Showing 33001 words to 36000 words out of 94971 words

Chapter 12 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt

09 Feb 2025

17211

dan zatin Allah ,kana ina rokon kamun kyakyawar fahimta kamar yanda kasabaman a lokutta da dama.


Hannuta ya kama suka haura sama É—akinshi.
Zama yayi akan gado tare da fuskantar ta yace.
Ina jinki fulani waye ÆŠAN DAKO da kikama kyautar yarinyata batare da nasani ba?
Anan takwashe komi ta faÉ—amai, har irin taimakon da ya musu sadda ake bibiyar su, da na maido Amnah gida.


Tsaye ya mike ya na zagaye yace" Wannan ba hujja bace Fulani, bazai yiyuba gaskiya, kwara a'samu mutum mai nagar ta da cikakken family, ba wanda ba Muson asalin sa ba.


Kuka ta samai tana sakin nishi mai zafi tace kafa duba Amnah har yau batason wacece ita ba. Yana da kyau ta fara rayuwar da zata koyi darasi a cikinta, inba haka ba to kawai boyayyan sirrin dake kulle zanje in'warware yanzu Wallahi, bazan iyaba, kason duniya zata zagen,i za amun kallon wadda ta gaza daga kurarin da tayi.


Rungumota jikinshi yayi yace.
Ki kwantar da hankalin ki kinga numfashinki ya fara canzawa, na yarda na amince da kalamanki, insha Allah gobe zanga yaron.


Cikin tsananin jin daÉ—i ta amince mai dan danan ta wartsa ke ta fara rikitashi da zafaffan wasanni. cikin lokaci kadan suka afka duniyar jin daÉ—i.


Sadeeq kam som idon shi baiga bacci ba, Saboda azabar da yakeji, ga sanyi da yarasa mizaimai maganinsa.
Har akai Asuba ya kasa tashi.


ƙarfe bakwai Mamy ta shigo palon dan bataji motsin saba.
Salati ta saki datagan shi yanata rawar sanyi.
Da gudu ta ƙarasa wajen shi ta tallaboshi tana faɗin" sadeeq! Dee nah! ka tashi Dan Allah karkamun haka haba sadeeq .
Ajigace ya É—ago fuskar shi da tayi wani irin ja ya zubama Ammi ido ko kyaftawa ba yayi.


Yana zuwa zai fara magana numfashin shi ya wani irin ja da ƙarfin tsiya.
Sanadin da yasa idanuwan shi Lumshewa kenan baki daya ko motsi baisake yiba ya saki...


Sadeeq! Sadeeq!! Dee!!! Ammi tace arikice tana Dukan kumatun shi.
Cikin matsanancin kuka ta tattaro shi baki É—aya jikinta ta saki wani mahaukacin kuka tana fadin shima na rasashi, shikenan Sadeeq, miyasameka ?miyasa kamun haka baka faÉ—amun ba, ko akan umarnin da na bakane ya saka HaÉ—iye zuciya ..


Wayar shi dake gefe ta shiga ring.


Cikin matsanancin kuka Ammi ta É—auka tare da sakin sabon kuka.


Dan Abbah yace a'kirasa su tattauna dan zai fita.
Afurgice mamy ta mike tsaye tana faÉ—in minene, miya faru daku, Ammi ina sadeeq ,miyasamu sadeeq É—in?


Sadeeq ya tafi ya barni Hajiya shima na rasashu, ya tafi da burin ɗaukar fansa ran mahaifin shi da na yar uwar sa, Hajiya narasa kowa Ammi ta ƙarasa cikin matsanancin kuka...


Daɓas Mamy ta faɗi ƙasa tare da kecewa da wani kukan da yafi na Ammi ƙarfi tana dafe zuciyar ta..


Cikin tashin hankali abba ya É—auki wayar anan Ammi tamai bayani ,ya nemi jin kwatancen unguwar da suke dan suzo.
Ammi tamai tana kashe waya tana jijjiga Sadeeq.


Da sauri ya sama Mamy hijjob inta tare da mikar da ita suka fita tanata kuka.
Da kanshi ya tuƙa motar har unguwarsu Ammi.
Da hannu Mamy ta nuna mai har gidan su.


Suna zuwa suka afka gidan Tare.
Inda suka jiyo kuka Ammi anan suka shiga.


Dai -dai lokacin da Ammi ta É—ago kanta cikin kuka dan ganin waye...


A É—imauce cikin rawar baki ta mike tana nuna Abba da hannu tace
Alh isa dama kana raye?
Dama kaine mijin ta? innalillahi wa inna ilaihi Raji'un.


Cikin rawaa baki Abba yace" ina nan Doctor wallahi ina nan.


Mamy data kasa fahimtar kalamansu hankalin ta naga sadeeq tace .
Kufa kamashi mukai shi a dubashi yafi wannan surutun kila ba mutuwa yayi ba.


Da sauri Abba ya fara ƙoƙarin ɗaukar sadeeq amma ya kasa ,saboda ingarman namijin gaskene.
Cikin sauke numfashi yace" ranki ya daÉ—e kiyi hakuri ki danne damuwarki dan Allah ki duba sa .


Ita sai lokacin ma ta tino da kayan aikinta .
Da gudu ta isa É—akinta ta kwasosu taci gaba da duba shi .


Cikin awa É—aya numfashin sa ya kawo.


Hamdala ga Allah Ammi ta fara tana dariya da kuka.


Cikin myutya marasa lafiya yace "Ammi zanyi wanka in Sallah .


Tace" to sadeeq kana iya tashi ko kabari ka karajin sauki.
Kai ya gilgizamata alamar A'a.


Su Mamy ya kallah tare da zubama Abbah dake kallon shi ido kamar ya son shi.
Cikin kulawa Abba yace sannu yarona.
Kai ya É—agamai yana duban mamy dake jeramai sannu cikin zallar tausayawa.
Itama kan ya gilgizamata tare da tashi cikin dauriya .
ÆŠakin Ammi suka zauna inda Ammi ta kalli Abbah tace yarinya kace kenan sadeeq zai aura, na amincema airyan koda nan da sati biyu ne .


Abba zai magana ta É—agamai hannu tare da cewa .
Ka adana kalamanka nan gaba samana rana ,aje a fara shiri, koma meye ya biyo baya.


Godiya ya hau jeramata wadda taba Mamy mamaki.


Cikin kwana biyu cikin ikon Allah sadeeq ya warke ya koma bakin aiki.


Yayin da Amnah ta hana kanta walwala kullum tana cikin ɗaki tana waya da Abul khairi , Dan shine kawai ke sata jin sauki, ko abinci tadaina ci duk ta rame,ga Bily bata ƙasar, hakan yasa ta rasa wazata fuskanta da damuwar ta, dan sauran ƙawayen ta tana ganin abun kunya ne suji magana su kuma rike sirrinta ,bayan sunson ƙudirinta..


Washe gari aka sanya biki wata É—ay..


Mamy ta zage ta fara gyaran Amnah duk da tana gardamamata saita hada da faÉ—a kana suke dai -dai tawa.


Amal kuwa ranar da ta samu labari har jinya tayi, Dan tin ranar farko take DAKON son Sadeeq amma ta fawwalama Allah komi , tare da rokon ya ciremata sonsa ya bata wanda zai fishi.


Ta ɓangaran Amnah kuwa Abul khairi ya kwantar mata da hankali akan tayi hakuri tayi auran, Tin da ba son mijin take ba anan ne zasu mafi samun damar sakewa su mulki soyayyar su son rai.
Hakan yasa ta ɗan saki kaɗan har tana cin abinci, Amma zuciyar ta fall take da nau'in azabar da zata gana mai , Dan da kanshi zai saketa ta tafi ta auri zaɓin ta.
Dan ita talaucin shine kawai kesata kinsa amma da da azzikinsa da tafi kowa murna saboda ya haÉ—a komi.


Biki na ragewa saura sati É—aya Nene ta dawo gida da zama tare da fara yima Annabin wankan lallai kullum , Da bata wasu magunguna irin nasu na mutanan da sai tace na tsarin jiki ne, haka take tausa mata
Magungunan da take bata dakyal suke barin ta bacci, Dan sai tayi download din kayan baɗalata kana take rarragewa ,wani yanayi na buƙatuwa kawai take jinta a ciki..


A ɓangaran Sadeeq kuwa ko ajikinsa, tin ma ranar da sukai mai magana ya watsar da magana harka gaban shi kawai yake.


Saura kwana ukku biki Ammi tace Sadeeq kayan lefe ya zamuyi dasu kana Sadakifa?


KafaÉ—arshi ya É—aga" yace banda su" .


Ammi tayi jim tana wani nazari zuwa cen kuma ta saki murmushi tace jiya ka kwashi albashinka ka zaro 20k abasu .


10k kayan sawa 5k tayi hidima biki, 5k sadaki .


Yace"shikenan tare da zuwa É—akinta ya dakko ya bata .


Waya tama Abba cikin kankanan lokaci sai gashi yazo.


Anan ta zaro kudin ta bashi ta fadamai duk abinda ta keso.


Kai ya jinjinamata cikin gamsuwa tare da mata sallama ya tafi.




Bayan yaje gida ya nunama Mamy abinda suka bada taita godiya .


Yace fulani kodai in ƙara akai ?wallahi abin nan na ɗagamun hankli banson halin da Amnah zata shiga ba.


Murmushi Mamy tayi tace'' A'a Hayatee zasuga mun raina mu da sukama Alfarma, Allah ya amfana ,kuma wannan ma ai ya na É—aya daga cikin darasin da nikeso rayuwa ta koyamata ko.


Yace shikenan tare da fara waya wa Abokansa ya sanar dasu ÆŠaurin auran Yarsa, da gidajen Radio ko ina dai.


Da yamma Hajiya Turai tazo ita da wata mata da ganinta ba cikakiyar bahausa bace tafi kama da shuwa'arab.


Tace ma Mamy ta kawota ne dan ta gyara jikin amarya.


Mamy tayi na'am da hakan tare da zama suka fara tsara yanda abun zai kasance.


Cikin kwana biyu gidan Mamy ya rikice da mutane wayan da aka gayyata da wayan da ba agayyata ba, kide -kide kawai ake.


Agefe ga yan unguwar su Nene ƙawayen ta tsaffi sunata buga kwarya sunyi layi da ankon su na sallah da Nene ta rabamusu.


Nene ce ta iso da sauri tasha kwalliya da uwaye gwala gwalai tace'' haba kukam anyi masu busashen hannu ,Yo ko zafi bakwaji,sai dukan kwarya kuke ,haba ku ajiye kuje kuyi wanka sai wari kuke muje É—akina kuci abinci ,inba haka ba wallahi baku shigar shi sai dai in buÉ—e maku wani.


Tashi sukai suna faÉ—in da wankan mu kwara kibamu muci anan.


Aiko ta tafi tana rausayawa ta kyalesu.


Washe gari da safe ta kama juma'a ranar É—aurin aure kenan.


Sosai gidan Mamy ake hada_ hada tana zaune palo ita da Hajiya Turai tasha wanka da wasu ƙawayan su sunsha kwalliya sai kyalli suke, fuskar su cike da farin ciki.


A ɓangaran amarya kuwa tana kwance ɗaki ko wanka ta kiyi sai waya take inda abul khairi ke bata shawara akan in taga zata shiga damuwa zai bata wani magani Bacci masu yawa ko gidan taje ta yawaita shan su dan tasamu hutu ta rage tinani .


Sosai ta yi na'am da shawara sa dan Haka taji daÉ—i haduywa dashi dakuma shawara Bily da ta bata akan tayi wayar sirri da yanzu an'dakushe farin cikin ta..




Matar dake mata gyara ce ta kwan-kwaso kofar. Amnah ta boye wayar ta tashi ta budemata.
Fuska a É—aure ta shigo da wani sabulu tace" muje toilet.


Cikin bacin rai tace ke nifa na gaji kinji, an turoki wani sangam -sangam to banaso bazan ba .


Mikike faÉ—a Amnah Mamy tace'' data shigo.
Aguje ta shige toilet din tana kuka.


Matar ta bita ciki anan ta gwada mata yanda zatayi amfani dasu kana ta juya baya dan ta samu tayi.
Wankan tayi tayi kyau sosai fatar sai sheki take.


Suna fitowa ta tsantsaramata kwalliya tare da bata wani dakeken lace silver color mai tsada aka shirya ta.


Ana sakkowa daga masallacin juma'a suka farajin kida da busa cikin gidan .
Yayin da Amnah ta ƙaraso wajen window tana karema zugar mutanan da suka halacci Ɗaurin aure ta.
Ga unguwar ta cika.
Kwafa tayi tace da kanka zaka maidoni talakka.


Karaf ta farajin maroka na faÉ—in an ÆŠaura auran Aminatu Isa mai zinari Da Sadeeq ÆŠAN DAKO akan Sadaki naira dubu biyar lakadan ba ajalan ba....


Ihu ta saki tana dafe kirjinta da yayi wani mahaukacin bugu.


Da gudu Hajiya turai ta turo kofar ta shigo Mamy na biye da ita ta janyo hannu Amnah tace" muje palo ga mijin ki nan ya iso....
5/18/22, 09:34 - MY MTN 2: *Littafin🌹DAN DAKO🌹 na kudi ne biya ki karanta cikin Aminci. Biya 300kacal to 0006454115 Amina Dahiru jaiz bank,or MTN card to this number 09165832002. then send the evidence of payment via 07038423451* ğŸ¤ğŸ™ğŸ¤²
🅿ï¸2ï¸âƒ£5ï¸âƒ£&2ï¸âƒ£6ï¸âƒ£

"" Kallon su tayi ta saki wani siririn kuka tana kallon kanta a madubi. Tace'' ni ! Nice aka bada sadakina dai- dai da kudin kazar da nike ci kullum a rana ,ni aka saya da masifar arha 5k kudin gyaran kaina, 5k ƙarama kyautata ga wanda na raina ,Ni Amnah Mai Zinari akama haka, ni akama sayan tsuntsaye , Mamy inaso kifaɗaman wacece mahaifiyata, Dan ban yarda ke kika haifeni ba , Duk kan uwa fatan ta yar ta taje gidan da zata huta, Amnah banson minai miki ba kikamun haka ,kika bani wanda ba kullum ma yake samuba sai karshen wata ,to mizan dinga ci Mamy,miyasa baki tambaya ra'ayina ba kamin ki yanke hukun ci?.


Tsawa Mamy ta dakamata cikin fitar kwallah tausayi Amnah dake zuboma ta.


Cikin kuka ta kama hannu Annabin ta rike tace .
Amnah bazaki gane gata na miki ba sai nan gaba, bansani ba lokacin zai iskeni da rayuwata ko akasin haka, Wallahi Amnah uwa bata yarda takai ɗiyarta wajen da zata cutu,da kike zancen mahaifiyar ki ni ɗin nan daice na haifeki cikin yanayi na ƙasƙanci da tausayawa na rashin gata.
Amnah ana dukana na haifeki , Amnah akan kwalta titi uwarki ta biya , Amnah ! Amnah ta saki kuka sosai mai ban tausayi ta kasa ƙarasawa.
Galala haka Amnah ke kallonta cikin tsananin tashin hankali, to mitake nufi?.


Da gudu ta karasa wajenta ta faÉ—a jikinta tana fadin Mamy wai minene kike boyewane ga rayuwata ,wacece ni? suwaye suka dukeki, ina Abbah na A lokacin.


Hajiya Turai dake kuka sosai ta share hawaye ta tace Fulani miyasa zaki ɓata farin cikin ki,Miyasa zaki fara sakin zance cikin gushewar hankali.


Amnah tace "Momy Turai mike faruwane.


Mamy ta riko hannu Amnah tace kimin alƙawarin zama gidan sadeeq , kimai biyayya Amnah, ki kyautatama sa, kirike sirrin sa, kidaina mai abinda kikaga dama , Dan na tabbata yafiki gata nesa ba kusa ba, nan da 12- 1-2023 na miki alkawarin zan sanar dake tarihin rayuwata , Amma kimin alkawarin kyautata rayuwarki agidan auranki, ina mai miki nasiha da kiji tsoron Allah Amnah, kiso sadeeq dan Allah badan yana da azziki ko bashi da shi ba, Azziki na Allah ne, wata kil in Allah yaso kizama Abokiyar azzikinsa, kana ki so uwar sa da ƙanwarsa dan sune kawai farin cikin sa, in'kinmin wannan alfarma ina rokon Allah ya lulluɓeki da rahma, yasa ki farin ciki har karshen rayuwaki, in'kuma kinɓataman Amnah zaki gani , ni dai nason na sauke nawin ki dake kaina, na miki tarbiyya dai-dai iyawa na.
Dole ta sani miki aure saboda halin da naga kina neman sa kanki na halaka, kuma saida muka sauke hakkin ki kikace baki da kowa.
A irin rayuwar da kika fara yanzu Amnah Aure shine mafitar mu,kuma rufuwar asirina, kitashi muje nace ta faÉ—a tana share hawayen ta.


Cikin sanyi jiki Amnah ta mike ta bita tana share hawayen ta, Tare da alƙawarin kyautatama umarnin mahaifiyar ta in zata iya insha Allah, sai dai ko sha'awar duniya zata kasheta bazata yarda sadeeq ya raɓeta ba , Saboda bashine burin rayuwar ta ba, Abul khairi ta yima wannan tanajin ,dan nlshine ke sonta shi zai tarai-rayeta ko bayan ya mallaketa, shikam wannan baya so ba taso da muguntama zai iya haƙemata ya yaga banza.


Hajiya Turai ta ƙara gyaramata fuskan ta sosai tare da kamo hannuta kanta akasa suka fito.
Anan ƙawayen Mamy suka fara guda Nene ma ta yo kanta da zugar abokanta da yan fans ɗin group ɗin ƊAN DAKO ga baki ɗayan su sunma Nene ƙara , Nene na taji dasu saboda tasan mutanan Azzikine ga haɗin kai da son juna.


Suna kawowa palo Sadeeq yayi sallama ya shigo shida Abbah .


Sanye yake cikin wani yadi yellow mai masifar saukin kuɗi wanda a'ƙalla duk yadi bai kai 500 ba, Sai hular shi taɓani kaji hadith daya sanya hannu shi rike da casbaha.


Cikin murna Mamy ta tarebeshi tana nunama ƙawayenta ga surikin ta, ga sadeeq mijin Amnah.


Lokaci guda gulma ta ciwo mutane aka fara gwara kawuna kowa da abinda yake faÉ—a.


Shikam Sadeeq murmushi kawai yake dokawa yana binsu da kallo ta ƙasan ido..


Hajiya tuyrai ta cema Annabin ga mijinki kije a muku photo na tarihi ko?


Ahankali ta É—ago idanuwanta ta zubasu a cikin nashi da ya tsareta da ido..


Hajiya tyiurai tace. "Affuwan na tino ganin mu bazaisa su iya ba, Dan Allah sadeeq kamata kuje palon sama, ke Amnah maza kuje sama na turo muku mai photo a cen.


Kamin ma ta rufe baki ya iso wajenta tare da cafkar hannuta ya fara janta A'hankali inda suka nuna musu.


Kamar rakuma haka take binshi som hankalinta ya gushe, tinaninta na neman barin ganga jikinta,wannan ne zata aura..
Suna bi ta step É—in karshe ya hango haÉ—aÉ—É—an palon da yafi na kasa tsaruwa.


Hannuta ya saki tare da samun kujera yayi zamanshi yana mai dora kafa daya akan daya yayi shuru..


Kwas !kwas !! kwas!!! ya fara jin sautin takowar ta da tsinin takal manta.
Gaban shi tazo bata tsaya komi ba ta durkushe kasa tare da kifa kanta akan kujera da yake ta saki kuka sosai.
Baice komi ba dan shima da da dama kukan zaimusu.


Sai da tayi dan kanta fuskar ta duk ta ɓaci da hawaye, majina, tayi kaca- kaca.


Ahankali ta É—ago fuskar ta tace.
Na rokeka da Allah ƊAN DAKO kayi hakuri ka sawwakemun ,na maka alƙawarin kudi mai masifar yawa da zasu isheka gina rayuwar ka.
Kai kason som babu dacewa tsakanin ni dakai.
Ka kalleni ka kalli zubinka katsan wutsiyar rakumi tayi nisa da kasa.
Tindaga kan sadakina na Tabbatar da zaka aureni ne dan wulakanta rayuwata, ni zaka bada sadakina 5k kudin wannan koÉ—aÉ—É—an yadin na jikin ka ,ka taimaka ka sawwakemun Dan Allah .


Baki ya taɓe tare da mikewa tsaye .
Ahankali ya taso da ita ya sanya duka hannayen shi ya dafa kafaÉ—arta, ido cikin ido suke kallon juna.


"Yace Amnah bana sonki som, Saboda ke baki da tarbiyya, kana bakiyi kala da macen da nike soba,farace ke nikuma bakar fata nike so,ke yar masu kudice nikuma talakka nikeso Yar uwata,banson wacece keba nikuma mai asali nike so,ki iya bakinki wannan auran auran taimako sunan sa.
Saboda darajata da son a taimaka miki har gaban mahaifiyata akaje neman auranki, kinga kam tabbas ni mai tsadane.
Da yanzu wayan da sukaje nema miki aure zasu dawo suce a sawwaƙemaki Wallahi cike da farin ciki zan sallameki, sabosa bana sonki,
Ke daga irin shigar danayi kinson cewa ba auranki ne gabana ba.
Duk talaucina bazan iya sanya wannan yadin ba.
Shiyasa ko da naje kasuwa nace abani yadi mafi sauki, mafi kuma muni , Saboda ni yau ba ranar farin ciki na bace.
Ni ba ustaz ba ,ba liman ba, amma kinga hular danasa saboda in nunama duniya duk tsadar da kike faÉ—in kina da ita to ga a inda kika kare, ita duniya budurwa wawace.
Albishir na karshe ina miki murna shigowa gidan ÆŠAN DAKO nan da kike cewa, nan da mint talatin ki shirya Mai adaidaita zaizo ya É—aukeki, dan dan ban amince ki shiga motar kowa ba.
Kana karki kuskura kisama ranki zaki tafi da takaddun aiki dan bazan fita kifita ba ban lamunce ba.


Hancinta ya lakace yana fadin sai munhaɗe yam mata ya ficce cike da ƙasaita batare da anyi photo ba...


Kwaraf ta faÉ—a akan kujera tacigaba da kukan ta tana faÉ—in kagama dani ka cuceni wallahi ka cuci rayuwa ta..


Bayan fitar shi su momy sukazo sukace taje taci abinci sunkusa tafiya.


Sadeeq kam cikin jin daÉ—i da nishadin takaicin da ya tusamata yafita ya zare kayan ya badasu wa Baba masu .


Ya zira wata farar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login