Showing 69001 words to 72000 words out of 113545 words

Chapter 24 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

ƙosa amma ba ta ce
komai ba, shi kuwa yanda ta ke hura hanci ke ba shi
mamaki da dariya. Ya ɗan murza karan hancinsa kafin ya
soma magana cikin nutsuwa.
"Satina sama da biyu a Adamawa, ba ki samu damar
yimin ko gaisuwar juma'a ba, why?"
Ranta ya sosu ainun.
"Ina tunawa da wadanda suka tuna da ni. Bana sanya ka
layin wadanda suka zamemin wajibi na nema balle na
gaida."
Ɗif ya yi kamar mutuwa ta ratsa, ta daurewa zuciyarta ba
ta kalleshi ba sai dai ta ji wani irin sanyi a zuciyarta ko ba
komai ta ɗan huce daga maganar da ya gasamata. Sai ta
tsinci kanta da murmusawa. A hankali ta saci kallonsa
don ganin yanayinsa, ga mamakinta murmushi sosai yake
haƙoransa a waje, ya juyo rabin jikinsa ya tallafi haɓarsa
da hannunsa ɗaya yana kallonta. Ta kauda kai.
"Hakan ma na gode sosai. Kin burgeni. Rashin wancan
mutumin ne yasa ki ka sauya har ki ke gasan magana ko?
Hum, za ki huce."
Ba ta ce uffan ba hakan yasa ya gama shan ƙamshinsa ya
ɗora.
"Alhamdulillah, na sadu da iyaye da yan uwana lafiya.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin Talikai.
Wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da har abada
Hussein ba zai mance da Ramlat ba. Na je Mubi kuma na
je Maiduguri. Ban taɓa zaton zuwan rana makamancin
hakan ba, komai ya faru bisa jajircewarki akan dukkan
lamurana. Na gode. Ina kara godiya da fatan alheri gareki.
Har abada ba zan mance da halaccin da ki ka yi gareni ba.
Allah Ya ba ki abinda kike so kuma ya ke sonki."
Ta dubeshi, idanunsa a lumshe har lokacin murmushin ya
ke, ganin zai bude yasa ta janye nata idanun kirjinta na
bugu. Ta rasa wane irin so ne na Hussein a zuciyarta. Son
da ba ta jin ya kai irin wanda ta yiwa ALIYUNTA. Idan Aliyu
da dadin kalamai ya rinjayi zuciyarta, ta rasa da me
Hussein ya rinjayi nata zuciyar.
"Zan tafi."
Abinda ya ce kenan.
Ta sa ƙafa kawai ta fice ta rufe mishi ƙofar ba ta ce uffan
ba kamar yanda bai tanka mata ba har ta yi gaba abinta.
Murmushin ya ƙara yi gami da lasar lebbansa. Allah kadai
Yasan sirrin da ke cikin zuciyarsa. Ya sauke ajiyar zuciya
ya tashi motar ya fice.
***
Hajiya Zeenatu ta rausayar da kai ta ƙara duban Hajiya
Batool da ta saki baki tana kallonta, murmushi ta saki ta
ce.
"Kina mamaki ne?"
Hajiya Batool ta furzar.
"Kema ai kin san dole akwai mamaki Zeenatu, shi Hussein
din ne ya sauyamaki mota? Har ya ke tambayarki abinda
kike da buri a yanzu? Kuma ya amince da ku bar ƙasar
babu wata gardama? Anya kuwa Zeenatu ba wani tarkon
ya ke shiryamaki ba? Ƴan uwansa kuma sun yarda da
zamanku tare? Anya babu lauje cikin naɗi?"
Ɗaure fuska kaɗan Hajiya Zeenatu ta yi.
"Me kike son ki ce? Na fiki sanin Hussein, bai iya yaudara
ba. Ko a baya balle kuma a yanzu. Duk isar mutum bai isa
ya kawo mishi wargi ba balle ya yi ƙarya dominsa."
Hajiya Batool ta tsaya kawai tana yi mata kallon sakarya.
"Ke ba wannan ne damuwata ba, wasu shegun ƙuraje ne
suka fesomin a cinyoyina. Ba ƙaiƙayi balle zafi, su dai
gasunan ne kuma suna ɗurar ruwa."
Hajiya Zeenatu ta katse tunanin Batool, kusan ma katse
zancen ta yi don ba ta son ji.
"Ya kamata dai ki je asibiti. Tunda dai ko ba komai za ku
ci duniyarku da tsinke yanzun."
Suka sa dariya gami da cafkewa duk kuwa da cewar jikin
Hajiya Batool bai gama gasƙata sauyawar Hussein ba.
***
Tsaye suke a farfajiyar katafaren shagon na A&Z, Hisham
sai faman shan ice cream yake a roba yayinda Hussein ya
maida hankali ga danna waya. Tattaunawa suke yi game
da abinda ya ke son shiryawa akan Hajiya Zeenatu. Shi
Hisham ma duk haushi ya ke ba shi don haka ya ja guntun
tsaki.
"Kai nifa wallahi haushi ka ke ban idan kana zancen
matarnan. Ban taɓa zaton ko second ɗaya za ka iya
ƙarawa da ita a gida ɗaya ba. Ban zaci za ka ƙara wayar
gari ka gan ta kuma ka bar ta a gidanka ba. Da kunnenka
ka ji ita Halima na yimin rantsuwar cewa akwai sa hannun
matarnan a abinda ta aikata. Na ji, babu kwakkwarar hujja
mai ƙarfi da kotu za ta kama Hajiya Zeenatu da shi akan
hakan, amma kai kana da hujjojin da za ka iya ɗaukar
kowane mataki a kanta ba dole sai hukuma ba. Kafin na
furtamaka cewa Zeenatu ce ta sa Nos Khadija aikata kisa,
kai ka soma furtawa kuma ka sa na nemi gidan
yarinyarnan da kaina na nunamata hoton Zeenatu ta
tabbatarmin cewa ita ce. Me ya yi saura? Me kake jira
bayan komai ya fito fili."
Hussein ya yi murmushi gami da zaro hankicif a aljihu ya
miƙamasa.
"Goge bakinka, ya ɓaci."
Hisham ya harareshi kafin ya warce ya goge ice cream din
da ya ɓatamasa gefen baki tsabar masifa.
"Ba na abu kai tsaye, na fi kaunar komai da cikakken hujja
Hisham. Sannan ma tsaya, me kake nufi game da
Matata? Ina sonta fiye da yanda ta ke sona. Har abada ba
na jin akwai wani ko wata da ya isa ya raba ni da Zeenatu.
Zan iya yin komai don ganin na sanya ta farin ciki. Kar ka
damu da komai, komai da na fada ko kuma ya faru, ba
komai bane. Abinda zai faru a gaba shi ne abin kallo. Shi
ne abinda zai fi burgeka a lamarin soyayya."
Hisham ya bishi da kallon taɓaɓɓe, sai dai wacce ya gani
tsaye bayansa ta jikin gilashin motar Hussein, yasa ya
gano dalilin sauya maganar Hussein din. Shigowarta wurin
kenan daga gidan Hajiya Batool, a waje ta yi parking ta
ajiye motarta don ba jimawa za ta yi ba tana sauri ta
koma gida ta girkawa mijinta abinci, wani abun ta mance a
ɗazun dole ta dawo ɗauka.
Hussein wanda ya yi kamar bai ganta ba, ya ci gaba da
magana.
"Kar ka yarda da maganar mutane, Zeenatu ba za ta taɓa
kisa ba balle har ta sanya wani ko wata ya yi yunkurin yi.
Na fika saninta. Don haka duk wanda ya faɗamaka
Zeenatu ita ce silar shigar Ramlat wannan yanayi, karya
ce."
Wani gumi ta ji ya yankomata, ta yi saurin juyamusu baya
ta sharce. A hankali ta saita nutsuwarta kafin ta juyo ta
tako inda suke tana murmushi.
"Ah, ku na nan?"
Sai a sannan suka yi kamar lokacin suka ganta.
"Sannunki, yaushe ki ka zo?"
Ta maida duba ga Hisham tana jifansa da wani irin kallo
kafin ta maida ga Hussein.
"Yanzu na shigo, mantuwa nayi zan dauka. Sannu
abokinmu, ya gida?"
Hisham ya sauke ajiyar zuciya, dakyar ya ƙaƙalo murmushi
ya jefamata.
"Lafiya kalau Uwargidan Hussein."
Ta gyada kai.
"A gaida mutan gida."
"Za su ji."
Daga haka ta yi gaba, Hisham ya bi bayanta da harara.
Murmushi Hussein ya yi.
"Hararar fa?"
Tsaki Hisham ya ja.
"Kai dai ban san sadda ka koyi makirci ba."
Dariya kawai Hussein ya yi, shi kadai ya bar wa cikinsa
abinda ya ke shiryawa.
***
"Resigning?" Darakta ya maimaita da mamaki da kuma jin
wani irin karyewar zuciya. Cike da ladabi Hussein ya jinjina
kai.
"Yes Sir."
Kwata-kwata abin bai mishi dadi ba, samun mutum irin
Hussein da ya iya gudanar da kasuwanci da amana da
kuma ƙwarewa abu ne mai matuƙar wahala. Kwandala
idan ba ta Hussein ba ce ba zai taɓa ci ba kamar yanda
duk wani marar gaskiya da ha'inci, nan da nan ya ke
ganoshi kuma a take ya yanke masa hukunci kafin ya
sanarmasa.
Hussein bai katse tunanin Darakta ba don dama ya san
za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya, Darakta Sa'ad
mutum ne da ya ke kaunarsa kamar ɗan da ya haifa. Don
ma Hussein din bai fiye son shigewa mutane ba, da ya
tabbata zumuncinsa da Daraktansa sai ya fi haka.
"Meye uzurinka amma?"
Darakta ya tambaya ransa ba dadi. Murmushi sosai
Hussein ya yi yana jinjina wannan kaunar.
"Adamawa zan koma da zama, cikin dangina."
Da mamaki ya ce.
"Dama kai din ɗan Adamawa ne?"
"Eh."
"Ikon Allah."
A karshe dai suka yi magana mai tsawo kafin Darakta ya
dakatar da shi zuwa lokacin da zai samu wanda zai maye
gurbinsa. Da wannan suka ajiye magana.
***
"Wai nikam Alhaji na rasa gane kanka. Ban san me zai sa
zuciyarka ta sauka daga dokin fushin da ka hau ba."
Kawu Modibbo ya daure fuska sosai yana kallon Anti
Amarya.
"Me kike son ki ce?"
Anti Amarya ta sauke ajiyar zuciya.
"Ya dace ace zuwa yanzu ka watsar da makaman yaƙinka
kamar yanda ƴan uwanka suka watsar. Ya dace ace yanzu
gabar da ke tsakaninka da su Dada ya wuce. Ko maƙiyin
Dada ya kira ya tayata murnar ganin Hussein amma kai
kam na..."
"Ni kike faɗawa maganar banza da wofi?! Ke kinsan waye
ni kuwa? Idan har kina so ki tsira da mutuncinki da kuma
aurenki, ki yi gaggawar fita a idona! Wannan ne gargadi na
karshe da zan maki game da lamarin Amina da iyalinta. A
wurinki ki ke ganin komai ya wuce, amma ni har abada ba
zan taɓa bari wata alaƙata shiga tsakanin ni da yara da
ba'a san asalinsu ba! Aminu dai ya zo ya kawomana
karuwarsa ya kuma tafi ya bar munda bara gurmi a cikin
zuri'armu. Na ji! Amma ba wanda ya isa ya yi min dole
kan na karɓe su. Shi kuwa Tahir yau ko ni ko shi tunda ya
zaɓi zama da su a kaina! Zan nunamasa ni ne nan
ubansa!"
Kawu Modibbo na kai wa nan ya mike ya nufi ɗaki, ransa
idan ya yi dubu ya ɓaci, ga Bokansa ya tabbatar masa
babu sauran ƙofar da wani asiri zai shiga jikin Hussein da
sauri sai dai a sannu. Yanzun ya gama gane ba iyakar
tsana kawai ya yiwa zuri'arnan ba, har da bakin ciki da
kuma jin tsantsar hassadar yanda ba su rayu a wulakance
kamar yanda shi da Innarsa a baya suke fata ba. Sai ya
kasance koyaushe sai dai ya yi ta jin labarin nasarorinsu.
Ga dai yaransa nan amma kowanne da kalar shashancin
da ya sa gaba, kalilan ne a yaran suka kama dahir. Wato
dai suka yi karatu kuma su ke aiki, aikin da bai kai darajar
na AlHassan ba. Ko iyaka nan aka tsaya ya san za su yi
mishi dariya, abinda ba zai jure ba kenan.
***
"Ya akai ɗan uwa?" AlHassan ya fadi kai tsaye daga ɗayan
ɓarin. Hussein ya kara gyara zaman wayarsa duk kuwa da
cewar tuƙi ya ke yi.
"Lafiya, batun maganar da muka yi, yaushe za ka zo?"
Murmushi mai sauti AlHassan ya yi.
"Ai ka ji, dama sai da na ce maka ka yi hakuri mu taho
tare komai zai fi bada ma'ana, yanzu gashinan tun ba ka
tafasa ba za ka ƙone."
Hussein ya ɗan cire hannunsa saman sitiyari ya shafi
sumar kai yana murmushi kafin ya mayar.
"I'm sorry, ka san.."
"Ko ba ka faɗa ba na sani. Na san kuma dalilinka. Hakan
ma ya yi daidai. Fadamin, me ka zo ka tarar?"
Tiryan-tiryan ya ba shi labari, AlHassan ya yi dariya.
"Alhamdulillah. Wannan ma nasara ce. Zeenatu get
ready."
Suka ɗan taɓa hira abinsu suka yi sallama.
***
Da yammacin ranar juma'a, tana zaune saman kujera suna
hira da Baban Hanif, damuwa karara ta bayyana saman
fuskarsa.
"Mamin Affan, ban san dalili ba, amma gabana faduwa ya
ke, sai na ga kamar zan rasaki, sai naga kamar duk
wannan rawar ƙafartawa zai zama mafarki."
Ta ɗago kai da zummar ba shi amsa da ɗan murmushi
saman fuskarta, ya yi daidai da bude ƙaton kyauren gidan,
motar Hisham ce ta shigo sai dai a gefensa mai zaman
banza, Hussein ne.
Kauda idanu ta yi gami da danne bugun da kirjinta yake ba
tare da fuskarta ta nuna ba.
"Me zai sa ka fargaba? Akwai wani lamarin da ya fi karfin
addu'a? Komai na Allah ne."
Ya jinjina kai, har sannan bai ji zuciyarsa ta sake ba. Yana
son faɗamata sakamakon da binciken tarihinta ya ba
iyayensa amma ya danne a ransa har zuwa sadda zai
kammala nashi binciken ya gane gaskiyar lamari.
Daga cikin motar kuwa, Hisham ji ya yi wani murmushi ya
suɓuce masa, abinda ya fi dadi, ya ji na zuwan da ya yi da
Hussein gidannan. A farko Hussein bai yi niyyar zuwa ba,
sai dai kwadayin ladan da ke cikin ziyartar iyaye da ma
yan uwa da asibitoci a ranar juma'a yasa shi cewa su je
din. Sai da suka soma zuwa gidan iyayen Hisham din suka
ci abinci kafin su zo gaisuwar surukai kuma yan uwa a
wajensu yanzun. A farko Hussein gardama ya ke mishi kan
zuwa ziyartar Kawu Modibbo da Hisham ya ke so su yi a
ranar, sai dai shigowarsu gidan da mummunan tozalin da
ya yi ya sa shi yin ɗif har hakan ya ankarar da Hisham
shima ya kai idanunsa garesu.
"Muje ko?" Hisham ya katse tunaninsa yana kara nazartar
yanayin sauyawar fuskarsa. Babu annuri.
"No, shiga ka fito."
Dariya mai karfi ta kama Hisham sai dai dakyar ya haɗiye,
idanun Hussein din akan Baban Hanif yana son tuna inda
ya taɓa ganinsa.
"Ah, wai Hajiya Ramlatu kake kallo? Kai wai dama Haris
ne? Bari na je mu gaisa."
Hussein a sannan ne ya watsawa Hisham banzan kallo
kafin ya ja tsaki, kusan a tare suka fito daga motar. Baban
Hanif na ganinsu ya taso da fara'a ya karaso. Maimakon
Hussein ya tsaya kawai sai ya yi gaba yana shan murr ko
inda suke bai kalla ba. Baban Hanif ya bishi da ido sadda
hannunsa ke cikin na Hisham su na musabaha. Ramlat ta
dora kafa daya kan daya tana fitar da wani irin murmushi
mai kama da yaƙe. Sauyawar Hussein ya mugun kasheta
da ba ta mamaki.
"Ranki ya dade, girman kujerarki."
Sai a sannan ta sauke ƙafar ta gaida Hisham fuska a sake.
Daga bisani shima ya yi ciki.
Kusan mintuna sha biyar suka kwashe a cikin gidan kafin
Ramlat ta shigo. Kiciɓus suka yi a bakin ƙofar. Kallon da
ya watsamata ne yasa ta hadiye gaisuwar a fatar bakinta.
Ganin shi bai ba ta hanya ba kuma bai ce uffan ba yasa
cikin dakiya bayan ta saukar da kanta ta gaishe shi.
"Ba girin-girin ba dai, ta yi mai."
Ya fadi a sanyaye amma zafin maganar ya fi komai buga
zuciyarta. Ta dubeshi, ya kauda kai ya bi gefenta ya wuce.
Ta bi bayansa da kallo cikin rashin gane inda zancensa ya
dosa.
"Ah Hajajju, har kin gama taɗin?"
Ta juyo ta dubi Hisham tana murmushin hadiye damuwa.
"Har za ku wuce?"
"Eh kinsan da yake ba iyakar nan muka tsaya ba. Yau dai
ladan juma'ar muke kwadayi."
Ta jinjina kai.
"Allah Ya saka da alheri."
Ya amsa da amin. Wani wawan hon da Hussein ya yi sai
ya ba Hisham dariya.
"Kinga bari na tafi kafin na ba shi haushi ya koma
Adamawa a ƙasa."
Ta yi dariyar da ta tsaya a fatar baki. Hanya ta ba shi ya
wuce.
***
BANKWANA DA MASOYI....
KARFEN KAFA Chapter 67
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


"Na kasa gane kanka. Wai me ya sauyaka haka?"
Hussein wanda ke jin kirjinsa har wani zafi yake ya kasa
magana sai guntun tsaki da ya ja.
"Allah Ya kyauta. Amma idan har dagaske kana son
Ramlat toh ya kamata ace zuwa yanzu ka bada kai bori ya
hau. Bana son wannan zurfin cikinnaka alhalin ni na sani
wallahi ko mijinta na farko sai an yi dagaske zai kamo ka
a son da ka ke mata."
Nan ma dai shirun ya kara samu maimakon amsa, Hisham
dole ya ja baki ya yi shiru don ya soma jin haushi.
"Zamu je Yakasan?"
Ya tambaya bayan ya yi tuƙi mai ɗan tazara daga gidan su
Ramlat. Ajiyar zuciya ya saki ya dubeshi da jajayen idanun
da ɓacin rai ya rinar.
"Ba zan iyaba. Mu yi hakuri ko zuwa gobe ne, ba ta ɓaci
ba."
"Ok!" Yanda Hisham din ya amsa sai ya tabbatar da fushi
ne don haka ya yi ɗan murmushi.
"Ka yi hakuri."
Shima Hisham don ya rama sai ya shareshi, a karshe ma
ɗaya daga cikin waƙoƙin Breaker ya kunna mai suna So.
A hankali Hussein ya lumshe idanu yana sauraron waƙar,
wani abu ke ratsa zuciya da gangar jikinsa sai dai kuma
yana ji a jikinsa ba mai yiwuwa bane. Daga yau zai mishi
iyaka da zuciyar da gangar jikinsa har sai ya ga abinda
hali ya yi.
***
Hajiya Zeenatu ta ƙara buɗe zanin jikinta, fitowarta daga
banɗaki kenan. Hankalinta idan ya yi dubu ya tashi,
maimakon da ta soma shafa cream na ƙuraje da likita ya
ba ta, kurajen su mutu sai abin ya kara yin gaba. Don a
farko iyakar cinyarta ne kadai, yanzun kuwa har su na
kokarin dabaibaye dukkan wata gaɓa daga ƙugunta zuwa
ƙasa. Ta kuma lura da wani abu guda, ko yaya ruwan ya
taɓa jikin fatarta sai wani kurjin ya fito.
"Na shiga uku ni Zeena! Me zan gani?!"
Ta dora hannu a kai nan da nan idanunta suka fito ƙululu
kamar za ta yi kuka. Wato dai don bakin ciki cuta bai tashi
yi mata kamun kazar kurkuku ba sai da ta ke dab da more
rayuwarta da miji? Sai da komai ha daidaita babu tsafi
balle asiri?
Wani irin miƙewa da ta yi sai da zanin ya faɗi, ba ta bi ta
kai ba ta karasa sif na kayanta, doguwar riga ta sauya
hannunta har wani irin rawa ya ke yi, ta gwammace yau ta
je babban asibitin Malam ta ga likitan fata. Tana ji a jikinta
abin daga fatarta ne. Ba ta yi tunanin ciro waya ta kira
Hussein da zummar neman izni ba, sai da ta shiga mota,
koda ta fadamasa a dawo lafiya kawai ya ce daga nan bai
ƙara uffan ba, itama ba ta son ya kara don yanzu ta
lafiyarta ake. Babban tunaninta yanzu komai na tafiyarsu
London ya zama ready, ga samu ga rashi. Haka ta ke ji a
ranta.
***
Yau kwanaki biyu kenan da Yusufa ke zaryar gidan su
Ramlat sai dai ba ya samunta. A karshe dai ya nemi
lambar wayarta ya kira. Bayan sun gaisa ya yi kata
kwatancen ko waye shi. Jin ya ce shi ɗin ƙanin Halima ne
yasa ta maida hankali ga sauraronsa.
"Aunty maganar ba ta waya ba ce, saƙo ne daga Yaya
Halima, tun ba yau ba ta ban ta ce na isar gareki. Na so
ajiyewa wurin Maigadin gidanku amma kuma bana so ya
kasance bai isa hannunki ba."
Da mamaki Ramlat ta gyara zama saman kujerar Office
din.
"Kana ji? Ko zan maka kwatancen ofishin da nake aiki sai
ka kawomin."
Cikin zumudin hakan ya amsa da toh ya kuma yi mata
godiya.
Wuraren karfe biyar da mintoci na yamma sai ga Yusufa.
Da kanta ta fita suka gaisa, sau ɗaya ta taɓa ganinsa,
rashin lafiyar Kakar Halimar da ya tashi suka je dubiya
asibiti daga tsohuwar ma'aikatarta. Suka gaisa kafin ya
ciro takarda a ninke ya miƙa mata.
"Ki yi hakuri wallahi saƙonnan ya fi sati a hannuna,
rasuwar Kakarmu ce ta sanya ban kawomaki ba sai
yanzun. "
Cike da jimami ta ce.
"Kaka ta rasu? Allahu Akbar, Allah Ya yi mata rahma. Yasa
aljanna makoma. "
Yusufa ya amsa da amin. Daga haka suka yi sallama
bayan ta mishi ihsani.
Kasancewar an kusan tashinsu daga aiki yasa kawai ta
jefa a jakarta.
Ba ita ta samu damar warware takardar ta karanta ba sai
bayan Magriba. Lokacin ta samu nutsuwar wanka har ma
da na cin abinci. Ga abinda ta kuntsa.
_*Assalamu alaikum Ramlat.*_
_*Da farko zan soma da ba ki hakuri, haƙiƙa na sani ni
Halima ban cancanci komai daga gareki ba ballantana har
ki yafemin. Sai dai duk da haka ina mai nadama da dana
sanin abinda na aikata gareki. Ni mai laifi ce, ina neman
gafararki Ramlat. Hassada da son abin duniya irin nawa ya
kai ni ya baro. Yau ganinan a gidan da ko a mafarki ban
taɓa zaton zuwansa ba.*_
_*Na aikata bisa tursasawar Hajiya Zeenatu da kawarta
Hajiya Batulu. Duk irin tsanar da na yi maki ba zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login