Showing 48001 words to 51000 words out of 94971 words

Chapter 17 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt

09 Feb 2025

17208

haka zasu shiga tashi hankali, Ya Allah ka araman tsawon ran zama da iyalina.


Ahankali ya dafata suka kakkamashi ya mike a duke yake tafiya kamar tsoho suka fita...


Suna isa kofar gidan Ammi ta fara shiga kana mai napep ya taimakamai ya shiga.
Amnah ta rufe gidan tashiga gidan su fatima tace musu zasu Asibiti mijinta babu lafiya.


Sosai Maman fatima ta jajantamata da addu'a Allah yakara lafiya mai amfani..


Fitowa tayi suka faÉ—a Napep din suka doshi hanyar Asibiti.
Suna zuwa kai tsaye Emagency suka nufa.


Kudin farko da aka fara cazata 20k dan sun lura ciwon nashi mai girmane.


Fada suka fara akan ba akawoshi da wuri ba.


Anan Ammi ta musu magana akan basu son da raunin ba su ma.


Anan suka rubuta takarda da zasumai aiki washe gari da safe dan sai yasha magani. kana suka miƙa musu.


Karɓa Ammi tayi ta duba batason sadda ƙafafuwanta suka fara rawa ba.


Amnah mah ƙarba tayi ta kalla .
kuka tasaki tare da buga kanta ga Bangon É—akin ta fara salati...


Ina zasu samu wananna maƙudan ƙudin da suka kai daraja Million ɗaya da dubu ɗari biyu ,innalillahi wa inna ilaihi Raji'un tace tana sake karfin kukan ta.


Agaggauce ta fito daga asibitin tare da samun Napep tayi gidan ta .
Tana zuwa bata shiga ba ta fada gidan su fatima, tare da faÉ—in tana neman Alfarma a haÉ—ata da masu sayen kayan daki.


Maman fatima kam batayi kasa a gwiwaba ta hadata da wata Yayar ta dake dillancin kayan ÆŠaki.


Cikin lokaci matar tazo da wasu samari.


inda Amnah ta É—aure fuska tare da faÉ—in bata yarda su shiga É—akin taba su tsaya ta fito.
Anan sukayi tsaye waje.


Itakuma ta buÉ—e
Gidan suka shiga ta rufe.


Ɗakinta suka ƙarasa anan matar ta saki baki tana kallon hamshakan kayan da aka ɗora ma wannan ɗan gidan.


. Amnah tace haba Hajiya kinyi tsaye uzurifa garan, dan Allah kiyi abinda ya kawoki.


Matar tace "to nace nawa zaki sai dasu''?.


Amnah tace dan Allah ba wannan ne gabana ba kibani ko nawane.


Ganin banza ta samu yasa Hajiya cewa" zanbaki dubu É—ari takwas yayi.


Amnah tace "eh bani ."


Tace ai sai dai in'miki transfer gaskiya ban fito da kash ba ,kana dole akwance kayan kinga banamu bane na nan...
5/18/22, 09:34 - MY MTN 2: *Littafin🌹DAN DAKO🌹 na kudi ne biya ki karanta cikin Aminci. Biya 300kacal to 0006454115 Amina Dahiru jaiz bank,or MTN card to this number 09165832002. then send the evidence of payment via 07038423451* ğŸ¤ğŸ™ğŸ¤²




Alhamdulillah! Alhamdulillah!!
Yan uwana mata ina kuke ku malmatso ga wanni sirri da nike son baku, ita ya mace sai da kamshi, ina macen da take ganin izgili da wulakanci da ake cewa maza nada shi, hmmm yar uwa to inkin kasance a haka da alama akwai ayar tambaya akanki. Tambaya ta ta farko gareki da wane irin turare kike amfani a jikin ki ?,da wane irin turare kike turara gidan ki,shin dawane irin turare kike Zukunni, hmmm to matso kusa kiji yar uwata.
Shi kamshi Annabi muma ya faÉ—a abin sone,kuma Abune mai sanya natsuwa da girmama ma'aboci shi , Da Yawon son kusantar sa.
Duk kan wulakanci da izgilanci na maza akwai turaran da zai miki maganin sa da izinin Allah,ba boka ba malam,wanda zai karkato da hankalin mijinki akan ki ku samu fahimtar juna.
Ko kin son kamshi na dakusar da fitinar É—a namiji yar uwa? kigarzayo ki kwashi rabonki ga shaharariyar yar mai Dugurin nan mai suna UMSAD INCENSE ,Mace mai kishin mata da son Fiddo martaba mu.
Nayi Amfani da turaranta naji masifar daÉ—in da yasa nakasa barwa raina. Nace bari in yaÉ—amuku dan kowa ya mallaki nashi cikin farashi mai sauki.
Da fari bari in zayyano muku su kamar haka.👇


Maleek Al'oud
Royal kush
Cous-cous
Kajiji
Original sandal
Sandal flex
Sandal bange
VIP mix
Hawi
Al'oud
Kindikay
Danal banat
Darot
Habil
Gaf-Gaf
Sirrun nisaa'i
Sandal chips
Kwalacca
Humra black and body milk
Attractive humra.


Yar uwa zanmiki Dallah- Dallah.
Akwai turaran da zaki sanyama kayanki .
Misali! kisa kabasa kiturare kayanki .
Akwai humra da bazaki sataba sai zaki turaka.
Akwai turaran kaya ,na jiki, Dakuma na ɗaki. Akwai kwallaca sirri, amma bama badata gaskiya sai ga wanda baida kishiya , Dan muddum kina amfani da ita tofa gabaki dayan hankalin mijinki akanki zai dawo,Dan yana juyo da hankalin namiji akanki baki ɗaya ,zaki zama shalele Baby, Akwai sirrin nisaa'i. hmmm Dagajin sunan kason na dabanne,na baki sati ɗaya ki gwada ki gani Hajiya ta, tsugunno ake akai ga mai buƙata ya tunɓe mu ta wannan layin 08028827241 karku manta UMSAD INCENSE mune na ɗaya.
Muna aika kayan mu duk inda kuke.
Kamshin jiki martaba mutum....
🅿ï¸3ï¸âƒ£5ï¸âƒ£&3ï¸âƒ£6ï¸âƒ£


Amnah tace" ba damuwa zan'biki gidan ki yanzu in ƙarba, amma kayan kibari gobe da yamma kana na dawo sai akwance, akwai buƙatar in kwashe kayan dake ciki.


Cikin murna sosai Matar tace "baki da matsala, zanma iya barmiki su har nan da sati biyu ko wata É—aya.


Amnah ta hau godiya. daga nan suka rufe gidan suka fita..


Bayan sun isa Amnah ta tsayar da napep ɗin ta shiga, matar ta ƙilgomata chip ta bata.
Godiya ta mata Sosai kamar ta bata kyauta. Aguje ta fita ta faÉ—a napep din sukayi Asibiti.


Anan ƙofar ɗakin da yake taga Ammi zaune waya a hannuta sai kangawa take akunne tana saukewa cikin damuwa.


Da sauri cikin sassarfa ta isa wajenta tace" Ammi sannu ,ya mai jikin?


Hawayenta ta share tace" Da sauki Amnah.


Amnah tace" ko zan iya ganin Doctor da zaimai aikin?.
Da hannu Ammi ta nunamata office É—in likitan daya duba shi.


Da sauri ta tashi ta shiga ta gaisheshi , Tare da neman alfarma afara karba kudin hannuta gobe zata ciko sauran.
Kasancewar sa dattijo kuma mai kirki yasa ya Amince.
Anan ya faÉ—amata inda zata kai .


Bayan taje takai suka bata Takada shedar biya ta dawo, ta dafa gwiwar Ammi tace'' Dan Allah Ammi mu ki share hawayen ki ,ki É—auka Amma Dee aiki angama, yanzu nariga da na biya dubu dari takwas insha Allah gobe zamu cika sauran..


Cike da mamaki Ammi ta mike tsaye tace'' Amnah kina nufin kinbiya kudin Aiki?


Kai ta jinjina tace "eh saura dubu dari hudu suma insha Allah zanbiya gobe.


Wata irin Runguma Ammi ta mata ta na sakin kuka tace'' Allah kenan! in yayika makaho sai ya baka É—an jagora, Daya kwantar da garkuwan mu sai ya bamu jaruma, Allah ya miki albarka ya Miki tukuici da aljanna , Amma Amnah ina kika samu wayan nan kuÉ—aÉ—an masu yawa bayan ya faÉ—aman Halin da kuke ciki?.


Amnah tace "Wallahi kayan É—akina na siyar.


Ido Ammi ta zaro tace anyi haka Amnah, to ke da mizakuyi Amfani?.


Cikin natsuwa tana murza yatsun hannuta tace" haba Ammi, komi namu zai kare ai zamu iya sadaukar dashi dan lafiyar sa,in Allah yasa gaba ya tashi ya samu sai ya mayar muna ko.


Cikin yabawa da maganar ta Ammi ta ÆŠagamata kai tare da dafa kanta tace" Amnah kin cika yar Halak,Allah ya Miki albarka ,ya baki abinda kike SO duniya da lahira...


"Ameen" Amnah tace " Tare da miƙewa ta tura dakin da yake , Anan ta ganshi kwance sanɓal idon shi sama yana kallon fanka.


Da sauri ta ƙarasa wajen shi ta zauna bakin gadon tare da riko duka hannayen shi ta rike tace'' Sannu Dee, ya jikin naka?


Juyowa yayi gareta da murmushi akan fuskar shi yace "Alhamdulillah ƙanwata ,ya kinci abinci kuwa?


Ta É—agamai kai alamar taci.


Cikin damuwa yace'' Amnah aiki zasumun, kuma da sassafe, Tinma yanzu sun hanani cin komi ,Babba damuwata bamu da komi ,kuma nason dole aikin yayi tsada ko...


Murmushi tayi cikin son kwantar mai da hankali tace" kasan mene Dee? nima nayi tinanin aikin zayyi tsada, to duka abinda zamu kashe 25k, kuma kaga Alhamdulillah ina dasu , Dan haka ka kwantar da hankalin ka kaji ? Fatana Allah ya fiddoka lafiya mu rayu cikin Aminci..


Cikin jin daÉ—in lafazinta ya ÆŠagamata gira guda yana lumshe ido da sakin yalwataccen Murmushi mai tafe da ma'anoni da yawa...
Ahankali suke fira har mangari ta kawo kai ,ta mai Alwallah ya tada sallah daga kwancen da yake .
Itama Sallah tayi kana tafito.


Tazo tace ma "Ammi ta shiga ciki zataje ta É—akko carfet da abinda za suci.


Kai Ammi ta ÆŠagamata tana yabawa da kulawarta akan su...


Bayan taje gida taga abincin su daya rage babu yawa, hakan yasa ta biya gidan Ammi dan dama key É—inta na wajenta ,ta É—akko wanda takai musu basu ciba ta nufi Asibiti.


Bayan taje ta samu ta zubama su Ammi abinci sukaci suduka sukayo Sallah isha..


Ammi tace" Amnah ki koma gida in kwana dashi nan.


Ido ta zaro tace "Ammi mizanyi agida, A'a kwara mukwana anan mufa kadai gareshi, babu abinda zanyi da safe naje.


Ahaka sukayo zamansu suna É—an fira sama- sama.


Karfe ukku na dare Amnah ta tashi tayo alwallah ta fara Sallah, Tana neman Allah yataimaka musu a mishi aikin cikin nasara, yasa a shiga lafiya a fito lafiya .
Addu'a take sosai tana kuka tare da neman gafara Allah da yafiyar sa akan watsi da tayi da marta ba mijin ta.


Jin shasheka kuka'n ta yasa Ammi ta tashi itama tayi alwallah suka zo suka hau Sallah.


Tin daga sadda ta tashi yake kallonta, dama shi ba bacci yayi ba.
Sosai abinda tayi ya burgeshi hakan ya Ƙara mata matsayi sosai acikin zuciyar sa...
Suna zaune a haka har akayi sallah Asuba, sukayi sallah suka fara azkar.


Karfe shidda wasu nursing maza suka shigo É—akin da wani gado na daukar marar lafiya.



Sosai jikin Amnah ya ɗauki rawa , Mussaman da taga ya zubamata ido ko kyaftawa bayayi, ga wata rama da yayi sai wani irin hanci zir kamar kuɓewa dan tsawo .


Ganin wani nursing zai samai riga yasa da sauri ta ƙarasa wajen ta karɓa tare da faɗin" ku bamu waje mu mishi Addu'a ko.


Fita sukayi Ammi ta matso ta mishi Addu'a sosai da fatan nasara kana ta fita.


Hamrat ta miƙo mai hannu tace "Baby Allah yabaka lafiya .


Kai ya ÆŠagamata ahankali yace "Ameen Baby'n Baby.
Fita tayi tana É—agamai hannu.


Hakan ya karyar mai da zuciya baison sadda hawaye suka zobomai ba,yana ganin wata kil bazai tashiba,shikenan yayi bankwana da ahlin sa.


Amnah mah kuka ta saki ganin yanda yarinya ƙarama jikinta yayi sanyi.


A'hankali ta rufe É—akin tare da zama gefen shi ta kama hannu shi ta rike, tare da ÆŠaura kanta bisa hannu ta fashe da kuka sosai.


Tace "Abokin faÉ—a, Abokin sabuwar rayuwa, Abokin mutuwa insha Allah...


Cikin ƙarfin hali yake jinjinamata kai ,siraran hawaye na bin gefen kumatunsa..


Amnah tace" in rokon Allah Mai rayawa mai kashewa ya fitomun da mijina Lafiya, Allah yasa yanda aka shiga da kai lafiya a fito dakai Lafiya,ina rokon Allah da yabani aran rai da lafiya na kula da ragamar rayuwar ka Dee har karshen numfashi na.




Ameen -Ameen yace natare da ƙara haɗa hannuwan su ya matse Sosai.


Kwankwaso kofar akai haka yasa A'hankali ta É—ago da kan shi ta sa mai rigar.


Bata tsaya komi ba ta kai bakinta wajen na shi, tare da Tura halshenta ciki ta fara bashi wani irin zazzafan kiss mai tsayawa azuciya.
Sosai take juya halshenta a cikin nashi tare da gangarowa kan Laɓɓan shi masu tsanani taushi ta tsotsa sosai.
Cikin mutuwar jiki ta zare bakinta ta sumbci goshin sa, da sauri ta juya baya tace" A fito Lafiya Baby ,tana faÉ—in haka ta ficce tana share kwallah..


Yah ALLAH yace lokacin da tafita, yaso yana da ƙafar da zai samu damar rikota, Sosai abinda tamai ya tsaya mai A rai,Abun ya masa masifar daɗi,Wani irin nishaɗi yaji yana tsintar kanshi ciki.


Ahankli wayan da zasu tafi dashi suka shigo, suka azashi akan gadon suka fito dashi


Ta gaban su Ammi suka wuce dashi yana ɗaga musu hannu sun ɗaga mai, har suka shige wata ƙofa dake nesa da ɗakin da aka ajiye shi Sosai..


Amnah naganin sun shige ta rushe da kuka tare da rugawa É—akin ta daura Alwallah ta fara Sallah tana kai kukan ta ga Allah, a kan ya tada Dee É—insu lafiya.


Suna zaune su duka babu wanda ya sama bakin shi wani abu, har karfe tara ba'afito da shiba.


Iya tashin hankali sunshiga sai wajen 10 kana sukaga an nufo É—akin dashi yana kwance kamar gawa akan gado.


Da wani irin gudu Amnah ta ƙarasa wajen tare da tare gadon tana kallon shi .


Shikam bacci kawai yake bai masom duniyar da yake ba.


Suna shiga É—akin Ammi ta shigo tana faÉ—in ya'ya Doctor da fatan anyi aiki cikin nasara?


Cikin fara'a sosai yace" Alhamdulillah Hajiya, Duk da aikin yaso bada matsala Amma Allah ya magance ta ,Anyi cikin Sa'a, sai fatan falfaÉ—owar sa lafiya insha Allah.
Inaso daya tashi A kirani.


Kai Ammi ta É—agamai suka ja gadon suka fita.


Duk rurrufe shi sukai suna kallon yanda yake bacci hankali kwance, amma daka kalli fuskar shi kason yaji jiki.


Ammi tace ma" Amnah taje gida tayi wanka, sai ta haÉ—omai Tea in ya tashi ya sha.


Kai ta jinjina mata kana tafita tana rike da hannu Hamrat suka hau napep.


Bayan sunje gidan ta dafa musu indomie suka ci ,kana ta É—ora ruwan tea da yasha kayan kamshi.
Bayan ta gama ta juye a Flak's mai kyau, ta silalamu su taliya ,dama tana da sauran miyar jiya hakan yasa bata daÉ—e ba ta haÉ—a komi ta yima Hamrat wanka suka tafi.


Suna isa suka iske Ammi zaune ta buga tagumi, ganin har karfe É—aya amma ko motsi bai ba.


Amnah ta zauna tare da haÉ—ama Ammi tea mai kauri ta bata tasha .


Sallah sukayi suka samu wuri suka zauna suna Addu'a tashin shi lafiya.


Basu jima da zama ba ya fara motsa kafar sa, hakan yasa har rige -rige suke wajen isa inda yake.
A hankali yake buÉ—e jajayen idanuwan shi har ya budesu fess akan ahalin sa.
Kallon su yake É—aya bayan É—aya.
Cikin sauri ya fara yunƙurin tashi.
Hakan yasa Amnah saurin dafe kafaÉ—un shi tana gilgizamai kai tace" A'a Baby Dee! ka kwanta Dan Allah, kaga yanzu suka fito dakai.


Ahankali yake motsa bakin shi yana jin ƙafafuwan shi da kugunshi kamar ba ajikinshi suke ba.
Yace Amnah an'mun aikin ne?
Murmushi ta saki sosai tace" an maka cikin ma nasara kuwa Alhamdulillah.
Idon shi ya lumshe bacci na fizgar shi..


Amnah ta fita daga É—akin ta faÉ—a office É—in likitan ta fadamai ya tashi.


Atare suka shigo anan su Amnah suka fita .
Sai da ya dubashi ya tabbatar da komi lafiya kana ya basu umarnin su bashi tea yasha.
Da sauri Amnah ta shiga haÉ—a mai.


GIDAN HAJIYA NENE.


Zaune take palonta sai kaÉ—a kafa take cikin tsananin bacin rai, tare da É—aukar waya ta fara kangawa a kunne.


Tanajin an É—auka ta fashe da kuka tare da faÉ—in Fulani! Fulani!! nace Fulani so nawa na kiraki?


Kasancewar wayar speaker take yasa Mamy sauke ajiyar zuciya tace'' Nene ina wuni?


Nene tace bansan shi ba, bansan gidan uban da yayi ba, Saude.


Yau ko kinki ko kinso sai jia karya dokar ki, inkuma kikace kikawoman ƙabali da'ba'adi wallahi zankwashe miki albarka. Yo in'bama wulakanci na yaran zamani ba ni dana haifeki kike bani umarni, kin hanani zuwa ga jikata.
Kwana na nawa banga Kwandon Sukari ba,ke kinson tinda ya É—auke kafarsa daga gareni kila fushi yayi dani , Dan haka natafi yanzu zani ÆŠAN Larai ya kaini..


Ajiyar zuciya Mamy ta sauke tace bakiji ba Nene.


Afusace tace bani ba ƙaraji kam har abada, munafuka kina nan ƙasar waje kinata cika kina tumbatsa, amma kin watsar da rayuwar tilon yarki ,Kin rabani dasu inata rayuwa ni kaɗai kamar mayya,to hukuncin yaci ubansa.
Ta datse kiran tare da tashi ta ɗakko mayafi ta sanya takalma, taja ƙofar palonta ta rufe.


Tana gama rufewa ta yanko da gudu harabar gidan hannuta bisa kai tana ihu tana na shiga ukku ÆŠAN Larai, tashi ka kaini unguwa .


Tim kakejin ya faÉ—o daga saman table É—in da yake kai yana bacci.


Nene tahau yarfa hannuwa tace" Yanzu dama aikin da aka kawoka kenan kayi ,shege ka barman gida awatse sala yara suzo su tsinkemun yan shukoki ,to tashi mutafi nace...


Cikin yanayi na mai bacci yace "wallahi Nene kiji tsoron Allah, ina bacci zakizo dawani mahaukacin gudu ki tashe ni ,nasama wuta ta tashi É—ak....


Wani irin mahaukacin bugu taima bakin shi da takalman ta.
Tace munafuki É—akin uwarka wuta zata tashi, ba dai nawa ba, tsoron Allah kuma ai'nafi ubanka wallahi ,hauka kuma kaine zakayi shi tuburan ma kuwa,shege da baki kamar motar icce...


Tashi tsaye yayi yana ƙokarin nufar mota.


Ta dakamai tsawa tace" maza zoka wanke wannan kodaddar fuskar taka da take ta maiko kamar sabon k
Ƙuli ,ka kuma durje ƙaton bakin ka kar kasama mutane cuta.


Kan shi ya taho yana gilgizawa ya wanke fuskar shi, kana ya tashi yanufi ƙofar still yana gilgiza kai.


Nene tace yo ƙadangarema da abun yake halittar shi yayi yagama sai kai da kayi haye,shegen kai ɗan mitsitsi kamar furar naira goma, Allah yasa ya cire sai kason ka ari halin ƙadangaru...


Dariya ya saki yace naji dai.


Shiga motar tayi suka fita ya rufe gidan suka É—auki hanya.


Ahankali take kallon hanya har taga masu saida zogala da ƙuli -ƙuli tace'' kai tsaya insai ma yar jikallena in naje in kwaɗamusu ita da kwandon Sukari, Allah sarki kwandon sukari I milisu Wallahi (I miss u)


Dariya ÆŠan Larai ya saki yace" Nenes ina sonki zan turaki kabari Wallahi.


Banza tayi dashi ta kyale dan zuciyar ta bugawa take.


Bayan sun saya ya É—auki hanya har korar gidan Amnah.


Anan sukaga gidan rufe.
Nene tace ikon Allah, Ƙudurar sama liman da Wawan zama ni Aminatu ina yar nan ta tafi?...


Fatima ta yanko da gudu zata shiga gida taga Nene da ƙaton dutsi tana kiran kwandon sukari ku buɗeman na kawomaku zogala.


Fatima tace "Inna ai basa nan suna Asibiti mijin ne bai lafiya .


Wata irin juwa ta fara ƙoƙarin kada Nene, da sauri Ɗan Larai ya tareta tare da buɗe mota ta shiga.


Cikin kallon Ruwa bebie tace "uban mi kikace yarinya?...


Dariya fatima ta saki ganin yanda Nene ta juya idonta tace "ÆŠan fulanine baya da lafiya ,shine suka tafi Asibiti, batama jima da tafiya ba tazo ta É—auki kayan Abinci.


Kururuwa Nene tasa ta É—akko wayar ta tana latsawa, hawaye suncika Mata ido ko gani batayi. Ta sake turo idon gaba amma ta kasa gano number da take so ta kira...


ÆŠan larai dake tsaye ya rike marfin motar yana kallon wani waje .


Nene takaima mahaukacin bugu a kirjin shi tace "kana gani ina ta wahala, munafuki bazaka iya kama man ba, amma kai kam anyi É—an asara wallahi..


Yace wai nenye yau sai kwasheman albarka kike minai maki?


Tace ubanka kamun! ƙarba ka kiraman Saude.


Ya karbi wayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login