Showing 84001 words to 87000 words out of 113545 words

Chapter 29 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

prove it."
Ta lumshe idanu tana shaƙar kamshin lemon mint da
bakinsa ke yi. A hankali kuma ta yi nufin yin baya ya rike
kanta kafin ba zato ta ji bakinsa a nata. Shirun kusan
mintuna biyu kafin ta tureshi ya yi baya, babu kwari a
jikinsa, don haka ya jinginar da kai yana kallonta da
soyayyun idanunsa. Ita kuwa sai afkin goge baki da ta ke
yi bayan ta zari tissue dake saman gaban motar. Ya kauda
kai kadan yana dariyarnan irin na wanda aka rainawa
wayau.
"Kai, ni kike gogewa baki don na taɓashi?"
Ta daure fuska ta harareshi.
"Saboda ban shiryawa hakan ba. Ai ba haka tsarin
zamantakewar tamu ya ke ba."
Daga nan ta wurga tissue din a jikin motar duk dacewar
hatta da kujerun baa ciremusu ledojinsu ba. Tana kokarin
bude kofar ta fita ya kara yi mata wata wawuyar fisga, duk
kokarinta ta kwace abin ya gagara. Haka ya taramata
miyansa a baki kamar yanda bai kauda bakin ba sai da ya
ji ƙarar tafiyarsa, loko da saƙo sai da ya tabbatar ya
gauraye a bakin kafin ya saketa. Iyakar shaƙa ta shaƙa, ta
bankamasa wata hararar. Ya ɗaga mata yatsu.
"Good night Love."
Ta bude kofar kawai ta fice, ya bita da kallo yana jin
kamar kar ta tafi saboda wani tsananin kewa da ya
kamashi nan take, har sai da ta shige gidan kafin ya
lumshe ido da murmushi can kuma ya buga sitayari.
"Ya Rabb!" Ya fadi cike da nishadi, soyayyar Ramlat na
kara ƙaimi a ransa. Dakyar ya samu kuzarin jan motarsa,
kafin ya fice daga gidan ma sai da ya kira wayar Hafsat ya
jaddada mata akan ta shaidawa Ramlat ta kunna wayarta.
Kusan gaba daya mutan dakin bacci suke yi idan ka cire
Amrah da ke zaune tare da amniyarta tana tayata wajen
shirya kaya a ƙatuwar akwati. Wasu kayayyakin kuwa su
na fitarwa domin bayarwa. Amrah na lura da yanda gaba
daya ba ta da sukuni, jefi-jefi takan sa hannu ta share
bakinta.
"Wai ke kam lafiyarki kuwa?"
Ta dawo hayyacinta.
"Me kika gani?"
Harara ta watsamata.
"Kamar ya me na gani? Alhalin ina lura da yanda tun dazu
kike wani shagala da shafa baki, saurin me kike?"
Ranta ya kara baci ta ja tsaki.
"Me kike nufi? Idan ma wani abin kike nufi gwara ki
watsar tun a nan don kinsan irin zaman da na shirya za yi
da Hussein."
Amrah ta jinjina kai.
"Ko wane irin zama ne ba zan hanaki ba tunda ke ba
yarinya karama ba ce da zan tsaya ɓata bakina, abu daya
da zan tunasar da ke, yanzu Hussein ya tashi a kowane
matsayi ya hau matsayin mijinki. Idan kin gyara kanki, idan
kin ɓata ma ke za ta shafa."
Shiru kawai Ramlat ta yi ba ta kara tankawa ba. Can kuma
aka kwankwasa kofar dakin da sallama aka shigo. Hafsat
ce sanye da riga da wando na bacci kasancewar ita ta
kafe ta ƙi bin yan uwansu Hotel, hakan yasa Hajiya ta
mata wuri a makeken gadonta. Hamma ta ke zabgawa
duk suka dubeta.
"Adda wannan Yayannamu ya hana ni bacci wallahi, don
Allah ki tausayamin ki kunna wayarki ku yi magana. Ni ga
wayata ma na bar maki a nan don wallahi da zarar na
soma nisa a baccin yake tashi na."
Dariya ta ba su, aikuwa ba wanda ya kai ga cewa komai
sai ga wani kiran. Da sauri Hafsat ta miƙamata.
"Yauwa gashinan. Sai da safe."
Ta fice Amrah na addu'ar Allah Ya tashemu lafiya. Ita
kuwa Ramlat wayar ta ɗaga ta ɗora bisa kunne yayinda
Amrah ta juyamata baya ta ci gaba da aikin da tuni ma
sun ƙarƙare sai tattarawa. Sallama ta yi, jin muryarta sai
ya sauke ajiyar zuciya. Shiru ya dan biyo baya kafin ya
tanka.
"Kin hana ni bacci Heart."
Ta ɗan saci kallon Amrah wacce hankalinta na can wurin
harhaɗe kaya ba ta ce masa komai ba.
"Meyasa ba ki kunna wayarki ba? Kinsan zan nemeki, zan
so na ji muryarki. Bacci ya kauracemin, ba ni da burin da
ya wuce na ganki a gidana. Heart, kin yi shiru."
Ta ɗan daure ta yi magana.
"Me zan ce?"
"Ko mene ne ki fada daidai ne. Amma kar ki kara kuskuren
da ki ka yi dazu, idan kuwa hakan za ki ci gaba a
zamantakewarmu, za ki sha wahala a wurina."
Murmushi ta yi mai sauti.
"Dariya ma na ba ki?"
"Ko kusa, bacci fa nake ji."
"Ni kuma ban shiryamasa ba, hira na ke son mu yi. Koda
dai tambayar da nake son yi maki ba ta waya ba ce, sai
mun haɗu ga ni ga ki."
Nan ma ba amsa sai shirun daga wajenta, har Amrah ta
mike ta fada bandaki ta dauro alwala, yana ta magana
Ramlat sai uhm ko uhm uhm. Tana kallo Amrah ta kashe
fitilar dakin ta bi lafiyar gado kusa da Babynta ta kwanta.
Cikin takaici Ramlat ta ce.
"Malam kowa fa ya kwanta, nima gyangyaɗi nake, ina
son..."
"Be serious Heart, ko kadan ba ki tunanina?"
Ta lumshe ido ba tare da ta tanka ba.
"Talk."
Ya fadi a hankali. Ita har mamaki ma ya ke ba ta.
"Shiru ma fa magana ce ko? Inji Hausawa."
Ya kara fadi yana yar dariya, ta cije lebba don takaici,
wato ma ya riga da ya fassarata.
"Kai ka san wannan, ni abinda ya tsayar da ni daban ne.
Sai da safe bacci nake ji."
Ba ta jira komai ba ta kashe wayar gaba daya. Mikewa ta
yi tana murmushi har ta na tuntube da ƙafar Dijen Daura
da ke bacci a saman katifa. Hakuri ta ba ta sannan ta fada
toilet. Alwalar itama ta yi ta nemi wurin kwanciya.
***
Tun da Asuba masu tafiya Adamawa suka tashi ba'a
koma ba. Daga mai wanka sai mai sanya kaya, wasu kuwa
da ba za su sami zuwan ba, sai suka fada kicin don yin
abin kari. Ramlat dake bacci sakamkon tana fashin sallah,
dolenta ta wartsake don ba karamin takuramata su
Rafee'ah suka yi ba akan ta mike ta yi wanka. Bayan ta fito
ta shirya cikin atamfar Holland kalar light blue da fari, ta
yafa farin mayafi sannan ta fita wurin yaranta. Ta dauka za
ta gansu cikin damuwar tafiyarta sai dai da sauki
musamman ga Ummi da Ansar wadanda suka shaku sosai
da Hajiya. Affan ne ma ya dan yi wuri-wuri da idanu da ya
tabbatar dagasken tafiyar Maminsa za ta yi. Itama
dannewa kawai ta ke amma tsananin kewarsu ta ke ji tun
kan a je ko'ina. Kiran da Hajiya ta mata ne yasa ta lallaɓa
Affan da ya kanainaye a jikinta ta fita. Can ƙuryar daki ta
isketa. Ba ita kadai ba ce har da Umman Amrah da ta
shigo tun sassafe da kuma su Baba Hajara da sauransu.
Nasiha sosai suka yi mata, Hajiya a karshe ta tofa da
cewar sun gama magana. Ta yiwa Ramlat addu'a kawai.
Ita kuwa banda afkin kuka ba abinda ta ke fitarwa.
Iyayenta masu sonta da komai, a baya ta bijirewa saboda
son zuciyarta. Nan ta bude baki ta na mai kara neman
gafararsu akan abinda ta aikata a baya. Murmushi suka yi.
"Banda abin Ramlatu, ai kowa ya fahimci kaddara. Ba
komai kedai komai ya wuce sai da kawai yanzu ki maida
hankali wurin biyayya ga mijinki."
Wata Gwaggonta daga Daura ta fadi.
***
ADAMAWA...
Hajiya Zeenatu hakanan ta ji faduwar gaba, shigar da
Hussein ya yi da irin fara'arsa sai ta soma wani tunani
daban. Ganinsa ta ke yi kamar wani Ango. Ya kammala
ɗora agogon hannunsa bayan ya idar da sallah, murmushi
ya ke tun sadda suka yi magana da Hafsat ta
tabbatarmasa da isowarsu garin su ma. Dama habyar da
ya biyo daban da tasu.
"Hussein."
Jin ta kira sunansa kai tsaye yasa shi dubanta.
"Duk wannan fara'ar ta mecece? Wani kyau ka yi kamar
wani Ango. Gabana faduwa ya ke yi. Yaushe za mu je ka
kaini mu gaisa da danginka?"
Ya yi wani banzan murmushi ya rike kafadunta.
"Kar ki damu, kin ga yau daurin auren yar uwata ake yi, ke
kuma na sanki ba kya son cunkuso da wani hayaniya, ki yi
hakuri gobe zamu shiga ku gaisa da kowa. Kallon banza
aka yi maki Hussein ba zai rabu da mai shi ba. Sannan
kina batun wai Ango, na dauka kodayaushe ni Ango nake
a wurinki? Toh ki kwantar da hankalinki, babu macen da ta
ishe ni kallo har naji ina sonta. Ke kinsan yanda nake."
Yanayin da ya furta kalmar karshen kawai sai ta kara shan
jinin jikinta, ga wayarta ta rasa ya aka yi ta fada ruwa balle
ta tambayi Kawu Modibbo ko akwai wani labari, yanzun
dai ta ƙi tashi Hussein kuma ya karɓe ya ce zai siyomata
wata da kansa. Abinda ba ta sani ba, da gayya ya
tankwaɓar da ƙaton jug na ruwan dake saman centre
table, burinsa dama ta rasa hanyar jin kowane labari.
Bai bar gidan ba sai da ya tabbatar ya kwantar mata da
hankali, har cewa ya yi ta dauko mayafi su fita tunda
hankalinta bai kwanta ba, soyayyar Hussein da ganin
tsantsar gaskiyarsa a yanzu ta rufemata ido ta yanda ba ta
tuna komai da kowa, hakan yasa ta kasa hasaso wani abin
musamman ma da ta ga ta fito falon Kausar na mishi
batun bikin da ake yi. Hankalinta ya kara kwanciya bayan
fitar Hussein din da Kausar ta shiga budomata hotunan
auren da ake yi tana kallo tana ƙara jin sanyi a ranta. Ta
na kuma kara tabbatarwa zuri'arsu Hussein kyawawa ne
tsantsa.
***
Bangaren Marigayi Baba Naziru wanda ya sha gyara da
fenti daga AlHassan, nan aka kai Ramlat kafin lokacin da
Hussein zai yi gininsa. A sannan yan uwanta suka hau
aikin jere da ma sauran abinda duk ya kamata. A ranar
daga su sai su, an kawomusu abinci da abubuwan sha.
Da daddare suna zaune ana hira, wayarta ta yi kara,
Mr.Wuff. Murmushi ta yi ta dan mike ta bar wurin zuwa
can wani dakin da ta tabbatar babu kowa ciki.
"Assalamu alaikum." Ta furta a hankali.
"Waalaikumussalam. Fatan an iso lafiya?"
Ta dan lumshe ido kafin ta bude tana bin dakin da kallo,
shima gado ne aka shimfida a dakin, don wannan karon
gatan da ta samu har gado biyu aka yi mata.
"Alhamdulillah."
Shiru kamar ba wanda zai tanka can kuma ya ce.
"Kin shiryawa abinda zai biyo bayan aurenmu?"
Ta ji maganar banbarakwai.
"Kamar ya?"
Murmushi ya yi mai sauti.
"Za ki haɗu da Uwargidana mana."
Ranta ya sosu matuka, kishi mai zafi na Zeenatu ya
mamaye koina na zuciyarta.
"Ina ruwana da ita? Zamana da nata ba iri guda ba ne. Ko
ba komai ita ai auren soyayya aka yi kamar a cinye juna."
"Sai aka fadamaki kema ba zan iya cinyekin ba? Wai
meyasa kike son koyaushe ki nunan babu soyayya
tsakaninmu? Dama akwai soyayyar da ta girmi aure?"
Ta kasa ba shi amsa don har lokacin kiran Zeenatu da
uwargidansa da ya yi yana mata zafi, ta rasa rashin zuciya
irinta Hussein da ya iya rayuwa da matar da ta rushe
dukkan wani tubalin ginin rayuwarsa saboda son zuciyarta.
"Shiru ki ka yi?" Ya tambaya.
Ta dan turo baki kamar yana ganinta.
"Bani da abin cewa."
"Saboda kin san ba ki da gaskiya ne kawai. Na dai
fadamaki, ki shiryawa hakan. Tsoro ba naki ba ne, dama
na riga da nasan ke jaruma ce. Amma ban sani ba ko har
a fannin kishiya."
"Wanda aka damu da shi ne ake kishinsa, tunda ba na
kishinka me zai dameni da matarka? Don haka kar ka
samu damuwa, ita dai za ka yiwa wannan kashedin. Zan
kwanta sai da safe."
Ta katse kiran ranta a tsananin ɓace. Me Hussein ya gani
a tattare da Zeenatu har yake mata son da ba zai iya
rabuwa da ita ba wai? Ita ta rasa dalilin da yasa duk laifin
da ta yi masa ba ya ganin ko ɗaya. Wato har shaidamata
yake ta shiryawa haɗuwarta da ita saboda ya san ba zai yi
kyau ba.
Ramlat ta yi kwafa, ta mike da zummar barin dakin sai ga
saƙonsa ya shigo.
"Kashe waya ba shi zai sauya zancena ba, ba kuma zai
hana na faɗi ba. Ki shiryawa haɗuwarki da Uwargidana.
Anan za ki gane so da kuma ƙiyayya."
Ta harari wayar tana jin kamar shi din ta harara, sai kuma
takaici yasa idanunta cikowa da kwalla ta yi azamar
daukesu ba ta bari sun zuba ba. Daga nan ta ja tsaki ta
fice daga ɗakin.
***
Washegari da safe suka gudanar da shagali irin na
al'adarsu da suke kira Fansa, inda dangin Ango ke kawo
kayan abin ci da sha ga dangin Amarya ba tare da sun ga
Amarya ba.
Da yammaci aka hau shirye-shiryen buɗar kai. Maryam
Sambo (Cutie) ta fente fuskar Amarya da kwalliya wanda
ya fi na ranar daurin aure. Maganar kyau ma na Ramlat ba
sai an tsaya ana ɓata baki wurin faɗa ba. Ta yi kyau iyakar
kyau, ga ta nan dai ba farar mace ba, amma Allah Ya
mata baiwarSa a halittarta. Wannan karon ma Leshi ne
golden cikin kayan da Hussein ya bata ta sanya an mata
dinkin gown. Bilkisu dai gaba daya sai ta kara raina kanta,
bakin ciki kuwa kamar ya kasheta. Ba ta taba zaton family
din da Ramlat za ta shiga su na da wannan kuɗin ba.
Hatta da muhallin Ramlatun, ya ci a kalla a ƙara kalla duk
kuwa da cewar tsohon gini ne sai dai ya yi tsari sosai.
KARFEN KAFA Chapter 72
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


Gaba daya suka fita katon rumfar da aka tanada a babban
filin tsakar gidan gadon na Marigayi Alhaji Gidado. An
lulluɓe jikinta gaba daya da turmin zanin atamfa yanda ko
fuskarta ba'a gani.
Nan kuma dangin su Hussein aka shiga fansar fuskar
Amarya, Dada nan take da ba da Dubu ɗari na fansa, haka
nan ma yan uwansu na Mubi da Maiduguri kowa ya shiga
kawo nasa. Amrah ce gwanar faɗin nawa Amarya ta
samu. Ita dai Ramlat na ƙunshe tana murmushi a ƙasan
zanin don al'adar tasu ta burgeta matuka sai dai da zarar
ta tuno batun haɗuwarta da Hajiya Zeenatu da Hussein ya
yi sai jikinta ya yi sanyi sai dai kuma ta tabbatar addu'a ne
maganin komai.
Hafsat a matsayinta na ƙanwar Ango ita ta mike don
zaɓawa Amarya suna, a karshe ta radamata suna Amal.
Sunan da kafatanin dangin za su dinga kiranta da shi
kenan. Bayan an kammala aka kwashesu zuwa gida.
Da daddare ana zaune gaba daya ana hirar bankwana.
"Amal."
Suka yi dariya gaba daya jin sunan da Amrah ke kiran
Ramlatun. Ita kam tasan kafin ta saba da sunan za'a jima.
Anan wata ma ke tambayar Kishiyar Ramlat.
"An cemin tana nan amma ban ganta ba."
"Anya ta zo Adamawa? Ina ji fa a Kano za ta zauna ita."
Cewar Rafee'ah.
"Ta huta. Zama da dangin miji gari daya ai sai tsautsayi."
Babu wanda bai kalli Bilkisu ba, ita kuwa sai karkade kafa
ta ke don dama da biyu ta yi maganar tana jira a tanka.
Umman Amrah ce ta hana kowa magana karshe ma aka
maida hankali ga hirar bikin yanda ya yi kyau.
Koda za ta kwanta tana ganin kiran Hussein ta ƙi ɗagawa
don ba ƙaramin haushi ya ba ta ba. Karshe ma ta katse
wayar.
***
A bangaren Hussein sam bai samu ya fita ko'ina da Hajiya
Zeenatu ba sai a washegarin bikin bayan dangin Ramlatu
sun kama hanyar Kano, ya zo tare da su AlHassan, Kausar
da ɗiyarsa. Har yanzu akwai yan Maiduguri da Mubi
wadanda ba su kai ga tafiya ba sakamakon dakatar da su
daga yin hakan a Hussein ya yi, kowannensu na da labarin
Hajiya Zeenatu, sai dai ba su ji cikakken ba sai yanzun da
suke burin ji. Falon a cike yake, tun da ta ji suna juya
harshe, wasu fulatanci wasu kuma yaren barbanci. Bayan
an gaisa Hussein ya gabatar musu da ita sai kuma kai
tsaye suka nufi ɗaya falon na Dada, babu cunkoson
mutane kamar na farkon. Dada ta ƙuramata idanu, kusan
koda ta girmemata ba da shekaru masu dumbin yawa ba.
Suka gaisa da mutanen dakin, ita dai Hajiya Zeenatu an
gaisa amma ba ta gamsu da kallon da kowanne ke
bibiyarta da shi ba. Anti Amarya matar Kawu Modibbo
itama gidan ta sauka, wannan karon dai Modibbo bai
hanata ba, da biyu ya bar ta ta je don ya gama shan jinin
jikinsa, yakan kirata akai-akai ya ji ko ana wani abin. Ita
har mamakinsa ma ta dinga ji, ta kuma soma wani
tunanin.
'Yanzu wannan ce azzalumar matar da ta raba ni da
ɗana?'
Dada ta faɗi a ƙasan ranta, nan da nan tsanar Hajiya
Zeenatu ya kara cika zuciyarta.
"Amm..Dada. Hafsat ba ta nan ne?"
Dada ta dubi Hussein, alama ya yi mata da ido akan kar ta
nuna wani abu. Ta yi dan murmushin yaƙe.
"Ta shiga wurin Amarya saboda kowa ya watse, kar a bar
ta ta yi zaman kaɗaici."
Hajiya Zeenatu dai ba ta ce uffan ba amma a ranta tana
ta tunanin dama Dadar ba ita kadai ce wurin mijinta ba?
"Zeenatu."
Muryar wata mata ta ji, daidai sadda ta juya ta dubeta.
Zumbur ta mike ido waje ta ke dubanta.
"Hajiya Binta?"
Hajiya Binta mahaifiya ga Rasheed ya karaso tana
murmushi. Hajiya Zeenatu ta dan saki jiki ta karasa suka
rungume juna amma gaba ɗaya jikinta ya yi wata irin
mutuwa. Ta dago ta dubeta.
"Yaushe kika zo ƙasarnan? Me kike yi a nan?"
Yanda ta yi tambayar a mamakince yasa Hajiya Binta
murmushi tana kara hadiye mamakinta, don koda ta ji
labarin duk abinda ke faruwa har kuka ta yi don tausayawa
Hussein. Ita ta ba Hussein dukkan shawara akan ya ɓoye
dukkan batun aurensa da Ramlatu gareta don ta san
komai na daga shaiɗancin Hajiya Zeenatu.
"Ina nan tun sadda Allah Ya bayyanamana Husseini. Ko kin
manta amintarsu da Rasheed?"
Ta gyada kai tana yaƙe.
"Ban mance ba. Rasheed din yana nan shima?"
"Eh yana nan, ya dan fita ne ma, yanzu za ki gan shi ya
dawo."
"Ok." Shi ne kawai abinda Hajiya Zeenatu ta iya faɗa
kenan jikin a matuƙar sanyaye.
"Dama kun san juna?"
Dada ta jefo tambayar ga Hajiya Zeenatu.
"Eh, Ƙawata ce."
Ta amsa a dake, saura kaɗan dariya ta suɓucewa Kausar,
AlHassan ya sa ƙafa ya ɗan taka ta don ta gimtse.
"Bayan an zauna sai Hussein ya fidda waya. Hafsat ya kira
ya ce ta taho sashin Dada tare da Amal. Hakan da ya fadi
yasa ta fahimtar komai, don haka da toh kawai ta amsa.
***
Ramlat da tun soma wayar Hafsat ta kafeta da ido.
"Hamma Hussein ya ce mu je."
Ta gyada kai, ta yi wankanta ta ci ado da wata shadda da
aka yi mata dinkin doguwar riga ya sha aiki. Ta cakare
ɗaurin ɗankwali don Ramlat ba baya ba. Ta ɗora mayafi a
saman kayan ta zura takalmi suka fita tare. Hakanan ta ji
gabanta na bugu da sauri-sauri, ta kara kallon Hafsat
wacce ke wani zumudin suna tafiya sai janta da hira take
amma ba ta fadi dalilin wannan rawar ƙafar ba.
A ƙofar falon farko suka yi sallama, kunya sosai ya kama
Ramlat don ba ta zaci ganin sauran jama'a ba. Ta durkusa
a kunyace ta gaishesu. Cike da fara'a aka amsa, nan
kuma wata tsohuwa ta ɗauki guɗa da biyu. Jin haka daga
cikin dakin, sai ga Kausar ta leƙo, Hafsat na ganinta ta
tsallaka.
"Adda, dagaske ta zo?"
Hafsat ta tambaya da raɗa-raɗa, Kausar ta yi dariya ta
nuna ƙofar falon.
"Tana ciki."
Hafsat ta harari ƙofar.
"Makira, yau ƙarshenta ai ya zo."
Suka yu dariya sabida duk da harshen fillanci suke
maganar, Ramlat ta karaso.
"Muje ko?"
Sai kuma ganin Kausar suka shiga gaisawa, wasu mutan
falon duk sun mike sun biyo baya don ba su kaunar abinda
za'a yi ya kasance babu su.
Gaba ɗaya ana zazzaune har Hajiya Zeenatu da ta soma
sakewa ganin Hajiya Binta har su na hira. Tana so ta
tambayeta yanda su Dada suka ɗauketa amma babu dama
tunda ba su keɓe ba. Ba su kadai ne a falon ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login