Showing 39001 words to 42000 words out of 113545 words
Chapter 14 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
ba ya amsa a gaggauce.
"Ki yi duk yanda ki ka so."
Yana kaiwa nan ya miƙe ya nufi sama. Ba ta dakatar da
shi ba don ita fa ya gama biyanta. Da wani irin farin ciki ta
kira Hajiya Batool ta fesamata. Dariya suka yi lokaci guda.
"Habawa! Wa ya faɗamasa Borno gabas ta ke? Ai wutsiyar
raƙumi ta yi nesa da ƙasa."
Cikin nishaɗi Hajiya Zeenatu ta gyara zama.
"Allah Ya barmin aminiyar kwarai. Yanzu ki yiwa ɗanmu
magana ina so ya yimin duk wani shiri na tafiya."
Suka yi dariya sannan suka ci gaba da ƙulla-ƙullarsu.
***
Kasa zama ya yi sai kwanciya, kwanciyar ma bai fi minti
uku ba ya miƙe zaune gami da dafe kai. A hayyacinsa ya
amincewa Hajiya Zeenatu, gani yake nisan da zai yi daga
gareta shi zai sa ya mance da dukkan lamuranta. Hisham
ba zai yi ƙarya ba don ya baƙanta ransa hakanan kawai, a
farko yana mata kallon wata halitta ɗaya tallin tal da ta
dakatar da shi daga biyewa Hajiya Zeenatu tun farko akan
su bar garin, yau kam har Ƙasar ya amince su bari idan
hakan zai ba shi farin ciki. Zai nisantashi da ita kuma ya
yaye damuwarsa. To wa ya ke da shi da zai damu? Ba shi
da uwa bare uba, ba danginsa babu na Hajiya Zeenatu.
Wannan abu sau da dama kan ɗauremasa kai matuƙa
kuma ya jefashi cikin tafkin tunani iri-iri. Nan da nan farar
fuskarsa ta yi ja kamar yanda idanun suka kaɗa. Ya riƙe
kansa da ke sarawa da ƙarfi yana salati. Tun yana gani
daidai har ya dawo gani dishi-dishi. Ya yi kokarin mikewa
tsaye sai ji kake tim! Ya fadi.
Ta turo ƙofar ta shigo ranta fari sol bayan kammala
wayarta da Hajiya Batool. Turus ta yi ganin Hussein a
ƙasa. Wani ƙara ta saki kafin da sauri ta nufeshi.
"Hussein! Hussein?!"
Babu alamar zai motsa, don haka ta dauko ruwa ta
yayyafa, nan ma shiru. Ganin haka ta yi wurgi da robar
ruwan ya malale a kafet ta fita daga dakin.
"John! John! Ola!"
Kusan lokaci guda ma'aikatan dake kicin har wajen su uku
suka fito.
"Yes Ma!"
Umarni ta ba su akan su hayo su taimakamata. Da gudu
suka nufi saman, suka cicciɓi Hussein. Mayafi kawai ta
dauka sai mukullin mota da ta damkawa John ta bi
bayansu tana kuka. Kai tsaye suka wuce asibiti.
***
Sun sauka lafiya a Kano. Bayan kimtsawa suka hadu suka
ci abincin rana. Fuskar Ramlat cike da fara'a don tun safe
bayan dawowarsu Muhibbat ta kawo su Ummi. Affan ya
maƙale mata duk inda ta sa ƙafa yana biye. Labarin gidan
su Aliyu da na Muhibbat kuwa ta sha har ta gode Allah. Ta
lura dai ba su fuskanci kowace matsala daga dangin Aliyu
ba don a yanda bakin Ummi ba ya shiru sai ta fesamata.
Da yammacin ranar gidan ya rage daga ita sai Hajiya da
su Ansar don tuni masu auren duk sun tafi gidajensu. Ta
shirya tsaf da niyyar zuwa ganin Kawu Modibbo kafin
zuwan AlHassan wanda tun safe ya shaidamata cewar
yana hanya. Ba ta ɓoyewa Hajiya komai ba na halin da ake
ciki. Hajiya ta jinjina lamarin.
"Ramlatu Allah Yasa a dace. Allah Yasa karshen wahalar
yaron nan ce ta zo."
Cike da tausayawa Ramlat ta amsa da amin. Suka yi
sallama ta fita, ba ta ɗauki mota ba don haka kawai ta
fice. Har za ta wuce ta ga kyautuwar leƙawa gidansu
Amrah su gaisa da Baba Dakta. Wannan yasa ta karya
kwana ta shiga gidan da sallama.
Umma ta amsa fuska a sake.
"Mutanen Daura, saukar yaushe?"
Dariya ta yi tana mai kama hannun Zaituna da ta
maƙalƙaleta tana oyoyo.
"Tun safe muka iso, Hajiya ma ta kira ba kya kusa."
Umman Amrah ta bude baki.
"Af, an yi haka. Na ga kiranta toh da alama dai wannan
ɗiyartaki ce garin son a kunna mata kallo ta kashemin
ƙarar."
Murmushi sosai Ramlat ta yi gami da shafa kan Zaituna
tana mitar yanda amosali ke cinyemata gashin. Can kuma
ta ɗago.
"Baba Dakta ya na nan kuwa?"
"Ba ki taki sa'a ba Ramlatu, yana asibiti."
Ta mike tsaye.
"Toh Umma zan dawo anjima in sha Allah. Zan ɗan fita
ne."
Umma ta amsa da toh, suka yi sallama ta fice.
***
Gidan ta tsaya tana ƙarewa kallo. Gida ne da ta sha zuwa
ta wuceshi, ba ta mancewa akwai sadda suka taɓa shiga
tun suna yara ita da su Amrah tsinko mangwaro aka koro
su. Murmushi ta ɗan yi tunawa da cewar gidan ƴan uwan
mutum mafi soyuwa a zuciyarta ne ashe. Ta ƙarasa ta yi
sallama ga mazauna ƙofar gidan sannan ta sa kai ciki.
Ɓangare biyu ta gani sai kawai ta faɗa na biyun. Wata
baiwar Allah dattijuwa ta soma cin karo da ita zaune a
tsakar gida, a gefenta wata budurwa tana gyaran alayyahu,
wanda nan take ta gane fuskarta dalilin hotunanta da ta ke
gani a status din Hafsat, sunan ne dai ba ta jin za ta iya
tunawa.
Suka amsa sallamarta suna dubanta, duba na rashin sani.
"Sannu da zuwa, bismillah. Rasheeda kai ta falo ina zuwa.
" Faɗin Amarya fuska a ɗan sake, sosai Ramlat ta ji dadin
tarbar da ta samu. Ta bi bayan budurwar da aka kira
Rasheeda zuwa falo. Falo ne mai girma ya sha ado. Ta
zauna a saman ɗaya daga cikin hadaddun kujerun da aka
zuba. Rasheeda ta gaidata ta amsa fuska a sake sannan
ta je ta kawomata ruwa da lemun zoɓo.
"Na gode." Cewar Ramlat sadda ta dauki ledar ruwan ta
sha kaɗan ta ajiye ragowa. Amarya ta shigo ta zauna. A
ladabce Ramlat ta gaidata ta amsa fuska a sake.
"Sai dai kamar ban shaida fuskar ba."
Murmushi Ramlat ta yi.
"Eh gaskiya ba ki san ni ba Anti. Sunana Ramlat Khalid
Mu'azzam. Kusan sanadin AlHassan Aminu Mamman
dake Adamawa na san gidannan. Kwanakin baya ma sun
zo biki nan suka biya ta gidanmu."
Kawai sai ta ga Rasheeda ta sa dariya haka Amarya.
"Ke ce Mamin Fatima ko? Mai zaɓamata takalmi? Ya
bamu labari."
Da wani irin salama na jin dadin kalaman Rasheeda itama
ta yi dariyar kadan.
"Ni ce, ai kema ina ganinki na shaidaki don ina yawan
ganin hotonki a status din Hafsat."
Jin haka Amarya sai ta samu nutsuwa sosai da Ramlat,
dama tun farko ba ta yi mata kalar mace marar kamun kai
ba. Nan aka kara gaisawa da tambayar su Hajiya wanda
ba karamin mamaki ya ba Ramlat ba. A karshe Ramlat ta
gangaro kan abinda ya kawo ta.
"Ina neman izni ne, ina son ganin Kawu Modibbo."
Jin haka Anti Amarya ta amsa cikin kwarin gwuiwa.
"Wannan ba matsala ba ce Ramlat. Bari na yi miki iso, ina
zuwa."
Hakan ya faranta ran Ramlat, ta dauka ganinnasa zai mata
wuya ko kuma wani ko wata zai nemi sanin dalilinta na
son ganinsa, sai dai akasin hakan ce ta faru. Ko ba komai
ta gaskata kirki na Amarya, wanda ya sha bamban da na
Hajja Fatuma kamar yanda ta ɗan ji kaɗan cikin labarin
matannasa a bakin Hafsat. Yarinyar akwai hira idan ta so.
Jim kaɗan sai ga Amarya ta dawo, yanayin sanyin jikinta
sai ya sa Ramlat shan jinin jikinta itama. Amarya ta daure
tana murmushi mai kama da yaƙe.
"Za ki iya jira har bayan Magriba kuwa? Ina gudun kar ki
dare."
Nan ta gano matsalar, don haka ta saki fuska.
"Lah ba komai Anti, Allah Ya kaimu."
Amarya ta yi murna da hakan, ta kunnamata kallo ta ba ta
remote koda za ta sauya tasha daga nan ita kuma ta
koma bakin aiki kasancewar girkinta ne. Ba jimawa da
kunna kallon aka dauke wuta, nan take jin Amarya na ba
Rasheeda labarin wai Hajja Fatuma ce ta ce tunda ba
lokacinta ba ne sai ta yi hakuri da duk wani baƙonta da ke
son ganin Modibbo, idan na ta lokacin ya shigo ta yi duk
irin damun da ta so yiwa furarta.
Murmushi Ramlat ta yi na yaƙe, ta dai lura akwai takun
saƙa tsakanin matan gida. Waya ta fiddo ta kira Hajiya ta
fadamata.
"Anya kya zaunar musu har Magriba? Ba kya dawo ba ki
hakura zuwa gobe?"
Girgiza kai Ramlat ta yi.
"Hajiya lokaci zai ƙuremin idan ya kai gobe, mu dai yi
hakuri tunda kinga biyar da rabi ma ta wuce, kamar yanzu
ne za'a kira sallar in sha Allah."
"Ai shikenan, Allah Ya kaimu anjima. Sai kin dawo."
Ta amsa da amin suka yi sallama. Ba ta kai ga ajiye wayar
ba, kiran AlHassan ya shigo. Suka gaisa.
"Dole ta tsayar da ni a Gombe sakamakon lalacewar abin
hawa. Na so kwarai na shigo yau, amma gobe da sassafe
in sha Allahu zan taso."
Hakan ya dan yiwa Ramlat dadi, ko ba komai lamuran
zasu tafi yanda ta so.
"Ayya ba komai, Allah Yasa hakan ya zama alheri."
"Amin, sai dai kin ƙi sanar da ni komai game da abinda na
nema."
Sauke ajiyar zuciya ta yi.
"Ka yi hakuri, idan ka shigo har wanda zai ba ka mamaki
duk zan faɗamaka kuma zan kaika ka ganewa idonka in
sha Allahu."
Ya dan yi shiru, shirun da yasa Hussein faɗomata a rai, shi
ya saba yi mata hakan. Kewar Hussein sosai ta ke ji ta
kuma kudurce ko bai mata magana ba ita kam yau za ta
taɓoshi ta whatsapp.
"Shikenan. Allah Ya jisshemu alheri."
Ta amsa da amin cike da tausayinsa. Dan uwan da Allah
kadai yasan tun sadda ya ke bulayin neman ɗan uwansa.
Ta ji idanunta sun cika da kwalla daidai sadda suka yi
sallama. Ta shiga whatsapp ta aikawa Hussein saƙo, ta
jima tana kallon profile dinsa wanda bai dora komai ba a
idanunta tana wassafo hotonsa, karshe ta sauka.
Ba jimawa aka shiga kiraye-kirayen sallah, Rasheedat ta
jagorance ta zuwa ɗakinta. Alwala ta ɗaura ta tayar da
sallah saman dardumar da ta iske an shimfidamata.
Ta jima tana addu'ar nasara akan lamarin Hussein, shi
kansa ta yi mishi addu'a kwarai kafin ta shafa ta miƙe.
Abinci aka zubomata, dolenta ta ci tana kallon tsarin
yaran Amarya gwanin sha'awa. An idar da sallah ana
kuma neman haddar karatun da aka biya na Islamiyya.
Can kuma sai ga Amaryar ta fito sharr kamar sabuwa, ta
shirya cikin riga da siket na leshi ta cakare abinta tsaf. Da
fara'arta ta dubi Ramlat.
"Yi hakuri fa Ramlatu, bari idan na shiga zan miki magana
sai ki zo."
"Toh Anti. Kin yi kyau tubarakAllah."
Hakan da ta fada ya ba su dariya har yaran. Amarya ta yi
godiya ta wuce ɓangaren Mijinta. Sosai abin ya ƙayatar da
Ramlat.
***
Taimakon gaggawa likitocin suka shiga ba Hussein har
Allah Yasa ya dawo hayyacinsa. Hajiya Zeenatu ta rasa
sukuni, banda safa da marwa babu abinda ta ke yi a
harabar bakin kofar dakin da Hussein ke kwance. Can
ɗaya daga cikin likitocin ya fito, da hanzari har mayafin na
sulalewa ta ƙarasa.
"Dakta ya farfado?"
Daktan ya yi murmushi gami da gyara zaman gilashinsa.
"Alhamdulillah Hajiya, ɗanki ya farfaɗo, ki kwantar da
hankalinki."
Ta tamke fuska.
"Mijina ne."
Mamaki karara a fuskar likitan kafin kuma ya haɗiye don
ba abinda ya shafeshi ba ne.
"Ok, idan ba damuwa ki biyo ni zuwa ofis."
Daga haka ya yi gaba.
"Matsalar Hussein damuwa ce da ta haddasa masa ciwon
kai mai tsanani. Sai jininsa da ya hau, sai kin kula sosai da
cimarsa har ma da walwalarsa domin irin ciwonsa na
bukatar kulawa kuma ba ya son yawan tunani."
Hajiya Zeenat ta yi shiru a ranta tana jin takaicin Hussein
da zai sa damuwar wani abu bayan ita ce duniyarsa.
"Kin ji abinda na ce?"
Tambayar ta katse tunaninta. Ajiyar zuciya ta saki.
"Naji kuma zan kiyaye. Yanzu ina iya ganinsa?"
Likita na ƙaremata kallo ya gyada kai.
"Eh Hajjaju."
Ta mike tana watsa masa kallo mai kama da harara, ba
shiri ya janye idanunsa tunda ya san shi ya jaza wa kansa
da ya bita da kallon kurilla. Ba kuma don sha'awa ba, sai
don ya ga abinda ya kwaɗaitar da mara lafiyarsu da ta kira
da Hussein har ya ji ita ya ke da muradin zama abokiyar
rayuwarsa.
"Su ta shafa." Ya ƙarƙare tunanin ta hanyar furta hakan a
fili.
Hajiya Zeenatu ta shiga ɗakin da Hussein yake, wannan
karon babu kowa sai shi ɗaya. Idanunsa a lumshe, a farko
ta yi zaton bacci ya ke, sai dai rufe ƙofar da ta yi yasa shi
kallonta. Ta sakarmasa murmushi tana mai ƙarasowa ta
zauna gefen gadon ta kama hannunsa.
"Sannu Hussein, ya jikin?"
Gyadamata kai kawai ya yi ya kara kauda kansa.
"Ba zan kwana a nan ba, su sallame mu."
Yanda ya yi zancen ka san iyakar gaskiyar kenan ba wasa.
Cikin rarrashi ta shigo kokarin fahimtar da shi kuskuren
hakan, sai dai yanda ta kafe haka ya kafe har abin ya
tsorata ta. Aikuwa dai karshe sai sallamar aka ba su da
lodin mgunguna bayan an ƙara jaddada masa akan ya kula
sosai da jikinsa.
Su na komawa gida ma'aikatan suka tarbeshi tare da yi
mishi sannu.
"Dalla Malamai ku matsa! Ba kwa ganin yanayin jikinsa
ne?"
Hussein ya dubi Hajiya Zeenat, a fuskarsa ta gane bai ji
dadin abinda ta yi ba. Ya tsaya ya amsa gaisuwarsu ita
kuwa ta yi gaba tana tsaki. Godiya ya yi musu san nan ya
shige ya bar su da gulmarta.
Sallar Magriba ya soma yi san nan ya shiga wanka. Yana
fitowa ya kimtsa, Hajiya Zeenatu kuwa tana ƙasa ta na
bada umarnin abinda za'a girkawa mijinnata.
Ya dauki wayarsa, ya ga missedcalls din Hisham sai kuma
na wani abokin aikinsa. Data ya kunna ya leƙa whatsapp.
Shiru ya yi ya ƙurawa sunanta idanu yana kallon saƙon da
ta aiko ba tare da ya buɗe ba, ya hangi dai sallama da
gaisuwa, sauran ne bai da masaniya. A hankali aka zare
wayar daga hannunsa. Hajiya Zeenatu ce, gabansa ya faɗi.
"Haba Yallaɓai, yaushe ma ka farfaɗo da za ka ɗauki
waya? Ba dai ka manta sharuɗɗan Dakta ba?"
Ta ƙarashe tana duban wayar, tuni ta shiga key, shima
yanda ta ke kallo haka ya ke kalla, ganin ta rufe ya sanya
shi sauke ajiyar zuciya. Gaba daya ta kashe wayar tana
mai duban soyayy duk a kokarinta na gudun kar ya sauya
shawarar da ta kawomasa a ɗazun.
"Wayar a hakura a bar ta zuwa gobe. Yanzu mu je ƙasa ka
jira abinci sai ka sha magani."
Ta faɗi gami da riƙe hannunsa. Ya ciji leɓɓansa, haka nan
ya ji bai kyauta ba bisa rashin ba da amsa ga Ramlat sai
dai maganganun Hisham na faɗomasa a rai sai ya yi
gaggawar fidda tunanin.
***
Mintuna kusan goma sha biyar sai ga kiran Amarya a
wayar Rasheedat.
"Muje na yi miki rakiya."
Haka kawai Ramlat ta ji faɗuwar gaba, ta amsa da toh
tana mai haɗiyar yawu mai ɗaci.
Da sallamarta ta sa ƙafa a falon. Dattijo cikin shigar
kamala, kana ganinsa ka ga cikakken bafulatani. Tundata
shigo yake yiwa fuskarta kallon tsanaki don son tantance
ko akwai inda ya santa ko kuwa yau ne farkon ganinsa da
ita. Ta karasa ta gaishe shi, Amarya tuni ta mike zuwa
ɗaki. Hakan kan faru, idan har Modibbo nada baƙo, sukan
ba shi wuri ya gana da ita.
"Baiwar Allah daga ina?"
Ya tambaya cikin hausarsa da har sannan ba ta ginu
kamar ta Bahaushe ba.
Ta hadiyi miyau gami da ambaton Allah. Ta gabatar da
kanta sannan ta ɗora bayan ya shaidamata eh ya san
Malam Abdullahi kakanta kuma ɗan unguwar da yake,
Yakasai.
"Kawu dama magana ce da ta danganci Hussein, dan
uwan AlHassan da ake nema."
Shiru-shiru, ba ta ji ya ce uffan ba don haka ta ɗago kai.
Yanayin dake shimfiɗe a fuskarsa ya tsorata ta, ya kuma
kaɗa hanjin cikinta.
"Kina da labarinsa? Ke wace ce?"
Wannan ne tambayoyin da ta samu da suka ƙara cilla ta a
kogin tunani da mamaki.
KARFEN KAFA Chapter 57
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
ALLURA TA TONO GARMA...
"Kurma ki ka koma?"
Ta dawo hayyacinta ta kalle shi gami da girgiza kai. To
me za ta ce bayan ta gabatarmasa da kanta?
"Ina gargaɗinki da ki cire kanki a abinda bai shafeki ba.
Idan kina son tsira da lafiyar kwakwalwa da na gangar
jikinki ki fita hanyar Hussein da Zeenatu."
Da wani irin razana ta dubeshi, wannan ƴar fara'ar dama
tun soma labarin ya kauda ita a saman fuskarsa sai ya
zama kamar wani Mugyambo a idanunta. Kwallar da ta
cika kurmin idanun suka soma sharara.
"Ka...ka..san Hussein yana nan? Ban ambaci Zeenatu ba,
ka san..."
"Ke Bingel! (Yarinya). Ke wacece da za ki tuhume ni? Ina
gargadinki karo na biyu kuma na ƙarshe ki tashi ki binne
maganarnan a nan wurin da kike zaune. Idan ba ki ƙi ji ba,
ba kya ƙi gani ba. Duk abinda ya faru gareki sanadin fasa
wannan zancen, ki yi kuka da kanki!"
Ramlat kirjinta na bugu, hawayenta na kwaranya,
kwakwalwar ta tsaya cak ta bar aiki. Ta kasa haɗa kowane
lissafi, jin ta take yi kamar ba'a duniyar mutane ba. Kamar
wata duniyar ta daban ta ke ciki mai tsananin ruɗani da
azaba. Kallonsa ta ƙara yi, girman tuni ya zube ƙasa
warwas! Kallo ne kamar wacce ke zaune gaban sa'anta.
"Ka na da hannu a komai? Ka na a ɓatar da Hussein daga
zuri'arku? Me ya yi maka haka da zafi?"
"Kina ƙara dulmiyar da kanki cikin tafkin nadama da da na
sani, kalaman da kike yi za su rushe duk wani farin ciki na
rayuwarki. Ki kama kanki! Ki tashi ki bar min gida tun kina
da sauran lafiyar aikata hakan!"
Miƙewa ta yi a sanyaye, har za ta fice ta juyo ta dubeshi
yana faman muzurai. Dattijon da bai kama daraja da
girmansa ba, babu amfanin ganin ƙimarsa.
"Kawu ka sani, Allah na bayan masu gaskiya. Ƙarya fure ta
ke ba ta ƴaƴa."
Daga nan ta bankaɗa labule ta fice, ba ta jin za ta iya jiran
yin sallama da Amarya. Babu inda ta ƙara shiga a gidan
haka ta fice tana hawaye.
Tafiya ta ke ƙafafun na harharɗewa, kalaman Kawu daki-
daki ta ke tunawa tana ƙarin fahimtar dagaske dai akwai
hannunsa a cikin ɓatan Hussein.
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!"
Ta ambata a fili, tausayi sosai da wata irin ƙauna ta
Hussein ya ƙara mamaye zuciyarta. Ji ta ke komai za ta
iya aikatawa muddin hakan zai dawo da Hussein cikin ƴan
uwansa. Wayarta ta yi ƙara, Hajiya ce. Yanda ta ke kuka ba
ta jin za ta iya amsawa, don haka ta mayar da wayar jaka.
Kafin ta bar lungun sai da ta tsaya ta saita kanta ta share
fuska. Abin hawa ta tsayar ta faɗa.
"Malama ba ki faɗi inda zan kai ki ba."
Ta haɗiyi miyau. Dakyar ta faɗi sunan unguwar ta yi shiru,
kanta ke sarawa ga wani zazzaɓi-zazzaɓi.
***
Tsam! Modibbo ya miƙe ya shiga ɗaki, Amarya na zaune
na kallon wani ƙaramin bidiyo na Ibro tana dariya, ganin
mutum ya faɗo ba sallama ya sa ta ɗan razana kafin ta
sauke ajiyar zuciya. Tun kafin ta nemi ba'asi ya katsemata
hanzari.
"Fita zan yi, ki je kawai idan na dawo zan kiraki. Akwai
uzurin da zan gabatar."
Ya faɗi a kausashe, ta miƙe jikinta a sanyaye ta fita fuskar
cike taf da tarin tambayoyin da babu mai amsa mata sai
Ramlatu. Sai dai sama ko ƙasa babu ita, hatta su
Rasheeda sun yi mamakin da ba ta biyo ta musu sallama
ba.
Fitar Amarya ya ba Kawu Modibbo damar buɗe sif ɗinsa
ta kaya, can ƙasan ya zura hannu ya ɗauko wani ɗan
akwati mai girma da duk faɗin gidan babu wanda ya isa
ya taɓa. Hankalin ma bai kai gareshi ba. Cikin rigarsa ya
zaro mukullin da ba ya rabo da shi a jikinsa, ya buɗe,
kwakwalwa ce! Kwakwalwa ta ƊAN ADAM! Ta yi baƙiƙirin
a madadin jan da ta ke da shi har da jini-jini a shekaru
masu yawa. Idanun Kawu Modibbo suka kaɗa.
"Ita ce! Ita ce yarinyar!"
Abinda ya faɗi kenan a fili kafin hannu na rawa ya maida
ya rufe. Gumi ya shiga tsastsafowa daga fatar jikinsa. Ya
sa hannu ya share. Tun komai bai ƙarasa lalacewa ba zai
yiwa abin tufka. Ya ayyana hakan a ransa yana