Showing 24001 words to 27000 words out of 113545 words
Chapter 9 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
kasa.
"My Zeenat, kin yi kyau sosai."
Wani sanyin dadi ya mamayeta, ta sumbaci leɓɓansa.
"Nagode Sweetheart."
Ganin tana kokarin wuce gona da iri yasa shi janye jiki.
"Bari nayi sallah."
"Sallah, wace sallar?"
Yanda ta fadi a mamakince shima sai ta jefashi cikin
mamakin kalamanta. Ya zubamata idanunsa mai adon fari
ƙal da baƙin kwayar idanu siɗik.
"Me kike nufi? Wace Sallah muke yi matsayinmu na
musulmai?"
Gaban Hajiya Zeenatu ya bada dam!
_*"Kiyi duk yanda za ki yi, ki dinga shagaltar da shi daga
ibada, zamu turamasa arnen aljan wanda zai tayaki yaƙi.
Ina kara gargadinki! Kar ki kusa ki bari ya dinga sallah
akan lokutanta!!!"*_
KARFEN KAFA Chapter 50
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Wannan yana daga cikin farkon abinda Gora ya fadi mata
sadda suka soma zuwa wurinsa a karon farko game da
lamuran Hussein.
Ganin ta tsaya tana kallonsa yasa shi giftawa ya fice zuwa
banɗaki. Ta bi ƙofar da kallo.
'Ke me zai dameki? Ba yanzu za ki yi aikin da za ki samu
ciki ba? Idan kika samu komai zai zo karshe!'
Wani ɓangare na zuciyarta ya tunatar da ita. Ta sauke
ajiyar zuciya tana wani irin murmushi kafin ta zauna gefen
gadon. Tana kallonsa ya yi sallah a tsanake, ya yi addu'a
kafin ya naɗe dardumar ya mike.
Mintuna talatin da suka biyo baya, komai ya kammalu
kamar yanda ta ke so, murmushi kawai take kamar
koyaushe cike da gamsuwa idan ka ɗauke Hussein wanda
ransa sam ba dadi. Kusan hakan ce ta saba faruwa da su,
zai iya cewa wahalar da shi kawai ta ke yi a kowace tafiya
don ba wani gamsuwa yake ba. Ganin ta soma jan
munshari yasa shi miƙewa ya faɗa banɗaki. Can ya fito ya
sauya kaya, yunwar ɗazun ce ta dawo mishi. Matsawa ya
yi ya tasheta. Cikin magagin bacci ta dubeshi.
"Lafiya?"
"Muje ki ɗan ɗumaman abinci, nasan yanzu John ya sanya
a fridge."
Yamutse fuska ta yi.
"Wallahi na gaji, ko nan da can ba zan iya motsawa ba.
Ka je kawai ka tasheshi ya yi maka."
Daga haka ta juya ta cigaba da bacci, girgiza kai ya yi
gami da gyaramata abun rufa. Wayoyinsa ya dauka ya fita
daga dakin cike da damuwa. Kamar akwai abinda ya rasa,
kamar yana da wata damuwa amma ya kasa gane kan
zaren.
Maimakon ya kira John da ya wuce Boysquarters, sai ya
ɓige da dafa ruwan shayi, ya zaɓi shan tea da bread
kawai. Sai da ya kammala ya dawo falon, wayarsa ya
fiddo ya kunna Data. Kwanaki biyu kenan rabonsa da hawa
online, wannan tasa saƙonni suka shiga faɗowa, da na
mutanen da ya sani da baƙin lamba kamar koyaushe. Ya
kuma riga da yasan baƙin lambobin bai wuce na mata,
idan da sabo ya ci ace ya saba.
Saƙonta ya ɗauki hankalinsa, ya kuma yi mamakin
ganinta online, ya kara duban lokaci. Ƙarfe goma daidai
na dare. Murmushi ya yi ganin amsar da ta ba shi a
wancan lokacin, maimakon mayar da martaninsa sai ya
ɓige da wata tsokanar.
"Ba ki yi bacci ba? Da wa kike hira toh?"
Yana aika hakan sai ya maida kai ya ci gaba da shan
shayinsa. Tausayinta ya ji ya mamaye zuciyarsa, shakka
babu sam bai kyauta ba.
***
A ɓangaren Ramlat, tana kwance ne tana kallon Status,
duk duniyarta ba dadi. Ga lamarin Chairman ga kuma
Hussein da ya yi fushi da ita. Tana shirin sauka ganin uban
hamman da ta ke dokawa, sai ta nemi baccin ta fasa ganin
saƙon da ya shigo. Da wani irin ɗoki ta buɗe ta karanta.
Murmushi sosai take yi haɗe da dariya ciki-ciki. Ko ba
komai hankalinta ya kwanta.
"Kai nake jira, hakuri nake so na ƙara ba ka."
Abinda ta aikamasa kenan.
***
Yana kammala shan shayin, ya dauki wayar, ganin abinda
ta ce yasa shi jin wani daam, lumshe idanu ya yi kafin ya
buɗesu. Sai kawai ya zaɓi kiranta. Kai tsaye ya dokamata
kira, sai da ya kusan katsewa sannan ta ɗaga.
***
"Kira war haka? Ina Madam dinka? Ka rufan asiri."
Abinda ta ce kenan bayan ɗaga wayar.
"Ni kenan na tonawa kaina asiri ko? So kike yi a gane
damuwar da ke kwance saman fuskata na jefaki a
damuwa?"
Maganarsa sai ta yi mata nauyi, ta rasa amsar bayarwa,
can ta daure.
"A'a, ni ce mai laifi, ni na zaƙe da yawa. Ka.."
"Kika ƙara bani hakuri ina miki rantsuwa da Allah za ki
ganni a gidanku yanzu."
Yanda ya yi maganar daga ji ka san ba wai faɗa ya yi ne
kawai ba. Kirjinta ya soma bugu da ƙarfi, ta ji kanta na
neman tarwatsewa. Ta kasa gane a maudu'in da za ta jefa
kalamansa. Ta rasa abinda ya haɗa kalmar hakuri da
batun ziyartarta a wannan lokaci don haka sai ta kasa
cewa uffan. Shiru ya biyo baya na ƴan sakanni sai
numfashin junansu da kowanne ke jin fitarsa.
"Ɗazun na ce kinsan me? Ba ki bari na ƙarasa ba, yanzun
ki bani damar na ƙarasa maganata."
Ta kasa ce mishi uffan. Har ya kara magana.
"Na baka." Ta furta a hankali.
"Ke ce mace ta farko bayan Zeenat, da lambarta ya shiga
cikin wayata har nayi saving. Ke ce mace ta farko da
ƙafata ya taka har gidansu, ke ce mace ta farko da na
zauna muka yi hira da ita har na tsawon mintoci ba tare
da naji hirar ta ishe ni ba. Kawai dai idan so ki sani, kina
da babban matsayi a rayuwata da ba zan ce gashinan ba.
I want you to keep staying in my life, ina jinki kamar wata
ƴar uwata mai bani ƙwarin gwuiwa. Kamar dai kina ban
ƙarfin ci gaba da rayuwa, na daina tunanin inama Allah Ya
dauki raina, na bar tunanin bani da kowa a duniya. Please
Ramlat, kar ki gujeni ko me zai faru, ko me zan miki. Kiyi
hakuri, nayi maki laifi a ɗazun da ni kaina ba haka na so
ba. I just can't do otherwise idan aka zo irin wannan
lamarin. Ban kuma san dalili ba."
Wani sabon yanayi ke shigarta game da HUSSEIN, wani
abu take ji na yawo tun daga tsakar kanta har yatsun
ƙafafu. Zuciyarta gaba daya ta cika da tausayinsa. Ganin
kamar tana neman wuce gona da iri yasa ta saurin
magana.
"In sha Allah hakan ba za ta faru ba. Allah ne Ya haɗa mu,
ban isa na kawo karshen zumuntarmu ba. Ina rokon Allah
Ya yayemaka dukkan damuwarka. Sai dai don Allah ina
roƙonka akan ka dage da kai kukanka gareSa. Kamar
yanda ka bani shawara a ɗazun, kaima yanzu ina so ka yi
amfani da hakan."
Murmushi ya yi mai sauti yana ƙara gyara mazaunin wayar,
ƙafafunsa a saman kujera.
"Kina shiga haƙƙin Madam ɗita fa."
Harara ta bugamishi kamar yana kallonta, wani abu ta ji
kamar ya soke ta a ƙahon zuci mai kama da KISHI.
"Ai ba ni na kiraka ba, sai da safe."
Tana ji yana dariya sadda ta datse kiran. Ita kuwa
kwanciya ta yi ta shiga duniyar tunani. Murmushi sosai ta
ke yi, wani sabon yanayi take ji game da Hussein wanda a
yanzu ta kasa ƙaryatawa. Tunaninta ya tsaya cak! A gefe
guda kuma tausayin kanta ya mamayeta. Wato dai ta
gama fahimtar ta faɗa SON MASO WANI.
Miƙewa ta yi ta faɗa banɗaki ta dauro alwala, nafila ta
shiga yi kafin ta yiwa Hussein addu'a ta musamman.
***
Washegari ta tashi ranta fari ƙal, kaso mai yawa na
damuwarta ya yaye. Ta yarda ta kuma aminta, ta rasa
dabara ko wani makami da za ta kare kanta na cewar ta
faɗa tarkon SO.
Tana kai yara makaranta ta wuce kai tsaye Head of
service inda ta kai takardar neman transfer da ta rubuta.
Kusan sun yi waya da Zulaihat da Rafee'ah, duk sun goyi
bayanta don a cewarsu mutunci ya fi komai.
Kai tsaye ofishinsa ta nufa ganin da ta yi ya iso.
Kwankwasawa ta yi gami da sallama, jin muryarta da
gaggawa ya bata umarnin shigowa. Ta shiga fuska a haɗe.
Kallonta yake har da ɗan miƙewa duk ya rikice. Ya san da
cewa ya mata laifi amma ba yanda ya iya, gani ya yi idan
ya biyemata to fa za ta kai shi ta baro ne. Ba tare da ta
damu ta gaidashi ba ta fiddo ƙaramar envelope waanda ta
sanya dukkan kuɗaɗen da ya bata.
"Idan har wannan ce damar da ka samu na zuwa
tambayar aurena a gidan iyayena, to ka sani daga yau na
rusata. Kuma kar ka manta, ni ba yarinya ba ce ballantana
ka yi tunanin za'a tursasani ko a yimin dole akan aurenka."
Ta zazzage kudin saman tebur.
"Ka ƙirga ka gani, idan da su kake taƙama har ka yimin
wannan aika-aikar, ko sisi ban taɓa a cikinsu ba. Ina fatan
daga yau komai zai wuce. Kar kuma ka kara tunanin cewa
zuwa wurin Kawu Bello zai ba ka dukkan wata dama a
kaina."
Daga haka ta juya da zummar tafiya ya dakatar da ita ta
hanyar kiran sunanta. Ta juyo tana dubansa fuska a daure.
Gaba daya ya sauya fuska.
"Haba Ramlat, saboda na bi hanyar da addini ya tsara na
neman iznin aurenki gurin magabata shi ne za ki watsan
ƙasa a ido? Wannan wace irin kiyayya kike nunamin? Ina
da kudi, ina da gidaje da dukkan matsayin da na cancanci
ki so ni dominsu, amma ke wannan duk bai sa kin saduda
ba. Idan don matana ne, wallahi wallahi ba zan haɗaki
gida ɗaya da su ba. Kin ji rantsuwar ɗan musulmi. Ya kike
nema ki yimin wannan kwalelan?"
Ta dubeshi duba na raini, ita dariya ma ya soma bata.
"Ni kudi bai isa ya siyeni ba, hakanan ba kuɗi ake nema a
zamantakewar aure ba. Yarda, biyayya, kauna, so,
mutunci, daraja da ƙima dama sauransu, su ake neman a
aure. Babu ko daya da ka samu a idona. Ina kara neman
alfarma akan ka rabu da ni ka fita daga rayuwata. Ba zan
iya aurenka ba."
"Idan kudi na siyan soyayya! Wallahi Ramlatu sai kin
aureni koda ba kya so! Mu zuba ni da ke!!"
Ya fadi a tsawance, kalaman sun faɗarmata da gaba, ta
dake ta yi murmushi.
"Allah Zai tsayamin."
Daga haka ta sa kai ta fice dama ba da niyyar zama ta zo
ba. Maimakon ta yi gida sai ta nufi gidan Amrah da aka
sallama, ƙara duba jikinta.
Ta sameta kamar ba ita ba don Magajiya har ta koma
gida. Tun a asibitin suka sauya shawara, da ace ta dawo
gida gwara Magajiyar ta biyota gidanta su kwana tare.
"Ya na ganki wata iri? Ke kullum dai da damuwa kike
zuwarmin." Amrah ta ƙarashe cike da zolaya. Harara ta
samu daga Ramlat. Sai kuma ta ja tsaki.
"Ke kinsan dalilin wai da yasa Kawu ke nemana?"
Amrah ta girgiza kai. Nan ta labartamata komai da komai
har haduwarta da Hussein da yanda ta kaya tsakaninta da
Chairman yanzun a Ofis.
"Kai jama'a! Wai shi wannan mutumin da me yake taƙama
ne? Ai sai ki yiwa kanki kiyamullaili, ba zama za ki yi ki
zuba ido ba. Wallahi ki yi kokarin fito da miji ki yi aure
abinki ya fiyemaki alheri, ke kanki kinsan tunda ya furta ba
kyaleki zai yi ba."
Ramlat idanunta suka cicciko, batun fito da miji sai ya yi
mata famin rashin Aliyu. Banda kaddarar mutuwa da ke
kan kowa, yanzun da ba tana cikin inuwar aure ba? Waye
zai ganta har ya ce yana sonta ko kuma ita ta ji son
mutumin da ya yi mata nisa?
"Ni wallahi da ace wannan Hussein din ba shi da mata,
wallahi zan so ki aureshi. Mutum ne iya mutum. Ke ko shi
ko dan uwansa Hassan."
Kalaman Amrah suka sa ta fiddo idanu tana dubanta,
Amrah ta yi dariya.
"Meye toh? Allah kuwa ni na fi so ma ki yi auren nesa.
Kinsan mutane magulmata ne. Abinda ya riga ya wuce ma
sai su ɗagoshi. Kuma fa ni sai naga kamar Hussein dinnan
sonki yake."
Guntun tsaki Ramlat ta ja. Gabanta na faduwa, yanzun ko
sunansa aka ambata sai ta ji sauyi a zuciya da kwanjinta
😜
"Malama mu bar maganarnan, ba ta da fa'ida."
Dariya sosai Amrah ta yi, ta fuskanci inda Ramlatun ta sa
gaba kawai dai ta yi shiru ta ga gudun ruwanta. Matar da
ko labarin Hussein ta ke bada wa sai yanayinta ya sauya.
"Uhum, a juri zuwa rafi." Fadin Amrah kafin ta kai
mangwaron da ta kammala yankamusu bakinta. Harara ta
kuma samu daga Ramlat.
***
ADAMAWA..
Ɗaure fuska ya yi kamar bai taɓa dariya ba yana duban
Dada, cikin harshen fulatanci ya yi magana.
"Akan me zai sauka a gidannan? Me hakan ke nufi?"
Dada ta harareshi.
"Taheer ɗan uwanku ne, don ya zaɓi gidannan matsayin
wurin kwanansa ba laifi bane. Kar ka manta ɗan ɗan
uwana ne."
AlHassan ya ɗan dafe goshi, sam bai ji dadin wannan
hukunci ba. Sallamar direba rike da ƙaton akwati yasa
AlHassan miƙewa.
"Ni zan wuce Dada, akwai inda zan je."
Ta bishi da a dawo lafiya, a kofar suka yi kiciɓus da
Taheer. Dauke kai ya yi kamar bai ganshi ba zai wuce, da
sauri Taheer ya karasa ya mika masa hannu da sallama.
Akan dole ya bude nashi hannun suka gaisa daga nan bai
ƙara cewa uffan ba ya yi gaba.
Taheer ya bishi da harara, dama ca ya tsaneshi saboda
girman kai. Shi kuwa ya zo kuma sai ya cimma
manufarsa, idan ana so dole sai Hafsat ta so shi ta
kaunceshi. Sai ya aureta.
Dada ta tarbeshi a mutunce, aka mika kayansa dakin su
AlHassan na baya.
Hafsat dake makaranta tana dawowa ta yi kiciɓus da shi a
falo yana cin abinci suna hira da Dada kamar dama can
sun wani saba. Turus ta yi tana kallonsa ranta na wani irin
zafi, Dada ce ta lura da ita.
"Mene na tsayawa haka kamar kin ga Dodo?" Dada ta
furta cikin harshen Fulatanci sanin da ta yi Taheer din
kusan ba abinda aka koyamusu, manyan yara Modibbon
ne kaɗai masu jin fulatanci. Su kam saura sai Hausa da
turanci.
Maganar Dada ya kai hankalin Taheer ɗin ga Hafsat,
ƙuramata idanu ya yi, ta watsamasa harara ta kauda kai
gami da karasowa ciki. Maimakon ta ba shi haushi sai ta
ba shi dariya. Ya yi murmushi.
"Welcome my dearest."
Ya faɗi sanin da ya yi shi ɗin ma Dada ba ji ta ke ba. Ciki-
ciki ta gaidashi saboda hararar da Dada ke watsamata. Ya
amsa a sake. Ta mike ta faɗa ɗakinta har wani kwalla ta ji
sun cikamata idanu tsabar ɓacin ran ganinsa. Ta rantse
ba za ta ƙara kwana a gidannan ba, gidan AlHassan za ta
wuce.
Tana soma haɗa kaya kenan sai ga Dada. Nan ta yi mata
kaca-kaca ta kuma rantse muddin ta ce za ta bar gidan
sai ta saɓamata.
"Ku kenan haka ku ke son na mutu da bakin cikin ban
shirya da ƴan uwana ba? Yayana ya mutu ya bar ni
zuciyarsa cike da burin ganin watarana su Hamma
Modibbo sun riƙemu matsayin jininsu kuma ƴan uwa, bai
samu ya ga hakan ba, sai yanzun da Allah Ya soma amsa
addu'a ta har gashinan wani a gidan Modibbo ya yi
sha'awar zuwa gidannan ku ke neman ku sanyamin ciwon
kai? Toh sa ƙafa ki fita daga gidannan mu zuba ni da ku!"
Dada na kaiwa nan ta fice ranta na suya. Hafsat ta yi cilli
da atamfar da ke hannunta ta fashe da kuka. Dada ba ta
san manufar Taheer na shigowa gidannan ba. Ita kuwa ta
rantse nan duniya ba wanda zai sa ta aurensa. Sai dai ko
me zai faru ya faru.
***.
_*So ne baƙin duhu zallah, a faƙaice zai yi ma illah,
ciwon so ba ya biɗar sassaƙe... *_
*Hamisu Breaker. *
KANO.
Karfe biyar da mintuna na yammacin Asabar, tsaye yake
jan abin motsa jikin na (Treadmill), daga shi sai riga da
gajeran wando. Ya sanya tawul a saman wuyansa, a
hankali yake tafiya ba kamar Hisham dake gefe yana
zabga uban gudu ba.
KARFEN KAFA Chapter 51
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Kacokan kusan hankalinsa ba'a jikinsa yake ba, Hisham
ya kalleshi ya fi a ƙirga, karshe ya tsayar ya sauka yana
maida numfashi, kai tsaye water bottle ya dauka dake
gefen jakunkunansu ya shiga kurɓa can ya ƙaraso ya tsaya
gami da dafe ƙarfen da Hussain ke kai, ya ƙuramasa ido.
"Lafiya?"
Ya fadi yana maida numfashin gajiya.
Hussein ya dubeshi. Sai a sannan ya yi amfani da ƙaramin
tawul din ya goge gumin da ke zirarowa daga goshinsa
har yana ɗiga daga karan hancinsa zuwa baki.
"Me ka gani?"
Gira Hisham ya ɗaga yana murmushi.
"Sai wani tunani kake kamar wanda ya faɗa tarkon so."
Kallonsa Hussein ya yi a karo na biyu kafin ya sauka ya
zauna saman kujera.
Hisham bai hakura ba ya ƙaraso ya zauna gefensa.
"Kai mutumin, na fa gama gane bakin zaren. Ka dai yi
gamo."
Guntun tsaki Hussein ya ja.
"Kai maganar ma da ba ta kamata ba yinta ka ke yi. So
kuma? Ban da lokacin shirmennan."
Murmushi kawai Hisham ya yi. Kamar ya ce wani abu sai
dai bai ce ba.
Wayar Hisham din ce ta dauki ƙara, ganin sunan da ke jiki
ya sanya shi satar kallon Hussein yana murmushi. Shi kam
bai ma san yana yi ba, wai harara a duhu.
"Ranki ya daɗe Antinmu."
Fadin hakan yasa Hussein satar kallonsa, ya basar kamar
bai gani ba, can ya ce.
"Af, wayarta ba chaji ne toh inaga don ba ta saba
kashewar ba."
Can ya ƙara faɗin.
"Toh Allah Ya kaimu goben, amma dai a tahomin da
yaranmu."
Hussein ya gaji da satar kallon ya juyo gaba dayansa yana
mai tsuramasa idanu.
Dariya Hisham ya yi, ba don bayanin Ramlat din ya ba shi
dariya ba sai dai yanayin amininnasa.
"Ayya toh Allah Ya maidomana su lafiya. Allah Ya kaimu
goben. In Sha Allah idan na koma zan sanarmata."
Daga haka ya kashe wayar. Yana dariya ciki-ciki ya ce.
"Kai kuma wannan mayun idanun da ka tsuramin fa? Toh
wallahi kurwata kurrr!"
Duka Hussein ya kai mishi a kafaɗa, ya yi dariya. Shi kuwa
ya mike ya dauki jakarsa ya yi gaba zuwa hanyar banɗaki.
Yana jin Hisham na fadin.
"Oho dai, na gane komai!"
Har ya kammala shiri yana maimaita kalmar na gane
komai din da Hisham ya furta.
Sai da ya kimtsa sosai ya fito, wannan karon dogon
wando ja ne ya sa da t-shirt bodyhug fara ƙal.
"Sai ka taho."
Hisham ya bude baki.
"Au haka za ka yimin? Toh ai shikenan. Nidai gobe kam ba
zan zo ba, inada baƙuwa ta musamman a gidana."
Taɓe baki Hussein ya yi.
"Matsalarka." Daga haka ya yi gaba bayan ya yi sallama da
ƙalilan da suke a dakin motsa jikin. Hisham ya bishi da
kallo yana dariya.
***
WASHEGARI...
Cikin shirinta tsaf na riga doguwa ta shadda kalar sea
green ya sha adon stones. Mayafi ƙarami ta ɗora
samansa. Tuƙi take hankalinta kwance, kaso na
damuwarta
Sati daya kenan da ta nemi sauyin wurin aiki, ta samu
takardar sauyi daga ma'aikatarta zuwa ma'aikatar ilimi.
Wani farin ciki na musamman take ji, ko ba komai za ta
rabu da alaƙaƙai. A gefe guda kuma ta gama fahimtar
yanda ta yi nisa a son HUSSEIN. Soyayyar da idan ta tuna
shi ma dadi take ji, murmushi take yi
Ta bude hirarsu ya fi a ƙirga, ta tuna zantukansu ya fi sau
dari a satinnan. Ji take inama yanda take jinsa shima haka
take a wajensa. Har ta ƙaraso gidan A'isha ba ta bar
tunaninsa ba.
"Assalamu alaikum."
Ta furta sadda ta isa ƙofar falon, ƴar aikin A'isha mai suna
Bingel, ta amsamata sallamar. Laulayi da ta soma ne yasa
dole Hajiya nemarmata ƴar aiki wata dattijuwa. Suka
gaisa ta karasa cikin falon daidai da fitowar A'ishar daga
ɗaki. Baki Ramlat ta saki tana kallon yanda duk ta zabge
ta rame. Ta ƙaraso ta zauna.
"Kai Auta, duk laulayin ne?"
Yamutse fuska A'isha ta yi kamar ta yi kuka. Cike da
shagwaɓa ta amsa.
"Wallahi Maman Affan ni duk cikin ma ya isheni. Allah
kuwa ji nake kamar a .."
"Astagfirullah! Kar ki karasa Princess. Ina rabaki."
Suka dubeshi, Hisham ne wanda ya fito daga dakin sanye
da jallabiya. Dariya ma