Showing 78001 words to 81000 words out of 94971 words
Chapter 27 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt
ne ?in ka fitar dani daga yaranka Baba sai inkoma inda na fito...
Kuka ya saki yace ina sonki Wallahi ÆŠiyata, ina sonki ,ni dama tin ranar da naga kinzo sayen gero Wallahi naji ajikina kedin nan jini nace.
A'hankali ya tashi ya isa wajen Mamy ya duka kasa yace" Saude dan Allah, Dan zatin Allah kimin hakuri ,ki'yafeni, wallahi nason na cutar dake ,ban baki kulawa da ta dace ba matsayin ki na ƙaramar yarin ya mai ƙananun shekaru...
Nene" tace kai nima zonan ka bani hakuri, ni dama kafi cuta ka taushemun baki,bana um bana uhm uhm...
Hakuri ya shiga bata harda hawaye, Amnah kau farin ciki taji sosai ko bakomi duk lalacewar iyayen ka nakane ,kuma baka da kamar su A duniyar ka...
Ya koma ga Sadeeq yace" Habu Allah ya maka Albarka, Allah kuma ya hada kanku, ashe Habu dama dai kai mai kudine shiyasa akaƙi yarda da kai ko?
Sadeeq yace" ai'kai ka yarda dani Baba, Nagode Allah ya ƙara tsawon rai, bazan taɓa manta Alkhairi ka gareni ba, Saboda ba Dan korar da kamun ba bazan ga Ahlina ba,Da matsayina na da baidawo ga reni ba,Ga kyakyawar mata daka haifamun tsakanina da kai sai godiya...
Yace "Ameen yana mai jin kunyar abinda ya masa.
Nene tace'' ka sake mai godiya da rokon ya rike jinin ka hannu biyu, Dan gabaki daya jarabaka yarin ya nan ta kwaso, ina tsoron jikan ya koma tsololo Wallahi ta shanyeman shi kadai ganshi kakkaura kirar ƙarfi...
Mai Malmala yace "Kuyi hakuri Hajiya Nene , Nima Wallahi lalurine da kuma halitta.
Nene tace oho dai ,Allah ya kwaci ÆŠiyata, da yanzu fallan zani sai yafita kyan gani..
Gaba É—aya kunya ta kamasu ,amma ita ko ajikinta ...
Ahankali Mai Malmala ya mike yace" Bari in É—akko mata magani, insha Allahu zata dawo dai- dai da halittar mijinta ,babu cuta ba cutar wa a tsakanin su..
Wani irin faÉ—uwa Sadeeq yaji gaban shi yayi, shida ke fatan kasan cewa da ita akaro na biyu kuma amai wannan sagegeduwa, ya fara raba idanuwa yana gudu amasa illah da bayajin zai jure...
Kai a ƙasa yayi gyaran murya tare da cewa" Nace Baba da ka barshi, duk jinsun mu ɗaya ne Wallahi...
Azabure Nene ta cire glass dinta, yayin da ta kalleshi sama da ƙasa tace" Na shiga ukku, na bani na lalace, yanzu ta gidan uban wa ka gane bayan Karan ku ɗaya,Taya zaka tantance yanzu ,Daga haɗa alaƙa so ɗaya zakacemun haka Dan kajaman sharri.
Ta saki kuka tare da cewa Wallahi Dan sujaman sharri , Kuma ni harna ƙare rayuwata ma tsoron Bashari nike ,inajin kamar in hau tsani in kwana saman katanga saboda kunya, Amma ku kau yan iska jarababbu har faɗamana kuke .
Kai dawo ka zauna mu muntashi ma taƙarasa a fusace.
Mai Malmala ya zauna yana murmushi yace ma Amnah.
Aminatu ina so kimana sati biyu ko ukku dan ki saba da dangin ki ko?
Ya ilahil alamina Amnah tace, tana mai jin tsananin faɗuwar gaba. taya zata iya rayuwar gidan da ko kyaure babu, sai tsohon zani da a kasa aka rufe ƙofar....
Sadeeq yace "am Baba Dan Allah kayi hakuri, zan maidota da kaina insha Allah,Saboda yanzu batajin daɗi, kuma akwai buƙatar kulawa ta mussaman daga gareni...
Kai Baba'n ta ya jin-jina yace" shikenan tare da zaro tsohuwar naira Hamsin ya miƙamata, yace'' ungo kisha ruwa da alawa.
Dariya mai haɗe da hawaye tayi kana ta karɓa ta mai godiya.
Yayin da ya É—auki naira goma yaba Amal yace" ungo ke ma.
Nene tace kadaiji kunya matsolon banza matsolon wofi, uban yarin ya nan baitaɓa ban-banta taka da tashi ba ,Hasalim yafi yima taka gata sama da tashi, Amma ji abinda kaba yarshi ,kai kumaida mai Dan ubanku ko in zubamaku mari ta faɗa a fusace.
Baban Amnah yace" tsaya fa Tsohuwa Sirikata, babu ta yanda zanyi in'saki kudi ina almubazaranci da su, Bayan naga yara tula- tula alamun babu abinda suka rasa, tomi zasu siyama in na basu da yawa?
Nene ta mike tana gyara glass dinta tace" ku tashi muje kar takaici ya ƙarasani.
Shima Baban Amnah ya mike yace "Dan Allah ku biyoni ciki in'gwadamusu ga ÆŠiyata ta dawo gareni ...
Ba suce komi ba ya fara tafiya sukabi bayan shi har tsakar gidan da yake kaca -kaca da kwanikka, ga awakai da kaji ,ga yara gasunan dai kwatsa-kwatsa kamar Æeraye, Ƙananu kuma sai rarafe suke ,wasu atsaye fuska ta kwaÉ“e babu kyan gani.
Wani irin masifaffan amai ya kawoma Amnah ziyara lokacin da taga yanda komi yake a wulakance.
Da sauri Sadeeq ya jawo ta jikincshi yana É—an shafa bayanta yace" ki!daina Sweety kinji, karsuga kamar akwai cin fuska.
Shuru tayi suna shiga yar rumfar dake gefe.
Mai Malmala yace "kai ga diyata tazo da ƙafarta nemana Saboda tason daraja uba,Kukau Munafukan sai kallonta kuke kunga baturiya ,To albishirin ku Soja take aure, Duk ɗan iskan daya tanka yanzu zaiga kwalwarshi a watse tsakar gida nan ..
Da gudu uwar gidan shi ta shiga É—aki ta dakko tabarma ta shimfiÉ—a musu.
Nene ta taɓe baki tace" bazamu zauna ba, gaskiya wucewa zamuyi, ga yar uwarku nan ankawo maku ,in kuna son ganin ta kuyi wanka mai kyau kuje ku ganta..
Aiko ƴaran da sunkai talatin da wani abu suka zo suka fara maƙalƙale Amnah suna tsalle, wasu nason taɓota sai jujjuyawa take, Dan gabaki ɗaya sunɓata mata kaya da datti.
Wani ÆŠan saurayine da yakai shekara shabiyar ya daka tsalle ya hayota da karfi yana faÉ—in" Bani biyar Yaya.
Kuka ta saki tana faÉ—awa jikin Sadeeq tace muje Dan Allah Baby bazan iya ba.
Kudi masu yawa Abba ya basu suka ficce suna toshe hanci.
Mai malmala yayi sufa ya kwashe kuÉ—in ya fito yana washe baki .
Yace" su sauka lafiya ya Dawowar sa ciki.
Bayan sun tafi Abba dake gaba ya É—auki hanyar Goruba roud.
Sadeeq kam cikin mamaki suke binshi badan sunson inda zaya ba.
Saida yazo wani Katafaran gida mai masifar kyau tindaga ƙan get ɗin zakason cewa lallai an kashe maƙudan kuɗaɗe wajen aiki sa.
Wani kyakyawan remote ya fiddo ya latsa take get É—in yayi sama suka fara shiga ciki.
Bayan duk sun shiga ya maida ya rufe, Fuskar Abba cike da murmushi ya karaso wajen Sadeeq ya mikamai hannu , Tare da bashi wani key yace my Son ga gida'n ku.....
Cikin mamaki suke kallon shi , yayin da Nene kuma tace kushigo in nuna muku.
Shiga sukai wani tafkeken palon daya linka na gidan Mamy so Biyu girma da kyau, ga wasu mahaukatan kujeru milk da Brown dake sanye cikin leda, Da labulaye komi dai na palon yaji dan yayi masifar kyau .
Cikin Mamaki Ammi tace" Alhaji isa kunsani a duhu fa?.
Yace" Doctor tin ranar da na dauki kudin ki na fara juyawa na fadama Nene ya zanyi da rivar da ake samu, gashi bangankuba.
Tace da aita ta rata kwara ace ansai abu mai amfani ana ajiye wa, Duk ranar da Allah ya bayyanaku sai indamƙamuku a bunku, yanzu Doctor ribar kudinki ne ya gina miki wannan gidan , Harma da katafaran masallacin da kika gani waje wanda shidama tuni nayi karambani buɗeshi ina fata ya zama sadaƙatul jariya wa mahaifin Sadeeq da Hamrat...
Gwal inki kuma suna nan an'miki sabbi na zamani, an baki ribar wancen da kika samu , Dan haka yanzu muje sama komi naku na nan a ajiye, kuma part biyu ne kinga saiki baro cen ku dawo nan dazama ya isheku ko?..
Nene tace tabbas kuwa ya wadatar,kuma zatana kula da lamarin yaran nan dake son cinye juna..
Cikin tsananin murna da farin ciki irin rikon Amana da ya masu Ammi tayi sujjada godiya ga Allah, ta fara masa godiya da kirarin baiwar da ya musu,Bayan ta gama ta hau godiya ga Abbah ...
Yace mata babu komi dukiyar su gabaki É—aya ya haÉ—ata zuwan da sukayi ya tattaro komi, kuma shima ya dawo kusa da iyalin shi dan sunfiye mai zama cen nesa.
Farin ciki sosai Sadeeq yaji lokacin da aka mikomasu kuÉ—in.
Amnah kau sosai jikinta yayi sanyi , Allah ya rufamata asiri da yanzu tason sadeeq korata zayyi Da bata gyara halinta ba..
Murna sukayi sosai suka tashi tafiya.
Sadeeq yace'' Sweety zauna in rakasu in dawo.
Ammi tace ai ba yau zamu dawo ba, sai anma gidan Saukar Alkur'ani kana ,ko nan da sati biyu haka.....
Ido shi ya zaro yace" Ammi Dan zatin Allah kubarni da matata,hab har yaufa bansamu damar keɓewa da ita ba fa tin jiya da safe, bafa ta da lafiya na faɗamuku taya zakuna rabamu bayan banji daga gareta yanayin jikin nata ba.
Nene tace'' kai Wallahi gidansu zata, sai ta warke zata dawo,muma aimun fahimci bata da lafiya rasa kunya ɓeran tanka,basai ka fadamuna ka santa ta sanka ba ...
Yace shikenan Nainah gatanan ku wuce. ya fada yana fita cikin fushi ya faÉ—a mota suka hau suka tafi...
Nene tace kadawo ɗan banza, Tinda yanzu kaga kafara canza sutura zuwa ta kakin soja ai'kwara kafara mana baƙin hali ,Amnah bazata koma ba sai taji sauki sumul ....
5/30/22, 10:57 - Ummi Tandama😇: *Littafin🌹DAN DAKO🌹 na kudi ne biya ki karanta cikin Aminci. Biya 300kacal to 0006454115 Amina Dahiru jaiz bank,or MTN card to this number 09165832002. then send the evidence of payment via 07038423451* ğŸ¤ğŸ™ğŸ¤²
Alhamdulillah! Alhamdulillah!!
Yan uwana mata ina kuke ku malmatso ga wanni sirri da nike son baku, ita ya mace sai da kamshi, ina macen da take ganin izgili da wulakanci da ake cewa maza nada shi, hmmm yar uwa to inkin kasance a haka da alama akwai ayar tambaya akanki. Tambaya ta ta farko gareki da wane irin turare kike amfani a jikin ki ?,da wane irin turare kike turara gidan ki,shin dawane irin turare kike Zukunni, hmmm to matso kusa kiji yar uwata.
Shi kamshi Annabi muma ya faÉ—a abin sone,kuma Abune mai sanya natsuwa da girmama ma'aboci shi , Da Yawon son kusantar sa.
Duk kan wulakanci da izgilanci na maza akwai turaran da zai miki maganin sa da izinin Allah,ba boka ba malam,wanda zai karkato da hankalin mijinki akan ki ku samu fahimtar juna.
Ko kin son kamshi na dakusar da fitinar É—a namiji yar uwa? kigarzayo ki kwashi rabonki ga shaharariyar yar mai Dugurin nan mai suna UMSAD INCENSE ,Mace mai kishin mata da son Fiddo martaba mu.
Nayi Amfani da turaranta naji masifar daÉ—in da yasa nakasa barwa raina. Nace bari in yaÉ—amuku dan kowa ya mallaki nashi cikin farashi mai sauki.
Da fari bari in zayyano muku su kamar haka.👇
Maleek Al'oud
Royal kush
Cous-cous
Kajiji
Original sandal
Sandal flex
Sandal bange
VIP mix
Hawi
Al'oud
Kindikay
Danal banat
Darot
Habil
Gaf-Gaf
Sirrun nisaa'i
Sandal chips
Kwalacca
Humra black and body milk
Attractive humra.
Yar uwa zanmiki Dallah- Dallah.
Akwai turaran da zaki sanyama kayanki .
Misali! kisa kabasa kiturare kayanki .
Akwai humra da bazaki sataba sai zaki turaka.
Akwai turaran kaya ,na jiki, Dakuma na ɗaki. Akwai kwallaca sirri, amma bama badata gaskiya sai ga wanda baida kishiya , Dan muddum kina amfani da ita tofa gabaki dayan hankalin mijinki akanki zai dawo,Dan yana juyo da hankalin namiji akanki baki ɗaya ,zaki zama shalele Baby, Akwai sirrin nisaa'i. hmmm Dagajin sunan kason na dabanne,na baki sati ɗaya ki gwada ki gani Hajiya ta, tsugunno ake akai ga mai buƙata ya tunɓe mu ta wannan layin 08028827241 karku manta UMSAD INCENSE mune na ɗaya.
Muna aika kayan mu duk inda kuke.
Kamshin jiki martaba mutum....
5ï¸âƒ£5ï¸âƒ£&5ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
Mamy tace'' Nene wannan bai kamata ba, yazo ya É—auketa sutafi kawai.
Ammi tace "barshi kuje gida kawai .
Haka sukatafi Amnah kuma batace komi ba, Dan jikinta yayi sanyi matuƙa....
Sadeeq kam bayan fitar shi kai tsaye wajen saida motoci suka nufa, ya siyo wasu dallah- dallah guda biyu nashi wayanda zai dinga fita dasu , Sai guda É—aya wadda tafi tashi sada mai masifar kyau.
Daga nan ya badasu aka kaisu gidan da zasu koma suka wuce.
Kai tsaye Army Break suka nufa.
Bayan sunje aka gwalgwadamishi mutanan da zasuna kulawa da lafiyan sa, da wayanda zai ajiye gidan shi , Da haÉ—É—an office din shi mai masifar kyau...
Farin ciki sosai yaji ya mamaye ranshi.
Anan wani matashin Saurayi da shekarun su bazai wuce daya ba ,mai kyau sosai ya iso wajen shi ya saramai yace" Yallabai ina matuƙar sonka ,ambani tarihin jarumtar ka inaso inyi koyi da kai,in'babu damuwa ina so muzama Abokin ni sunana Abbas.
Lokaci guda Sadeeq ya samu aminci dashi ya mikamai hannu suka gaisa a mutunce, kana yaÉ—au hanya da niyyar sai monday zaifara fita aiki ,Dan muna Thursday.
Bayan suntafi kai tsaye gidan Ammi ya isa yana kumbura baki.
Ammi tace'' zonan Dee.
Bayan ya isa tace'' Dee nah kasan mene yasa nace ta koma gidan su?
Kai ya gilgizamata yana sadda kanshi ƙasa.
Tace Saboda yakamata ace mun haÉ—a gagarumar walima ,Mu mata lefe muma da kayan kece raini saboda ta haihu Yar halak,tinda Allah ya kawo muna wadata kwara itama ta sheda.
Inaso ka shiryamun tafiya Dubai yau ko gebe .
Ga Hamrat nan ka É—auketa ka kaita gidan Nene ,Kacemata tazo mata sati daya kaji ko,Karka faÉ—a mata zanyi tafiya ba...
Kai ya gilgiza cikin gamsuwa da bayanan ta yace''shikenan.
Fita ya sakeyi yama rasa wazai kira, dan shi duk ya manta wasu abubuwan.
Abbas ya faÉ—omai arai, bayan sunyi waya yace'' Aboki kana ina ? Ammi nah zatayi tafiya inaso inganka.
Cikin tsananin jin dadi Abbas yace "ganinan zuwa yallabai , Bani mint kadan kuma ka turoman address din gida'n.
Dee yace shikenan sai kazo yana mai kashe wayar ya turamai, yayi n da yayi zaman shi bisa mota yana mai latso number Amnah.
Bayan ta É—auka tace" Baby ya kake.
Yace babu lafiya sweety..
Azabure ta mike tana fadin minene! mike damunka? kana ina haka?
.
Yace masifar zazzabi nike da ciwon zuciya, Amnah ina buƙatar ganin ki yau ko gobe, in kau har kika hanani zaki tsinci gawana..
Kuka tasa tace'' haba Dan allah kadaina fadamun haka, yanzu kana ina ,kazo gidan Mamy yanzu inganka wallahi bata barina fitowa.
Da sauri ya diro daga motar yace shikenan anjima zanzo ya kashe wayar yana Sakin huci mai zafi ..
Yana tsaye saiga Abbas da motar shi , Bayan yazo suka gaisa kamar sun daÉ—e da sanin juna, anan ya nunamai yanda zayyi komi ta online hankali kwance cikin É—akin ka.
Cikin lokaci akama Ammi komi zata hau jirgi daga kano zuwa Abuja, daga Abuja zai cala dasu.
Godiya ya mashi sosai kana ya wuce.
Sadeeq ya koma ciki ya mata bayani, Taji daÉ—i sosai hakan yasa ta haÉ—ama Hamrat kayan ta tace" ya wuce da ita tinda yamma.
Hamrat kau taita murna zata wajen Nene.
Bayan ya isa gidan ya shiga har palon ta kai tsaye.
Inda ya iske Nene zaune tasha wanka tana taunar naman kaza, daga gefe kuma ga sassanya fura mai sanyi sosai tana korawa.
Zama yayi fuska a É—aure .
Da sauri Nene ta mike tana fadin oyoyo ga Hamami kike ko ÆŠoyi?
Hamrat ta fashe da dariya yayin da tace" ke Aunty Nainah Hamrat fa.
Nene ta rike baki tace" minikeji haka yarinya, ni kike cema Aunty, Dan ki wulakantani, to kar inkumaji, Nene sunana, ko kice Hajiya Nene, Dan isa ya kaini makka so biyu.
Hamrat tayi Murmushi tace "Nene to zankwana anan inji Ammi.
Nene tace "Alhamdulillah kaga yanzu nason nayi jikanya, su kau wayan cen in'sunzo kwana biyu suke su koma, aiko bazaki sake komawaba tinda ina da hakki mai girma kanki ko Hamta. .
Cikin dariya Hamrat tace" eh tana kallon sadeeq daya É—aure fuska.
Nene kam ta shiga labari da Hamrat tayi shuru ta kyale Sadeeq.
Yace'' nainah bakison ina fushi dake ba?
Tace ikon Allah Bashir mi naimaka?.
Cikin mamaki yake kallonta yace'' Bashir kuma?
Tace ta yo eh mana, naji kana bani wani umarni irin kamar kai ka haifeni, ko kuma ƙasan igiyoyin auran ka nike ,to wallahi ba ayika ba sanholo kawai ,ka ɗauka tsoronka zanji.
Sakkowa yayi ƙasa cikin lallashi Yace" to Nainah naji kiyi hakuri bazan sake ba , Amma dan Allah ki taimakamun kicema Mamy Amnah tazo nan ,ina kunyar ta wallahi, Dan Allah ta dawo nan gidan da jinya, wallahi Nainah bazan ɓoyemiki ba ina kewar matata ,ina tsoron faɗawa halaka ta rashin ganinta kusa dani ,Nainah Dan Allah.
ya karasa kamar yayi kuka.
Dariya sosai Nene tasa tace'' shegiya mace mai maida soja É—an daudu.
To kayi hakuri mana har saita warke.
Yace shikenan Nainah ga Hamrat nan, ni na wuce.
Tace ok sauka lafiya.
Cikin takaici ya Duƙa ya kwashe kajin da furar tanacen tanama Hamrat magana ,akan ta kai kayanta ɗakin su Amal ya ficce.
Bayan ya shiga mota ya tada ya fita.
Kai tsaye wani Katafaran shago yaje yasiyo wayoyi masu kyau guda biyu, ya fito yaje gidan Ammi.
Bayan yaje suka É—an tattauna kana ya shige dakin shi ya jona charge.
Ana gama mangariba yaji wanka mai kyau ya dakko waya É—aya ya saki murmushi ya fita.
Anan ya iske wani gandareren kato shida Abbas tsaye.
Cikin mamaki suka gaisa yace "bakamun waya ba Aboki zaka zo.
Abbas yace "Yallabai Wallahi jirgin da Ammi zatabine tashin asuba zayyi, to shine kawai nazo da aminataccen driver da aka baka kan ya kaita , Dan kaima oga Ali na nemanka da safe balle mumata rakiya.
Yace "shikenn ya shiga ya faÉ—ama Ammi.
Cikin jin dadi ta tashi ta ɗauki yan abubuwan buƙata suka fito yanatamata Addu'a. itama tana mishi.
Motar David ta shiga suka dauki hanyar kano.
Yayin da ya rufe gidan suka shiga Motar Abbas suka É—auki hanya gidan su Amnah yana nuna mishi har suka isa.
Bayan sun isa ya gaisa da Baba madu a mutunce suka kutsa kai.
Abbas yace" Yallabai ni juyawa zanyi.
Sadeeq ya kalle shi yace" Abbas lokaci guda naji na amince da tayin Abotar da kamun , Dan haka babu zancen Yallabai, muddum ba wajen aiki mukeba, ka kirani da Aboki ko sadeeq kawai zanfi jin daÉ—i.
Yace insha Allah Aboki.
Yace yawa nan gidan su matata ne kuma cousin muke da ita, zanshiga in'zakaje muje.
Yace ''A'a Aboki watarana zanje, zan tafi gida wajen Umma nah tana jirana .
Sallama sukayi ya fita da motar shi...
Da sallama ya shiga gidan inda ya iske su zaune su duka , Amnah ce kawai babu.
Amal tace Yah Dee ina wuni ya gajiya?
Yace lafiya klau Sister ya kike?.
Tace Alhamdulillah.
Bayan sungaisa dasu Mamy yayi shuru yana motsa baki.
Many ta taɓo Abba ta gwadamai shi da ido.
ya saki murmushi yana mata alamun sutaimakamai su bashi abinshi.
Kan tayi magana sukaji
Sadeeq yace Mamy ya Amnah da jiki ,ga waya na siyo mata tata ta faÉ—a ruwa yafaÉ—a yana raba ido dan baya son karya, Shiyasa in yayi zakaga yanata wiki- wiki da ido .
Da sauri Abba Yace" tashi ka shiga ka bata