Showing 18001 words to 21000 words out of 94971 words
Chapter 7 - DAN DAKO Complete Book Hausa Novels by Ummu Aysha .txt
raira karatun Alkur'ani,baya wasa da sallah ko kaɗan, taya zanji natsuwa da farin ciki in irinshi ya kufcemun? Wallahi Amnah bata kyutamun ba som,Tinda taje US ta dawo iskancin ta ya ƙaru, ya zama dole ana gama sallah in ɗauki mataki a kanta, saboda lamarinta kullum gaba yakeyi ba baya ba.
Hakuri Amal taci gaba da bata har saida taga ta sakko.
Tace Mamy kibani number yah Sadeeq inje gidan Nene! Na son suna shiri sosai dan ko cikin azumin nan yana yawan zuwa tacemun, in'haÉ—asu nason zata lallaso miki shi.
Cikin farin ciki dajin daÉ—i ta bata.
Ita kuma batayi sanya ba ta fita ta hu mota sai gidan Nene.
Anan ta kora mata bayani saiga Nene na kuka tana tsinema Amnah.
Cikin kuka tace'' latsoman shi dan Allah, inji awane hali yake , Allah yasama bayyi zuciya ba ya hau saman titi ya kwanta yace mota tabi tasaman shi,Koda yake ƙatone bazai ji ciwo sosai ba.
Sai kuma ta kwaɓe bakinta tare da faɗin'' wannan ai fatar banzace ina azumi yan Ameen su amsa in'cuci maraya nima walakiri Yaci man uwa.
Arikice ta kwace wayar tan halo- halo Saddi dan Allah ka É—auka kar in'maka baki .
Abangaran Sadeeq kuwa yana fita masallacin dake kofar gidan ya shige yayo alwallah tare da ɗaukar Ƙur'ani ya fara karatu.
Take yaji zuciyar shi ta fara sanyi.
Jin ƙarar wayar shi ne yasa shi ɗauka da sallama.
Nene najin ya ɗauka tasaki shewa tare da amsawa tace" yawwa Abubakari kwandon sukari, Dan Allah kayi Hakuri kaje ga fulanina, Wallahi fulani kullum ceman take ita dai I lovulu to saddi , Amma kaga wannan yal banzar da batada kunya ta ganka Ƙato ita kuma tayi zubi da Buta lamba 2 tace zatama rashin kunya , Wallahi na baka dama duk in ta kuma kasanya makwal-kwasa ka fiddama shegiya rabin hakori,kai saddi kaji tsoron Allah rabi fa ba ɗaya ba, A'a toh karka maidata kamar kofar Rijiya, inki samun Dan jikallan da zai sota.
Nainah dama kina sya number nah amma baki taɓa kirana ba?
Yakatse Nene da keta zuba.
Nene tace
"Eh mana kwandon sukari ina da number ka. Kai wallahi karya haramun ina azumina yanzu Amalulu ta sanyaman , Uwar ta Fulani ta turota akan tazo ta ÆŠaukeni mufita gantalin nemanka, cikin rana da kishi, shine nace naga kason mutunci nah kuma kaga ina kyautatama , Nason kamun alfarma ka koma ko?
Shuru yayi yana murmushi jin yanda take rattafo zance.
Da kyal Nene tasha kanshi yace zaikoma yanzu insha Allah.
Dadi taji tace' um muah saddina, kason munyi zama da laraba ko Tusa ɗansu yayi sai sunyima Takashin yaron suu sunba,Suga Tantabaru iyayen kauna ,haba inama amfani wannan ai Iskancine da ƙazanta,Saddi kason nataɓa ganin wani Balarabe zaima matar shi a laɓɓ... .
Dariya ta bashi da sauri ya kashe wayar yana gilgiza kai.
Saida yayi Sallah kana ya koma gidan Mamy anan takara bashi hakuri yace mata ya wuce.
Ahankali kwanikka keta shudewa yau harya zamana sallah saura kwana ukku ko biyu .
inda kafatanin al'umar musulmi kowa shiri yake dan ganin ya kerema sa'a .
Aɓangaran sadeeq kuwa gabaki ɗaya cikin damuwa yake ta Rashin abinda zaima Ammin sa da Hamrat koda shi baisamu ba , Amma yason lokacin biyan sa baiba dole sai ranar Daran Sallah.
Bayan ya kammala komi kamar yanda ya saba ya shiga yima Mamy sallama anan ta tsai dashi ta shiga sai gata da manya ledoji guda biyu ,dakyal ta jawosu tace yawwa "sadeeq ga kayan sallah ku mai Ɗinki kane yabani matsala shiyasa ba a kammala da wuri ba, akwai na Ɗiyata Hamrat dana Ammi duka dai baki ɗaya, kana ina neman alfarma akawoman Hamrat ranar Sallah, kason gidan namu na cike da kewar ƙananun yara.
Kallon ledar yake yana kallon Mamy wai shi da minene zai sakama matar nan, yanzu kayan sallah tami shi kenan? Wani irin girma da darajata yaji sun lunku a cikin zuciyar shi ,yana rokon Allah ya bashi abinda zai faranta ranta kamar yanda take faranta nashi dana Ahalin shi.
Karba yayi ya mata godiya da addu'a da ganan sukai sallama yayo gida cikin farin ciki.
Koda ya iso ya shigo da kayan tsakar gida tare da komawa ya shigo da machine dinsa ya rufe gidan.
Sallama yayi ya shigo inda ya iske Ammi zaune tanata shafa kan Hamrat dake neman yin bacci.
Amsawa Tayi tana mai sannu da zuwa, tare da matsawa gefe ya zauna yana mai jan yatsun Hamrat yace'' Baby'n Baby tashi kiga abunda nakawomiki.
Da sauri ta tashi tana murza ido tare da turo baki tace ''baby munɓata yanzu baka da lokacina.
Dariya ya sanya sosai yana ganin yanda takeyi kamar budurwa.
Ammi ma cikin dariya tace" To ke Hamrat bakyaso Yayan naki yaje aikine yasamo miki abunda zakici?
Inso Ammi amma inason mudunga tafiya tare sai in ragemai wata wahala ko.
Dariya sukayi su duka yayin da ya fara buɗe ledojin da keta zuba kamshin da yarasa kona minene yana jin kamar ya son ƙamshin.
Lumshe ido Ammi tayi jin wani kamshi daya daki hancinta wanda ya sata tinawa da lokuttan baya,take jikinta ya fara bari ,wanda ya sata jingina da bango tana Addu'a dan samun sauki.
Saida yagama fiddo komi kana ya kalleta wanda hakan ya sashi faÉ—uwar gaba.
Da sauri ya ture kayan tare da kamo hannunta yace ''Ammi nah mike damunki ,ko bakya farin ciki da kayan, kinson bafa nina sayaba, Anan ya faÉ—amata abunda ya faru.
Ajiyar zuciya ta sauke tace" Dee ka tino wannan kamshin kuwa?
Nazari yashiga kamin ya shiga jijjigamata kai cikin cikowar hawaye yace'' Ammi nah natina, wallahi natina Ammi nah, Amma babu damuwa Allah yakai Damo ga harawa ko baici ba zayyi wawaso,Gaba kaÉ—an gaskiya zatai halinta,lokaci kaÉ—an yarage zaki yayi ciki da Kura Dan magance handamar ta,kimanta baya Ammi na mu fuskanci goben mu.
Kai ta gilgizamai tare da faÉ—in insha Allah" Dee .
Wasu tsadadun lace da atamfa ya daga masu kyau sunsha ÆŠinki ya ajiye gabanta yace "Ammi ga wannan nakine ,ga mayafi da takalma duk nakine .
Cikin murna da sa albarka ta gwada komi taga cif- cif da jikinta taita godiya.
Wasu zafafan dogayen riguna na yaran yan gayu masu tsananin kyau ya É—aga guda ukku masu masifar kyau.
Pink ,blue, milk sai sheki suke ya damkama Hamrat yace ''eyye Baby tayi kayan yan gayu.
Hawaye ya zuboma Ammi tace Allah sarki rayuwa! Hamrat ɗita tazama yar gayu, bana bazata sanya atamfa roba ba taƙarasa cikin hawaye.
Kai ya gilgiza cikin damuwa yace ''Ammi nifa som kayan nan sunfita raina,Duk Irin kyautar da za'aman wadda zata saki shiga wani yanayi inaji kwara Abar ta.
Kan shi ta shafa tace'' kayi hakuri sadeeq bamu da bakin magana wa baiwar Allah nan sai dai godiya.
Cigaba yayi da fiddo kayan hadda takalma, Hamrat kuma dai -dai kafarta guda ukku kalar riguna ta masu kyau da tsada , Sai kit na kayan make up da tiraruka,Daga ƙasa yaga wata Farar kwalba mai kyau , Anan ya fiddota yaji wani mahaukacin kamshi , Da sauri ya mikama Ammi yace to hasashen mu ya zama gaskiya.
Hannuta har kyarma yake ta karbi kwalbar tare da kwaƙumeta ta fashe da kuka gwanin tausayi , sai da tayi ta gaji sukabata baki kana tayi shuru.
Gudar ledar ya buÉ—e inda yaga wasu shaddodi É—inka ku masu masifar kyau angoge an'sanya a leda yar ciki da babba rigace guda ukku na shadda masu tsada sai wasu boyel da a kaima tazarce guda biyu.
A takaice kayan sunyi kyau,sai hular su zanna mai kalar kayan, sai takalma taki biyar da agwago da wani glass mai masifar kyau.
Farin ciki sosai yaji ya kawomai ziyara Lokacin da yaga kayan mutunci da aka haÉ—a mai.
Murna sukaitayi shi da Ammi,daga karshe suka kira Mamy suka mata godiya da ƙudirin ranar sallah tare zai kaisu Sumata godiya ita da Hamrat.
Washe gari ta kama Daran Sallah kuma anasa ran ganin wata. Hakan yasa a keta hada- hada , na shige da fice.
Abangaran sadeeq ma yana tashi bayan yaje gidan Mamy ta bashi kuÉ—i yayo musu cefane da kaji masu yawa tace'' ya raba biyu ya kaima Ammi shi rabi.
Da" to "ya amsa yaje yakai ya dawo suka cigaba da Abinda ya dace.
Amnah ce kwance ɗaki tana waya da wata ƙawarta da sukai karatu US wadda ke shedamata tana Najeria ranar sallah zata kawo mata ziyara ita da cousin din ta .
Murna tai tayi dajin daÉ—i dan ta son Billy babba yarinyace, shiyasama tasu tazo É—aya ko a makaranta batada tamkar ta, Dan yar babba gidace duk da batason gidan suba Amma ta shedamata Nijeriya take karatune ya kaita cen..
Karfe goma na dare sukaji ƙarar bindiga daga masarautar katsina tabbacin ganin wata. Hakan yasa gari ya rikice da murna yakoma tamkar ba dare ba.
Haka yake wajen sadeeq wani irin farin cikin da baison daliliba yaji yana saukar mai, sai goma yakoma gida bayan ya ƙarbi Albashin sa yayo sayayya abun buƙata.
Anan ya iske Ammi nata aiki ya cire kaya tare dasa ƙananu yaci gaba da kamamata aiki sai sha biyu suka kwanta.
Washe gari take Sallah Babbar rana zuciyar kowa cike da farin ciki, Duk Yanda rai yakai ga baci farin cikin wannan ranar kan goge damuwa da takaici kowane bawa .
Karfe bakwai Sadeeq ya faÉ—a wanka ya jima sosai kana yavfito yanata zuba kamshin sabulun lemon Safe guard .
Cikin kuzari ya faÉ—a É—akin shi tare da maida kyauran ya rufe.
Wani tsadddan maine ya fiddo da ya saya daran jiya ya shafama fatar shi.
Body spray na Tiraran Deal ya É—auka ya mulkama farar fatar shi.
Tare da É—aukar wata farar vest da wando ya sanya .
Kayan da Mamy tamai ya buɗa dan zaɓar kala da zaisa,Anan yaga da Royal Blue , sai Brown, da Ash sune keda babba riga.
Sai boyel Blue Black da milk.
Royal blue din ya Ɗauka tare da Addu'a saka kaya ya sanya wando da yar ciki ,hular data haɗamai da ita ta ƙayan ya sanya tare da fesama jikinshi tiraran Arabia oud mai sanyi, ya ƙara da Burmi oud ya murje jikinshi tare da murzama babba rigar daya baza bisa gado.
Wani ni'imtaccen kamshi mai sanyi ya mamaye ÆŠakin.
Ahankli ya É—auki rigar ya zirama jikinshi tare da kafa hula da agogo ya zura takalma.
Masha Allah bi'ahsani khalik,shine Abinda Ammi tace sadda ta buɗe ƙofar tashigo, dan tinda taji kamshi ta tabbata yagama sanya kayan shi,Cikin tsanin so take kallon tilon yaron nata da yayi mata masifar kyau, kamar shi da mahaifin shi ta fito sosai..
Cikin murmushi yana zura links É—in hannu shi ya isa wajenta tare da kamo hannunta ya sumbata yace" Ammi nah Takabbalalahu minnah wa minkum.
Kanshi ta shafa tace shukran laka .
kaga yanda kayi kuwa Sadeeq É—ina , Yau Dee Appy nane ya fito kamar Ango, sadeeq dama rayuwa kanjuyawa , kaganka kuwa, bantaba sha'awar zamanka da iyali ba sai yau Dee da kayi wannan shigar, wallahi ka dace da zama magidanci sadeeq, ka taimakamun ka samoman yar da zata haifaman jikokina ingansu tin kamin rai yayi halin sa.
Gabaki ɗaya kunya yaji takama shi wane irin aure kuma, abun ma harda jikoki, kai Ammi yafada cikin ƙasa da murya tare da sakin murmushi.
Murmushin tayi tace to bari inje in'shiryama Hamrat itama kuwa blue zansamata kuyi iri É—aya ko?
Kai ya jinjina mata yana kallon gefe dan wani nawie yaji ya saukar mai da tayi mai magana aure, Dan shi bashi da ra'ayi aure ,baya kuma kawoma rayuwar shi , to damai zai rike matar, ga baki É—aya albashin shi a tsare yake da hidimar ahlin shi, to in yayi aure kuma yazata kaya, wama wama zata so shi.?
Ganin lokaci na tafiya ya sashi gyara sajen shi tare da fesa wani spray, take yakara kwanciya yayi shar -shar ga fuskar shi.
Cikin tako na isa da wadatacciyar lafiya ya doso kofa É—akin Ammi ,a inda yashiga ya iske tama Hamrat kwalliya tayi masifar kyau, yarinya kamanni shi da ita sun fito sosai , Ga tulin gashinta na fulanin Asali yasha parking É—in Tsakiya, an'samata rigar mai hade da Bandana tsakiyar kanta.
Tirare ya É—auka gefe yaci gaba da fesamata yana yaba kyan da tayi itama tana yaba nashi.
Ammi ma tayi wankanta cikin lace din da aka bata tayi kyu sosai.
Lokaci guda yaji sha'awar rike babbar waya da yanzu sai yamusu photo kodan tarihi..
Agulguje suka fito ya fitar da machine dinsa, Hamrat ta hau sai masallacin G.R.A na unguwar su Mamy kenan.
Amma babban masallaci na Idi.
Sahun farko suka samu dan karfe tara ake fara sallah sukuma sun iso tin 8:50.
Sallah sukayi tare da addu'a kana aka fara watsewa inda kowa ya dinga fitowa masu photo nayi ma mutane,wasu nayi a waya, sai su karɓi number ka su turoma.
Wani mai photo ne yana ganin ya fito da gudu ya doso shi yace" Yallabai dan Allah ka tsaya kaida ÆŠiyar ka inmaka Photo kyauta, wallahi kunyi kyau Allah ya horemaka kyau da zati.
Murmushi yayi tare da gyarawa ya musu photo masu kyau shida Hamrat har ukku, kana ya ƙarbi number shi tare da cewa zai Turo mai ta waya.
A takaice
"Yace bana da waya" .
Cikin mamaki mai photo ya kalleshi zai magana ya wuce batare da yace komi ba.
Cikin natsuwa yake tafiya shida Hamrat suna Dan labari.
Assalamu Alaikum .
Yaji wata murya tamai sallama cikin sanyi......âœï¸
5/18/22, 09:34 - MY MTN 2: 🌹ƊAN DAKO
MALLAKI🌹
🌹UMMY AYSHA 🌹
1ï¸âƒ£5ï¸âƒ£&1ï¸âƒ£6ï¸âƒ£
"""Shuru yayi dan yanajin kamar ba dashi ake ba.
Sallama ya sakeji a karo na biyu hakan yasa ya dakata da tafiya ba tare da ya juya ba.
"Yallabai girmankane dan kazama mai shariya, Amma karka manta ita sallama Allah mai girma ya umarcemu da am'sata a duk sadda akamuna,Dan haka Assalamu Alaikum tasake mai maitawa .
Ahankli ya juyo dan tabbatar wa kanshi dashi ake ko-ko?
Wata mummuna faɗuwa yaji gabanshi yayi da mugun ƙarfi lokacin da idanuwan shi suka sauka akan fuskar kyakyawar budurwa dake gaban shida.
Ta kasance wanka Tarwaɗa ce ,Amma tana da kyau sosai, tana sanye cikin Abaya Black sai sheki take ,ta yane kanta da mayafi tayi fess da ita hannuta riƙe da Iphone ɗinta.
Tsayuwar shi ya gyara sosai batare da yabari fuskar shi ta tona asirin zuciyar shiba,Na É—imuwar da ya shiga da ganin ta.
Murmushi ta saki tace "Uncle Dee Dama zuciyana bata taɓa Amincewa da mutuwar kaba Wallahi ,bantaba tinani samunka cikin garin katsina ba,Saboda .
Ya isa Bily,ya isheki, kisani yanzu ba da bace, kana zanmanta da alƙawarin dake tsakanina dake zan miki wanki babban bargo , kikama kanki fiye da yanda na kama kaina , Dan yazu ta canza zani...
Murmushi ta saki sosai tace "Dee kenan! nason dole a wannan karan kaji ka tsani kowa, Dan duniya tamaka hankali ,Amma wallahi billahi ni Bily rayuwata cike take da tausayin ka, da ƙudirin taya ka cimma burinka, fatana kabani dama kawai.
Shekeke ya kalleta tare da fincikar hannu Hamrat suka tafi.
Kai Bily ta dafe tare da faÉ—in allah ya taimakeka akan abinda kasa gaba Dee, ina nan ina bibiyar lamurranka har sai na tayaka cimma burinka..
Waya ta zaro tare da magana ,sai kuma naga tayi gaba cikin sauri tare da tsayawa da mai photo nan ta bashi Damen kuÉ—i ta wuce abinta ta faÉ—a cikin mota.
Wani matashin Saurayine zaune fari kal dashi tace" maza Abul khairi kaini gidan su Amnah, na mata Alkawari zuwa.
Kai ya jinjina tare da tada motar suna tafiya suna fira cikin nishaÉ—i.
Aɓangaran sadeeq kuwa takaici da kuma ɓacin ran ganin Bily cikin rayuwar shi lokacin da baya sa buƙatar kowa.Hakan yasa ya fasa zuwa gidan Mamy kai tsaye ya fara yawa da mashin kota ina cikin katsina, har inda baitaɓa takawaba kusan tsawon shekara takwas da zamanshi saida yaje.
Tin hamrat na murna yana yawi da ita har tagaji tafara rihimar ya mayar da ita gida.
Tafiya yake yana waiwaye saida ya Tabbatar babu mai binshi kana ya fara bin lunguna, har saida ya cimma unguwarsu kana ya sauke ajiyar zuciya.
Abanza ta sashi karya alkawarin,da yason da haÉ—uwar su mizai kaishi masallaci g.r.a ,da wani zaije tinda akwaisu da yawa.
Gida suka koma Ammi na tamai faÉ—a akan Baizo ya kaima Mamy abinci ba , Dan tayi sinasir da alkubus da miyar kajin da takaimasu, da yawa tazuba akuloli manya ta aje da niyyar ya kaimasu.
Hakuri yabata tare da faÉ—in tabari sai bayan sallah la'asar ya kai.
Wanka sukayi sukaci abinci suka fara fira cikin jin daÉ—i.
Aɓangaran Bily kuwa tana zuwa gidan su Amnah bayan sunshiga get din ta ma Amnah waya akan Ta shigo.
Da sauri Amnah da tasha wata kafurar kwalliya cikin wani skit da riga na lace Royal Blue ta fito cikin tako da yauki ko ina na jinki na juyawa, bakajin komi sai kamshin da take zubawa.
Ƙasa ta sakko tace Mamy nayi baƙi zan'shigo dasu.
Baki many ta taɓe dan har lokacin bata sakar mata fuska sosai.
Tashi tayi ta haye sama abinta.
Asanyaye ta fita daga gidan tana tafiya cike da natsuwa .
Masha Allah itace kalmar da Abul khairi ya furta lokacin da yayi tozali da ita kamin ta ƙaraso yace" Bily wannan mai zafin fa.?
Murmushi tayi tace'' ka rufama kanka asiri wallahi ita É—an sarkine burinta , Dan batason koda dan gomna ne,Tafiso tana tafiya ana mata kirari .
Yace Abu mai sauki mu yan duniya har an'fadamana Tako! tsaya kiga
Ya wani sha mur tare da kishin giÉ—awa ya fiddo dalleliyar wayar shi yana chart din bogi.
A'hankali ta ƙaraso wajen tare da buɗe bayan motar tashiga ba tare da ta rufe ba.
Bily ta jiyo cikin murmushi ta bata hannu suka gaisa. Tare da cewa" na sameki lafiya?..
Cikin isa da Aji na ya mace tace" lfy kefa.?
Alhamdulillah ta amsa tana murmushi .
Tace muje ciki ko?..
Bily tace Amnah baki gaisa da Prince ba...
Wata irin faÉ—uwar taji gabanta yayi batare da tace komi ba ta buÉ—e motar ta fita.
Da ido ya bita ganin yanda take tafiya albarkacin halitun ta nata juyawa.
A rikice yace dan Allah Bily karki yarda ki fito saida zuciyar ta ahannu, ni kuma zan saya ko nawa ne dan Allah,Wallahi son gaske nike mata auran ta zanyi.
Kai ta ƙadamai tare da fita tabi bayanta har palon Mamy.
Hannu Amnah ta kama sukayi sama É—akinta ta fara kawomata abinci da drink anan suka fara fira yaushe gamo.
Amnah tace Bily ya naga duk kincanza kinƙara kyau fa?..
Murmushi tayi tace" ai'kedai aka bari baya, nayi- nayi kizo inɗoraki ahanya kinƙiya ,Kullum sai dai ki kawana da takaici kibi