Showing 105001 words to 108000 words out of 113545 words

Chapter 36 - KARFEN KAFA Book 2 Complete end document by Rufaida Umar .txt

sai ya kawomin ziyara duk kuwa da tarin
kiyayyar da nake mishi, sai dai na gasamishi baƙaƙen
maganganu wanda har ya mutu a lokacin ban yi dana
saninsu ba sai ma dadi da naji a lokacin ganin ya bar min
filin duniyar na ci karena babu babbaka."
Kawu ya numfasa saboda kukan da ya shaƙe shi, iyalinsa
da su Dada kuka suke yi cike da mamakin irin wannan
salon ƙiyayyar da bawan Allahn ke yiwa ɗan uwansa na
jini. Shi kuwa Hussein ba zai ce ga yanayin da yake ciki
ba, sai dai ko kallon Kawun ba ya son yi.
Kawu ya ci gaba da magana bayan ya sharce majina.
"Bayan shekaru da dama, a wani ziyara da Amina kika sa
Husseini ya kawomin, lokacin ya samu hutun karatun da
yake yi a Dubai. A wannan zuwan ne yaron ya ban tsoro
har nake ganin nan gaba zai iya cin mutuncina a gaban ko
su waye. Saboda tunda nake da ke da Aminu, babu wanda
wuyansa ya taɓa yin tsaikon da zan faɗa ya faɗa, sai
Husseini, ko Hassan bai taɓa yimin cin fuskar da nake
ganin Husseini ya yimin a lokacin ba. Wannan ne dalilina
na farko da na ci alwashin sai na tarwatsa rayuwar
Husseini. Sai ya rasa dukkan farin cikinsa. Sai dai me?
Kafin na kai ga aikata duk wani abu da na yi niyya, na
samu labarin ɓacewar Husseini, ya gudu ya bar gida ba'a
san inda ya shiga ba. A lokacin idan ka tona zuciyata
banda tsananin farin ciki babu abinda na ke ji, har addu'a
nayi Allah Ya dauki ransa ma. Bayan watanni uku da
ɓacewar Husseini, wataranar lahadi ba ni mancewa, ni da
kaina ke tuƙi a mota daga kasuwa zan koma gida, a hanya
na hangi wata tsohuwar kwastama ɗita, a baya takan zo
ta sararwa Hajiyarta atamfofi a shagona ko kuma yadika
na maza ta tafi, a sannan tana budurwa ko kuma nace
mace mai zaman kanta amma a karkashin ikon wata
Hajiya mai safarar yara zuwa Makkah da sauran ƙasashen
waje don aikatau ko akasin haka. Zeenatu kenan, tun a
baya Hajiyar ta sha aiko ta shagona tun ban kai ma ga
auren ita Maimuna ba, (Anti Amarya), tun a wancan
lokacin muka saba, nakan ba ta shawara akan ta yi aure
gudun kar ta ɓata rayuwarta don ni nasan wace ce Hajiya
Balki uwar ɗakinta, saboda na sha zuwa gidan muyi
cinikin kaya ta siyawa ƴan matan yaran da ke gabanta ko
kuma ta siyar, na kuma san irin kalar sana'arta. Daga baya
kuma sai na bar ganin Zeenatu, sai wata Raliya ake
turowa. Koda na tambayi Raliya, ta bani tabbacin ai
Zeenatu ta tafi Makkah, a sannan na ji ba dadi kwarai don
ban so ta cuci kanta ba sai dai dama daga yanayin
Zeenatu na fahimci maganata ba wani shigarta ya ke ba."
KARFEN KAFA Chapter 78
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
@Whatsapp 08083232323 or 09060202323


By Rufaida Umar


Second to the Last


Kawu ya numfasa, nan kuma dai dakin tsit ya yi babu mai
kuka sai jin wannan labarin mai ban mamaki daga bakin
Kawu. Ya ɗora zancensa.
"Ganin da na yiwa Zeenatu a haɗaɗɗiyar mota, bai sa na
kasa ganeta ba, asalima fuskarta ko kaɗan ba ta sauya ba
duk kuwa da ɗumbin shekarun da aka ɗiba. Parking ta yi a
gaban wani katafaren shagon siye da siyarwa na
maƙulashe, na juya kan mota da sauri na faka a gefenta.
Sai dai ban kai ga fitowa ba, idanuna su ka sauka akan
Husseini, ba karamin razana nayi ba, sai nake ganin abin
kamar a mafarki, fuskokinsu kadai ya nuna suna cikin
tsantsar farin ciki. Ban karasa ba, har suka shiga suka fito,
mantuwa suka yi ko mene? Ban sani ba, na ga Husseini ya
fita ya koma ciki, har zan je wurinta sai naji tsoron kada
ya fito ya gan ni, sai kawai na koma cikin mota na jira har
ta tashi motarta ta kama hanya ta bar wurin, na bi su a
baya har suka isa gidansu. Koda na ga gidan kawai sai na
juya da zummar zan dawo na same ta don ba na kaunar
Husseini ya gan ni. Bayan kwanaki biyu, a wani yammaci
na isa kofar gidan, cikin saa na isketa tana kokarin shiga
cikin kyauren, ganin ita kadai ce na yi hon ta juyo, ni kuwa
na ja na tsaya na fito. Ta shiga bi na da kallo kamar na
neman ƙarin bayani da kuma son tuna inda ta san fuskar,
nan take ta tambaye ni. "Kamar na sanka." Na ba ta amsa
da eh, kafin na ce kin manta Modibbo na Kwari? Nan da
nan ta saki fuska muka kara gaisawa. Na ce "Yaushe kika
dawo?" Nan ta ke sanarmin ai ta kai shekara guda da
dawowa, daga nan kuma na nemi mu keɓe don mu
tattauna wata muhimmiyar magana. Sai dai na tambayeta
ko akwai wani saurayinta a ciki? Idan akwai na juya. Ni
kuma na dadi haka don na gane irin zaman da suke yi da
Husseini, burina ta cemin ba zaman aure ba ne.
Abin ya ba ta dariya. "Aa ai kuma yanzu an girma da
wannan kalar rayuwar, aure nayi." Na jinjina kai ina
murmushin da bai kai zuci ba don ba haka na so ba. Sai
dai ina bukatar mu zauna na ji bayani sosai. Koda muma
shiga ciki, ta sanya aka kawomin lemo da ruwa, abinci
kuma na ce aa. Bayan mun nutsu na kara kai duba ga
hoton Husseini da ita wanda tun shigowata ya dauken
hankali, shakka babu aure ne suka yi. Anan na sanar da ita
gaskiyar alaƙarmu da Husseini, a farko ta razana sosai har
ma ya ɗaure fuska tamau. Nayi dariya sosai na ce ta
kwantar da hankalinta ina bayanta domin ba na shiri da
iyayensa, don haka ni ko nan da bangon duniya ma tana
iya kai Husseini muddin ba za'a gan shi ba. Faɗin hakan
keda wuya ta kwantar da hankalinta saboda na biyomata
ta sigar da dole ta samu nutsuwa. A karshe ta ban labarin
duk yanda aka yi na dinga dariyar mugunta. Ni kuma na yi
mata alƙawarin ko na ji ana raɗe-raɗin an gan shi zan
sanarmata, zan kuma yi asirin da zan rufe bakin duk
wanda naji yana raɗe-raɗin ya ga ko mai kamarsa ne a
kwaryar Kano. Na kuma kara mata da cewa dole tana
bukatar asirin da zai kara jin nan duniya ya tsani a tayar da
zancen danginsa ko a tambayeshi, amma ta bar komai a
hannuna. Wannan ne abinda na san na aikata, ya kasance
ana neman Husseini, ni kuma nasan inda ya ke, amma na
yi gum. Shiyasa koda Ramlatu ta zo da zancen Husseini,
na kore ta na ce ba ruwana. Ban yi ƙasa a gwuiwa ba na
sanar da Zeenatu, nan muka ce kawai a kashe ta yanda
babu wata hanya da za'a san labarin komai. Sai dai kuma
abinda Allah Ya riga ya tsara, ba wanda ya isa dakatar da
shi."
Kawu Modibbo na kaiwa nan ya dakata ya ci gaba da kuka
sosai. Falon banda salatin da Baffa Surajo ke maimaitawa
cikin zubar hawaye, ba ka jin komai sai sheshshekar kukan
yaran Kawu Modibbo.
"Ku yafemin, ku yafemin don Allah. Na tsaneku akan ba ku
aikatamin komai ba, na cutar da rayuwarku. Na hana
yarana zumunci da ku duk don bana kaunarku. Ku
yafemin. Husseini ka yafemin, Aminatu, Hassa.."
Ya kasa ci gaba saboda kuka, Hussein kawai miƙewa ya yi
ya bar falon, Baffa ya yi nasiha mai ratsa jiki gami da
nuna ladan da ke tattare da wanda ya yi hakuri. Dada nan
take ta yafemasa, ta ce komai ya wuce, hakanan shima
AlHassan. Wannan abu ya yiwa Kawu da iyalinsa dadi,
itama Hajja Fatuma ta nemi gafarar Dada na yanda ta
dinga wulakanta ta ita mai miji dadi, Dada na murmushin
da ya fi kuka ciwo ta ce babu komai ya wuce. Haka dai
aka yi ta neman yafiyar juna. Taheer sai satan kallon
Hafsat ya ke, ita kuwa gaba daya kunyarsa ta ke ji, a gefe
guda tausayi da kaunar dan uwanta Hussein ya kara
mamayeta, wato dai shi ya san dalilinsa na tsanar Kawu.
Ashe mugun abu ya ƙulla masa har haka.
***
Ramlat da ba ta san hawa ba ba ta san sauka ba, ta ga
mutum ya fado falon, kallo daya ta yi mishi ta gane ba
lafiya. Ya zube saman kujera ya runtse idanu, fuskarsa
abinka da farar fata ta koma jawur da ita. Ta shiga
ambaton Allah a ƙasan ranta, miƙewa ta yi ta zauna
gefensa, ba ta ce komai ba amma ta kamo tafin hannunsa
ɗaya tana murzawa a hankali, a ranta addu'oi kawai ta ke
karantomasa. A hankali kuma ya shiga sauke ajiyar
zuciya, ya bude jajayen idanunsa ya dubeta. Sai da ta ji
gabanta ya fadi, gaba daya sai ta tsinci kanta cikin
damuwa mai tsanani.
"Lafiya Haskena?"
Gyara zama ya yi, bai ɓoyemata duk abinda ke faruwa ba,
kawai sai ta shiga hawaye tana mamaki da tsoron lamarin
mutum. Idan naka ya yi maka haka, ina hujjar da za ka ji
haushin wani don ya yi maka? Sai kuma ta fahimci
kuskurenta, hawayen ba zai ƙarar da Hussein da komai ba
face ya kara ganin girman laifin da Kawun ya mishi har ya
kasa yafemasa. Don haka ta yi azamar sharesu, ba ta kai
ga magana ba sai ga AlHassan ya yi sallama ya shigo,
Dada tafe a bayansa. Ta mike da sauri tana musu sannu
da zuwa, Allah Ya taimaka ma tun fitarsa ta suturta jikinta
sakamakon shanyar da ta kwaso a bayan gidan wurin
shukoki. Ta gaida su Dada, Dada ta amsa fuska a ɗan
sake. Sai dai itama fuskarta kamar na Husseini, ta yi ja,
kuka kam ko ba'a faɗa ba sun yi shi, balle AlHassan.
Za ta shige ɗaki, Dada ta hanata, ta bata umarnin zama.
Shiru ya ɗan biyo baya. A hankali kuma Dada ta shiga yiwa
Hussein nasiha, sosai ta ke yi mai ratsa jiki tana
kawomishi misalai na irin hakurin da Annabi s.a.w ya yi da
yan uwansa da ma sauran mutane.
"Ka yi hakuri ɗana, ka yafemishi, idan ba ka yafe ba, da
me zai ƙare ka? Me kake nema a duniya yanzu da Ubangiji
bai maka ba? Babu shi, ka saka a ranka ba yanda ka iya,
haka Allah Ya so ya jarabceka kuma Ya jarabta. Idan har
na isa da kai, kuma har zuciyarka kana jin za ka iya
yafewar, domin Allah muje ka fadi ya ji da bakinsa ka
yafemasa."
Hussein wanda gaba daya jikinsa ya yi la'asar, ba shi da
sauran kataɓus, miƙewa kawai ya yi suka fita tare da Dada
zuwa sashinta. Ta ba Ramlatu umarnim biyo ta, hijab
kawai ta sanya ta bisu a baya.
Kawu ya yi murnar sake ganin Husseini, da kansa ya mike
jiki na rawa ya kasa gareshi ya rike hannunsa, kawai sai ya
soma kokarin durkusawa yana kuka. Da sauri Hussein ya
rike hannunsa ya ɗagoshi tsaye.
"Ya wuce Kawu, na yafemaka a bar zancen haka."
Ba wanda kalaman Hussein bai wa dadi ba, Ramlat ta
gaishesu, itama dai gafararta Kawun ya nema, take kuma
ta ce ba komai ya wuce.
Nan fa gida ya yi dadi amma Hussein bai wani sake sosai
ba, sai da aka yi Magriba kafin su Kawu su wuce, Baffa
Surajo ya ce lallai gobe duka a hadu a babban gida yana
neman kowa da kowa. Ya bada umarnin a sanarwa wanda
ba ya nan, na nesa kuwa a rabu da su. Da wannan komai
ya wuce.
***
Washegari kuwa misalin karfe biyu, Baffa Surajo ya haɗa
taron da kowa na zuri'ar Gidado dake a Adamawa ya
hallara. Bayan addu'a da doguwar nasiha, ya ba Kawu
damar neman afuwan yan uwansa. Nan Kawu ya ba kowa
hakuri da kuma daukar alkawarin ba zai kara aikata ko
makamancin hakan ba. Kowa ya ji dadin hakan kuwa,
karshe kuma ya nemi alfarmar haɗa auren Taheer da
Hafsat, nan take Dada ta ce ita ba ta da ja. Hussein zai yi
magana ta harareshi, murmushi ya yi.
"Cewa zan yi an bayar." Maganar ta ba kowa dariya, Baffa
Surajo ya yi mishi daƙuwa.
"Ai ba kai ke da alhakin bayarwar ba."
Bai ce uffan ba, Hafsat kuwa ai kamaran mata albishir da
gidan aljanna.
***
MURFI....
ADAMAWA
BAYAN WATANNI BIYAR..
Amarya Ramlat ta kara kyau da ƙiba sai dai ba irin mai
munin nan ba. Sanye take cikin doguwar riga na leshi
lemon green an mata dinkin bubu, ta fito daga motar
yayinda Hafsat da Rasheeda suka yi gaba niƙi-niƙi da
kaya, ita kuwa tare suka jera da Kausar rike da wasu
ledojin. Dawowarsu kenan daga kasuwa, zuwa lokacin sun
yi nisa da shiryen-shiryen bikin Hafsat har ma da
Rasheeda wacce za ta auri ɗan Barrister Hansatu (Babbar
Yayar su Kawu Modibbo), Mujaheed.
Tun da suka rubuta jarrabawar karshe kasancewar tare
suke tafiya da Hafsat a karatu, sai Rasheeda ta tubure ta
ƙi zaman Kano, ta dawo gidan Adamawa wajen Dada ta yi
zamanta. Wannan abu ya yiwa Dada dadi, wai yau ta budi
ido ta ga jinin Kawu Modibbo a gidanta, kuma da son ran
mahaifin, sai ta ji inama ɗan uwanta baban su Hussein na
raye ya ga ranar da ya dinga ce mata za ta zo in sha
Allah, ashe kuwan tana tafe.
Hamida babbar ƴar Dada wacce aure ya lula da ita har
Saudiyya, ta jima rabonta da ƙasar don ko Ramlat
tsakaninsu sai dai ta waya ko kuma idan ta kira Hussein
videocall suke gaisawa. Ta dube su da kulawa tana ba
karamar ɗiyarta Mama.
"Sannunku da zuwa. Kun sha wunin kasuwa."
Suka yi murmushi lokacin da kowa ke kokarin zama.
"Wash!" Fadin Hafsat tana mai kwantar da kai jikin Dada.
Ture ta Dada ta yi.
"To raguwa, ni matsa ki ban wuri. Gwara ma ki tattara ki
bar gidannan ko na huta."
"Aa Dada, ina hutu ba kya ganin Auta? Faɗa dai ki ke yi."
Cewar Adda Zahra, mai bi wa Hamida, ita a Lagos ta ke
da zama.
Aka yi dariya. Haka kuma aka shiga bude kaya ana ganin
siyayyar da suka yi na abinda ya yi saura na tarkacen
kayan girki har ma da sauran kayan kicin da ba'a siya ba.
Sosai an yaba da kayan, sai da suka ci abinci kafin Ramlat
ta koma sashinta. Wanka kawai ta yi don wani irin zafi ta
ke ji, ta sanya kananun kaya riga da siket marasa nauyi
kafin ta faɗa kicin. Lissafi ta shiga yi a ƙasan ranta, su
Rafee'ah bai fi saura kwanaki shida su zo ba saboda biki.
Ta ƙagu ta ga yaranta da kuma Aisha da babynsu. Ta shafi
cikinta kaɗan tana murmushi, tana burin Allah Ya ba ta
haihuwa ko don ta ga kalar farin cikin Hussein wanda
yanzu koyaushe ba shi da zance sai na baby, baby. Haka
dai Ramlat tana aiki tana tunane-tunanenta. Sai da ta yi
nisa, sai ga Kausar ta shigo, itama kam ciki ne da ita wata
uku. Sallama ta yi mata akan za ta tafi, har ƙofa ta yi mata
rakiya.
"Kai aa ki koma hakanan, ga mijinki can na baro sashin
Dada, idan ya ganki haka kin fito ai ni zai ɗorawa laifi."
Ramlat ta yi dariya, sai yanzun ta tuna da kalar suturar
dake jikinta. Ko ba komai daga rigar mai hannun vest har
siket din wanda yake dogo amma kamar roba, duk sun
matse ta.
"Toh Maman Twins, Allah Ya saukeki lafiya. A gaidamin da
Fatina sosai."
"Twins dai yana jikinki Madam, amma ba ni ba. Ki bar
yimin wannan fatan. Fati kuma za ta ji sosai."
Ramlat abin ma ya ba ta dariya, tana mamakin yanda
Kausar ke gudun twins. Ita kam da ace za ta samu tana
son abinta. Anan dai suka rabu ta koma kan aikinta. Babu
jimawa Gogan ya shigo. Ganin tana kicin kawai ya nufi
ɓangarensa ya watsa ruwa. Duk tana ji, Allah Ya taimaka
dama girkin ƙarashe ne don ta dafa markade ta kuma yi
tafashen kazarta kafin su wuce kasuwa. Wannan yasa
kawai miyar ta haɗa ta kuma dafa kuskus da ya sha karas
da koren wake. Komai ta haɗa a gaggauce ta kawo falon
ta jera saman ledar cin abinci.
Ƙamshinsa ya soma dukan ƙofofin hancinta, ta ɗaga kai ta
kalleshi. Wando ne mai jikin cotton ya sanya sai farar
tshirt mai gajeran hannu. Koyaushe Hussein ƙara kyau
yake yi a idanunta, kullum ƙuruciyarsa ta ke gani. Har
kullum idan zai fita daga gida hakanan sai ta ji wani kishi
ya kamata. A kwanakin baya sai da ta kwashi takaici
sadda wata Meena ta matsa mishi da kira, hankalinta bai
kwanta ba sai da ya tabbatar mata babu komai tsakaninsu
karshe ma ya rufe Meenar ta yanda babu damar da za ta
ƙara kiransa. Da wannan ya samu hankalinta ya kwanta.
Har ya ƙaraso ta shagala ba ta ko lura ba sai da ya kai
hannu ya shafi mafi soyuwa a wajensa. Ta dawo
hayyacinta ta sauke ajiyar zuciya lokaci guda ta ɗan
harareshi da wasa gami da murguda baki. Ya shafi
lebbanta da yatsa hana murmushi.
"Ni kike wa haka? Tunanin me kike?"
"Ba komai."
Ya matso da ita jikinsa ya kwantar da kanta saman
kirjinsa.
"Ko? Faɗamin gaskiya Malama."
Ta lumshe idanu tana shaƙar ƙamshinsa mai sanyamata
nutsuwa.
"Dagaske fa ba komai. Tunaninka nake yi."
Ya sumbaci saman kanta yana murmushi.
"Uhum, faɗamin, me kike tunani alhalin ni ɗin naki ne."
Ta yi wani tattausan murmushi a hankali ta ɗago kai har
hancinta na gogar sajensa. Suka dubi juna. Ya ja karan
hancinta.
"Ko ba haka ba?"
"Hakane."
"To kin gani, me zai dameki?"
Ta jinjina kai kawai ta murmusa. Nan kuma ta zubamishi
abincin, koda ta ce ta ci bai matsamata kan lallai sai ta ci
ba.
Haka dai a kwanakin nan kusan kullum sai sun fita
siyayya, sai da suka jera kwanaki uku, kafin Hussein ya
murtuke ya ce abin ya ishe shi. A gaban Dada aka yi, suna
zaune ne sai ga Waleeda cikin shiri ta dubi Ramlat.
"Adda Amal, muje ko?"
Ya haɗe fuska, ita kuwa Ramlat da ido ta nunamata
Hussein alamar bai yarda ba. Waleeda ta dubeshi baki
sake sai dai tuni ta haɗiye abinda ta yi niyyar faɗi dalilin
kallon da ya yi mata. Dada ta dara.
"To kai Husseini banda abinka, ai fitar ta su ce, ɗinkinsu
za su kai. Ka yi hakuri su je a auna su."
Ya mike zaune.
"Aa bari na aunata sai ita Waleedar ta kaiwa telan. Ba
shikenan ba?"
Kunya ta kama Dada, ba ta kara uffan ba ta mike ta yi
daki, Hussein dama ba yau ya saba ɓaram-ɓaramarsa ba.
Ramlat da ta ji kamar ta nutse ta rasa bakin magana.
Waleeda dake dariya ciki-ciki ta dubeshi kawai yayinda
Hamida ta hau dariyarta sosai a fili don kusan sa'anni
suke da ƴan biyu. Sai da ma ta faɗo duniya da watanni
biyu aka haifesu.
"Me na ce ne?"
Ya furta yana neman ba'asi ganin Dada ta mike ta yi daki,
su kuwa na falon na dariya.
"Au ba ka san me ka ce ba kenan? To ai Dada wuri ta ba
ka idan ka auna matartaka sai ta dawo."
Ya taɓe baki yana yamutsa fuska.
"To meye a ciki? Dada dai ta so jin kunyarta ne. Idan
muka haifamata jikoki ta daina. Tashi ita kuma wannan ta
ɗauko abin awo."
Ramlat ta mishi wani irin kallo kamar ta yi kuka. Ya yi
murmushi ya girgiza, kallon ya ji shi a dukkan wata gaɓa
ta jikinsa. Miƙewa ya yi ya mata duban zan haɗu da ke
kafin ya musu sallama ya fice wurin aiki, lokacin goma da
ƴan mintuna.
"Dagaske dai mijinki bai bari ba. Ai shikenan, kawai ki
ɗauko rigar da za ta yi maki daidai a yi amfani da ita."
Waleeda ta faɗi tana murmushi. Kafin Ramlat ta ce wani
abu sai ga kiransa. Ta ɗaga da sallama.
"Kwalliya ta biya kuɗin sabulu, amma kallon da aka yimin
yanzu idan na dawo zan zauna a yimin sau ɗari. Kuna iya
tafiya, Allah Ya tsare. Drive carefully."
Daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login