Showing 9001 words to 12000 words out of 94971 words

Chapter 4 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt

Advertisement

09 Feb 2025

17289

zamuna kiran ka Sadeeq dan yafi daÉ—i.


Amal tace yamafi dacewa dashi.


Wayar shi ya zaro tare da cewa zan je Sallah Hajiya..


Mamy tace akwai masallaci a'kofar gidan nan kaje ka dawo zan baka sako.


Yace ok tare da nufar wajen mai gadi ya gaisheshi amutunce tare da fita daga gidan .


Harya fara tafiya ya juyo tare da cewa Baba ba zaka Sallah bane?


Baba Habu ya rike baki yace "Yaro Hajiya Amnah tazo bana nan aini nason dubu hamsin din da suke bani zatabi Ruwa, Anan nike kayana..


Cikin ƙanƙantar da ido yace akan duniya Baba da shekarunka zakayi gudun zuwa masallaci dan kar ka ɓatama wata rai?Wai miyasa mutane ke ɗaukar raini akan wasu yan canji da ake basu,Danmi zaka saɓama mahalicci ka
Akan abokin halittar ka,Baba kasamu kwaÉ—o kasanya kawuce muje sallah ,Sallah cikin jam'i tafi lada, Baba kaji tsoron Allah kaida ka fara manyanta ma ...


Jikin Baba yayi lakwas kamar an'watsama kaza gishiri.


Yace shikenan yaro bari in rufe.mutafi Nagode da tinatarar wa.


Ido Sadeeq ya lumshe batare da yacekomi ba.


Baba ya ÆŠakko kwado ya dannama gidan tare da faÉ—in muje.


Fita sukai suna fita saiga masallacin jere da gidan.


Sadeeq yace kenan ma masallacin na gidan ne kawai fita ne bakayi.


Baba Madu Yace_ Wallahi" Yaro ina tsananin tsoron Yarin ya abun har mamaki yake ba'n, Dan Akwai Hannatu jikata na tabbata ta girmeta, sai dai in nayi duba da kasansu nike sai inga wajibine in mata biyayya.


Hanci Sadeeq ya hura tare da cika baki shi da iska, Tura hannayen shi yayi cikin aljihu tare da fadin muje.


Shiga sukai sukai sallah ana sallamewa Baba yafara kyarma tashi.


Sadeeq ya kamo hannushi Yace" Karka tashi mana Baba, Ya kamata ka nemi gafara Allah, kayi karatu koda aya gomane, in san samune ma katsaya ayi Isha kana ka koma,Saboda Lahiraka tafi duniyar ka faÉ—i..


Baba Madu ya koma ya zauna dan yasha alwashin gyara goben shi kodan samun rabauta, kwara yasama ranshi zamanshi da ƙorar shi duk Allah ne zai tsara su acikin ƙundun ƙaddara shi.


Suna zaune suna lazumi har akayi isha kana suka fito.


Suna fitowa suka koma gidan ya buÉ—e masu suka shiga su duka suka zauna akan bencin dake wajen.


Baba ya'ce" yaro ya sunan ka.


"Sadeeq" ya bashi amsa atakaice tare da danna ma Mamy kira yace" na dawo.


Amal ce ta fito da kayan abinci niki -niki tayo wajensu tarr da cewa "Yah Sadeeq ga abinci inji Mamy.


Da sauri ya kalleta yana mamakin sunan da ta kirashi da shi ''Yayah'' yasake mai maitawa tare da taɓe baki .


Atakaice yace ki mayar nako shi Alhamdulillah, Sai dai ko Baba amma ni kamin in fito naci Abinci wajen Ammi nah..


Cikin langwabar da kai a:lamun bataji daɗin yanda yamata ba tace. "Dan Allah kaci wallahi saboda kai na girkashi fa Takarasa cikin yanayin shagwaɓa...


Kasa yayi da kanshi akaro na farko yace. "Amalll banajin yunwa nace ki mayar ba.


Wani sanyi dadi ya ziyarce ta jin yanda yakira sunan ta da wani kala jan baki da bata taba jiba, Ita batamason sunan ta yana da daÉ—i ba sai yau da tajishi abakin ÆŠAN DAKO Gidan su.


Baba dake kallonsu Murmushi yasaki ba tare da yace komi.ba.


Amal tace shikenan. Mamy tace kashiga ciki. Ta faÉ—a tana ajiye tiren wa Baba madu.


Tashi yayi yace "muje.


Tafiya ta fara yana biye da ita har suka ƙaraso palon da Sallama, Inda suka iske Mamy zaune cikin kwalliya .


Cikin yan second ni ya karema palon kallo tare da samin kujera dake nesa da ita kaÉ—an ya zauna.


Kai ta ÆŠago ta kalleshi tare da sakin murmushi dan gabatar shi na burgeta da alama bayason raini,Koda kasancewar shi talakka Annabi bai yarda mutunci da Allah yayi Mashi ba ya zube, Da wanine ta tabbata zai zauna akasan kujera in yaga tana sama.


Barka da dare yakatse mata tinaninta tare da Turɓune fuska dan bayasan acika kallon shi ana nazari abun na sosa ranshi...




Tace yawwa "Sadeeq Zaka iya tafiya yanzu Baba sai ya dinga kwana gobe da safe zakazo kamar yanda kacemun karfe takwas .


Yace baki da matsala indai wannan ne insha Allah.


Mikewa tayi sai gata da wasu ledoji manya guda biyu da ta zuba Kaji, kifi ,Naman rago.


Cikin É—aya'n kuma kayan fruit ne ta zuba akai tace ka kaima Ammin ka ina gaisheta sosai wannan kuma albashin kane na farko ta Damkamai dubu dari da hamsin.


Ledar ya karaba tare da cewa Allah ya ƙara arziki Nagode sosai, Amma albashin dubu dari kikace naga nan kuma akwai karin hamsin?.


Murmushi tayi tace'' saboda zaka sha wahala sosai ne wajan raba kayan abinci shiyasa namaka ƙari, Kuma akwai bukatar kasai kaya masu kyau dan ni ba matsayin bawa nikeson rikeka agidan nan ba inajinka ne kamar kanena, Kana ga Amanar Amnah da Amal nan ka kula da lafiyansu da kuma tarbiyyan su, Mahaifin du bai kasance ma'aboci zaman gida ba,inaso katayani saka ido ga tarbiyya yarana saboda shi namiki jigone agida.


Kanshi ya jinjina cike da tsare gida da kamun kai yace "shike nan na amince , Allah ya sadamu da alkhairi natafi nagode Allah ya amfana.


Sosai taji dadi dan harga Allah ta aminta dashi tace" Nagode Sadeeq Nima.


Yace ba komi tare da mikewa.


Amal tace yah sadeeq agaida Ammi da kanwar mu.


Murmushin gefen baki yasaki tare da furta" insha Allah yasa kai ya ficce.


Yana fitowa yaga Baba madu nata kwasar gara tare da ƙulla wani ga leda.


Sallama yamai ya wuce.


Fitar shi bada jimawa ba Amnah ta fito cikin wasu mahaukatan riga da wando da suka masifar yinata kyau kasancewar su read color, kanta ko É—an kwali babu sai parking din da tayi tsakiya ta tufkeshi da read din bant ta sakeshi yana Lilo,,Kunnata toshe da read din Bluetooth don da ya haska farar fatar ta.


Bakinta ta turo tare da kallon Mamy da som hankalinta bai kanta.


Cikin shagwaba tace "Mamy ina Namana ?


Kallonta mamyy tayi batare da race komi.ba sai tashi datayi ta haye sama tana latsa waya dan tana so taga Amnah ta gyara halin ta.


Amal ta kallah tana lumshe ido kamar mai jin Bacci.


Da hannu Amal É—in ta mata nuni dakan dinning da aka ajiyemata .


Cikin natsuwar tafiyar mai jan hankali ta mike tana juya.manyan hips dinta wanda wasu suke tinanin tsabar gayune kesata haka , Amma som ba hakaba ne yanayin tane haka.


Fridge ta Bud'a ta Äauki Hollondia yoghurt tare da karasa wa wajen dining ta zauna.


Naman ta zuba kaÄan
Ta tsakure shi ta zuba yoghurt din taci tare da mikewa tsaye ta nufi hanyar d'akin ta.


Kallo Amal ta bita dashi tare da cewa "Aunty Amnah wai kinga wannan mutumin ashe mahaukacin kyau ne dashi, Wallahi kamar Balarabe, Allah kika ganshi sai ya ruÉ—aki, bakiji yanda naji ina son shi ba, kema Wallahi inkin ganshi zakice kina son yazama YaÆ´an ki, nidai daga yau yazama Yayana kema...


"Ya isa!!!
Takatseta cikin daka tsawa.


Ke in'banda kina wawiya talakka har kyaune dashi, shashasha, insoshi!insoshi kike faÉ—a!!


To bakin banzanki ya faÉ—a miki, Amma nida wancen talakkan sai na azabatar da shi wallahi, ai naji duk kullin da kukai na kawoshi gidan nan, kuma hakan yamun daÉ—i, kana da kanshi da kafarshi zai bar gidan nan, Tinda har yayi sanadin da aka mare ni ni yar gidan .mtsss ta watsama Amal yawu ta haye sama..


Kukan takaici Amal din tasa tare da diddire kafa tace Wallahi nidai ina sonshi wallahi..


Rai aɓace amal ta haye sama itama..


Æangaran sadeeq kuwa yana fita yasamu acaÉ“a ya hau tare d kaishi unguwar su da shatara ta Arziki ,Sosai ya yaba da karramawar matar dakuma halaccinta gareshi.


Yana shiga gida da sallama ya iske Ammi da Hamrat waje sun shinfiÉ—a Tabarma suna shan iska , ga kuma karamar fitila data haska gidan maici da battery.


Oyoyo Babyyyy..


Hamrat tace cikin ihu tare dayo wajenshi ta faÉ—a kanshi.


Da sauri ya ajiye ledojin hannunshi tare da cewa oyoyo Baby'n Babyyyyy. ya faÉ—a yana rungumeta tare da daygata sama yana juyi da ita cikin tsanain farin ciki.


Dariya suke sosai cike da shauki .


Ammi tace nishikenan bakwa tani ko?


Sauke Hamrat yai tare da sumbatar hannunta ita kuma ta sumbaci goshin shi.


Tare da cemai i miss you so much Baby.


Yave.mee too Baby'n Baby.


Tashi tayi tsaye tayi cikin jindaÉ—i ta nufi É—akinsu tana ta dan tsalle tsallanta da rigar jikinta mai kyau sosai.


Kallo ya bita dashi har ta shiga kana ya maido hankalinshi ga Ammi Ya gaisheta yana sakin murmushi..


Hararashi tayi tare da cewa bana amsawa sadeeq kaga Hamrat mantawa kake dani dan haka nayi fushi..


Kyakkyawa sumar shi ya turamata tare da faÉ—in" kaina bisa wuya Ammi nah, Lefa ta daban ce, kinson dole muyi kewar juna yau banganta da rana ba.


Sumarshi ta shafa mai tsananin taushi da yawa tace hakane "ina jin daɗin Alaƙarku Allah ya dora da zumuncin ku har jikoki.


Ameen-Ameen ya amsa tare da janye ledojin da yazo dasu wanda baiso ko na miye ba .


"yace gashi hajiya tace akawo maki kana ya kwashe komi yanda sukai ya fad'amata..


Hamrat ta.fito tare da wani dan cup mai kyau ta bude Randarsu mai sanyi ta ÆŠebomai ruwa tace Baby gashi kasha ruwa.


Ƙarɓa yayi yace yawwa Baby'n Baby Allah yabar k'auna.


Idonta ta juyamai masu kama da nashi "tace Amin tana bashi hannu suka kashe ..


Yana gama shan ruwan ya juyo ya fuskanci Ammi tare da buÉ—e ledojin yace "Ammi kinga ashe Nama ne ma bansani ba ga kuma fruit.


Godiya da Addu'a tashiga yima Allah da kuma Mamy data kyautata musu yau daya taɓasu abunda suka kwana biyu basu ciba.


Kudin da aka bashi ya fiddo ya gwadamata tare da faɗin Mamy inaga silar warakamu tazo yakamata muyi amfani da damar muyi.abunda mike buƙata inaga zansiyo muna fridge D'an madai daici dan mudinga samun abun sanyi,kinga Zafi ake sai kuma in siyo kayan abinci masu yawa a ajiye in sai miki gas ki huta kunna icce ko Garwashi.


Idonta dake cike da hawaye ta ÆŠago tace hakan yayi sadeeq ubangiji Allah yamaka albarka yabaka lada yasa kagama da duniya lafiya.


Ameen ya amsa tare dashafar kan Hamrat yace 'Baby zanje indawo mizan siyo miki?


Cikin jin dadi tace ka siyomun Baru(Tantabara) Sai ka siyomun sweet mai daÉ—i...


Dariya ya saki daba koda yaushe yake yin taba yace insha Allah" wai miyasa kikeson Tantabara ne?


Murmusi tayi tare da cewa Baby ya sayyadi ke cemuna muna karatu in mundawo gida?


Sai muce "eh."


Sai yace muzama masu cika Al'kawari muyi halin tantabaru, Dansu akwai amana da cika Al'kawari, wanan dalilin ne yasa nike sonta Baby.


Kanta yashafa yace angama zan siyo miki Amnah sai gobe insha Allah




Ihu ta saki tare da rungumeshi.


Fita yayi sai gashi da kayan masu yawa ya siyomusu fridge madaidaici buhun shinkafa taliya.maca kus- kus semo da yan kaya masu sauki ya siyoma kanshi.


Farin ciki sosai ya bayyana ga Ammi tai tamai Addu'a tare dacewa naga mutun cin matar nan Sadeeq, Daka bari nima na dinga mata aikin in tana da bukatar hakan..


Take fara'a fuskarshi ta Äauke yace ""Ammi na ke zakiyi aiki da raina da lafiyana zan barki kihi aikatau? hmm Allah ya kiyaye kima daina wannan tinanin keda akaima...


Ya isa sadeeq jekayi wanka ka huta. ta katseshi da hanzari akan magana da yakeson yi..


Shuru yayi tare da leka
ÆŠakin ta ya ajiyema Hamrat kayan da ya siyo mata gefen ta ganin tayi bacci.


Kai tsaye yashige nashi É—akin bayan ya fito ya shirya cikin wasu kayan bacci farare sol masu tsanani taushi da kyau.


Babbar jikkashi ya bude tare da fiddo wata computer mai kyau ya fara dudduba wasu sakwanni na abubuwa da sauri.


Tare da É—aga wayar shi yafara kofe wasu number da banson na minene ba.


Yana gamawa yasaki wani mahaukacin tsaki tare da jinjina kai.


Take jijiyar kan shi ta mimmike idon shi ya canza launi.


Cikin sautin dake bayyana bacin rai yace Rana DUBU TA BARAWO DAYA TAK TA MAI KAYA...
5/18/22, 09:33 - MY MTN 2: D'AN DAKO 🌹

MALLAKI 🌹


UMMY AYSHA 🌹
9ï¸âƒ£&🔟


""Cikin yanayin na fushi ya rintse hannushi tare da kaima jikka dake kusa dashi duka.


Saida ya kwashe sama da awa biyu kana ya jonata charge yatashi yayi addu'a ya kwanta.


Bacci ya ƙoso ya zomai amman yakasayi ,saboda tinanin inda rayuwa tamayar dashi ayau daya ya tashi daga Ɗan Dako ya koma mai gadi, koda yake bazaice hakan ba tinda cenma DAK'ON zai dinga musu.


Tsaki ya saki yana taune jajayen lips É—in shi.


Ahanka bacci ya yi nasara kwashe shi.


Washe gari da asuba ya tashi tare da walwatsa ruwa dan garin akwai zafi, Yana fitowa yayi shiri cikin farar tattausa jallabiya data mishi kyau sosai ta fiddo zatin shi kamar wani balarabe..


Masallaci yaje yayi Sallah.


Bai shigo gidan ba sai Bakwai, yana shigowa ya iske Ammi kiching tana mishi breakfast dan tason da wuri zai fita .




Suna gaisawa ya shige dÉ—akin shi tare da cire kayan jikinshi ya É—aura haramin shi yafito yayi wanka.


Yana fitowa yazo yashafa mai tare da fesa tiraren E collection mai daÉ—in kam shi da sanyaya rai.


Wasu riga da wandone Black masu ratsin white ya É—akko ya sakama jikinshi tare da murza turare a'hannun shi yasake mulke kan shi take wani daddaÉ—an kamshi ya fara tashi daga É—akin.


Tattasau sumar shi ya gyara tare da É—aukar wata Black p-cap yasama kanshi ya É—auki bakin maks ya mannama dogon hancin shi.


Madubi ya kalla tare da lumshe ido dan shi kan shi ya yaba da shigar tashi duk da duka kayan jikin nashi ko 5k basu kai ba amma yayi masifar kyan da wanda yakashe 100k bazai yi kwatankwacin kyan shi ba, dan kyau ajinin shi yake.


Da sauri ya fito yana kallon agwogo ganin yaci four mint acikin awa É—aya kuma baya fatan karya alkawarin dan ba fatan shi bane kuma baya cikin tsarin shi.


Ammi ya iske zaune tana fiffita mishi tea'n data haÉ—a mai .


Zama yayi ya ƙarɓi tea yasha tare da ɓallar bread da kwan data soyamai kaɗan yakai baki.


KaÉ—an yaci ya aje sai tea daya shanye.


Kallan shi tayi cikin fuskar damuwa tace wai miyasa sadeeq bakason cin abinci ne?kana aikin karfi kana wahala zafi inuwa ƙuna amma baka da lokacin cikin ka miyasa? Takarasa cikin raunin murya.




Kallon ta yayi sosai yana murmushi tare da riko hannunta yace "karki damu Ammi nah kinson duk sadda ka cika cikin ka lokacin rauni da kasala ke kawoma ziyara .


Nikuma bana fatan abunda zai dakushemun kuzarina da rashin cika muradina dare da Rana .


Shiyasa nama kaina wannan sabon kuma yabi jikina .


Amma Ammi kidaina damuwa dan ni ba yaro bane duk sadda naji yunwa zan nemi abinda zanci na barki lfy .


Tsororo tayi tana kallon shi dan tabbas maganar shi akwai kamshin gaskiya.
Addu'a ta mishi dafatan nasara kana ya shiga É—akin ta ya shafa kan Hamrat kana ya ficce da sauri.


Takwas saura minti biyu ya isa kofar tafkeken get din gidansu Amnah.


Bayan ya shiga sun gaisa da baba madu ya É—aga waya yama Mamy waya akan ya iso.


Dadi taji sosai tare da faÉ—in "akwai sabuwar mota na nan compound ka karbi key wajen Baba Madu ka fara shirya kayan aciki kamun su Amnah su gama shiri saiku wuce.


To yace tare da latse wayar.


Key ya ƙarba tare da nufar motar ya jata har wajen kofar ɗakin kana yafara sungumo kayan cikin tsantsar jarumta yana shiryawa.


Cikin kankanan lokaci ya take bayan motar taf da kaya,Kana yakoma wajen Baba madu yana sauke ajiyar zuciya dan cikin kwanakin'nan da yayi aiki da yawa sai yaji ƙasan zuciyar shi namai masifar ciwo da bayan shi,Daure wa kawai yake dan baya fatan yaba gangar jikinshi muhallin hutu har sai ranar da burun shi ya cika.


Kimanin awa ɗaya suna zaune saiga Amal cikin shirinta na atamfa tasanya hijjob madaidaiciya tafito da ƙaton basket a'hannunta shake da kayayyaki.


Kai tsaye ta iso wajensu tana doka murmushi tare da ajiye kayan gaban shi ta tsugunna tana dafe kumatunta ta zubamai ido cikin narkakka murya tace "yah Sadeeq ina kwana, kana lafiya yasu Ammi da sst Hamrat.?


Alhamdulillah ya bata amsa agajarce yana kallon gefe.


Tace yawwa" Ammi tace ga breakfast ka farayi kamin Aunty Amnah ta gama shiri.


"Yace ayyah kimayar kice ngd naci agida kamin inzo Naci.


Kallan shi tayi tana kwabe fuska tare da faÉ—in
"Dan Allah kaci mana miyasa duk sadda zamu baka abu bakaci ko kana tinanin zamu cutar da kaine ?


Murmushi ya saki da bai shiryaba yayi ganin yanda tayi magana kamar zatai kuka .


Yace "A'a ko É—aya kawai naci abinci agida Amma bani ruwa.


Ruwa ya ƙarba yasha kaɗan ya rike sauran ahannun shi.


Baba madu ta turama sauran takoma ciki cikin rashin jin DaÉ—i.


Saida suka shafe kusan awa É—aya sannan suka fito su duka.


Mamy Amnah Amal.


Kai tsaye wajen motar su Amnah ta nufa yayin da Amal da Mamy sukayo wajen shi suka sake gaisawa tare da fad'amai yanda takeso ayi tsarin abun dan washe gari ake sanya ran ganin wata.


Kai ya jinjina tare da mikewa cikin kuzari ya isa ga motar ya ajiye ruwan tare da shiga ya zauna yana lumshe ido tare da wasa da hannunshi daya rike styarin ...


Tada motar yayi dai-dai lokacin da Amnah ma ta tada tata tayo hanyar get.


Shima hanyar get É—in ya nufo tare da kashe motar ya fito ya tura get É—in da hannu daya kan ya koma mota yadosi get din.


Sosai Amnah ta sheko da gudu asan ta samu ta rigashi fita.


Cikin kwarewa ya kaucema motar ta tare da fita yayi parking ya fito .


Cikin bacin rai ta fito tana sanye da maroum din Abaya mai duwatsu kota ina tasha kwalliya data mata mugun kyau.


Wajenshi ta nufo cikin gadara tana zuba yauki kamar sabuwar ƙubewa




"Uban waye ubanka dazan fito kafito bazaka jurema fitana ba kamin kafita É—an talakawa marar tarbiyya? miye ai'kinka inba takemun bayaba ka rikemun jikka amatsayinka na ÆŠan Dako uhum nace waye ubanka?


Wata firgitacciyar tsawa ya dakamata data sata daka tsalle ta koma gefe.


Afusace ya zare hular kanshi kyakyawan gashin shi ya bazu tare da cizge maks din da yasama fuskar shi ya cilla gefe.


Jajayen idanuwan shi da suka cika da ɓacin rai ya dago ya zubamata Tare da nuna kanshi da yatsa cikin ɓarin da jikin shi keyi yace.


" Ni tsaran kine?ke wace irin wawiyar yarin yace marar hankali da tinani,Natabbat nabaki shekara goma a haihuwa,Saboda bakida wadatacciyar tarbiyya ko?ko Dan kinganni agidanku akacemiki kisamu damar wulakantani!To bazan É—aukaba, bazan jureba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login