Showing 42001 words to 45000 words out of 94971 words
Chapter 15 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt
bazan sakeyi da kowa ba, ka tashi dan Allah .
Ganin bai ko motsa ba hakan yasa ta kara buÉ—e rigar sa ta sanya hannuta ta danna ramin da É—an karfi.
Wata irin zabura yayi da ƙarfi batare da ya bude ido ba.
Yayin da ita kuma taji wani ɓull kamar kwanciyar ruwa cikin abin.
Ganin ya motsa yasa da sauri ta ƙarasa wajen bakin shi bata saya komi ba ta dinga huramai iskan bakinta da masifar ƙarfi.
Wata irin ajiyar ziciya ya sauke yana bude idon shi kadan da suka ƙanƙance sukayi ja..
Tace sannu Sadeeq! kanaji ba, ko in fita in É—an samo maka maganin da zai ragemaka raÉ—aÉ—in ciwon.
Ido kawai yake binta dashi yanajin wani irin radadi a ciwon sa.
Da sauri ta mike ta shiga É—akinta hijjob inta ta sallah ta É—akko tasa.
A karo na biyu kenan ta fita tinda tazo gidan.
Tana fitowa taga Wata budurwa da ta É—akko icce zata shiga gidan dake kusa da nasu.
Da kallo ta bita kamar zatai magana kuma ta kyaleta ta tare Napep tamai kwatancem sulhu pharmacy.
Yana kaita tace ya jirata. Bayan ta shiga ta faÉ—i mishi abinda takeso bayan sun bata suk mta list É—in 4100 .
Sosai taji gabancta ya faÉ—i dan ya kama saura 900 kenan ,ga mai Napep.
Haka ta karba ta fito.
Bayan ta fito ta shiga ya maidota ya ƙarbi 300 .
600 din hannuta tabi da kallo wasu hawaye masu zafi suka zubomata.
Ya kamata ace kamin yasha magani ta bashi wani abu yaci, dan tin jiya baici komi ba.
Da kafa ta ƙarasa wata rumfa mai shayi dake kusa da gidan da take
Ta mika duk ƙudin tace abata madara da sugar da bread sai a bata ruwan Lipton tinda bata da gas babu kuma wuta.
Mai shagon yace haba Hajiya wai duk cikin dari 600, toko madara yanzu 300 ,kinga kudin bazai isaba ko.
Shuru tayi tana kallon yanda ya balbaka wuta da itatuwa yanda suke ci sosai a Murhu.
Yace Hajiya ina magana fa.
Tace ka bani na É—ari ukku ka bani ciko, amma kamun hadin shan mutum É—aya dan yayi kauri sosai.
Yace angama aiki nane.
Bayan ya bata tace dan Allah ina ake saida wannan iccen, kana yazan kunna shi yaci sosai.
Shekeke yake kallonta irin kallon kinma raina mutane.
Afusace yac order sa nayo daga chaina. in'kinaso kawo ayo miki...
Murmushi kawai ta saki dan yanzu ita ta riga ta dawo rakiya rayuwa, som babu tabbas ga rayuwa, wai yau itace ke zullimin fidda kudi.
Tace kayi hakuri Malam. ta faÉ—a tana juyawa da Sauri ta shiga gidan ta rufe....
5/18/22, 09:34 - MY MTN 2: *Littafin🌹DAN DAKO🌹 na kudi ne biya ki karanta cikin Aminci. Biya 300kacal to 0006454115 Amina Dahiru jaiz bank,or MTN card to this number 09165832002. then send the evidence of payment via 07038423451* ğŸ¤ğŸ™ğŸ¤²
🅿ï¸3ï¸âƒ£1ï¸âƒ£&3ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
""Da Sallama tasa ƙafar ta tare da saurin ƙarasawa inda yake .
Anan ta ganshi yanda yake, Amma ko numfashin kirki bayayi, idon shi kuma duk sun juye sunyi jawur.
Gilgizashi tayi sosai tare da cewa .
Sadeeq! ka tashi ka sha Tea in'baka magani , Dan Allah.
Shuru yayi dan yana son yayi magana amma yakasa, yanajin ciwon dake damun shi kamar zayyi sanadin tafiyar sa lahira ,ya kuma hana shi cika Burin shi ..
Hijjob in jikinta ta cire ta ɗakko cup kiching tare da ƙarasowa wajen shi tasa hannu da kyal ta ɗago kanshi ta ɗora a cinyar ta.
Saida ta tabbatar ta dai& dai yanda zaisha batare da matsala ba kana ta É—agoshi dakyal tana numfashi ta kafamai cup É—in bakin shi.
Kanshi ya gilgizamata alamar bazaisha ba.
Tace'' Dan Allah karkamun haka mana, kasha zanbaka magani, zaka ji sauki insha Allah, ta ƙara kafamai kasancewar yanajin yunwa yasa ya ɗan sha kadan ya kauda kai tare da ƙoƙarin tashi Amma ya kasa.
Wayar ta dake gefe ta shiga ring.
Da sauri ta duba ganin Abul khairi ne yasata jan tsaki.
Haka nan ta samu kanta da datse kiran.
Kusan so biyar yana kiranta tana kashewa, Tare da sanya wayar airplane mode...
Kallon ta yake sosai yana mamakin abinda ya hanata É—auka .
Ido ta É—ago karaf ya faÉ—a cikin nashi.
Kallo- kallo suke ma juna kowanne da abinda yake tinani .
Ita tana tinanin waya halbeshi har wajen yamai wannan mummun illah.
Yayin da shikum yake tinanin wai yau Amnah ce ta fara sanyi haka ,har take ɗora talakka bisa kafarta lallai Duniya juyin ƙosai.
Idonta ta janye tare da mikomai magani da ruwan pampon data Tara dan yanzu sune ruwan shan su.
Bakin shi ya buɗe ta bashi tare da kwantar da kanshi bisa hijjob inta ta tashi tana miƙar gajiya, dan Sadeeq in'garman namiji ne.
Drip din da ta siyo ta sargafa ga wata ƙaramar igiyar da yake musu wanki ta ɗora akai , Tare da duƙawa ta kama hannu shi ta sanya wata siririyar roba ta ɗora mishi , tare da ɗan dukan saman hannu kadan-kadan .
Tana gani ta samu jijiyar da take buƙata ta zaro Allura tare da kallon shi.
Idon shi fess akanta yana kallon yanda take Abu cike da sanin makamar aiki.
In maka mai zafi ta faÉ—a fuska a É—aure..
Kai ya ji jinamata yana lumshe ido dan zaton shi da gaske mai zafin zatamai..
Bakinta takai saitin jijiyar hannu ta kafa tana É—an zuko wurin KaÉ—an -kaÉ—an tana danna mishi yawun bakin ta.
Ido ya lumshe tare dajin tsigar jikin shi na tashi.
Sai da takai 5mnt kana tasa Tissue ta goge anan jijiyoyin sukai raÉ—a -raÉ—a.
Allura ta É—akko tare da lumshe idonta tana cije baki ta soka masa kaÉ—an- kaÉ—an har ta shige baki É—aya ,kana ta sauke ajiyar zuciya.
Kallon ta yayi yana mamakin miyasata wannan lallamin bayan yayi tinanin da mugunta zata mishi.
Tana gamawa tace" sannu zaka iya magana.
Kai ya ÆŠagamata.
Tace to kace wani abu mana .
ta faÉ—a cikin shagwabar da batason ta iyaba.
Murmushi yayi yana juya kanshi gefe dan shima yana fatan ace ya samu bakin magana ko godiya ya mata saboda Sosai yakejin raɗaɗin na ƙasa..
Tea'n dake gefen shi ya nuna mata alamun tasha.
Tace aa zaka buƙata dan akwai Allura dana maka cikin ruwa zakaji yunwa sosai , kuma babu komi gidan.
Wayar shi ya É—auka ya fara rubutu kamar haka.
"Dan Allah kisha mana ambah ,Hakkin ci dake yana kaina, amma bana iya fita samo miki wani abu,kisha ba damuwa ni bazanji yunwa ba insha Allah.
Ya mikamata wayar.
Tana gama karantawa batason sadda wani irin tausayin shi ya dirar mata azuciya ba.
Wato bayaso Amnah yana son ya tsare hakkinta kenan, lallai yason daraja aure. Astagfirullahu lathi la ilaha illahuwal hayyu qayyum wa atubu ilaik ta fara jerowa cikin zuciyar ta ,tare da dana sanin ruÉ—un da shaidan yamata,duk da bataso bai kamata tayi wasa da igiyoyin auran sa dake kanta ba.
Tace bari in dafa Abinci.
Wayar ya karba yasake rubuta.
" Babu Wani mahaÉ—i ga abincin ki barshi..
Tace karka damu bari in ɗan fita ƙaɗan.
Kanma yayi magana ta ficce tare da shiga gidan dake kusa da nasu, inda taga yarin yar nan ta shiga.
Sallama tayi tare dayin tsaye tana ƙarema gidan kallo komi tsaf ga girki suna tayi da icce.
Sallama ta sakeyi aykaro na biyu.
Wata matashiyar mata ta fitito da shekarunta sunkai 30 ta girmema Amnah.
Da fara'a ta ce sannu da zuwa baƙuwa mukayi shigo mana.
Amnah ta ɗan shiga ƙaɗan tare da cewa "ina wuni.
Tace lafiya lau sai dai ban waye kiba?.
Shuru tayi tama rasa mizatace.
Wannan budurwa da zatakai shekara 15 ta fito tare da cewa" laaa Mama wannan ai Amaryar ÆŠan Fulani mai shago ce , nima É—azu naga ta fito gidan..
Cikin fara'a doysai matar tace "kai Dan Allah Fatimah, aiko bata taɓa shigowa ba muma bamujeba, sannu da zuwa Amaryar. ta nunamata kujera tace zauna.".
Amnah tace "ba zama zanba , Dan Allah yanda zan kunna wuta nikeso ingani zanyi girki ne.
Tsororo matar ke kallonta tace" iccen ne baki iyaba ko-ko ? Ba nan garin kike bane..
Amnah tace "eh gas ɗina ne ya ƙare, to yanda zataci kamar naki nike so..
Matar tace tofa ikon Allah, inkana da rai kasha kallo, to ga Fatima nan ta biki ta haÉ—amiki ko..
Amnah tace" aiko nagode, amma banda wannan. ta nuna murhu.
Mamaki ya ƙara kashe matar tace" to ina zuwa.
Ɗaki ta shiga sai gata da sabon Murhu ta bata tace gashi, Sabone bai siyo , nawa sun farayin ƙasa ..
Amnah tace ngd zan maido in nagama.
Da suri tace "aa haba Dan kama makwafcin ka abu babu komi Wallahi.
Fita sukai fatima na biye da ita .
Suna shiga gidan ambah ta juyo da niyyar mata magana..
Anan taga ga baki É—ayan hankalin fatima naga sadeeq da yake bacci cikin rashin jin DaÉ—i.
Wani irin takaici da haushi ya kama Amnah har batason sadda tace" ke ki fara abinda ya kawoki mana.
Yarin ya tayi furgigit tare da cewa" ai babu icce.
Amnah tace ina ake sayar wa, kuma nawa?
Tace wajen baban mu, Mai sayar da shayi, naira É—ari .
Amnah ta zara ta bata ta fita sai gata ta dawo tace'' Aunty gashi harma da ashana na ƙarɓo.
Tace to..
Nan ta fara haÉ—a mata dan -danan wuta takama.
Tace Aunty Abada tukunyar da za'aÉ—ora.
Amnah ta shiga kiching sai gata da tukunya mai masifar kyau nata da aka samata.
Yarinya tabi tukunyar da kallo tace" aka sata zata lalace, Bari in É—ebo toka gidan mu.
Amnah bata fahimci mitake nufi ba, ta dai É—agamata kai kawai tana mai rufama sadeeq wani bedsheet marar nawi a jiki....
Da sallama fatima tashigo tare da ƙarasawa wajen pampon ta zuba tokar ƙasa tare da zazzaga kill ta kwaba ta murje tukunyar tass ,kana ta tarba ruwa ta ɗora tana mai iza wutar
Ganin tanaci sosai tace" Aunty mizaki dafa?
Amnah tace "shinkafa..
Fatima tace A'a kikawo asiyo miki wake da mangyaÉ—a da tashi in'dakamiki na iya sosai, muma ita zamuyi, harma da salat.
Tace zan kashe nawa?.
Tace 150.
Ido Amnah ta zaro ganin in'tabada saura 50 naira kenan ," Ya Allah" tace tanajin idonta na cikowa da kwallah...
Tace karaɓa kisiyo Man Ƙulin mai yawa ,ki kashe kuɗin duka.
Fatima ta É—agamata kai tare da ficcewa.
Bata jimaba sai gashi ta dawo saura cikin Naira biyar ta ba Amnah.
"Tace rike shi ,wannan yazan masa.
Yarinya ta zauna ta gyara waken tsaf ta wanke ta zuba , tare da wanke salat din ta yayyanka shi tare da tumatur da albasa.
Bayan ta gama ta dakama Amnah yaji mai daÉ—i, irin wanda mamanta ke dakawa.
Tana ganin waken ya Nuna tace "Aunty ki zuba shinkafar fa.
Amnah ta debo mai yawa ta wanke ta zuba tanajin hayakin har cikin kwalwarta, ga jikinta duk ya ɗauki ƙauri, kai innalilli tace tana sakin kuka.
Da ido yarinya ta bita tare da cewa "Aunty mai akaimaki, ko hiyaki ke akwai?..
Kai kawai Amnah ta ÆŠagamata.
Fataima tayi dariya tace'' niko munsaba shiyasa ba maji.
Amnah batace komi ba sai gishiri da ta É—ibo ta zuba akai.
Ta tashi da niyyar É—akko mataci tsanewa taga idon Sadeeq akanta alamun ya tashi kenan.
Da sauri ta ƙarasa wajen shi tace" sannu! acire ya ƙare ko,ya saukin jikin naka? bakajin komi? yunwa kake ji ko ?ingama girki kaci? zakaci ko.? ta faɗa cikin rikicewa dan duk batajin daɗi itama.
Cikin ƙasa da murya ya fara magana .
*Amina kece da hura wuta ,waya koya miki? miyasa zakiba kanki wahala, kiciremun in tashi in'fita insamo miki abinda zakici..
Kai ta gilgizamai tace'' bazaka iyaba Sadeeq, wannan wajen akwai wata matsala na tabbata,kayi addua ALLAH ya baka lafiya, amma zanso muje Asibiti kar ya zamemaka wata illah.
Yace" banda komi baki da komi Asibiti kuma sai kana da kuÉ—i.
Kallon wayar hannuta tayi taga aƙallah zatakai dubu dari da wani abu, Dan ko sadda ta sayeta kusan 200k .
Tace karka damu bari in'ƙarasa dai...
Kai ya jinjina mata yanajin tausayinta har cikin ranshi, lallai duniya juyi -juyi, rayuwa babu tabbas.
Bayan ta tsane abinci fatima ta kashe itatuwan tare da mayar da murhun gefe ta dora itatuwan akai, ta gyaramata wajen tace na tafi.
Amnah tace zokici abinci.
Kai ta gilgiza tace A'a Aunty shine mukayi na tafi.
Amnah tace Dan Allah karkice haka, duk wahala da kikasha?.
Fatima tayi murmushi tace wallahi bazan ciba, ta faɗa tana sanya ki ta fita tana mai jan ƙofar.
Amnah ta shig kiching ta É—akko kuloli ta zub abinci mai yawa, tare da zubawa akula madaidaiciya ta aje gefe, kana ta juye sauran awata kula.
ÆŠakinta ta shiga ta cire kayanta tasa a wadrob da ta cika da kayyaki babu kudin sabulun da zasu wanke.
.
Babban towel ta É—akko ta É—aura tare da É—ira hijjob akai, kana ta fito tashig wanka.
Bayan ta fito ta zare mai ruwan , Tare da ta dashi dakyale ta jinginar dashi ga bango ,ta zubomai ruwa a buta tace kayi al'awallah, daga nan sai kayi Sallah.
.Yace wanka nike buƙata yi..
Ta zaro ido tace to wazai iya daukar ka, kana kato da kai..
Murmushi ya saki a hankli yace kece mana..
Harara shi tayi tace bazan iyaba ,bayan duk kajama na gaji.
Yace "uhm" Tare da ƙoƙarin dafa ƙasa ya tashi amma ina ya kasa.
Yace Amnah ki kamani Dan Allah .
Amnah tace to" tare da zuwa ta rike hannuwan shi taja baya sosai da niyyar ta kamoshi ya mike.
Wani irin jigif taji yayi kuma ko motsi bai ba.
Tace wayyo Allah kashin bayana, Dee ka taso man.
Cikin dauriya ya kama ya mike dakyal yana dukewa, dan baya iya mikewa tsaye sosai.
Wani irin jiri ya kawomai ziyara, hakan yasa yayi baya zai faÉ—i.
Aguje Amnah tayi kanshi ta rungumoshi jikinta sosai .
Anan suka fara layin faduwa dan yamata nawiem
Arikice take kallon shi tana kallon yanda zaisha ƙasa, karshentama kan shi zai bugu ta fara tinani.
Cikin hanzari ta wullo filo da ƙafarya tare da durkushewa dashi har towel din jikinta na cirewa.
Wash tace da karfi dan gwiwoyinta sun bugu sosai.
Numfashi ya fesar tare da juya da kanshi kanta yace" Allah yasaka da Alkhairi nagode .
Itakam hannu kawai take yarfewa dan gwiwar ta zafi.
Baison sadda yasa hannushi ya jawota jikinshi ba suna fuskanta juna.
Yace Sorry Ragguwa yarinya ,Nine ko?
Pink lips dinta ta turo tace wallahi nawie kamar buhun masara ,duk kaine kasa kayi wannan nawin da kake É—aukar kaya masu nawi.
Murmushi kawai ya saki yana ƙara lafewa cikin jikin ta.
Amnah ki debomun ruwan anan sai inyi wanka na yace..
Ido ta zaro tace kai baka da kunya ne?
Yace zama da kene ya kawo hakan.
Tace yo ai na daina bazakayi ba, ka hakura da wankan dama ai sanyi- sanyi ake.
Yace uhm yana gyara kwanciyar shi , Yana tinanin mahaifiyar shi da ƙanwar shi ,shine kawai garkuwan su gashi kuma abubuwa na neman kwantar dashi.
Akaro na biyu yayi ƙoƙarin tashi Allah ya taimakamai ya mike amma baya iya tsayuwa sosai, sai ya rankwafa.
Ahankali yake bin hanya har ya shiga toilet.
Amnah ta bishi da kallon tausayi dan ta fahimci akwai matsala ga raunin nashi sosai , Tinda ya fara irin wannan tafiyar.
Tana nan zaune ya fito dagashi sai jallabiya ya isa ɗaki ya sanya kaya marasa nawie ya fito a dudduƙe ya zauna yayi alwallah ,yana gamawa yayi sallah daga zaune.
Itama Sallah tayi bayan ta gama ta sanyo wata atamfa riga da skit sun mata masifar kyau ta fito waje ,tare da shiga kiching ta zubomai abinci takawomai da ruwan pampo ,dan basu da ko pure water ,kuma babu kudi hannu ta balle ta siya.
Kai ya kaÉ—amata alamar ya koshi.
Tace Dan Allah kaci.
Yace ke kika fi dace wa da kici Amnah, ina lura dake baki ci komi ba, kinaso ciwo ya kamaki, ke kwance ni kwance?
Kai ta gilgiza alamar aa.
Yace to matso muci wannan, amma kar kisamun yaji sosai.
Kai ta É—agamai tana ci tana bashi Ahankali, Duk a takure take dan dai kawai baya lafiya ,bayan sungama ta tashi ta É—akko sabon gyale cikin kayanta tace am nace kamun kwatancen gidan su Ammi sai inje in kaimusu, kaga kar suyita jin yunwa ko.
Cikin mamaki yake kallonta,tinda tazo gidan bata taɓa mai magana maman shi ba.
Da wani irin zallar farin cikin da yakasa ɓoyuwa a fuskar shi yace "Amnah taya kikayi abinci dasu, ina kika samu kuɗin?.
Tace Allah ne ya bani. ta fada tana murgudamai baki.
Yace to kina da na Napep din da zakije?.
Tace ga napep ɗina nan. ta nuna ƙafar ta.
Ido ya zaro yace" A'a kibari inje kawai akwai tafiya fa.
Tace aa kayi kwanciyar ka, kamun kwatance zanje.
Anan ya kwatantamata tace to natafi sai dare zandawo.
Yace wai dagaske tafiya zakiyi ki barni ?
tace'' eh sai nadawo ta ficce.
Ahankali take tafiya hannuta rike da kula sai tambaya take ana nuna mata hanyoyi, har sai wajen ukku ta isa ta masifar gaji ,duk ta jigata,ƙafar takam duk tayi fushi. .
Wani yaro ta tambaya gidan su Sadeeq anan tamai kwatancen shi.
Yace gyisan da ba a shiga?.
Kai tsaye ta É—agamai kai.
Anan ya nuna mata ta sanya kai da sallama tana nishi.
Ammi dake zaune hannuta rike da alkur'an sai Hamrat dake kan cinyoyinta tana Bacci ta É—ago kai cikin mamaki tana amsa sallama ...
Kallo É—aya Amnah tamata ta ta janye kanta gefe , dan hakanan ta samu kanta da jin nawin matar Da ke amsa sunan sirikata.
Cikin fara'a sosai Ammi tace sannu da zuwa.
Amnah tace yawwa tare da zama cen gefe kanta a ƙasa tace" Ammi ina wuni .
Ta faɗa cikin sanyi da kuma sakkowar zazzafan zazzaɓi da ya mata sallama..
Ammi ta amsa tana mata kallon rashin sani.
Kular gabanta ta ajiye kusa da ita tace ga abinci nan yace A kawomiki, Hamrat bacci take?...
Salati Ammi ta saki tana tafa hannu tace'' wai dama É—iyatace bansani ba , Allah sarki sannu dazuwa, tare kuke ne? Ai sai yanzu nagane danaga kamanni Mamy ki.
Kai ta gilgiza alamar A'a batasake cewa komi ba.
Ammi ta karemata kallo tare da zancen zuci ita bataga wata isa da gadara da akace yarinya nada ita ba.
Amnah ta tashi tsaye tace" ina kiching in É—akko miki flat.
Cikin jin dadi Ammi ta gwadamata.
Anan ta shiga ta É—akko taga komi a tsaftace tabbacin Ammi yar gayuce kenan .
Tana zuwa ta Duƙa ta zubama Ammi, tare da tashi ta isa wajen jerin butoci da ke jere ta wanke ƙafarta da fuskar ta da tasha zufa ,kana ta dawo ta zauna.
Ahankali ammi ta fara janta da labari tare da nunamata ta saki jiki ita bata da matsala ,kuma sirikata ai yartace..
Tace hakane Ammi.
Karfe hudu nayi tayi sallah tace ma Ammi zata tafi.
Tace wai tin yanzu? na dauka sai anjima zaizo ku wuce.
Tace aa zanje da kaina dai.
Ammi ta mata