Showing 1 words to 3000 words out of 90241 words

Chapter 1 - TAMBARIN SARAUTA Book (1 to End) Complete by UMMU SAFWAN.txt

18 Feb 2025

9809

ο»Ώ
πŸ‘‘ *TAMBARIN SARAUTA*🀴
πŸ‘‘ 🀴 πŸ‘‘





*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)






*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


_we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_






#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com









*AM BACK AGAIN BY THE GRECE OF ALLAH*




*Alkhairin dake ciki Allah yasadani dashi, shairin dake ciki Allah ya tsareni dashi*
*muje zuwa masoya ana bala'in tare🀝 (UMMU SAFWAN CE*)








*1*










"Sauri takeyi domin ganin ta k'arasa gida, dan tasan yanzun *kaka* tana can hankalinta a tashe ganin lokacin dawowarta islamiya har ya wuce,
kallon agogon hannunta tayi, taga 7:30pm
Taja wani dogon ajiyar zuciya had'ida k'ara yin sauri harda d'an gudunta domin ganin sallar isha'i ake neman akira yanzun."


taja wani dogon tsaki ta juyawa ta kalli k'awarta Maryam da itama ganin *Afnan* d'in na sauri hankalinta a tashe ya sanyata itama yin saurin."


Sannan Tace "Maryam duk kece kika b'ata mana lokaci wurin biyan haddarki, gashi yanzun dare yamana a hanya kuma bayan kinsan kaka ta tsani na kai magariba bana gida, ni yanzun bansan yanda zan cemata ba idan na koma gidan."


Maryam tace "kiyi hak'uri Afnan bada son raina muka kai iyanzun bamu koma gidaba, koma meye laifin malam *Nura* ne da ya tsayar damu a cewarsa sai mun iya karatunshi sannan zamu dawo gida."


*Afnan* bata kuma tankawa *Maryam* ba, domin batason yawan suruto, magana d'aya biyu takeyi sai tayi shuru,
da zarar da cika magana sosai,
ko kuma ana yawan yi mata surutu a akai to kanta ciyo yakeyi."


Wannan dalilin ne yasanya ko k'awaye bata dasu, k'awarta d'aya ce *Maryam* itama unguwarsu d'aya kuma mak'otane sosai domin gida biyu ne a tsaninsu,
Tare suke zuwa makaranta Arabic da Boko."


sauri kawai sukeyi ba Wanda ya kuma yiwa d'an uwanshi magana domin *Maryam* tasan halin *Afnan* sarai bata son yawan suruto


Karya kwanar da zasuyi, da zata b'ullewa dasu gaban gidansu,


saiji sukayi anja burkin mota da k'arfi."


A razane suka firgita musamman *Afnan* gaban ne yashiga fad'uwa jikinta na rawa,


domin tasan kwanar gidansu mota bata fiya shuguwa ba, ga kuma duhun dare da somayi ba kowa ne mutum ke yawan wucewa ta wurinba."


Kashe mata ido akayi da fitilar motar hankalinta ya kuma tashi idonta ta cika da hawaye, taja gefe d'aya ta tsaya tana jiran kowaye ya wuce sannan suma suwuce."


Ganin motar tak'i tafiya kuma ankashe masu ido da fitila,
Maryam kuma na ganin hakan taja da baya da baya a tsorace ta antaya da gudu ta barta nan."


Wani saurayi tagani yafito daga motar da alama a buge yake da giya, sai tangad'i yakeyi yanufota gadan gadan."


*Afnan* naganin wurinta ya nufo, a tsora ce, ta k'ank'ame jikinta tadin ja da baya da baya cike da tsoro a fuskarta."


Shima biyarta yakeyi yana kallonta yana murmushi."


itama kallonsa takeyi domin bata tab'a ganin kalar wannan fuskar tashiba,
amma alamu sun nuna cewa d'an sarkine diba da tayi da kalar shigar da yayi da kuma hularshi mai *Tambarin sarautar* masarautar sarki Ahmad Moh"d,
Sai kuma alkibbarshi dake rataye a kafad'arshi,




" *Bassam* kenan d'an sarki maiji da kud'i da mulki ya taka duk Wanda yakeso a garin yanda yaga dama."


nufarta yakeyi da wani kalar murmushi a fuskarshi,
domin ganinta yakeyi sak kamar budurwanshi *Basma* wanda suka rabu da ita yanzun a club."


Kamota yakeso yayi ya rungume amma besamu sa'ar yin hakanba, sai yashiga fad'in "haba *Basma* yau kuma guduna kikeyi?" Yana nuna kanshi cike da maye."


ita kuma tana ja da baya cikin tashin hankali,
Tana zubarda hawaye "wannan bala'i daya keso ya tunkarota cikin daren nan, gashi unguwarsu mutune basu cika wucewa ba idan dare yayi hakan."


Wannan dalilin ne yasanya *Kaka* bata barinta fita waje, da zarar suntaso daga makarantar islamiya k'arfe shida, to bata barinta Zuwa ko ina sai kuma gobe."


"Amma yau gashi kaddara takirata har isha'i tana waje, gata yanzun ta had'u da wannan bala'i a gabanta,


"Tasan yanzun wannan mashayin ko kasheta zaiyi ba Wanda zai fito ya taimaketa."


Ta kuma fashewa da kuka mai sauti tana addu'a a zuciyarta "Allah yakawo mata d'auki."


cigaba tayi da Jada baya shima yana kuma kusan tota, har takawo jikin wani shago dake kulle taja ta tsaya, had'ida runtse idonta tana zubar da hawaye, tana addu'oi."


Yana zuwa daf da ita ya kuma ganin takoma mashi *Basma*shi sak,πŸ‘ŒπŸΌ ya kuma sakin wani murmushi irin na mashaya, yarik'o hannunta ya murzashi yace "haba *Basma* baki ganeni bane kike guduna?"
Wata gyatsa yasaki mai d'auke da warin giya, da tsami."


*Afnan* tayi saurin toshe hancinta, cike da tsoro da kuma b'acin rai, "domin tunda Allah ya halinceta babu namijin da yatab'a rik'a mata hannu sai yau."


Bata ankaraba saijinsa tayi ya rungumeta yana fad'in *Basma*yau ni kike toshewa hanci?" Warina kikeji ?"


Aikuwa wani k'arfi ya zo mata,
cike da b'acin rai ta tureshi daga jikinta tasanya hannu biyu ta kwad'a mashi lafiyayyen mari mai kyau a kuncinshi, wadda sai da ya kusan dawowa hankalinshi,


Hakan yayi dai dai dawowar wutar Nepa, *Prince Bassam* rik'e da kunci yayi tsaye tsam, ya kurawa *Afnan* ido ko gyaftawa bayayi kamar wanda ke tunanin wani abun."


Bata ankaraba taji muryan *Maryam* tareda mahaifinta Malam *Iro*,


Malam *Iro* yace "kinyimin dai dai *Afnan* dakika mari wannan mutumin Wanda besan darajar d'an Adam ba."
yanunashi da yatsaπŸ‘‰πŸ»



Malam *Iro* ya zagayo ta gabanshi ya tsaya."
yaci gaba da cewa, "wannan hukuncin da taimaka shine dai dai da kai,
Domin kana tak'ama da kai d'an sarki ne, kake taka mutane yanda kaga dama, ka kuma tare 'ya'yan Mutane a hanyan lungu sak'o kana cutar dasu,
Dan kana tak'ama da sarauta wadda mahaifinka ba hakan yakeyiba."


To kasani mulki ba hauka bane, kuma Allah zai saka mata abunda kayi mata."


Yana kawowa nan yaja hannun *Afnan* da *Maryam* suka nufi hanyar gida."


*Bassam* dafe da kunci yayi tsaye yana kallonsu d'aya bayan d'aya, har malam *Iro* ya gama zazzaga mashi masifa bai motsa daga inda yakeba."


Malam *Iro* yaja hannunta tare da *Maryam* suka tafiyarsu,


Tafiya sukeyi yashiga yimata nasiha had'ida bata hak'uri akan abunda yafaru da ita a yanzun."
Yashiga kwantar mata hankali, domin a zahirin gskiya *Afnan* tausayi take bashi.


Ya kuma ce mata "wannan abun da yafaru karta fad'awa kowa tabarshi iyasu uku da suka sani, har *Kaka* karta fad'a mawa."


Nan ta share hawayenta tace "insha Allah *Baba* ba Wanda zanfad'amawa,
Sukayi sallama ko wannensu yashiga gida."


*Bassam* kuma tsaye yayi yana kallonsu sai da yaga sunshige gida, sannan ya girgiza kai ya cije baki, cike da maye yake tafiya zuwa wurin motarshi yashiga yajata da k'arfi yabar layin
πŸ‘‘ *TAMBARIN SARAUTA*🀴
πŸ‘‘. 🀴 πŸ‘‘




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)






*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


_we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_








#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com






*2*










" *Afnan* na shiga gida tareda sallama, *Kaka* tayo kanta ta rungumeta tareda ajiyar zuciya mai k'arfi, sannan daga k'arshe tace " *Afnan* ina kika tsaya?"
Gaba d'aya kin d'aga min hankali, tund'azun nakasa zaune na kasa tsaye ke kad'ai nake tunani a zuciyata ina Addu'ar Allah yasa ba wani abun yasameki a kan hanya ba."


Murmushi *Afnan* tayi had'ida zame jikinta daga jikin *Kaka* sannan tace "tsuhuwa mai ran k'arfe babu abunda yasameni a hanya, kuma lafiya k'alau nake."
Abunda yasa muka dad'e malam *Nura* ne ya tsayar damu har sai lokacin da muka iya karatunsa."


*Kaka* tayi dariya sannan tace "Kai Allah yayi malam *Nura*Albarka yasa yazamo mijinki har a gudan Aljannah, domin yanda yake kula dake da kuma karatunki inajin dad'i sosai."


*Afnan* tasaki wata kalar dariya domin *Kaka* tayabi masoyinta,
Cike da murmushi a fuskarta tace. "Kai *Kaka* kinsanfa sainayi karatu sosai nazamo cikakkiyar lauya,
domin sai na amso dukiyarmu a hannun azzalumi can, Alhaji *Aminu* sannan kuma daga k'arshe nayi masa hukunci dai dai da abunda ya aikata mana."


Idonta ya cika da hawaye, ta rab'a *Kaka* tashige d'aki tashiga zubar da hawaye."






*Wacece Afnan*?"
Mahaifin *Afnan* Alhaji *Ibrahim Sani*
cikakkin bakane ne, a anan cikin garin kano yake da zama, yana kasuwancinsa Nijer zuwa Dubai, idan ya d'auko kaya zai shigo dasu garin kano ya sayar, ko kuma yasara a kano yakai Niger ko Dubai yasayar."
Allah yayiwa Alhaji *Ibrahim* rufin asiri dai dai kwarkwado, Wanda ya d'an manyanta amma beyi aureba, ya gina katafaren gida daga shi sai mahaifiyarshi ke zaune cikin gidan, kullum maganar Hajjah mahaifiyarshi itace "yayi aure,


Domin itama mahaifiyar tashi rashin yin auren nashi abun yana damunta sosai kullum maganar ta d'ayace "yadaiyi aure."
Ya kuma samu mace 'yar gidan mutunci ya aura, amma zaman shi a hakan ba aure be kamata ba."


Kwatsam wata rana yaje garin nijer saro kaya yaci karo da wata kyakkyawar mace mai natsuwa da kamala,
Anan take yaji tashiga ranshi kuma yashirya zai aureta."


anan take yaje yayiwa *Liman* magana akan yanaso abashi auren yarinyar da yagani,
Ai kuwa dasa hannun mai *Liman* aka aura masa aure da *Halimatu Sadiya* wato mahaifiyar *Afnan* ba dan Mahaifanta naso ba."


Mahaifiyar *Afnan* 'yar asalin Agadas ce, irin buzayayen nan ce na Agadas masu masifar kyau kamar sune suka halicci Kansu, saboda kyau da diri."


A can Alhaji *Ibrahim* ya gano *Halimatus Sadiya* ya aurota, yakawota mahaifarshi garin Kano ya ajiyeta gida d'aya da mahaifiyarshi *Hajjah*


*Hajjah* najin dad'in zama da *Halima* domin kuwa bata da matsala sai dai rashin jin hausar da batayine, koshi kad'an kad'an zatafara ji."


Haka sukaci gaba da zamansu cikin jin dad'i da kwanciyar hankali da walwala, Alhaji *Ibrahim* kuma kasuwanci sa sai bunk'asa yakeyi, domin yanzun Alhmdulillah kud'i sun zauna masa sosai Wanda har ana iya sanya lissafinshi a masu kud'in garin kano."


Alhaji *Ibrahim* yana da wani Aboki ko kuma nace babban Amini mai suna Alhaji *Aminu* Wanda yakasance ya bashi amana Sosai,
duk wasu harkokishi na kasuwancinshi babu Wanda baya fad'awa Alhaji *Aminu* domin ya yarda dashi, kuma yayi Imani da cewa Alhaji *Aminu* bazai cutar da Shiba."


Shi kuma Alhaji *Aminu* a wurinshi ba hakan bane, domin a zuciyarshi babu Wanda ya tsana, yake kuma hassadarshi sama da Alhaji *Ibrahim*."


a gabansa zai nuna masa so,
sosai a bayan shi kuma yana muna furtanshi, burin shi a d'aya a kullum yaga mutuwar Alhaji *Ibrahim* ko kuma yaganshi ya durk'ushe ya talauce."




___________________________


Haka dai Rayuwa taci gaba da tafiya tsakanin Alhaji *Ibrahim* da matarshi *Halima* rayuwa sukeyi cike da jin dad'i da kulawa,
kwatsam tafiya takamashi zuwa Dubai d'auko kaya, a lokacin *Halima* tana d'auke da ciki na tsawon wata tara."


Tun lokacin da ya fad'a mata tafiyar taji hankalinta be kwantaba, kullum idan yafita cikin kuka take domin ganin takeyi kamar idan ya tafi bazai dawoba."


Idan yaga tana yawan tunani zai dinga kwantar mata da hankali a kan cewa, "tasanfa ba yanzun yafara tafiye tafiyeba kuma da yardar Allah yanda yaje lafiya haka zai dawo lafiya."


Haka dai ya dinga kwantar mata da hankali har lokacin tafiyar yazo,
Ana gobe zai tafi saida yasaya mata komai na haihuwarta, domin a koda yaushe tana iya haihuwa,
Bayan yasaya mata komai kuma yafad'a mata sunan da yakeso a sanyawa abunda ta haifa, "idan mace ce, yana so sanya mata sunan mahaifiyar shi, *Ayshart* adinga kiranta da *Afnan*."


idan kuma namiji ne yana son a Sanya mashi suna Abdullah."


Kuka tafashe dashi, tana fad'in "Dan Allah Alhaji kadaina fad'in hakan, sai nadinga jin kamar wasiyace kake barmin,
"Wlh duk tafiyar da kakeyi bantab'a shiga tashin hankali sama da wannan tafiyarba."


Jawota yayi jikinshi yana fad'a mata kalamai masu dad'i da kwantar da Hankali."


Ahaka dai har hankalinta ya kwanta tana murmushi har barci yazo yayi awon gaba dasu."


Safiya na wayewa yashiga had'a kayanshi tana taimaka mashi, amma zuciyarta a dagule take,
Haka tarakoshi b'an garin *Hajjah* domin yayi mata sallama."


Bayan sungama sallama da Hajjah tayi masa fatan Alkhairi, anan ne yaciro wani zobe na azurfa mai kyau, a hannunshi yana murmushi ya mik'awa *Hajjah* yace "gashi ki ajiye a wurinki idan yarona ko yarinyar da za'a haifamin yakai shekara 12 ki sanya mata a hannuta, domin kinfini iya ajiya."


Ta amshi zuben tana murmushi had'ida yimashi addu'a da Sanya mashi albarka, sukayi sallama gaba d'aya yatafi."


Misalin k'arfe hud'u na yamma *Halima* na kwance a kan kujera taji ana sanarwa a gidan redio cewa "jirgin da yatashi zaitafi Dubai misalin k'arfe uku na rana, ansamu labarin yayi had'ari kuma rahoto yabada cewa duk mutanen da keciki babu Wanda yarayu."


Batasan lokacin da tasaki wata kalar k'araba ta fad'i k'asa a some."


Jin k'ararta da Hajjah tayi yasan yata yin saurin nufo b'angaren nasu domin ganin lafiya meke faruwa?"


Da Sauri ta k'araso tana fad'in "lafiya Halima meke faruwa?" kike kuwa hakan?"


Dakatawa tayi da tambayar ta, saka makon mugun labarin da taji ana sanarwa a gidan redio."


Cikin tashin hankali da k'arfin hali,


tayi kan Halima Wanda ke kwance k'asa a some ga tsuhun ciiki a jikinta."


Cikin gaggawa takira direba suka tallabeta suka nufi asibiti da ita."


Likitici suka dukufa kanta domin bata taimakon gaggawa,
Dakyar akasamu ta sauka lafiya ta haifi 'yarta Mace, kyakkywa sak mahaifinta wani b'angare kuma tana kama da mahaifiyarta."


Kuka ta fashe dashi, ta kamo hannu Hajjah ta dank'amata jaririyar a hannunta tace " Hajjah "gata ayi mata hud'uba da sunan da mahaifinta ya bar wasiya a nad'a mata,
wato *Ayshart* *Afnan*


Taci gaba da cewa "Hajjah ga Amanar *Afnan* nan a hannunki, nasan bazaki cutar da itaba, amma idan ta girma kibata labarin cewa mahaifanta na tsanin sonta,
Domin nasan nima bazan tashi daga wannan rad'ad'in ciyon da zuciyata takeyi min ba, "Hajjah ki yafemin duk abunda nayi maki."


idan kuma mahaifana suka zo amsar gaisuwata kice masu suyafe min."


Tana kaiwa nan tadinga kalmar shahada anan take Allah ya k'arb'i abarshi😭


Hajjah taga tashin hankali wanda sai da tayi Neman hawaye amma ta rasa."
Fita tayi rungume da Afnan ta kira likita, anan likita ya k'ara sheda mata
Da cewa "sai dai hakuri domin *Halima* Allah ya karb'i abarshi."


Haka direba ya d'auko gawar *Halima* ya kuma ya d'auko gawar Alhaji *Ibrahim* a kayi masu wanna lokaci d'aya, a kuma mak'abarta d'aya aka rufesu."😭


Bayan mutuwar nahaifan *Afnan* da sati biyu, saiga Alhaji Aminu yazo tareda 'yan sanda, sukayi sallama da *Hajjah* tafito."


Tana fitowa taga 'yan sanda a tsaye a k'ofar gida, saida gabanta yafad'i amma ganin tare suke da Alhaji Aminu* sai taji sanyi tayi murmushi hankalinta ya d'an kwanta,
domin yanzun Alhaji *Aminu* take gani kamar Alhaji Ibrahim."


sai Tace " *Aminu* kaine kuma ka tsaya a waje kamar wani bak'o?"
Kashigo daga ciki mana."


Be tanka mataba sai dai yaba 'yan sandan umurni dasu shigo."


Bayan sun zauna ne, Alhaji *Aminu* ya kalli *Hajjah* yace mata, "* Hajjah* munzo ne domin maganar dukiyar Alhaji Ibrahim, domin tun lokacin da zaiyi tafiya ya barmin wasiya da cewa wad'an nan bayin Allah,
suna biyarshi miliyan arba'in, tareda gida uku wad'anda Dama be biya kud'in gidajenba."


Sannan kuma "wannan gidan dakuke cikinshi da sauran gidajenshi guda biyu manlakina ne, domin tun kafin yatafi yasayar min kuma nabashi kud'inshi."


"Kuma Munduba account d'inshi babu wasu kud'i a ciki illah miliyan shidda, duk ya tattara kud'inshi yatafi dasu Dubai kuma sai ga yanda ta Allah ta kasance dashi."


Hajjah dake zaune rungume da Afnan tana barci, tunda Alhaji Aminu ya fara magana take kallonshi domin tasan ba gaskiya ko kad'an a maganarshi, domin duk abunda Ibrahim zaiyi sai yaneme shawararta idan ta amince ya aikata idan kuma bata aminceba bazaiyi aikata shiba duk yanda yakeson abun nan zai barshi."
πŸ‘‘ *TAMBARIN SARAUTA*🀴
πŸ‘‘. 🀴 πŸ‘‘




*NA*
*UMMU SAFWAN*
( Farida Bashir)






*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


_we don't just entertain and educated we tauch the heart of the readers_






#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com








*3*








"Kallo *Hajjah* tabishi dashi cike da tuhuma,
Sannan tayi k'arfin halin yimashi magana tace " "Amma *Aminu* kabani mamaki a tunanina ko wani kaji labarin zai cutarmu zakayi mana tsaye tsayen daka domin ganin ka karb'ar mana incinmu,


Idan kayi dibo da irin haliccin da marigayi *Ibrahim* yayi maka, amma sai gashi abun mamaki kai da kanka za a had'a baki dakai a cucemu, domin a kwace dukiyar marainiyar Allah da k'arfi da yaji."


Amma bakomai rayuwace dama duk Wanda kake ganin zai taimakeka wata rana shizai sanyaka a rana."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login