Showing 27001 words to 30000 words out of 94971 words
Chapter 10 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt
indai wannan ne damuwar ki, kana ki daina ƙoƙarin magana har sai namiki allurar da zata tsaida jinin ,ina fatan kingane?.
Wata irin guÉ—a Nene ta saki tare da tashi ta fara rawa tana gilgiza kirjinta mai kama da slipas .
Mamy fuskar ta tacika da annuri tana É—a gama Ammi hannu Alamun godiya.
Murmushi itama ta mata tana jin faÉ—uwar gaba.
Cikin 20mnt ya dawo ya kai mata allura ya fito.
Anan ta yima Mamy tare da É—oramata leda ruwa guda danjin kwarin jikinta. ta samata ita da É—an gudu dan ta kare .
Bayan awa biyu Mamy ta tashi ba laifi jikin da dama .
Anan ta fara jerama Ammi godiya.
Ammi tace Hajiya wani hanzari ba guduba.
kana akwai sharaÉ—i.
Mamy tace'' minene sharaÉ—in.
Ammi tace".
Kin amince ki aurama sadeeq yarki bakison ko waye shiba, kana bana da buƙatar ki sani, kin yarda?
Da sauri Mamy ta kaÉ—a kai tace" na yarda Hajiya dan dama itama burinta karkowa yason wanda ya auri Amnah.
Mamy tace" Masha Allah.
abyu na biyu y'arki zata iya zama da Sadeeq a cikin halin da yake ciki, bayan ita bata saba da irin wannan rayuwar ba?.
Mamy tace "na Amince dan ina buƙatar inda za a killaceta, abata sabuwar tarbiyya, da koyar da ita darasin Rayuwa.
Ammi tace abu na ukku Hajiya kin amince da babu dangin Sadeeq a auran nan, saidai aje ga liman yazama waliyyin shi ko kuwa ?
Cikin faduwar gaba Mamy tace "to ina ah'linshi?.
Murmushi Ammi tayi tace" indai kin Amince ahaka babu damuwa, in kuma saida ahli gaskiya kiyi hakuri dan nima bana buƙatar jin komi daga wani ahlin yarki, dan na fahimci akwai lauje cikin naɗi, dan dan haka kawai wannan auran yazamana auran taimakekeniya.
Mamy tace" shikenan insha Allah zansamu wanda zai zamemai waliyyi .
Daganan sukamata godiya suka fito.
Sadeeq ya fito ya mata sannu suka shiga mota ya maidasu gidan Nene.
Suna isa Mamy tace zai iya komawa gida da daddare yazo ya É—auketa.
Yace shikenan ba damuwa.
Yana isa gidan su yayi tsinke É—akin Ammi ya isketa zaune ita da Hamrat ta na shafa kanta amma som hankalinta na wani wuri.
Sallama ya sakeyi a'karo na biyu.
A furgice ta kalleshi tana yaƙen dole tace ''Dee ka dawo?
Yace eh Ammi tare da zama kusa da ita ya tankwashe ƙafar shi "yace Ammi miya faru ɗazu hankalina ya tashi fa,Daga zuwan ta abu harda tashin ciwo.?..
Kuka tasamai tare da riko hannu shi tace" ka yafeni Sadeeq, ka yafeni dan girman Allah, Nason zakaga kamar cutar da kai nayi,zakaga na yanke hukunci ba tare da shawaraka bayan bani da wanda ya fika, to Wallahi ba hakabane sadeeq ka kyautatama wanda ya kyautatamaka, kamata wannan alfarma kamar yanda ta buƙata.
Anan ta kwashe duk maganar da sukayi da Mamy ta faÉ—amai...
Gabaki dayan jiki shi ya É—auki bari wata zufa mai masifar zafi ta fara ketomai.
Hular kanshi ya cire yana fiffita da ita tare da miƙewa ya fara zirga- zirga cikin ɗakin.
Kimanin 30mnt yakasa cewa komi sai zarya yake.
Dakyal ya É—aga jajayen idanuwan shi ya sauke su ga Ammi da ke binshi da kallo tana share hawaye.
Hamrat ma kukan take.
"Ban amince ba ,kana na bar aiki agidanta , bakin da Allah ya halitta bazai hanashi abinda zai ciba.
Ammi yana da kyau ki haɗa kayanki dana haynrat yanzu insamo mai sayen gidan nan Abani abunda ya samu. kwara in dumfari ƙasata koda babu kayan yaƙi. in yaso komi zai faru ya faru.
Da in zauna inda ake juyi da rayuwata kamar Ball. "Aure" ni za ama aure. Lallai na yarda talakka gatanshi Allah ,wato inbaka dashi kenan rayuwama tsaramaka ake, To ban amince ba, kuma bazan ba, kayan duk datamana tm zanje in mayar mata da abinta. ana dole ,Banaso. ya ƙarasa cikin wata razananniyar ihun dayasa Hamrat daka tsalle ta rungume Ammi tana sakin kuka.
Cikin tashin hankalin Ammi ta tashi ta rikoshi dan taga yana ƙokarin fita.
Rungumoshi tsami tayi jikinta ta fara shafa bayanshi.
kamar wani ƙaramin yaro haka ya zage yana sauke ajiyar zuciya .
Hannushi Ammi ta kama suka zauna tace "Sadeeq inaso ka fahimceni ka fahimci uwa bazatama É—anta abinda zai cuceshi ba, Sadeeq matar nan nada ciwon zuciya abu kaÉ—an zai iyasa zuciyar ta bugawa,baivkamata muna da hanyar magance matsalata ba amma ace munkasa , Duk kan kyautatawar ta garemu mu sai mumata butulci?
Ta karɓeka hannu biyu tana mutuntaka Sadeeq tana kyautata mun, muna da damuwa kuma muna fatan ganin karshenta da izinin Allah,haka itama tana da tata muke mata fatan ganin karshen tata da izinin Allah,to ita tata mai saukice tinda har zata iya bayyana buƙatar ta, to danmi bazamu taimaka mata ba?
Kana Auran naku duka na Taimakekeniya ne fa babu tsaurara bincike.
Ina mai baka umarni da ka karbeshi hannu biyu ka kuma tsaya ka sauke hakkin yarinya dake kanka ,kaji tsoron Allah shine kawai abinda zakmun ,daga nan taci gaba da lalashin shi tanamai nasiha.
Kai ya jinjina ma Ammi yace" shikenan na Amince.
ya tashi yabar ɗakin da sauri dan inya zauna yana iya saɓama umarnin mahaifiyar shi abinda baya fata.
Cikin tsananin jin daÉ—i ta bishi da sanya Albarka tare da kwanciya gefen Hamrat tafara tinanin wani kuma rayuwa zasuyi a'sadda suka tashi daga su ukku zuwa hudu .
shine yarinya zata iya zaunawa dasu Ahalin da suke ciki,shin tanama son É—an nata ko kuwa?Ya hayyu ya qayyum ka kawoman agaji da mafita, Allah in haÉ—in nan alkhairi ne Allah ya tabbatar, in kuma ba Alkhairi bane Allah kai kason yanda zakayi damu.
Aɓangaran Mamy kuwa tinda ta koma gidan Nene ta samu gado ta kwanta.
Haka nan take yawan jin faÉ—uwar gaba wadda tarasa ko ta minene, Yanzu babbar Damuwar ta Sadeeq da Abban Amnah, ya zai É—auki maganata, shin zai fushine dan tayi gaggawa yanke hukun ci ko-ko zai fahimci manufar ta.
Nene da tashigo hannuta rike da kofin fura mai sanyi dai madai-daicin flat data shaƙoshi da felfesun yan ciki sai kamshi yake.
Tace ma Mamy" Fulani tashi kici abinci dan Allah kiyi sallah kifaÉ—ama Allah damuwarki danshi zai maki maganin komi.
Mamy ta tashi tace Nene damuwata Abba Amnah.
Nene ta taɓe baƙi tace ''ke nifa nafarama gajiya da wannan gantalallan auran naku Wallahi.
Na taɓa ganin miji kamar naki ace kayi tafiya neman kudin ka sama da shekara biyu bakazo ga iyali ba, wannan ai wulakanci ne da rashin sanin hakkin Aure.
Murmushi kawai Mamy tayi tare da karɓa furar ta shanye tass tace" na koshi da yan cikin sai anjima.
Nene tace" shikenan ki kwanta kihuta zuwa anjima .
Abangaran Amnah kuwa suna fita ta faÉ—a É—akin Amal anan taganta kwance tana bacci .
Da sauri ta É—auki wayar ta da tasa charge ta lallasa number Bily.
Bugu buyu ta É—auka cukin kasa da murya tace" inaji.
Tsaki Amnah tayi tace ke akwaifa damuwa Bily wallahi ,kinson mene ya faru kuwa?
Da sauri Bily dake kwance kusa da Prince ta mike tana gyara zaman É—aurin kirjin da tayi jin murya Amnah" tace'' A'a sai kinfaÉ—a minene?
Amnah tace waya ta Mamy ta ƙarba Bily, ina cikin tashin hankali kar ta fahimci wani abu.
Bily ta kalli Prince ya É—agamata gira da sauri tace" tamiki magana?
Amnah tace aa batace mun komi ba, kana komi bai canza ba.
Bily ta sauke ajiyar zuciya Tare da cewa haba karki wani damu babu komi kinson tin jiya mutumin ki ke nemanki. Amnah Wallahi Prince na masifar sonki, kinson wanda baitaɓa soba inya afka abin na bashi matsala. takarasa tana kaimai duka.
Amnah tace Allah sarki ina gaidashi.
Bily tace yanzu taya zan iya kawo miki wata waya ki ɓoyeta ya zamana ta sirrin kice ko Amal karki bari ta sani.
Cikin matuƙar jin daɗi Amnah tace'' yawwa hakan ma yayi, amma ina da kuɗi bari inje in siyo, in nadawo nayi miki magana.
ta faÉ—a tana datse kiran.
Dariya Bily ta tuntsire da ita tace waini su Abul khairi an'zama prince.
Sajenshi yaja yana kashe ido yace "dole komi ma inzama akan Baby nan tayi fa da kyal na yi bacci fa.
Bily tace "to yanzu in iyayenka zasuje gareta yaza'ayi?
Yace" ke kika sansu na bogi zan'samu ins'akar musu Æ´aÆ´an banki kawai suje suyi abinda za'ayi.
Cike da gamsuwa ta É—agamai kai tana Murmushi..
Sadeeq kuwa tinda yashiga É—aki yaji wani masifaffan ciwon kai na kawomai ziyara , Wanda bai rasa nasa ba da tashin hankalin da yake ciki ya tabbata.
Yanzu shida ke burin barin Katsina cikin wata ukku an'mishi aure to ina zaije da yar mutane ?som bayajin son koma wacece a'cikin yaran ta, Dan ba auran zaiba shi minene ma zayyi da mace , Bayan Aikin da yasama gaba wanda ko iyayen shi sai ya musu nisan kiwo .
Aɓangaran Mamy kuwa zaune take tana nazari yanda Sadeeq zai ɗauki magana su,da fahimtar bayanin ta, sam takasa natsuwa tana tinanin an sanar masa ko-ko.
Waya ta É—auka ta danna mishi kira dan samun natsuwa ta .
Kwance yake rigin-gine ya faÉ—a Duniyar nazari wai shi zaiyi Aure, To mi ake acikin Aure,Mizai iyama mace shikam.
Yana tsaka da tinani yaji wayar shi na ring.
Yana duba wa yaga Mamy ce harya juya kafaÉ—a kuma ya tina da abinda Ammin shi tace. wayar ya jawo ya É—auka cikin sallama.
Ajiyar zuciya Mamy ta sauke tace am "Sadeeq ina wuni .
taƙarasa cikin rikicewar murya.
Kamar yanda ya saba ya mayar mata da gaisuwar. Tare da cewa kingama ne mutafi?
Tace aa ina daiso kazo gidan Nene ne yanzu zan aikeka gidan Hajiya Turai kaida Amal.
Kai ya jin-jina tare da cewa" ina zuwa ya kashe wayar.
tare da sakin tsaki.
Amnah kuwa ganin babu kowa palo yasa cikin sanÉ—a ta fito daga ita sai Yar jikka ta fita da sauri daga gidan Nene.
Sama ta kalla ganin wani irin hadari da yayiwa saman kawanya.
Cikin sauri ta fara tattakawa dan ƙarasawa bakin hanya dan tasamu ta hau napep tayi sauri. Abinda bata taɓa yi ba.
Napep ta tsare" ta mai kwatancen inda zai kaita.
Yace "maza shige Hajiya kinga hadarin nan ya kwacema mutum waje akwai damuwa.
Shiga tayi suka É—auki hanya.
Dai -dai lokacin da garin ya kara rinewa.
Tace'' Malam bara in ƙarbo Abu ka mayar dani .
Yace ohk maza.
Da sauri ta shiga ta dauko dalleliyar waya tare da sim cart ,ta Musu transfer ta fito.
Napep É—in ta faÉ—a suka É—auki hanya.
Wani gagarumin iska ya taso mai tsananin ƙarfi wanda yasa mai napep ɗin samun wuri yace. "Gaskiya bazan iya tafiya cikin wannan iskan ba, Hajiya tafiya cikin iska haɗari ne.
Fada ta rufeshi dashi akan yaje a'haka zata bashi ko nawane.
Yace ba kuÉ—in ki nike soba lafiyana nike mawa, dan haka sallamani kawa i dama kusa da gida nike.
1k tazaro ta jefamai tare da fita ta fara tafiya tana kama mayafinta da iska keta son janyewa.
Sadeeq kam saida ya mila yasha iska kana ya tashi ya watsa ruwa yace ma Ammi zaije ya dawo.
Tace to Dan Allah kabi A'hankali kaga iska da alama ruwa zamu samu,kuma karka nuna mata komi ko a fuska kamun wannan alfarmai.
Yace shikenan insha Allah.
Fita yayi da machine din ya É—auki hanyar gidan Nene.
Ganin wani irin iska da ake ya sashi zaro glass ya toshe idon shi dashi tare da fara tafiya cikin natsuwa.
Cikin tashin hankali Amnah ke É—agama masu abun hawa hannu Amma kamar an'hanasu tsayawa, kowa sauri yake, sai masu mashina ita kuma bata iya hawa ba.
Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un tace lokacin da ta doso ta wani titin da babu yawan mutane akai Ta fara tafiya .
Sadeeq kam ganin yayyafin da ake ya sashi ƙarama machine dinsa gudu ,yana gab da cimma unguwar su Nene ya ga wata babba mota ta tare hanya da alama matsala tasamu ga mutane nata jira sai faɗace -faɗace ake.
Tsaki yayi ganin yanda ruwa yaketa ƙara karfi duk yajike.
Kawai ya karya wani lungu ya fara sheka gudu duk da yason yayi dogon zagaye.
Amnah kuwa tashin hankalin da take ciki ba a magana, ga wayar ta a hannu, ga rashin abin hawa, ga rashin mutane, a titin, ga rashin faÉ—ama iyayenta, hakan ya sata dana sanin fita.
Cikin sauri take tafiya ruwa nata jiƙa jikinta yayin da shadda jikinta tabi shape ɗinta ta lafe har shatin pant ɗinta kana gani, saboda bata sanya ondie.
Wata motace fara ta sheko da gudu har ta wuce kuma tayo baya da gudu tasha gaban Amnah.
Wasu matasane guda biyu da ganinsu babu tarbiyya ko ƙadan a tattare dasu duba da shigar da sukayi da kuma askin dake kansu.
Cikin muytya yan iska ɗaya yace haba "Baby mai kayan daɗi bai dace kamarki kina yawo da ƙafa ba ,haka ai sai duniya ta tsinemuna mu bayin mata, Dan Allah ki an'taya motana in wullah dake duk inda kike so.
Cikin faÉ—an da yazama halinta na rashin ganin kowa da kirki yasa ta fara musu masifa .
"Ubanwa zaku ɗauka da wannan gwarama motar taku yan iska , Sai wari kukeyi, kudai kam daganin ku yayan matsiyatane ,inba Akuyanci ba daga ganin mace sai kufara binta? ɓaccemun da gani ko in laftamaka mari , Da Wata shegiyar fuska taka ƙatuwa Kamar giginya.
Cikin bakin ciki da takaici É—aya yace Bashow an:tayama shegiya a yau zakison kin faÉ—o hannu mai fuska giginya, zakison komi namu ma siffar giginya gareshi yar iska.
Tsaki tayi tacigaba da tafiya cikin sauri.
Da sauri suka rufe motar su suka fara binta, É—aya yasa hannu ya jawo mayafinta data rufe jikin ta.
Tashin hankali wanda ba'asamasa rana tashiga lokacin da taji hannu É—aya bisa mazaunan ta.
Ihu ta saki tare da cire takalmanta ta fara kwasar gudu.
Baya suka rufamata suna tika gudu cikin ruwa.
Tana shawo wata kwana taji tayi ƙaro da wani katon dutsi,take ta faɗi a wajen ƙafar ta tayi wani mahaukacin buguwa.
Dariya suka saki suna biyota tare da gyara wandunan su É—aya harda cire belt É—in shi.
Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un tace lokacin da tayi ƙoƙarin tashi amma ta kasa, haka ta fara jan ƙugunta tana matsawa suna binta tare da wata shedaniya dariya da suke saki.
Daga nesa ta cikin farin glass É—in shi yake hango abinda ke faruwa duk da baigane ko wacece ba.
Ganin yanda suketa binta yasa ya ajiye machine É—ina sa tare da takowa a hankali cikin ta fasa zuciya da kuma bacin ran da yake ciki dana abinda mazan zamani suke aikatawa mata wato fyade.
Hannaye Amnah ta haÉ—e waje guda tana rokon su akan su barta zata basii duk abin da suke so.
Dariya ɗaya yayi yace ga abinda muke so nan. ya faɗa yana nuna jikinta tare da riko rigar ta daga ƙasa.
Cikin ta fasa zuciya sadeeq ya lallaɓa ta bayansu tare da musu wata kafurar shaƙa.
Cikin tashin hankali sukeso su juya dan ganin wake masu wannan abun amma kamin sukai ga ganin fuskar shi ya gwara kansu, ihu suke sosai dan gabaki É—aya kawunan su juyawa suke.
Amnah ganin Allah ya kawo mai cetonta duk da batason ko waye ba hakan yasa ta lallaɓa ta mike A'hankali tana ɗan gyasa ƙafa, ta ɗauki kwalin wayar ta da yasha ruwa ta ciro wayar tasa a leda da sim ɗin tasa a rigar ta tare da zubar da kwalin.
Mayafinta ta fara sawa tana tafiya tana jan ƙafar da takejin kamar zata cire.
Saida ya basu Azaba son ranshi yaga sun jigata ba tare da sun ganshi ba, kana cikin zafin rai da ƙunar da zuciyar shi kemai ya jasu keeee har zuwa cikin wata ƙatuwar kwalbatin da keta ambaliyar ruwan da akai .
Cikin ɓacin rai ya tausa kawunan su ciki sosai sai da ya tabbatar da sun sume kana ya sakesu ya juya..
Cikin ɓacin rai yake tafiya yana sakin tsaki.
Ta gaban Amnah yabi ya wuce cikin sauri.
Wani irin faduwar gaba taji ta saukar mata lokacin da ya shayata ya wuce.
Har ya hau machine ya tada zai juya kuma ya juyo da fuskar shi dan yimata gargadi.
Karaf idonsu ya sarƙe dana juna lokaci guda bugun zuciyoyinsu ya ƙaru.
Baki ya buÉ—e zai magana kuma ya fasa yana cije lips É—inshi.
Amnah ganin yana ƙokarin juyawa yasa cikin sauri tace ƊAN DAKO.
banza yayi da ita ya kyale tare da tada machine É—insa ya fara tafiya. zuciyar shi na fad'amai bai kyautama mahaifiyar taba in yabar mata É—iya a wannan yanayin duk halaccin da tamai bata can-canta ba, uwa uba yaran da keson keta mata haddi duk da baisani ba ko suncimma buri ma oho.
Afusace ya juya machine ɗin har zuwa inda Amnah take tsaye ,dan tsayawar da tayi da niyyar mai magana ƙafar ta kasa motsa wa.
Hawaye ta share tason yau ita kashinta ya bushe.
Afusace ya tsaya gaban ta cikin tsawa yace "wuce muje.
Sosai ta samu kanta da shakkar shi cikin sanyin murya ta nunamai ƙafar taa da tayi sasur tace" bana iya tafiya.
Wallahi zan tafi in barki duk abunda zasu miki su miki, Tinda kafiya ne dake ,wato kin iya biyo Centre da ba mutane amma baki iya ƙare kanki ba ,to ki wuce mu tafi.
Da sauri ta cira ƙafar ta ɗaya mai lafiya, tazo cira mai raunin ji kake tim tayi wata mahaukaciyar faɗuwa.
Ihu ta saki tana yar fe hannu.
Kallonta yayi ganin da gaske dai take bata iyawa.
Wajen yabi da kallo ganin babu alamun abun hawa gashi in yatafi baison yazai bar taba tinda amana suke hannushi, hakan yasa ya cije baki tareda fadin kizo ki hau machine É—in nan.
Da kyal ta dafa kasa ta mike tace "wallahi ban iya ba kaji na rantsema bantaɓa hawa ba.
Tsawa ya da kamata tare da cewa wallahi tallahi zantafi dana kilga ukku. ukku biyu...
Wani irin tsalle ta daka ta faɗa kanshi tare da cimamiyoshi da mugun ƙarfi .
Azabure ya kalleta itama shi take kallo ga ruwa na dukan su.
Kallon juna suke sosai babu ko kyaftawa kuma kowan ne da tinnin dake ranshi.
Cikin mutuwar jiki da sanyin murya" yace zaki taka nan zaki hau.
Da sauri tayi yanda yace Amma mai makon tayi zamanta hakanan kawai tasa fararan yatsunta ta sargafo dasu ta wajen cikin shi ta rike gam tare da kwantar da kanta a bayan shi dan in'tace ta kalli hanya zata na ganin jiri.
Innalilli wa inna ilaihi Raji'un yace lokacin da yaji.....
Alhamdulillah nagama free.
Maiso ya 300 ne kacal.
Hmm karku bari abaku labari.
Ku tuntubeni ta wannan number dan neman ƙarin bayani
07038-4234-51
Akwai lagwada cakwakiya🥰
Zallar soyayya da babu algus.
Wayyo dad'i 😅😅🥰🥰🥰
5/18/22, 09:34 - MY MTN 2: *Littafin🌹DAN DAKO🌹 na kudi ne biya ki karanta cikin Aminci. Biya 300kacal to 0006454115 Amina Dahiru jaiz bank,or MTN card to this number 09165832002. then send the evidence of payment