Showing 36001 words to 39000 words out of 94971 words
Chapter 13 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt
shadda da Abbah ya bashi suka ficce
sai gidan Ammi shida Abbah bayan ya sallami Abokansa.
Cikin farin cikk sosai fuskar ta cike da annuri, tasa wata atamfa mai kyau tana ta zuba murmushi.
Sallama sukai suka zauna.
.
Ammi tace "Sannu Alh Isa da kokari, an'samu muhallin zaman kuwa?
Kai ya jinjina mata fuskar shi babu yabo ba fallasa, yace an'samu Doctor! Amma miyasa kika kafe akan Bazai karɓi gidan dana mallaka musu ba?.
Tace'' saboda nayi magana sirri da mahaifiyar ta , Dan haka abar ta hakanan kawai.
Kai ya jinjina yace ''to wanda dai muka samu mai kyau Mai haske yanzu, ÆŠaki daya ne tal , sai tsakar gida da baifi zaman mutum biyu ba, sai kiching da toilet ajere, kinji fa tsarin gida .
Tace ya ishesu Allah ya am'fana.
Yace Ameen tare da tashi ya tafi jiki a'sanyayye.
Bayan ya tafi suka fara tattauna magana da banajin mi suke faÉ—a. na daiga sadeeq É—in ya natsu sai gilgiza kai yake.
Tace ka tashi kasamu mai napep kaje ku dauketa, Nason zuwa yanzu sunkammala aikin da zasuyi ,am ban tambayeka ba ya sunan unguwar da zaku zauna?.
Kai ya shafa danshi kunyama yakeji ace dagashi sai mace cikin gida kamar wani kwarto.
Yace cen sabon layi ne.
''Ta gilgiza kai cikin gamsuwa tare da cewa. "Sadeeq kaji tsoron Allah kayi aiki da hankalin ka karka cuci yar mutane, Daka cuta kwara a ciceka, Sadeeq dan girman Allah karkayi amfani da karfinka da ikon hakkin dake kanka nata ka juya musu ɗiya kadai son irin halaccin da suka mana ko? ko ka bata wahala, A'a ina umartaka da duk abinda zakayi kayi wanda bai saɓama sharia ba kaji,Kana ayanzu dole kana mata uzuri koda zaginka zatai,na baka umarnin kabata wata biyar in ta sauya Alhamdulillah, daganan sai ka fara aikin ka,in kuma bata canzaba to sadeeq ina mai baka umarni ka rabu da ita saboda ba macen aure bace kasamu wadda ta kwanta ma...
Yace'' insha Allah tare da tashi ya canza kaya zuwa na wayan da ta fara ganin shi da su ranar farko na Buzaye ya fita, tare da tare Napep yayi gidan Mamy.
Yana zuwa ya zaro wayar shi ya kira Mamy .
Bayan ta É—auka tace .
Ya samesu palon Abbah.
Sallama yayi ya shiga tare da samun wuri ƙasa ya zauna.
Anan Hajiya Turai ta fito da Amnah dake sanye da wata Atamfa mai masifar kyau Ash, an'samata Alkyabba silver sai kamshin take aka zaunar da ita kusa da Sadeeq.
Abba da idanuwa'nsa sukayi jawur ya É—ago ya zubama Amnah da kanta ke kasa ta nata kuka ido.
Anan ya fara musu nasiha mai ratsa zuciya.
Daganan ya janyo 5k din sadakinta ya dam ƙamata.
Yace" gashi Amnah sadakinki ne, ki rike abinki zasumiki amfani.
Magana ta karshe Amnah ana nemana wajen aiki dole gobe zan koma ,kuma wannan karan da mahaifiyar ki zantafi da yar uwarki saboda ta kammala karatun ta acen.
Ina fatan in harhaÉ—a dukiyar kasuwancina indawo kasata nima.
Dan haka yanzu duniya baki da wani makusanci sai Sadeeq.
Ina miki fatan Alkhairi da fatan nasara a'cikin sabuwar rayuwar da zaki tsinci kankk,ina fatan Allah ya baki ikon cin jarabawa da ya É—ora miki.
Sakacinki yasa Mamy ki dauke gwala-gwalan ki dan karkiyi wasa dasu zata ajiye miki,kana takaddun makarantaki suma za a ajiye, magana aiki kuma yace bai amince ba ,dan haka kiyi hakuri ki fuskanci buƙatar mijin ki.
Sako na nan na ajiye miki acikin Dakin ki cikin lakar gadon ki dake ƙasa, Allah ya baku zaman lafiya da zuria dayyiba.
Ya zaro ƙarama waya ya bata yace "gashi zamuna waya insha Allah gobe zamubi jirgin safe..
In akwai abunda kike buƙata ga Momy Turai nan ki faɗamata, ko Nene, duk zasu miki maganin matsalaki insha Allah, sadeeq ku tashi ku tafi.
Kuka Amnah take kamar ta HaÉ—iye zuciya ,Tanaji da taga wannan bak'ar rayuwar kwara mutuwar ta.
Kam ta kama Abbah ta rike tana kuka tana bazani ba bazanje ba, Wallahi nadaina abunda bakwa so,Bazan sake ba dan Allah karku badani wa ÆŠAN DAKO.
Da sauri Abbah ya kwace daga rikon da tamai ya faÉ—a É—akin shi .
Duk dauriya ta namiji wani irin kuka ya saki yana faɗin why! why!! Doctor, Miyasa Fulani, Nene miyasa kuka zaɓi wannan rayuwar wa ƙarama yarin ya.
Mamy ma kuka take Amal kam gefe ta koma tana kallon sadeeq tana kuka tana kuma tausayin Amnah da rayuwar da taji ana tsara zatai.
Lokaci guda tsannin tausayin su ya mamaye zuciyar sa .
Tashi yayi tsaye baison sadda ya jawo Amnah jikinshi ba yace" kiyi hakuri Aminatu muje.
Turjewa take tana kuka akan bazata ba ,amma cak ya É—agata yana rike da akwatin ta suka fita.
su Mamy suka bita suna ÆŠagamata hannu suna share hawaye.
Ganin sunshiga napep yasa Mamy dawowa palo tasaki wani mahaukacin kuka tana faÉ—in Amnah dole tasa, inaso kizama mai zuciyar tausayi,inaso kifahimci rayuwa ,inaso kisan daraja Dan Adam tin kamin kiji ko wacece ke,ya Allah ka cikamun burina, kasa wannn auran yazama Alkhairi ga ahlina da kuma dawwama farin ciki na.
Ameen Amal tace suna komawa ciki.
Anan sukaga Nene tana kwance ykasa sai burgima take tana kuka, idonta yayi mahaukacin kumburi kamar fitila besfa.
Shikam Sadeeq tinda suka tafi take ihu tana kururuwa tare da kiran sunan Abba, Dan ta riga ta yardama kanta ba Mamy ce Maman ta ba.
Ganin duk inda suka wuce tana tara mai mutane hakan yasa da karfi ya riko hannayenta. Tare da tausa halshensa cikin bakinta ya danne mata halshe.
Hakan yasa ta waro idanuwa akan nashi tana gilgizamai kai alamar ya barta.
Banza yayi da ita dan in ya kyaleta kowa sai ya kalleshi.
Ajiyar zuciya taita sauke har suka kawo Sabon layi Mai Napep ya tsaya basu saniba sai da ya juyo yace" am
Malam ina..
Kan ya karasa yayi Saurin juyawa yana" haba Yallabai, ya kake haka? mu gwauraye ai sai muyi sama da yan matan titi..
Akasalance ya juyo ga baki ɗayan idanuwancshi sunyi jawur, da hannu ya nunamai wani ƙaramin gida da yasha sabon penti milk.
Saukesu yayi ya sallame shi i yace ta fito.
Cikin masifa tace bazan fito ba, wallahi babu inda zani sai ka maidani gidan ubana, ɓarawon banza barawon wofi.
Kanshi ya gilgiza tare da jawo hannuta ya saɓa a kafaɗa kamar buhun gero, hannu guda kuma ya ja akwatin har ƙofar gidan .
Ajiye akwatin yayi tare da sanya key ya buÉ—e gidan .
Bayan ya shiga ya rufe tare da jera Addu'a kana ya direta yace" kishiga da ƙafar dama.
Da karfi ta taka bakin kofar da ƙafar Hagu tana murzawa tace nashigo da hagu nashiga, kayi duk abinda zakayi ,Albarka nike nema a auran naka akacema?kuma bazan kwana agidan nan ba shegen gida kamar kabarin sheɗani ,ni zaka kawo gidan da ko Tsuntsuwa bazan iya ajiye wa ba, wallahi sai ka sakeni taci kwalar shi da ƙarfi.
Akwatin ya ajiye gefe tare da kama duka hannayenta yace "Amnah ni É—ane, kana na halak, mai kuma burin faranta ran iyayen shi ta hanyar yi musu biyayya, zansake maimaitamiki wallahi bana sonki som, bakya cikin ra'ayim matan da nike so,Amma na karbi kyautar ki bisa ga umarnin da iyayena suka bani.
Cikin kuka tace ba dole ka karɓa ba ,makwaɗaici kaida iyayen naka, banzaye wanda baida uba,talakan ƙauye kawai,Wayan da babu abunda suka ajiye sai maula, daga karshe kayi kulle- kullen ku na yan iskan kauye ka auroni, to baka isa in'zauna da kaiba, in'kau harka matsa to ba shakka zanyi auran Ƙauna akan Auran ka.....
5/18/22, 09:34 - MY MTN 2: *Littafin🌹DAN DAKO🌹 na kudi ne biya ki karanta cikin Aminci. Biya 300kacal to 0006454115 Amina Dahiru jaiz bank,or MTN card to this number 09165832002. then send the evidence of payment via 07038423451* ğŸ¤ğŸ™ğŸ¤²
2ï¸âƒ£7ï¸âƒ£&2ï¸âƒ£8ï¸âƒ£
""Sakin hannuta yayi ya matsa gefe tare da jawo wata ƙarama kujera ya zauna ya zubamata ido yana mai jin zafin yanda take surfamai zagi da iyayen sa, Amma yayi alkawarin kyaleta zai bata wata biyar kamar yanda mahaifiyar shi tace ,saboda ya tara laifikan da tamai dan yasamu hujja rabuwa da ita.
"Cikin natsuwa yace'" Dan kinyi aure akan aurena ni ba damuwata bane ,kana bani da hukuncin da zanmiki, amma wanda ya yiki ya yini zakiga yanda zayyi da rayuwar ki ,Ruwanki ne kishigo ko kibi ta sama kifita .
yayi tsaki ya shige É—akinta.
Masha Allah É—aki É—ayane tal ba laifi yayi kyau amma ko bedroom babu aciki, a kasamata Italian bed fari sol mai kwalliyar pink mai masifar kyau, sai wadrob da sauransu, sai sai wata kujera mai masifar kyau irin ta hutawar nan kwara É—aya .
Dakin babu Ac amma akwai fanka.
Kallon É—akin yayi ba tarry da ya ce komi ba ya sakko kasa ya zaman shi yana latsa waya.
Aɓangaran Amnah kuwa rai bace ta zare alkyabbar jikinta tare da banka kyauran da take tinanin kichin ne, anan taga ɗan karamin toilet amma yayi kyau, kuma an ƙawatashi da kayan zamani.
Gudan kyauran ta tura taga kiching ne babu wasu tarkace sai abun amfani ,sai kam kayan abinci jibge babuce kawai babu wajen.
Tsaki tayi sosai tare da share hawayen ta ta
Samu wuri tayi zamanta tare da fiddo wayar ta ta fara chart tana kuka.
Abul khairi yace .
Baby har an kaiki an É—aura miki nawin wani kato akanki ko , Dan Allah kimin alkawarin killace kanki kar kiba wani wawa damar ko da rabar inda kikeğŸ˜ğŸ˜ğŸ˜ya nuna alamar kuka.
Kuka take sosai tace.
Kai ne muradina Abul! babu shegen da zan iya bari ya raɓeni ,wallahi kai nike so.
Daganan sukaita fira ya kwantar mata da hankali akan ta saki jikinta. an'jima tasha maganin da ya turo mai gadin ayu ya kawomata.
Tinowa da hakan yasa cikin jin daɗi tace nagode masoyi ,tare da datse wayar ta ɓoye taci gaba da zamanta nan har aka fara kiran salla mangariba yazo yayi alwallah tare da cewa kitashi kiyi sallah.
Tace" bazan ba kabarin ka daban nawa daban..
Kyaleta yayi yana gamawa ya juya baya yana tafiya.
Kallo ta bishi dashi na harara daga sama har kasa tana sakin tsaki!
Da faÉ—in namiji har namiji amma jibi shigar shi wawa kawai ,Dama dan ya samu aurena ga Sallah yay ta kashe kala, aiko zaka gane kuran ka, duk sai na toya kayan ka in'yaso ka zauna tsirara .
Murmushi ya saki dan duk kan abinda ta faÉ—a yaji.
fita yayi daga gidan tare da samai key, yana zuwa masallaci yayi sallah, bayan angama ya zauna har saida yayi isha'i, tare da zama waje É—aya ya fara kwararo Addu'a shirya wa Amnah, da kuma neman Allah yabashi dan gana ya taushe zuciyar shi dagaji da ganin mumman abinda zatamai, ko ta faÉ—amai.
Wayar shi ta shiga ring .
Fitowa yayi tare da É—aukar .
Anan yaga Mamy ce.
Bayan ya ɗauka ya gaisheta tace mai in yana kusa dan Allah ya zo ya ƙarbi sako.
Yace gashinan zuwa.
Mashine ya tsaida sai gidan su.
Bayan ta fito ta mikamai wasu manyan kuloli tace gashinan sadeeq abinci ne, ga kuma key É—in machine din ka.
Karba yayi ya mata godiya sosai tare da fatan nasara a tafiyar da zasuyi .
Hakuri taita bashi game da abinda Amnah za tamai, daga nan ta mikamai wata leda mai girma da keta masifaffan kamshi, tace'' gashi kabata sai yanzu aka kawo.
Yace shikenan mungode ya hau machine dinsa ya biya gidan Ammi tare da buÉ—e foodflaks É—in dake cike da kaji ya É—ibar musu dai -dai yanda zasu ishesu ,kana ya mata sallama ya fito kamar yayi kuka, wai shine yau zai raba makwanci da iyayen shi , Allah gamu gareka yace.
Ammi ta biyoshi ta rufe gidan ta koma.
Kai tsaye gidan shi ya nufa bayan yaje ya shiga da machine soron gidan ya Rufee gidan tare da sallama ciki.
Itakam Amnah tinda ta shiga É—akin taji wani kafurin zafi ,hakan yasa ta cire duka kayanta ta daura wani towel tayi kwanciyarta ta É—au waya dan dama ba sallah take ba.
Akaro na biyu da yayi sallama bata amsaba ya sanya kai.
Sosai yake jin yanda take waya wadda ya kasa tantance dawa take, dan muryarta baya ko fita.
Ita kuwa ganin shi som baisa ta katse ba taci gaba da soyayyar ta tana samun saukin zuciya.
Gefe ya koma har saida ya kwashe wajen awa daya kana ta katse wayar tayi shuru.
Yace ga abinci nan inji mamanki kichi.
Da sauri ta duro dan dama masifar yunwa takeji.
Kiching din da tagani taje ta É—akko flat ta buÉ—e fridge ta dakko ruwan sanyi da lemon chi exotic ta dawo ta zuba nama sosai ta koma gefen gado taci nama,saida ta koshi ta ajiye gefe, tare da tashi daga ita sai towel ,sai kam gashinta da yasha gyrata ta sakeshi sai yawo yake ta fita.
Da ido ya bita yana mamakin rashin kunyar ta, daga zuwa gidan miji sai hunce wa, lallai wannan som ba tada kunya ,dan koni bazan iya haka ba.
Bakinta ta wanko tare da kunna pampon deke tsakar gidan ta cire towel din ta tarba babban boket ta fara kwarara ma jikinta, hankali kwance take wanka, dan tayi alkawarin gana mai azaba da dakan shi zai sallame ta.
Fitowa yayi da niyyar É—aukar flat É—in da zaici abinci.
Anan ya ganta tsaye duk da tsakar gidan babu haske amma akwai na farin wata, hakan ya sashi zaro ido tare da komawa da masifar karfi yana dafe saitin zuciyar shi, dan shi bai taɓa ganin babba mace tsirarra ba inba Amnah ba.
Tinani ya fara anya ba akwai wata a'ƙasaba da aka bashi wannan yarinya ?shi ya taɓa gani ko jin sabuwar amarya haka ,anya yarinya nan cikakiyar budurwace kuwa? Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un yace yana jingina da bango.
Itakam hankali kwance ta gama duk Abinda zatayi kana tayo É—akin tana tako...
Hanya ya bata ta shige tare da fitowa.
Anan ya dauki flat din ya zuba kaÉ—an ya dawo waje yaci.
Yana gamawa yaje yayi wanka ya dawo da kayanshi ya mayar a jikka sa ,ya ɗauki wasu ƙananu yasa ya koma kan sopa ya kwanta.
Amnah kuwa chart tai tayo sai É—aya na dare ta kwanta.
Washe gari bayan ya dawo Sallah Asuba ya shigo tare da cewa" kina lafiya?
Banza tayi dashi ta kyale sai wayar ta da ta daina jin shakkun boyewa.
Shima shareta yayi ya son dai Alhamdulillah yafita hakkin ta.
Mamy ta kirashi tamai bankwana suka tafi ,yana mai kara jin girmanta har cikin ranshi, dan som bata nemi yar data haifaba takashe wayar.
Daga haka bacci ya kwashe shi.
Karfe goma ya tashi ya kalli inda take kwance tana bacci.
Ƙarasawa wajenta yayi yana kallon fuskar ta ,tsaf irin ta Mamy, dan dai zuciyar ba ɗaya ba.
Bakin gadon ya É—an kaima duka kaÉ—an .
Cikin magagin bacci ta bude idonta ta zuba ma fuskar shi ido, tare da shafo sajen shi tace ina sonka Abul khairi, babu wanda ya isa ya mallakeni sai kai ,kaine burin raina, kai naiwa tanajin rayuwata,karike alkawarin mu,dan kai nike fatan bama makullin sirri nah...
Idon shi ya lumshe tare da janye hannuwata yace.
" Miza'asiyo miki wanda zakiyi amfani da shi?.
Cikin wani irin zafin nama ta mike tana watsam@i harara tace. "Miye Haka, ina mafalkina zakazo kamun wani tukus gabana, ba'aso, waye zaimaka girkin ,aiko sai dai kayi duk abinda zakayi mtsss .
Baice komi ba sai zuciyar shi da ya farajin tana mai zafi kan yanda take mai magana son ranta,da sauri ya bar É—akin ya faÉ—a toilet ya zuba wanka ,yazo ya É—auki wata dakekiyar shadda ya sanya, kana ya dawo ya zauna yana latsa karamar wayar shi.
Tsaki ta jera sosai tana faÉ—in" aci kayan aro aita buÉ—awa.
Bai ko kalleta ba yana gama abinda zayyi ya fita.
Gidan Ammi yaje bayan sun gaisa take cemai ya Amnah?.
Yace Alhamdulillah.
Tace to ya zaman naku badai matsala ko?.
Jim yayi sai kuma yace. "Alhamdulillah.
Hamrat ta fito bayan sun gaisa ya tashi ya tafi gidan Nene.
Anan ya yini yaci abinci ya koshi sai bayan la'asar ya koma gidan shi.
Anan ya isketa tsakar gidan tasha wanka cikin wasu mahaukatan kaya tana Video a Tik tok tana ta juya jiki...
Shafata yayi ya wuce ya shige É—aki.
Atakaice haka suke ta rayuwa ba wata shakuwa kowa har karshi yake waya kam kullum tana hannu ta tana soyayya,Shikuma baitaɓa fahimta ba yana ganin da ƙawayen ta kawai take mu'amullah ko yan uwan ta.
Suna samun wata É—aya Amnah ta fara girki. Amma na dai -dai cikin ta shikam ko oho.
Gashi Kuma ya samu kanshi da kasa faÉ—ama Ammi,ko tace yazo yaci zaice Alhamdulillah.
Sai dai yaje gidan Nene yaci Abinci wani lokacin kuma ya siya tasha yaci, gashi kuma baya aikin komi, ga zara bata barin dami, da kaÉ—an kaÉ—an kudin shi sunfara karewa.
Bayan wata É—aya.
Amnah ce kwance dan yanzu ta saba da zaman gidan kuma tanajin daÉ—in zaman ,saboda tana sakewa tayi soyayyar ta da Abul khairi , Dan yanzu har Vidio call suke. agefe kuma ga kallo BF dinta sai abinda yaci gaba, Kullum da ciwon mara take kwana, danma tana kwan-kwaÉ—a maganin da Abul khairi ya bata tana rage damuwar ta sosai ta hanyar yawaita bacci.
Sadeeq ne ya fita kasuwa dan samun abinda zai É—anyi dan ya samu ya rarrage , Amma haka ya karaci yawan shi ya dawo.
Haka yake fita kusan kwana ukku amma sai dai ya dawo a wahalce.
Shawwara ya yanke akan zai Sayar da machine É—in sa akwai shago kofar gidan shi sai ya bude ko kayan provition ne
Bayan yayi shawara da Nene da Ammi suka goyamai baya.
Hakan ya sashi fara neman takardun machine É—insa amma duk inda ya duba bai gani ba , Hakan yasa ya rikice har yazo cikin bedsite .
Anan yaga kwalabe kayan shaye- shaye sun kai hamsin.
Ido ya zaro jikin shi ya É—auki rawa , wake shan wayan nan abun, Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un yace lokacin da ya kalli Amnah yaga yanda tayi muguwar rama,Dama ya lura kullum bacci take, dan ko abinci batacika ciba.
Kanshi ya dafe tare da faɗin duk tsananin kiyayya ce yasaki jefa kanki cikin wannan mummuna halin ,yah Allah ka kawoman mafita ya fada yana kwashe kwalaben tass ya fita dasu yasa a machine, kana ya dawo dakyale ya gansu yaje yakai kasuwa suka bashi kudin shi ya shiga kasuwa yayo sayayya abinda zai buƙata, Anan yazo ya shirya shagon shi.
Agajiye cikin yunwa ya shiga gidan ya iske Amnah ta tashi sai layi take.
Da sauri ta faÉ—a jikincshi cikin tsananin maye ta fara mai magana tana fadin ina sonka Abul khairi, kasoni kaima kaji, inajin yunwa