta shigo ta
yi parking ta fito. Ta sauke ajiyar zuciya ganin motar
Hussein. Ta shirya tunkurarsa, ta shirya fuskantar kowane
irin ƙalubale. Ita din mace ce, kissa ba komai bane.
Murmushi ta dan yi tana mai jin ƙwarin gwuiwa da haka ta
shiga gidan.
***
Yusufa ya zaro ido yana duban Halima da ke faman zuba
zance.
"Yaya Halima anya kina da imani? Yanzu saboda kudi ki ka
yarda ki aikata duka wannan? Yaya Halima ba ki yi tunanin
rana irin wannan za ta zo ba? Ke fa talaka ce, ba ki da
makaman yaƙi, su kuwa masu kuɗi ne, kinsan ba za su
kamu ba. Meyasa kullum shi talaka kwadayi ke kai shi ya
baro? Anya kuwa kin yiwa kanki adalci? Kin mana adalci?
Ɗan abinda kike samu na albashi bai wadace ki ba?"
Yanda Yusufa ke hawaye haka itama ta ke sheshshekar
kuka.
"Na cuci kaina, ban san cewa ni din mahaukaciya ce ba
dai yanzu Yusuf. Nidai don Allah ka taimaka ka je ka sami
Hajiya ka yi mata bayanin komai, nasan ba za ta rasa
hanyar da za ta fitar da ni ba musamman idan ta ji ina
barazanar tonamusu asiri."
Ya share fuskarsa, shiru ya yi don babu alamar zai je din.
Halima ta dinga yi mishi magiya da roƙo har tana
durƙusawa. Ɗan uwa daban ya ke, nan da nan ya ji
zuciyarsa ta karye, ya daukar mata alƙawarin a yau zai je
ya sami Hajiya Zeenatu tunda washegari ne shiga kotu. Ta
ba shi kwatancen gidanta har ma da na A&Z, daga bisani
suka rabu akan duk yanda ake ciki zai dawo ya
sanarmata.
***
Ramlat ta yi shiru tana tunani bayan tafiyar abokan aikinta
wadanda takanas suka zo dubiya. Can dai ta kasa hakuri
ya dubu Hajiya dake zaune saman darduma tana shan
kankana.
"Nikam Hajiya ya ake ciki batun mayar da kudi? Su Kawu
sun ƙara magana?"
Hajiya ta yi murmushi.
"Ina fa Ramlatu, Hajja ta ce na bar komai a hannunta.
Yanzu dama abinda ake ciki, ina so ke ki bada katin ATM
dinki na damƙawa Yayanki ya je ya ciro ya kawomin. Da
kaina zan je na same su na damƙamusu kuɗaɗen idan ya
so ko a yaransu ne su nemi ɗaya su aurawa Dikkon. Ke
dai ki kwantar da hankalinki kawai. Kuma kada jin hakan
yasa ki dauka na goyi bayan ki yi ta zama a gabana ne
babu aure, sam, ba zai yiwu ba. Shima wannan din
halayyarsa ce ba ta yimin ba kema kin sani. Don haka ki yi
kokarin fitar da mijin aure. Ko Baba Dakta ai kin ji me ya
ce."
Murmushi ta yi mai kama da yaƙe gami da gyaɗa kai.
Hajiya ba ta san me ke damunta ba, ba kuma auren ne ba
ta so ba. Kawai dai ba wanda ta ke jin kaunarsa a ranta
irin Hussein. Bayan Aliyunta, shi ne namijin da ta yi
amannar za ta iya rayuwa da shi a kowane yanayi. Sosai
yanzun tana jin saukin hannun don ita kam da ace za'a ba
ta sallama a ranar za ta so hakan. Sallamar da aka yi yasa
duk suka dubi ƙofar gami da amsawa. Nos Khadija ce, ta
ƙaraso ciki.
"Ke kuwa ɗiyata daga cewa bari ki ke ki dawo na ji shiru
sai wata na gani a madadinki."
Murmushin yaƙe Khadija ta yi. Ta rasa ma me za ta ce,
tuno zantukan Hajiya Zeenatu kaɗai yakan kaɗa hanjin
cikinta balle idan ta ci karo da salihan bayin Allahn nan da
ba su yi kama da mugaye ba. Ita kuwa in za ta iya aikata
wannan ɗanyen aikin? Ai koda babu ƴan sanda tsaye a
bakin ƙofar ba za ta iya ba.
"Ayi hakuri Hajiyarmu, ɗazun sallah na tsaya yi bayan na
idar kuma wani aikin ya ɗaukemin hankali. Sannu Ramlat,
ya jikin?"
Da murmushi itama Ramlat ta amsa.
"Alhamdulillah. Jiki ya yi sauki."
Ta jinjina kai.
"Dama zuwa na yi na muku sallama sai kuma Allah Ya
kaimu. Zan wuce gida."
Suka yi mata godiya sosai sannan ta juya ta fice idanunta
cike taf da kwalla. Ba ta tunanin har a ba su sallama za su
ƙara ganinta.
***
Sallamarta ta sanya su maida hankula gareta musamman
AlHassan wanda ke zuci-zucin ya haɗa ido da matar da ta
yi sanadiyyar rushewar dukkan farin cikinsu na tsawon
shekarunnan.
Tun daga bakin ƙofar shigowa ta saki jaka gami da
ƙarasowa tana kallonsu kamar wasu sabbin halittu.
"Hussein! Kar ka cemin wannan ɗan uwanka ne. Ku ƴan
biyu ne dama?"
Ta shiga nuni da Alhassan da yatsa da wani rawar baki ta
karasa zancen. Kawai a karshe ma sai ta karasa da sauri.
"Innalillahi, wallahi kuna kama. Wa ye wannan din? Huss.."
Bai bari ya ci gaba da sauraron rainin hankalinta ba ya yi
saurin katse ta.
"Yes yes, shi ne. AlHassan Aminu Modibbo, ɗan uwana
ne. Daga Adamawa."
Ya fadi yana kallonta da burin ya ga yanayin da za ta
shiga, sai ta maze ta hau sharar hawayen munafurci.
"Alhamdulillah. Allah Ma ji roƙon bayinSa. Allah yanda Ka
nunamin dan uwan mijina ina roƙonka da Ka sadar da ni
da nawa dangin." Kawai sai ta fashe da kuka sosai.
Hussein ya ɗora kafa ɗaya saman kujera gami da rike baki
da hannu ɗaya yana wani murmushi, AlHassan shi kansa
abin nata dariya ya ba shi. Ido Hussein din ya mishi don
haka ya shiga acting.


"Haba Hajjaju, ki kwantar da hankalinki. Komai ai na Allah
ne. Ai ko shekaru miliyan za'a yi ana shuka rashin alkhairi,
akwai ranar ƙin dillacin. Kinsan hausawa sun ce ramin
ƙarya ƙurarre ne. Ina nufin da sannu kema Allah zai sada
ki da naki ƴan uwan. Mun jima muna nemansa, a zatonmu
ma ya mutu, sai dai kwatsam labari ya iso mana can
Adamawa cewa an ga mai kama da ni a Kano, kamar da
wasa ina zuwa na haɗu da shi. Ai ba abinda za mu ce ga
Ubangiji sai godiya. Ya ban labarin irin kulawa da soyayyar
da ki ke nuna mishi, muna godiya sosai sosai fa."
Mamaki, tsoro ko farin ciki? Oho, Hajiya Zeenatu ba ta san
wanne ta ke ji ba. Dagaske ne Hussein bai zarginta da
komai haka ma dan uwansa ko kuwa dai su na mata
shigo-shigo ba zurfi ne?
_*"Kin manta waye Hussein? Mutumin da bai iya ɓoye ɓacin
rai ba? Ga dukkan alamu son da ya ke yi miki ya hana ya
zarge ki. Wannan ne zai sa ɗan uwansa ma ba zai zargeki
ba. Ko ba komai daular kadai da suka tarar da dan uwansu
a ciki, zai hana su zargi komai a kanki." *_
Wani sashi na zuciyar Hajiya Zeenatu ke mata wannan
tunin, nan da nan ta gaskata hakan, wani farin ciki ya
dabaibaye ta. Ta shiga rawar ƙafa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login