Showing 108001 words to 111000 words out of 113545 words
Chapter 37 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
haka ya katse kiran bai jira cewarta ba, ganin yanda
ta ke zabga murmushi yasa Hamida kallonta.
"Ya bar ki kenan ko?"
KARFEN KAFA Chapter 79
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
End! End!! End!!!
001
Ta gyada kai, suka yi dariya. Mikewa ta yi ta koma
bangarenta, mayafi kawai ta dauko sai jaka da mukullin
mota ta rufe ko'ina. Koda ta dawo, Dada na zaune ta
dawo falon. Sallama suka yi mata suka wuce. Wani
tsadadden leshi da ya haura dubu ashirin, iyakarsu ne
kawai, iyalan Dada, surukai da kuma ƴaƴa, ranar
Dinnerparty zasu sanya. Sai atamfar da zaa sanya ranar
wuni gaba daya dangi. Sai kuwa wata shadda ta Ramlatun
da za ta sanya ranar ɗaurin aure.
***
Ana gobe za'a sanya Amare a lalle ne, ƴan Kano suka
iso, dama iyalan Kawu Modibbo tun ana saura kwana uku
suma dira. Ramlat ta rasa inda za ta sanya su Rafee'ah
don murna. Ga yaranta, Affan ya zama babban mutum, ba
kuka sai ma yawan sunkuyar da kai wai shi a dole mai
kunya. Yaran sun yi wata irin ƙiba da kyau ga murjewa. Ta
dauki Babyn Aisha, kyakkyawa da ita, sunan Mahaifiyar
Hisham ta ci su na kiranta da Afnan. Kyau kam wane
iyayenta.
"Ke kina ta cewa wasu sun yi kyau, kina kallon kanki kuwa
a madubi Ramlat? Lallai aurennan ya karɓeki
tubarakAllah."
Maman Twins ke maganar tana kallonta sosai. Nan fa
sauran suka shiga tofa albarkacin bakinsu, ba wacce
zuwanta ya ba ta mamaki sai Bilkisu don ita Hunainah ba
ta zo ba saboda laulayin ciki na biyu da ta ke yi, ba ta jima
da haihuwar ɗanta ba kafin ta kai ga yin wani tsarin iyalin
sai ga ciki. Bilkisu kuwa wata uku kenan da dawowarta
gidan Muniru, nan ma sai da ta sha baƙar wuyar rayuwa a
gidansu, ta duba ta hango babu rayuwar da ta fi ta gidan
mijinta dadi wannan yasa dakyar da siɗin goshi ta lallaɓa
Muniru har ya sauko ya maidata ɗakinta. Tun komawarta
musamman ganin su Yasmeen babu wani alamar wahala
tattare da su, sai ta yi sanyi, ta kuma karɓi Hunainah
hannu bibbiyu suka zauna lafiya.
Hussein sosai ya ke jan yaran a jiki, wani irin so da
kaunarsu ya ke ji na musamman a ƙasan ransa har yake ji
inama daga jikinsa suka fito. Ya yi amannar son da ya ke
musu, ko mahaifinsu sai hakan. Ramlat kuwa banda
murmushi ba abinda ta ke yi, ganinsu tare na karamata
annashuwa. A ranar dai da kansa ya ce ta kwanta tare da
yaran, ya tabbatar ta yi kewarsu.
Washegari aka shiga cikin biki, komai ya tafi cike da tsari.
Ranar babu batun anko don kowa kayansa ya sanya, a
rana ta biyu ne suka gudanar da yini da rana wanda
kowaccensu ta sha ankon atamfa har su Aisha mutan
Kano, don tun kafin su zo Ramlat ta aikamusu hoton
ankon suka ɗinka.
Tun soma sabgar biki ba ta da wani lokacin kanta balle
kuma na Hussein, hira ta ragu sosai a tsakaninsu. Sai dai
ta kai mishi abinci, zaman da za ta yi wurinsa bai fi na
mintoci ba. Wannan abu ya kai Hussein bango, gaba daya
ma sai ya daina bari su haɗu. Da daddare idan ta leƙo, ya
rufe kofar gam, da safe kuwa duk irin sammakonta ya fice
daga gidan, waya kam ko ta kira bai ɗagawa. Text na
duniya ba ya kulata, sam ya kasa yi mata uzurin tana da
baƙi kuma su na hidimar biki. Wannan damuwar ta sa a
ranta, shiyasa ko ranar da ta kama na dinnerparty, kasa
wani kataɓus ta yi. Tana zaune tana kallon kowa na
shiryawa, maganar duniya su Zulaihat da su Kausar sun
mata akan ta tashi ta shirya amma ta ce sam ta fasa.
"Adda Amal kina cewa ba za ki je ba, ga Hamma Hussein
can ya ci uban kwalliya ya fita, kuma wallahi idanun
ƴanmatan nan kamar su tsiyaye tsabar kallonsa."
Jin abinda Falmata yar uwar su Hussein ta Maiduguri ta
fadi, ai sai Ramlat ta mike tsaye ranta na susa. Nan aka
kwashe da dariya, har itama ta murmusa.
"Kishi kumullon mata, ki zauna dai kar ki je. Wallahi sai
dai ki ji ana wani labarin."
Ita dai Ramlat ba ta biyewa zancen Rafee'ah ba ta shiga
bandaki bayan ta rage kayan jikinta, tana ji su na mata
dariya. Wanka ta ƙara yi duka rabin hankalin na ga tunanin
Hussein, abinka da zuciya, sai nan da nan ta ji itama ai ya
mata laifi, ta ji ya bata haushi sosai. Kwafa ta yi tana ƙara
cuɗa sabulu a jikinta, aikuwa ta ci alwashin itama ko kallo
bai isheta ba a wurin taron. Ta fito ta shirya, da yawansu
sun fice har su Rafee'ah da maman Twins. Aisha da
Falmata da kuma Asma'u diyar Hajja Fatuma uwargidan
Modibbo sai wata Hannatu itama daga Maiduguri, su ne
kadai suka yi zaman jiran Ramlatun don su wuce a
motarta.
Leshinta da suka yi anko kalar milk kai adon golden
brown ya yi masifar sama a jikinta, ya sha aikin stones shi
ta fiddo ta zura. Falmata ta yi mata make-up na fitar
hayyaci, kasancewar kwalliyar zamani mai kama da na
aljanu bai damu Ramlat ba don ba irinsa ta fi yi ba, sai ta
fito ta yi wani azababben kyau. Daman su Rafee'ah yanda
suka ga ta sauya fatarta ta kara kyau da sulɓi yasa suka
dinga yi mata zargin mai ciki, ita kanta sauyawar na ba ta
mamaki.
"Wallahi na fadamaki wani abu? Nidai ba ki taɓa kyau irin
na yau ba, ko bikinki albarka."
Aisha ce ke maganar tana dariya, harararta Ramlat ta yi
ta ja guntun tsaki ba ta ce komai ba, wannan duk abinda
ta yi ɗanawa Hussein tarko ta ke son yi yanda zai yi dana
sanin wannan fushin da ya ɗauka da ita. Har tunani take
ko wa ya sanya a gaban mota suka tafi? Nan fa ranta ya
ƙara sosuwa. Ta mike ta yafa mayafinta golden ta dauki
purse dinta mai kyalli shima golden, turare mai sanyin
ƙamshi ta fesa kafin ta zura takalminta da ya kasance
mahaɗin purse din, ta dauki mukullin motarta. Kuɗin liki
kam dama tuni sun tsufa a cikin ƴar jakar don tun safe
suka bada aka yi masu chanji kowacce ta adana abinta.
"Muje." Ta basu umarni, duk suka fito ta rufe ko'ina na
gidan. Su Ummi na sashen Dada da yara ana ta wasa don
yanzu ba su fiye wani kewar uwartasu sosai ba balle su
liƙe mata.
Tana tuƙin amma fuskar ba wawalar a zo a gani
musamman da ta ga dagasken dai babu motar Hussein a
farfajiyar gidan. Aisha ta karanceta tsaf, ta san kishi kawai
ke cin ƴar uwarta don haka ta bar janta da hira ta maida
akalar hiran ga su Falmata dake zaune a baya haka har
suka isa ƙayataccen ɗakin taron na FARHAS Event Centre
(Dan Adam).
Farfajiyar wurin sai ɗaiɗaikun jama'a, sai da duk suka fita,
sannan ta bi bayansu. Aisha ko jiranta bata tsaya yi ba
don ba ta son a huce a kanta. Ta na takunnan mai girgiza
zuciyar masoyinta kuma mijinta, wanda ya zama normal
tafiyarta. Haka ta ƙarasa har ta shiga ciki. Wuri fa ya cika,
gaba ɗaya kowa na zaune ana kallon MC wanda ya fiddo
Amare da Angwayensu tsakiya yana basu umarnin zama
saman wasu kujeru a tsakiyar wurin, wannan yasa
hankalin da dama suna kansu ana dariya a nishaɗance.
Sun haɗa ido, sai ta dauke kai kamar ba ta ganshi ba,
wani irin tururi kanta ke yi ganin wata kyakkyawar budurwa
a gefensa zaune, shi kuwa AlHassan Madam dinsa ce a
gefensa sun ba MC hankulansu. Takaici ya sanya kawai ta
ja kujera ta zauna ba tare da ta ƙarasa wurin su Rafee'ah
ba, sai ma bayan ta zauna ta ɗago kai ta ga ashe
ƴanmatan gidan kakannin su Hussein ɗin ne.
"Kai Adda Amal you look beautiful wallahi."
Ta dubi mai maganar Teema ta yi murmushin da bai kai
zuci ba.
"Thank you. Kuma kun yi kyau."
Daga haka ta maida hankali da fiddo wayarta dake faman
vibrating, ganin lambar Hussein kawai sai ta maida wayar
jaka. Tana ɗaga kai kuwa ta hango su Kausar na ɗaga
mata hannu alamar ta ƙaraso. Hannu kawai ta ɗagamata
shaidar inda take ya ishe ta. Sai da aka kira dangin Ango
Tahir don su yi liƙi sannan ta mike suka ɗunguma har su
Teema, a hanya suka haɗe da su Rafee'ah aka shige fili,
Maman twins na rantsuwar a farko ba ta ganeta ba. Sai
dai su na liƙin tuni mazan suma suka taso don zazzage
nasu aljihun, ta ɗaga hannu da nufin somawa ya kai
hannunsa saman nata. Juyowa ta yi har fuskarsu na
haɗuwa numfashinsu na gauraya wuri ɗaya. A hankali ya
zare kudin a hannunta ya shiga liƙawa kaf a kan Amarya
da Angon, ta juya za ta wuce ya riƙe hannun gam suka fita
tare. Maimakon su koma mazauni sai kawa ya yi waje da
ita har wurin motarsa. Ta fincike hannunta, tuni
idanunnata sun cicciko da kwalla.
"Ka kyale ni."
Hussein ya tsaya kawai hannunsa a kirji yana karemata
kallo, ta yi mishi irn kyan da baki ba zai iya faɗi ba.
Tsananin kewarta da son kasancewa da ita ne ke cin
zuciyarsa.
"Da iznin wa ki ka zo nan?"
Ta tsuke baki, ya kuwa bishi da kallo yana cije lebba.
"Ka riga ka san da fitar ai."
Ta fadi cike da dakiya. Bai ce uffan ba ya juya ya yi
amfani da mukullin motarsa ya bude, hannunta ya kama
ya zagaya da ita ya bude gaban motar da nufin sanyata
ciki. Ta dubeshi da zummar magana, sai dai yanayin
ɗaurewarsa ya kaɗa hanjinta ba shiri ta hadiye abinda take
shirin fadi ta shiga a fusace tana huci. Sai da ya zagaya ya
zauna sannan ta dubeshi.
"Motata fa?"
Bai ce mata uffan ba ya yi ribas suka fice. Ranta ya ƙara
zafi gashinan ko hoto ba su yi ba da Amaren balle kuma
ƴan ankon.
"Amma kasan ba kai ka kawoni ba ko?"
Idan motar ta bata amsa, toh Hussein ya bata. Wayarta ce
ta shiga ringing, ta ciro, kafin ta duba ko ta ɗaga ya karɓe.
Ba ta san me aka ce ba kamsr yanda ba ta san wace ce
ba.
"Muna tare."
Daga haka ya katse kiran ya jefa wayar aljihun gaban riga.
Ramlat dai har da hawayen takaici, ba ta bar haskoshi da
waccan budurwar ba kamar yanda ta ke jin zafin raba ta
da wurin bikin da ya yi.
Su na isa gidan ya sa hannu ya zare purse dinta yana
kallonta tsakar ido Ta kauda kai tana tura baki. Dariya ma
ta ba shi ya murmusa. Mukullin motarta ya zare ya miƙa
mata. Yana unlocking kofofin ta bude ta fice zuwa
sashinta ranta a jagule. Shi kuwa sai da ya ba direba
mukullin da kudin mota akan ya koma idan an tashi ya
taho da waɗanda suka je a cikinta.
***
Tana shiga ɗakinta ta faɗa saman gado ta shiga rera kuka
kamar wata yarinya ƙarama. Ganinta kwnace saman gado
tana kuka ya hau doka murmushi, kawai ji yake ya rama
shariyar da ta dinga yi mishi a kwanaki biyunnan. A nutse
kuma ya soma takawa har ya karasa gadon. Jin ƙamshin
turarensa sai ta ɗago ta share fuska, kokarin mikewa ta
ke yi ya riƙo hannunta gami da jawo ta ta faɗa jikinsa.
Kanta bisa kirjinsa gaba daya fuskarta ta nutse yayinda
hancinta ke shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa. Lumshe
idanu ta yi sadda ya sa hannuwansa gaba daya ya
rungumeta tsam. Sai a sannan ta kara tabbatar da cewar
ta yi kewar mijinta. A hankali ya zame ɗankwalin kanta ya
shiga shafa gashinta.
"Duk kawaici da kauda kan da nayi maki don naga gudun
ruwanki, ba ki gane ba ko? Kin maida ni kamar wani hoto,
kin nunan sabgar gabanki ya fi ni ƙima da muhimmanci.
Tun soma bikinnan ba ki da lokacina, ba ki damu da ni ba.
Shikenan ni kuma sai na kasa nuna ɓacin raina?"
Yanda ya ke magana a tausashe sai jikinta ya yi sanyi,
shakka babu kam, ba ta kyauta ba. Ta ɗago a hankali ta
dubeshi tana narkar da fuska.
"Ka yi hakuri. Na sani ban kyauta ba, amma don Allah ka
yimin uzuri tunda dai ka sani biki ne ake yi, ga baƙi ina da
su."
Ya kama haɓanta suka tsurawa juna ido.
"Sai kuma ki ke jin nauyin kwana da mijinki don kina da
baƙi? Ki ka kyalewa wasu ƴan matan shi su samu
matsugunni a nan?" Ya nuna kirjinsa yana ɗaga mata gira
da murmushi.
Nan da nan kishin ya dawo sabo fil ta tureshi za ta mike,
ya kara fisgota ya rike gam yana dariya.
"Na dauka kishiyar kike ra'ayi."
Ba ta san sadda ta harareshi ba, don mamaki sai ya yi
dariya.
"Shiyasa na ganka da wata busashshiya kana yawo da ita
a cikin bainar jama'a don ka zubarmin da ƙima a gane ni
Ramlat ban da wata daraja da.."
Bai bari ta karasa ba ya tallafi haɓanta ya haɗe bakinsu
wuri guda da zafi-zafi.
Tun tana yunkurin ƙwatar kanta har dai ta saddaƙar. Can
kuma da kansa ya sake ta, ya mike yana dubanta da
shanyayyun idanunsa. Da wata irin kasala ya miƙa mata
hannu, ba musu ta miƙamasa, suka ɗunguma zuwa nashi
ɓangaren. A nan kam alƙalami ba zai iya wassafa yanda
masoyan suka kasance ba cike da matsanancin kewar
junansu. Ranar dai dinner anan suka ci suka sha abinsu.
Koda jama'a aka dawo, ta sha tsokana sai toshe
kunnuwanta ta yi kawai.
***
Sati biyu da kammala biki, jama'a kowa ya watse, an
miƙa Amarya Hafsat zuwa Kano, tafiyar da ba'a yi tare da
Ramlat ba don sam Hussein ya ce ita da Kano ba yanzu
ba. Haka ta hakura, Rasheeda kuwa Abuja aka miƙa ta
wurin aikin mijinta.
Tun bayan bikin ya kasance Ramlat ba ta da kuzari,
koyaushe tana kwance, wani lokacin bacci wani lokacin
kuwa yanayin jikin ne kawai ba ya mata dadi. Dada kanta
ta soma fahimtar sauye-sauyen Ramlatun, abinka da
babba, sai ta ce mata lallai ta yi zamanta a ɓangarenta ta
dinga hutawa tunda a sannan Dada ba ita kadai ba ce,
wata dattijuwa kuma yar uwarta dake Mubi, Mariya ta
dawo nan domin taya Dada zama. Mace ce da ba ta taɓa
haihuwa ba ga kuma girma da ya ɗan kama ta babu mijin
aure. Ita kanta tana jin dadin zama da Dada.
Kamar koyaushe, yau dinma tana kwana a falo, daga ita
sai vest fara mara hannu da wando pencil da bai karasa
ƙaurinta ba. Tun fitar Hussein take jin tashin zuciya, ta
rasa meke mata dadi. Kamshin komai a gidan ma ji ta ke
yana hawa kanta, karshe ma miƙewa ta yi kawai ta zura
dogon hijabinta ta zagaya ɗan barandarsu da ake hango
garden ta shimfida ƙatuwar dardumarta ta zauna. Ba laifi
ta ɗan ji sauyi, ahankali kuma bacci ya yi awon gaba da
ita.
Sallama ya yi har sau uku shiru, da mamaki ya karasa
shigowa falon a karshe ya shiga leƙa kicin da dakuna.
Bandaki ma wayam, yana shirin leƙawa sashinsa ya hango
ƙofar fita ta hanyar kicin a bude don haka ya karasa. Sosai
abin ya ba shi mamaki, ba ta taɓa yin haka ba, ga dai iskar
fanka da komai a falon amma ta dawo nan ta kwanta,
yanzu kam ya yarda ba ta da lafiya. Karasawa ya yi ya sa
hannu saman goshinta. Zafin da ya ɗan ji ne ya sa shi
shafa gefen fuskar.
"Ya Salam."
Jin hannunsa ta yi firgigit ta farka da salati. Ya kama
hannunta.
"Sannu Heart, dama ba ki da lafiya? Tashi muje asibiti."
Ta mike zaune tana shafe fuskarta, sosai kam ta yi bacci
don har yamma ta kawo kai, ta tuno ko sallah ba ta yi ba.
"Ban yi sallah ba."
Ya taimaka mata ta mike, yana rike da ƙugunta suka
ƙarasa ciki, sai dai su na sanya kai a falon ƙamshin
airfreshner da ta fesa ya hautsina mata ƴan hanji. Tana
kokarin zama jikinsa daga natata hanyar amfani da
hannun damanta ta dora saman kirjinsa za ta tureshi, shi
kuwa ƙara riƙo ta yake a rude yana tambayar lafiya. Sai dai
ina! Tuni ta soma sheƙa amai har yana ɓata jikin Hussein.
Nan da nan ta zaro ido a rikice, ba ta mance sadda ta
yiwa Aliyu amai a jiki ba ya ɗauketa da lafiyayyan mari
yana ɗura ashariya.
"Ka yi haku.."
"Shii! Muje ki wanke jikinki." Ya ja ta suka nufi bangarenta,
sai da ya cire rigarsa da ta ɓaci har da singilet, kafin itama
ya ciremata nata dogon hijabin. Bandaki ya shiga ya hada
ruwa. Wankan suka yi tare, duk wani abin ƙamshi da ya
ɗauko za ta girgiza kai ta ce ita ba ta so, Hussein dai
murmushi ya ke da fatan Allah Yasa abinda yake tunani ya
tabbata. Sai da ya daukomata kaya sannan ya wuce
sashinsa ɗaure da tawul a ƙugu. Ƙananun kaya ya sa
kawai ya fesa turare. Aikuwa tana jin ƙamshin turarensa ta
fada bandaki a guje ta shiga sheƙa wani aman, koda zai
shigo ya dakatar da shi kamar ta yi kuka.
"Ni bana son kamshin turarenka."
"Toh fa." Ya tsinci kanshi da faɗi, turaren da a baya take
masifar so kenan, Sorry kawai ya furta sannan ya fita daga
dakin. Kaya ya je ya sauya sai dai wannan karon bai yi
gangancin fesa turaren ba. Suka ɗunguma suka wuce
asibiti, ta waya ya shaidawa Dada ya kai Ramlat asbiti.
Dada murmushi kawai ta yi da addu'ar Allah Ya bata lafiya.
Kyakkyawan albishir din da ya yi fata kuwa shi ya samu,
wato dai ciki ne da ita. Yanda ya dinga tarairayarta tun
daga asibitin har gida, ita abin ma kunya ya dinga ba ta.
Tun daga ranar kuwa kulawar da Hussein ke ba ta na
musamman ne, tausayi sosai ta ke ba shi ganin yanda ta
ke laulayi mai wahalarwa. Ita kanta abin tsoro ya dinga ba
ta, gani take kamar wannan haihuwar farko ne za ta yi don
komai sabo ta ke ganinsa.
Kafin watannin haihuwar su cika gaba daya ta sauya, ta
rame, sai ƙaton ciki wanda scanning ya nuna ɗa ɗaya ne
kawai. Kowa kallon mai haihuwar biyu yake mata, duk
yanda ta so ya bari ta je Kano ta haihu ya ƙi, itama don
kanta ta hakura da batun zuwa don ko nawa za'a ba ta a
yanda take ji, ba za ta iya bin hanyar Kano ba.
***
Bacci ya ke sosai, yayinda ita kuwa baiwar Allah ta
zubawa silin din ɗakin idanu wanda hasken farin wata ya
haska, mararta da bayanta babu inda ba ya ciwo, a hankali
ta miƙe zaune tana cije baki, ta rasa ma ina za ta sa ranta,
wani irin murɗawa da ya yi ba ta san sadda ta ɗakawa
Hussein duka ba. Ya mike kuwa firgigit don a farko bai
dauka mutum ne ya dakeshi ba, hannu yasa ya kunna
fitilsr bedside yana kallonta gami da ruƙo ta.
Ta matse hannunsa ƙam!
"Mutuwa zan yi wallahi!"
"No! Naƙudar ce? Bari muje asibiti."
Haka ya mike tsaye yana gyara zaman pyjamas dinsa.
Dakyar ya samu nutsuwar ganin mukullin motar, ficewa ya
soma yi da ita, Buzu Maigadi da fitowarsa daga bandaki
kenan, ya ajiye butar ya karaso da sauri ya taimaka ya
karbi mukullin motar ya budemishi yana kwaranyo addu'ar
Allah Ya bata lafiya. Lokacin wuraren ukun dare ne. Sai da
Hussein ya zaunar da ita kafin ya koma a guje ya dauko
akwatin da tun shigar cikin wata tara ta haɗa abinta.
Su Dada basu sani ba sai ƙarar buɗe kyaure da rufewa
suka ji. Ba shiri ta fito ita da Baba Mariya a ruɗe, nan Buzu
ke fadamusu Madam ce ba lafiya. Nan da nan a rude suka
kira wayar Hussein, amma ina tana ta ringing bai ɗaga. A
dole suka koma ciki don ba direban da zai kai su. Nafiloli
suka shiga yi da addu'ar Allah Ya sauketa lafiya don sun
sani loda