Showing 6001 words to 9000 words out of 94971 words
Chapter 3 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt
bawa ke tsarama kanshi halitta ba , Shikenan sai ace gidan talakawa ba zasu samu yara masu kyau ba ko me? Halitta" Ubangiji ke yinta yayi Æaki acikin fari haka yayi fari acikin baÆ™i, Da haka ka daina mamaki inka amincemun zan zauna da kai ,in kuma baka amince ba kana ganin babu yarda zan fita in samu wani aikin..
Illahirin jikin Baba rawa yake jin yanda yake rattafo zance da halshen hausa dan ko makaho yaga Habu yason ƙaryane yace shi bahaushene, Dan ko kaɗan shi bai kama da hausawa ba sai dai ko kasashi cikin jinsin Larabawa ko indiya wa....
Cikin Rawar murya yace Habu kaga dai da gaskiya na rikeka ko? To Dan Allah karka cutar dani ka kama gabanka Dan Allah nagode kuma kamun kwatance inda gidan yake a'ida kai masu kayansu in ÆŠakko motata.
Murmushi ya saki mai ciwo tare da kwatan tabmusu cikin fahimta ya tashi ya musu bankwana da godiya akan Alkhairi da sukaimai na rikeshi tsawon kwanaki.
Cikin sauri Baba yace bakomi bakomi jeka ga hakkinka ya bashi dubu biyar.
Karba yayi tare da turawa aljihu yafita daga rumfa yafara takawo cikin ruwan da basu da niyyar tsayawa.
Gabaƙi ɗaya'n masu shagunna kasuwar kallo shi ake wasu harda fitowa bakin rumfunan su suna leken baturen da yashigo kasuwa yana tafiya da kafa ganin irin cikakkiyar sumar shi tayi linkim da ruwa duk ta balbaje tayi masifar kyau.
Sosai ya tsargu da irin kallon da ake binshi dashi hakan yasashi fara tafiya da sauri cike da sasarfa da kuma ɓacin rai.
Dan kallo na É—aya daga cikin abinda ya tsana arayuwar shi ya rasa ubanda yasa mutane ke kallonshi haka kamar sun samu Tv.
Gabaki É—aya ya fita kasuwar yana fitowa ya tare keke napep ya shiga.
Tinda yashiga napep din kaɗan kaɗan mai napep ya juyo ya kalleshi amma bai ce komi ba shikuma tinda yaga haka ya ƙara haɗe fuskarshi tamau.
''yallabai wace unguwa zan kaika?
"Tudun wada.*
Yabashi amsa agajarce.
Kai tsaye suka nufi unguwar ahaka ya dinga nuna mishi har suka karaso wani dan matsakaicin gida da ƙofar ke saye.
Sauka yayi ya bashi kuÉ—in tare da kutsa kai cikin gidan ya tura kyauran yashiga da sallama.
Yason ruwan da ake bazai ba na ciki damar jiba kamar yanda bazai bashi damar jin ko an amsa ba.
Ɗan ƙaramin gidan nasu yatsaya karema kallo da keda Ɗakuna ukku biyu ajere sai daya dake kallon su sai dan karamin tsakar gida da baifi zaman mutum biyar ba sai toilet da karamin kiching.
Ba laifi tsakar gidan nada kyau dan ashafe yake tas ga pent da yasha komi a'killace yake ba wasu hayaniya.
Dayan É—akin da ke aware yayi saurin turawa tare da shiga ya maida kofar ya rufe tare da danna Sakata
Babu komi.acikin É—akin sai wata tabarma da kuma karama katifa sai Alkur'ani sai wani truly babba guda É—aya ..
Yana shiga yabi É—akin da kallo jin yanda yake ta busa kamshi tsintsiya da akasamai gashi agyare tsaf.
Cikin natsuwa ya fara cire kayanshi tare da sasu awani babban boket dake bayan kyauran, Yana gamawa ya É—aura wani HARAMI akugunsa tare da É—aukar É—aya'n ya yafa akafaÉ—ar sa.
Wani irin mahaukacin kyau yayi kamar wani Balarabe dake filin Arfa.
Soso da sabulu ya É—auka tare da boket din dakayanshi ke ciki ya fita dasu .
Ajiyesu yayi tare da faɗawa toilet din dake tsakar gidan ɗan madaidaici ba laifi yana da kyau akwai shower da toilet sit da ƙaramin pampo ciki.
Wankan ya faɗa tare da murzar jikinshi sosai cikin lokaci ya fito tare da duƙawa ya wanke kayan daya cire tass ya shanyasu akan igiya.
Alwallah ya É—aura saboda Al'adar shi ce zama da Alwallah yana gamawa ya nufi É—akin shi ya zaro wata tattausa brown din jallabiya dake linke mai gajeran hannu ya sanya.
Wani irin mahaukacin kyau tamai gashi ta sake fito da Hasken farar fatar shi da kuma zatin shi da murzazza fatar da Allah yamai mai kama data ya'yan hutu.
Kai tsaye ya fito tare da nufar É—akin dake kallon nashi ya tura guda da salllama a'
bakin shi.
Wata murya ce mai sanyi ta amsamai sallama tare da bashi izinin shigowa.
Shiga yayi cikin ɗakin yana takawa A'hankali kamar wanda ke tsoron ƙasa.
Wata farar matace dake hakim ce akan kujera hannuta rike da littafin Adduo'1i tana dubawa ,hukunta sanye da wani kace mai kyau da tsada.
Kai ta ÆŠago ta kalleshi tare da fadin.
SADEEQ Kadawo?Sannu ya aikin naku?Ina fata komi yana tafiya yanda ya dace? Da fatan dai bakajin yunwa ko? tamai tambayoyin duk ajere.
Wani kyakyawan murmushi ya sakarmata tare da Duƙawa kasa ya ya dafa gwaiwar ta yace. "Ammina Barka da gida kin cikani da tambaya waccen/ kikeso in am'samiki? ya ƙarasa yana turo baki cike da shagwaɓa .
Murmushi Ammi tamai mai tsananin kama dashi ta ya mutsa sumar kanshi tace duka nike so ka amsamin,Saboda É—an jarumi ne ,kuma Nason in akwai wadda tafi wannan zaka amsamun.
Hannunshi da Amnah ta rike ya ɗaga yana murzawa A'hankali saboda yana tinanin tamai rauni, cikin Raɗaɗin da zuciyar shi kemai yace" Ammi nah komi lafiya klau Alhamdulillah , Sai dai inaso kisani Addu'a da bakin ki mai Albarka, wanda nike ƙasan shi sama da wata shida yau ya koreni tinda yaga fuskana yana ganin kamar cutar su zanyi kuma na fahimtar dasu sun kasa ganewa yakarasa cikim.ƙuna rai da taune jajayen lips ɗin shi.
Shuru matar tayi batace komi ba sai kanta da ta sadda ƙasa cikin kankanan lokaci ta fara kwallah masu tsananin zafi da ƙuna rai.
Saurin Ɗago kanshi yayi arikice tare da karasawa wajenta ya rike gwaiwarta illahurin jikinshi rawa yake idonshi yayi jawur cikin ƙanana lokaci,Murya na rawa yace.
"Ammi Dan girman Allah da manzon sa karkimun kuka na rokeki Ammi, ku kanki shine zai raunata zuviyata inkasa zama Namiji na ,Ke kinson waye ɗanki Ammi akan ki zan iya ɗauke komi amma banda ganin hawayen ki, Bani da mafita shiyasa na zaɓi faɗamiki saboda ko ba komi nason zakimun Addu'a kuma addu'arki gareni batada hijabi karbabiyane muyi hakuri mu fauwalama Allah,Domin shi ne zai kawo muna mafita, in kuma kina ganin in dingama fuskana penti kamin in fita sai inyi Ammi, Amma wallahi ni kaina abun na da nike naɗawa na matukar damuna Ammi kinson Ni banason zafi da abu mai nawie...
Hawayenta ta share cike da tausayin yaron nata.
Rungume shi tayi sosai tare da sakin wani mahaukacin kuka taf ara kiran shi da Sadeeq!Sadeeq!!Sadeeq!!! Munga rayuwa, Rayuwa tamuna juyin waina a Tanda, Sadeeq yanzu kaine wai....
Saurin rufemata baki yayi tare da gilgiza kanshi idonshi jawur yace" ki daina wata magana Ammi abunda ya wuce ya wuce munma rasa mahaifinmu mun hakura ballantana wata rayuwa cen ,karki damu Ammi nah ina Hamrat?
Hawayenta ta share tare da nunamai inda wata kyakyawar yarinya ke kwance akan katifa da ba tafi shekara goma ba, Bacci take cikin jin DaÉ—i da kwanciyar hankali.
Cikin natsuwa ya zare jikinshi daga na Ammi ya ƙarasa wajen yarinya ya aza gwiwowayin shi ƙasa tare da riko hannunta ya Ɗan murza ahankali yana kallon fuskarta da ke tsananin kama da tashi...
Kanta yafara shafawa A'hankali yanajin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa game da yarinya,baison dalilin da yasa duk sadda zai kasance da yarinya ba yakejin wani tarin rauni dakuma matsanancin tausayin ta ,ƙanƙanuwar yarinya ke cikin wannan rayuwa da suke ciki fatanshi ya nema dan ya wadatasu amma yau gashi an koreshi akan abunda bai kai ya kawo ba.
Amma ya tabbata babu wadda ta jamai kamar wannan yarinya da som batada É—a'a da tarbiyya.
Hannu shi ya kalla inda ta takemai har ya fashe gashi yayi jawur.
Lips ɗinshi ya ƙara taunewa akaro na ba a Dadi..
Mamy ta katsemai tinani da faÉ—in ga abincin ka nan kazo kaci.
Cikin ladabi yace"Ammi minene kika dafa muna?
Murmusi tayi tare da faɗin"Wakene sai shinkafa da salad harma da ƙwai na siyo nasamaka takarasa tana Murmushi.
Tausayi tabashi sosai ganin yanda take farin cikin ta Da ɗaɗamai ta hanyar samai kwai duk da cikin shi a'cike yake amma bazaiso ɓata farin cikinta ba,Haka ya zuba kaɗan ya fasa kwan yaci yanata mata santi ita kuma tana tajin daɗi tare da mai kallon tausayi.
Gidan su Amnah kuwa Baba Habu yaji anama gidan wani mahaukacin bugun da yasashi Ɗakko Sanda da yar ƙaramar wuka ta yanka albasa yafito tare da buɗe kyauren cikin kasada ba tare da ya tambaya ba ya lafe baya.
Iro ne ya turo kyauran da karfi wanda yasashi matse Baba madu .
Ihu ya saki tare da watsar da Sanda da wuka .
Cikin furgici Iro ya juyo tare da fadiyn lafiya malam kake ihu munzo É—aukar mota ne muna tare da Bakanike ba masu Sata bane..
Ajiyar zuciya Baba Madu ya sauke tare da É—aukar waya Yace" Dama Hajiya tace in anzo É—aukar motar a'mata magana Bari in fad'ama ta.
Tsaye sukayi suna jira har ya mata waya ya fad'amaka sai gashi tafiyo ita da Amal suna sanye da hijjob.
Ƙarasawa tayi tana binsu da kallo ganin bataga buzun da ya kawomata kaya ba.
Cikin dube -dube tace yo ina ÆŠAN DAKO kayan yake?
Cikin matsananci Ɗumi dake cin Iro ya fara magana" Ai Hajiya ɓarnar da yama Baba mu ta mota yau shiyasa aka koreshi , Saboda Baba bayaso amai ɓarna ga mota, sabodama yarda da shine yasa ya bashi to amma kinga harda marfi ya cire mata uwa uba kuma Baba baison fuskar shiba tsawon watanni shidda sai ɗazu ya buɗemuna ita, Wallahi Hajiya abun mamaki ashe Bature ne shegen aka turoshi ya ga asirin Dukiyar Baba Dan yaje ya faɗama yan uwanshi azo ayi KIDGWASHIN ɗin Baba asaceshi, Aiko Baba ya korai tin ɗazu ba mu son inda yake ba...
Wata ityin dariya Amal ta kwashe da ita ganni yanda yaketa rattafa zance harda ambatar sunan kidnapper's da kidgwashin ..
Sosai jiki Mamy yayi sanyi hakanan taji yaron ya shiga ranta cikin sauri tace" Toni yanzu wazai ida kawoman sauran kayana, Gashi gobe zanyi rabon nan, Kana dan Allah inda hali ni ku nemomanshi inason ganin shi .
Iro Yace" Ga sauran kayanki nan cikin babbar mota wasu suzo mukama dan gaskiya ni ko Rabin buhu ban iya dakkowa, Saboda Hakarkarina ciwo suke banima da isasa lafiya.
Cikin bacin rai "tace to ina wancen yake ku kiraman jarumin mana sai aturoman lusari irin ka mizakaman wannan ma ai haukane inane gidan su?
Iro yace wallahi bansani ba Hajiya.
Mamy tace "number wayar shi fa?
Iro yace" eh ina da ita gatanan ya faÉ—a yana nuna mata wayar shi.
Karba tayi ta kwafe awayar ta tare da kangawa a'kunne.
Shi kuwa Habu dake É—akin Ammi suna fira yaji wayar shi na Ring. Ganin bakuwar number ne ke kiranshi hakan yasa ya É—auka tare dayin sallama.
Daga ɓangaran Mamy amsawa tayi cikin Dattaku tare da mai bayanin kanta akan tanaso ɗan allah ta Ɗaukeshi aiki duk wata zata biyashi dubu ɗari in ya amince zai dinga kulawa da wasu hidimar gidan sauran bayani dai in yazo yaji.
Shuru yayi kan shi a'kasa saima wani irin ɓacin rai dake tasomai akasan zuciya "Dubu dari yasake maimaitawa akan laɓɓanshi tare da taɓe bakinshi ya saki wani murmuahi Mai ciwo.
Ammi dake jin duk abunda suke faÉ—a ta É—agami kai alamun ya amince..
Bazai iya tsallake umarnin taba duk da baisoba saboda Yarinya gidan amma bazai iya fad'amata ba.
Cikin dusashiyar muryarshi yace" Na amince.
Farin ciki sosai mamy taji inda ta hau zubamai godiya kamar yamata wani abu.
Idon shi ya limshe batare da yace komi ba.
Cikin É—oki tace to kazo yanzu.dan Allah akwai aikin da zakamun.
Uhm yace yana kashe wayar shi.
ÆŠago kan da zayyi yaga fuskar mahaifiyarshi ayalwace da farin ciki.
Hakan yashi tsiramata ido ko kyaftawa bayayi aduniyar da suke ciki yana fatan yagan ya zama farin cikin iyayen shi, Yana so yaga mahaifiyar shi ta samu gata ta dalilin shi da yar ƙanwar shi da baida kamar ta da ta taso cikin halin Rayuwa.
Murmushi ya saki Dan ƙaramata kwarin gwiwa, murmushin daya bayyana asalin kyanshi da kwarjinshi gawata siririyar wushirya data bayyana a tsakiyar fararan jerarun hakoran shi.
Mamy ta É—aga hannu sama tace" Allah nagodemaka daka kawomana mafita cikin gaggawa, Allah ga bawanka ka saukaka mai wahalar da yakesha ubangiji ka jibanci lamurran mu.
Ameen ya amsa yana mikewa ya tsaye yace "zanje in dawo.
Mamy tace "Yanzu Sadeeq haka zaka dinga fita ko kuwa zaka dinga sanya Rawanin?
Shuru yayi yana nazri saikuma yace" Bari in maida wayan cen kayan kawai inkuma sanya rawani inyaso gaba in naga sun aminta dani sai in daina sawa.
Cikin Amincewa tamai fatan ALKHAIRI da kuma fatan nasara a'rayuwar shi.
Ameen ya amsa yana juyowa ya shafi Fuskar Hamrat ya ficce.
Sauri -sauri ya sanya kayan da basu gama bushewa ba ya naÉ—a Rawanin tare da fitowa yana duba lokaci yaga biyar da rabi, Cikin sauri yamata bankwana ya fita tare da tare Machine ya faÉ—amai inda zai kai shi.
Tinda suk shigo layin yaga babba J5 yason aiken su aka kawo shiyasa ta nemeshi.
Siririn tsaki ya saki tare da karasawa wajen ya sallami mai machine É—in.
Ana ya gansu tsaitsaye yakarasa tare da cema Mamy" Barka da marece Hajiya.
Tace yawwa Habu ko kaifa, Naji daÉ—in zuwanka yanzu ga kaya nan ashigo dasu asasu inda yan uwansu suke zuwa gobe za afara rabasu zansa akawoma mota.
Kai ya jinjina tare da cema Iro daya saki baki yana kallon shi "kashigo da motar ciki.
Bakaniken yace ai ta garejin muce bari ashigo da ita.
Wangale musu get din Habu yayi cikin kuzari suka shigo da motar ya nunamus inda zayyi parking dinta kusa da D'AKIN.
Anan sukayi kam cikin jarumta ya fara kwasar kayan akafaÄar shi yana shiga dasu.
Cikakken mint talatin baiba ya tsauna su cikin Äakin.
Iro ya saki ihu tare da fad'in Hokai jarumi Jarunaj wallahi dole Bab yayi misir (Missing)dinka saboda samun jarumi yanzu kamarka babban aikine ,wallahi Allah yasa inyi K'arfi irin naka.
Baice komi ba haka kuma bai amsa ba.
Ita kanta Amal ya masifar burgeta dan ta yaba da zaɓen Mamy tasu da tace tanaso yazamana mai aikin gidan su...
Bayan sun gama mamy ta cema su Iro zasu iya tafiya ta gode.
Bankwana sukai sukaja motacin sukayi gaba ..
Wata kyakyawar Bukka da akayita saboda hutawa tace ya biyota.
Binta yayi har zuwa wajen inda ta samu wuri ta zauna shikuma yayi tsaye kanshi a sunkuye...
"Ina son ganin fuskarka Habu saboda inson da wa nike zaune, in'yaso daga yau saika cigaba da lullube abunka ba damuwata bace mamy tafad'a cikin natsuwa...
Baitsaya gardama ba ko wani fargaba a'hankali ya since rawani..
Tin kamin yagama amal ta mike tsaye jikinta na rawa tana nunashi da yatsa......
5/18/22, 09:33 - MY MTN 2: D'AN DAKO 🌹
MALLAKI 🌹
UMMY AYSHA 🌹
🅿ï¸7ï¸âƒ£&8ï¸âƒ£
"""Fitunannu idon shi ya watsamata tare da kauda kanshi gefe yana sakin ƙaramin tsaki.
Cikin tsanani ruÉ—u Amal tace" da gaske kake kai ÆŠan Dako ne?
Kai ya jin-jinamata batare da ya kalle ta ba.
Ita kanta Mamy saida taji zuciyar ta ta buga da karfi ganin kyakyawan saurayi kamar shi wanda som babu alamun da suka nuna yayi kama da ÆŠan Dako , Dan ko kayan sa fess suke babu wata lalacewa babu kuma faci jiki...
Amal zatai magana Mamy tace zauna ya isa haka kaima zaka iya zama.
Cikin girmamawa Yace" Aa Hajiya basai na zaunaba ina sauraran ki dai...
Mamy tace shikenan. "Dama inaso gobe zansa akawoma mota zan haÉ—aka dasu Amal ku kaimun kaya cen gidan mahaifiyata, Zaka tsaya ta lissafamaka duk wanda za'aba ,zaka É—auka ka kaima mutane, Bayan angama inaso ka dawo gidan nan da zama kana É—an kama ma Baba Madu aikin bude get din cen , Naga ya fara manyanta, Sannan yan aike -aike da suka dace zaka dinga zuwa kana muna, Wannan shine kawai aikin ka, inaso ka haÉ—o kayan ka ka dawo gidan nan ,ga É—aki cen daka tsauna kaya idan ka kwashe zaka sanya naka a'ciki, Ina fatan tsarin yamaka haka?
"Bai manba Hajiya.
Ya bata amasa cikin Natsuwa..
Kallon mamaki suke binshi dashi ganin irin gatan da akaimai amma babu wata shakka yace tsarin baimai ba.
"Komi yasa kace haka "?
Mamy ta furta.
Saboda ina da mahaifiya da ƙanwa da nine jigonsu, Ni suke gani suji daɗi, Ni mike zama muyi fira dasu in maye musu kewar mahafina! Wannan shine kawai.
Murmushi Mamy ta saki tare da cewa indai wannan ne karka damu zaka iya maidosu gidan nan da rayuwa suyi zaman su ,Nidai na aminta dakai, Bana tinani wata cutarwa daga gareka, In ma mahaifiyar taka zata iya sai ta É—an dinga kamamun wasu aikace -aikacen nan part É—ina.
Wani kallo ya mata da yasata shan jinin jikinta, ta rasa miyasa take shakka yaron da baifi shekara 30 ko Da 31 ba, Yana masifar yimata kwarjini tana jinshi kamar É—an da ta haifa..
Cikin fushin da yatasomai murya a'kausashe yace mahifiyata bazatai aiki ko inaba,In hakane haihuwata batai mata rana ba kenan,Ayanzu data ajiye kamata tafi bukatar hutawa fiye da da,in dai har zanfita ta fita to menen ribar haihuwar tawa ma Hajiya? Ina son Ammi na bana fatan ace wai tayi wani aikin wahala Dan zata samu abunda zataci,Nidai da nike namiji Zan iya iya aikin karfi wanda yafi Dako wahala dan sama mata farin ciki, In zaki amince ma zuwana karfe 8 na safe in tafi bayan isha to shikenan, In kuma bazaki yarda ba to gaskiya asamu wani saboda nima inaso in samu lokacin da zan tattauna da mahaifiyata inji matsalarta data Ƙanwata data ragemun,Dan nine garkuwan su .
Ya faÉ—a cikin gaskiyar shi tare da tsuke baki dan ya daÉ—e bayyi irin wannan dogon sharhin da wani ba sai da mahaifiyar shi ko sst shi....
"KAIFI ÆŠAYA"Mamy ta furta ,Dan ta fahimci yana da tsatstsauran ra'ayi sosai..
Tace shikenan na amince ma hakan, Ina fatan ka rike amana shiga da ficen gidan nan .sannan miyasa kake son rufe fuska? Ko buzayene ku..
KafaÉ—ar shi ya É—aga.
Tare da faÉ—in ko É—aya, kawai Bakowa ke yarda dani ba idan yaga fuskana shiyasa,Suna ganin kamar zanzama É—an leken Ashirin su..
Amal da ta ke binshi da ido cike da burgewa tace.
"Ai kana da kyau sosai Wallahi kamafi Aunty Amnah kyau ba kaÉ—an ba Shiyasa ake kin yarda..
Kallonta yayi tare da kauda kanshi gefe.
Mamy tace sunan ka Habu ko?
Yalwatacciyar sumar shi ya murza tare da cewa. "Sadeeq ne sunana, Tsohon da nike aiki dashi yasamun Habu, Saboda bazai iya faÉ—in sadeeq ba.
Mamy tace shikenan daga yau