Showing 24001 words to 27000 words out of 94971 words
Chapter 9 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt
suka wuce.
Bayan sun isa gida Hamrat taita yaba kirkin Mamy da Aunty Mai kirki' tana ba Ammi labari.
Farin ciki sosai tayi tace'' lallai Aunty Mai kirki wato har kinmata suna kenan.
Sadeeq ya taɓe baki batare da yace komi ba.
Cikin damuwa yake faÉ—ima Ammi halin da yake ganin Mamy yau ciki kamar ba bikin Sallah a keba som batada walwala.
Ita kanta duk sai taji bataji daÉ—i ba saboda kyautatawa ta garesu tafi gaban ace tana cikin damuwa suyi burus..
Cikin sanyi tace musata Addu'a Sadeeq.
Daga nan yaje masallaci,sai da aka gama isha kana ya dawo gida yayi wanka da wuri yama Ammi sallama yashige É—aki.
Itama É—akinta ta kama Hamrat suka shige abinsu.
Yana shiga ɗakin yahi ya cire haramin sa tare da ɗaukar wani ƙaramin towel milk ya ɗaura ma kugun sa .
Wajen wani babban madubi dake É—akin wanda ke like da bango yaihi tsaye ya tsirama faffaÉ—an kirjin shi ido
Ko kyaftawa ba yayi.
Ahankali yasa fararan dogayen yatsun shi ya fara Zagaye wani babban tabo dake kasan zuciyar shi wanda yayi kama da halbi bindiga.
Lotsa wurin yayi da ƙarfi baison sadda yayi ƙaramin ihu ba yace ashhh.
Jajayen idanuwan shi suka kaÉ—a sukayi jawur.
Da sauri yake lailaya wurin yana cije leɓe .
Afusace yace "kamar yanda nike jin zafin nan haka nike fatan ku ƙare rayuwar ku cikin zafi da bakin ciki, Baku Raunata banza ba, ina nan dawowa gareka bada jimawa ba.
Alkawari nayima rayuwata duk ranar da wani wanda ya sanni ya ganni to tabbas zaki zai koma Dawa.
Wata daya..
Wata biyu...
Wata ukku..
Kacal na É—ibar ma rayuwa Ahalin dake zaune daram akan kwaraga zalinci.
Zan yanke maku farin ciki kamar yanda kuka yanke nawa,Kukasa Kasata ta gagareni zama, haka zan koreku da rarrafe kubar iyalan ku.
Daga nan Kurar da ta daÉ—e da yunwa zata fara fatattaka naman jikin ku dana Ahlin ku.
Daga nan ne angulu zatayi dirar mikiya gidanta na tsamiya.
Cikin wata irin fuskar da bantaɓa ganin shi ba ya juya ya faɗa kan katifar shi, tare da ɗakko sistem dinshi ya fara aiki yanayi yana latsa waya, tare da magana da banajin miyake faɗa dan cikin wani bahagon yare yake magana.
Sama da awa É—aya kana ya ajiye ya kwanta.
Washe gari kamar yanda ya saba bayan yaje masallaci ya dawo yayi shiri cikin boyel din da Mamy tamai wanda yayi masifar yimai kyau, ya kashe hula tare da feshe jikinshi da turare .
Break Ammi ta haÉ—amai yaci ya koshi kana yamata sallama ya tafi. Hamrat tayo mai rakiya tana faÉ—in ya gaida mata Aunty mai kirki.
Banza yayi da ita ya kyale tare da fita da machine É—insa.
Kai tsaye gidan Mamy ya nufa .
Waya ya mata akan ya iso.
Tace "to sadeeq gamunan fitowa.
Shuru yayi yana mamakin to wai daga Dan Dako driver ya koma kokuwa? tinda yaga in'zata gidan Nene ita kekai kanta ko Æ´aran ta, toshi minene nashi?
KafaÉ—a ya idaga irin ko ajikin shi yaci gaba da zaman jiranta.
Bayan 30mnt ta fito cikin shiri har lokacin fuskar ta akwai fushi kaÉ—an, suka sake gaisawa, saiga Amnah ta fito cikin wata dakekiyar shadda pich da tasha kwalliya Royal blue, komi na jikinta royal blue ne.
Ganin idon Ammi ya sata cemai "ina kwana."
Sarai yajita amma ya shareta sai motar da ya faÉ—a .
Bayan Mamy ta shiga tace ma Amnah shiga gaba.
Kallon Mamy tayi sai kuma tayi saurin buÉ—ewa tashiga tana turo baki ganin yanda Mamy ta dallamata harara.
Cikin natsuwa yake murza sityarin ya É—auki hanyar gidan Nene.
Dai-dai Rowl É—in Lada wapa traffic ya tsaida su.
Anan ya maida hankalin shi akan mutumin daketa binshi akan machine.
Gaba ki ɗaya'n Hankalin shi ya maida kan tukinshi ganin anbasu hanya, yanayi yana kallon mutumin ta mirrow kamar ya taɓa ganin sa.
Suna É—aukar hanya gidan Nene yajuya kan mota zuwa wata hanyar ta daban.
Mamy tace Sadeeq lafiya kayi wannan zagayen.
Arikice yana kallon mutumin yace Affuwan Hajiya zanyi abune.
Shuru tayi yayin da Amnah keta zuba mai harara.
Wata kwana ya gani ya bulla ta ciki yayin da ya fado ta hagu inda yaci gaban mai machine É—in ya rufeshi ruf dan babu wata hanyar da zata fitar dakai .
Da sauri ya tsaida motar tare da fitowa a fusace hannushi rike da sit belt din da ya ciro .
Mai machine na ganin ya fito cikin tashin hankali ya fara neman hanyar da zai bulla, dan sadeeq ya riga da ya datse hanyar baki É—aya.
Da sauri ya fara ƙoƙarin tada machine ɗin dan juyawa amma karfen bature bashi da tabbas yaki tashi.
Ganin da gaske ya Dumfaroshi yasshi aje mashine din ya fara ƙoƙarin guduwa.
Cikin zafin nama Sadeeq din yayi taku biyu ya taɗemishi ƙafa sai gashi ya faɗi.
Hankali tashe Mamy ke kallon shi yayin da Amnah ke kallon ikon Allah" to miyami shi?.
Hular kanshi ya tura baya yayin da yalwatacciyar sumar shi ta zubo saman goshin sa, tare da sanya ƙafar shi dake sanye da takalma cover ya take yatsin mutumin.
Cikin ta fasa zuciya dawata irin murya yace" waya turoka wajena?.
Waye kai?
Minaimaka?.
Zan kasheka har lahira in kaima wanda ya turo ka kasheni gawar ka.
Afurgice mutumin yace" Wallahi wata ce bansonta ba, Dan Allah kayi Hakuri.
Cikin nazari yace" bakaine kamun photo ba jiya ?waya turoka.?
Cikin rawar jiki yace" itace Yallabai, Dan Allah kaÉ—agamun yatsu zasu cire.
Tsawa ya dakamai tare da faÉ—in wacece ita? kuma miyasa take bibiya na.?
Nima bansani ba Yallabai, Dan Allah kayi Hakuri .
To uban mi tace kabiyoni kamun yanzu?
Cewa tayi inbika inga masaukin ka.
Yabashi amsa cikin rawar baki.
Murmushin mugunta ya saki tare da kwantar da mutumin ya danne mai duka yatsun shi na hannuwa ,Tare da riko ƙafafuwan shi, zaro belt din yayi ya fara tsulama ƙugun shi.
Ihu mutumin yake yana bazan ƙaraba Yallabai, Wallahi bazan ƙaraba, Dan girman Allah kayi hakuri ,ga wayatama ka rike bazan sake bibiyar kaba ,wallahi dan Allah kabari ,wayyo mazaunaina .
Saida yamai bulala jamsin a ƙugunshi kana ya ɗago yana sharce zufa ,ƙafar shi yasa ya halbi mutumin kana ya ɗauke wayar shi ya dawo motar cikin murtuke fuska...
Da fari Hankalin Mamy dana Amnah a tashe yake musamman da sukaga ya rufesu babu damar su buÉ—e su fita.
Lokacin kuma daya naÉ—e mutumin yafara dukan mazaunans hi yasa Amnah bushewa da wata kafurar dariya cike da mugunta take dariya. Ganin yanda mutumin ke shure shuru.
Ganin yanda ya dumfaro motar ne cike da sassarfa yasata binshi da kallo.
Akaro na farko a rayuwar ta da taji jarumtar shi ta burgeta .
Agaskiya tanason jarimin namiji, som bata muradin lusari, jibi yanda ya hukunta mutumin da basuson miya mai ba.
Motar ya buÉ—e ya shigo tare da É—aukar tissue ya goge zufar data zubomai ga fuska .
Mamy ta sauke ajiyar zuciya tace" Sadeeq baimaka komi ba dai ko? kuma miyamaka kamai wannan dukan?
Motar ya tada tare da faÉ—in kibarshi Hajiya.
Irin yan iskan nan ne da akeba kuÉ—i suna shiga unguwanni masu kuÉ—i suna ganin shige da ficcen su, Dan asamu damar kidnapping din Mutane, Tinda muk fito yake binmu kinga yanzu sai yakoma ma wanda ya turoshi ya kaishi Asibiti...
Cikin tsoro da tashin hankali tace" Sadeeq kuma bugun nashi bazai zama aibuba, yanzu abunda mukeji cen wani garuruwan har yana neman ya shafemu.
Zufar data cika sajen shi ya yarfe sai bisa fuskar Amnah.
Da sauri ta kalleshi dai- dai lokacin da shim ya juyo ya kalleta.
Batace komi ba kuma bata goge ba.
Cikin ƙasa da murya yace" Affuwan tare da mikamata Tissue.
Ƙarba tayi amma bata goge ba , Dan sosai take jin yana burgeta da irin kasadar da yayi. A ɓangare ɗaya kuma tsoro yakamata tare da kudirin bazata sake fita ita ɗaya ba, dole asama mata driver, Mussaman da take shirin fara aiki.
Godiya Mamy tamai sosai da jajir cewa.
* yace bakomi yiwa kaine.
Bayan sunje gidan Nene ya sauka kan Mamy ma ta fito ya buÉ—e mata kofar tare da juyawa ya shige cikin palon Nene.
Da ido Mamy ta bishi tana kissima abubuwa da dama aranta.
Yana shiga Nene" tace oyoyo my lot oyoyo.
Fuska ya yatsina yace"" gaskiya Nainah kidaina cemun my lot,Infa matata taji bazataji daÉ—i ba kina cemun masoyin ki.
Nene tace yo daga abun arziki Allah ya kashe yabakani saddi ,Harma zaka raina.
Yace to banaso kibani ruwa in'tashi in fita ga Hajiya nan .
Nene tace yo Fulani micece! daga ganin ta saika tashi katafi dama dan ita kake zawa gidan ne ?.
Yace hmm tare da duba gefen da yaji Ajikin shi kamar ana kallon shi.
Karaf ko idon shi ya faÉ—a cikin na Amnah da tayi tsaye ta zubamai idanuwa .
Fuskar shi ya É—aure sosai tare da mikewa ya buÉ—e fridge din Nene ya É—akko ruwa mai sanyi ya rufe .
Ya daga murya yace" Nainah na wuce fa.
Da gudu ta rugo tana haba" Kwandon Sukari sauran kaÉ—an kaja infaÉ—a cikin a kurkin tumatarina dan sauri, fura fa na ajiye maka naje É—akkowa.
Mamy da ta shigo ta gansu sosai abun ya burgeta, kenan ya saba da Nene amma ita ko magana inba ta dole ba baya mata.
Cikin zaulaya tace oniii Sadeeq! Wato nice ka kasa sakin jiki dani sai Nene ko.
Cikin kunya ya sosa kanshi tare da kallon Nene ta gefen ido data saki baki tana kallon Mamy.
Afusace tace ni dake matsayinmu É—aya, nima my lot É—ina ne.
Da sauri yabar palon dan yaga Nene na neman sashi kunya.
Abinci da ta haÉ—amai taba Amnah tace ke fitsarariya maza je ki mikamai, sala kigaya mai magana.
Fuskarta ta yatsuna tare da ƙarba ta fita ta iskeshi zaune ƙasan bishiya yana ta latsa wayar wanda ya zane.
Cikin isa da yanga ta ƙarasa wajenshi ta ajiye tiren, kamar ta juya sai kuma tace Nene tace gashi.
Sanin rashin cin magana zai jawomi wajanta yasa ya É—aga kai kawai.
Harara ta zubamai tare da faydin sai isa shi ba kowa ba.
Aɓangaran Mamy kuwa f
ÆŠakin Nene sukashiga anan ta koramata bayanin komi.
Inda Nene tasa kuka tana fadin shikenan "Asirin mu zai tonu, maza shirya muje gidan mahaifiyar sa ayi komi yanzu,su su Amal din abarsu Anan.
Mamy tace shikenan tare da miƙewa suka fito.
Suna fitowa ta iske shi tsaye yana waya.
Sallama tamai ya ajiye waya tare da cewa mutafine.?
Kaka tace ''Aa zamuje mugaida maman kane, muje ka kaimu a ida sanin juna.
Gaba shi yaji ya wani buga da ƙarfi, haka nan yaji bai samu natsuwa da zuwan nasu ba.
Kanshi ya sosa yace" miyasa bazaku bari in É—akko maku ita ba.?
Nene tace ai anzama É—aya.
Yace shikenan muje.
Hawa wukai sai unguwar Tudun wada.
Sosai mamy ke kallon hanyar har suka ƙaraso Dan kofar gidan nasu.
Tindaga bakin kofar zaka tabbatar da tsaftar masu gida'n.
Fita yayi tare da musu nuni da gidan ya rufe Motar yace" Bissimillah.
Da sauri Nene tayi gaba tana faɗin wai kuyi ta rangwaɗa saman ƙasa. Ƙuda za'atausa ciki, ai'kwarama kayi sukuwa kayi yanda kakeso tin kamin ita ta dafe ka.
Su dukansu Murmushi sukai suna bin bayan ta.
Sallama ta rafka da ƙarfi cikin gidan.
Da sauri Ammi data gama girki tafito cikin shigarta ta kamala cikin daya daga kayan da Mamy ta mata ta amsa tana fadin sannu ku da zuwa ganin su da Sadeeq.
Yawwa Nene tace tana faÉ—in in shigo .
Mamy tace Bissimillah.
Sadeeq da Mamy sukai sallama suka shigo.
Fara'a fuskar Ammi ta ƙaru tace marhababukum lale da zuwan ku.
Sadeeq dama kana tafe da baƙi bazaka faɗaman ba.
Yace Mamy banson da zuwan suba sai yanzu.
Wannan itace Hajiya ya nuna Mamy.
Wannan kuma Nainah .
Nene tace kai tsaya my lot, Wallahi ƙarya kake kace Nene ce ni kawai duk da kana gyara man sunan,Bari kaji Naira 1000 naje makka in'faɗamaka tin Duniya na zaune kalau, har zakaceman Nene babu Hajiya ba komi dan ragemun matsayi , kabar haka dan Allah. .
Dariya yayi kadan yace to Hajiya Naina na dai na.
Tace" yawwa kwandon sukari ko kaifa.
Yace wai dan Allah miysa kike cemun haka? nifa ba yaro bane.
Afusace tace na cema kwandon sukari daka buga tusa sai sukari...
Da sauri ya faÉ—a dakin shi yana murmushi.
Dariya Ammi ta tuntsure da ita tace "dole yake yawan maganaki ashe chapter kuke.
Mamy tace" lallai kam, ni kaina banson haka suke ba sai yau, ta karsa tana kallon Bakin Ammi dake sanye da hakorin makka tabbacin har saudiyya ta taɓa zuwa kenan .
Fira sukayi cikin mutuntawa ta zubo musu abinci ita da Mamy. Na Nene kuma daban.
Duk da basajin yunwa Amma zama sukai sukaci sosai suka gode.
Bayan sungama cin abincinne Nene tace dama magana mukazo yimiki da kuma neman alfarwa dan Allah Hajiya badan muba.
Bakuma dan halin muba, sai dan rufuwar asirin mu, da kuma taimako da zakima baiwar Allah nan da batada wadatacciyar lafiya.
Cikin mamki Ammi tace alfarma kuma Nene? To nikam mizaku nema ku rasa daga garemu bayan kunmana komi,Ai dan dai sada zumunci da nace bama sai kunzoba ,ta waya kaÉ—ai zamu iya magana.
Nene ta share hawayen ta tace "mudai ya can-canci muzo.
Ammi tace Nene ke uwace in kina mun kuka wallahi hankalina na masifar tashi , Dan Allah kifaÉ—amun mikike so kai tsaye, ko aiki kuke so in maku ?indai wannan ne babu komi zanyi wallahi.
Mamy tace aa ba aiki bane.
Nene tace kai tsaye alfarma muke nema ta haÉ—a É—anki sadeeq da Aminatu É—iyar Fulani Aure...
Dam-Dam haka zuciyar Ammi tayi wani mugun bugu .
A furgice ta mike tsaye tana ja baya tare da kaÉ—a kai ....
5/18/22, 09:34 - MY MTN 2: 🌹 ƊAN DAKO
MALLAKI🌹
🌹UMMY AYSHA
🅿ï¸1ï¸âƒ£9ï¸âƒ£&2ï¸âƒ£0ï¸âƒ£
""Wasu kwallah masu tsananin zafi suka fara ambaliya a kan fuskar ta.
Cikin kuka tace'' Dan zatin Allah Hajiya Nene ku daina wannan magana inba so kuke kufamamun tsohon miin dake zuciyata ba,Tayama Sadeeq zai auri yarki, Bayan shida bashi da kowa,taya zayyi aure babu magabata,Hajiya ina son yarona yayi aure amma gudun tonuwar wani sirri mu na kyaleshi har zuwa yanzu da yake cikin shekara ta 32, Jiya jiyan nan nagama mishi magana aure , Sai bayan yatafi kuma naga hakan ma kuskurene,kwara muyita zaman mu haka cikin guntun farin cikin da yafara ratsa zukatanmu,shigowa da bare azaman takewar mu babban haɗarine, Shi ba kowa ba, ba komi ba Hajiya, Baidace kuyi tinanin hada yarki da Sadeeq aure ba. taƙarasa cikin wani irin kuka mai cin zuciya.
Nenema hawayen take.Da kyal ta share tace "shikenan É—anki ne bazamu miki dole ba.
Mamy kam kuka ta saki tare da durƙusawa akan gwiwoyinta tace" Dan zatin Allah Ammi ki taimaki rayuwata data yata dake cikin haɗari da ƙalubale, Wallahi bandamu da sanin kosuwaye kuba,nidai rokona gareku ku aminceman sadeeq ya auri Amnah saboda nagar tashi,Hajiya zuciyata namun radaɗin da take gaf da kaini ƙasa,a wannan karan muddum nayi kuskuran da maƙiya suka samu galaba akaina to tabbas zansha kunya da kalaman dana furta abaya, kuma Wallahi zaman Katsina sai ya gagareni,dan zatin Allah kitaimakamun,..
Ammi tace" taya zan'taimakamiki wai?
Yar taki muni ne da ita da kike neman mararaba da ita komi?
Wannan wane irin bahagon zancene kike Mun?
Taya mace zysta zo neman aure namiji haka al'ada ta tsara mana ne hayjiya?
Indai kina ganin aikin da yake gidan kine zaisaki tilastamu akan abinda bamu da buƙata to kiyi hakuri sadeeq ya daina zuwa...
Wani irin kuka mai cin zuciya maganganun Ammi suka sanya Mamy,Cikin lokaci kam magana tayi sanadin tashin ciwon ta, cikin lokaci tafara wani irin tari tana dafe saitin zuciyar ta.
Kuka Nene ta saki tana cire mayafinta ta ajiye gefe tare da tallabo Mamy data durkushe tana ta tari akan sawunta..
Ihu Nene ta saki ganin wani uban jini dake bin hancin Mamy da bakinta, lokaci guda idanuwan ta sunfara juyewa..
Ihu Ammi ta saki da yasa Sadeeq dake aiki da sistem nashi ajiyewa ya yanko da gudu ya faÉ—o É—akin.
Cikin rawar baki yace" minene? mi akaimata Nainah?
Ya ƙarasa a rikice hankali tashe.
Nene dake kuka ta ciccibo mai fuskar Mamy tace sadeeq kagani. Ciwon ta na zuciya yatashi, Wallahi Sadeeq itama zata mutu ta kyaleni, ina son Fulani sadeeq tinda yarin tatta tashiga matsaloli na rayuwa sosai ,wanda suka sakar mata da babban ciwo na zuciya,Sadeeq ka kamaman ita in kaita Asibiti, inda rabon ta tashi Allah ya rayamana, in kuma babu to Allah shi yason yanda zayyi dani. Nene ta faÉ—a cikin kuka sosai gwanin tausayi...
Ammi dake gefe kuka kawai take baki ɗayan hannayenta akanta ,jitake inama babu wata alaƙa tsakanin sadeeq da su Mamy, inama ba Katsina suka yada zango ba inama ace ƙauye'n ƙayau suka sauka,inda babu mutane .
Wato shi Æ™alubale rayuwa duk inda kake sai ya iskeka kenan ,Æata taÉ“a tinanin zata sake fuskantar wani tashin hankali ba ayanzu da suka keÉ“e kansu da kowa ba,bata da buÆ™atar kowa yason su suwaye ,to amma shi lamarin aure akwaishi da bankaÉ—o sirrin É“oye.
Da karfi sadeeq ya gilgiza Ammi yace "Ammi minene haka? Ammi dami zanji , Hajiya bata lafiya ke kuma bakya cikin hauyacinki , Nainah na kuka .
Dan Allah ku Tausayamun .
Nene tace "Sadeeq kasata mota muwuce Asibiti.
Tinanin ta yanda zai fara É—aukar matar mutane yake .
hakan yasa shi cikin in ina shi da tashin hankali ke tasomai yace Nai..nah baniii...da...hurumin ɗaukar ta ..ya ƙare magana a wahalce.
Nene ta tallabo Mamy da bata motsi tace shikenan- shikenan ni Amina nashiga ukku na lalace ..
Cikin ɓarin baki sadeeq yace Ammi kinafa gani dan mi bazakiyi wani abu akai ba? Lfy tane fa .
Da gudu ta tashi ta shiga dakinta sai gata da wata babba jikka anan ta zazzage duk kayan duba marasa lafiyane masu kyau sabbi daganin su zasuyi kudi sosai.
Da sauri ta iso ga Mamy tare da fara du bata cikin hanzari tanayi tana tausasamata wasu abubuwa masu kama da dutsin guga a kirji.
Cikin ƙanƙanan lokaci Mamy ta fara kawo ajiyar zuciya.
Ammi ta duba Bp É—inta anan taga yayi muguwar hawa.
Kai ta gilgiza tare da bata taimakon gaggawa.
Mamy na falfaÉ—owa ta tsare Ammi da ido ko kyaftawa batayi.
Yayin da Sadeeq ya fita tsakar gida dan basu waje .
ÆŠakin sa yashiga ya fara kai komo.
To miya janyo haka? ita kuma Ammi shi kukan minene take?
Amsa da baya da ita.
Saida Ammi taga komi ya tsaya kana ta É—akko takadda ta fara wani shegen rubutu irin na likitoci tace'' Sadeeq ga shi ka nemo maza.
Da sauri ya karyba ya fita dan yana da kuÉ—i A hannu.
Yana fita Mamy ta tashi tana cije baki.
Bakinta ta buÉ—e da niyyar magana sai kuma ta fara bleeding.
Ammi cikin tausayi tace" ki kwantar da hankalin ki kinji .
Na amince