Showing 63001 words to 66000 words out of 94971 words
Chapter 22 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt
kuma sunan da nasamu kenan?.
Yace yees ke dince kin zama zumata wadda nike fatan inta lasar ta har ƙarshen numfashi...
Murmushi tayi kawai tana kallon shi .
Yace tashi kimun Tatata inga in da sauki ,inkuma sai A'hankali muje Asibiti.
A'hankali ta yinkura tare da cemai zan iya My love, mazane kawai naji, amma kwana biyu zan koma dai- dai ,zan kula da kaina Insha Allah.
Kanta ya shafa yace" Masha Allah sweety nah ALLAH yabar mu tare.
Tace" Ameen Baby.
Bacci suka koma sai goma na safe ya tashi. yana tashi ya sake sungumar ta ya gasata sosai kana ya maidota d
ÆŠaki.
Bayan ya mai dota yaje yayi wanka ya haÉ—a musu tea suka sha suka koshi ko bread babu.
Zama yayi kusa da ita yana jawota jikinshi Yace" Matata zanyi tafiya,inaso kimin Addu'a nasara,Daga karshe kuma karki manta dani Dan Allah, Amnah ki kulamun da kanki, Na baki Amanar kanki data Baby nah in ALLAH ya bamu rabo,Ki zamema su Ammi garkuwa da zata maye gurbina kinji ,na so mallakarki tin kamin wannan ranar dan zama inyi jinyar ɓarnar danayi,to amma nayi alkawrin duk ranar dawani nawa ya son muhallina ko inda nike to ya zama dole indoshi Kasata.
Da a iskeni kwara in iske ...
Hawayenta ta share tace" taya zan iya kwana babu kai,bani da fili sai hannuka ,Kirjinka shine katifana,taya zaka barni adaidai lokacin da muka zama abu daya muke buƙatar zama ƙalƙashin inuwa ɗaya?
Yace na sani Amnah nima bawai tabbacin bazan dawo gareki ne bani dashi ba a'a kawai dai ..
Tace kawai mi ,wallahi ni bazan iya zama ni É—aya ba.
Yace shikenan tashi muje gidan Ammi.
Cikin kuka tace yanzu yau rabuwa zamuyi?...
Yace ganga jikin ce kawai zasu rabu Amma ruhin da zuciyar a'tare Allah ya halicce su kinji.
Kai ta É—agamai ya É—akko mata wata riga milk ya bata ta sha,tare da bata maroom din hijjob tasa.
Kana ya miƙar da ita tare da sata cikin kirjin shi haka ya rufe ɗakin.
A'hankali take takawa har suka fito soron gidan.
Anan ya ɗakko ƙaramar kujera yace "ta zauna yana zuwa, zai tsaido Napep.
Kai ta É—agamai tana sakin kuka sosai tare da lallatsa wayar ta.
Kangawa tayi taji bata shiga kamar ma layin ƙasa yake.
Tsaki ta saki, ta sake kiran wani.
Sai ga murya Nene RaÉ—au tana faÉ—in" ja'ira kinji uwarki tazo shine harda mun waya ko...
Cikin rauni batare da ta fahimci mitace ba tasa kuka tace" Nene wai kinga zai koma mahaifar sa zai barni , Dan Allah Nene kice yaje dani, wallahi bazan iya rayuwa ko kwana babu shiba,kana Nene ina tsoron wani abu ya sameshi, Nene zuciya na bazata jure ba..
Da sauri ya shigo ya tallabota ita kuma wayar na akunnata tanajin Nene na salati.
Kuka ta sake sawa tac"e yanzu gida Ammi zamuje Nene.
Nene tace to" muhaÉ—u cen mu duka ta kashe wayar.
Tsaye yayi yace" Amnah bazaki daina kuka ba, bakyaso inyi abunda ya kaini.
kedawa ke waya.?
Tace Nene ce mana .
Murmushi yayi kawai ya sata a Napep din tare da jawota jiki , kana yaci gaba dalallashi har suka isa gidan Ammi.
Anan sukaga motoci manya -manya sun kai guda goma, wayanda ke cike da Sodoji ko wanne na rike da bindiga suna mazurai, fuskar nan babu rahma ga unguwar ta cika da mutane sunata kllonsu .
Azabure tace Baby miyafaru Dan Allah, mi akayi naga sodoji kofar gidan Ammi?.
Murmushi yayi yace lafiya ƙalau my wife.
Sauka sukayi suka sallami mai Napep da jikin shi keta rawa.
Sadeeq ya fito hannu shi rike da Amnah, yana mai sake rungumeta cikin jikin shi.
Ganin sun doshi inda suke wani soja É—aya ya ganshi hakan yasa da sauri ya É—akko wata sarewa ya fara busa mai daÉ—i.
Hakan yasa suka fara É—irkowa daga kan mota jif -jif suna jera layi gwanain sha'awa.
Da sauri wani babban mutum ya fito daga gaban mota fuskar shi cike da Annuri.
Sadeeq na ganin shi ya ɗaga hannuwan shi guda ya saramai tare da sadda kanshi ƙasa....
Da sauri mutumin ya ƙarasa wajenshi cikin tsananin farin ciki yace" Conal ya dawo bakin aiki, Alhamdulillah Gwarzo mu, jajir taccen jarumin mu yau Allah ya haɗamu dashi...
Sadeeq ya É—ago kai yace" Yallabai ga matata .
A'hankali Amnah da mamaki keson kasheta tace .
Good Morning sir.
Cikin farin ciki suka gaisa ya mikama Sadeeq wata leda tare da faÉ—in zamuje Ran gadi mudawo, munbaka awa biyu kamun mu wuce.
Yace tnx u sir...
Matsawa yayi inda sauran suke fuskar shi da sassanya murmushi ya É—aga musu hannu.
Ji kake taf -taf suna sarawa tare da doka kafafuwan su ƙasa. Daganan busa ta tashi ta murna dawowa shi bakin aiki......
5/23/22, 10:31 - MY MTN 2: *Littafin🌹DAN DAKO🌹 na kudi ne biya ki karanta cikin Aminci. Biya 300kacal to 0006454115 Amina Dahiru jaiz bank,or MTN card to this number 09165832002. then send the evidence of payment via 07038423451* ğŸ¤ğŸ™ğŸ¤²
Alhamdulillah! Alhamdulillah!!
Yan uwana mata ina kuke ku malmatso ga wanni sirri da nike son baku, ita ya mace sai da kamshi, ina macen da take ganin izgili da wulakanci da ake cewa maza nada shi, hmmm yar uwa to inkin kasance a haka da alama akwai ayar tambaya akanki. Tambaya ta ta farko gareki da wane irin turare kike amfani a jikin ki ?,da wane irin turare kike turara gidan ki,shin dawane irin turare kike Zukunni, hmmm to matso kusa kiji yar uwata.
Shi kamshi Annabi muma ya faÉ—a abin sone,kuma Abune mai sanya natsuwa da girmama ma'aboci shi , Da Yawon son kusantar sa.
Duk kan wulakanci da izgilanci na maza akwai turaran da zai miki maganin sa da izinin Allah,ba boka ba malam,wanda zai karkato da hankalin mijinki akan ki ku samu fahimtar juna.
Ko kin son kamshi na dakusar da fitinar É—a namiji yar uwa? kigarzayo ki kwashi rabonki ga shaharariyar yar mai Dugurin nan mai suna UMSAD INCENSE ,Mace mai kishin mata da son Fiddo martaba mu.
Nayi Amfani da turaranta naji masifar daÉ—in da yasa nakasa barwa raina. Nace bari in yaÉ—amuku dan kowa ya mallaki nashi cikin farashi mai sauki.
Da fari bari in zayyano muku su kamar haka.👇
Maleek Al'oud
Royal kush
Cous-cous
Kajiji
Original sandal
Sandal flex
Sandal bange
VIP mix
Hawi
Al'oud
Kindikay
Danal banat
Darot
Habil
Gaf-Gaf
Sirrun nisaa'i
Sandal chips
Kwalacca
Humra black and body milk
Attractive humra.
Yar uwa zanmiki Dallah- Dallah.
Akwai turaran da zaki sanyama kayanki .
Misali! kisa kabasa kiturare kayanki .
Akwai humra da bazaki sataba sai zaki turaka.
Akwai turaran kaya ,na jiki, Dakuma na ɗaki. Akwai kwallaca sirri, amma bama badata gaskiya sai ga wanda baida kishiya , Dan muddum kina amfani da ita tofa gabaki dayan hankalin mijinki akanki zai dawo,Dan yana juyo da hankalin namiji akanki baki ɗaya ,zaki zama shalele Baby, Akwai sirrin nisaa'i. hmmm Dagajin sunan kason na dabanne,na baki sati ɗaya ki gwada ki gani Hajiya ta, tsugunno ake akai ga mai buƙata ya tunɓe mu ta wannan layin 08028827241 karku manta UMSAD INCENSE mune na ɗaya.
Muna aika kayan mu duk inda kuke.
Kamshin jiki martaba mutum....
🅿ï¸4ï¸âƒ£5ï¸âƒ£&5ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
"""Sunkai 10mnt kana suka fara sara mai suna juyawa cikin tsari suka shiga mitocin su suka tafi..
Amnah kau sai lafeeay take cikin jikin shi dan mamaki abinda ta gani.
Motocin na karya kwana motar su Nene na shigowa layin.
Yayin da Abbah ke tukin motar Mamy kusa dashi, Nene da Amal a baya...
Afurgice Nene tace "kai Isa minene haka ake cikin wannna unguwar, ko kisa akai?..
Abba shima cikin mamaki yace" A'a Hajiya bana tinani nima bansani ba gaskiya.
Suna isa kofar gidan amymi sukaga Amnah da Sadeeq tsaye yana mata magana.
Cikin farin ciki Amal ta bude kofar ta fito ,tana isowa wajen Amnah da gudu ta faÉ—a kanta ..
Da sauri Sadeeq ya tallabota yana kallon Amal yace "Sst bata da lafiya fa, Kimin A'hankali da ita.
Asukwane Amal tayi baya tana sake kallon Amnah data lafe jikin shi. tace''" Aunty Amnah baki da karfi jikine, kuma bakya nurna dawowa na ko?
Amnah tayi murmushi tana mai jawo hannu Amal tace "A'a Amal ina murna dawowar ki sosai.
Su Abba da ma6my suka fito motar su duka ido suka zubamusu, dan sun masifar dace da juna, daka gansu kason akwai shakuwa da soyayya mai girma a tsakanin su...
Ahankali Amnah ta zame daga gare shi ta nufi wajen Mamy tana tafiya A'hankali ta faÉ—a jikinta, kana ta juyo ga Abbah. Haka nan taji tanajin kunyar rungumar shi kamar yanda suka saba, da kyal ta É—an sunkuya ta gaida shi.
Da sauri yace" tashi Amnah basai kin duƙa ba muje ciki.
Ahankali ta mike tana tafiya tana cije baki...
Nene kam ta kasa motsi sai kallon Amnah take har saida Mamy tace muje ciki ko Hajiya Nene.
Kana Nene tace" to" ta rufe motar.
Sadeeq kam sosai yakejin kunyar su, haka nan yake musu sannu da dawowa kai a ƙasa.
Da sallama suka fara shiga gidan inda sukaga
Ammi zaune cikin shiga ta kamala fuskar ta cike da Annuri.
Da sallama suka shiga ta tashi ta É—akko musu tabarma babba ta shimfidamu su, Dan babu wuta kuma É—akin akwai zafi...
Su duka suka zauna aka shiga gaisawa...
Nene kam hankalinta naga Amnah ta naso tayi magan tanakuma jin nawin sirikinta...
Ammi tace" Nene ina fatan jikan naki yaje miki sallama yau zaije Abuja? ...
Nene tace "ya za'ayi yaje Maryama baccin naga yana ta tarbo Amnah, kila cinyoyinta ke ciwo ko.
Hala sune suka hanaka zuwa ko kwandon sukari na sani....
Ƙasa yayi da kan shi yana doka Murmushi.
Duk kansu babu wanda ya fahimci zancen ta ,sai shi da Amnah.
Wayar shi ta shiga ring da sauri ya tashi ya tura É—akin da yake ya shiga ya rufe.
Yana gama wayar ya dauki ledar da ogan shi ya bashi ya zazzage.
Sabbin kaya ne na Kakin soja.
Kallon kayan yayi sosai tare da rungumesu ya fashe da kuka sosai yana faÉ—in "Allah sarki Abba nahhhhh.
Saida ya gaji dan ƙanshi kana ya sanya su jikin shi,
Ya dakko bindiga ƙarama ya soka ga aljihunshi na gaba, ba tare daya sanya hular ba ya isa ga madubi.
.
Masha Allah ya furta shi da kanshi, Dan ganin yanda kayan suka masifar yi mishi kyau, suka fiddo da kwarjinin sa suka haska farar fatar shi.
Tattausan sajen shi ya shafa yana sakin murmushi , tinowa da daransu na jiya.
"A'hankali yace" ka ɓarani, ka samun barkono,Ashema babu daɗi sai masifar zafiiiiii....
Idon shi dake lumshe ya bude ya zubasu ga madubi,inda yaga lokaci guda har sun canza launi.
Da sauri ya fesa turare kana ya fito ..
Kamin kowa ya mike Nene ta mike tana zuba salati ta shige kiching ɗin su tare da maida ƙofar ta rufe, jikinta na ɗaukar rawa....
Amnah kam tsaye ta mike ta zubamai ido, yayin da shima ita yake kallo cikin so da ƙauna ya ware mata hannayen shi.
Cikin sassarfa ta isa gareshi ta faÉ—a cikin jikinshi tare da sakin kuka.
A'Hankali yake murza bayanta yana ambata sorry ,sorry my life ,am so sorry kinji Sweety...
Mamy, Amal, Abbah, ga baki É—aya tsaye suka mike suna kallon shi cikin tsananin mamaki.
Ammi kam sai cewa take masha Allahu. Alhamdulillah! Alhamdulillah!!!....
Daga cikin kiching suka farajin wani irin bugu kamar ana fasa bango.
Da Sauri Sadeeq ya zaunar da Amnah cikin natsuwa, kana cikin sauri yayi wajen yace" Nainah ki fito mana nine fa...
Kuka tasaki tace" wallahi bazan fito ba, bango zan huda infita, ka cuceni, ashe kason kai ɗan Sanda ne kake zama dani, bayan kason ina tsoron ku, Wallahi Kwandon Sukari babu ni babu ku, kuma sai ka saki jikata. ta kara dan nama wajen turmi ita da tsiya dashi zatayi ƙofar da zata fita.
Da sauri ya leƙa ta window yaga sai zufa take zanan ta na gefe daga ita sai Ɗan kamfai..
Da sauri ya ja baya tare da banka kofar da kafa É—aya take ta buÉ—e .
Ihu Nene ta daka da sauri yayi wajen ta yana mai riko hannuta yace "Dan Allah Nainah ki natsu nine fa.
Ammi tazo ta kama hannuwanta tace" Nene ku zauna inbaku tarihin rayuwar mu ,a gulgije dan Sadeeq yanzu zai tafi gida.
Gabaki É—aya suka zauna suka zubamata ido.
Shikam Sadeeq gefe ya zauna yana jawo Amnah jikin shi ya rike hannuwata yana É—an murzawa kaÉ—an.
Ammi tace.
""Kamar yanda kuka sani ni sunana Maryam haifafiyar garin sudan ce,Acen nayi karatuna har nataka matsayin babba likita, Mun haɗu da mahaifin Sadeeq a ƙasar mu da yaje sarin kaya, daga nan shaƙuwa ta shiga tsakanin mu har iyaye suka shiga tsakani, daga nan aka bashi ni ya kawoni Gidan shi dake Abuja.
Su ukku ne agidan su,akwai Musbahu shine babba Æ´aÆ´an shi, Sai Sadeeq kana Jidda autar su.
Na iske Musbahu da sabuwar Amaryar sa mai suna Rabi'a...
Cikin ikon Allah muka fara zaman lafiya dasu kasancewar muduka gida daya muke harda iyayen su, sai dai kowanne da part in'sa, sai kaso zakaje inda wani yake.
Soyayya da ƙauna zalla ina ganin wajen mijina, kullum fatan shi in zayyi tafiya ya sani gaba muje duk inda zaya,Saboda ya hanani aiki,Yason ni ƙadai zan zauna,gashi babu dangi,Dama mahaifiyata ta rasu kuma ni ƙadai Allah ya basu.
Kimanin shekara ɗaya da Auran mu amma babu ciki babu alamun shi , Hasalima ko ɓatan wata bantaba yi ba.
Daga nan ne Mahaifiyar Sadeeq mai suna Hajiya Suwaiba na É—an fara ganin canjin fuska daga Gare ta.
Akwai wata tafiya daya shirya muna zuwa Dubai, yaje gaidata da daddare shine take cewa.
"Ta fara nunama sa in'zaya waje wurin aikin sa dole ne sai yatafi dani, kamar inya barni cikin su zasuman wani abu , Bayan ga matar É—an uwan shi nan shima ai yana tafiya ko sai shi na Mamajo mayen Juyar macen da bata haihuwa ..
Kai ya gilgizamata tare da bata hakuri akan bazai sake ba.
Asanyaye ya dawo da jikinsa part É—ina" yace mun tafiyar da zamuyi inyi hakuri in zauna yaje ya dawo..
Kuka nasa mai dan baitaɓamun haka ba ,
Anan yake faÉ—amun Umma su ce batajin daÉ—i, tana ganin kamar bai yarda dasu bane.
Bani da yanda zanyi haka na hakura inaji ina gani yayi tafiyar sa.
Alokacinne kuma matar dan uwanshi Musbahu dake da yaro dan kimanin wata hudu na fara ganin canji daga gareta , Saboda ko yaron ta nazo É—auka zata dauke abinta tana nunaman bazata bada ba, inyi zuciya in haihu amma na tsaya soyayya da miji.
Banacemata komi saboda ba tashin hankali nike so ba ..
Tafiyar nan da yayi saida naji dama Mahaifana kusa suke, inkoma garesu saboda zama nike cikin kunci da baƙin ciki ,som abinda basamun suka Fara mun, Duk inda naje Hantarata suke, har Umma su da batamun haka.
Alokacin ne kuma yayi daɗewar da bai taɓayi ba, Dan saida ya kwashe wata ukku kamin ya dawo.
Zo kaga murna da farin ciki ranar da ya zo gida.
Aranar ne kuma nasha mamaki, dan umma da matar Musbahu sukaita lallaɓani suna tarairaya tare da nuna mai kewarsa tasa duk na rame ko abinci banaci.
Murmushi yayi yana mai sunkuyar da kanshi dan Sadeeq akwai kunya.
Bayan mundawo party in mu Yake cemun" mike damuna ,in faÉ—amasa gaskiya ko akwai damuwa?.
Kai na gilgiza mai ina faÉ—in duk kewar sace.
Atakaice dai haka muka fara sabuwar rayuwa cikin jin daɗi, koda wane lokaci muna tare bai taɓaman zancen rashin haihuwa na na damun sa ba.
Kwatsam Allah maji rokon bawa ya bani ciki wanda bana laulayi, ni kaina banson da shi ba sai da yakai wata huÉ—u na fara jin motsi .
Alokacin ne na fad'amai mukaje Asibiti aka tabbatar mun da ciki ne da ni wata huÉ—u.
Zo kaga murna wajen mu, anan na nemi alfarma da kar kowa ya sani ina jin kunya.
Ya amince mun dan yanason abin da nike so.
Haka naita rayuwata da ciki na babu mai zuwa part É—ina nima bana fita sai da daddare in'zuba doguwar hijjob inje gaida Umma sa , Dan mahaifin shi ba mazauni bane...
Ciki na nada wata takwas naje gaida Umma.
Sadda na mike zan dawo naji ta kurma ihu da salati tana faÉ—in mi zata gani haka?.
Cikin jin kunya nayi saurin fitowa bansake komawa part din ta ba dan naji kunya sosai ....
Ashe takaici da bakin ciki suka cika zuciyar ta, wanda hakan yasa har jinya tayi.
Ciki na nada wata tara na haifo yarona santalele mai masifar kyau ,da yayi kyau na dana mahaifin shi , Dan som mahaifin shi baikama da yan uwanshi ,dan yafi su ke sosai yafi kala da buzaye ko fulani......
Ahaka muketa rayuwa da yaron mu mai shiga rai, wanda tinda na haifeshi na matsama mahaifinshi akan ya sa mai Sadeeq .
Yace shi Sadeeq, Baby shi Sadeeq, abun yayi yawa.
Nace aini naga ranar sadeeq ya samai ina so .
Haka kau ya samai ,anan ma saida umma ta tada hankalin sa ...
Bayan Shekara hudu Allah ya sake bani wani cikin, a nan na haifo ya mace mai kyau sosai kamar Dee.
Ranar suna aka samata Halimatu muna kiranta da Sady.
Haka na kammala Yarana biyu inata ji da su, Daga nan kuma haihuwar ta tsayamun cak, babu wanda ya damu Acikin mu ,tinda munhaÉ—a jinsu biyu da muke fatan Allah yasa musu Albarka...
A ɓangaran Umma kuwa bata kaunar yarana Som, tafison Ƙaseem da ƙanwar sa dake zanan goyo mai suna Bilkisu suna cemata Bily,....
Duk ranar da tsautsayi ya fidda Sadeeq ko Sady Tofa sai sunshigo da kuka, Dan Umma duka take musu bana wasa ba.
A haka muketa taƙarƙara rayuwar ,in mijina na nan munajin daɗi, in kai baya nan sai azaba, da wahala.
Sadeeq nada shekara goma mahaifin su Abban su ya rasu.
Munyi kukan rashin sa dan mutumin kirki ne.
Bayan Sadaka Bakwai da rasuwar sa Akazo zancen rabon gado .
"Tofa anan ake yinta.''
Bayan lauyoyin sa sun bada duk kan wani Ƙundun kaddarasa zasu fara bayani.
Umma ta fara magana cikin fushi tace" to ranar wanka ba a'boyen cibiya.
Mai haɗawa dai yanzu ta raba, Dan haka kai Sadeeq dama bani na haifeka ba ga yara na nan daga Musbahu sai Jidda, Dan haka maza tashi ka tattara tsummanka ka tafi neman yan uwa da abokan arziki , Dan nikam ko kaɗan banson waye kai ba, na dai raine ka ne dan daraja mijina, yanzu kuma baya nan sai ka tashi ka kama gaban ka, abar yan gida ƙaɗai suyi magana.....
Arazane ya tashi tsaye inda muma mu duka muka tashi muna kallonta, Dan munji maganar kamar saukar aradu.
Tace kwaraiko maza ka ficcemuna daga gida.
Dariya sosai Musbahu keyi yana nuna Sadeeq da yatsa yace" Wato anyi luf akwashi dukiya aƙara cikin wadda ake kwamushewa ko ,to ita kanta duk muna nan zamu kwace babu kai babu ita...
Hawaye Sadeeq ya fara yace" Umma to waye ni? kuma ina kuka samoni?..
Tace" A kano muka sameka, kana Tafiya tabbacin baccewa