Showing 21001 words to 24000 words out of 94971 words
Chapter 8 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt
maza subaki mazajen kudi, ki zauna gida kiga abun da ya samu..
Amnah tace Bily ina masifar tsoro wallahi, ni dai kamar bazan iya ba.
Tsaki tayi t afara tsaramata yanda zasu kasance.
Bily tace kinga wannan cousin ɗinane ɗan gidan Abdul mutallab ne sarki maici yanzu, shine babbn ɗansa amma baya da buƙatar hawan sallah, shiyasama na samu dakyal ya biyoni dan sauran yan uwansu duk suna bisa dawakai yanzu haka, Amma shikam duk ya ɗauki abin bidia,gashi Babban likitam kwalwa Amnah, Gaya baya ko magana Saboda jinin Sarauta dake yawo jikin sa.
Murmushi Amnah tayi tace" kinson duk yanda namiji yakai ga aji ni ya mace nazarce shi, dan haka koda yaÉ—an hada wasu abubuwan amma ba duka ba bazan iya tunkarar saba , Dan haka kibarshi kawai indai har lafiyayye ne to zai kawo kanshi...
Dariya Bily tayi tare da faɗin shegiya ƙawata kingano inda na dosa kenan, kina wuta ,wato ashe kinama sane da tarkon ki ya kama kurciya kenan, to wallahi kintafi da bawan Allah, Dan ba kiji yanda yake gamani da Allah akan inzo in karɓi number kiba.
Amnah tayi Murmushi tace wlalhi duk da kinfadaman Prince ne amma som baiman ba, sai dai zanyi malege da shi, shima fa dan Aure ne da nike so.
Tsaki Bily tayi tace" tin school nike fama Dake akan ki fara harka kisamu kudin da zaki magancema wani matsala shi bama Taki ba,bawai kullum gida kice abani dubu dari biyar ba Abaki ukku ace kiyi hakuri wallahi Amnah yaci ace wayewar ki ta zarce wannan gida dancin da kike,mene ma matsala daga shan mint?.
Harara Amnah ta zubamata tace Wallahi ko abinda kike turomun inajin daÉ—i ne a lokacin da nike kallo, amma da lokacin ya shiÉ—e ina fadawa duniyar dake cike da tashin hankali, abun baza ace komi ba Bily, kawai iyayena su taimakamin suman aure, danshi Abba babban burin shi da ya dawo yasamoman aiki infara zuwa Asibitin shikenan.
Amma ke kanki kinson yanda nike da ajin nan mijina ya ganni a banzace aiko ajin ya tashi a banza.
Bily tace "to yanzu kina da masu zafi ko in turomiki?
Amnah tayi shuru sai kuma tace kituroman amma wallahi Bily.
Dariya Bily tayi tace" bari intashi in wuce yana jira na.
Da sauri Mamy dake tsaye jikin kyaure ta zarce ÆŠakin Amal hankali tashe tana yarfe hannu. Illahirin jikinta rawa yake dan Ta sauka falo taga wayar bily anata kira shiyasa ta haura takaimata, ashe rabon zataji mummunan zance. nashiga ukku kardai ace Amnah halin mahaifinta gareta, Innalillahi.
innalillahi wa inna ilaihi Raji'un, Ya Allah.
Da sauri ta É—auki wayar ta ta kira Hajiya Turai ta fashe da kuka tana bata labari.
Ciki ƙaɗuwa tace ta tsaya ga tanan zuwa.
****
Aɓangaran sadeeq kuwa bacci sukayi su duka gidan, sai da la'asar ya tashi yayi wanka ya maida shadda shi.
"Yace ma Ammi ta shiryama Baby ya kaita wajen Mamy.
Da to ta amsa ta shirya Hamrat tare da fiddo masu kulolun data zubama Mamy abinci tace yakai mata.
Yana dawowa suka É—akko hanyar har gidan Mamy .
Suna ajiye machine Hamrat tace ''Baby kalli bishiyar mango Dan Allah ka kaini in tsinko.
Yace aa Baby ba nawa bane ,babu kyau kinji sai ka tambaya.
Kai ta É—aga mai tana bin mango din da kallo.
Hanun ta ya kama suka ƙarasa bakin kofar.
Bayan ya kwan-kwasa kofar Mamy dake zaune idonta ya kumbura dan kuka .
Tasowa tayi ta buɗemai duk tinaninta Hajiya Turai ce ta ƙaraso.
Gaisawa sukai ta kama hannu Hamrat ta rike tana mai tambayar lafiya Ammi.
Gaisheta Hamrat tayi tana faÉ—in lfy klau tana gaidaki gashi tace akawomiki.
Kulolin ta karba tai ta godiya tare da cewa" Sadeeq kayi kyau sosai Amma Autata tafika kyau, kushigo ciki kuci abincina nima mana.
Yace A'a Hajiya zan jirata inta fito mutafi.
a koshe muke yanzu mukaci abinci.
Mamy tace ta shikenan Hamrat ina barkana da sallah ?
Baki ta rike tace "kai ai Baby ya hanani karɓa, saboda yankema mutum hannu ake ,kinga aka yankeman hannu dami zanci Abincin ammi nah.
Taƙarasa cikin Alhini tare da duba yatsun ta.
Dariya tayi tace hakane Babu ma wanda ya isa ya yanke miki hannu insha Allah, zaki kwana wajena?..
Kai ta gigiza da sauri tace" A'a Hajiya bazan iyaba gaskiya Baby muje gida.
Dariya many tayi sosai ta rungumota jikinta tace karki damu bazaki kwanaba amma wani lokacin zakizo ko.
Kai Hamrat ta Daga mata .
Mamy ta É—ago ido ta kalleshi dai -dai lokacin da ya kalleta yaji gaban shi ya faÉ—i.
Ganin yanda idonta yayi sasur .
Da suri yace Hajiya lafiya dai naga kamar kinyi kuka Allah yasa dai bawani abu ke damunki ba.?
Murmushi tayi tace "aa karka danu Sadeeq babu komi.
Yace shikenan allah ya qarware miji matsalolinki kamar yanda kike warware na mutane .
Ameen Ameen ta amsa cikin jin daÉ—i..
Yace Hamrat shiga kifito muje gidan Nene ko.
Mamy tace aa bazatajeba gaskiya, kai kaje inka dawo kwatafi.
Fita yayi yana dagamata hannu suka rufe palon Mamy ta zaunar da ita akan kujera suna fira.
Yana fitowa ya nufi wajen machine dinshi dai -dai lokacin da motar su Hajiya Turai ta turo kai cikin gidan , sukai parkin kusa da machine dinsa.
Fitowa tayi tana kallon shi kallo na rashin sani .
Gaishe ta yayi tare da tada abinshi yayi gaba.
Cikin gidan ta shiga tare da tadda mamyy zaune tana shafa kan Hamrat dake cinyar ta ,dan har tasoma sakin hamma dan Hamrat badai bacci ba..
Bayan ta zauna sun gaisa take tamabayar waye yafita a machine.?
Mamy ta bata Labarin alakar su har zuwa kawomata Hamrat da akayi yanzu.
Kai ta jinjina tana faɗin yanzu ya ake ciki game da lamarin Amnah? ,ya zama dole fa a aurar da ita cikin ƙanƙanan lokaci,inba hakaba matsala da zata kunno nan gaba wallahi sai tafi ta baya,kana in son samune abata wanda baida yawan Ahli, Amma akai kuskuran kaita gidan sarauta toke kanki sai zaman Katsina ya gagareki,Kana a lokacin ne mahasada zasuyi tsalle suyi shewa ,Alokacin ne zasu nunamiki ikon da kike faɗin kina dashi akan y'arki ya tashi abanza, Dan haka shawara ki fita ki nema ma Amnah miji.
Cikin damuwa Mamy tace nashiga ukku ni Saudat,Inaji kamar in aura mata ALMAJIRIN GIDA NA da ina dashi,koda kuwa yaro ne cen sutafi suyi AUREN YARINTA,Saboda kullum maganata ita gada wanda ta CANCANTA,Hajiya turai ina tsoron ɗiya ta ta fara mu Amullah da ƙawaye yan ZAMAN TASHA,kwara nidai in tafi koda masallacine in samo ko liman ne in auramata, da tarbiyyata ta lalace kwara ace tana AURAN USTAZ ,duk da nason halinta nason dole hankalin ta ya tashi, to Amma da in kasance kullum cikin magana TAYA ZAN GANE Wanda ya lalata Rayuwar Yata kwara ko ƊAN DAKO Na samu In bashi.
Hajiya Turai tace" wannan magana taki haka take, Dan Wallahi kyan Amnah tasamu dan gida wanda zai tausayamata ya riketa da mutunci , Wallahi Hajiya fulani da ina da Yaro saurayi dana haÉ—asu aure, Amma Allah bai bani ba sai Sudais kuma kinga ko shekara goma bai kai ba.
Mamy tace nasani wallahi ,nason fiye da haka zakimun, tashi tayi tare da ɗaukar Hamrat tace bari in kaita ɗakin Amnah nan ƙasa nason tana ciki.
Hajiya turai tace kifa kula da yawan kebb kanta da take Wallahi, Tinda har tafara faÉ—in aure takeso to kijawota jiki kiji wanda takeso kuma ki fahimci yanayin da take tafiyar da Rayuwar ta..
Mamy tace'' insha Allah tare da tura kofar ta shiga cen ta hango Amrah cikin É—akin tana waya bakajin koda abinda take cewa.
Tana ganin Mamy tayi saurin katse wayar tare da mikewa tana zare ido.
Kwantar da Hamrat tayi ta juya ga Amnah tace'' mikike É—akine ke É—aya? kinki zuwa ki gaida uwata kuma kinyi zaune kamar mai jego ,to bani wayar ki nan in ita ke saki kebe kanki daga gareni.
Wani irin kyar ma jikinta ya É—auka tace Dan Allah kiyi hakuri bazan sakeba Yayan Bily ne ya kirani Wallahi.
Tsawa Mamy ta dakamata tace babu ke babu wannan yar iskar yarinyar, dan bataiman ba, bani nace.
Cikin ɓarin jiki ta mikamata tare da dafe kirjinta tason shikenan tashiga ukku ta lalace, gashi bata sama waya security balle ta samu saukin wani abu .
Fita Mamy tayi tare da kama hannun Hajiya Turai suka haura sama É—akin ta.
Tace dole yau in'son ma dawa take mu'amullah, yarin ya kullum waya a hannu..
Anan ta fara bincikawa contact taga number ukku ne , Daga ta Bily, saita ƙawar ta Dr fatima Bello, sai wata Khairy Barno duk ƙawayen ta ne.
Message ta shiga taga babu komi .
Har zata ajiye wayar takuma shiga gallary.
Hankali tashe ta mike tana murza ido tace" Hazbunallahu wani imal wakim, A gidana, yar dana Haifa ,Nayi sakacin da na barta tana kallon wayan nan yan iskan Vidio, kuka ta saki tana miƙama Hajiya turai wayar.
Kallo tayi taga BF ne sunkai É—ari cikin wayar gasunan babu tsari.
Hankali tashe tace Fulani in har kika bar Amnah ta ƙara wata ɗaya cikin gidan nan wallahi akwai matsala,Kuma kema zaki samu rabonki awajen Allah, kawai kinson gadon masifa tayi dan haka cikar mutun cinki da nata ki miƙata ɗakinta, ki samu kowayema indai kin yarda da tarbiyyar shi toki auramai kamar yanda musulunci yace.
Cikin kuka Mamy tace insha Allah daga nan suka shiga tattauna yanda zasu bulloma lamarin.
Abangaran Amnah kuwa safa da marwa kawai take cikin É—akin hankali tashe, tana tinanin ya zatayi in Mamy taga abunda take Ai katawa.
Tinowa da Hajiya Turai na cikin gidan ya sata sauke ajiyar zuciya dan ta tabbata magana suke, zatayi amfani da damar ta É—auke wayar ta goge komi kana ta mayar mata.
Da wannan gurguwar shawara ta samu natsuwa.
Wajen shidda saura Hamrat ta tashi tana faÉ—in zanyi fitsari Hajiya akaini Fitsari Dan Allah.
Kallonta Amnah tayi tace masha Allah, Allah yasa in na hauhu in'haifi irin wannan kyakywar yarinya, ko ina Hajiya turai ta samota.
Azahyure Hamrat tace wayyo babu zaimun duka Dan Allah zanyi fitsari.
Amnah ta tashi da sauri takamata tashiga toilet tayi ta gyara ta kana suka fito.
Suna fitowa ta kalleta tayi Murmushi tare da shafa dogo'n gashinta tace Baby ya sunan ki?
"Sunna Hamrat.*
Tabata amsa.
Amnah ta jinjina kai tana kallon tsadaddun kayan jikinta kai da gani kason iyayanta sun jiƙu da nera,Haka takeson taga yara yan gayu.
Hamrat tace "Aunty dan Allah ki kiramun Baby ya maida ni gida ,na gaji inaso inga Ammi nah fa.
Cikin mamaki take kallonta tace waye Baby? To kiyi hakuri sugama za kutafi kinji ko ,zakici Abinci ne?
Hamrat tace aa nagode.
Amnah tace to mikike so?
Cikin yarinta tace wallahi Mango Amma Baby ya cemun bakyau ka É—auka saika tambaya, nikuma ina so.
Amnah tayi Murmushi tace to "muje in tsinko miki.
Da sauri ta taso ta biyota tana murna.
Hannuta cikin nata suka fito har cikin lambun gidan.
Suna isa Amnah tayi tsalle Amma takasa kamowa dan yayi sama.
Tsalle ta ƙara dakawa amma bata kamo ba.
Hamrat tace Wallahi Aunty zanyi kuka, kiyi girma irin na Baby mana(TantaÉ—o)
Dariya tayi tana faÉ—in karki damu zakisha kinji sweety nah.
Dai-dai lokacin Sadeeq ya shigo gidan Amma bada machine din saba, Dan yabar shi waje dan kar ya yita wahala shiga da fita, Tin da Hamrat zai mayar gida..
Tsalle Amnah ta daka sai gata ta ciro wani danye, dariya ta saki Hamrat kuma tayi ihun murna.
Hannu Amnah ta bata suka kashe tace" Bari in sakeyin wani tsallan sai in baki wancen ƙaton ko?
Cikin jin daÉ—i Hamrat ta É—agamata kai.
Ihun ta yasa shi kai duban shi wajen .
Anan ya hangosu Amnah nata daka tsalle.
A gabanshi ta sake wani wahallan tsallan dayasa rigar ta mikewa farar fatar cikin ta ta bayyana, Yayin da Albarkacin kirjin tama suka daka tsalle.
Faduwa yaji gaban shi yayi sosai .
Siririn tsaki ya saki tare da nufar wajan su cikin takon isa da ƙasaita.
Baitsaya komi ba yayi sama da Hamrat tare da fadin Baby tsinko .
Cikin ihu tasa hannu ta É—akko biyu tana faÉ—in" sai Baby.
Afurgice Amnah ta kalleshi shima ita yake kallo .
dai -dai lokacin da Mamy da Hajiya Turai suka fito da niyyar yimata rakiya.
Ido suka zubamasu suna kallo ....âœï¸
5/18/22, 09:34 - MY MTN 2: 🌹ƊAN DAKO
MALLAKI 🌹
🌹UMMY AYSHA
🅿ï¸1ï¸âƒ£7ï¸âƒ£&1ï¸âƒ£8ï¸âƒ£
"""Wani Murmushi Hajiya Turai ta saki tace "Ƙawata ashe kina da Nama har gida amma kike fama da maita, to mukoma na fasa tafiyar sai nayi Sallah.
Cikin Rashin fahimtar inda magan'ganun ta suka dosa Mamy ta bita suka shiga.
Hannuta Hajiya Turai ta kama har Ɗakin Amnah na ƙasa ,inda ta isa da ita wajen window ta zuge labulan tace" kina ganin abinda nike gani kuwa? kwalwarki na faɗamiki cancanta da sukayi da juna kamar yanda tawa ta nuna man? Fulani Allah ne yakawo miki Dama har gida shiyasa ya samiki soyayyar yaron da bakison ko waye shiba, Fulani yanzu kika gama ceman zaki iya ba ALMAJIRIN GIDA'nki Amnah,To tinda baki dashi amma ga ƊAN DAKO ko?
Dan haka kinga shine kawai zai rike mutunci y'arki, Tinda kin yaba da halayyar shi ,kuma kin yarda ba macuci bane, Tinda har yataɓa ɗaukar ta suka wulla wani wuri yakuma yimata Hukunci akan Abinda tamai ya maidomiki abinki,Abu na biyu kuma ga shi baya ɗaukar raini ,Na tabbata bazai yarda Amnah ta dinga mai abinda take so ba ya kyale ta.
Darasi na ukku da zata É—auka shine zama da talakka.
Tason daraja shi ta kuma haƙura da buƙatin shi dole ,saboda da ganin sa bazai yarda da Halayyata ba.
Kinga kin jefi Tsuntsu biyu da dutsi É—aya kenan fulani.
Na farko kin kaita inda za'akula da ita.
Na biyu kin kaita inda rayuwa zata koyamata darasin girmama ɗan Adam, da kuma sanin daraja talakka tin kamin Duniyata ta bankaɗo tsohon Sirrin dake binne cikin ƙasa ...
Wani irin tsuma jikin Mamy ya ɗauka sai kai da komo take tana yarfe hannu, tana ta Auna magana Hajiya Turai a mizani daya dace, tabbas ta yarda da maganata,To amma waye shi ,Ina dangin sa shima sadeeq din, koda bata tambayeshi ba bata taɓajin yamata wata magana ba,Karfa suyi Abinda zasuyi dana sani.
Cikin jimami tace'' shawarar ki haka take Aminiyata , Amma kina ganin zai amince? Nasha faÉ—amiki baya jire raini wayo, kar zuciyar shi tabashi kamar dan in haÉ—a shi da Amnah nike kyautata mai, bayan bayan ni Wallahi billahi dan Allah nayi.
Murmushi Hajiya Turai tayi tace A'a bana tinanin hakan daga gare shi insha Allah.
Amma kamin nan yana da kyau muyi istakhara dan neman zaɓin Allah, duk abinda kika natsu dashi to ki dunfareshi kai tsaye, Allah zai warware komi ,mudai mafita muke nema.
Kai Mamy ta jinjina cikin gamsuwa tare da ƙara zubama
Windon ido inda ta gansu Amnah namai magana da hannu tana jawo Hamrat shikuma sai binta da ida yake yana nuna ta da yatsa kai kace magana soyayya suke .
"Tsananin dace wa fa sunyi Fulani, jibi kayan jikinsu wallahi ni in'bama idona gizo yakemun ba kama suke sosai. Hajiya Turai da ta dafa kafaÉ—ar Mamy ta faÉ—a cikin zakuwa.
Mamy tace "magana ki dutsi, inshaah zanyi yanda kika ce.
Aɓangaran su Amnah kuwa cikin sanyi tace" ka sauketa mana, ya daga ganin yar mutane zakayi sama da ita ka ajiyeta fa.
Shareta yayi ya sakko Hamrat ya kama hannuta da niyyar tafiya.
Da sauri Amnah ta rike hannu Hamrat tana mai zubamai ido tana tabe baki.
yayi da shikuma yake mata kallon sama da kasa na ganin raini wayon da takemai .
Afusace yace bazaki sake ta ba muwuce.
Itama cikin fusata tace" bafa tsoronka nike ba, karkaga inama magana cikin sanyi kayi tinanin wai tsoro nikeji, A'a ina gudun fushin mahaifiyata ne ,daga ganin yarinya saika fita da ita, wannan dacewa ce ko tarbiyya ce? kabani amsa mana. ta faÉ—a cikin ihu tana yarfe hannu.
Cikin takaici yace Ƙanwar kice ko ƙanwa ta?
Babu ko É—aya amma kaima miye matsayinka wajen ta, ina kai ina wannan yarinya.
Bar ganin kasha wasu kayan aronka cen kazo ka rainamun hankali fa.
Hamrat tace "Aunty Baby nefa kikema ihu .
Baby kayi hakuri kema Aunty kiyi Hakuri babu kyau manya na faÉ—a ko Baby? muje gida inga Ammi nah..
Tsororo Amnah tayi dan sai yanzu ta lura da masifar kamar da suke, kenan ƙanwar sace take ta lallaɓawa haka,.
Waji shegen tsaki ta saki tana juyawa cike da takaicin kanta,Jibi.yanda tazage tana mata hidima.
Shima tsakin yayi yana faÉ—in mahaukaciya kawai. ya kama hannu Hamrat suka tafi.
Da sauri Mamy ta zuge glass din window ta kwala mishi kira.
tsayawa yayi tare da juyowa yana kallon saitin da take.
Da sauri ta cemai ina zuwa tashiga ɗakinta ta ɗakko wani ƙaramin akwati ta fara loda kayan yara da take saidawa kala- kala aciki, Masu kyau dana wasanni ta haɗa da sabbin kudi dubu ashirin ta tura ciki, kana ta jawo ta fito fuskar ta asasure da kumburi.
Hajiya turai tace kwara kiƙara lafkacewa tin yanzu ya gano kina cikin tsananin damuwa, in ya tambayeki fashe masa da kuka.
Murmushi Mamy tayi ta fita.
Cikin sanyi tace" Sadeeq da tafiya zakuyi babu ko sallama .
Kallonta yayi cikin tausayawa yace" Hajiya yau fa naga kamar bakyajin daÉ—i, kuma kar a barta ta isheki da surutu, kwara mu wuce kawai.
Gefe Mamy tayi da kai cikin damuwa tace" katayani da addu'a sadeeq , Allah ya sauƙaƙa lamarina, ya kuma kawoman komi cikin sauki.
Ameen yace yana gyara tsayuwar shi yace.
' "Hajiya in kinson zan iya taimakamiki kifaɗaman Amma bawai tilasti bane, Wallahi billahi kullum Addu'a ta Allah ya kawo ranar da zaki nemi alfarma wajena kowace irice na miki Alkawari zan miki ,in kinson zan iya shiga hurumin abin kifaɗamun duk girman Haɗarin sa, in'kuma kinson ba hurumina bane to zantayaki da Addu'a Allah ya warware miki matsalaki . Ya ƙarasa yana zubamata idanuwa..
Cikin lokaci hawaye suka fara gudana Acikin idonta.
Tace Sadeeq kamun alƙawarin magancemun matsalata ?
Cike da kwarin gwiwa yace insha Allah indai bata saɓama Addini na ba.
Murmushi tayi tace'' shikenan nagode inka samu lokaci gobe Kashigo da wuri sai ka kaini gidan Nene .
Kai ya ÆŠagamata tare da faÉ—in insha Allah.
Hannu Hamarat ta kama ta turamata É—an madai-daicin akwatin tace Autata ga kayan wasa .ai kina wasa ko?
Da sauri ta kaÉ—a kai tace" inayi ,shikenan ma nasamu abun wasa bazan sake bacci ba ko Baby?.
Kai ya ÆŠagamata tare da yi ma Mamy Godiya .
Tace yawwa bama sai ka dawo ba kayi zamanka gida sai gobe insha Allah.
Godiya yamata