Showing 3001 words to 6000 words out of 94971 words
Chapter 2 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt
yabata sosai wato yana ganin bai kai matsayin da zaici abinci cikin kwanan da zasu ciba kenan.
Cikin natsuwa tace aa mudakai duk yan Adam ne bawani abu kaci kawai.
Jin cikin shi namai wani mahaukacin yatsinawa ne yasashi mika hannu biyu ya É—auki kayan abinci tare da buÉ—e Bayan motar ya ajiye kana yashiga ciki shima yayi shuru yana jiran ta tafi.
Fahimtar hakan yasata juyawa ta koma ciki tana mamakin yanda yake da kamun kai haka da kunya kamar ba DAN DAKO ba dan tason su da fitsara.
Yana ganin wucewarta ya juya ya kalli ko ina ganin babu kowa sai mai gadi da shima ya juya baya yasashi kai hannushi bayan rawani ya kwance tare da fara zagaye fuskanshi dashi har ya kwance.
Ahankaki ya ÆŠago kanshi yana sauke numfashi.
Wani irin tsalle zuciyata tayi da tasani sakin wayar batare da na shirya ba......
5/18/22, 09:33 - MY MTN 2: 🌹D'AN DAKO
MALLAKI
UMMY AYSHA🌹
3ï¸âƒ£&2ï¸âƒ£
""Masha Allah itace kalmar da ta samu fitowa daga cikin baki na.
Wani irin haɗaɗɗan saurayine fari sol irin farin larabawa, ga wata tausassa sumar da tayima kanshi ƙawanya, ga sajenshi da yayi ma sumulmula fuskarshi kyau yayi shar sakamakon zufa da fuskarshi tayi, Wani irin dogon hanci gareshi da yatafi D'oɗar har baka, ga wasu jajayen lips da suka dace da kyakyawar fuskarshi, yana da idanuwa masu masifar kyau da ɗaukar hankali.
Ahankali yaja hannun rigarshi sama kutt na furta lokacin da idanuwana sukai tozali da kyawawan hannayenshi da suka kasance farare sol, Ga galgasa da tama hannu rumfa irin dogayen nan mai tsananin sheki da sulɓi.
Robar ruwan ya É—auka tare da fidda hannunshi waje ta window mota ya fara wanke hannun shi.
Yana gamawa yaja kwanikkan tare da buÉ—e su.
Idon shi ya lumshe dan yaushe rabon da yaga abinci mai kyau kamar wannan.
A'hankali yayi Bissmillah tare da fara tsakurar abincin kaÉ—an -kaÉ—an yana ci.
Baiwani ci da yawaba ya ture tare da turo hannun shi still ya wanke ya É—aga cup din Kunin Ayar yasha sosai saida yayi rabi kana ya ajiye.
A'hankali bakin shi ke motsawa alamun Addu'a yake ta bayan gamacin abinci(ALHAMDULILLAHI LAZI AÆŠÆŠA'AMANI HAZA, WARA ZAKNIHI MIN GAIRI HAULIN MINNI WALA KUWWA)
Idon shi ya lumshe tare da jingina kanshi da motar.
Dai -dai kuma lokacin ne aka fara iska mai tsananin karfin dake nuni da ana gaf da sakko da Ruwan sama.
Idon shi ya lumshe tare da shaƙar kanshin ƙasa dake tasowa.
Da kallon gefen da kayan daya ajiye musu yake wanda ya tabbatar da in ruwa ya safka akansu sun gama yawo.
Cikin natsuwa ya maida rawanin fuskar shi tare da fitowa yafara tsakula motar dan yasamu ta tashi yakara gaba kar ruwan ya safko amma motar taki tashi.
Tsananin fushi yatasomai wanda yasashi kaima motar wani wawan dukan dayasa marfin ɓallewa ya fita.
Aƙufule ya kwaso tiren kayan abinci tare da ajeshi cen gefe inda za'a iya gani kana ya dawo yana ɗaga kanshi sama ganin yanda garin ke rinewa sosai.
Tsaki yasaki tare da fara kokarin tafiya.
Dai -dai lokacin ne kuma Amal da mam6y da Amnah suna fito cikin sauri Amal tace .
"ÆŠan uwa dakata mana."
Shuru yayi batare da yatsayaba kuma bai fasa tafiya ba.
Yana gab da cimma get Amal tace katsaya Dan Allah.
Cak yatsaya batare da yajuyo ba.
Rai ɓace da ganin yanda yaketa izza Amnah da tasha wasu riga da wando da suka masifar yimata kyau rigar orange mai ratsin Black sai wandon kuma daya kasance Black mai ratsin orange kanta sanye da wata Black din hula data ɗan turata baya yalwataccen gashin goshinta duk yafito, daga Baya kuma foygon gashinta ya bazu akafaɗata sai sheki yake,Cikin isa tafara tako cike da izgili har zuwa inda yake.
Cikin tsananin ɓacin rai tace.
"Mene Acikin Tumbi banda kashi,Ina ɗan burburi ina niganci,Ina talakka ina girman kai,Ina D'AN DAKO ina iskanci da har za'adinga kiranka amma kayiwa mutane banza ka kyalesu kai ga shashasha ko? Wawa baƙauyen da yakasa gane gabas da yamma, Kayi maza kaje anason ganin ka koba sallamaka za'aiba da kake nunama mutane iko, Takarasa tana nunamai inda su Mamy suke tsaye akan Bagala..
Da zata lura baki dyayan jikinshi kyarma ya d'auka kyarma da rashin ganin fuskarshine yasa aka kasa ganewa...
Amal tace Mamy kije da kanki kartamai wani abu fa.
Cikin amincewa da maganata Mamy ta tattako cikin dattako har inda suke tsaye.
Sallama tayi tare da cewa bawan Allah munata magana amma shuru .
Baice komi ba sai juyo da kanshi da yayi ganin Babba maca ce cikin mutunci ya buÉ—e bakin shi ya gaishe ta .
Amsawa tayi cikin fara'a .
" Tace dan Allah ko zaka iya zuwa ka kwashemun kayan nan, Naga kamar za'afara ruwa kuma munan bamu da masu kwashewa wancen Tsohon bazai iyaba saboda halin girma ta nuna mai gadi.
Kai ya jinjina batare da yace komiba yayi gaba cikin sassarfa.
Yasa hannu zai É—auki kayan kuma yayi tsaye yana tinanin ta ina zai dosa dasu ga bakin shi yayi Nawin da bazai iya magana ba.
Mamy takatse mai tinani da faÉ—in ga inda zaka ajiyesu acen, Wancen store É—in dake kusa da dakin Baba Madu.
Baice komi ba sai kwasar kayan da ya fara cikin jarumta yana kaiwa kamar ya d'auki kwali.
Yana gab da gamawa akafara iska mai matsanancin ƙarfi.
A'hankali ya duƙa yakama kowanne buhu da hannu ɗaya yazamana buhu biyu ke ahannunshi yafaraja da sauri.
Suduka kallo suka bishi dashi inda Mamy jarumtar saurayin ta burgeta, Hakanan taji sha'awar samunshi amatsayin wanda zai dingamata hidimar gida koda kuwa aikin kula da get ne, Dan taga dakyal Baba Madu ke buÄeshi yana rufewa.
Zai kai buhun karshe cikin sauri jin ana yayyafi gefen buhun ya fashe wanda yasa Dawar dake ciki fara shatata.
Saurin ajeshi yayi cikin zafin nama ya sungumi É—aya'n yayi É—aki.
Dawowa yayi ya kai wanda ya fashe tare da Sunkuyawa yana kwashe wadda ta zube.
Fararan ya tsunshi yasa yana tattarawa yana tsaka dayi Saiji yayi an takemai su da ƙarfi da tsinin takalma.
Wanda hakan yasashi saurin juyowa da karfi ya sauke kwayar idon shi cikin ta Amnah.
Bin dogayen yatsunshi take da kallo ganinsu wasu irin farare tass har wani jaja sukeyi ga tsintsiyar hannu A yalwace da galgasa..
Ido takashe tanamai kallon kurullah tare da kara É—aro idonta a murzazza fatar shi datayi lumi.
""Kai ÆŠan Dako ne kuwa? In har takasance haka miyasa kamuna asara? Kana aiki da hankali kuwa? Kai da kake Talakka kai ya kamata ace kafin kowa iya tattali, Amma saboda ba gidan Tsoho bane sai a wifintas?
Shuru yayi har lokacin kanshi a sunkuye yake sai hannunshi data danne da takalma da yake kallo wanda still tana akai taki É—agawa shima bai motsa ba..
Mamy takaraso wajen tare da dakamata tsawa da ta sata matsawa.
Kuɗi mai yawa Mamy ta ƙilgo tabashi tare da cewa.
"Dan Allah kayi hakuri kaji ko,Yarinta na damunta ,Ƙarɓi wannan maza katafi kaga am'fara yayyafi wannan kabarshi ba damuwa ko Baba ya ba tsuntsaye.
Mikewa tsaye yayi tare da Ƙarɓa kudin ya kilga ya dauki dubu biyar yace.
Ga sauran nan na kilgi abunda ke hakkina .
Mamaki sosai yaba Mamy wanda ta bishi da kallo na ganin yanda yabata maƙudan kudin da ita kanta batason adadinsu ba.
Murmushi ta saki tare da cewa" ka rike nabaka ai.
Kai ya gilgiza alamun a'a...
Tsawa Amnah ta dakamai tare da faɗin basu kazo nema ba? Kuma zaka tsaya kana ja'inja da ita munafuki ka Ƙarɓa ka wuce daga nan ka cikamu da warin talauc....
Tass!Tass!Tass!!!
Haka Mamy ta wanketa da kyawawan maruka guda ukku wanda sukasata Tuntsirawa.
Kamin mamiu ta juyo har yakai get cikin sauri tare da kwance rawanin kanshi yafara tafiya.
Kiranshi mamy keyi ko tsayawa baiba.
Cikin ikon Allah yana fita yaga mai Machine ya. Haye tare da" faÉ—in ya kaishi kasuwa.
Ganin mai machine na kallon shine ya sashi tunowa da ashe fuskarshi ba É—aure take ba, Da sauri ya naÉ—e fuskar yabar kwayar idon shi.
Cikin rawar jiki da son samun shiga mai machine yace
"Wallahi Dan uwa kaman kama da wani Soja mai suna Sadeeq daya ƙasance Ɗan Gidan Matawalle...
Tsawa sosai ya daka mai tare da faÉ—in saukeni! Dan na hau machine É—inka shike nuni da kasamu damar da zakamun tambayoyin da Ranka keso ?Maza saukeni anan kamin in maka abunda bakai tinani ba, Duniya ba akamane da zaka tsareni da tambayar banza yakarasa cikin sauti da rawar jikin da ta furgita Mai Machine.
Cikin Rawar ɗari mai machine yace "Kayi hakuri Wallahi nima cewa nayi kamace saboda na taɓa ganin shi so ɗaya gidan da nike kai yaransu makaranta Lokacin ma da kek....
Kan ya ƙarasa ya saki wata gigitatta tsawa da tasanya mai machine saurin yin parking tare da direwa ya yanka da gudu..
Tsaki sosai ya saki tare da sauka yafara tattakawa da sauri dai-dai lokacin ne kuma aka tsuge da ruwan sama sosai.
Babu abunda yashamai kai tafiyar shi yake cike da zafin nama sa hannayenshi da yasa ya tare Duka aljihun shi saboda wayarshi da kuma kudin Baba daya karb'o.
Abangaran Mamy kuwa afusace ta kalli Amnah tace ke da kinson Asalina da naki da kuma wahala rayuwa danasha Wallahi da baki kyamaci talaka ba , Saboda...Sai kuma tayi kwafa tare komawa ciki tana share Kwallah a fakaice.
A ɓangaren Amnah kuwa.
Kyarma sosai jikinta ya É—auka akan talakka yau aka mareta aka kaskantar da rayuwar ta agaban wanda baida matsayi.
Jin ruwa ya kaule da karfi yasata tashi jiki asanyaye tayi É—akin ta tare da É—aga waya ta Daddana.
"Please Abbah ka dauka"
Tafada tana yarfe hannu tare da matse Kwallah.
Jin ta kase bai ɗaga ba yasata hakura sai kwanciya da tayi akan makeken gadonta ta saki wani mahaukacin kuka mai tattare da ƙunar zuciya..
Aɓangaran Mamy kuwa tana shiga ɗaki ta dyauki ƙaramar wayar ta tare da kiran Mijinta Alhaji Isa mai Zinarai da number shi ta sirri da bakowa yason shi da itaba sai amintaccen shi.
Bayan ya É—auka suka gaisa .
mamy take tambayar yaushe zai dawo sunyi kewar sa?
Murmushi ya saki tare da faÉ—in nima haka amma next week ina nan dawowa insha Allah ina Yara na?..
Farin ciki sosai Yakamata inda tace" To Allah yakawoka lafiya zanma tarba ta mussam man .
Murmushi yasaki mai sauti yaire da faÉ—in nasani matata nason zakimun fiye da haka .
Dan jim tayi batace komi ba dan gane da yabon da yamata.
Daga cen ɓangaran yace. "Are you ok Sweetie?
ÆŠan nisawa tayi kana cikin raunatata murya mai haÉ—e da roko tace Hubby wallahi alfarma nike nema awajenka.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin Alhamdulillah da awajena kike nemanta ba awajen kowa ba, indai har kinsanni kinsan waye ni to kinson babu Abinda zan gagara yimiki, Dan haka faɗi buƙatunki kai tsaye nida abunda kikeso duk mallakainki ne ...
Wani irin sanyi ya ratsata cike da kwarin gwiwa tace "Hubby agasjiya ina da bukatar sabon mai aiki , Saboda Baba ya manyanta, Ga rabon nan da zanyi bazan iya cewa komi sai su Amnah zasuyiba kadai son halinta zamuyita samun matsalane da ita.
Shikenan Tsadadda "Matata duk abunda kikeso haka za'ayi insha Allah zanyi ƙoƙari sosai wajen samo miki wanda ya dace.
Da sauri tace ''Am nace ba ...
Nan ta kwashe duk abunda ya faru game da wanda yama su Amnah Dako tare da jaddada mai cewa zai iya dayuke duka ragamar gidan baki É—aya, Fatan ta dai ya bata izinin zuwa nemanshi wajrn mahaifinshi dan taga alamar yayi fushi da abinda Amnah ta mai duk da ba komi ta fad'amai ba tana ganin sirri ta ne tsakaninsu da Yar ta. ..
Cike da fahimta haÉ—i da kwarin gwiwa yace "Na amince miki Hajiyata duk abunda kikeso ina sonshi, Ke kinson matsayinki awajena sannan kinson burina da farin cikina inga kinsamu abunda kikeso.
Fira suka shiga yi cike da shauki kana ya kashe wayar.
Ganin babba wayar shi Amnah ta kirane yasa da sauri ya maida mata kira.
Cikin shagwaɓa take faɗin
"Abbana bakasona yanzun kwana nawa banjika ba?
Murmushi yasaki tare da cewa "Amnah nah in bansoku ba wazan So?
Cikin jin dadi tace babu Abbah .
Dama faÉ—a ma zanyi Mamy ta mareni akan ÆŠAN DAKO ko,kuma Abbah agabansa fa,Basai ya rainani ba ya raina ajina?takarasa tana sakin kuka mai sauti.
Take muryarshi ta canza cikin byacin rai yace Mamy taku ta mare ki akan wani banza barni da ita anjima zamuyi magana yakashe wayar yana Huci.
Lokaci guda kuma ya É—auki wayar shi Afusace ya kira Mamy da dai-dai lokacin ta fito daga toilet ta É—auro Alwallah.
Mamaki ya kamata ganin wayar shi bayan yanzu suka gama waya.
ÆŠauka tayi tare da yin sallama......
Amsawa yayi.cikin ɓaci'n rai yace mi"Amnah ta miki da kika Mare ta akan wani Ɗan Dako..
5/18/22, 09:33 - MY MTN 2: D'AN DAKO🌹
MALLAKI🌹
UMMY AYSHA🌹
🅿ï¸5ï¸âƒ£&6ï¸âƒ£
"" Shuru tayi ba Tare da ta ta kaba.
Cikin fushi yasake cewa "kina fa jina Fulani!
Nasha faɗamiki ban yarda da abunda zai shafi ɓacin ran Yarana ba, Akan wani sakarai zaki zauna ki Mari yarin yata ,in kika mata illah fa, mizakice ,Ki kiyaye daga yau ya kashe wayar...
Shuru tayi ranta na ƙuna akan bin bayan rashin gaskiya da yayi.
Sai da ta bada kamar ten mint kana ta É—auki wayar shi tamai Text kamar ''haka."
""Hubby Kayi hakuri banyi wani abu dan ɓata ranka ba Amma ni nason som Amnah halin da take ba mai kyau bane amatsayinta na ya mace, Amma in maganata tamaka zafi kayi hakuri ka yafeni kason fushinka masifane akaina, Har kullum fatan neman yarda Allah da taka nike saboda aljnnata na kasan tafin kafarka, Ina sonka sosai mijin marainiya(SUNAN DA TAKE KIRANSHI KENAN IN TAGA YANA CIKIN FUSHI SABODA YAKAN KARYA MISHI DA ZUCIYA) ta turamai.
Cikin kankanan lokaci wayar shi ta shigo wayar ta.
Murmushi ta saki tare da É—aukar tace'' Ka sirace Hubby..
Murmushi ya saki yace kiyi hakuri da abunda ya faru kinji sweety ,kinson bana iya control din kaina akan soyayya yarana, É—an allah ki daina cewa kedin nan marainiyace bayan kina dani ga kuma NENE ..
Murmushi tayi mai sauti ta ce" shike nan yanda kace.
Daganan sukai sallama ta ajiye wayar tare dayin Sallah.
Bayan ta gama ta É—aga hannu sama tana kwararo Addu'a da hawaye jage- jage a fuskar ta wanda banson na minenen ba.
Aɓan garan Habu Ɗan Dako kuwa cikin sauri yake tafiya baki ɗaya kayanshi sun jike inda suka lafe jikinshi suka fiddo kyakyawan zatinshi na zama cikakken Namiji mai zarra.
Bayyi wata tafiya ba ya ƙaraso kasuwa saboda dama sun kusa.
Koda yazo kai tsaye Rumfar da Baba suke yashiga ya samesu tsaitsaye suna É—aure Buhun hunan hatsin su.
Sallama ya musu suka amsa ya koma gefe tare da kwaso Damen kuÉ—in yaba Baba.
Murmushi yayi yace "Habu ka kasa hakurin ruwa ya É—auke ka taho cikin su.?
Kamar bazai magana ba kuma ya nisa cikin ƙasa da murya yace" Motar ta lalace bata tashi shiyasa na barota acen .
Ido Baba ya zaro cikin ɓacin rai tare da cewa" Wai kai wane irin mutum ne, Haba ina dalili nan da G.R.A din amma sai da kamun asara ɓatamun mota, To da ubanmi zan koma gida ?Habu kana da matsala wallahi badan Amanar kaba da tini na rabu da kai ,kai kason kaf ɗin kasuwar nan babu wanda ya rufama asiri kamar ni ɗan kwal uba har yau banson fuskar kaba na yarda dakai na sakar ma dukiyata na baka Amintatta motata da ba kowa nike ba 'ba , Amma saboda Ƙaton banzane kai sai da ka lakata to Wallahi sai kabiyani yaƙarasa yana neman yin kuka saboda tsananin son motar da yake...
Duk da Habu na cikin ɓacin rai hakan bai hana kwayar idonshi ta kasa fallasa yalwattace. Murmushin dake rufe da fuskar shi ba.
Kallonshi Baba yayi baki asake yake karema idonshi kallo.
Kuka yasaki yace "Habu ni kake ma dariya?Ni ka É—auka mahaukaci ka sacemun mota kuma kazo kace lalacewa tayi Habu ni????
Dakyal ya gimtse dariya dake tasomai yace.
"Baba zaka iya bina muje kaga motar ka tana cikin aminci , Sai dai na ɓalle murfi ɗays data batamun rai yakarasa hankali kwance cikin kuma tabbatar da gaskiya....
Salati Baba yasaki yana zama ƙasa tare da ɗora hannunshi akai yasaki kuka mai karfi da yasanya matasan wajen kwashewa da dariya dan kowa yason yanda yakeji da motar shi da Abun hannushi ,Baya tauyema kowa hakki amma kuma bayasoAmishi asara kota kwabo, Mafarin ko tukin motar bai yarda kowa yayi ba sai shi sai ko Habu daya Amincemawa gashi kuma yau ya zalunce shi...
Cikin shasheka da rikicin tsufa yace" Habu ka cuceni ka zalinceni bansonkaba na baka amana kayi ha'inci Allah yasakamun kuma ba zan bika ba kaje ka saidani babu ni babu kai har abada, Kaje na koreka kai
Iro bishi ka karɓomun motana yafada yana nuna wani matashi.
Dariya Iro yayi yace walkahi bazan bishi ba nima fa ban sonshi ba kawai kai dai ka aminta dashi ya zauna cikin mu.
Duk kan maganar da suke Habu na jinsu kuma yason Gaskiya sukai su kadai suka aminta dashi batare da sun taɓa ganin fuskarshi ba yazama dole ya cire musu kokwanto a ransu! A'hankali yasanya hannun shi yafara warware Rawanin shi har ya gama tass.
Wata irin zabura Baba yayi tare da ƙoƙarin shiga cikin buhun geron dake gabanshi da bai wuce kwano goma ba.
Iro da jikin shi ya É—auki rawa shida wasu samari guda biyu dake cikin shagon yakamo hannu Baba ya makalkale yana zare ido.
Ihu Baba yasa tare da faÉ—in" DAGA TAIMAKO Ashe aljani muke tare da shi tsawon wata shidda, Wayyo ni Audodo naga ta kaina nashiga ukku na lalace Zai kasheni yau namai faÉ—a, Wayyo Allah na yakarasa cikin kyarma.
Kyakyawar fuskar shi ya ÆŠago ya zubama su Baba ita tare da cewa" Ka kwantar da hankalinka Baba ni mutum ne bawai Aljani ba, Kuma ni ba Macuci bane dole tasani rufe fuskata bawai dan ra'ayina ba , Amma namaka alkawari daga yau bazaka sake ganin fuskana arufe ba amma kataimaka ka barni bakin aikina kai kaÉ—ai kamun halaccin ÆŠaukana.Sama da wata biyu ina cikin kasuwar nan ina yawo lungu da sako dan samun wanda zai taimakamun da aiki amma haka nike gama yawo na inkoma inda nafito bansamu komi ba, Saboda mutane naganin cewa ni wanine ko kuma kyan da Allah yamin yafi karfin ace ina neman Aiki DAKO, bayan Allah shike tsara halittar bawan shi ba wai