Showing 3001 words to 6000 words out of 113545 words
Chapter 2 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
ɗan biyo baya, ba wanda ya ce uffan tsakaninsu.
Ga Hisham, dama ya bata ta nutsu ta bashi amsa, ga
Ramlat kuwa jinin jikinta ta sha da kuma fargabar dalilin
Hisham na nemanta. Can dai ta nisa.
"Shikenan, gobe In sha Allah daga wurin aiki zan biyo."
"Yauwa Antinmu, Nagode sosai. A gaidamin ƴaƴana."
Daga nan ya miƙa wa A'isha kan wayar ya shige daki cike
da damuwar abokinsa.
"Auta, lafiya dai ko? Ba wani laifin kika yi ba?"
Dariya A'isha ta yi jin tambayar da Ramlat ta watsomata ta
cikin wayar.
"Wallahi lafiya sumul, bansan menene ba amma ina fatan
alheri ne."
Ajiyar zuciya mai karfi Ramlat ta sauke.
"Shikenan Auta, sai Allah Ya kaimu goben."
Daga nan suka ajiye wayar.
***
Ramlat ta kasa sukuni tun bayan wayar, har ta kasa
hakuri sai da ta faɗawa Hajiya. Shiru Hajiya ta yi na ƴan
daƙiƙa kafin ta ce.
"Toh ko wani laifin Auta ta yi ne yake ɓoyewa?"
Girgiza kai Ramlat ta yi.
"Na tambayeta ta tabbatarmin lafiya kalau. Ko mene dai
idan naje goben in sha Allah zan ji."
"Ya za ki yi da kiran da Dakta ke miki?"
Gabanta ya fadi, ɗazun da yamma a hanyarta ta dawowa
daga wurin aiki ne ta amsa wayar Baba Dakta akan yana
nemanta a gidansa. Tun sadda ta ji hakan ta rasa sukuni,
tasan tatsuniyar gizo bai wuce na ƙoƙi.
"Kin yi shiru." Hajiya ta furta tana kallon yanda ta ke dama
fura cikin nono ba tare da ta san me take ba don inda
ludayin ya ke kallo daban da abinda ta ke.
Maganar Hajiyar ya maidota cikin nutsuwarta. Sauke
ajiyar zuciya ta yi.
"Nasan ba wani jimawa zan yi a gidan A'isha ba, da zarar
mun kammala zan wuce gidan Baba Dakta kafin na
shigo."
Girgiza kai Hajiya ta yi tana murmushi.
"Ramlatu kenan, ba haka za'a yi ba. Ina gidannan ina
gidan Baba Dakta? Ki tashi dai ki je yanzu kinga goben kin
huta. Miƙomin furar na dame abata."
Ta kalli Hajiya a raunane, babu damar ta ce a'a, ta mike
jiki a sanyaye ta miƙamata.
"Mami zan bi ki!"
Ummi ta furta tana ɗago kai daga zanen da take na
makaranta. Daƙuwa Hajiya ta mata.
"Gidanku, wato ma ba karatun kike ba kunnenki yana nan
ko? To babu inda za ki je, idan kuma kika bi ta babu ke ba
shan fura."
Ai da sauri ta ce ta fasa. Murmushi kawai Ramlat ta yi ta
nufi daki, hijabinta kawai ta zura ta dauki wayarta ta fito. A
sannan ko sallar Isha'i ba'a yi ba, an dai kusa kira. Ta yi
musu sallama ta fita.
***
Zuciyarta kamar ta yi tsalle ta fito sadda ta gama jin
dogon jawabin da Baba Dakta ya ɗauko game da batun
aure. Sai da ya gama nunamata muhimmancinsa ga
rayuwar ƴa mace kafin ya bita da nasiha mai ratsa jiki,
daga karshe ya tafi kai tsaye ga inda ya sa gaba.
"Lokaci ya yi da ya dace ke da kanki ki yiwa kanki faɗa ki
fiddo mijin aure Ramlatu, na kyaleki don a ganina kina da
ƴancin da za ki zaɓawa kanki abokin rayuwa wannan
karon ba tare da waninmu ya tilasta maki ba. Ki tsaida
hankalinki ki yi tunani mai kyau. Akwai da dama waɗanda
suka zo wurina neman aurenki kamar yanda shima
kawunki Bashir ya sameni da batun maneman aurenki sun
sameshi. Toh koda a baya bamu ba su damar neman
yardarki ba, wannan karon ba zamu hanasu ba Ramlatu.
Babban burinmu shi ne mu ga kema kin yi aure. Aiki ba ya
hana aure idan har mijinki ya amince, idan kuwa bai
amince ba sai ki zamanki a daki ki nemi wata sana'ar
kamar yanda ƴar uwarki ta yi."
Yana nufin Amrah. Wato ma dai ana zuwa har can Yakasai
neman aurenta? Wannan abu ya dauremata kai, kodayake
yana daga dalilinta na dauke ƙafa a gidan Hajja, a gidan
ma akwai ɗan Kawunta da ke sonta sai dai mahaifiyarsa
ta ce sam ba da ita ba. Wannan shine rikici ma na karshe
da akai har zuwa gidan ya fice a ranta. Basu da masaniyar
babu Kamalu a ƙoƙon ranta, ba ma shi kadai ba, kowane
namiji ma ba ya gabanta. Aliyu ta so, kuma har gobe
akwai kaunarsa a zuciyarta. Rana bai taɓa fitowa ya faɗi
ba tare da ta yi mishi addu'a ba.
"Kinji ko?"
Maganar Baba Dakta ya katsemata tunani. Gyada kai ta yi
tana share kwallar da ta cikamata idanu. Cikin sallamawa
ta amsa.
"Eh Baba Dakta, da yardar Allah zan yi yanda ku ke so."
Murmushi ya yi gami da gyara zaman gilashinsa.
"Allah Ya yi maki albarka. Ya zaɓamaki abokin rayuwa
wanda za ku rayu har abada cikin aminci, so da yarda."
Kunya ta sanya ta kasa amsawa sai murmushi.
"Sai abu na gaba, meyasa bakya tura yarannan su gaisa da
dangin mahaifinsu?"
Ta ƙara russunar da kai.
"Kwanaki ma fa sun je family meeting dinsu."
"Aa, wannan ba hujja ba ce, ai inada labarin shima ba da
son ranki ba wannan yarinyar ta wurin Justice ce ta zo ta
tafi da su kina cika da batsewa kamar alkubus ko?"
Dariya ta yi shima ya tayata don dama ya fadi ne don ta
maido walwalarta. Mamaki take yi na inda ya samu
labarinnan amma ta fi zaton a bakin Amrah ne.
"Ba'a haka Ramlatu, yanda kike da iko a kansu, su ma
suna da iko. Wannan karon idan aka yi hutu idan ma ba ki
sanya an kai su ba, da kaina zan kwashesu na kai.
Dolensu ne fa, idan kika hanasu zumunci da su, wataran
da ƙafarsu zasu taka su je, lokacin ne kuma za ki sha
kunya."
Har sannan murmushi take, kaunar Baba Dakta na ƙara
ratsamata zuciya da gangar jiki, tana jinsa kamar Abbanta.
Irin kulawa da kaunar da yake nunamusu, ko Abba yana
raye abinda zai yi kenan. Daidai gwargwado yana kokari
wurin kula da gidansu, abinci duk wata sai Nana Dakta ya
ajiyemusu, samun mutum kuma amini irinsa abu ne mai
matukar wahala a wannan ƙarnin.
Ba ita ta bar gidan ba sai da suka ci abinci ta yi sallah.
Hajiya ta ji dadin dalilin kiran Baba Dakta, ta kara da fadin.
"Ai gwara dai ya tunasar da ke, idan kuwa kin fi kaunar mu
zauna muna haɗa ƙugu a gidannan sai ki yi kiga idan zai
ɓullar da ke. Gwara ni na tsufa na ci ƙuruciyata yanda ya
kamata."
Dariya ma maganar ta ba Ramlat, furarta da aka bar mata
ta sanya a fridge, ta tashi yaran da suka sheme a ƙasa
suna bacci ta kai kowannensu makwancinsa. Affan kuwa
sai da ta tabbatar ta kai shi ya yi fitsari kafin ta kwantar da
shi saman gadonta bayan ta kakkaɓe. Ta yi mishi addu'a
sannan ta faɗa wanka.
***
WASHEGARI...
Tunda ta ji kira daga sama wai kuma daga Chairman Aliyu
Dikko ta ji kanta ya yi ringingin, ma'aikata dai sun fi dubu
a ƙasan bawan Allahnan, ta ina har ya ganeta da har zai
turo Oganta ya kirata? Sai kuma da ta tuna Oga ya nema
kafin ita ne yasa ta gane bakin zaren.
Kai tsaye tare da Oga suka shiga wurin Chairman. Matar
da ta gani zaune yasa ta shan jinin jikinta. Sanadin aikinta
dai Hajiya Zeenatu za ta yi mata. Sai cika take tana
batsewa, kallon da take watsamata tun shigarta ofis din
ya sanya Ramlat daga kallo ɗaya ba ta ƙara duban inda
take ba har suka karasa.
Chairman ya na juyi saman kujerarsa yake duban wacce
aka kira da Ramlat duba irin na ƙurillah. Ya haɗiyi miyau
maƙwat. Koda ya taɓa ganinta ya manta saboda dubunnan
matan da ke zirga-zirga a Revenue.
"Yallaɓai gatanan."
Oga Ɗalhatu ya ƙara magana a karo na biyu ganin kamar
Chairman ba ya tare da shi, Chairman ya yi gyaran murya
kafin ya maido nutsuwarsa ya saita kansa.
"Yauwa Ɗalhatu, kana iya tafiya." Cike da girmamawa Oga
Ɗalhatu ya amsa gami da barin wurin.
"Wannan ita ce?"
Chairman ya fadi gami da ɗauke kallonsa kamar ba ya so
daga kan Ramlat zuwa na Hajiya.
"Ita ce! Karuwa la'ananninyar Allah! Ita ce ke bibiyar
mijina.!"
Zuciya ya zo wa Ramlat wuya, wannan suna da Hajiya ke
laƙabamata ya isheta.
"Ni ba karuwa ba ce, kuma da kike fadin wai ina bibiyar
mijinki, ki tambayeshi ki ji sau nawa shi ya tako zuwa
gidanmu da sunan zance."
Ba zato Hajiya ta shammaceta ta kifamata mafi, itama ba
ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta ɗaga hannu da zummar ramawa,
tsawar Chairman ta dakatar da ita ta sauke hannun tana
kara zura dara-daran idanunta cikin na Hajiya. Itama
Hajiya Zeenatun kallonta take kafin cike da zafin rai ta
dubi Chairman.
"Me na faɗamaka?! Me nace game da yarinyar nan?!
Wallahi Dikko idan ba ka sallami wannan yarinyar a
ma'aikatarka ba ka sani abinda ka binne a hannuna yake,
da kaina zan tona asirinka a ..."
"Haba Hajiya Zeenatu, ya isa mana! Haba!"
"Ke wuce ki bar nan!" Ramlat ta haɗasu duka ta
watsamusu banzan kallo kafin a fusace ta bar ofis din, ba
ta jin ko ɗarr, ta shirya abinda ya fi kora daga aiki ma a yi
mata idan har akan Hajiya ne. Matar da ba ta san darajar
dan adam ba, ba ta kaicon a koreta daga aiki.
"Me kake nufi da hakan Dikko?!"
Hajiya Zeenatu ta furta rai a ɓace. Shima daure fuska ya yi
yana saita tunaninsa.
"Na ce ki bar komai a hannuna zan dauki mataki a kanta
ko?"
"Dikko na sanka kamar yunwar cikina, kar ka yi wasa da
hankalina."
Wani murmushi ya yi.
"Haba Hajjaju, na fadamaki da kaina zan dauki mataki don
wallahi nikam na ga abinda ba zan kyale ba."
Ta yamutse fuska.
"Me kake nufi?"
Ya gyara zama ya kora ruwa a cikin ƙaton tumbinsa
sannan ya yi mata bayani daki-daki, wani murmushi ta yi
kafin kuma ta kwashe da dariya yana tayata. Da yatsa ta
nuna saitin kwanyarta.
"Kai dinnan na yarda akwai ƙwaƙwalwa!"
Ya shafi sanƙonsa.
"Haba Hajjaju! Ai mun ci dubu sai ceto. Ke dai ki kwantar
da hankalinki."
Da wannan ta mike ta fice.
***
Da wani irin fushi take tuƙi, yanda Hisham ya matsu ta je
su yi magana haka itama ta matsu ta je ta ba shi saƙo ya
faɗawa Hussein akan matarsa. Har ta isa ƙofar gidan
A'isha ba ta ji wani sassauci a zuciyarta ba. Maigadin zai
budemata ƙyaure ta dakatar da shi, ko'ina ta rufe ta faɗa
gidan.
KARFEN KAFA Chapter 42
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Falon babu kowa shiru, sallama ta yi ba amsa don haka ta
yi zamanta tana jijjiga ƙafa, tunawa da ta yi ba ta yi sallar
La'asar ba ne yasa ta miƙewa ta faɗa ƙaramin ɗakin
saukar baƙi na A'isha.
***
A'isha ta fito daga daki ta yi turus ganin jaka da mayafi,
can kuma ta fahimci ko na wace, da wani ɗoki ta faɗa
ɗakin da ta san za ta iya ganinta ciki, ai kuwa ta ji motsin
ruwa a banɗaki, ba jimawa Ramlat ta fito. A'isha ta tsaya
wani sakaka tana kallonta.
"Ke kuma ina kika shiga na zo ina ta sallama shiru?"
Maimakon ta ba ta amsa, sai ta jefamata tambayar da ke
cinta.
"Lafiya kuwa? Kinga yanda idanunki suka kumbure suka yi
ja?"
Guntun tsaki ta ja, tana jan skirt din atamfarta don ya
sauka sosai.
"Bani hijabi."
Abinda ta ce kenan ba ta ko damu da ba ta amsa ba,
A'isha ta juya ta fita can kuma ta dawo dauke da Hijab.
Warware hijabin ta yi ta shiga kokarin zurawa.
"Ki kira mijinki idan ba ya gida ki ce na zo, sauri nake ba
zama zan yi ba A'isha."
Daga haka ta shiga kokarin tayar da sallah hawaye na
ciccikowa daga idanunta.
A'isha dai ta lura akwai matsala don haka ta fita ta ja
mata ƙofar. Wayarta ta fitar ta kira Hisham kamar yanda
ta nema ta sanar da shi zuwan Ramlat din. Ya yi mamaki
don a zatonsa sai zuwa yamma.
"Ki ce ta ɗan ƙara hakuri, nan da awa In Sha Allah zan
iso."
Daga haka A'isha ta katse wayar. Kicin ta faɗa ta
haɗomata abinci a faranti da lemu da ruwa. Komai ta
haɗa ta kai mata ɗakin, a sannan ta idar da sallah ta
zauna kawai ta yi shiru. Ƙarasawa ta yi ta ajiyemata a
gefenta kafin ta ce.
"Mun yi waya ya ce nan da awa zai iso in Sha Allah."
Gyada kai kawai Ramlat ta yi.
"Wai don Allah meke faruwa haka ne? Duk kin tayarmin da
hankali na rasa nutsuwa."
Sai a sannan ta ɗan yi murmushin yaƙe.
"Ba komai."
Haushi ya sa A'isha miƙewa ta fice. Sai duk kuma ta ji ba
ta kyauta ba, ai laifin wani ba ya shafar wani. Don haka ta
janyo plate din ta tsakuri abincin gami da korawa da lemu.
A falon ta tarar da A'isha ta ƙura wa talabijin idanu tashar
Zee World. Babu tabbacin ma hankalinta na wurin. Zama
ta yi.
"Ke Auta sarkin fushi, ba wani abu bane ba fa. A wurin aiki
ne aka ɓatan rai."
Ganin haka itama A'isha ta sauko.
"Kai amma kin faɗarmin da gaba, dama nayi tunanin
hakan. Allah Yasa dai ba wannan Halimar ba ce."
Murmushi Ramlat ta yi. Ta tuna irin walwalar da Halima ke
yi na ganinta cikin wannan yanayi, wanda dai ba ya sonka
zai wuya ya so ka.
Share batun suka yi suka koma hirar abinda ya shafi bikin
Munir. A hankali kuma zuciyarta ta ɗan yi sanyi.
Karfe biyar da wasu mintocin, Hisham ya shigo gidan.
Gaisawa kawai suka yi yana jan ta da zolaya sannan ya
faɗa ciki don kimtsawa, A'isha ta mara mishi baya.
Ba jimawa ya fito da alama wanka ya yi, ya sauya daga
manyan kaya zuwa jallabiya.
"Antinmu ina wuni."
Ta ɗan harareshi.
"Na gaji da wannan doguwar gaisuwar, na ƙagu ka
faɗamin dalilin wannan neman don nima inada magana."
Ya yi dariya.
"Allah Ya ba ki hakuri toh."
Daga nan ya bata labarin komai har zuwa kan kauracewa
Hajiya Zeenatu da Hussein ke buƙatar ta yi. Wani huci take
yi har hancinta na buɗuwa da rufewa.
"Ka gama?"
Cikin haɗiye dariyarsa ya gyaɗa kai.
"Zan so ace shi wanda ya turo ka da wannan saƙon yana
zaune tare da mu..."
"Sai na kirashi."
Ya katse ta da hanzari, ta ja guntun tsaki.
"Banda wannan lokacin, sai dai ka fadamasa ta cikin gida
ake fara komai kan a duba waje. Ya isa da matarsa ne za
ta dinga bibiyata har wurin aiki tana ɓatan suna? Waye
mijinnata da har ya ishi mutum kallo? Wallahi nikam na fi
karfin zama inuwa daya da wannan banzar matar tasa ko
nace uwar mata don a haife ma ta haifeshi."
Ta shiga basu labarin abinda Hajiya Zeenatu ta yi yau a
ofishinsu. Hisham kansa shima ransa ya ɓaci.
"Amma wannan dai ba ta da hankali ko?"
A'isha ta furta cike da ɓacin rai.
Ba tare da Ramlat ta kula ba ta ci gaba da magana tana
duban Hisham
"Don haka ka yi mishi magana, matarsa ta fita hanyata!
Wallahi darajar zumuntarku da shi nake dubawa, amma
idan har bai dau mataki a kanta ba, ni kuma ba zan fasa
gasamata magana a ko'ina muka hadu ba idan ta taɓoni.
Abin nata ya wuce hankali har wurin aikina? Me ma
tsaremata wai? Ni ba son Mijinta nake ba, shima ba sona
yake ba! Ya kamata ta san wannan!"
Gyada kai Hisham ya yi.
"Hakane, gaskiya kuma abin na neman wuce gona da iri.
Kiyi hakuri don Allah, ni da kaina daren yau ba gobe ba da
yardar Allah zan sameshi mu yi maganar. Sai dai fa
Ramlat, akwai abinda ya ban mamaki da kuma ɗaurewar
kai game da Hussein."
Za ta so su yi maganar sai dai a yanda yau ranta ke a
ɓace sunansa ma ba dadin faɗi yake mata ba, don haka
ta mike tsaye tana yamutsa fuska.
"Nikam mun gama magana ai inaga, gida zan wuce kafin
Hajiya ta neme ni."
A'isha da Hisham suka dubi juna, murmushi Hisham ya yi,
ya mata uzurin halin da take ciki na ɓacin rai. Har mota
suka yi mata rakiya sannan suka koma ciki. Kai tsaye ya
dau waya ya kira Hussein ya sanarmasa yana son su yi
magana, suka ajiye wajen da zasu haɗu.
***
Hajiya Zeenatu ta dubi mijinta da ya ajiye waya.
"Fita za ka yi kenan?" Ta fadi zuciyarta na wani irin sanyi
na farin ciki, ko ba komai za ta samu ta fita nata aikin.
Fuskarsa cike da mamakin yanda yau ba ta mishi ƙorafin
fitar dare ba ya dubeta. Dariya ta ɗan yi ta kama hannunsa
ta ɗan murza.
"Naga kamar da Hisham ka yi waya. Ai ba zan hanaka
zumunci da shi ba. Ko ba komai ya so ka da alheri bai bar
min kai cikin mawuyacin hali ba rannan. Amma naga
kamar da ɗan hadari a garin."
Murmushi ya ɗan yi.
"Kar ki damu Hajjaju, ba nisa zamu yi ba ai, dayake shima
nan Lamiɗo Crescent ya ke."
Ba haka ta so ba don haka da azama ta tari numfashinsa.
"Toh amma fa gaskiya ina son ka tahomin da Balangunnan
na rijiyar zaki mai dadi. Na kasa cin abincin John."
"Yanda kike so hakan za'a yi."
Suka yiwa juna murmushi kafin ya mike ya dauki
wayoyinsa da mukullin mota.
"Sai na dawo ko?"
Ta gyada kai tana wani lumshe masa idanu a son ta
burgeshi karshe. Tana jin fitarsa ta mike da azama ta hau
sama tana nishi da gyara ɗaurin zaninta da ke neman
faɗuwa. Sai da ta soma fiddo ruwan maganinnan ta faɗa
banɗaki ta yi tsarki da shi tas ta maida cikin jarkar sannan
ta maidashi maɓoyarsa. Daga nan ta sanya layar a jaka ta
dauki mukullin motarta ta fita.
Maigadin dai ba abinda ya shallesa, tashi ya yi ya bude ta
fice ya maida ƙyauren gida.
Tuƙinta take tana mai jin wani ƙarfin gwuiwa na
zuwarmata wanda ke ƙara sanyata jin ba za ta fasa abinda
ta yi niyya ba. A farko ta dauka lamarin Ramlat mai sauƙi
ne da za ta iya maganceshi da hannunta, gari ne ba za ta
bari ba, asalima ba za ta taɓa aikata yin wanka a tsakar
dare ba kuma ba don ba za ta iya bane, sai don a ganinta
asarar lokaci ne don babu abinda zai sa ta bar garin
saboda Ramlat. A cewar ta Ramlatu ta yi kaɗan, gwara dai
ta yi wanda za ta mallake Hussein yanda fita ma sai da
izninta zai yi. Kallon sararin samaniya ta yi yanda ake zuba
walƙiya. Ta ƙara maida hankali ga tuƙinta tana sharara
gudu kamar wata namiji.
Ba ta tsaya ko'ina ba sai a wani filin Allah da ba gida gaba
babu a baya. Gari sai walƙiya ake yi da iska mai daɗi.
Wani rami ne ƙato wanda a ƴan unguwar basu komai da
shi sai aiken almajirai su zubarmusu da shara sai kuwa
ƴan shaye-shaye da kan zo su maida wurin matattara.
Babu tsoron jinnu balle shaiɗanu ta nufi bolar gadan-
gadan.
Tsammaninta babu kowa a wurin saboda yanayin iskar da
ake da kuma walkiya, a zatonta za ta yi aikinta ta
kammala kamar yanda Isuhu ya ce kar wanda ya ganta,
sai dai tana hawa saman bolar gami da kokarin zura layar,
wata fitila ta hasketa ga kuma hasken walƙiya.
"Kaii...wa..ye anan?"
Daga yanayin maganar za ka san ɗan maye ne.
Cikin Hajiya ya ɗuri ruwa, ba ta yi aune ba wani ruwan
hawaye ya tahomata, ba wai tsoron ɗan mayen ne ya
shigeta ba illa ɓatamata aikin dubunnan da aka yi.
"Allah Ya isa Batool!"
Abinda ta ce kenan a fili don da shawararta ta zo wannan
bolar, sam ba nan ta so zuwa ba.
Hankali a tashe ta sauko duk da hakan sai da ta soke
layar. Daidai nan ɗan mayen hannunsa riƙe da wuƙa ya
zagayo yana ƙara kallonta sosai. Zobunan gwal ne a
hannunta duk da ta saka mayafi bai hana a gani ba. Da
sauri ta ce.
"Kana so? Gwal ne?"
Wata dariya ya yi yana rangaji. Ta saba karawa da irinsu.
Kafin ya kai ga magana ta ciro ta damƙa masa.
"Kai Hajjaju! Kin san homular! (Formular)"
Ita dai haushinsa take ji kamar ta shaƙeshi, ta fice