Showing 36001 words to 39000 words out of 113545 words

Chapter 13 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

ta iya motsa leɓɓan.
"Ka yi hakuri."
Shiru ya biyo bayan can kuma ya sauke ajiyar zuciya.
"Naso yau na ganki."
Ta yi luum da idanu, ta kasa yarda da abinda kunnuwanta
suka jiyemata.
"Uhm?" Ta nemi ba'asi.
"Hoton zan karɓa ta ƙarfi tunda an hana ni."
Ya faɗi a shagwaɓance, ya sanyata murmushi tana mai
sunkuyar da kai kamar yana gabanta.
"Zan turomaka."
"Promise?"
"Yes."
"Kinsan hoto ɗaya rowa ce ko?"
Ta ƙara faɗaɗa murmushinta.
"Uku fa?"
Tana jin sautin murmushinsa. Can ya amsa.
"Thanks. Allah Ya kaiku lafiya."
Bai jira amsarta ba ya katse kiran, karatun ya ci gaba.
Kaso saba'in na damuwarta ya ragu, ta ji wani kwarin
gwuiwa. Nan da nan ta shiga Gallery dinta ta hau kallon
hotuna. Duk wanda ta ga shi ya dace ta aika sai ta ga
kamar bai kai ba. Ruwan ido, abinda ta tsana ta ke jin
haushi a wurin Amrah, ita ce yau ta ke yinsa. Dakyar ta
haƙura ta zaɓi wasu guda uku ta aika kasancewar da
network a wurin da suke nan da nan ya je, ba ta jira
godiyar ba ta sanya wayar a Airplanemode tana murmushi.
Koda suka isa yan uwan sun sha mamakin sauyawarta.
Ƙofar Baaru kusa da gidan Sarkin Daura, nan ne ainahin
gidan iyaye da kakannin su Abba da Hajiya yake. Gida ne
babba na gandu, zaman iyaye da ƴaƴa. Sun tarar da su
Nusaiba mutan Kano duk an hallara. Hajja da abokiyar
zamanta ma suna nan. Gida ya cika da ƴan uwa gwanin
dadi. Sashen Ƙanin Malam Abdullahi kakanta nan ta yada
zango wurin su Nusaiba sa'anninta, don ba ta kaunar
zama da su Rafee'ah, zancen dai daya ne, na Chairman.
Ta fiddo miji ta gujewa aurensa.
Karshe ta watsar da duk wani tunani ta rage sutura ta
shiga wanka. Bayan ta fito ta tarar su Nusaiba gaba daya
na zaune ana kari da doya da kwai da shayi wanda ya ji
citta da kanumfari.
"Ke kuwa Ramlatu yaushe za mu sha naki bikin?"
Ta yi kamar ba ta ji maganar Gwaggo Hansai ba, ta ci
gaba da goge ruwan jikinta. Ba ta ce uffan ba. Duka Dije
kanwar Gwaggo Hansai din ta kai mata bakinta cunkushe
da burodi.
"Ja'ira, ai tana jinki. Ta fi kaunar muje ana daurin aure ta
dawomana. Maimaita tarihi ko? Toh dagaske banni ƙara
zuwa bikinta."
Aka yi dariya don an san zolaya ce ta Dije, ita dai Ramlat
ta kara tamkewa ta mike ta kwashi kayanta, ta fasa shirin
a falo, ta koma uwar ɗaka.
***
Kamar wanda aka daskarar da jinin jikinsa haka ya yi ɗif,
a hankali ya sauke ƙarfen da ke hannunsa yana maida
numfashi, gumi kam kamar ruwa haka yake ɗiga daga
cikin gashinsa, saman fuska har zuwa jikinsa. Kallon
Hisham ya ke yi da wani irin faɗuwar gaba. Hisham ya
toshe kunnuwansa da earpiece yana gyada kai alamun
waƙar da yake ji na tsumashi sai dai kacokam hankalin
yana ga Hussein. Yana sane ya fesamasa batun auren
Chairman da Ramlat duk kuwa da cewar yasan maganar
rawa take yi ba ta tabbata ba. Amma ɗan hakin da ka
raina ai shi ke tsonemaka ido. Gwara tun wuri ya yiwa
abin tufka, ko ba komai zai ƙara karantar inda Amininnasa
ya dosa.
Tasowar ta Hussein, da kuma fisge Earpiece din daga
kunnensa duka-duka abin ya zamewa Hisham kamar
kiftawar idanu. Ya haɗiye dariyarsa ya kara daure fuska.
"Lafiya Malam? Me ya yi zafi? Daga cewa Chairman Aliyu
Dikko zai au.."
"Kar ka ƙarasa." Ya fadi a kausashe yana nunashi da yatsa
idanun sun kaɗa cike da wani irin matsanancin kishin da
bai san mafarinsa ba. Hisham ya cika da mamaki don bai
zaci abin zai kai haka ba. A hankali Hussein ya zauna a
gefensa ya yi shiru, can kuma ya dubeshi a sanyaye.
"Wasa ka ke yi, sai dai irin wannan ba maganar wasa ba
ce. Please kar ka ƙara."
Hisham ya karkace yana dubansa.
"Don me? Toh kai mene naka ciki? Me zai dameka?
Menene haɗin biri da gada?"
Ran Hussein ya yi tsananin ɓaci.
"Ni ka ke kira biri? Hisham har wuyanka ya kai tsaikon da
za ka haɗani da biri?"
Dariyar Hisham ta kasa ɓoyuwa, lallai ya ƙara yarda
Hussein bai iya Hausar ba. Dariyar ta kara fusata Hussein
wanda dagaske ya ji zafin birin da Hisham ya ambata.
Abin ya haɗemishi biyu don haka ya mike ya dauki jakarsa
don suturta jiki. Hisham ya bishi da kallo yana mai ba shi
tausayi. A yanzu ba shi da abar kauna sai Ramlat, sai dai
ya rasa dalilin abokinnasa na ƙin ba wa zuciyarsa
abincinta. Ko a ɗazun, kasancewar Hussein ya rigashi
zuwa wurin motsa jikin, kama shi ya yi dumu-dumu da
hoton Ramlat din yana kallo yana murmushi. Ganinsa ya
wartsake ya sanya wa wayar muƙulli.
Yana nan zaune ya fito, madadin gajeran wando, ya sanya
dogo mai santsi fari ƙal mai haɗe da riga. Ya sanya baƙin
gilashi yanda idanun suka ɓuya.
"Sai Allah Ya kaimu."
Ya furta can ƙasan maƙogwaro yana duban Hisham din a
fisge. Hisham ya rike hannunsa.
"Haba abokina, ka yi hakuri idan ɓacin ran da na jefaka ya
kai girman haka. Karin magana na yi maka, haka
Bahaushe ke karin maganarsa. Ba wai da gayya na haɗaka
da dabba mafi muni ba."
Hussein ya sa hannu ya dan ja karan hancinsa kaɗan yana
duban gefe.
"Wani abu na ƙara faɗi?"
Hisham ya dubeshi dakyau.
"Ba ka faɗa ba, amma ba haka muka saba sallama ba.
Mafi yawan lokuta tare muke fita. Yau kuma ba alamar za
ka jirani."
Guntun tsaki Hussein ya ja.
"Sauri nake."
Ya furta kai tsaye har da duban agogonsa kalar silver.
"Karin maganar ce ko damuwar Ramlatu ce?"
Ya ji tambayar Hisham kamar daga sama, shiru ma
mintuna kafin ya dubi Hisham ta cikin gilashin.
"Abinda ka fadi gaskiya ne?"
Yanda ya yi maganar a sanyaye, sai hakan ya sanyaya jikin
Hisham. Shirun da ya yi, Hussein ya samu amsarsa.
"Sai da safe."
Daga fadin haka ya yi gaba. Murmushi Hisham ya dan yi.
Shakka babu da Ramlatu za ta samu Hussein ba karamin
farin ciki zai mata ba. Yana matukar son ganinsu tare sai
dai kuma sanin tarihin Ramlatun kan sanyaya masa jiki.
Anya Hussein zai gan ta da gashi?
***
_*Nan kusa za'a yi bikin Ramlat da Chairman Aliyu Dikko
don na ji labarin zai kai kuɗi. *_
Wannan kalaman ke yawo a kwanyarsa har ya hanashi
maida hankali ga tuƙin da ya ke yi. Dole ya gangara gefen
titi ya kashe wayar ya kwantar da kai bayan kujera. Runtse
idanu ya yi na ƴan mintoci kafin daga bisani ya ƙara fiddo
waya ya buɗe hotunan Ramlat yana ƙaremusu kallo. Saura
ƙiris ta zama mallakin Chairman yana nufin abubuwa da
dama. Shugabanta wurin aiki, wanda ya fi shi kudi da
muƙami, wannan na nuna kwaɗayi ƙarara. Hira da ita da
ma kallon hotunan har da ganinta a zahiri zai zama haram
a gareshi, wannan ma wata damuwar ce mai zaman
kanta.
Ransa idan ya yi dubu to ya ɓaci, kirjinsa zafi yake.
Mafarkinsa na ƙara yawo a kwanyarsa, gaba daya ya
hargitse lokaci guda. Ya tuna abu daya kwakkwara da ya
danganci rayuwarsa ya kasa. Neman haske cikin duhu
yake amma abin ya gagara. Koda ya tsananta tunani,
kansa ya ci gaba da sarawa da ƙarfi, cikin dauriya ya kai
hannu ya kunna CD na karatun Al-kur'ani da ke kan
rediyon. A hankali ya soma samun nutsuwar zuci da na
gangar jiki, ɗif, sai ya nemi yanayin ya rasa. Wannan kadai
ya tabbatar da zargin da ya sha yiwa kansa a baya, wato
ba shi da lafiya, kuma ya zamar mishi dole ya ga likita.
Ya kwashe mintuna biyar a wajen yana kallon motocin da
ke safa da marwa kafin daga bisani ya ci gaba da tuƙinsa.
***
BAYAN KWANAKI UKU..
ADAMAWA
Tun fitowarta daga ɗakin ta ke ƙunƙuni tana zuba abincin
zuciyarta na tuƙuƙi ga wani ƙololon abu dabya tokaremata
ƙahon zuciya. Tahir kallonta yake kamar ya haɗiye, nan
duniya ba ya jin akwai wacce zai so sama da Hafsat. Aure
ne yana ji a jikinsa tamkar an yi an gama.
"Kin yi kyau."
Ya faɗi kamar mai raɗa bayan ya ƙaremata kallo cikin riga
da siket din jikinta na Atamfa. Harara ta watsamasa, ba
don ta so ba ta dawo gidan don a farko tattarawa ta yi ta
koma gidam AlHassan da zama. Ya yi murmushi madadin
hararar ta ƙona ransa, wannan ya ƙara ba Hafsat haushi,
ta ja tsaki. Ita kuwa Dada ta ci gaba da hirarta da Tahir
ranta na mata wani irin dadi. Kusan yanzun ta saba da shi
sosai don kamar ba yaron da a baya ya ke wucesu kerere
babu ko gaisuwa ba. Ta kuma ƙara fahimtar ɗabi'un yaron,
jikinta na ba ta cewar duk wani mugayen halayensa akan
waɗanda ba ya so ya ƙare. Kuma zuga ce kawai.
"Dada anya ba nan zan dawo da zama na dindindin ba?"
Ya fadi yana mai kallon Hafsat, ta dubeshi da sauri, ya
kashemata ido ɗaya, ta mike sadda Dada ke ba shi goyon
bayan maganarsa fuskarta a sake.
Ya yi daidai da sallamar AlHassan. Suka amsa, Tahir ya
gaisheshi, ya amsa a ɗan sake don yaron ya soma ɗan
sakin jiki da shi, ya fahimci koda yana da matsalar, a
yanzun ta kau.
"Ke kuma zo dama ina nemanki."
Muryar AlHassan ya katse Hafsat daga tafiyar da ta soma.
Ta ji kamar ta sa ihu, Tahir kam ransa ya ƙara fari ƙal
sadda ya soma kai lomar abincin da ta girka da hannunta.
Ta dawo ta zauna ta gaidashi kamar ta yi kuka. AlHassan
ya murmusa don yasan kanun zancen.
"Jiya ina kika je? Na zo ance kin fita."
Ta ɗan tura baki.
"Gidan su Iklima na je."
Ya ɗan ɗaure fuska.
"Kuma ai na hanaki zumuncin da yarinyar ko kin manta?"
"Ka yi hakuri."
Ta faɗi a ƙagauce don Allah-Allah ta ke yi ta shiga ciki
don tserewa kallon da Tahir ke mata.
"Shikenan, je ki."
Ya ba ta umarni lura da ya yi har sannan babu wata
shaƙuwa tsakaninta da yaron. Shima ya fi kaunar hakan ko
don gudun abinda zai je ya zo. Wayarsa ta yi ƙara, ya
duba, Rasheed ne daga Saudia.
Ya ɗaga suka gaisa a mutunce.
"Ina ta so na kiraka sai dai Allah bai ban iko ba sai yanzu.
Ya su Dada?"
Alhassan ya murmusa.
"Alhamdulillah, gamunan duka lafiya. Nima rashin
lambarka ne ya sa na hakura. Fatan ka iske mutan gidan
lafiya?"
"Duka kowa lafiya. Akan Hussein ne nayi kiranka. Na tuna
wani abu."
Jin haka AlHassan ya miƙe da sauri har Dada da Tahir na
binsa da kallo.
"Lafiya?" Dada ta tambaya. Ya ɗan dubesu.
"Babu komai Dada, bari na amsa waya ina zuwa."
Daga nan ya fita waje da sauri-saurinsa. Hannunsa har
rawa ya ke yi.
"Ina jinka Rasheed, me ka tuna?"
Rasheed ya ba shi labarin kaf abinda ya faru a ranar da
suka yi bikin kammala makarantarsu a DUBAI shi da
Hussein. Bai ɓoyemishi wani labari da Hussein ya ba shi
ba a ranar har suke dariya.
Safa da marwa AlHassan ya fara gami da dafe goshi.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!Meyasa ban tuna da
hakan ba? Meyasa muka kasa tunawa da cewar itama za
ta aikata?!"
Rasheed ya amsa.
"Nima ban tuna da lamarinta ba sai yanzun da Mamina ta
ankarar da ni!"
Cikim gigicewa AlHassan ya ƙara jefamasa tambaya.
"Maminka? Ta santa?"
"Eh ta san ta, farin sani ma! Zan tambayi dukkan wani
bayani game da ita zuwa safiyarku zan kiraka, ina ji a
jikina ɓatan Hussein nada alaƙa da ita. Mu binciki inda
take don mu tabbatar."
Gumi sosai AlHassan ke yi, kirjinsa na bugu da ƙarfi. Ya
dafe goshi karo na biyu.
"Please kar ka ɓata lokaci Rasheed."
Ya fadi kamar zai yi kuka.
"Na damu da Hussein, na daukeshi dan uwa ba aboki ba.
In sha Allahu komai zai zo karshe. "
Jinjina kai AlHassan ya yi cikin son gasƙata hakan. Daga
bisani suka yi sallama.
"Meyasa ban tuna da ita ba?!" Ya fadi a fili zuciyarsa na
wani zafi. Kamar faifan bidiyo haka komai ya shiga
dawomasa filla-filla. Ya runtse idanu yana addu'ar neman
dacewa.
***
DAURA..
Idan Ramlat ta ce bikin ya yi mata dadi toh fa ƙarya ce
kawai saboda kusan faɗa iyayen aka yi game da aurenta
da Chairman wanda ba su da labarin zuwansa har Daura
gaida tsoffin sai a sannan. Hankalinta da na yayyun ya
tashi.
"Wato dai Chairman makircinnasa ya kai inda ya kai!"
Cewar Sauda bayan sun gama sauraron labarin Chairman
daga bakin Ramlat.
"Mtsw, iyayenmu ne abin duniya yanzu sai ya rufemusu
ido wallahi, daga ƙin gaskiya sai ɓata fa. Yanzu idan aka
bari kika aureshi mene makomarki? Nikam gaskiya ke na
fi jin haushi ma wallahi Ramlat, kiyi hakuri kinsan ban iya
ɓoye abinda ke raina ba. Amma kefa bazawara ce, ta ya
ya kuma ta ina za ki zauna a tauye hakkinki? Kamar ba ke
ce kika jajirce a baya har kika auri wanda ranki ke so ba?"
Naja ta fadi ranta na ƙuna, Ramlat dai dubansu take kowa
da irin kalar ƙorafinsa. Zagi kam Chairman ya sha. Tsam!
Ta miƙe ta fita dama hijab ne a jikinta, tana ji suna kiranta
da tambayar ko haushinsu ta ji amma ba ta ko iya
waigowa ba. Kai tsaye ɗakin Malam Yahaya tsoho mai
ran ƙarfe, cikin maza shi ɗaya tilo ya yi saura a ɓangare
iyayen su Abba, wato Malam Abdullahi, Mu'azzam da ma
sauransu. da suka rasu.
Yana zaune yana shan fura ga rediyonsa a kusa,
sallamarta ya dauki hankalinsa, ya amsa ta karasa ta
zauna.
"Wace ce ne? Ko Uwani ce?"
Ya tambaya yana kakkanne idanu don ba kasafai ya ke
gane mutane ba. Bakin har rawa yake ta amsa
"Malam ni ce, Ramlatu."
Ya yi ƴar dariya.
"Ki ce Amaryar Dikko ce. Ince dai lafiya?"
Kiranta Amaryar Dikko ya ɓata ranta ainun, ta haɗiyi miyau
mai ɗaci. Idanunta sula cicciko da kwalla.
"Malam don Allah ka taimakamin, kai kadai za ka yiwa su
Kawu Bello magana su ji. Wallahi bana son Dikko, don
Allah ku ban lokaci na muku alƙawarin kawomaku wanda
zan aura nan kusa da yardar Allah."
"Wane magana kike yi haka Ramlatu? Abinda ki ka aikata
a baya ne kike kokarin maimaita shi a yanzun? Ki fita
idona wallahi! Ni ba ubanki ba ne da kika raina."
Zuciyarta ta yi wani irin nauyi, ta kasa daurewa sai da
hawayen suka zubo. Wannan baƙin fentin da ta gogawa
kanta ba ta san sadda zai gogu har yan uwa su yi mata
kallon mutum mai ƙima ba. Ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta
zayyanemishi duk wasu munanan ɗabi'un Chairman da ta
sani. Ya yi shiru yana saurare har ta kai aya. Shiru ya biyo
baya kafin ya jinjina kai.
"Shikenan, zan wakilta Iro (babban ɗansa) ya bincikamin
a can Kanon. Idan har babu ɓurɓushin gaskiya game da
abinda kika faɗa lallai ki sani, ni da kaina zan ɗaura
aurenki da mutuminnan."
Ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin dama-dama. Kusan
tun zuwanta banda Gwaggo Hansai da ta fahimceta da
ɗaiɗaiku cikin gwaggonnin nata, sai yanzu ta samu
nutsuwar da ba ta ji ba. Ga zafin Hussein ba ta ƙara
magana da Hussein ba yau kwana huɗu kenan da zuwanta
garin.
A sanyaye ta mike ta fita, kiciɓus suka yi da Harira ɗiyar
Amaryar Kawu Bello ta biyu, dagaske laɓe ta yi a zauren.
Sai dai ta wayance.
"Af, ke ce a ciki? Dama abincin Malam ne Gwaggo ta ce
na miƙa."
Ta gyadamata kai kawai ta yi gaba. Ta rantse dai ba ta
auren Chairman. Don haka za ta bi ta salama ta san yanda
akai ta rabu da shi. A baya ta yi tunanin za ta iya hakurin
zama da shi ko ba so, sai dai yanzun da so da kaunar
Hussein ke ƙara ruruwa a zuciyarta, ba ta jin ko kusa za ta
iya. Allah-Allah ta ke yi su koma Kano don tuni ta samu
cikakken sunan Kawun su Hussein dake Kano a wurin
Hafsat. Dabara ta yi mata da cewar ta shiga Yakasan ta ga
wata mai kama da ita. A haka har ta gangaro inda Hafsat
ta yi mata bayanin cikakken sunan Kawunnasu. Babban
burinta ta koma Kano ta je ta sameshi. Ta fi kaunar bin
komai daki-daki.
Maimakon ta koma ɗakin, sai ta wuce sashin surukar
Malam, matar Iro, Hajara, anan ta yi zamanta tana danna
waya. Muhibbat ta kira suka gaisa sannan ta haɗata da su
Ansar da Ummi aka gaisa. Ba karamin kewar yarannata ta
yi ba, ta yi musu albishir na dawowarsu a gobe.
Saƙo ta ga ya shigo, saƙon daga AlHassan, ta mike zaune
da azama ta shiga whatsapp.
*"Ƙanwata, kinsan wata Hajiya Zeenatu Bashir a Kano? Ta
taɓa zaman Saudiyya, kuma tana taɓa siyasa a baya. Yanzu
dai ban da masaniyar komai a kanta." *
Dafe kirji ta yi. Shikenan duk yanda aka yi NESA CE TA
MATSO KUSA!
KARFEN KAFA Chapter 56
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


"Eh na san ta." *_
Har ta rubuta hakan, sai ta goge da sauri. Toh idan ta ce
ta san ta kai tsaye me ta yi kenan? Girgiza kai ta yi.
Shiru ta yi na ƴan sakanni ba zato wayarta ta shiga
ringing. Ta duba, AlHassan ne. Ta danna gami da karawa
a kunne. Dakyar ya samu nutsuwar amsa sallamarta.
"Kin buɗe saƙona ba ki ce komai ba. Kin san ta?"
Ramlat ta sauke numfashi.
"Ka yu hakuri sai dai magana ce mai tsawo da ba za ta
yiwu ta waya ba, yaushe za ka samu shigowa Kano?"
"Ko gobe ne zan iya tahowa Ramlat. Ki amsamin da kin
san ta ko aa."
Ganin irin ruɗanin da muryarsa ta nuna, yasa ta saurin
amsa mishi.
"Na san ta. Har abinda ba ka zato duk na sani, idan da
dama gobe.."
"Kar ki damu, gobe in sha Allah zan zo Kano."
Ya katse hanzarinta da gaggawa. Ta amsa da toh, godiya
ya yi mata ya katse kiran.
Abu na farko da ya daurewa Ramlat kai, ta yaya Hussein
ya gane zai iya samun wani bayani ta hanyarta? Sannan a
ina ya san sunan Hajiya Zeenatu? Wannan tambayar babu
mai amsamata sai shi da kansa don haka ya haɗiye
abinta. Ta shiga zullumi ba kaɗan ba, ganin ta kasa danne
abin, kawai sai ta kira Hisham.
"Ran Amarya ya daɗe."
Ta ja guntun tsaki, Hisham tun sadda ya ji labarin
Chairman ya ke zolayarta.
"Ba wannan ba please, magana ce da ta shafi Hussein."
Jin haka sai ya maida hankali. Ta ba shi labarin yanda
suka yi da AlHassan har da ƙudurinta na zuwa ganin
Kawun Hussein dake zaune a Kano
"Da mamaki ace mutumin dake zaune cikin ƙwaryar Kano
ya kasa sanin akwai wani jininsa a Kanon. Sai dai ban san
irin raunin alaƙar dake tsakaninsu ba. Ina goyon bayan ki
gwada zuwa ki sameshi. Sai dai wani hanzari ba gudu ba,
ta ya ya Hussein zai soma fuskantar lamarin? Anya ba
kuskure ba ne kai tsaye AlHassan ya tunkareshi ba?"
Ramlat ta jinjina kai.
"Shiyasa nake son zuwa na faɗawa Kawunnasu. Idan ma
ya sani ka ga za mu sani, amma ba na jin zai sani. Haba,
ɗan uwansu fa."
"Hum, shikenan Ramlat. Allah Ya maidoku lafiya. Ya ɗora
mu a kansu."
Ta amsa da amin kafin ya ba Aisha wayar suka gaisa da
taɓa hirar Daura daga bisani suka yi sallama.
***
WASHEGARI...
*LAMIƊO CRESCENT *
"Na yarda, wace ƙasar ki ka zaɓa mana?"
Mamakin amsar Hussein ya daskarar da Hajiya Zeenatu
lokaci guda, ta ƙara matse layar hannunta domin ta yi
imanin shi ne dalilin da yasa ya yi amanna da zancenta.
'Allah Ya yi maki albarka Hajiya Batool aminiyar kwarai.'
Ta fadi a ƙasan ranta bayan ta tuno shawararta ta bi ta je
wurin Bokansu ta karɓo layar.
Farr ta yi da ido baki yaƙi rufuwa tana duban Hussein da
rabin hankalinsa ke kan Laptop ɗinsa yana shigar da wasu
takardu don son kauda damuwar da ke sukarsa a ƙirji.
"London nake son mu je, ka ga daga nan sai a binciki
lafiyata sosai akan matsalar haihuwa. Kana iya ɗaukar
annual leave."
Ta fadi cikin dabara tana mai kissimawa a ranta shikenan
Hussein ya yi bankwana da Nijeriya har abada.
Ba tare da ya kalleta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login