Showing 60001 words to 63000 words out of 113545 words
Chapter 21 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
murnar shari'ar da ta gudana,
ta ta yi ta musu addu'a sosai. Ana haka sai ga Zulaihat da
Rafee'ah suma, sun ji labarin sallama.
Suka karaso daidai sadda AlHassan ya dubi Ramlat.
"Kanwata ya jiki?"
Ta yi murmushi. Ta gaishesu. Ya amsa shi kuwa Hussein
ya yi kamar bai ji ba yana kallon twins din Zulaihat.
Bayan zamansu aka kara gaisawa su na muu godiya.
"Zamu wuce Adamawa Hajiyarmu."
"To ƴaƴana, sai kuma yaushe?"
Hussein ya amsa wannan karon.
"Nan ba da jimawa ba za mu dawo in sha Allah."
Ta jinjina kai ta yi musu fatan isa lafiya. Hakanan suka
kama hanya. Rafee'ah ta yiwa Ramlat ido, ba musu ta
mike ta takamusu, ba laifi yanzu hannun da sauki sosai. A
daidai barandar shiga dakin ta ci burki.
"Allah Ya tsare, Ya kaiku lafiya. Na gode sosai."
"Ke za mu yiwa godiya sosai. Allah Ya bar zumunci."
Ta yi murmushi.
"A gaidamin Fatina."
Ya yi murmushi.
"Za ta ji in sha Allahu."
Daga haka ya yi gaba, Hussein ya dube ta.
"Yarinyar da kika aikomin hotonta?"
Ta gyada kai tana murmushi. Sai a sannan ta ga ya yi
mata murmushin shima.
"Ina kara godiya gareki. Allah Ya ba ki miji nagari. Oh, ashe
kin samu. Allah Ya nunamana aurenku."
Ya karashe yana taɓe baki. Ta rasa ma me za ta ce, ya
bita da wani irin kallon da ta kasa fassarawa.
"Ki kula da shan magungunanki, kada ki tsorata, likita da
kansa ya rubuta da kaina na karɓomaki. Ba za ki mutu ba."
Ta dan yi murmushin yaƙe, ya juya ya tafi. Jiki a saluɓe
itama ta koma ciki.
***
HUSSEIN AMINU MAMMAN GIDADO...
Alhaji Aminu Mamman Gidado, haifaffan garin Adamawa
ne gaba da baya. Su goma sha biyar cif mahaifinsu ya
haifa. Mamman Gidado yana da mata uku, uwargidansa
wacce suke kira da Inna, ta haifamasa yara tara cif a
duniya, sai mai bi mata Yakumbo wacce ta haifi yara biyu.
Hassan da Hussaina wanda a karshe suka koma hannun
Inna da zama. Hajara (Hajjo) kuwa tana da yaranta huɗu
cif a duniya.
Wani irin rayuwa ake gudanarwa a gidan Mamman
Gidado, rayuwar da hatta da maigidan shakkar Inna yake
yi balle a kai ga mata da yara. Inna wata irin mace ce
murɗaɗɗa mai baƙar zuciya, a duniya ba ta kaunar ace
wani ne sama da ita koda a matsayi ko wani abin. Auren
gida na zumunci aka yi musu da Mamman Gidado.
Sai kuma cikin ikon Allah ya zamana Yakumbo ta fito
daga gida na sarauta a garin Mubi. Mahaifinta shi ne
wazirin Sarki. Wannan girma da nasaba ta Yakumbo sai ya
jazamata baƙin jini fiye da na kowa a wurin Inna.
Ita ta soma yiwa Yakumbo gorin zama bare a gidan don
Hajjo ma ƴar aminin kakansa ce aka aura. Yakumbo tana
shakkar Inna sosai, tana kuma bin ta sau da ƙafa.
Mijinsu ba karamin so yake yiwa Yakumbo ba, tana
matsayi babba a zuciyarsa da bai jin ko Inna ta samu.
Wannan ta sanya mutuwarta ba jimawa shima ya soma
jinyar ajali. A gaban idanunsa Inna ta sha hana Amina da
Aminu abinci, wataran Hajjo a sace take basu. Dangi kuwa
ba'a taɓa ganin laifin Inna don a waje nunawa take nan
duniya tana sonsu kuma tana riƙe da su da amana.
Wannan tasa hatta ga yaranta maza da mata sun tsani su
buɗe idanu su ga Amina da Aminu musamman ganin irin
kyauta da gatan da ake nunamusu duk sadda suka kai
ziyara Mubi suka dawo. Kayan da Inna ba ta sanyamusu
kenan, duk zuwansu dama gargadi ne sosai da jan kunne
ta ke musu akan kar su sake su yi yunkurin tonamata asiri.
Modibbo wanda ya kasance ɗa na bakwai a wurin Inna,
kusan shi ne babban mugun da ya fi kowa tsanar yaran
Yakumbo. Ya sha kama su a makaranta ya jibga ya kuma
kwace abincin da Hajjo ta girkamusu. Gori na uwa da uba
bai fasa yi musu ba.
"Wai meye amfanin riƙon da ake musu anan? Tunda suna
tutiyar dangin uwarsu masu arziki ne, ki tattara ki maida
su mana!"
Modibbo ya fadi a zafafe. Yar uwarsa kuma Yayarsa Adda
Salma ta karɓe.
"Ashe ka gane, ni wallahi haushinsu nake ji,wannan
Aminar ma kyanta ya yi yawa, ko makaranta muka je sai a
yi ta wani zuwa ana daukarta. Ji nake kamar na shaƙeta
na huta. Da zan samu reza na tsaga fuskar ma zai fi."
Sauran suka yi dariya har Inna Idan ka cire Karime da
Adamu wadanda su kadai suka fita zarra akan sauran,
basu taɓa nuna kiyayya ga Amina da Aminu ba.
"Allah ne Ya ba ta kyan, kuma ai..."
Buge bakinta Modibbo ya yi da ƙarfi.
"Dama ke da Adamu ina kula da yanda ku ke shishshigewa
yarannan! Marasa zuciya da kishin uwa!"
***
Da wannan irin kiyayyar Amina da Aminu suka taso, boko
dai basu isa su je ba sai yaran Inna, islamiyya kadai suke
zuwa. A wannan rayuwar, Waziri ya fadi ya mutu,
kasancewar mahaifiyar Yakumbo ta jima da rasuwa ne
yasa babu wanda ya kara waiwayarsu balle ya maida
hankali wurin kula da su daga Mubi. Yar uwar Yakumbo
tilo, Zahida, ita kuwa tana aure a Saudiyya. Kafin ta shigo
gari akan jima sosai.
Shekaru suka ja a wannan halin, Aminu ya yi saukar
littatafai da dama na addini. Mutum ne mai matukar
kokari da saurin daukar karatu. Lokaci ɗaya kuma ya
bazama neman ilimi a garuruwa daban-daban. Inna ko a
jikinta, don a ganinta ba wani ci gaba da zai samu face ya
ƙare a almajiranci. A sannan babbar ɗiyarta Hansatu, ta
kammala karatunta a fannin shari'a a jami'ar Adamawa.
Yayinda Salma ta karancifannin Kasuwanci. Duk an musu
aure a sannan.
Modibbo yana ajin karshe inda shima dai yake karantar
fannin Kasuwanci. Adamu da Karime su ne a babbar
Sakandire sai Hadiza, Safiya, Tahir a karamar Sakandire,
Maimuna Autar Inna a firamare.
A islamiyya ba su taɓuka abin a zo a gani, gwara ma
Karime, tana da kokari sosai don ta yi sauka.
Yaran Amarya Hajjo hudu, suma duka suna karatu.
Bayan tafiyar Aminu almajiranci da watanni biyar sai ga
Hajiya Zahida da yaranta daga Saudiyya. Sun dawo kenan
sakamakon sauyin wurin aiki da mijinta ya samu zuwa
Adamawa. An saukeshi daga Ambasada. Kai tsaye wurin
ƴaƴan yar uwata ta soma zuwa. Ranar da ta je ta tarar da
Inna na jibgar Amina da sunan wai ta tsaya sauraron bare
wanda kwata kwata ma ba jinin Fulani ba ne. Da biyu Innar
ta yi hakan ganin yaron mahaifinsa mai kudi ne, sunan
zuri'arsu ba ɓoyayye ba nema ƙasar. Ya ganta ne a hanyar
dawowarta daga islamiyya.
Wannan tashin hankalin da Hajiya Zahida ta tarar yasa ta
rantse ko sama da ƙasa za ta haɗe sai ta tafi da Amina.
Kaca-kaca suka rabu da Inna, a karshe ta ci nasarar dauke
Amina tana kukan rashin sanin inda Aminu ya tafi.
Da wannan suka wuce Mubi, sosai ta nunamusu ɓacin
ranta akan yanda suka yi halin ko in kula da yaran
Yakumbo, hatta aiken da takan yo a kai musu ba ya
riskarsu.
Da wannan bakin cikin ta zauna, sati na cika ta tattara
yaranta har Amina suka wuce sabon gidansu a cikin Yola.
Wannan ne dalilin ingantuwar rayuwar Amina wacce gaba
daya yaran ke kiranta Dada. Babban ɗan mijin Hajiya
Zahida (ɗan Uwargidansa da ta rasu, riƙonsa ya koma
hannun Zahida) Naziru, tunda ya dora ido a kan Amina ya
ji nan duniya ita yake so da aure.
Sosai abin ya yiwa Hajiya Zahida dadi, hakanan shima
mijinta bai ƙi ba. A yan uwan mahaifiyarsa ba wanda ya
nuna kiyayyar abin ko don irin rikon da Hajiya Zahida ta
mishi, ba jimawa kuwa aka sha bikinsu. Amina ta yi kukan
rashin dan uwanta a kusa, haka ta hakura ta fawwalawa
Allah suka tare a gidan Naziru wanda babu nisa sosai da
gidan Hajiya Zahida.
***
Bayan shekaru masu dama, Dada ta haifi yaranta uku duk
mata, tana da cikin na hudu ne ba zato ba tsammani
Naziru mijinta ya ɗaukesu sai gidan Hajiya Zahida. Wanda
ta gani ne ya sanya ta zuwa a guje ta rungumeshi sai kuka,
tana yi shima yi yake. Ta ɗago ta dubi wata mace fara ƙal
da ita kyakkyawa, a gefenta wasu kyawawan yara ne su
biyu da zasu girmi yaranta, komai nasu iri daya. Haka
kawai jikinta ya bata wannan iyalin Aminu ne. Ta rungume
matar kafin ta rungumi yaran tana cike da farin ciki.
Sai bayan an zauna an nutsu ne ya ke basu labarin inda ya
je.
Ashe bayan tafiyarsa da tawagar almajirai ba inda suka
yada zango sai Maiduguri, ya fada hannun wani Malami
kuma barebari cikakke, Malam Banakura. Mutum mai
sanin daraja da ƙimar almajiransa. Aminu bai ɓoyemishi
komai dangane da Asalinsa ba. Tausayi da kaunar Aminu
suka shiga Malam. Ya rikeshi tamkar ɗan cikinsa, duk da
tarin Almajiran Malam, Allah bai ba shi haihuwa ba. Kuma
matsalar daga gareshi ne. Uwargidansa Yakura, mace ce
mai halin Dattako, ta rike yaran yan uwa da dama ta kuma
aurar da su. Yara biyu kadai suka rage a hannunta sannan,
Zahra da Yusha'u.
Zuwan Aminu sai ta haɗa da shi ta rikesu duk kuwa da
cewar ya girmi Zahra nesa ba kusa ba. Sai dai zai iya
sa'an Yusha'u.
Haka suka rayu har suka kara girma, noma da kiwo shi ne
sana'ar Malam bayan koyarwa, Aminu ya tsunduma wurin
taimakawa Malam. A hankali kuma Allah Ya sanyawa abin
albarka. Koda shekarun aure suka kai, Malam ya fahimci
irin soyayyar dake tsakanin Zahra da Aminu, bai yi ƙasa a
gwuiwa ba ya auramasa ita da iznin iyayenta. Mahaifinta
buzu ne kuma Maigadi, mahaifiyarta ce ƙanwa ga Yakura
matar Malam. Kyakkyawar mace mai gashi har ƙugu,
yarinya mai yawan ibada da kunya.
Zamansu ya yi albarka sosai, sai da suka shekara kafin ta
samu cikin ƴan biyu. Ta sha wuya sosai kafin ta haifesu.
Sai da ƴan biyu suka shekara goma cif a duniya, Malam
ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Sosai ya gargadi
Aminu kamar koyaushe akan ya je ya nuna iyalinsa a gida.
Wanna tasa ana yin arba'in na Malam, shima hankalinsa
ya yi gidan.
Shi ne zuwan da ya yi a yanzun, Dada ta ci kuka ta kuma
yi korafin nisanta kansa da ya yi da ita har ba ya tunanin
halin da ta shiga. Hakuri sosai ya ba ta, ɗan uwa rabin jiki,
nan da nan kuma ta mance da komai. Ya nemi labarin
abubuwan da suka faru bayansa, anan yake jin labarin
mutuwar Inna bayan ta yi fama da jinya. Addu'a kawai ya
yi mata tsoron Allah na ƙara shigarsa. Nan yake jin auren
da Modibbo ya yi da kuma zaman da ya koma yi a Kano
inda yake kasuwanci, sai Adda Salma da mijinta ya koma
Gombe. Sauran yan uwa kuwa suna nan a Yola, Karime
ma ta yi aure hakanan Adamu. A yaran Amarya Hajjo ma,
autanta ne kaɗai bai kai ga yin aure ba sannan.
Washegari suka dunguma zuwa dangin mahaifinsu.
Sun samu tarba ta ban mamaki a wurin yan uwan
mahaifinsu wannan ya kara tabbatar musu cewa dama
can shakkar Inna ce ta sanya ake baya-baya da su, ko dai
kuma don yanzun Dada na auren mai kudi ne shima kuma
Aminu ya samu rufin asiri daidai gwargwado ne don har
gidajen gona da dabbobi yana da su? Oho, ba su da
masaniya.
Aminu bai yi ƙasa a gwuiwa ba sai da ya je gida yayyunsa
mata duka idan ka cire Adda Salma da ke Gombe. Ya yi
mamakin ganin yanda har sannan babu ɗigon kaunarsu a
cikin idanuwansu, asalima sai da suka goranta masa na
auren Bare a cikinsu don dukkansu auren gida akai musu.
"Kai da Amina kun fita zakkah! Gwara ita, ta auri Fulani kai
kuwa bayinmu ka je ka kwaso mana. Har abada ba zamu
taɓa daukarki daya a cikinmu ba. Tsana yanzu aka fara."
Wannan shi ne munanan kalaman da Gwaggo Hansatu ta
watsawa Zahra da har ya sanyata hawaye.
Karime ce dai ta rasa inda za ta sanyasu don farin ciki. Ta
rungume HASSAN DA HUSSEIN cike da murna da jin dadi
har da kukanta.
Haka aka rabu cikin aminci, suka dunguma zuwa Mubi.
Nana ba laifi an musu tarba.
Aminu bai ƙasa a gwuiwa ba sai da ya shirya zuwa Kano
sada zumunci da Modibbo. Ya tarar da matansa biyu,
Hajja Fatuma da Amarya. Tun shigowarsu ya dinga
watsamusu banzan kallo yana gyara zaman malun-malun.
Ba haka ya so ganin Aminu ba, so ya yi rayuwarsa ta
lalace yanda rigar jikinsa ma zai gagareshi. Ya mishi
tsanar da ko a inuwa ba ya son ganinsa sai rana. Da
harshen fulatanci Aminu ya gaida shi.
"Gaisuwar ta mece ce? Ni waye a wurinka? Shekaru nawa
ka tafi yawan maula, sai yanzun ne za ka je ka dawomana
da SADAKAR YALLAH?"
Cikin dakiya Aminu ya amsa.
"Ba sadakar Yalla ba ce, sunanta Zahra. Matata ce."
Harara Aminu ya watsamata, ƴan biyu suka ƙara nanewa a
jikinta suna bin wanda aka kira Yayan Babansu da kallon
tsoro da tsana.
"Bare ce! Yanda uwarka ta shigo gidanmu tana matsayin
bare, kaima haka ka je ka kwasomana abin fadi da gori!
Har abada wannan matar ba za ta zauna cikin zuri'armu
ba. Sai yanzun ka tuna da mu ka kwaso jiki ka taho
zumunci ko? Toh ni Muhammadu, ban sanka ba! Bani da
wata alaƙa da kai, ƙafarka na ƙara gani a gidana Allah Ya
isa. Duk abinda na yi maka kuma kai ka ja wa kanka. Ku
kuma kuma kallona kamar Mayu!"
Ya maida akalar zancen kan Hassan da Hussein da suke
kallonsa, duk da karancin shekarunsu, haka bai sa sun
gaza fahimtar wasu abubuwan da yake faɗi ba don Hausa
sak ya yi ko don ya baƙantawa Zahra.
Da wannan cin kashin da rashin mutuncin na Modibbo,
Aminu ya tattara iyalinsa suka juya ko kwana ba su yi ba.
A mota ya yi ta rarrashin Zahra da ban hakuri. Ita kuwa
murmushin yaƙe ta yi kawai ta nuna ba komai tunda dai
bai ɓoyemata alaƙarsu da su ba tun farko. Labarin komai
na irin riƙon da ya samu a hannun uwarsu ta sani.
Watansu daya suka yi shirin komawa, nan fa Dada ta
rikice da kuka da rantsuwar ba ta yarda ba, a karshe ta
dage ma sai dai a bar mata ƴan biyu ta riƙe, dabararta na
yin hakan, don kawai su dawo da wuri a dinga ganinsu.
Aminu ya rasa ya zai yi da yar uwarsa, ga mamakinsa
Zahra da kanta ta riƙe hannun Hassan da Hussein ta
damƙawa Dada tana murmushi.
"Yarana mallakinki ne Dada. Gasunan na bar miki su
duniya da lahira."
Wannan abu har gobe Dada ba za ta mance shi ba, kuka
sai ya koma dariya. Har tasha suka yi musu rakiya suka
dawo. Abin mamaki Hassan da Hussein ko a jikinsu don
sosai sun saba da Dada da iyalinta a ɗan zaman da suka
yi tare.
***
Mummunan labarin hatsarin mota da rasuwar Aminu da
Zahra ya riskesu. Wannan ya yi sanadin fitar cikin Dada, ta
sume.
KARFEN KAFA Chapter 64
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Sosai mutuwar ta girgizasu, anan suka ƙara jinjina kudurar
Ubangiji. Wato dai da yanzun har yan biyun za'a rasa
shikenan babu tarihin Aminu da Zahra a doron ƙasa.
Allah Ya taimaka, Aminu ya bada kwatancen inda suke
zaune a Maiduguri, da haka suka karasa bayan an sallaci
gawar Aminu da Zahra an binnesu a nan cikin Yola.
Yakura ta ji mutuwarnan ba kaɗan ba, dama tana cikin
takabar Malam. Hakanan iyayen Zahra su kansu mutuwar
ta dake su. Sai da aka yi arba'in aka raba gadon ƴan biyu.
Ba wanda ya hana Dada tahowa da Hassan da Hussein.
***
RAYUWAR ƳAN BIYUN
Rayuwa mai dadi suke yi a wurin Dada da mijinta, basu
san matsalar rashin uwa ko uba ba. Kaunar da Dada ke yi
musu har kusan matsala ta so ba ta da Naziru don gani
yake kamar ba ta kula da yaransa irin yanda take rike da
yan biyu. Wannan ne dalilinta na ɓoye son a zuciyarta.
Makaranta mai kyau na masu gata suke zuwa don dama
sun soma firamare, ci gaba kawai suka yi.
Tafiya ta ci gaba da tafiya har ƴan biyu suka kammala
firamare suka soma kokarin tafiya Sakandire. A sannan ne
Dada ta danne zuciyarta ta shirya da yaranta kaf suka
halarci bikin ƴar Modibbo a Kano. Yaran babu mai murna
haka Dada ta yi ta lallaɓasu gami da nunamusu
muhimmanci da ladan dake cikin sada zumunta.
Koda zuwansu suka sauka a gidan wani abokin Baba
Naziru don yaran sun rantse baza su je kwana gidan
Modibbo ba har da kukansu, anan ne Dada ta goyi
bayansu, ita kadai ce ta karasa gidan dan uwannata ta
sauka dakin Amarya don duk ta fi mutan gidan kirki da
dadin mu'amala. Ita ke yawan ba Dada hakuri akan yanda
rayuwa ke tafiya. Hajja Fatuma ta yi bakin ciki da saukar
Dada dakin Amarya ganin ita ce ke aurar da ɗiyarta.
Ranar wuni direba ya kawo yaran Dada kaf. Basu samu
matsala sosai ba don hidimar biki ta sanya ma ba wanda
ya hadu da Modibbo sai dai a wurin yaran su Adda Salma
da sauran yan uwa, sun sha hantara.
Sai da aka kammala bikin sannan Dada a karo na biyu ta
kwashi yaran suka shiga bangaren Modibbo don su
gaidashi su yi mishi sallama, wancan karon ya ganta sarai
amma ko amsa gaisuwarta bai ba.
Modibbo zaune shi kadai a falonsa, ta samu damar shiga
dalilin ranar girkin Amarya ne. Yana ganinsu ya daure
fuska tamkar bai taɓa dariya ba.
"Ke har yanzu ba ki tafi ba?"
Dariya ta ɗan yi.
"Eh, amma gobe zan wuce. An yi biki, Allah Ya..."
"Dakata, ke har wani bakin alheri ne da ke? Ai ni kaf
zuri'ata ba za ta ga rashin alheri ba. Tashi ki ficemin daga
gida! Zaman ya isa hakanan, biki ya ƙare tunda kin zo
gayyar soɗi ai sai ki tattara ku koma."
"Dada tashi mu tafi! Ba zamu kara dawowa ba! Na
tsaneshi!"
Da sauri Dada ta kalli Hussein ta rufemasa baki, shi kuwa
Modibbo ya mike ya zo ya fisgoshi.
"Kai! Dan iskan yaro, ni sa'anka ne? Haka aka koyamaka
ka zageni?"
Ya bubbuge bakinsa kafin ya murɗe kunnensa, Hussein sai
huci kawai amma kukan ma ya ƙi yi. Dada na hawaye
yaran na tayata ta mike ta ja hannunsu ta fito ba ta kara
magana ba.
Sosai ta gargadi yaran akan kar wanda ya fadawa Baba
Naziru abinda ya faru, suna cike da ɓacin rai da jin
haushin Modibbo wannan ta sa ba su amsamata ba. Ba
ma kamar Hussein da ya ji duniya ya tsani mutumin.
***
Tafiya na ci gaba da tafiya, yan biyu suka kammala
Sakandire, a sannan sun zama matasa, Hassan na sanya
farin gilashi a sannan a dalilin matsalar ido da yake fama
da shi. Wannan ne ya taimaka wurin bambance su.
Baba Naziru bai yi ƙasa a gwuiwa ba wurin nema wa
kowannensu gurbin karatu a fannin da yake so, AlHassan
ya samu fannin Accounting a jami'ar Oxford, London.
Yayinda Hussein ya tafi AUD a Dubai.
***
Tsakaninsu da Nijeriya sai an musu hutu. A wani zuwan
ƙarshe da Hussein yi hutu, don wani lokacin hutunsu kan
bambanta da na Hassan. Hutu wanda daga shi kuma sai
kammala karatunsu. Bisa tursasawar Dada ya ziyarci ƴan
uwan Babansu. Sosai ya samu tarba a hannun Adamu da
Karime kamar koyaushe, zuwa Kanon da Dada ta ƙaƙaba
ya fi komai dagula lissafinsa.
"Nikam ba zan je ba." Cewar Hussein ransa a tsananin
ɓace. Daƙuwa Dada ta mishi gami da harara, ya kauda kai.
"Duk rashin ƙaunar da zai nunamaka ai hannunka bai taɓa
ruɓewa ka yanke ka yar ba. Mu mun san muhimmancin
zumunci don haka dole ne ka je idan har na isa da kai."
Ganin yanda ta dage har da ɓata rai yasa shi lallaɓa ta ya
kuma shirya tsaf ya bi motar kasuwa ya tafi har da
tsaraba Dada ta shirya ya kai.
Tun a ƙofar gidan Kawun ya soma cin karo da samarin
gidan, haɗe girar sama da ƙasa ya yi kamar bai taɓa
dariya ba ya ƙarasa.