Showing 12001 words to 15000 words out of 113545 words
Chapter 5 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
ta ke ji.
Mace ta riga da ta raina mijinta ko kadan ma ba ta ganin
girmansa.
"Allah Ya kyauta." Ta faɗi a fili.
Kayan islamiyya ta fiddowa yaranta ta ba kowanne nashi
kafin ta shiga shirya Affan. Har ta kammala ta fito ta
zubamusu ruwa a robobi ta basu Hajiya na ta shari'a
tsakanin miji da matar. Idanunta ya kai ga Bilkisu, wata
uwar harara ta watsamata, ita abin ma sai ya ba ta dariya
ganin ai ba ita ta kai zoman ba, ratayar ma ba'a ba ta ba.
Hijab ta sanya don ta fi kaunar ta bar musu gidan wannan
yasa ta dauki wayarta ta yiwa Hajiya sallama da zummar
za ta kai su Ummi makaranta daga haka ta fice don
hankalin Hajiyar ma ba ya gareta kawai ta amsa da jeki.
***
Koda ta miƙa yaran ta wuce gidan Umman Amrah. Ta
saki baki ganin Zaituna.
"Wai Umma har yanzu ba su ɗauketa ba?"
Umma ta dara.
"Sun dauka mana, maidomin abata suka yi. Kusan tun
bikin Muniru."
Ramlat ta murmusa.
"A'a wannan dai ta zama kishiyar ta gaske. A bar maki ita
kawai."
Kama baki Umma ta yi.
"Wannan Babannata ne zai bar ta?Bari kiga nan kusa za ki
ganshi ya zo daukarta. Yaran yanzu da shegen son ƴaƴa,
wa ya sani ma ko ita ke turoshi."
Dariya sosai abin ya ba Ramlat.
"Kema dai ɗiyata ina nan ina addu'a Allah Ya zaɓamaki
miji nagari mu sha biki. Ba na jin dadin ganinki a gida da
kuruciyarki. Ai ina jin ba ki yi talatin ba ko?"
Da murmushi ta girgiza kai.
"Ban kai ba Umma. Kin manta watanni kawai na ba
Amrah."
Umma ta yi dariya.
"Ke da Amrah ai rigimarku sai ku, ki ce kin girmeta itama
ta ce ta girmeki."
"Allah na girmi Amrah."
Ita dai Umma ta amsa da toh sannan ta mike zuwa daki
tana dariya, can ta fito rike da wani littafin adduo'i ta
mikawa Ramlat.
"Ki dinga karantawa, akwai adduo'i sahihai da kuma
nafiloli. Kar ki yi wasa don Allah."
Ta amsa da toh, mutanennan suna da burin ta yi aure, ba
za ta ce ba ta so ba. Sai dai tana duba yaranta, ba ta
kaunar yin nisa da su. Aure kuma ance ba inda ba ya kai
mutum.
Kwanciya sosai ta yi saman kujera sadda Umma ta mike
ta wuce bangaren mijinta da ta ji tsayuwar motarsa.
Wannan ya ba Ramlat damar danna waya, lambar Hussein
ta bude ta ga dacewar ta yi saving. Cak ta tsaya tana
tunanin sunan da za ta ɗora akan lambar, can kuma ta yi
murmushi ta rubuta Mr Wuf. Ita kanta abin dariya ya bata.
Daga haka ta faɗa whatsapp ta shiga duba contact har
ta faɗa saman lambarsa. Dp dinsa na wani ƙaton ocean
ne sai rana da ta ɗauko faɗuwa daga sama. Murmushi ta
yi ta je kan Status na profile. Busy kawai aka rubuta da
alama kuma ya jima sosai a hakan.
Tana komawa kan whatsapp ta ci karo da sallamar
Alhassan. Ganin yana online ta amsa da sauri. Suka gaisa
ta tambayi Dada da iyalinsa. Ya amsa har da turo emoji na
nuna jin dadinsa da hakan. Ya tambayi mutan gidansu
shima.
_*"Ina nan shigowa Kano karshen satin da zamu shiga in
sha Allah. Zan kawomaki Fatina ku gaisa idan ba damuwa.
Address?" *_
Ganin abinda ya rubuta ne yasa ta saurin miƙewa zaune.
Alhassan zai shiga Kano? Kodai yana da ƴan uwa a Kano?
Wannan tambaya ce da ba ta da amsarta. Ga haɗiyi wani
yawu kafin ta amsa mishi.
_*"Kano na marhabin da ku, Allah Ya kawoku lafiya. Ashe
muna da ƴan uwa a Kano kenan._*
Ta tambaya cike da ƙaguwa . Dariya ya aikomata kafin ta
ga yana recording. Ta bude ta saurara.
"Eh toh, muna da yan uwa. Akwai yayan Babanmu a Kano.
Yanzun ma biki za'a yi na samarin yaransa har biyu, shi
ne zan kawo su Dada da Maman Fatima. Ina fatan za ku
hadu ku gaisa?"
Abinda ya ce kenan, ta yi shiru, gaba daya ya dulmiyar da
ita cikin tunani. Kenan Alhassan suna da dangi a Kano?
Toh ta yaya zai yiwu ace ba su taɓa cin karo da Hussein
ba? Anya zai yiwu? Ace kuna gari daya ba ku taɓa sanin
juna ba. Kodai Hussein din ne bai da zumunci?
Abinda ta yi ta rayawa kenan,can ta tuno ba ta ba shi
amsa ba, gudun kar ya yi tunanin wani abin ne yasa ta ba
da amsa.
_*Wow, Allah Ya kaimu toh. Zan so na ga Fatima. *_
Suka ɗan taɓa hira kafin su yiwa juna sallama. Ita dai ta
ajiye wayar kawai amma hankalinta gaba daya ya tafi ga
tunanin wannan lamarin mai ban mamaki da ɗaure kai.
Ba ita ta bar gidan ba sai da lokacin tashin yaranta ya yi,
ta so ta ƙi shiga wurin Baba Dakta saboda kar ya yi mata
batun aure, a karshe dai ta daure ta shiga kuma har suka
gaisa ta fito suka taɓa barkwanci, bai mata zancen ba.
Tana shiga da yaran falon Hajiya, ta ga babu su Munir
balle yaransu sai Hajiya da Ladidi da ke tattaunawa.
Hajiya na ganinta ta yi dariya.
"Ja'ira, wata kika gudu kika bar ni da su ko?"
Tana dariya ta zauna.
"Me zan ce? Na saka baki Yaya Munir ya ce na mishi
rashin kunya? Ya suka ƙare?"
Taɓe baki Hajiya ta yi.
"Na yi musu dai nasiha daidai gwargwadona. A karshe
sun ba juna hakuri suka kwashi yaransu suka yi gaba."
"Allah Ya daidaita lamarin."
Suka amsa addu'ar Ramlat da Amin.
***
LAMIƊO CRESCENT.
Kallon abincin ta ke kamar ta fasa ihun kuka tsabar takaici
da bakin ciki. Ta dage ta yi girki da ruwan maganin
tarkinta amma Hussein ya tahomusu da wasu manyan
kifaye har uku gasassu da aka sanya chips a gefe da
kayan tumatir albasa sai ɗan yaji a wata ƙaramar roba. Ci
ya ke yana jin dadinsa ya dubeta.
"Madam tunanin me kike ne? Wannan fa don ke na siyo.
Please come and join me."
Ita a dole shagwaɓa irin ta masoya, ta yamutse fuska.
"Ni a'a gaskiya, na dage na maka girki da kaina da
hannuna yanzun kuma ka cemin ka ƙoshi?"
Ya yi murmushi.
"Shikenan, ki sanyamin a fridge I promise you, da shi zan
yi breakfast. Hankalinki ya kwanta?"
Ta ji sanyi a ranta, murmushi ta kasheshi da shi, ya maida
kai ga abinda ya ke ci. John ta kwalawa kira ya shigo
sanye da rigar kuku, umarnin ya juye ya sanya a fridge ta
ba shi sannan ta matso ta soma tayashi cin kifin. Sanin da
ta yi Hussein ba ya magana biyu, zai wuya ya ƙi yin abinda
ya furta yasa hankalinta kwance ba ta ko damu ba.
Sai dai kuma ga mamakinta da safe tashi ta yi sai filin
gado ita kadai babu shi ba dalilinsa. Takardar da ta gani ta
dauka ta karanta, sanarmata ya yi ya samu kiran gaggawa
zai wuce Abuja meeting, abu ne da suka sanya rai har sun
fidda za'a samu sai gashinan ya yiwu, ta yi hakuri idan ya
yi rashin kyautawa. Hawaye ne kawai Hajiya Zeenatu ba ta
yi ba. Ta kirashi a waya sai dai a kashe, ta ja tsaki ya fi a
ƙirga.
***
Kuɗin take ƙarewa kallo ba tare da ta iya kataɓus ba. Ta
kasa bin umarnin Chairman ɗin nata ta dauka balle har ya
je jakarta. Kuɗin da ya ninka albashinta sau biyu. Da
mamaki ta dubeshi, kallonta yake ƙasa-ƙasa.
"Me zan yi da su?"
Dariya ya yi, duk a zatonsa ta ruɗe ne saboda yawan
kuɗin, bandir na dubu har guda uku ai ba wasa ba. Ya kara
turo kuɗin.
"Dauka dai ki riƙe tukunna Madam Ramlat."
Girgiza kai ta yi.
"Ka yi hakuri Yallaɓai ka faɗamin kudin na menene
tukunna."
"Kyauta ce daga gareni, wannan ba komai bane daga irin
kyautar da nayi maki tanadinsu. Don Allah kar ki ce ba za
ki karɓa ba. Ke musulma ce,k kuma kin san ba kyau
maida hannun kyauta baya."
Har wani gumi ta ji ya tsastsafo saman goshinta duk da
sanyin nu'arar Ac dake kaɗawa.
"A'a, a'a, ka yi hakuri. Nagode wallahi amma ba zan iya
karɓa ba."
Daga haka ta kama hanya har tana tuntuɓe ta shiga
kokarin ficewa daga ofishin, kiranta ya yi ta tsaya cak jin
muryarsa ta koma irin ta ubangida da bawansa.
Sai da ta juyo ya ɗan saki fuska ya koma magana a
tausashe.
"Ga duk wanda ya sanki a wannan ma'aikatar, yabon
kyawawan dabi'unki ke fitowa daga bakinsa, ban ci karo
da wanda har yau ya kusheki ba. Don Allah kar ki sa na ga
baƙinki, ki karɓi kyautarnan domin girman Allah da Annabi
s.a.w"
Kallonsa ta ke kawai, ya koma kamar ba Chairman ba, ya
maida kansa mutum mai rauni. Banda ma rainin wayo, su
waye suka santa a wannan ma'aikatar har haka da yake
cewa wai an shaideta. Bandir daya kawai ta dauka shima
sai da ta ji wani faduwar gaba, ta kudurta a ranta ba za ta
kashe ko sisi daga kudin Chairman ba. Za ta adana ko
don gaba. Zai kara magana ta ce.
"A'a, ka yi hakuri don Allah, wannan ma ya isa. Kar ka
yimin dole. Nagode Allah Ya kara girma."
Ya yi murmushi, ko ba komai ya ji dadi. Ta sanya kudin a
jaka ta fice ta barshi da shafa sanƙo. Gani yake kamar
yanzun ba son jikinta kadai ya ke yi ba, har da ma
halayyarta da ɗabi'unta. A hankali ya shafi sanƙonsa yana
jin kamar ya samu mata ta uku.
***
A hanya tana tafe tana juyayin wannan lamarin, ta kasa
gane inda Chairman ya dosa. Tana tsaka da wannan
tunanin ne wayarta ta yi ƙara. Ganin sunan Hilal na yawo
yasa ta kasa ɗagawa, can dai ta ga bai kamata ba don
haka ta ɗaga. Maimakon muryar Hilal ya doki kunnuwanta,
muryar matarsa Fa'iza ce. Sallamar da ta yi ma ba ta
samu amsarta ba.
"Ai shaiɗanu irinku basu bukatar a amsa sallamarsu. Ke
ba ki ji kunya da kike bibiyar mijin aure ba? Mijin da kika
so cutarwa har kika yi ikirarin kashe shi? Koda dai, ba ke
ya kamata na fadiwa hakan ba, shi marar zuciyar da kika
lashewa kurwa shi ya dace na tunkara da batun! Ina miki
gargadi tun wuri ki fita daga rayuwar mijina! Ki fita! Mijina
ba sa'an aurenki ba ne! Ya fi karfinki! Ke ba ma shi ba, duk
wani kamilin miji da yasan me yake ba zai tunkareki da
sunan aure ba sai da karuwanci! Ko ba komai ba wanda
bai san kina da ƙanjamau ba, kowa yasan tsohon mijinki!"
Tun soma maganarta, Ramlat ta gangara gefen titi ta faka
motar. Shiru ta yi mata har ta kai aya. A zantukan ba
wanda ya yi mata zafi kamar na sanya Aliyu da ta yi a
zancen. Ta sa hannu ta share hawayen da ke sauka daga
kwarmin idanu har suna kokarin shigewa bakinta. Ta bude
baki da zummar magana ta ji muryar Hilal a ɗage yana
yiwa matarsa masifa.
"Wane rashin hankali kenan?! Da iznin wa kika ɗauki
wayata?...
Ba ta jira ta ƙarasa jin hayaniyarsu ba ta kashe wayar gaba
daya don ba ta bukatar ji daga kowa. Kwantar da kai a
saman sitayari ta yi zuciyarnan na tafarfasa. Ko mene ita
ta aikata abinda dole a zageta don shi, sai dai babu dalilin
da za'a sanyo Aliyu cikin sabgarnan. Aliyu ya yi kyakkyawar
mutuwa irin wanda ko mutumin kirki ne ya samu ya dace.
Da ace Fa'iza ta kwantar da hankalinta, babu Hilal a
zuciyarta, ba ta yi mishi so irin na aure. So take mishi na
ƴan uwantaka, tana mishi kallon yayanta da suke ciki
ɗaya. Ajiyar zuciya ta saki kafin ta maida hankali ga kallon
yanda hadari ya yiwa garin luf. Wani murmushi ta saki mai
ciwo tana share hawaye, addu'a ta yiwa Aliyunta sannan
ta kunna karatun Alkur'ani, ta ja motarta.
Ba ta faɗa wa Hajiya abinda ya faru ba sai dai har dare
wayarta a kashe. Kamar daga sai ga Hilal, lokacin suna
falo zaune saƙon zuwansa ya isketa daga bakin Malam
Bala. Ta yi shiru, Hajiya ta dubeta don dama ta lura gaba
daya ba ta da walwala. Sanin da ta yi koda ta tambaya
babu amsa yasa ta yin shiru kawai ta zubamata idanu.
Yanzun da saƙon zuwan Hilal ya risketa, ta lura da yanda
ta ƙara ɗaure fuska.
"Meke faruwa ne da ke? Tun shigowarki kin wani cukune,
yanzu an ce ana kiranki kuma kin ji wanda ke tafe amma
ba ki da niyyar zuwa."
Ramlat ta dubeta kamar ta yi kuka.
"Hajiya ba komai, kawai..."
"Tashi ki je." Ganin umarni ne kai tsaye ta ba ta yasa ta
miƙewa ta shige daki, can ta fito yafe da gyale akan
doguwar rigar atamfarta ta fice.
Yana tsaye kamar koyaushe jikin motarsa, ta karasa ba
tare da ta bari sun hada idanu ba. Sallama ta mishi kafin
su gaisa sannan ta ja bakinta ta yi shiru.
"Ramlat na miki laifi, kiyi hakuri."
Murmushin yaƙe ta yi.
"Ba abinda ka yimin, asalima ko me Fa'iza ta fadi gaskiya
ce ta faɗa. Sai dai don Allah ina roƙonka akan muyi hakuri
hakanan. Kaunar da ka nunamin Allah Ya saka da alheri.
Har abada nasan banda masoyi kamar ka."
Ta ƙarashe da wani irin rauni, kuka ke son kwacemata,
tunaninta ya tafi a shekarun baya na irin cin kashin da ta yi
mishi. Hawaye ta shiga fitarwa ba tare da ta sani ba.
Ta ɗago ta kalli farin hankicif da ya miƙomata kafin ta
dubeshi, murmushi ya ke mata wanda ya fi kuka ciwo
yayinda idanunsa suka kaɗa. Zuwa yanzun shima ya
saduda kuma ya ji zai hakura ko don kar ya faɗa fushin
iyayensa. Akan Ramlat, yau Fa'iza ta kai ƙararsa gurin
iyayensa. Sosai aka buɗemishi wuta kuma sun kara
rantsuwa akan tsinuwa gareshi idan ya dage akan aurenta.
Ta sa hannu ta karɓa ya soma magana.
"Ramlat kar ki damu, nima na ji a raina yanzun zan iya
hakura da ke ba kuma don ina so ba. Ina miki kyakkyawan
fata a koyaushe. Ina roƙon Allah Ya kawomaki sauyi a
rayuwa, Ya zaɓamaki mijin da ya fi ni, mijin da zai
kularmin da ke ya kuma nunamaki dukkan kauna da
soyayya. Allah shaida ne, na so na aureki, sai dai a
matakin da nake kai yanzu zan iya faɗawa fushin iyaye da
na Mahaliccina. Ya zamemin dole na hakura kar biyewa
son zuciyata ya jazamini."
Ya ci gaba da kalaman da ke nuni da irin alhininsa na
rabuwarsu. Haka ta yi ta fidda hawaye a karshe suka rabu
ran kowannensu babu dadi.
Allah Ya taimaketa Hajiya ba ta falon sai yara da suka
sheme duk sun yi bacci, jiki a saluɓe ta kai kowannensu
makwancinsa ta yi musu addu'a sannan ta koma falon da
zummar kashe kayan kallo.
"Yaushe kika shigo?" Ɗagowa ta yi bayan ta kashe socket
din talabijin ta dubi Hajiya.
"Ban jima da shigowa ba."
"Lafiya?"
Ta watsomata tambayar ganin yanda take fidda hawaye,
ta kasa danne kukanta, kawai sai ta fashe da kuka. Umarni
ta bata akan ta zauna su yi magana. Nan ta zayyanemata
yanda suka yi da Hilal. Jinjina kai Hajiya ta yi.
"Allah Sarki, yaron kirki. Dole ki yi kuka Ramlatu, rashin
mutum mai hakuri da nagarta kamar Hilal abu ne mai
ciwo. Da ace ba mai hakuri bane, hanyar ma da kika bi ba
zai kalla ba ballantana har ya bi ɗin. Allah Ya sasanta shi
da mai ɗakinsa, ke kuma Allah Ya yi maku zaɓi."
Ta amsa sannan suka yi sallama kowannensu ya shige
ɗaki. Wanka ta soma yi ta sauya kaya gami da kwanciya
saman gado. Tausayin Hilal kawai ta ke ji yana
nukurkusarta, a karshe ta yi addu'a ta kwanta.
***
Washegari tun safe ta shirya ta fita da yara makaranta.
Caa suka yi mata kowanne da nashi kalar ƙorafin, daga
ba'a ga fensir ba sai mai kawo ƙarar Antinsu ta bugeshi.
Ita dai ban da murmushi ba abinda ta ke yi, idan da sabo
ta saba, kowanne da nashi ƙorafin musamman Ummi da
Ansar wadanda har sun soma koyawa Affan.
Ƙarar wayarta ne yasa ta dauka, ganin sunan Mr Wuff ya
ba ta mamaki. Ta dakatar da hayaniyar su Ummi kafin ta
ɗaga da sallama daidai sadda aka tsayar da su a junction.
"Yaranmu ne suka sanyaki murmushi ko tunanin
bazawarinki?"
Abinda ya ce kenan bayan amsa sallamar, hakan ne yasa
ta saurin kallon titi. Gaban wata Jeep ta hangeshi zaune a
kujerar kusa da direba. Da alama wani abin ya tsayar da
su, kallonta ya yi kafin a hankali ya rufe gilashin motar.
"Hey, kar ki cinyeni da kallo. Kamar ma kin manta cewar
tuƙi kike ko?"
Harara ta bankamasa don ta san koda ita din ba ta
kallonsa, shi idanunsa yana kanta.
"Meye abin kallo a fuskarka? Nikam ban ganshi ba. Na
kalleka ne don na tabbatar kai dinne da sassafe haka ba
wani ba."
Murmushi ya yi tamkar tana kallonsa.
"Allah Ya tsare hanya, drive carefully."
Daga haka bai jira cewarta ba ya katse kiran. Ta ajiye
wayar ba ta kara kallon inda motarsu take ba amma ya
sanyata dariya.
A bangarensa kuwa, ƙara jingina ya yi yana ƙaremata kallo
daga ita har yarannata, ya lura babbar ta fi ɗiban kama da
ita akan na tsakiyan da ƙaramin. Yanda suke ta hira suna
karkatowa da zummar kallon fuskarta ba karamin
burgeshi ya yi ba.
Direba dai ya yi bakam, ga labari na sukarsa amma ba
wani da zai faɗawa. Burinsa kawai su kai gida ya samu
Joseph mai gadinsu, inyamuri kuma mai jin yaren Hausa
sosai su tsegunta. Da alama dai Yallaɓai aure zai yi, sun
tabbata ba karamin bomb ne zai fashe ba.
KARFEN KAFA Chapter 46
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Har aka ba su hannu yana satar kallon Ogannasu,
hankalinsa duka yana ga Ramlat da yaranta. Kusan tunda
ya daukoshi daga Airport bai yi mishi wani kwakkwaran
magana ba sai yanzun da ya ga budurwarsa. Farin ciki
sosai direban ke yi, ko ba komai Yallaɓai zai samu sa'ida
daga wurin Hajiya Zeenatu. Su kansu suna mamakin
yanda akai ya ƙare da auren mace kamarta.
***
Har ta sauke yaranta a makaranta ta kama hanyar ofis ba
ta bar tunanin wayar da suka yi da Hussein ba. Sosai ta ke
mamakinsa, idan da a farkon ganinta da shi wani zai ce
mata yana da sauƙin kai har haka toh fa za ta musanta, za
kuma ta ƙaryata nan take. Da alama wannan yana daga
cikin nasarar jihadinta. Ta shaƙu da shi sannan a ƙarshe ta
shiryashi da ƴan uwansa. Wannan kaɗai ne burinta.
Tana faka motarta ba ta kai ga barin parking space din ba,
suka ci karo da Halima. Wani irin kallo Halima ke bin ta da
shi tana murmushi. Bayan sun gaisa ta ce.
"Sakatariyar Chairman, wato ko nemanmu ma kin daina."
"Ko rannan na shiga ke kuma ba ki zo ba." Fadin Ramlat
cikin dakiya don yanzun ba ta kaunar shiga duk wani
lamari da ya shafeta. Ta riga ta gane ba masoyiyarta ba
ce. Halima ta ɗan taɓe baki.
"Oh, haka fa. Ai mancewa na yi, an faɗamin. Ina fatan dai
za ki saki jikinki ki ajiye kauyanci gefe ki ci arziki inda kika
ganshi."
Ɗan haɗe gira Ramlat ta yi tana mata duban ido cikin ido.
"Bangane hausarki ba, me kike nufi?"
Dariyar ƴan duniya ta yi.
"Dama ba lallai ki gane ba, amma nidai ina mai ba ki
shawarar kar ki yi wasa da damarki."
Daga nan ta ficewarta ta bar Ramlat tsaye. Wani
murmushi ta yi gami da girgiza kai itama ta soma tafiya
nutse.
Ta rasa ranar da Halima za ta nutsu ta yi hankali, kullum
tunaninta iri guda ne.
'Allah Ya shirya.' Ta furta a ƙasan ranta.
***
"Wannan asarar kuɗi har ina wai?!! Duk aikin da na ɗauko
sai ya lalace! Abu ne da bai taɓa faruwa da ni ba duk
tsawon wannan shekarun! Ina tsoro kuma."
Hajiya Zeenat ke wannan ƙorafin kamar ta zubda hawaye
a tsakar falon Hajiya Batool da misalin ƙarfe uku da
mintoci na rana.
"Ni na rasa ma me zan ce. Kusan duk