Showing 9001 words to 12000 words out of 113545 words
Chapter 4 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt
mata ya shigo
bayansa daya daga cikin ma'aikatansa ne rike da jakarsa.
Kallonta ya yi sannan ya shige ciki bayan a ladabce ta
mishi barka da zuwa.
Jimawa kaɗan ya kira wayar dake saman teburinta, ta
mike ta shiga ciki tana kara gyara zaman ƙaton hijabinta
don ta yiwa kanta alkawarin ba za ta ƙara sanya mayafi ta
zo aiki ba ko don tseratar da kanta daga sharrin
Chairman. Idan ma wancan karon wani abin ya hango,
wannan karon sai dai ya gama baza idanun ya haƙure.
Abinda ba ta sani ba shi ne, tafiyarta kaɗai ma abin ɗaukar
hankali ne.
Yana zaune ya na waya, ta shiga da sallama bayan ta
kwankwasa ya mata iznin shigowa. Tana tsaye har ya
kammala wayar wannan mayun idanunnasa yana kan
fuskarta kamar ya cinyeta. Ta yi tsaki ya fi a ƙirga a ƙasan
ranta.
"Malama Ramlatu, have a seat."
Abin ya mata banbarakwai namiji da suna Hajara, ta zauna
a ɗarare. Bayani ya shiga koromata akan abinda ya shafi
aikinta, ita dai kai take gyaɗawa a ladabce tana amsa da
kuma fadin za ta kiyaye. Abu ne da Staff Officer ya gama
shaidamata, ba ta ga dalilin da a karo na biyu zai
maimaita ba, a ganinta don hira ne kawai.
Bayan ya kammala ya ce.
"Ba ki yi mamakin dalilin da yasa kika dawo ƙarƙashina
ba?"
Sai lokacin ta dubeshi, ta yi saurin kauda kanta don ba ta
kaunar wannan shegen kallon ƙurillar da yake jifanta da
shi. Kallo na ƴan duniya.
"Aiki ba inda ba ya kai mutum."
Abinda ta ce kenan kawai. Ya yi baya ya kwantar da kai
jikin kujera yana ƴar dariya.
"Hakane kuma. Har kin kara burgeni, da alama kina da
kyautata zato. Nayi tsammanin za ki firgita ganin
kusancina da Hajiya Zeenatu."
Fadin hakan yasa gabanta ya fadi, ta dubeshi cikin dakiya.
"Ko kusa, ai mutum bai isa yi maka abinda Allah bai yi
ba."
Maimakon ta ba shi haushi matsayinsa na shugabanta, sai
ta burgeshi ainun, ya kara jin kamar wani magnet na
fisgarsa zuwa gareta. Ba ya so ya yaɗa manufarsa da
wuri, don haka cikin dakiya ya sallameta bayan ya ba ta
umarnin duk wanda ya zo idan har staff ne ba ya buƙatar
ganinsa. Da wannan ta amsa sannan ta fice daga ofis din
don dama abinda ta ke jira kenan.
Bayan fitarta Chairman Aliyu Dikko ya runtse idanu ya ɗan
bugi tebur yana murmushi.
"Wannan ita ce daidai da ni, ita ce kalata."
Ya fadi a fili cike da jin wani nishadi. Abu na farko da zai
soma siye zuciyarta da shi, shi ne kyauta. Zai yi komai da
zai sa ta saki jikinta da shi ta kuma daina yi mishi kallon
banza. Idan har hakan ta faru shi zai san yanda zai yi ya
shawo kanta.
Da wannan ƙudurin ya ji wani sauki daga abinda ke cinsa
duk akan Ramlat.
***
Ruwa ake tamkar da bakin ƙwarya, tana tsaye gefen titin
da babu yawaitar ababen hawa sai tsilli-tsilli, kamar ta yi
kuka haka take ji don tsabar baƙin ciki. Ace motarka ba ta
tashi ɓaci ba sai a wannan lokacin? Ta dauki duk abinda
yake da muhimmanci ta fito bayan tsagaitawar ruwan
hannunta rike da lema. Sai da ta buɗeshi kafin ta rufa
jikinta. Ta dauki jakarta ta rufe dukkan gilasai da kuma
motar. Nan kuma ɗan sahu ya yi mata wuyar samu. Tsaki
ta ja ya fi a ƙirga, ranar Asabar din ƙarshe wata ne, daga
gidan Rafee'ah ta ke nan kan titin Rijiyar Zaki. Ba don ta
riga ta yi mata sallama ba ta fito, kuma daga titi zuwa
lungun gida Rafee'ah akwai tazara sosai, da babu abinda
zai hanata juyawa ta koma.
Daidai sadda wata baƙar Ford ta wuce ta a guje, a
hankali kuma mai motar ya yo baya har zuwa gabanta. Ta
kalli motar ta kauda kai, za ta yi gaba ne ya sauke gilas.
"Assalamu alaiki."
Juyowa ta yi ta dubeshi, sanye cikin baƙar rigar sanyi
marar nauyi, hular rigar mai igiya biyu kwance a baya
wuyansa, duka duka tsawon hannun rigar iyakar
damtsensa ne wannan ne ya bada damar bayyanar
murɗaɗɗun hannuwansa masu zubin ƙarfin, tsintsiyar
hannunsa daure da agogon fata baƙi sai zobunan
azurfarsa da ba ya rabo da su.
Ta tsinci kanta da maida mishi martanin murmushin tana
mai amsa sallamar. Ba ta taɓa tsammanin ganinsa a
wannan lokacin ba.
"Motar ce ta samu matsala?"
Maimakon ta yi magana sai ta ji kamar an ɗaure bakinta,
hakan ya sa ta gyaɗa kai. Ya ɗan dubi sararin samaniya
har ruwa na ɗigarmasa a saman karan hanci.
"Gashinan kuma ina tsoron ruwa balle na fara gwada aikin
kanikanci a kan motarki. Shigo na kai ki."
Turus ta yi, kamar ta ce a'a, maganganun da suka yi da
Amrah ya faɗomata a rai, ta zagaya ta shiga sannan ta
zuge lemarta, za ta ajiye a ƙasa wurin kafarta ya karɓa ya
cilla baya. Ta rufe ƙofar ta dubeshi.
"Nagode."
Ya ja motar yana murmushi.
"Rike godiyarki ki fatan Allah Ya kaimu lafiya tukunna."
Murmushin itama ta yi.
'Matsoraci mijin hajiya.'
Duk a zatonta a zuciya ta fadi, sai ji ta yi ya yi wata dariya
kafin ya ce.
"Hajiyar da na yi wuff da ita ko?"
Da sauri ta dubeshi duk sai ta ji kunya ya kamata ta hau
kame-kame.
"Lah ni wallahi ban ce ba. Me ma nace? Me wai ka ji na
fada? Don Allah I'm sorry."
Ya kannemata ido ɗaya yana murmushi kafin ya maida
idanunsa saman titi.
"Alright, naji ba ki ce komai ba. Ni dama ban ce kin fadi
ba duk kika wani tsargu kanki. Kin dai kirani da Your Heart
ko?"
Wannan karon ji ta yi inama yana da halin buɗe motar ta yi
ficewarta.
KARFEN KAFA Chapter 44
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
"Shiru?"
Ta maida kai ga kallon gilas duk ta rude.
"Ramlat."
Ya Rabb, tamkar wani balarabe haka ta ji sunan ya fito
raɗau a bakinsa. Ba ta san sadda ta juyo ta kalleshi ba.
Hankalinsa na kan tuƙi, hanyar da ya ɗauka bai mata
kama da inda ta nufa ba, asalima miƙa wa cikin rijiyar zaki
kawai ya ke.
"Ina zamu je?"
Ta fadi murya na rawa. Murmushi ya ɗan yi.
"Siyar da ke zan yi, ko ba komai hankalin Madam zai
kwanta."
Abin sai ya bata dariya, ta yi murmushi mai sauti gami da
lumshe ido ta budesu.
"Nikam ba zan siyu ba."
"Really?" Ya furta gami da ɗan ɗaga gira yana jifanta da
wani irin kallo. Cikin dakiya ta amsa.
"Kwarai ma kuwa, idan ka siyar da ni ba wanda zai
kyaleka."
Ya yi ƴar dariya.
"Kuma sai ya kasance ba wanda ya ga shigowarki
motata."
"Amma ba ka daga cikin marasa imani, ba ka yi kama da
ɗaya ba. Ina kyautata maka zato."
Bai ce komai ba banda murmushi irin wanda har fararen
haƙoransa suka bayyana. Hannu ya kai ya kunna music,
waƙa ce ta yabon Annabi s.a.w da harshen larabci na
Maher Zain mai taken Ya Nabi Salam Alayka. Shiru ta yi
duk da ba jin larabcin ta ke ba amma yabon yana ratsata
sosai, muryar Hussein mai bin waƙar ya fiye mata muryar
mawaƙin daɗi. Ta kara yin laƙwas gami da bada dukkan
nutsuwarta. Daidai wurin wani tukuba wacce a gefenta
kujeru ne wuri-wuri cikin wata ƴar rumfa, ya nemi wuri ya
tsaya.
Ta kalli wajen tana mamakin yanda ruwa bai sa babu
cunkoso a wajen ba, kamar ta ce mishi sai ya bi uban
layinnan zasu tafi sai kawai ta fasa ta yi shiru.
"Ban mintuna kaɗan." Bai jira amsawarta ba ya ɓalle seat
belt ya fita. Sai a sannan ne ta lura da cewa three-quarter
ce jikinsa, kunya ta sa ta kauda kai daga kallonsa.
Fitarsa ba jimawa wayarsa ta shiga ringing.
"Zeenat." Sunan da ta gani kenan saman kafcecan screen
din da babu tsaga ko ɗis, gabanta ya faɗi. Har ta kammala
ringing ba ta yi karambanin ɗagawa ba, kafin dai ya dawo
ta yi ƙara fiye da sau uku. Anan ta ƙara gane naci da
rashin hakuri irin na Hajiya Zeenat. Ta tsinci zuciyarta da
daukar zafi, har hura hanci take don takaicinta, ita kanta
ba ta da dalilin jin hakan.
Yana zuwa ya ajiye ledojin a baya hadi da kallonta.
"Sorry, na bar ki kina jira."
Duk sonta da ta saki fuska ta kasa.
"Bakomai."
Hannu ya kai ya dauki wayar, nan da nan ya ɗan sauya.
"Ɗan yi shiru please." Kallonsa kawai ta yi ganin yanda ya
nutsu, waya yake latsawa kafin ya ɗaga. Anan ta ji yana
ban hakuri kafin daga bisani ya ce yana hanyar dawowa.
Taɓe baki ta yi ta kauda kai gefe, tasan da za'a ce tsoro
yake zai ce ba haka ba. Can kuma ya ajiye wayar ya tashi
motar suka tafi.
Jin wannan karon bakinsa ya mutu ne yasa ta kalleshi.
Fuskarsa kamar a sake kamar kuma ransa a ɓace, ta
kauda kai cike da jin babu dadi don haka ta ja shi da hira.
"Yaranka nawa?"
Murmushi ya yi ya ɗan dubeta.
"Kina son yara ne?"
Ta maida dubanta ga titi tana murmushin itama.
"Yara ai abin so ne. Wa zai ƙi su?"
"Naki ba su isheki ba?"
Ta ɗan yi shiru tana tunanin wa ya fadamasa tana da yara
ne? Ko dai Hisham ne? Muryarsa ta katse tunaninta.
"I saw your WhatsApp profile."
Fadin hakan da ya yi shi ya tunasar da ita hoton yaranta
ne akan dp dinta sannan a settings dinta kowa yana iya
ganin dp idan har yayi saving lambarta.
"Hakan na nufin.." Ta fadi da sauri tana kallonsa. Wani
kallo ya jefamata da ta kauda ƙwayar idanunta.
"Wajen Hisham na karɓi lambar, ba don komai ba kuma,
kar ki fassara please ki yi zaton sabon kamu kika yi."
Ta murmusa.
"Dama kai kam ai sai Hajiya."
Ya yi shiru kaɗan yana murmushi, har ta fidda rai zai yi
magana can ta tsinkayeshi.
"Amma dai kin san ni mijin mace huɗu ne ko?"
Ta dara kadan.
"Um um, ban ga alamun hakan ba. Kai da aka kafamaka
ƙahon zuƙa ana bi duk inda ka yi?"
Ya shiga jinjina kai gami da kaɗan yatsa jikin sitiyari.
"Ke ba'a kada ki a magana ko?"
Ya ba ta dariya.
"I'm sorry."
Ta furta kanta tsaye. Ya kai hannu ya dauki gilashinsa baƙi
ya manna a idon, ta saci kallonsa, murmushi kawai ya ke
dokawa da ya ƙara masa kyau. Wani ajiyar zuciya ta
sauke. Ba ta ga baƙin Hajiya na kishin wannan haɗaɗɗen
ba.
Har suka isa bai ƙara magana ba banda muryar Maher
Zain da ya ƙaro a waƙarsa ta Thank You Allah. Nutsuwa
sosai ta yi har da kwantar da kai jikin kujera tana sauraron
waƙar. Koda suka iso Sharada, shiru ta yi ta zuba ido tana
so ta gani ko zai gane gidansu. Ta sha mamaki ganin ya
shiga kan layin. Kamar wancan karon ta juyo ta dubeshi.
"Zan sauka anan."
"Don me? Kar saurayinki ya ganni?"
Ya furta yana tafiya a hankali a dalilin ruwan da ya cika
wurin. A raunane ta ce.
"Ni wallahi ba wani saurayi, kawai dai.."
"Kar ace ni saurayinki ne?"
Ya fadi wannan karon idonsa a kanta, daga cikin gilashin
yake ƙare mata kallo. Ganin kamar kallon na ƙurillah ne ya
sanya shi kauda kai ya maida bisa hanya. Ita ta ma rasa ta
cewa. Ganin ya tsaya daidai ƙofar gidansu ne ta fahimci
rannan dai ya gane gidan da ta shiga. Dubansa ta yi, ya
fidda gilashin ya dubeta.
"Shikenan?"
Tsuke baki ta yi kafin ta bude motar za ta fita ta ce.
"Nagode Allah Ya saka da alheri."
Murmushi ya yi ganin tana shirin rufo ƙofar.
"Ji mana."
Dakatawa ta yi gami da duban ƙyauren gidan a tsorace
sannan ta sunkuyo kanta ta dubeshi kamar ta yi kuka.
"Mene ne?"
"Ban mukullin motarki. Zan sa a kawomaki."
Ta ciro ba musu ta miƙa masa har da godiya. Dama
burinta su saba yanda za ta tunkareshi da batun ƴan
uwansa. Tasan kuma tana bukatar jin ta bakin Hisham ko
akwai abinda ya sani shima.
Hannu ya kai ya ɗauko lemarta da ƙullin leda ɗaya na
nama ya miƙamata yana faɗin.
"Idan ba so kike mu dawo gidannan da Madam ba, riƙe ki
tafi da su."
A tare suka yiwa juna dariya, ta karɓa ta mishi wani irin
kallo kwatankwacin wanda ta yi don baƙanta ran Hajiya.
"Itama ta san ni din ba kanwar lasa ba ce yanzu."
Ya ɗaga gira.
"Really? Idan kin yarda za ki maimaitan kallonnan a
gabanta, shigo mu tafi."
Wani irin kunya ya mamayeta, ta yi saurin ficewa ta
rufemishi ƙofar, ya lumshe idanu ya bude yana kallonta,
dab da za ta shige gidan ta juyo ta ɗaya mishi hannu tana
murmushi, ga mamakinsa shima ɗagamata ya yi, ta juya
ta shige ciki shi kuma ya ja ya tafi duk jikinsa a sanyaye.
Kamar yanda mamaki bai bar shi ba hakanan itama ta ke
ta mamakin kanta. Abin mamaki har ta shiga falon Hajiya
murmushin ta ke yi.
Ta tarbi yaranta har da ɗaga Affan ta juya da fadin
"Oyoyo Babyn Mami."
Suna ta dariya ta karasa ta zauna gami da fadin wash.
"Sannu, amma kin jima. Mun yi waya da Rafee'ah ta cemin
kin bar gidanta da wuri. Ina kika tsaya?"
Ta ajiye mayafinta a gefe bayan ta ajiye ledar a saman
tebur, lema kuwa Ummi ce ta karɓe ta nufi ɗaki da shi.
"Mota ce ta macemin a hanya wallahi."
"Ya Salam, to yanzu ya kika yi?"
Murmushi Ramlat ta yi, fuskar Hussein ke yawo a kwayar
idanunta.
"Abokin Hisham ne ya ganni, shi ya kawoni har ƙofar
gidannan."
"Mijin Hajiyarnan?" Yanda Hajiya ta fadi ido waje sai ya ba
ta dariya.
"Shi."
"Ai shikenan ke kika sani, ki yi ta jajiɓo yaronnan idan ta
zo har gidannan ta jibgeki ba abinda zan ce."
Dariya ta yi.
"Ta jibgeni fa Hajiya? A gabanku?"
"Atoh, ai naga alamar kamar alaƙar taku ƙara yin gaba ta
ke."
Jiki a sanyaye ta girgiza kai.
"A'a fa Hajiya, ba komai tsakaninmu wallahi banda
mutunci."
Hajiya ta murmusa.
"Allah Yasa toh."
Ramlat ta basar da zancen.
"Ga nama nan ma ya siyamin."
Daga nan ta mike ta nufi ciki don sauya kaya sai dai
maganar Hajiya ta ɗan shigeta. Dagaske sabo ke neman
shiga tsakaninta da Hussein. Kamar kuma irin sabonnan
da ba shi ta nema ba, irin wanda ba shi suka shirya da
Amrah ba.
Ta kai hannu ta fiddo wayarta daga jaka, kai tsaye ta shiga
whatsapp kan dp dinta. Hoton yaranta ne, Affan da Ansar
sanye da shadda iri daya, hular Affan har goshi, Ansar
kuwa ta zauna ɗas a kansa. Ummi daga bayansu ta dafa
kafadunsu suna dariya kamar yanda mai hoton ya basu
umarni. Murmushi ta yi ta shafi hoton tana tuna kalaman
Hussein. Wato dai ya san tana da yara kuma ba ta da
aure? Da alama a wurin Hisham ya nemi ƙarin bayani.
'Har zuciyarki ta soma saƙa wani abu akan wani ɗa
namijin?'
Wani bangare na zuciyarta ya ankarar da ita, ta yi saurin
kashe wayar ta ajiye gefe, rage kayan jikinta ta yi ta faɗa
wanka. A ganinta wannan kuskure ne babba. Don haka
dole ta yi takatsatsan, kyakkyawan jihadin da ta yi niyya
kawai za ta aiwatar akan wadannan ƴan biyun. Daga nan
babu komai!
***
Washegari safiyar Lahadi da misalin ƙarfe takwas na
yamma, Malam Bala ya yi sallama a kofar falon. Ita kadai
ce a falon tana taimakawa Ladidi da tsintar shinkafa, yara
na ɗaki wurin Hajiya,ta amsa ta leka suka gaisa. Muƙulli
ya miƙomata.
"Gashinan wani ne ya kawo ya ce a ba ki inji Yallaɓai, ga
motarnan an shigo da ita ma."
Ta karbi mukullin.
"Ya tafi?"
Malam Bala ya amsa da eh. Ta mishi godiya sannan ta
dawo ciki ta ajiye mukullin. Wayarta ta yi ƙarar shigowar
saƙo. Ta dauka ta duba.
"Mota duk ta yi datti ba wanki, gashinan, za ki biya kudin
wankinta."
Abinda aka rubuta kenan, wannan ya ba ta tabbacin har
wankemata ya sa aka yi. Dariya ta yi kafin ta maida mishi
martani bayan ta ƙare wa lambar kallo.
"Nagode Yallaɓai, Allah Ya bar zumunci."
Ta aikamasa kenan ta ga akwai saƙon da ya shigo ba ta
ko lura ba. Hilal ne. Kirjinta ya fadi, idan ba ta mance ba
yau an zarta sati da maganarsu, damuwa ta sauka saman
fuskarta a yayinda ta karanta saƙonsa.
"Ban sani ba ko hidima ce ta miki yawa kamar yanda ta
sha kaina har ban samu zuwa akan lokacin da muka
tsayar ba. Ina fatan komai lafiya? A sanyamin ranar da
zan zo idan ba damuwa."
Sauke ajiyar zuciya ta yi, ta rasa ma amsar da za ta ba shi.
Ita ta sani, babu soyayyar bawan Allahn nan (Hilal) a ranta
face tausayi da kuma ganin daraja da ƙimarsa. Ta yi
addu'ar istihara sosai amma ba ta jinsa ko kaɗan. Ta rasa
amsar bayarwa don haka ta ajiye wayar kawai ta ci gaba
da aikinta.
Ita da kanta ta yi musu girki, shinkafa da miya. Tana
kammalawa ta fito falon inda suke zaune ya yi daidai da
shigowar Munir gidan dauke da yaransa. Daga ganin
yanayin fuskarsa da irin daurewar da ya yi ka san cewa
akwai matsala. Ya zauna yana gaida Hajiya a daure, ta
amsa gami da jefamasa tambayar dake zuciyar Ramlat.
"Lafiya kuwa? Meyafaru na ganka da su Yasmeen?"
Ya shafi kai yana amsa gaisuwar Ramlat kamar ba ya so.
Ya ba Yasmeen umarnin su shige ciki da su Ummi.
Yasmeen ta ja ƙannenta uku suka ɗunguma gaba daya
zuwa ciki. Da yake yarinya ce mai wayo, gaba daya itama
fuskarta ta koma kalar tausayi.
"Wata ƴar hatsaniya aka yi da Bilkisu da Hunainah akan
kawai yarannan su na shiga bangaren Hunainah. Ita
yarinyar tana sonsu tana kuma jansu a jiki, toh ashe ita
Bilkisu ranta na baci. Dama ba sau daya ba, kuma ba sau
biyu ba ta ke nuna ba ta kaunar zuwan yaranta wurin
Hunainah. Yau da na gaji don Yasmeen ta kwana sashin
Hunainah shi ne ta kama yarinyar ta buga, ni kuma na
yanke hukuncin zamansu a wurin Hunainah tunda abin
haka ne, toh wai shi ne Bilkisu ta dauko wuka har da kai
wa Hunainah yanka a kafaɗa ta yankamata hannun riga,
wai ita ta rantse idan har na rabata da su za ta kashe
Hunainah. Wannan ne dalilin da yasa ni kuma na korata
gidansu na kwashi yaran na ce bari na kawosu nan idan
ya so zuwa anjima sai na tafi da su. Haba! Wannan
masifar ta ishe ni, Hajiya kusan kullum sai Bilkisu ta ɓullo
da sabon rikici. Daga wancan sai wannan! Nikam gaskiya
ta soma isata don zan iya sauwaƙe..."
"Kar ka fara! Nace kar ka fara! Idan ka yi ba da yawuna ba
wallahi. Wane shashashan namiji ne zai saki matarsa ta
farko kuma Uwar ƴaƴa? A'a kar na kara jin batun
rabuwarnan a bakinka. Yanzu kai dama anan ba sai da na
gujemaka irin hakan ba? Ban maka magana game da haɗa
matannan gida ɗaya ba? Ka nunamin kai namiji ne da
mace ba ta isa tankwarawa ba. Ai zaman lafiyar ake
nemamaka. Toh ga irinta nan, tun ba'a je ko'ina ba ta
soma yunkurin kashe baiwar Allah."
"Hajiya ɗan rigima fa ɗan rigima ne, koda ba gida ɗaya
suke ba, sanin da na yiwa Bilkisu za ta iya takawa har
gidanta. Toh Hajiya a hakan ma fa zargina take da rashin
adalci ina kuma ace gidansu ba daya ba?"
Ramlat dai ta yi shiru tana kallonsa yanda duk ya fice a
hayyacinsa.
Yanda aka banko labulen falon aka shigo yasa duk suka
kalli kofar. Bilkisu ce buguzuzum da ita. Kalar mayafin
daban da atamfar da ke jikinta. Da ganinta ka san ba'a
nutse ta ke ba.
Kai tsaye wurin Munir ta tunkaro hannunta a ƙugu.
"Ka bani yarana tunda ba kai ka haifamin ba!"
KARFEN KAFA Chapter 45
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323
By Rufaida Umar
Idanunta jage-jage da ruwan hawaye. A fusace ya mike
Hajiya ta yi saurin riƙe hannunsa.
"Kai bana son hauka. Yi shiru abinki Bilki, zauna don Allah
ki nutsu. Yaranki suna nan, kuma zan ba ki kayanki ki tafi
da su."
Wani kwafa ta yi ta zauna tana kuka har da share majina.
Ramlat ta mike ta yi ɗaki don ita takaicinsu ma