Showing 12001 words to 15000 words out of 94971 words
Chapter 5 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt
tinjiya naga take taken nothing kanki akwance suke.
To Wallahi ni Sadeeq S Sadeeq zan iya saita ki yanzunnan kimatsa kibani waje kamin inmiki abunda baki taɓa tinani ba dakikiya kawai ko Anfaɗamiki kyauta za'asallameni ba sai nayi aikiba, bana tinanin cewa hakana za'kuna ɗaukar kuɗi kubani kyauta, Yajarasa yana sakin siririn tsaki tare da kifa hularshi ya fita cikin kasaita da cikar zati.
Duk abunda ya faru akan idon Mamy da Amal
Sosai abunda yayi ya burge mamy ganin irin furgici da tashin hankali da tsawar shi kadai ya jefa Amnah.
Murmushi tasaki batare da tace komi ba sai ciki data koma waya makale akunnanta cikin farin ciki taci gaba da magana da ƙawar ta Hajiya Turai.
Amal takarasa wajenta cikin rashin jin daÉ—in abunda aka mata ta kama hannunta tace.
Auntu Amnah kiyi hakuri muje kinji ko.
Fuzge hannuta tayi idanuwanta sun cika da kwallah amma taki basu damar zuba dan kar ya gani ya rainata.
Cikin rawar murya tace "agaban Mamy akaiman haka amma tashige ciki tana doka murmushi, D'an Dako yafi dan gida, nida gidan ubana, anya mamy na sona, kodai ba Mamy ta haifeni ba,?
Taƙarasa tana yarfe hannu tare da kutsa kanta cikin mota ta kifa kanta da styari tana sauke ajiyar zuciya, ga mamy ta mata shamaki da kai ƙarartaa wajen Abban ta,kuma tason babu wanda zai goyi bayan ta sai shi.
Amma tayi alkawari koyama wannan baƙauyen hankali.
Tada motar tayi tawani fizgeta da ƙarfi tare da fita daga gidan.
Tsaki yaja tare da taɓe baki ya kunna tashi yabi bayansu.
Duk yanda take tsula gudu bisa titin dan tabashi wahala ta hanyar bacce mai amma abun ya gagara.
Dan yanunamata namiji namiji ne mace kuma macace.
Tafiya mai É—an tazara suka karaso unguwar su Nene.
Unguwace dake da yawan mutane mabuƙata da almajirai, Dan ta tara makarantun allo da dama .
Parking tayi awani gida mai babban get black da yasha fentin lemon green
Hon tayi wani saurayi hannushi rike da Radio ya keto da gudu ya É—an buÉ—e yana faÉ—in.
"Yau sain tsulamaku bulalai yan iska masu kawunan Agwagwa shikenan baku barina in huta masu gida basuce in buɗeba saiku yan banza duk ruwan da aka fidda muku waje amma saikun karbi na cikin gida saboda hassada, Nace uwaku ya saki daƙuwa dai -dai lokacin da idon shi ya sauka kan na Amnah data tsareshi da lumsassun idonta fuska a tsuke..
Salati ya saki yana yankowa da gudu ya zube ƙasa tare da cewa "Dan Allah kiyi hakuri Hajiya Amuna wallahi banyi tinanin ke bace naga jiya kikazo.
Afusace tace zaka buÉ—emun get kosai nabi ta bisa bakaken yatsunka masu kama dana gizo- gizo na wuce?..
Hannunshi ya kalla kana ya tashi da gudu yashiga ya bud'É—e get É—in yana cillama bayan motar harara tare da "fadin wannan mai kama da manja Allah yamamu maganinki fitinaniya ga kyau kamar zoben zinari amma kafurar zuciya gareta kamar ta haÉ—a iri da sheÉ—an..
Yana kokarin rufewa sadeeq ya dallo tashi ciki.
Wait !wait !!! ya ciga da cewa amm ko tsayawa baiba saidai ya samu wuri kusa da motar Amnah yayi parkin tare da zamanshi yana latsa wayarshi hankali kwance batare da yace komi ba.
Su Amnah Fita sukayi suka faɗa cikin gidan inda Suka iske wata dattijuwa da a'ƙalla takai shekaru sittin da biyar tanata faɗa da mai lallaɓe mata kai.
"Haba zulfa sai shafar mun kai kike kamar kwartuwa nace ko dad'i kikeji?Dan masifa kingama kitsemun tin É—azu amma bazaki barni inje inyi walha ba dan dai kisa inmakara ko? Miyasa wai baki da imani da tausayin wanda ya kwana biyu.
Mai kitson tayi murmushi tace" Haba Hajiya Nene tattare miki nike dan karya dameki kin tsufa amma har yanzu kanki masifar yawa ga tsantsi dole sai an tufkeshi gudun karya warware.
Baki ta murguÉ—a tace tubarkallah kali kuss mai bakin banza sala kija ma'askin dare yamun aski tinda kincikani da baki, ni sakeni in sammaki nama dan in banbaki ba nason ba ci kike ba kuma karshenta bala'in bakinki kan kyakyawan gashina zai kare, Duk inkinmun kitso saikinyimun baki.
Dariya makitsiya ta tuntsure da ita harda kwallah tanason Nene sosai shiyasa take jure abunda take mata.
Amal dake tsaye fuskarta cike da murmuahi yayin da Amnah ta zauna ta É—ora É—aya kan É—aya tana kallon mai kitson cike da takaici irin yanda ta samu damar zama tana yanda take so .
Amal tace "Nene mu!.
Afurgice ta É—ago ta kalleta tare da mikewa tana kokarin gudu wa.
Dariya Amal tasa tace ga faÉ—a ga masifar tsoro to nice.
Dariya Nene ta saki tana mikewa ta ƙaraso wajensu ta cire kallabinta ta yarfama Amal din afuska tare da cewa "ja'ira na ɗauka aljannu zulfa ne suka tashi kinson suke gareta kusan buhu goma akai.
Dariya suka sanya Amal da zulfa inda zulfan ta tashi tana faɗin Nene bari in wuce sai da daddare nazo inci tuwo mai sulbinnan in kintuƙa selonita kike cemai komi?
Baki Nene ta saki tace kai kedai wannan kanki kamar na Zabo wlh bakya rabawa" semovita" akecewa wannan tsamin bakin naki yana kasheki da yawa.
Dan ma Allah ya rufamiki asiri bakinki baya wari da babu ni.babu ke kinson ni nafison É—an gayun mutum koya yake kuwa.
Dariya tayi tace shikenn bari inwuce sai nazo.
Tsaidata tayi tashiga ta shakomata kula da naman da fura mai sanyi tabata tare fa sabullan wanka dana wanki dan Nene akwai kyauta.
Godiya zulfa tayi taryr da fita dan atsorace take da irin kallon da Amnah kemata.
Tana fita Nene ta juyo wajen Amnah tare da sanya kafarta ta noshi ta amnah datake kaɗawa cike da ƙasaita.
Da sauri ta É—ago idonta tazubama Nene su.
Cikin bacin rai tace ta sannu hakima!wadda gaba ɗaya zuri'arku babu wanda akaba koda sarauta kwasar kashi ce, Amma in akaga kina abu sai ayi tinani dai- dai da ƙudan gidanku sarkine minafuka.
Kinsha wasu jajayen kayan banza kamar yar shan jini Amnah ki kiyayi duniya wallahi, zulfa ba tsara uwarki bace da ba zaki gaisheta ba ,sai ma hararata da kike kika furgitata kika hanata zama.
Fuska ta yatsina tare da faÉ—in nifa kin cikamun kunne da hayani dan Allah kibarni Nene
Ko infita inbar gidan ki. Haba safiyar fari a cikama kunne da faÉ—a,kina da masifar hayaniya.
Ido Nene ta murza saiga hawaye tace shikenan Amina kici gaba da zagina kina wulaƙantani jiyama kamin kibar gidan nan saida kika kwashemun albarka tass daga kiranki yimakai abun arzi to kisani daga yau babu ni babu ke, Allah kuma ya isa zagina da kikai.
Amalulu muje kici dambun shinkafa yasha kayan dad'i wlh .
Amal tayi murmushi tace to kishare hawayenki kana muna tare da ÆŠan Dako ne zai sauke kaya.
Mamy tace danki samu sauki zai rabamiki iyaka kifita kibashi umarnin inda zai kaisu.
Baki Nene ta washe Tare da faÉ—in kai Allah yama fulanina Albarka ya É—aya tilo mai share ma iyayen ta kuka Allah yajikan Bashari da É—an uwanta,da yana nan da yaga yanda duniya takeyi damu wayyo Allah na mijina ta kece da wani irin kuka zuwa cen kuma ta saki dariya tare da gyara zani tace muje muje Amalulun Nene.
Fita sukai suka doso harabar tsakar gida inda suka iske sadeeq zaune akan motar.
Yana ganin sun fito da yar farar dattijuwar ya tashi tsaye tare da zame hular kanshi .
Daga nesa Nene ke kallonshi tare da É—an lallekawa dan san sanin ina yan uwanshi suke.
Suna gab da zuwa taja wani wawan burki tare da cewa ubnmi akaimka zakazo kaiman tsaye kamar bishiya Dabino, wato shine daga campany suka turoka kenan to maza kabar gidan nan wallahi tin kamin in dakko barkono da mai in laftamaka ga fuska,Dan iskanci banace bana so ba.
Ahankali ya ɗago ƙanshi dan yaga dawa take.
Karaf idon shi ya faÉ—a cikin nata hakan yasa Nene daka tsalle takoma bayan Amal tare da Daga hannu tace Sukusmie(excuse me) tana dagamai hannu alamun yabata waje.
Kallonta yayi sosai tare da sakin murmushi dan yana tinanin shigr da yayi yasa take ganin shi kamar Dan sanda.
Ƙarasawa yayi wajenta tare da duƙawa yace" ina kwana.
Gabaki É—aya idanuwanta ta fiddo tana kallon yanda yayi hausa raÉ—am a'bakinshi.
Amal tace nene gaisheki fa yake shine kuma yakawo kayan daga gidan mu .
Mamy ta sameshi zai dingamata aikace- aikace fa.
Wani irin ƙanƙance ido Nene tayi can ciki tare da fitowa daga bayan Amal tace kina nufin wannan ne Dan Dako? Mike damun Saudat da zata ɗauki wannan saurayin aiki?Lalli kune ya rufema ido amma ninan Nene babu shegen dazaiman rufa ido dagani turoshi akai gidan ku dan ya sace ku, Mussaman waccen mai girman kan bala'i dam ansan in an ɗauketa za akwashi kudi.
Duk maganar da take yana jinta babu abunda yake sai murmushi tare da jingina da motar ya harde kafarshi hannunshi kuma daya sai gilgiza key din yake..
Nene ta matso wajenshi tace kai tsakanin ka da Allah wazaka sace? wa akace kasace kaji tsoron Allah ka fadamun gaskiya? wa akabaka kongila daga acikin zuria ta?
'"Kece''
Yabata amsa agajarce fuskarshi Daure tamau kamar bashi ke sakin Murmushi ba..
5/18/22, 09:33 - MY MTN 2: 🌹 Ɗan Dako
Mallaki🌹
Ummy Aysha🌹
🅿ï¸1ï¸âƒ£1ï¸âƒ£&1ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
"" Duk da zuciyar Nene ta buga amma cikin jarumta ta daka tsalle ta iso gaban shi, tare da "faɗin kai uban Turajima yayi kaɗan balle kai, barganinka da kirar samudawa Bashari ya tsumani kamin ya Mace, Dan haka daga yau bana son ƙara ganin ka cikin zuri'a ta, saboda ban'yarda dakai ba.
Yo inbama haukaba irin na Saude taya zata iya zama gida É—aya dakai jibifa nan inka.
Takaima faffaÉ—an kirjin shi naushi.
Idon shi ya lumshe tare da sakin fuskar shi da yalwataccem murmushi yarasa dalilin da yasa tsohuwa ke masifar burgeshi, yana tsananin sonta lokaci guda acikin ranshi.
Ido a lumshe ya fara magana cikin sanyin murya
"Nainahh yaja sunan da wani sauti mai masifar daÉ—i wanda yasa Amal rintse idonta da karfi tare da buÉ—esu lokaci guda ta saukesu akan pink lips dinshi dake motsi A'hankali.
"Nainah bantaɓa cutar waba,duk da ni ancuceni amma kuma hakurina yafi gaban zuciyana,banshigo zuri'a kiba dan cuta saboda bana fatan cutar da Dabba mai tafiya a hanya balle Ɗan Adam da Allah ya karrama, Abu ɗaya nasani tabbas ni ƊAN DAKO ne ,a kasuwa suka ganni nakaimusu kaya mahaifiyar su ta amince dani....
Atakaice yabata labari duk abunda ya faru cikin natsuwa.
Nainah ni maraya ne Baban ya rasu kana ina da ƙanwa da mahaifiya, wayanda sune gatana na duniya kuma nima duk kan wahala da zanyi dan farin ciki'n sune.
Banji haushin kiba dan kin haÉ—ani da mai sace mutane gaskiyan ki saboda rayuwan babu amana aciki.
Amma kisani bawai dan kibarni inyi aiki gidan y'arki ba aa ! Gaskiya ta zanfaÉ—amiki banacin amana amma kuma ina hukunta wanda yaci tawa.
Ya rage naki ki amincemun ko karki amincemun duk É—aya ne awajena, Saboda ita kofofin rahma ta Allah yawa garesu ,
Kisani ranar da nakai kaya gidansu Amall aranar wanda nikema aiki ya koreni , Muna tsaka da magana yanda zan samu wani aikin da zan kula da mu da mahaifiyata naji kiran y'arki.
Zaki iya kiranta yanzu kimata magana kin hanani dan bazan iya tinkarar taɓa gaskiya.
Yakarasa yana É—ago fararan idanuwan shi ya saukesu akan Nene da tinda ya ambaci Maraya ne shi ta É—ora kanta akan motar ta fara kuka marar sauti.
Gaban shi ya faɗi sosai har baison sadda ya ƙarasa wajenta ya ɗagota tare da zube gwiwoyin shi ƙasa yace nine ko?
Kimin hakuri bazan sake ba kiyi hkuri na tafi. ya faÉ—a yan juyawa .
Da wani irin gudu da kuka shaɓe -shaɓe Nene ta kamo hannun shi tare da rikewa gam tace" wallahi kai ba maraya bane, kana dani kana da mahaifiyar ka, Yaro ina sonka zanzamemak a gata kamar yanda allah ya zamemamu a'sadda muma mukayi rashin jigon mu, Dan haka i lovulu wallahi.
Baison sadda dariya ta kwacemai ba sosai yake dariya harda wasu kwallah da suka masifar mai kyau.
Nena ma dariya tayi tana jin tsananin tausayinshi har cikin zuciyar ta.
Tace muje palo na kaci abinci, ya sunan ka?
"Sadeeq" yabata amsa atakaice.
Hannu ta tafa tace sunan ƴaƴan Saudat Wallahi shine ya ɓata tin yana karami ta faɗa tana share hawaye.
Cikin jimami ya mata jaje tare da faÉ—in ina za asauke kayan.
Mai gadinta takira tare da cewa" ÆŠan larai kama mashi mana ya saukesu.
Da" to" ya amsa ya samu ya kinkimo buhu guda ya ajiye yana mayar da numfashi.
Sadeeq ya tattare hannayen rigarshi ya fara saɓosu akafaɗa yana direwa gaban Nene, sadda ya kusa gamawa kana Ɗan Larai ya ajiye buhu ukku.
Tsaki Nene tayi tare da cewa" Huhulahun banza huhulahun wofi, Duk uban abincin da kake ci amma ji abinda kayi .
Cikin nishi yace "Hajiya Nene kowa fa da aikinsa yafi kwarewa, Dan haka aikina buÉ—e get bawai DAKO ba, shikuma aikin sane karshenta kiga inzai bude get har kuka sai ya fashe dashi.
Murmushi kawai sadeeq yayi yana gamawa ya hango pampo ya karasa ya wanke fuskar shi tare da zama kasan wata bishiya Mango dake gidan yayi shuru.
Nene tace to ai yayi mai wuyar dan haka É—akko Baro kazo ka kaima kowa tinda kason inda ake kaiwa shiÉ—in ya kula da get din.
To yace yana sakin mika.
Nene ta koma ga sadeeq ta tsuramai ido cikin tausayi tace" Sadidi in'kawomaka abinci anan .
Kallonta yayi tare da kaÉ—a kai alamar aa.
Amal tace Nene bayacin abincin ko inafa wallahi saina Ammin sa,Ban sani ba ko yana zargin zamu masa wani abune.
Cikin tausasa murya yace babu wanda ya isa yayi sai da yarda Allah, ni bana zargin ku sam kawai ra'ayinane haka,nason duk inda Ammi na take yanzu tanacen tana bukatar taga tamun abinda zanyi farin ciki, to nafito kuma nacika ciki waje kinga bazataji daÉ—i ba taga na koma nace banaci ko?
Yakare magana awahalce dan matsanancin ciwon da yakeji a ƙasan zuciyar shi.
Nene tace" kai Saddi wallahi na fita iya girki, Sala katafi kana tsinemin albarka da zagina akan namaka tayin rowa ko?
Amalulu É—eboman abinci kihaÉ—o da ruwa da kaina zanbashi.
Da sauri ya É—ago kai ya kalleta tare da kawar dakai gefe yana motsa baki.
Cikin hanzari Amal takoma ta jero komi ta kawoma Nene .
Nene tayi zaman dirshan gabashi tare da cewa kadaiga ni "Tsohuwace inka wahala dani allayh zai Sakaman Saddi kaci ko in baka.?
Ganin mutuncin Tsohuwa da kulawa da take nunamai yasashi ƙarba cokalin yayi Bissimillah yafara ci cikin natsuwa.
Ido ya lumshe danjin yanda Danbun da yasha zogala da kayan lambu ya ratsa bakin shi.
Bai an'kareba saida yaci rabin flat kana yaji ya koshi.
Nene ya kallah tare da É—an fiddo ido yace shikenan" Nainah yau babu ni babu cin abincin Ammi nah, kincikamun ciki da girkinki mai daÉ—i ya yfada yana lumshe ido.
Dariya jin DaÉ—i Nene tayi tace" kai nifa gwanace a girki dan shekarun baya har Matar Masari saida taso É—aukata aiki saboda yanda nike baÉ—e kofofin hancinta da kamshi da kuma labarin iya girkina da Bashari ke bata .
Cikin rashin fahimta inda ta dosa ya kaÉ—a kai baice komi ba.
Nene tace to taso muje ciki.
Yace aa zanje in É—akko sauran indawo.
Tace yawwa Saddi maza.
Tashi yayi cikin jin kwarin jiki yafaÉ—a mota ya fita.
Me gadin Nene yadawo da almajirai sunkai talatin.
Azabure Nene ta mike tana faɗin ƙudira sama Liman da wawan zama, Ɗan Larai uban minene haka? mizasuman .?
Yana nishi yakaima kirjin wani dake kusa dashi naushi yace kingansu nan kullim da kinkawoman abinci zakigansu kamar jamfa a jos sun taso suna buÉ—e hancina kamar kofar guga, Suna ya bayin Allah, Minafukan Allah dan suja in'masu rowa Allah yakamani tinda sungani.
To abun yazamemasu jiki kullim saina basu loma É—aya shiyasa da naga zanyi wannan aikin wahala naje na gayyatosu dan karsuci banza , dan haka kowane shege shi zai É—auki na gidajen da ake kaiwa.
Nene tace kamun dai _dai dan Larai wani lokacin fa akwaika da hankali , Dan haka basu suci gaba da kaiwa kana tsaremin get.
Ahaka duk suka karar dana wajen yayin da Nene ta koma ciki.
Anan suka iske Amnah zaune cikin wasu riga da wando gabaki É—aya'n su pink sunmata kyau sosai tayi parking É—in dogo'n gashinta tsakiya ,ta kunna kayan kallon tasa kida mai taushi yana tashi ahankli sai kaÉ—a kafa take tana latsa waya.
Koda suka shigo basu kalletaba itama bata kalle suba.
Saida sukai alwallah sukai sallah Nene" tace amalulu waccen kota hada iri da kafuraine da bata sallah.
Amal tace aa Nene yau batayi fa.
Fusk Nene ta yamutsa tare da cewa kazamar banza kawai dole taita shiga jajayen kaya ashe cikin jini take.
Dariya Amal tayi ta linke abun Sallah tare da mikewa tace" Nene wallahi yunwa.
Tace kije kici abinci ni banaso tuwo zanyi.
Zuwa tai ta zuba abinci ta dawo palo tace" Aunty Amnah in zubo miki!.
Akasalance ta kalleta tana lumshe ido kamar yar maye dan Abinda take gani awayata yana masifa tayar mata da hankali.
Kai ta kaÉ—a mata tare da faÉ—in naci nawa kuna waje.
Nene ta kalleta tace ke" Amina ubanwa ya baki izinin zuba Abincina, ke waima tsaya ke zuwafa yanzu yakamata a'miki aure naga sai wani iskanci kike kina ganin mutane É—ai-É—ai.
Cikin natsuwa ta muskuta ta gyara zamanta tare da fuskantar Nene.
Cikin taushi murya tace "Nima inason kumun auran amma kaf faɗin katsina banga wanda yadace da rayuwata ba, Saboda ni inason saurayi mai kuɗi mai masifar kudi fa Nene bawai kaɗan ba, kana ɗan gidan Sarauta maiji da jinin mulki,in ma so samune ya ƙasance sarkine,kana fari kyakyawa mi yalwataccem saje, kana karfaffa bawai soko ba, ina so in son samune ya kasance Soja ko Likita, cikin biyun nan dai, Dan bana da ra'ayin auran ɗan kasuwa saboda masifar matsolanci dabin ƙa'ida.
Cikin ta fasa zuciya da takaici Nene tace dan ubaki in sai dashi ake kije kisiyo mana kana da ba'ason asalin anguluba sai muce daga ƙasar masar take, ke nan har zaki zaɓi mijin da ke zaki lissafashi,to in saukin samu garai kije kisiyo,Shiyasa ko ɓera baita ɓa sallama dake ba.
Murmushi ta saki tace wallahi Nene in bansamu wanda na lissafamiki ba banayin Aure, Muddum mijina bai fito daga gidan sarauta ba bana sanshi, ko satin nan kamal ɗan gidan Gwamna Sani Baba yazo nemana, Amma karkiso kiga yanda namasa, saboda fatana in'samu masu takemun baya da kamar masu kudinsa kona tsohon sa, Dan bazan ɗauki talakaba dan som baison daraja mutane ba, kidubamun wancen wawan ƊAN DAKO, Yau ɗaya ya ɓatamun rai