Showing 66001 words to 69000 words out of 94971 words

Chapter 23 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt

Advertisement

09 Feb 2025

17265

kayi, kana kuka Alokacin bakafi sheara biyu ba aduniya.
Amma Allah ya baka bakin iya faÉ—in Sadeeq, Saudat ,sune kawai abinda ka iya ,in ance yasunan ka kace Sadeeq Saudat...


Azabure Nene ta tashi jikinta na rawa tace'' kikace a kano aka tsince shi? Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un ,wallahi billahi É—ana ne , Dan girman Allah ku kaini inganshi na shig ukku, dama Sadeeq ina yana Abuja, yanzu wanna dama jikanane , Ni nason ba banzaba nikejin Sadeeq a raina wallahi,ashe jika nane, ga yar uwar sanan itace Saudat É—in, Dan Allah kutashi mutafi.....




Kuka Ammi da sadeeq suka sanya a tare sukace
Musbahu ya kashe shi..


Ihu nenyw ta kwallah sai gata ƙasa a sume


Azabure Sadeeq ya É—akko ruwa ya yayyafamata ta tashi tana sauke Ajiyar zuciya tace .
Maryam sun kashemun yaro, minene ya musa?


Ammi tace'' Nene bayan sungama rabon gado muna gefe muda Sadeeq muna kuka.


Sai lauyan ya buÉ—e wani shafi yace to" Alhamdulillah Alhaji ya bar wasiyya, kuma dasa hannu yace" Duka dukiyar shi dake hannu sadeeq ya bar masa ita halak malak yaci gaba da juyata.


Kamin mu an'kara Umma ta faɗo daga kan kujera. faɗowar da tayi silar shanyewar ɓarin jikinta..


Bayan anje Asibiti aka tabbatar musu da abinda ya faru yasa ta kamu da ciwon shanyewar ɓargo.


Anan Musbahu yama Sadeeq kallon tsana yace" wallahi tallahi saika sani, kuma saika maidomana dukiya mu.
Afusace ya ja Bily dake hannu shi tana kuka tana kallon sadeeq tana faÉ—in banzuwa wajen mijina zan zauna dan tana son Dee dan ma iyayen su basa barin su shigowa part É—in mu.


Sadeeq baice komi ba sai gida da muka dawo ya fara haÉ—amana kayan mu, anan muka kwashe komi.
Washe gari da safe muka doshi wani tamfatsetsen gida Dani kaina banson yana gina shi ba,Zagaye yake da ma'aikata maza masu yawa.


Bayan munje muka iske komi Ashirye, anan yake shedaman nashine daya gina, dan haka muyi zaman mu a ciki babu wansa ya son dashi...


A'hankali Muke sabuwar rayuwar Mu cikin farin ciki da jin daÉ—i da walwala, har muka samu shekara biyar Biyar a ciki, Alokacin Sadeeq nada shekara Ashirin, inda ya matsama uban akan ya kaishi aikin soja ,Dan shi soja zaizama fatan shi kenan..


Kasancewar shi mai son cika muradin yaran shi yasa yamai hanya har aka samu..


Dee Na Tafiya da wata biyu wata rana Abban su yazo gida a gigice ,ya fara haɗa wasu takaddun tare da kuɗaɗe masu yawa ya ɗaga kason gado na ,anan naga wata ƙoface karama da ba kowa yason da ita ba, anan ya fara tura duk kan Ƙadda rasa..


Kamar zan mai magana na kyale, saida aka samu kusan wata daya kana Yake faÉ—aman shima yana ganin rayuwar shi tazo karshe, Dan bilhakki Musbahu ranshi yake nema , Bayan fadamai maganganu da yayi, da kuma turowa da yake ana bibiyar sa basu mai ba .
ya fahimci yana so yaga ya tagayyara ..


Jikina yayi sanyi Anan nabashi kwarin gwiwa akan babu wanda ya isa ya masa wani abu....


Bayan shekara 3.


Sadeeq ne ya mana Dirar Bazata, inda yake sanye cikin kayansu na Sodoji yayi kyau sosai ,ya ƙara zama namiji Saboda illahirin jikinshi abuɗe yake, Dama gashi da, tsawo da kuma kwari kamar kirar Baban sa.


Anan mukaita murna inda Sady taita haba-haba dashi.


Cikin zaulaya take fadamai tayi saurayi wanda mu kanmu bamu sani ba.


Cikin muskilancin shi ya jinjin mata kai tare da faÉ—in" zaigan shi..


Dariya tayi tace mai kamar wani babba.


Kanta ya dungure yana tashi ya shiga É—akin shi, Anan Abban shi ya bishi suka fara tattauna magana, wadda ni kaina banson mi suka faÉ—a ba.


Washe gari muna zaune mukaji sallama ta
Ƙaseem da Bily da Alhaji Musbahu.


Kujera ya samu ya zauna yana zaro jajayen idanuwan shi rai a ɓace yace "ka gama guje- gujen? gani gaka yau a tsakiyar Katafaran Palon ka, Dan haka bani kuɗunmu kawai ...


Abba Sadeeq yace'' gaskiya tinda bani na roka ba aka bani bazan maidosu ba Yaya ,kayi hakuri kata shi ka tafi...


Afusace ya mike yana faɗin na baka kwana ukku, in ka bada katafiyar da rayuwar ka dai -dai, in'kuma ka ƙiya to anan zakayi bankwana da duniya baki ɗaya..


Azabure Dee ya mike cikin tsananin fushi yana fiddo bindiga yace" ka sake gayama mahaifina magana sai na fasa koƙon kanka, ware nace kaida kutaren yaranka ya fada cikin ihu da motsuwar Allura su ta sodoji...


Mahaifinshi bai tsaya komi ba ya fara yanka mai mari akan ya faÉ—ama dan uwan shi magana.


Alhaji Musbahu kau Kwafa yayi ya tafi yana mai jan hannu Bily dake kuka tana fadin ita bazataba tana son Uncle Dee shine mijinta ..


Saida Musbahu ya kwadamata mari kana ta bishi suka tafi.


Anan nake cema Abban su ya bashi kuÉ—aÉ—an muzauna da rawayuwa mu lafiya.
Murmushi yayi Yace bazai bada ba, in kyale su kawai...


Haka muke ta zama AÉ—arare har kwana ukku , akayi sat,i har sati na biyu ya shiga, Aranar da DEE ke shirin komawa bakin aikin su dan hutun su ya kare har ya fita ya dawo yace" ya fasa tafiya sai washe gari da safe, Dan Saurayin Sady yace zaizo su gaisa .


Dariya mukai tamai muna jinjina son girma da gabata irin nasa.


Kimanin biyu da rabi na dare muna kwance É—aki muka fara jin kamar motsi.


Da sauri na mike daga É—akin Abbah da nike na leka window, anan naga wasu mutane sunkai su hamsin palon mu sanye da bakaken kaya.
Agigice na buÉ—e kofar dazan iya ganin harabar gidan.
Anan naga ma'aikatan mu duk kwankwance ƙasa kamar sun mutu....


Kyarma jikina ya ɗauka da kyal na tada Abban Sadeeq nace" ya tashi ga ɓarayi nan..


Murmushi kawai yayi yana kallona, idon shi na zubar da hawaye yace" muyi maza mukira su Sady suzo, akwai kofar sirri tanan ciki muɓuya ko mu gudu.


Azabure na kalle shi nace" kaifa?...


Yace" in baiga na barmishi duniyar ba duk inda zani zai bini maryam..


Kuka nasa na faÉ—a kanshi, ina faÉ—in karyamun haka mana, ya son muna da bukatar shi A rayuwa bamu da kowa sai shi..


Murmushi yayi ya buɗe ƙofar, dai-dai lokacin da wani murtukeken kato ya banko kofar ya shigo, tare da ɗora mai bindiga akai yace" muje palo..


Cikin rawar jiki muka fita palo, anan naga sun fito da Sady sun kwantar da ita.


Cikin kuka na ƙarasa inda take na ɗagota naga jikinta sai rawa yake tana kuka....


Dee ne ya fito da wani kato yasamai bindiga akai, ya taso keyar sa gaba.


Suna isowa ogan su ya dakamai tsawa da umarnin ya sauke bindigar shi ko ya halbi iyayen shi, ganin da gaske zai iya abinda yace yasa ya sauke jiki shi na ɓari zuciyar sa ta motsa,Cikin bakin ciki yake bin iyayen nashi da kallo da aka zagaye su gashi babu damar yayi wani abu.


Kason kujer ogan ya Wullah bindigar Dee tare da nuna Abban Sadeeq da ita yace bamu kaddarori ko ranka.


Abba zai magana Nace" wallahi nason inda suke, aje ÆŠaki na aÉ—aukko suna kason gado..


Tana gama faÉ—an haka suka tada mutum biyu, anan sukaje sai gasu da kaya niki -niki suna nishi...


Kuka Abban su yasa yace" inaji ina gani rayuwar ku zata tagayyara .


Kamin ya rufe baki wani ya É—auke shi da mari.


Sanadin hakan ne yasa zuciyar sadeeq motsawa yayi tsalle ya fara Dukansu da hannu yana fatan yayi magana amma ya kasa,Saboda Dee Nah tsananin ɓacin Rai kan sashi in ina ya kasa magana in yana cikin fushi.


Bindiga suka dora akan Sady, Nace ma Dee yayi hakuri ya daina karsu kasheman miji.
kana y zauna yana numfashi sama- sama...


Waya É—aya Ya É—auka yana faÉ—in "komi ya kammala..


Munajin murya Musbahu na dariya sosai yace" to ku karshi, kamin ya Wullah kuma kumai abinda zuciyar sa zata buga, yaji bakin cikin danaji da yayi ta wahalar mun da Rayuwa ....


Cikin dariya iskanci suka amsa suna kashe wayar.


Wata ƙatuwar igiya ya tillama wani dake kusa da Dee,cikin shammata suka kamashi kuson su ashirin suka fara daureshi kamar goro.


Sai da sukamai É—aurin da ko motsi bayayi sosai.


Abban shi damu muna ta kuka.


Dariya suka sanya tare da daure hannu na dana Abban su wajen guda.


Kana sukazo suka ja sady da karfi suka fara since mata kaya.


Kuka su Ammi keyi sosai tana ganin kamar lokacin abun ke faruwa.
Gabaki É—ayan su suma kukan suka sa, sai Abba Amnah ne kawai ke hawaye.....


Dakyal taci gaba tace" A gaban idona da mahaifinta da É—an uwanta suka mata tsirara kana É—aya ya maidota gaban mu Agabana yama É—iyata fyade, Agabana Mutum ashirin yama Sady fyade, hakan bai masuba suna ganin tana numfashi sama -sama amma suka É—auki bindiga suka Halbeta a'ciki ,kamin mu an'kara sun halbi Abban su akai take ya faÉ—i shikenan...


Daga nan ne banson minene ya sake faruwa ba, nadai ganni wani dan karamin É—aki nida Sadeeq yana gefe yana kuka....


Cikin kuka da tashin hankali nike kallon Sadeeq ina tambayar shi ina suke ,in mafalki Nike ya ta dani, ina ahlina, Dan Allah karya tabbatar mun da mafalkina....


Kuka yasa yana mai sake bani hakuri tare da faÉ—in"Ammi sun kashemana farin cikin mu, bamu da kowa bamu da komi, Mamy yau kwanan mu bakwai kauyen nan, bayan sun kashe Abba sukaman wata Allura ni dake kana suka barmu.


Sai washe gari da yamma Na falka, bayan gawar Abba data Sady har sunfara canzawa,....


Da yan kuÉ—aÉ—ena na samu wata mota ta kawomu kauyen nan aka musu sallah aka binne su,Saboda koda na tashi banga wani ma'aikaci ko É—aya ba gidan mu wanda zai kama man,Gashi ke kuma har lokacin baki dawo hayyacinki ba.


Cikin kuka yace"Ammi mun rasasu, suna cen gidan su na gaskiya.


Cikin kuka sosai Nace "to miyasanya ka kawomu nan.?


Tace fansar ran Abba da Sady zan Ɗauka, kema bana fatan a sake kashemin ke shiyass na ɓoye ki nan inda babu wanda zai sani.


Kuka nayi sosai daga nan na fara kwarara amai baji ba gani.
Wata matace sanye da kayan buzaye ta shigo cikin É—akin, ganina zaune yasa ta rug da gudu sai gashi ta shigo da wani Dattijo....
Bayan ya mun ya jiki kana ya jiƙa magani a kwarya ya bani, sukamuna sannu suka tafi.


A takaice wata biyu na samu wannan kauyen dagani sai Sadeeq muke rayuwa bama cin wani abun kirki saboda damuwa .
Akuma lokacin ne muka fahimci ciki ne jikina, wanda nake Tinanin ya kai wata biyar.


Bani da abin so da ƙauna sama da cikin nan .
Lokacin daya cika wata tara Sadeeq ya zauna gabana yana kuka tare da faÉ—in dole muje gidan mu, akwai sakon da Abban sa ya bashi.


Nace mai bazanje ba babu ni babu gidan..
Anan yake nausar dani fa'idar zuwan saboda akwai kudade da kaddarorinsa dan dama duk kan takaddun da wayan nan mutanen suka É—auka na bogine, kudin ma dake hannu su na bogine.


Banyi wata murna ba saboda wanda ya tara su nafi bukatar kasancewa dashi akan kudin, sai dai kuma lallurina yafi gaban ace haka .


Dattijon da muke gidan sa mai suna Baba Lawandi "Yace yaro kaje da kanka, ina ga zaifi, saboda it halin da take ciki kar wani abu ya tada hankalinta ,kason mace da rauni..


Cikin yarda da sgyawarar shi Sadeeq yasa kai ya tafi..


Anan ne na farajin wani irin faÉ—uwar gaba da nadama akan barin shi da nayi ya tafi.


Atakaice kusan awa ukku muna jira shuru, Hankalina ya tashi da na Baba.


Muna tsaitsaye sai gashi mun hango yana isowa da manyan jikkunoni guda biyu hannu sa.


Da sauri na nufi inda yake, Dai-dai lokacin da mukaji halbin bindiga tah! tah !!tah !!!har ukku, inda cikin tsautsayi ɗaya ya samu Sadeeq a ƙason kirjin sa, take kuwa awajen ya faɗi ba rai.


Ihu muka sanya nayi kanshi ina gilgizashi cikin tashin hankali, lokaci guda kuma ciki na yayi wata murɗawa wadda ta sanya ni matse cikina da karfi jin dan cikin nawa na ƙoƙarin fitowa duniya ,bayan baya da ko pant din da zanmasa Amfani da shi...


Baba Lawandi ya tashi abunka ga mazauna kauye sunson sirrin hatsabibanci ya fiddo wata powder ko toka zance bazan iya ganewa ba , Ya fara faffesamuna yana fesama gefe da gegen mu.


Ashe gani yayi sundo so inda muke dan kare rayukan mu yasa yayi wannan siddabarun, sai gashi wajen ya koma Jeji mai tsananin duhu da ban tsoro , Da kuka'n manya -manya namin Daji, hakan yasan ya wayanda suka biyo Sadeeq rugawa da gudu..


Yayin da ya kira matar shi ta jani É—aki ,shikuma ya isa ga Sadeeq banson mi suka mai ba..


Cikin ikon Allah lokaci kankane na haifo yar kyakyawar É—iyata mai tsananin kama da sadeeq.


Ina samu ta faÉ—o Duniya banbi ta kantaba ko kallon ta banba, Saboda bata ita nike ba, aguje na fito É—akin anan naga Baba da sadeeq da baya hayyacin shi bakin wata bishiya duk ya ÆŠaÉ—É—aura ma kirjinshi Bedi, Da wasu ganyayyakin da banson kona minene ba.


Da gudu naje gunshi nace" miyasamu Yaro na, ko sun kashe shi?


Yace mun "A'a yana da rai.
Haka muka fara jinya shi ina kuma jegon ÆŠiyata da ko Pant sai da Baba ya birni ya siyomata.
Ranar data cika bakwai nace ayan kamata Rago ayi sadaka muka ba da kudin wa Baba Lawandi.
Ya bukaci sunan ta nace ya samata Sady.
Kuka sadeeq yasa yana gigiza kai.
Nace to Asamata sunan ya É—aga kai dan baya magana.


Watan mu ɗaya kana Sadeeq ya ɗan maro, Cikin ikon Allah jikin shi yayi sauki sosai babu laifi,Amma in zai tafiya sai kaga yana dudduƙewa.


Aranar daya cika wata biyu da tashi Baba yace" akwai matsala muyi maza mubar shiyyasu, inba haka ba tom abu marar dadi zai biyo baya...


Aiko cikin hanzari na goya ÆŠiyata suka nuna muna Æarauniyar hanya muka taho da manya jikkunan mu muna musu Godiya da Alkawari dawowa duk ranar da komi ya lafa....


Fuskar mu a kulle muke tafiya , Yayin da sukuma mutane suke binmu da kallo.


Muna shigowa cikin gari Sadeeq ke cemun Umma nan fa gold ne, akwai hadari shiga motar haya dashi.


Jin haka yasa nace mai muje shagon Alhaji Isa mai gold dan munyi school É—aya da shi kuma ina yawan sayan gold wajen shi.


Muna zuwa bakin shagon Anan na cema Sadeeq ya samo muna abinda zamu ci,yana tafiya na shiga ciki na bashi Ajiya ,sama -sama nafara mai magana tare da faÉ—in zanzo in karba ,
Ita kuma gudar jikka muka buÉ—esu kaÉ—aÉ—ene da yawa sai uwaye takaddu.


To kudin ne Na dibo da yawa sosai, kana na bashi ajiya sauran yana ta so inmai karin bayani amma ina agulguje na fito ganin Sadeeq ya doso wajen mukayi Tasha.


Anan mukaji ana Am'batar motar Katsina, bamu tsaya komi ba muka Haye sai Katsina, muda bamu taba zuwan ta ba.


Bayan munzo munsha wahala babu wanda muke neman alfarma daga gareshi ya taimakamuna ,kowa kallon mugaye ake muna, ganin yanda muke a jigace..


Dakyal muka samu wani mutum ya taimaka muna Muka sayi gidan da muke ciki.


Amma abun damuwa som yan unguwar basa yarda damu, Hakan yasa bama shiga harkar kowa, mukaÉ—ai ke rayuwar mu.


Yan sauran canjin mu mukasayi abin buƙata, Irin su Kayan Abinci dana sawa, Dan namu duk suna gida.


Haka mukaita rayuwa a ƙuntace , Sadeeq yana warkewa sosai ya fara shiga kasuwa yana neman Aiki ,amma babu mai bashi har Allah ya hadashi da Wannan Dattijo daya Bashi Aikin DAKO , Bayan ya rabu da shine kuma Allah ya haɗaku.


Ahaka muke rayuwa inda shakuwa mai karfi ke tsakanin shi da Hamrat, duk abinda ya samu ita yake fatan kashemawa.


Shekara mu biyu kunci da tsada rayuwa tasa in Sadeeq yayi Aiki sai inga kudin basa isarmu, dan aikin ba kullum ake samu ba ,Kunson DAKO'N Hatsi.


Hakan yasa na yanke shawarar turashi wajen Alhaji Isa ya karbo kudaden mu ya kawo muna.


Bayan yaje ya dawo a sanyayye tare da Nunamin shagon ma an mayar dashi garejin manyan motoci, an tabbatar mai da tashin sa sama da shekara É—aya ba ason inda ya koma ba....
5/23/22, 11:03 - MY MTN 2: *Littafin🌹DAN DAKO🌹 na kudi ne biya ki karanta cikin Aminci. Biya 300kacal to 0006454115 Amina Dahiru jaiz bank,or MTN card to this number 09165832002. then send the evidence of payment via 07038423451* ğŸ¤ğŸ™ğŸ¤²




Alhamdulillah! Alhamdulillah!!
Yan uwana mata ina kuke ku malmatso ga wanni sirri da nike son baku, ita ya mace sai da kamshi, ina macen da take ganin izgili da wulakanci da ake cewa maza nada shi, hmmm yar uwa to inkin kasance a haka da alama akwai ayar tambaya akanki. Tambaya ta ta farko gareki da wane irin turare kike amfani a jikin ki ?,da wane irin turare kike turara gidan ki,shin dawane irin turare kike Zukunni, hmmm to matso kusa kiji yar uwata.
Shi kamshi Annabi muma ya faÉ—a abin sone,kuma Abune mai sanya natsuwa da girmama ma'aboci shi , Da Yawon son kusantar sa.
Duk kan wulakanci da izgilanci na maza akwai turaran da zai miki maganin sa da izinin Allah,ba boka ba malam,wanda zai karkato da hankalin mijinki akan ki ku samu fahimtar juna.
Ko kin son kamshi na dakusar da fitinar É—a namiji yar uwa? kigarzayo ki kwashi rabonki ga shaharariyar yar mai Dugurin nan mai suna UMSAD INCENSE ,Mace mai kishin mata da son Fiddo martaba mu.
Nayi Amfani da turaranta naji masifar daÉ—in da yasa nakasa barwa raina. Nace bari in yaÉ—amuku dan kowa ya mallaki nashi cikin farashi mai sauki.
Da fari bari in zayyano muku su kamar haka.👇


Maleek Al'oud
Royal kush
Cous-cous
Kajiji
Original sandal
Sandal flex
Sandal bange
VIP mix
Hawi
Al'oud
Kindikay
Danal banat
Darot
Habil
Gaf-Gaf
Sirrun nisaa'i
Sandal chips
Kwalacca
Humra black and body milk
Attractive humra.


Yar uwa zanmiki Dallah- Dallah.
Akwai turaran da zaki sanyama kayanki .
Misali! kisa kabasa kiturare kayanki .
Akwai humra da bazaki sataba sai zaki turaka.
Akwai turaran kaya ,na jiki, Dakuma na ɗaki. Akwai kwallaca sirri, amma bama badata gaskiya sai ga wanda baida kishiya , Dan muddum kina amfani da ita tofa gabaki dayan hankalin mijinki akanki zai dawo,Dan yana juyo da hankalin namiji akanki baki ɗaya ,zaki zama shalele Baby, Akwai sirrin nisaa'i. hmmm Dagajin sunan kason na dabanne,na baki sati ɗaya ki gwada ki gani Hajiya ta, tsugunno ake akai ga mai buƙata ya tunɓe mu ta wannan layin 08028827241 karku manta UMSAD INCENSE mune na ɗaya.
Muna aika kayan mu duk inda kuke.
Kamshin jiki martaba mutum....
🅿ï¸4ï¸âƒ£7ï¸âƒ£&4ï¸âƒ£8ï¸âƒ£


""""Kuka Nene take sosai kamar zata shiÉ—e, Dan mutuwar É—anta ta daketa sosai ,ta motsa mata tsumin kaunar gudan jinin nata.


Da rarrafe Mamy dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login