Showing 15001 words to 18000 words out of 94971 words

Chapter 6 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt

Advertisement

09 Feb 2025

17268

amm yakasa zuwa ya bani Hakuri.


Kuka Nene ta fashe dashi na takaici tare da tashi ta haye sama tana faÉ—in" na zauna wajen wannan yarin ya wallahi zuciyana bugawa zatai inma fulani na asara.


Amal tace Gaskiya " Aunty Amnah bakya kyutawa,ƙo fa babu komi ya girmeki kana ba ayiwa Allah haka, kedai ki nemi zaɓin Allah.


Shutt up kika sakemin magana zan wankamiki mari tsarar kice ni? tashi kiban waje.


Cikin ɓacin rai Amal ta tashi tayi ɗakin su dake nan gidan Nene tayi kwanciyar ta tana tinanin sadeeq , ita tarasa dalili tin jiya yaki barin zuciyar ta, koda wane lokaci tinani wani abun nashi take, yakan sata ɓata fuska ko tayi murmushi, A'hankali tace
Ga aji, ga kyau ,ga ƙasaita, ga rashin son Raini ,wallahi yah sadeeq kayi Allah yabani Mai irin halinka.


Jin ƙarar buɗe get ya sata tashi da sauri ta fito palo tare da leƙa wa anan ta hango shi ya danno hancin mota ya shigo.


ÆŠan Larai namai magana saikuma yaga al'majiran nan suntaso sunfara kwasar kayan da sauri.


Gefe ya koma ya naÉ—e hannuwa yana lumshe ido dan dama bayajin daÉ—i som.


Da sauri Amal ta nufi dakin Nene ta iske ta fito wanka .


Nan ta faÉ—amata ya dawo.


Da suri Nene ta canza kaya tace muje suka fito Tare.


Suna fitowa Nene ta kamo hannunshi tace" muje ciki Sadiq ka huta,yanaji hannunka da zafi ko baka lafiy ne.?


Kai ya gilgizamata tare da faÉ—in" Nainah lfyna fa kawai dai.


Kawai mi ? Nene tace.


Kai ya sosa yace muje inga É—akin naki ta yanda zansanu saukin kwasheki da daddare.


Dariya tayi tace haba dai yaro mukwashe juna dai ni ai da dare yayi nikeyin layar ɓata in bacce ɓat..


Kallonta yayi yasaki Murmushi har suk isa ciki.


Suna shiga ta nuna mai saitin kujera da Amnah take anan ya zauna danshi baima lura da ita ba kamar yanda batason sunshigoba hanklinta na ga abunda take kallo.


Fira Nene kemai yana É—an amsawa sama- sama daga baya yace mata zai koma .


Tace amma zaka dinga zuwa nan ko.


Yace" Azumi fa za afara, na daizo karɓa barka da sallah na.


Nene tace shikenan Allah ya nunamuna.


Ameen yace yana mikewa da sassar fa yayo hanyar fita, cikin akasi Amanah ta mike tsaye da sauri duk tinaninta Nene ce ke son leƙo ta.


Bam kakeji ta faÉ—a cikin kirjinshi.


Lumshe ido tayi jin wani irin sassanyan kamshin daya mamaye hancinta, kwakumeshi tasakeyi kasancewar cikin yanayi take wanda ita kanta batason miyakawo mata hakan ba.


Wata irin faÉ—uwar gaba ta kawomai ziyara jin yadda ta af'komai bisa kirji, kuma saitin zuciyan shi dakemai ciwo.


A fusace ya fisge ta tare da dannata bisa kujera yasaki tsaki ya wuce.


Ido ta É—ago cikin wani irin tashin hankali dajin tsanar kanta ta kalli bayan shi, Dan ko alama batason shibane, to taya tazo jikin shi? innalilli yanzu shikenan ya sake rainata.


Jikinta ta kallah tare da sinsunawa taji yssbon kamshin ma take akan nata, Amma dan sharri fuska ta yamutsa tare da faɗin ta yama zakaƙi hamami da wari kana aikin Dako , Dole in'sake wanka .


Nene ta kallah da Amal wand som hanklin su naga kallon da suke basu lura da abinda ya faru ba.


Da sauri ta mike ta shige toilet tayo wanka ta fito.


Koda ta fito ta shirya kanta tare da faÉ—awa kan gado ta fara tinanin abunda ya faru ,tsaki kawai take jerawa wani bayan wani.


Abangaran Sadeeq kuwa yana fita ya fara kakkaɓe jikinshi yana yatsina fuska, tare da faɗin ƙazama shashasha, marar kirki, wadda batason daraja mutane ba ,kawai kinfamamun ciwo hakanan kawai Makauniya.




Gidan Mamy ya koma ya faÉ—amata duk an'kammala !


Taita samai albarka tare da gashi wani sabon key na machine tace'' gashi kaima ka dinga hawa ka huta da zirga -zirga zuwa da komawa, kana akwai buhu shinkafa ,masara, gero, dawa ,alkama, sugar, taliya ,macaroni, indomie, ka kaima Ammin ka .




Kace ga kayan Azuminan ina gaidata, amma kyanshi ka fara kaisu a'mota suna store kason bazasu É—akku a machine ba .


Tsororo yayi yana kallonta cikin wani yanayi yace" Hajiya kintina kuÉ—in da kika bani jiya ,ga nama, wallahi kibar abinki nagode Allah ya saka da Alkhairi..


Mamy tace" sadeeq bakayi islamiya bane.?


Ido ya zaro tare da cewa nayi Hajiya mikika gani.?


"Tace to minene ribar abaka sadaka kace bakaso, ko rainawa kayi ne Sadeeq ?banaso daga yau in nabaka abu kanunamun yayi yawa ko kuma kuna dasu.


Yanzu in'ka kai mata wannan ai na tabbqta tana da yan uwa da makwafta da abokan arziki ko? ta ai'zata rabamasu kuma duk tarayya zamuyi cikin lada, dan haka ka kwashe kawai duk rabon azumine kuma kason Allah naso ka kyautatama mabukata a cikin azumi ta hanyar ciyar wa, kana ni ina jinka ajikina wallahi ba ɗauka ɗan aiki nikema ba,Aa jinka nake kamar jinina,ina jinka kamar babban ɗana wanda na haifa, ka ɗauka Allah ne ya haɗamu dan mu ƙaru da juna, wannn bakomi bane zaka iya tafiya.ta faɗa tana faɗawa ɗaki ta bashshi sake da baki.


Fitowa yayi jiki babu lakka ya ƙarasa store din da tace ya kwashe kayan, Anan yaga hadda jarkar Mai.




Kwashe su yayi ya tura a'mota tare da fita yayi gidan su yana tinanin maizaicema ammiyn shi dan abun ya fara bashi tsoro.


Yana isa gidan ya sakko daga motar anan ya fara.kwasar kayan ya saukesu tare da kammalasu soron gidan lana ya rufe motar ya fita
Kofar y atura da sallama yafara kai kayan .


Ammi ta fito tana faÉ—in ikon Allah sadeeq lafiya'n ka kuwa? wayannn kayan fa, bayan wayanda ka kawomana jiya?.


Saida ya kammala kana ya zauna ya koramata bayani tare fa faÉ—in" nifa Ammi banaje gidan su dan aita kashemun kuÉ—i ba ,,aa subani iya hakkina ya isa abun fa y isheni.


Murmushi Ammi tayi tace karka manta kila zakka Azumice, kaga kenan muma Allah yaci damu, dan haka muma bazamuci mu cinyeba zamu kyautatama wanda suke cikin yanayi, duk da bama shiga harkar kowa unguwar nan kuma babu mai shiga tamu, hasalima tsoronmu ake to amma zamu kyautata iya iyawar mu da yarda Allah.


Kai ya jinjina tare da faÉ—in in Baby?


Tace tana ciki ka sonta da bacci tinda mukai sallah ƙarfe ɗaya take bacci.


Yace shikenan tare da zaro wayar shi yace" bari in'kirata kimata godiya ko.


Ammi tace eh kirata kuwa kayi hangen nesa.


Mamy ya dan nama kira cikin lokaci ta É—auka.


Cikin natsuwa yace" Ammina zata miki godiya.


To Mamy tace tana sakin Murmushi.


Karba Mamy tayi suka gaisa a'mutunce a inda taita godiy da Addu'a buÉ—in Alkhairi.


Mamy taji daÉ—i ta amsa da ganan sukai sallama.


Abinci Ammi tamai tayi yace" yaci gidan Nene anan yabata labarin Tsohowa taita dariya itama tare da faÉ—in ai tsaffi akwai daÉ—in zama.


Gab da la'asar yace mata zaije masallaci daganan zai wuce, misuke buƙata na sahur dan ana sanya ran ɗaukar azumi yau.


Tace babu komi sai dai ko fura inzai dawo.


To" yace tare da fita.


Gab da sallah mangariba suna fira da baba madu su Amal suka dawo.


Anan take shedamusu da anga wata saudiyya.


Ido y lumshe tare da faÉ—in Allah yabamu ikon kyautata halshen mu da zukatan mu.


Ameen ta amsa ta wuce...


Bayan sun dawo isha yama Mamy sallah ma ya wuce.


Sai da ya tsaya ya saima Ammi fura mai kyau da yoghurt yayi ma Hamrat tsaraba kan ya kom gida da sabon machine É—insa.


Yana isa gida anan ya shiga da abin shi.


Da gudu Hamrat ta taso tayo wajen shi tana "oyoyo ga Baby yayi sabon machine zai kaini yawo'n sallah.


Da sauri ya gyara parking kana ya kama hannunta suka ƙarasa wajen ƙofa yana"oyoyo Baby acici harta ƙagara sallah tazo, to mikika tanadar mata?..


Tsalle tayi tace "Baby ice cream ,kadaiga wannan karan kana da machine bazaka ki ƙaini ba ko?


Rufe gidan yayi kana ya kamota suka dawo har gaban Ammi bayan sungaisa ya shedamata anga wata.


Addua tayi tare da fatan farawa cikin sa'a.


Hamrat tace baby baka bani amsaba?.


Murmushi yayi yace" insha Allah baby'n baby zamuje duk inda kike so, saboda banda wanda yafiki kedai kishirya kawai Allah ya nuna muna wannan lokacin.


Ameen ta amsa tana karba abinda yabata da godiya..


Da wuri suka rabu inda ya koma É—akinshi ya fara bincike a sistem É—insa saida ya daÉ—e kana ya kwanta.


3:30 ya tashi yafara nafilfulu har sai karfe 4:30 kan yayi sahur da tea da Ammi ta bashi, yana gamawa yayi raka'atul fijr kana ya wuce masallaci,bayan yayi sallah yayi azkar yayi karatu sai bakwai da rabi ya doso gida.


Cikin sauri ya shirya kanshi cikin wasu kaya dogon wando brown da yellow riga sunmishu masifar kyau.


Sallama yama Ammi tace mai da yamma ya dawo ya kai abincin masallaci lokacin ta kammala.


Yace insha Allah ya fita.


Bayan yaje gidan Mamy sun gaisa ta bashi ya karɓo musu kaji da yan ciki yana dawowa" tace shikenan zai iya zuwa ya kwanta.


Carfet ya ɗauka yatafi lambu ƙason bishiyar Mango ya kwanta ,sai azahar ya tashi.


Sallah yayi sai masallaci, bai fitoba sai biyar na yamma dan karatu ya yini yi.


Bayan ya fito ya É—auki mashin sai gidan su, anan ya iske Ammi ta cika manyan kuloli da waina da ruwa mai sanyi sosai.


DaÉ—i yaji ya kwasa ya kai masallaci biyu ya dawo, ta Zubamai kayan buÉ—a baki ya É—auka ya tafi.


Yana isa Amal na zuwa da kaya masu yawa ta bashi.


badan kar taga kamar wani Abuba ya karba Yamata godiya.


Ana kiran Sallah yaci Dabino da kankana ya tashi yatafi masallaci.


Bayan ya dawo sukayi buÉ—a baki awadace, ana sallah ya tafi masallaci sai tara na dare ya dosyi gidan su.


Haka sukaita rayuwa yayin da Azumi keta tsula gudu dan har yakai goma sha biyar suna ta rayuwa mai daÉ—i.


Aranar da aka É—auki na sha shidda yana zuwa Mamy ta shedamai zai kai su Amal kasuwa.


"Yace shikenan.


Bayan sun fito Amal ta shiga gaba Amnah ta zauna a baya.


Suna ɗaukar hanya Amnah ta fara sakin tsaki mai ƙarfi.


Amal tace mike damunki Aunty amnah?


Hancinta ta toshe da yatsunta tare da fiffita da gudan hannu tace" Amal bakyajin wani masifataccen wari da ƙarni kamar na jaɓa.?


Nifa bazan juri yawo da Gardiba wallahi saboda yana cutata,haka kawai n
Mamu ta HaÉ—amu da, masifa ,ni bazan jureba yazama dole Abba in yadawo a sallami wannan gardin ,yayi ale-ale cikin mota kamar ta tsohon sa.....




Wani wawan burki yaja daya tada hankalin mutane dake kan titin dana su Amnah.


Afusace tace kai talakka motar Uban nawa ka keso kamun asara? Harda neman bugama wani wawa gwame kawai babu abinda ka iya sai warin talauci.


Kanshi y dafe da masifar karfi yace Amalllll fi...t..ttah ya faÉ—a cikin ihu da in ina.


Hankali tashe tace ina zani Yah dadeeq.


Tsawa ya Sakar mata mai mugun tada hankali batason sadda ta buÉ—e ta ficce ba da sauri.


Belt ya sanya tare da tada motar da wni mahaukacin gudu.


Salati mutanan wajen suk saki ganin yanda motar ta wu....âœï¸
5/18/22, 09:34 - MY MTN 2: ƊAN DAKO 🌹


🌹MALLAKI

UMMY AYSHA 🌹

🅿ï¸1ï¸âƒ£3ï¸âƒ£&1ï¸âƒ£4ï¸âƒ£


""Salati Mutanan wajen sukai ta saki ganin yanda motar ta wullah saman titi har wani tsalle take saboda azabar gudu.


Wasu na faÉ—in É—an shaye- shaye ne wasu na faÉ—in Azumi ake kila motar ke janshi ,kowa da abinda yake faÉ—a dai.


Amal kam hannu ta É—ora akai ta saki wani siririn kuka.


To mizaima yar uwar ta?kodai da gaskiyar Nene Amnah akeso ya sace? innalillahi wa inna ilaihi Raji'un.


Ya zatace da Mamy? miyasa bai tattarasu suka tafi baki ɗaya ba?Ta yarda da magana Nene abinda babba ya hango yaro bazai taɓa hango sa ba.


Abangaran sadeeq kam wani mahaukacin gudu yake ido rufe , Da kuma hannu ɗaya, ga baki ɗayan idanuwan shi sun'mai duhu, har Yaji- Yaji, kwallah- kwallah yakeji masu tsananin Zafi a cikin idon sa, ga kanshi ga baki ɗaya saramai yake, fatan shi ya buɗe baki yayi magana amma yason in ina dake kawomai ziyara duk sadda yake cikin ɓacin rai bazata barshi ba .


Afusace ya tura hannunshi cikin yalwatacciyar sumar shi ya dinga bazata kota ina.


Amnah ga baki É—aya jikinta rawa yake ganin har sun fita daga garin Katsina sun naushi hanyar Dutsama.


Cikin Daure tsoron ta tace" kai ina zaka dani baka da hankaline.?


Kamar jira yake ya ƙarama motar gudu jikake fiiit -fiit yana wuce yan tsurarun motoci'n dake tafiya da dawowa.


Saida ya nausa da ita wani É—an daji mai yawan duwatsu kama yayi parking.


Afusace yafito ya buɗe inda take tare da buɗe idon shi dakyal ya watsasu bisa fuskar ta data zubami ido, A karo na farko kenan da suka tsaya sukaima juna kallon ƙurullah.


Abangaran Amnah kallon mamaki takemai dama haka yake.?


Shikuwa zallar tsanace afuskar shi tare da tinano irin fansar da zai É—auka akan iskancin da take mai harda zagin mahaifinshi dake kwance cikin kasa.


Cikin ihu da in ina yace" Fii..t.toooo.


Gabaki É—ayan jikinta ya saki jajayen idanuwanta ta É—ago ta yarfamai tare da faÉ—in" ina zaka kaini.?


Gi..dan uban..kiii...
Ya bata amsa a wahalce.




Ido ta zaro tare da fitowa tace'' kai ni kake zag...


Kanta ƙarasa ya bata wasu kyawawan maruka guda ukku wanda ya sata tintsurawa cikin wasu manyan Duwatsu.


Cikin wata tafiya ta Namiji duniya ya ƙarasa wajenta tare dasa ƙafarshi ya take yatsun hannunta da masifar ƙarfi ,wanda yasata sakin ihu da karfi tare da kallon shi da sauri..


"Bani da ra'ayin zalintar kowa, bakuma niso azalinceni, yau in namiji ne ɗan uwana yamun abunda kikamun Wallahi Wallahi ina mai shedamiki saina ɓatamai fuska ,ta yanda uwar da ta haifeshi bazata gane shi ba.


Kirike azziƙin ƙi da iskancin ki.


Nima kuma kikayale ni, in rike talaucina da mutuncin kaina.


Amma in kinƙiya ko gaban uwar kine zan casaki kamar gero, wawiya daƙiƙiya.


Wallahi billahi daga rana mai kamar ta yau kika sake zagina ko kuma ki kira mahaifina da baya raye saina ɓatar dake a faɗin duniya, daƙiƙiya jahila,tinda kika zama mai wannan halin ni ina da tantama akan asalinki wallahi.


Duk wanda yayo gadon Azziki baya iskanci da tinkaho, saboda abin a jininsa yake.


Dan haka kije kiyo binciken Asalinki karshenta ke agolace agidan da kike takama na ubanki ne, dan ita yar uwarki ina tinanin itace yar gidan da yake ita gadon azziki tayi ba haye ba gashinan ta rike mutuncinta tason daraja mutane.


Tashi muje jaka kawai. yadaka mata tsawa.


Gabaki ɗaya'n doguwar magana da yayi cikin in ina yake yinta wadda ta kara shagalar da ita wajen kallon pink lips dinshi dake motsi ahankali ga idon shi da suka canza kala kamar wanda ke tsaka da buƙatuwa.


Bata fara fahimtar miyake faÉ—a ba har saida taji ya fara Ai banta asalinta kana tafarajin faduwar gaba da wasu kwallah masu tsananin zafi.


Akaro na farko ta nuna kanta jikinta na rawa tace "ƊAN DAKO nikakema sharri? Nizaka aibantama Asali? Wallahi wannan magana Taka sai kayi dana sani? Court zata rabani dakai koda abinda na mallaka zai ƙare.


Tsaki yayi ya juya yayi gaba abinshi cikin ƙunar zuciya da bacin rai. tabbas yau sai ya ajiye aiki agidan su bazai jure ƙarama yarinya namai wulaƙanci ba.


Ganin yayi nisa yasata tashi duk jikinta ya lalace da ƙasa ga hannunta har yayi fushi.


Dakyal ta taso ta gangaro ta faÉ—a motar da kyal , Duk tsorace take dashi ga faÉ—uwar gaban da takeji in ta tino furucin shi.


Gudu da yake yafi wanda yazo dashi gaba É—aya hankalinta atashe yake, tana ganin tayi bankwana da gidan su kawai.


Cikin mintina ƙalilin ya isa inda ya sauke Amal, anan ya isketa zaune tayi zaman Dirshan tana ta kuka .


Som ta kasa kiran Mamy batason wane yanayi zata shigaba, gata da hawan jini.


Tana ganin mota ta tsaya gabanta da sauri ta tashi ta faÉ—a baya tare da tallabo Amnah tace.


"Aunty minene ya miki, ina yakaiku, dukanki yayi? Takarasa cikin kuka.


Kai Amnah ta gilgizamata tare da maida kanta cen gefe ta fara nazari Magan-ganu shi.


Hanyar kasuwa yayi Amal tace kabar ayhi ka maidamu gida.


Tsaki ya saki tare da juyawa ya doshi unguwar su.


Yana shiga ya buÉ—e motar ya fita tare da isa kofar palon Mamy cikin sassarfa.


Wayar shi ya É—auka ya kirata .


É—auka tayi cikin faÉ—uwar gaba tare da fadin sadeeq lafiya?


Alhamdulillah yace cikin kasa da murya tare da cewa "gani nan kofar palon ki.


Da sauri ta kashe wayar tare da fitowa ta buÉ—e.


dai- dai lokacin da Amal ta kamo hannu Amnah suka doso wajen.


Mamy na buÉ—ewa ta zubamusu ido cikin barin jiki tace "miya sameku.?


Amal tace" Mamy muje ciki babu komi fa.


Hanya ta basu suka wuce ta maida hankalinta ga sadeeq tace" ina jinka.


Hannushi ya tura cikin sumar shi tare da turata baya duka, har lokacin kuma muryar shi bata fita sosai.


Da kyal yace'' na ajiye aiki ga key dinki na gode da hidima da kikamun.


Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un, Hazbunallahu wani imal wakim," sadeeq minai maka ?


Babu abinda kikamun Hajiya.


Amma gaskiya bazan iya zama ƙalƙashin inuwa ɗaya da yarki ba,Saboda bata kauna haɗa jini da talaka,kana tana muzantani,Anan yafaɗamata abinda ya mata da wanda ta mashi. Daga karshe ya ajiye key ɗin ya juya abin shi..


Hankali tashe take kiranshi Amma yakasa juyowa .


Afusace tashig palon cikin matsanan cin fushi ta zari wayar charger tafara tsulama Amnah ajiki, Abinda bata taba yiba.


Ihu Amnah keyi sosai tana neman É—auki amma Mamy ido ya rufe bataji bata gani.


Amal ma kuka take tana neman agaji akan yar uwar ta , Amma babu wanda zai iya jiyota ,saida mamyy tayi mata RuÉ—u-RuÉ—u kana ta koma gefe tana sauke numfashi.


Dakyal Amnah ta mike ta haye sama tare da faɗawa toilet tayi wanka tana kuka sosai ta fito daga iya sai ƙaramin towel tayi kwanciyar ta, tana kara jin tsanar Sadeeq aranta sosai, duk da wani sashin na zuciyar ta na hasasomata yana masifar kama da irin mijin da take fatan samu.


Tsaki tayi a fili tace'' aiko nafasa bazan taɓa auran mai kama da talaka ba,Kuma Ɗan Dako.


Anan palo kam Amal ta Rarrafa ta rike ƙafar Mamy ta fara bata hakuri, sanin Mamy batada isashiyar lafiya tinda takasa magana abun ya dameta sosai.


"Mamy dan zatin Allah kiyi hakuri kar halin Aunty Amnah ya dameki,kibar wa Allah kitayata da Addua, ni kaina banajin daÉ—in abinda take .


Ajiyar zuciya Mamy ta sauke tace" Amal taya zan iya samun mai amana kamar sadeeq, nasha auna shi da bashi kudin da suka zarce da niyyar wani abu amma haka zai maidomun canji,ga natsuwa ,uwa uba ilimi, kinafa jin shi kullum cikin Lambu yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login