Showing 33001 words to 36000 words out of 165901 words

Chapter 12 - SAMARIN SHAHO Completed Book Surayyhms.txt

Advertisement

Surayya   

06 Jun 2024

13839

of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*


_YOUR BIRTHDAY IS OF NO DIFFRERENT TO MINE,we are two living bodies in one soul,i love you to the moon and back#temi tope adeniyi happy birthday to us._




_PAGE 10_


Nazo cikin kasar india a washe garin ranar da za'a bamu cikakken gurbin fafatawa na zaben kwanaye da zasu samu karin girma da daukaka a harkan career su na gaba..


_Dev singhania imperial_ _college of human right and philantropism india_ .


Kasashe bakwai ne muka samu shiga kama daga China,india,south africa,nigeria,usa,bahrain sai mu yan france.Anan duka muka hadu 7 first class students team daga makarantu daban daban wanda suka samu shiga kenan kuma ba bata lokaci aka fara fafatawa..


Wata shida ne kawai so Kowa akan bashi cases na true life events aga iya kaifin basirar sa da hikimar sa.


"abubuwa dayawa sun faru Daga kadan kadan ake disqualifyn teams yanzu haka saura team biyu ne.
France and india.




" anan mahfud yayi ajiyan zuciya mai nauyi duba da lokaci ya tafi sosai,asubahi ya kusa dosu su..sai ya dada kame hannun sarah dake tayi pouse itama sai ta da ta kankame shi da shi don ya gyara musu position din su sarahn tana daga kwance ajikin sa,


Shiru ne ya ratsa wajen sarah bata sake furta komai ba,da shike ma ayayin datake maganan tin daga farko sunyi kukan zuci sosai amma yanzu hawayen ne kawai yayi saura a fuskokin su.


Duk jikin sa yayi tsami kuma ya sace sai ya sa hannu zaii tallafo ta ,kafin yayi wani juyi sai ta dan kwace kadan daga jikin sa tana shirin mikewa tsaye..


Still suprise da yaga tana layi har yanzu amma sai ya daure ya kure ta da ido har ta tsaya da kanta ta harde hannu tana maida masa kallon nitsuwa..


Tace"gashi yau na zo fafatawa na na karshe and i just completed my final rounds today"my hero,ta dan dube mahfud din tace "kasha cemin zan lashe gasar nan,cos u have full confidence in me ko?


Ya gyada kai a hankali


Ta dan tabe baki a takaice Tace
I too feel the same way..nima na yarda da kaina sosai akan haka, na dauka ko zan iya taimako a kowani irin yanayin rayuwar da dan adam zai shiga a duniya..


Na dauka ko kwakwalta da zuciya ta tana shirye da daukar ko wani labarin cin zarafi na rayuwar dan adam....


Kaima ka yarda da hakan Ko?


Kafin ya gyada kai tayi murmushin takaici gami da share hawayen ta da suka dada saukowa"


A hankali ta furta "but i dont think i can handle it anymore,i dont wanna win anymore.i think its over mahfud ive lost my confidence today..
anan ta karashe cikin wani sassanyar kuka mai dauke da raunin zuciya.




Yana shiru tukun but He clearly understand her "yanzu yake fahintar komai wato case din da tayi na karshe na matashiyar budurwa vashika da mahaifiyar ta shi ya sake tuno mata bakar rayuwan da suka binne da ita da ummahn ta"a baya


Shima kukan ne ya kufce masa marar sauti,amma sai ya cije yana share hawayen sa a dabaran ce


Anan ya mike ya karaso daf da ita ya na shirin kamo hannayen ta dake karkawa tare da sautin kukan dake fita.


A nitse Yace"Sarah....cikin hankali ba tare da ya sake magana ba ya shiga jawo ta jikin sa don ya taya ta calming mood din ta,anan sai ta birkice masa cikin kukan dake cinta rai sosai tana cewa no,kar ka ce komai mahfud..nasan bazaka taba cewa bazan iya ba...but believe me im weak,i cant..im helpless now.


Zai sake magana ta dakatar da shi tace"....

"Ka tsaya kaji ni,im just like that girl vashika kaina nake gani a rayuwan ta mahfud,na daure na daure sosai...but everthing its toturturing me...ko haryan zu baka fahimce ni bane..hero, vashika is just like me babu wani banbanci...!


sai dai me ya faru da mahaifiyar tan da tayi tunanin da na so da ace ummah na tayi wajen kare mutuncin ta?she too was raped countlessly on the street,mahfud maza shida suka keta haddin mahaifiyar vashika duk don akan ta na neman taimakon da zata rufa nakan ta asiri batare da ta watsar da kanta ba


But vashika is dead now"Yanzu duk da mutuncin mahaifiyar tan ma ya tabu don ta bata lpya da kariya it all in vain?...ai gwara mu musulmai ne, but them they sufferd alot sabida tsananin al'adan dake zagaye da abubuwan bautar su da kuma dokokin tsarin tarbiyan su...life is soo unfair to them hero.


"vashika ta mutu,she died with her dad's uncompleted child...irin wahalar dana sha shi ya kashe ta,yanzu maman ta na fama da radadin zuciya irin wanda muka ji dani da ummah na bakar qaddarar rayuwa,ga fama da sabon ubangiji da rugujewar tarbiya,amma kaga ni nata ya dauke mata yar ta ,ita kadai ne yanzu a duniyan nan sai tarin bakin ciki da kunci...
I think her own is even worst.


Tun da na fara case din na nake ganin abubuwan da ummah ta so nagane ada chan amma ban gane ba..


Dazun da muka je wajen gawar vashika Naso na ba mahaifiyar ta tabbacin rayuwar ta zai banbata da yadda take tunani,i wanted to be there for her
...
But she told me alots of things,abubuwan data gaya min shi ya dada karya min zuciya ta,..


abunda yafi damu na shine tace"da ta san in ta tsaya jayyaya wajen bada kanta wa wani namijin tun farko zai kawo karshen rayuwar vashikan ta da bata bata lokaci ba but tayi jayayyan a farko ta kare mutuncin ta agaba kuma she was raped mercilessly for the same reason,..
it was also a hard time for her kamar yadda ya fada kan ummah na,..now i get it
Shiyasa kawai sai na fara tunanin kaina..


Abun ya dame ni sosai...
Yau na fara jin ashe bazan iya daga kowani gwiwa ba...she lost all hope


my heart becomes so heavy,inajin zafin abun araina fiye da yadda kake tsammani..
Sai dai bansan nauyin da yayi zai iya hanani sukuni ba,
I lost control over myself mahfud..
catherine ke tare da ni,ina ganin kuma ta tsora ta ne Shiyasa ta bani giya,ai kasan bana sha ko?


Shi dai kallon ta kawai yake tana pouring heart din ta...
jimami take yi ciikin wani shakurarren kuka ta kuma cewa"huhhh amma bansan meya sa na sha ba yau din im sorry...




Kuka ne mai karfi ya kufce mata wanda yayi kokarin kaita kasa cikin tsumayin sa da rudewar tunani..


This time around mahfud bai bari hawayen sa sun sauko ba, ya kamo ta jikin sa ya dan rungume ta batare da ya fadi wasu kalmomi masu yawa ba ya shiga rarrashin ta yana ce mata its ok..


A lokacin ana neman karfe hudu da minti arbain da biyar na safiya,...


Duk hankalin sa ya gama tashi ya rasa meke masa dadi..


Bayan kamar minti 10 da sassauata kukan nata ya shinfida ta akan gadon ya shige bathrum ya hada mata warm bath...
cikin lallami ya sa ta shige ciki ta kimtsa kanta..


Gaba daya baida gwarin gwiwa,amma hakan ya kaucar da duk wani tunani aran sa ya hada mata warm milk..


Daure da towel ta fito daga wankan kanta ne ke bugawa sosai sabida halin data ke ciki ga azaban gajiya da bacci dake bin jijiyon ta she's super stressed




Dakan sa ya kamo hannun ta ya zaunar da ita gefen gadon ya dauko milk din yana bata a baki har ta kai karshe

Tun kafin ya kai cup din kan take ta kishingide ta lumshe idanun ta tana maida nunfashi ahankali,


Kallon tausayi ya tsaya binta da shi tsawon minti goma bai motsa ba...
Ko da ya dan yi yunkurin taba ta don ta shi ta suturce kanta a gani yayi ta sake sai ninshari take mai dauke da ajiyan zuciya....


Gwanin tausayi ya shiga shafo gefen fuskan ta"cikin wani yanayi da zai tabbatar maka alkwarin sa da tabbatacen amanar sa a kanta da yau ya kulla azuciyan sa..


Lallai wannan babban ciwo ne a zuciyan ta amma ta zabi ta gaya masa a duk da ma bata cikin hankalin ta...


Tunani yake shin sarah ma tana jin irin abunda yake ji aransa game da ita kenan..? Gani yake kawai don ita akayi shi a duniya duk dama bai taba gaya mata yana kaunar ta ba, sosai kaunar tan ke ratsa hanyoyin jinin sa...


Dama ya taba sawa aransa cewa tabbas rayuwar sarah na baya suke masa katanfmga daga bayyana mata yadda yake kaunar ta kuma yake son ya kasance da ita..


Amma yau komai ya wuce tunda ta sanar da shi mafi munin labarin ta amanan ta qaddarar ta da raunin ta...


Dama shi kam bai boye mata komai game da nashi rayuwan ba duk dama babu dadin ji, amma ta nuna masa iya amanan ta da tausayin ta, ta bashi karfin gwaiwa..he knew he have to do the same now dan ita ma ta bude masa nata..


Toh me ya rage in ba ya gaya mata yana kaunar tan ba,?kallo ya sake bin ta da shi, cikin ransa ya titse yana rokon Allah ya sa sarah ta amince da shi yace" insha Allahu ni zan aure ki i will wipe away all ur sorrows sarah...im here . Ya karashe ahankali yana dada duban kyakywanr fuskan ta.


Sake saken kauna amana da tausayi zuciyan sa ke kan sakawa ayayin da ya gyara mata kwanciyar nata ya rufe ta da soft duvet comforter sa Ya juya ya shiga bayi..


Wanka yayi shima ya sauke nauyin dake dawainiya da zuciyan sa...
Kafin nan biyar ya buga ana shirye shiryen kiran sallahr asubah.


Sai ya dakata yayi sallahn sa sannan ya kishin gide gefe da ita atake wani gajiyayyen bacci yayi awon gaba da shi..




Bacci mai cike da yanayin ajiyan zuciya suje kwasa dukan su biyu musamman ita sarah da shike yanzu ne giyan ke asalin fita a jikin ta.....juyi take son ranta tana neman juye nauyin zuciyan ta akan baccin.


Sai wajen 7.56am ta bude idanun ta gani tayi haske ya dan fara dokar windown sa da shike upstairs ne kuma windown glassses ne..



Shiru tayi na dan lokaci daga kwancen kamar bata gane inda kanta yake ba tukuna..don sosai kanta ke warwarewa lokaci guda ta soma tunanin abuwan da suka faru jiya...


Bit by bit komai yake dawowa mata wani mummuanan tsoro da fargaba ne ya ziyar ce ta take ganin kamar a mafarki komai ya faru...


daga cikin bargon sai tayi juyi a hankali tana feeling naked bodyn ta dga cikin towel din dake neman karkacewa da kansa anan ta dafe kai cikin rudani ta juyo a dan sace "don ta tabbatar makanta ba tare da namiji yau ta kwana ba ...


But where is he? Don ita kadai ce yanzu akan gadon ba kowa


Ko da taga yanayin kwanciyar sun a shatin bedding din She has to closed her eyes tsam tsam sabida wani azabbaben kunyar da ya rufe ta,nan ta daure dai ta shiga duba ko ina da kwayan idanun ta anan ne take ganin alaman kamar wani abu ne ya faru wanda bai kama ta ba..


Har ta fara Kawo tunanin sai kuma rudewan tunanin hade da tashin hankalin tuno da abubuwan da tayi jiyan ya sa ta mike a kan gadon da sauri kamar mai ciwon hauka ...


Zuciyan ta har na sama da kasa tsaban ta rikice
MAHFUD!!!!!ta kwalla masa kira amma shiru babu shi,


Da sauri ta Ja curtain din dake jikin window tana duba saba t inda ya saba tsayawa bata gansa...


Cikin rudani ta juyo nan idon ta ya ci karo da wasikar sa akan madubi..


Da dark blur pen ya rubuta"
Zama tayi gefen gado bayan ta dauko
Tafara karantawa a hankali"


_"forgive me..da na jira har sai kin tashi a bacci na fada miki but im helpless.. heroien, nasan zaki iya wannan don kin riga da kinci gasar_
_u won the battle of your destiny, and for this you must win too.. becos your confidence is still with you,abinda ya faru jiya ki dauka ba komai ba ne illah wani qaddarar da_ _rayuwar mu ya zo mana da shi tare dake..idan kin tashi ki shirya kije ki karasa abun da kika fara.i will neva let you back down from this.. A yanzu ne kike da bukatar ki zama abunda kike so a rayuwan ki..yau nasan idan har akwai digon yarda dani azuciyan ki zaki fahimci me nake gaya miki yanzu wanda bazan iya fuskantar ki na fada miki ba_


_go sarah lokaci yayi da zaki zama macen da kike buri,today i feel like im not ur role model but ure my role model._
_Zan jira ki anan sama idan kin karbo abun da ya kasance naki ne ki taho ki same ni,i have a confession to make_ .


_yours Mahfud lingard_








Sauke ajiyan zuciya tayi tayi zugum cikin radadin tunanin yadda ta zubda kan ta ajiyan gaban sa,komai ma cunkushe mata yake dada yi a zuciyan ta da kyar ta lallaba ta shiga bath ta kimtsa kanta sananan ta dauro alwala tayi sallah..




Duk jikin ta a muce yake..musamman idan ta tuno da abubuwan da ummah ta dade tana mata tsoro game da bayyanar siiririn su a wajen wani"musamman namiji," wa iya zubillah me ya kaini shan giya'tafada makanta cikin zazzafan nadama.


Hawaye ne suka wanke fuskan ta tuntuni ta ma arasa wani tunani daya zata bada hankalin ta kai..


Amanan su da ummhan ta data ci wajen bude sirrin ta jiya ma mahfud.


Ko nadaman shan giyar data yi ta bata kimar ta a idon Sa..


"Koko zata rufe ido ne kawai ta fuskance aBunda mahfud din yake gayawa mata a wasikar sa..


Sam ta kasa sa hankalin ta waje daya..




Ta dan jima a haka daga bisani ta tashi ta shirya ta fuce zuwa masaukin ta..




Da shike bata taba kwana wani waje ba ya sa yau take ji daban da tambayoyin da sauran team mates din ta ke mata..


Amma bata cikin yanayin da zata amsa ma kowa maganan sa musamman cath da ke shakkun abunda ta aikata mata ajiyan.


Shiri tayi mai kyau ta kama hanyar Fara aiwatar da shawarar da ta yanke na karshe aranta..




After 6 hours misalin karfe 4.30 na yamma
Devh singania imperial college cike take dam da mutane da manyan officials don tabbatar da sakamakon fafatawar..




Ana daf za'a fara sarah ta samu damar isowa...


Duk dama Tayi duk abubuwan data ga ya dace amm Still zuciyan ta bai kwanta ba da taga babu mahfud anan din..


Anyi speech masu ilmantarwa cike da tunatar musu da su wanene a idon jama'a..


Duba da su mutane dayawa afadin Duniya musamman kaskantatu marasa galihu zasu na kallo a field din aikin su yanzu
Yasa Board members na humanatarin activist da human right suka bada gargadi mai tsauri akan su jajirce wajen kare nasu tarbiyan su kafin suce zasu karbe ma wani dan adam nashi hakkin...


A cewar su Bazai yiyu marar mutunci da kima ya yi ikirarin zai kare hakkin dan adam ba..


Darajah, tausayi,mutunci da jajircewa wajen basiran zama da al'ummah Shi ake fi bukata don kare suna da martaban organisation din Gaba daya na duniya


Don haka ba bata lokaci


Aka sanar da sakamakon gasar,
Sai dai wannan karon daban ne..sabida yarda kowa ya nuna zakowar sa ma wayannan jajirtaccun dalaibai


A cewar su kowa yayi kokari amma team din da suka basu daman shiga org sunfi kowa nuna tausayin su da kulawar su..uwa uba jajircewa da gskiya.


Sarah bukar ita ta jagiranci award din da kuma licenced din sa aka bada kowane memebr team din ta..




Murmushi mai dauke da Kuka ne ya dan kufce mata amma ta kasa bari ya sauke mata da hawaye...


Shikenan burin ta ya cika..


Mahfud is always right gashi ta sake tashi
Ta bada mahaifiyar vashika karfin gwiwa a yayin da nata ma ya dawo mara..


Taga mutane kam ba adadi,
Musamman ma Memebers din sabon office din da zata fara aiki da su na human right


Tun daga nan suka fara dada cusa mata ra'ayin kara zage damtse wajen daukar aikin ta da muhimmanci ....




Sosai abun yayi tasiri a zuciyan ta..musamman da yazo a yanayin da take ciki na wani nl rauni da rashin Sanin Me zatayi nan gaba..






Bayan waje ya lafa kowa ya dan watse hutun sati biyu da aka bata take so ta koma gida gaba daya nigeria tun da yamma ya rufa sai ta sa aranta Haduwar su sa mahfud anan sama sai da dare


Dama abubuwa da yawa na damun Ta game da haduwar nasu


Kunyar sa take ji yanzu, sannan zuciyan ta na matukar bugawa musamman idan ta tuno da yanzun yasan sirrin ta da duk abunda take ciki a rayuwa


Hakan ya sa ta nitsu sosai ta shiga kundun tunani


bayan ta gama shirin ta tsaf misalin karfe 10 saura na dare ta taho rai walia hotel..




Ta dan kwan kwasa door din Shiru
Hakan ya tabbatar mata da cewa yana chan saman kenan ba bata lokaci ta bishi..


Anan yaje ya bada kofa baya yana kallon bakin titi daga saman verandar benen daya zauna kamar yadda suka saba..


Durus ta tsaya tana bin kyakkwar hallitar sa da ido duk dama yasan ita din ce ta zo amma bai juyo ba tukun..




Shiru ne ya ratsa wajen na dan mintoci


Bugun zuciyar su na dada karuwa..
Gani take kamar bashi ba..


Haka shima ya dade da shiga wani yanayin da bazai iya fassara shi ba..




Har ta iso daff da shi, hasken bakin suman kansa sa da ya dada haska fatar sa dake shekin kyau ke dada dauke mata ido..


A sanyaye ta dan dafa kafadar sa wanda ya sashi lumshe idanun sa yana zugar iskan daya zo da sabuwar kaunar ta da tausayin ta aranshi...


Hero,I did it..
Tace cikin sanyin murya mai dadi da ke sarkafewa har yana cracking cikin kunnen sa


Tana jin yadda yake gode ma Allah duk dama bai fada da karfi ba..


Hannun da ta dafa shi ya kamo a hankali ya juyo ya kure ta sassanyar idanun sa..


Sun dade a haka suna kallon kallo kowa da kalar abunda yake ganowa .


Sai dai a lokacin Bayan Tsantsar so da kaunar Har da tsoro da fargaba na gauraye da nunfashin su..




A karo na biyu data yi yunkurin sauke idanun ta daga nashi,don sosai zuciyan ke ke naman rikita ta ta rasa sukuni..


Gashi ra riga ta yanke shawarar ma rayuwan ta..


Cikin sanyin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login