Showing 90001 words to 93000 words out of 94971 words
Chapter 31 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt
da turo baki dan son faranta mishi tace "nidai gaskiya yunwa nikeji kuma ga goyo ina so kamun.
Yacei to muje kici abinci sai ingoyaki amma taya?
Tace "gashi ba, ta faÉ—a tana nuna kanshi.
Ido ya zaro tare da sakin dariya farin ciki gabaki daya ya sungumeta suka haura sama, cikin lokacin ta mantar dashi sunan sa sai gashi bayan shiÉ—ewar wani lokaci sun sakko suna ta sakin fara'a.
Rakiya tamai ya fita dai-dai lokacin da Amal ta shigo, bayan sungaisa ta wuto ciki Amnah kau saida taga ya fita kana ta dawo fuskarta cike da Annuri.
Sosai sukasha fira sai dare Amal ta tafi bayan suncikata da kayan azziki..
Bayan wata daya suna zaune akan gado sai ihu suke suna kwasar garaɓasa ,ihu kawai sadeeq keyi yayi'n da Amnah kena azaba, Dan iya galabaita tagaji ga katon ciki amma haka yake haƙarta baji ba gani.
Saida wayar shi ta shiga ring kana ya sarara mata ya mike yana haÉ—a hanya yashiga toilet , bayan ya tsarkake jikinshi ya fito fuskar shi som babu annuri ya fito asalin sojan shi.
Amnah da tayo wanka ɗakin shi ta shigo tana kallon shi, tayi ƙasa dakai tare da share hawayen ta dan bataso ya gani.
Wayar shi da aka sake kira ya É—auka afusace.
Abbas yace Yallabai munafanan airport kaikawai muke jira.
Tsaki yayi yana kashe wayar...
Amnah ta ƙaraso wajen shi da kyal ta ɗan tattaimakamai yasanya kayanshi, Dama jikka shi ta shirya mai ita, ta ɗakko ta tayi tsaye tana kallon shi..
Kallonta yayi yace "kema bakyaso Sweety amma kin tirsasa ,bayan inada sana'a da zata rikemu.
Wannan tafiyar ma ni bana da tabbacin dawowana ko akasin haka,amma bani da yanda zanyi tinda Nasa ba tafiya na tattare da kwarin gwiwarki..
rungumeshi tayi ta fara jeromai Addu'a tsari da kariya daga Allah Subhanahu wata'ala..
SundaÉ—e a haka kana sukayi sallama ta yomai rakiya yanata shafa cikin ta.
Abakin ƙofa sukaga Ammi sukayi mai bankwana yana dagama su hannu suna dagamai, har suka ficce idon shi fess akan Amnah daketa hawaye tana ɗagamai hannu...
Kamar kar yatafi amma ya daure suka fita cike da kewar ahlin shi.
Amnah kau na ganin ya fita ta rushe da kuka. Ammi ta kamota tafara aallashi akaron farko tajata suka nufi part É—in su Amnah anan suka zauna tashiga bata baki.
Suna a haka saiga Nene da Hamrat da Amal da katuwar jikka .
Nene tace'' a'a ikon rabbi.
Yar kwal uba kamar ba itace kecewa bataso ba, to miyasa kike kuka, dan baya nan kawai?ke kaji ɗiya, inya zauna Uban mi zakimai,m da wannan tuƙeƙen cikin naki kamar mai girmana zaki haiho..
Cikin kuka Amnah tace tubarkallah Bissimillah.
Hamrat kau da sauri ta isa wajen Amnah tana shafa cikinta tace" Aunty da gaske zaki haifo muna Baby ,To mai kama dake ko mai kama da Baby?.
Cikin murmushi ta share hawaye tace" insha Allah mai kama da Baby zamu haifo Baby'n Baby kinji?..
Kai Hamrat ta É—aga cikin gamsuwa da farin ciki.
Amal dake waya tana yar kwallah ta kalli suka haÉ—a ido da Amnah...
Harara Amnah ta sakarmata hakan yasa ta mike tayi ɗakin Amnah tana tama Abbas kuka shagwaɓa duk ta rikitashi.
Amnah ta shigo É—akin hannuta rike dana Hamrat ta zauna bakin gado.
Amal tamai bankwana ta kalle Amnah.
Amnah tace saboda baki da kunya saurayin ma zakima kuka, toni da mijina ya tafi nace mene?
Amal tace" Aunty bazaki gane ba, Abbas yayi arayuwa ,bashi da hayaniya som , Abinda yasani kuka bikin mu da suka aiko aka ƙara ɗagashi an'maidashi wata shida, sai bayan yadawo da wata daya kinga kuwa dole inyi kuka,Ina son Abbas bana fatan yaga wadda ta fini ya koma mata.
Zatai magana sukaji Nene na salati tana faÉ—in" Allah ya tona muku asiri munafukan Allah....?
6/1/22, 20:33 - Ummi Tandama😇: *Littafin🌹DAN DAKO🌹 na kudi ne biya ki karanta cikin Aminci. Biya 300kacal to 0006454115 Amina Dahiru jaiz bank,or MTN card to this number 09165832002. then send the evidence of payment via 07038423451* ğŸ¤ğŸ™ğŸ¤²
Alhamdulillah! Alhamdulillah!!
Yan uwana mata ina kuke ku malmatso ga wanni sirri da nike son baku, ita ya mace sai da kamshi, ina macen da take ganin izgili da wulakanci da ake cewa maza nada shi, hmmm yar uwa to inkin kasance a haka da alama akwai ayar tambaya akanki. Tambaya ta ta farko gareki da wane irin turare kike amfani a jikin ki ?,da wane irin turare kike turara gidan ki,shin dawane irin turare kike Zukunni, hmmm to matso kusa kiji yar uwata.
Shi kamshi Annabi muma ya faÉ—a abin sone,kuma Abune mai sanya natsuwa da girmama ma'aboci shi , Da Yawon son kusantar sa.
Duk kan wulakanci da izgilanci na maza akwai turaran da zai miki maganin sa da izinin Allah,ba boka ba malam,wanda zai karkato da hankalin mijinki akan ki ku samu fahimtar juna.
Ko kin son kamshi na dakusar da fitinar É—a namiji yar uwa? kigarzayo ki kwashi rabonki ga shaharariyar yar mai Dugurin nan mai suna UMSAD INCENSE ,Mace mai kishin mata da son Fiddo martaba mu.
Nayi Amfani da turaranta naji masifar daÉ—in da yasa nakasa barwa raina. Nace bari in yaÉ—amuku dan kowa ya mallaki nashi cikin farashi mai sauki.
Da fari bari in zayyano muku su kamar haka.👇
Maleek Al'oud
Royal kush
Cous-cous
Kajiji
Original sandal
Sandal flex
Sandal bange
VIP mix
Hawi
Al'oud
Kindikay
Danal banat
Darot
Habil
Gaf-Gaf
Sirrun nisaa'i
Sandal chips
Kwalacca
Humra black and body milk
Attractive humra.
Yar uwa zanmiki Dallah- Dallah.
Akwai turaran da zaki sanyama kayanki .
Misali! kisa kabasa kiturare kayanki .
Akwai humra da bazaki sataba sai zaki turaka.
Akwai turaran kaya ,na jiki, Dakuma na ɗaki. Akwai kwallaca sirri, amma bama badata gaskiya sai ga wanda baida kishiya , Dan muddum kina amfani da ita tofa gabaki dayan hankalin mijinki akanki zai dawo,Dan yana juyo da hankalin namiji akanki baki ɗaya ,zaki zama shalele Baby, Akwai sirrin nisaa'i. hmmm Dagajin sunan kason na dabanne,na baki sati ɗaya ki gwada ki gani Hajiya ta, tsugunno ake akai ga mai buƙata ya tunɓe mu ta wannan layin 08028827241 karku manta UMSAD INCENSE mune na ɗaya.
Muna aika kayan mu duk inda kuke.
Kamshin jiki martaba mutum....
6ï¸âƒ£3ï¸âƒ£&6ï¸âƒ£4ï¸âƒ£
The end.
Alhamdulillah Allah na gode maka daka bani aron rai da lafiya na kammala wannan littafi nawa mai taken ÆŠAN DAKO, kuskuran danayi Allah ya gafartaman,Naga so da kauna a masoyan littafin nan, bana da bakin magana gareku dan kun nunamun so da kauna, zallar kulawa da babu algus, kyautatawa da darattawa , Nagode- nagode over, ina yinku fans É—in DAN DAKO, dama duk kan wasu mabiyan sa, da masu sata duk inayinku kuma nagode sai munhaÉ—u Asabo mai zuwa nan kusa insha Allah mai suna ÆŠIYAR SHEKH, Hmm fans karkubari ayi baku ,farin cikin ku shine nawa, kaÉ—an daga cikin labarin É—iyar Shekh zaizo muku kasan page nan nagode....
-------""Amnah ta kalleta cikin mamaki tace mene mukai miki Nainah kike cemana haka.?
Nene ta sake tafa hannu tace "shegiya soyayya, harda sunan da mijin ta ke kirana dashi ta koya, to ai gani nayi kunzama yan iska kuna labarin Samari,.
Amnah tace "Nene iskancine ? bayan begen mijina nike , Wallahi nidama banbashi shawarar ya tafi ba tafada tana turo baki.
Dariya Nene tayi tace" ke taso yar jikanyata kinji ko, ga KwanÉ—on zagale cen namiki, nizan zauna dake in'kula dake harki haihu, kinga harda sabuwar reza nazo da ita dan Bansani ba kar tashin hankali rashin miji yasa ki haifi Biyar ni Bama bakwai ni ba.
Dariya Amnah tasa tace" Allah ya kiyaye Nene, Taranni na zan haifa insha Allah.
Dariya suka sanya suka sakko ƙasa,Anan suka iske Ammi ta shirya musu dinning.
Bayan sunci suka fara lallaɓa Amnah,Dan ko motsi tayi zasu tambayeta ya'ya?
Zatace bakomi agefe guda kuma kewar mijinta ne sosai a ranta.
Bayan wata ukku.
Rayuwa Amnah keyi mai daɗi da Ah'linta, da Maman Dee, dan dai akwai kewar mijinta sosai ga rashin waya da basayi sosai, dan aiki suke sosai ga Dajin da yake babu network, hakan yasa tinda yaje so ukku sukayi waya, sosai kuma hakan ya damu Amnah har rama tayi, dan ma su Nene na iyakar ƙoƙarin su wajen ganin sun inganta kulawarsu akanta ,da Baby'n ta, Dan har awo take zuwa itada Amal suje sudawo .
Lokacin da cikin ta yakai wata tara dole Amnah tabaka tausayi, Dan dukkan halittunta sun canza, ta fita hayyacinta ga kewar Miji kullum sai tayi kuka,ga zullimi haihuwa ,ga cikin yayi masifar girma hakan yasa wata rana Nene sai ta sata gaba ,ta buga tagumi tana kuka .
"tana faÉ—in nidai Allah yasa ki iya haihuwar wannan ciki, Kamar an'maki ciko da tankin ruwa , Amnah abun nan na bani tsoro Wallahi, kodai an'maji jifane ciki kar ace harda jinjirin jaki ciki kamar yanda naga Amma wata mata ,sai sufashe da kuka baki daya har sai Ammi ta shigo ta lallahe su kana su daina.
Wata safiyar talata suna waya da Sadeeq, sai murna take hakan yasa yacemata yana kan dutsi tayi maza ta nunamai Baby shi zaikoma bakin aiki, wasu ɓarayi ne suka kaima farmaki.
Cikin sauri ta mike tsaye ta yaye ƙaramar rigar dake jikinta tana gwadamai ,sai sakin murmushi yake yana fadin Saleem ga Daddy'n ka ,kamun Addu'a nasara kaji, ka daina bama Mommy wahala kaji ?
.
Amnah zatai magana taga wani ya lallaɓo ta Bayan sadeeq ya bugamai sanda.
Ihu ta kwallah cikin tsananin tashin hankali dai-dai da faÉ—uwar wayar tashi komi ya dauke sai duhu.
Kuka ta fashe dashi sosai tana faÉ—in. "Allahumma a'jirni fi masibati, wa ak'lifni khairan minha. Hazbunallahu wani imal wakil, la'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu mina zalimin.
Ya rabbi ,ya hayyu, ya ƙayyum,kar kaba magauta damar sukar Mijina, ya Allah kaji tausayina, kaji tausayin abinda yake fatan gani dare da rana, Ya Allah! ta fashe da kuka tare da kasa ƙarasawa lokaci guda kuma cikinta yayi wani mugun murɗawa.
Hannu ta yarfe tana mai ƙoƙarin sakkowa daga kan gadon ,ta cike baki ta sakko ƙasa tana salati, tare da ƙoƙarin jawo wayar ta dake kan mirrow amma ta kasa.
Sosai takejin cikinta na yamutsawa, ƙugunta,da bayanta sun wani irin rike sai neman cirewa suke.
Koda batason haihuwa ba ta tabbata haihuwa zatai Tinda ta karanta, Hakan yasa ta fara kwalama Nene kira. Amma da yake cikin Muryar galabaita ne babu wanda yajita, dan zaune suke palo taga kiran Sadeeq ta haura sama, har Nene nacemata kilbabba tace bata iya tashi amma da miji ya kira ta mike...
Kimanin awa É—aya Amnah na wajen tin tanajin dai-dai har ta fara fita hayyacinta. Hankalinta in'yayi dubu tashe yake, ta tabbata itama mutuwa zatai, gashi bata son makomar halin da mijinta yake ba.
Cikin kuka tace" Allah ka fitar mun dashi da karfi tanajin wani abu na turomata, Hakan yasa da sauri ta Dauki bargo ta shimfaÉ—a ta haye sama, tafara sakin dogon nishi dakesa taji kamar ranta zai fita.
Ciki ikon Allah tana sake wani nishi taji Kan yaro, hakan yasa cikin jarumta ta sake dafe gadon ta tafara sakin nishi da masifar ƙarfi tana rintse ido.
Gabaki daya yaron ya faÉ—o bisa bedsheet yana Yan-yara kuka .
Ajiyar zuciya ta sauke cikin Tsananin galabaita, tare da fara yunkurin tashin dan É—akko akwatin gaggawa, amma ta kasa jin wani masifaffan ciwo ya sake tunkarota, tare da dannowar wani Baby gabaki É—aya.
Ido ta zaro tana sakin kuka tare da yarfe hannu tace "Shikenan Nene, mutuwa zanyi kun kyaleni ,na shiga ukku, zan haifo yan cikina ta karasa tana yarfe hannu tare da sakin nishi, sai ga Baby ta fado tana canyara ihu mai masifar ƙara, da alama akwai zajin murya..
Ajiyar zuciya ta sauke ganin uwa ta biya, hakan yasa ta dora kanta akan gado tana sauke ajiyar zuciya ,tare da bin yaran da kallo cikin tsananin galabaita...
Kamar wasa Nene tazo daukar abinci ta kaima Amnah taga taki sakkowa sama da awa biyu taji kamar kukan jariri.
Shuru tayi tana sake saurarawa.
Tabbas kunnanta ba gizo yake mata ba ,hakan yasa cikin sauri ta ajiye abincin ta ruga da gudu É—akin Amnah, gabanta na faduwa ta tura ta shiga.
Wayam taga palon, da sauri ta tura bedroom É—inta inda sautin yafi fitowa.
Anan taga Amnah duke ƙasa ta ɗora kanta akan gado, sai lumshe ido take ga yara zube bisa bargo.
Ihu Nene ta saki tare da fashewa da kuka aguje tayi ɗakinta ta ɗakko sabuwar reza tana share hawaye, tazo ta rungume yaran ta yanke cibinsu tare da shimfiɗasu bisa gado,Da kyal ta miƙar da Amnah suka nufi toilet.
Suna shiga ta zaunar da ita a kan sit ta fito da gudu tayi part din Ammi.
Ko sallama batayi ba cike da ruɗani take faɗin zaman mu yazama na banza ,munzama ƙattin wofi ,,bamu rike Amanar kwandon sukari ba wallahi, Maryam fito kiga ..
Aguje Ammi da Amal da Hamrat suka biyota hankali tashe suka haura sama,Tare da tura É—akin Amnah.
Anan sukaga yara biyu sai tsotsar hannuwa suke...
Gaban ammi ya fadi tace" Nene minike gani haka, ina diyar tawa?.
Hararata Nene tayi tace" bansani ba, Bayan tagama duk kan ƙoƙarin ta kana mukazo , Wallahi Amina jarumace, Ita kaɗai ta haifo yaranta biyu sak, ga sunan ki kula dasu in'kinga dama bari inje wajenta toilet..
Cikin tsananin farin ciki da godiyar Allah Ammi ta karasa wajen, kyakyawawan yaran da idonsu yake abuÉ—e sai kokarin tura hannu suke cikin baki ta zubama ido ,Tana ganin tsananin kamarsu da iyayen nasu..
Gabaki É—aya ta haÉ—esu ta rungume ta saki kukan farin ciki, tana godiya ga Allah, Amal da Hamrat kau sai ihu suke suna farin ciki Sunyi Ya'ya.
Ammi ta bada umarni wa Amal a haÉ—omata ruwan zafi toilet din Sadeeq.
.
Dan Danan ta kawomata ta wankesu tas aka naÉ—esu cikin towel É—in su mai tsananin taushi...
Nene kam bayan ta shiga toilet ta iske Amnah zaune sai kuka take, kamar ranta zai fita.
Itama kukan tasa tace'' wallahi Amina bansani ba ,kiyi hakuri kinji tawajena, banson haihuwa zakiyi ba, naga yanzuma watan naki yakama, baifi kwana ukku ba,Nason sai kince dan naga ubanki gero yake saidawa to bahaka bane banjiba kinji...
Amnah tace'' Nene Yah Sadeeq, akwai abinda ya faru dashi ,muna tsaka da waya naga wani ta bayanshi ya daga sanda ya zubamai ,daga nan wayar shi ta faÉ—i, kinji silar haihuwa ma Nene, Wallahi wani abu ya faru bazan yafewa kaina ba, saboda harda son ya farantamun yasa yace muyi Vidio call, gashi na dauke hankalinshi har wani ya cutamun shi.
Salati Nene tai ta saki tana tafa hannu,, sosai Hantar cikinta ta kaÉ—a, amma ta lallasheta tare da faÉ—in ta tayashi da addu'a insha Allah yana lafiya, Allah zai É—orashi akan su...
Shuru tayi har Nene ta gyaramata jikinta tass kana suka fito .
Inda taga su Ammi taita jeramata sannu cikin tsananin so da kulawa.
Suna palo zaune saiga Mamy da Hajiya Turai,m sunyi sallama sun shigo, fuskar su cike da farin ciki.
Anan suka gaggaisa Hajiya Turai taja Amnah wani É—aki, nan ta umarceta da ta tsaya ta dubata.
Bayan ta dubata ta fahimci dole a mata É—inki, dan ta Karu Sosai.
Haka ta fiddo kayan aikin ta dan dama Asibiti take Mamy ta mata waya shiyasa ta haÉ—o komi Tinda ta gida ce...
Anan ta ÆŠinke Amnah tass ,kana ta kamo hannuta suka fito tana tafiya A'hankali, dan ita bama murna haihuwar take ba lafiyan mijinta take neman taji.
Tana zama tace'' Amal kirawoman Abbas,kiji ya suke.
Da sauri kam ta É—aga wayar ta, anan tayi Sa'a tashiga, dan itama ba kullum suke wayar ba.
Bayan ya É—auka taji muryarshi ba cikin walwalaba, hakan yasa tace" Honey lafiya?..
Yace ki tashi daga cikin mutane muyi magana.
Tashi tayi tana kallon Amnah da ta bita da ido cike da hawaye,
Amal na shiga tace" inajinka lafiya dai ko? ina Yah Dee?
Abbas Yace" Amnah mutayashi da Addu'a Dan ita yafi buƙata,, ɗaya daga cikin yan ta'adda ne ya bugamai sanda agefen wuya , Amma yayi nasara kasheshi ta hanyar halbi,yanzu haka muna babba Asibitin cikin garin munkawoshi, Dan baya mikar da wuyan Sosai..
Salati tasa tana sakin kuka tace" kar dai kacemun ya samu naƙasu?.
Yace'' A'a Amal insha Allah bama fata, buguwace kawai, ai'munmayi nasara insha Allah bazamu jima ba zamu dawo .
Hawayenta ta share tace'' to yanzu..
Da sauri yace yawwa likitocin sunfi to ina zuwa ya kashe wayar.
Zama tayi É—akin cikin zullimin abinda zatacema yar uwar Tata..
A palo kau Nene ta shiga kiching ta haɗoma amnah Tea mai kauri tabata Amma tace A'a ta ƙoshi.
Nene tace'' wai miyasa kike haka?
Kuka tasa tace Nene" bansan ya yake'ba, kuma Amal ta tashi daga kusa dani, Dan Allah kice tazo ta fadamun halin da ake ciki, Wallahi inaji ajikina Baby na cikin matsala..
Anan duk yan palon suka fahimci akwai damuwa, bayan Mamy ta tambayi ba'asi Amnah ta faÉ—amusu, Hankalin kowa ya tashi sukayi jugum- jugum..
Nene tayi ƙarfin hali ta kwalama Amal kira.
Bayan ta fito suka zubamata ido.
Ƙasa tayi da kanta tana share hawaye.
Jikin Amnah ya É—auki rawa tace "sun kasheman shi ko? dama ya faÉ—aman ta tafi luuu zata fadi , Ammi ta tare ta tana share hawaye tace muyi Addu'a kinji.
Taƙarasa cikin dauriya dan ita kaɗai tason yataji....
Amal tace Aunty" bai mutu ba ,sundai bugamai sanda agefen wuya, sunje Asibiti Abbas yaban tabbacin kwana kusa zasu dawo ,saboda aikin ma ya kare tinda duk sun kashe wayan da ake zargi, da kuma wa'yanda keda sanya hannu a ciki..
Nene tace to sake kiramana Abashen kiji mana.
Amnah ta sake kira ya É—auka cikin farin ciki yace "Dear Alhamdulillah Abinda muke tinanin zai faru bai faruba , Buguwace kawai yayi, yanzu haka sun'samai abu a'wuyan sunbashi magani, kai tsayema gida zamu wuto insha Allah, zuwa dare ko yamma muna tare daku.
Ihu ta saki cikin jin daÉ—i hakan yasa ta datse kiran tana faÉ—amusu, take palon ya rikice da murna saiga Annabin na fadin Nene kubani Tea da abinda na haifa...
Dariya suka sanya su duka .
Suka bata su ta shiga kallonsu, kyawawa ne ajin farko,masu tsananin kama da juna ,sunbiyo ta, sunbiyo Baban su sosai, take taji ƙaunar su na ratsa bargo da jijiyar ta.
Nene ta kawo Tea da felfesu sai kamshi yake ta zaunar da Amnah ta bata taci sosai ,kana tace su tashi su tafi sukwanta ta huta.
Anan Amnah ta tashi Amal ta biyo ta da yaran,suna shiga ta iske ɗakinta tass sai masifaffan kamshin turaran wutar UMSAD INCENSE yake, duk kan wani ƙarni haihuwa ya dakushe shi, ga lafiyayyan zanan gado mai taushi.
Amal tace''" Aunty kibasu Mama sufara sha saiki kwantar dasu, sai kema kisamu bacci ko?.
Cikin gamsuwa ta É—aga kai tare da