Showing 9001 words to 12000 words out of 165901 words
Chapter 4 - SAMARIN SHAHO Completed Book Surayyhms.txt
waje anan ne ma ta san cewa dagaske inna wuro na raye tana kuma family house dinsa tare da sauran matan sa
A nan ma sai da aka tada zaune tsaye sa ummah ta sake maimaita abunda ya faru ko da zasu fahimce ta amma hakan bai faru ba
Karshe ma a hannu a hannu aka dawo da ummah kamar mahaukaciya tana surutu.
Sanadiyar kokarin bin gaskiyar ta ya sa Duk garin sai aka daura mata laifi aka ce itace batada mutunci..
bata da gaskiya ai baba babaji baice komai ba itake tada hankalin jama'a..
Babu wanda Ya taba tsaya mata in ana zagin ta ana cin zarafin ta amma kowa yana bada muhimmaci sosai akan reaction din ta da zatayi don ta kare kanta..
Ranar da kwana uku suka cika da asubahi da azabbaben amai na tashi kamar zan cire hanjin cikina na..
Sosai hankalin umma ya tashi sosai don ita ta zo kaina..
sai yanzu ne ma take kallo na da kyau take
Gane yanayi na
Don dama Sosai jikin ta ya dan bata kamar ena dauke da juna biyu amma dai tayi saurin dannewa tana tayani kintsa kaina..
Kaina na kasa ina kan Jin Abubuwa da dama na ci na a rai nan na fashe da kuka mai radadi
"Ummah Tana dago ni na shiga kukan da dan sauti ina rawan dari gaban ta..
Tace Saratu? Me ke damin ki dama baki da lpya ne ? Cewar Umma tana kure ni da ido cikin dauriya.
Ina sane da yan labe dake jin mu amma haka na cire komai araina na mata bayanin komi daga tushen sa ban boye mata abunda ya faru ba koda na miskala zarratin daga abubuwan danake fuskan taba har yanzu
Umma ta rike ni gammm amma bai hanani jin karkarwawa da tsuman da take yi ba.,
Magana take so tayi amma muryan ta ya sarkafe yana fidda i i na tsaban bacin Rai ji kawai nake tana" b..aaa. .baji,
Dum umm..a ta yanke jiki ta fada gaba na summamiya..
tun kafin Na tsala ihu aka yo chaaaa akan mu jikin umma na fada ena bata hakuri ena kuka..
Ruwa aka dan yauyafa mata kafin ta farfado a kasale Ta kalle ni gaban ta duk na gama fita hayyaci na kuma ban fasa ba..
Ido tabi kowa da shi batace uffan Ba tayi yunkuri ta tashi ta kamo hannun na muka shige daki...
Munaji ana rade raden maganan ana raba gulma a tsakar gida..
A kan gado ta zauna Hawaye kawai take yi agaba na ta riko hannu na sai sheshheka nake tace"Allah sarkii diyata ki yafe ni, kaico na saratu, ni nayi silar shigar da ni dake cikin wannan mugun rayuwa kar ki sake daura makanki laifi ni na jawo mana fitina arayuwan mu dana auri babaji,.
Gashi ya lalata na nawa ya lalata naki tace sarahtu Inaga fa babaji kamar ciki yayi miki.
Cikin wani irin bugun zuciya Na dada kame hannun umma na fashe da kuka mai tsumayin radadi da
Tashin hankali..
Wayyo Allah na imma na shiga uku Ciki fa kikace ummah?
na daura hannu na akai hawayen na har turririn zafi suke fiddawa ena kan kuka ina cewa na shiga uku...
Tausayi yasa Umma ta jawo ni jikin ta amma
Shiru ne ya ratsa wajen
Aka rasa wanda zai dakata da nashi kukan kuncin da kyar ummah ta dago ni " idanun ta sunyi jajir tausayin ta tuni ya gauraya zuciyata naji inama ace mutuwa mutum ne da nace ta dauke mu baki daya mu huta da duniya...
Ummah ta shiga shafa fuska na cikin kulawa " yace kiyi hakuri saratu, duk da ni jahila ce yau nasan mutum ne kawai bai wuce qaddarar sa, kin kare kanki a bayan ido na ,nasan da alokacin ma ko kin gaya min ba shi zai hana ya sake fito da wani mummunan hanyar cimma burin sa ba, nima nan kinga abunda ya min ban aikata komai ba amma yanzu na dauka abubuwa da dama akaina...
in har Goguwar munafurcin babaji yafi karfin kowa nasan karyan shi ya ja da Allah don
Shi ne gata na dani dake..
nayi miki miki alkwari saratu bazan taba barin ki a wani hali ba har na mutu ina tare da ke yata sai na karbe miki rayuwar ki daga bakin qaddara dayake so ya jona miki..
Na sake sauke hawaye na rungume ummmah ina kuka bata fasa rarrashi na ba ta cigaba da cewa
kiyi shiru abunki,ko duk duniya sun guje mu ni dai nasan babu mai raba ni da ke har abada sai mutuwa.
Nace Nagode ummah, na gode da kika fahimce ni, nayi miki alkwarin biyayya duk rintsi duk wuya ba mai raba ni dake ummah ummah Allah zai saka miki Allah zai tona asirin kowa zasu ji kunya wata rana..
..Cikin shshesehka nake fitar da maganan da kyar
Ummah bata ce komai ta shiga share hawayen ta tana kan bubbuga gadon baya na a hankali
A hakan muke zauna cikin bakar kunci da jiran abinda zai faru nan gaba gidan sarki.. abincin ma na gaban mu amma bamu wani masa cin kirki ba.
Yau ne ummah bata fita neman babaji ba don tasan duk yadda akayi ya gama shirya mana tijarar da zaiyi agaban sarki anjima.
Wajen karfe 3 saura aka aiko sako cewa bayan lasar ake so mu hallara acahn.
Sosai Gaba na yayi mummunan faduwa amma hakan na yi ta lazimi ina rokon Allah ya saukaka mana lamarin.
3.45pm Makil da manyan dattujan gari a kofar gidan mai girma shugaban kurwala..
Ladiyo, laure hansato da maman dukku da kishiyon ta rabi da hassana sai dukan kishiyoyi ummah da dangin miji watoh baba babaji da mata guda uku sune a gefe akan tabar ma duk suma babaji ya sa aka kira su domin shari'ar ..
Hmm jahilci baiyi ba , ashe idan abu ya kasance na cin mutunci baza a yi shi a sirri ba sai an taro jama'an gari?
"Hakan Ni kadai ya dama amma ummah na kam tun agida na lura da babu fuskan imani a tattare da ita sosai ta dauke fuskan rahma ta bushe zuciyan ta
Kamar wasu barayi haka aka gurfanar da mu biyun a tsakiyan fada kan tabar ma..
Sarki ya soma jawabi da jan hankalin mata da dai daikun matasan dake wajen akan illahn safaran miyagun kwayoyi acikin gari da sauran garuruwan makwabta,
Yace " na kira ku ne badon komai ba sai don na yi hukunci ma wannan baiwar Allah bisa laofin data aikata ma yankin nan ..yadda kowa in yaga ni zai san bada wasa muke yi,
Ummah tasha mamain wanna furucin A zuciyan ta tace Kenan sarki ya amince da maganan su har ya laka min hukunci? Tayi shiru dai tana sauraro
Anan ya sa maga takardan fadan sa ya gaya musu duk abunda ya faru da umma na ni kuwa nasha mamakin yadda aka juya kan zancen aka laka ma ummah komai a take hawaye suka wanke fuska ta .
Bayan angama Tuni dattijai suka hau zagi da bakar magana
Ana Allah ya wadar da ummah wasu suna cewa ashe duk halayen ta da aka santa da shi na nagarta da chan na munafurci ne?
Ni da umma bamu ce komai ba muna shiru
Sarki ne ya dakatar da surutun da ake cikin raderaden,
Yace"
Ya isa haka , ya kamata muyi abunda ya kawo mu..
Yace"A matsayin na na mai gari na bada dama wa duk wanda ya san wani abu mai alaka da lamarin wannan baiwar Allah muna sauraro kafin a fadi hukunci ta.
Ah'a ranka shi dade ayi mata hukuncin ta kawai..ga gaskiya boro boro me za ajirah?
babban aminin baba babji wato dan masani ya fada a zafafe
"Tuni wasu suka bi bayan sa nan ma har da mata kishiyoyin ummah ne kawai basu tanka ba
Nan ma sarki ya tsawatar ,
Yace tunda haka ne baria shi mijin ta babaji kawai ya fada mana ta bakin sa muji,kar kuma wani ya sake tsoma mana baki
Shiru ne ya dan ratsa wajen.
Sannan sarki ya dubi baba babaji yace yayi magana"
Har da gyaran muryan sa ya mike tsaye kamar mumuni
Farko ya fara da fada ma jaama'a wai ya auri umma ne sabida ya na mata kallon kuruciya zai biye mata hakkin ta amma halayen dayaje ya tarar da ita sun dade suna sashi mamaki,
Ana shiru ana jin sa.anan ya dada bata ma ummah na suna ya nuna a idon jama'a cewa bata da tarbiya,fitsarariya ce.
Nikuma Anan raina ya soma baci..
ummma kam na shiru ta dago tana duban sa cikin wani murmushi mai dauke da sarkakkiya.
"Yace ni bani da abun da zance tunda sarki da al'umman sa masu adalci masu girma sun kama ta da laifi dumu dumu kawai ayi mata hukuncin da ya dace da laifin ta...
nima ayafe ni domin da haka nake neman shaidar mutane da yan uwa cewa na saki gambo saki uku..bazan iya zaman aure da ita ba
"A take Ummah ta rangwada guda mai kauri mai sauti tayi wani irin dariya mai cike da jin dadin wanda ya nuna alama ko ajikin ta.
" Surutun da ake yi kasa kasa ya faadada aka cigaba da cece kuce matan nan kamar zasu tashi su buge ta kowa na zagin ta,
"Raina yayi mummunan baci da irin yadda ake nunawa ummah na ita barauniya ce kuma karuwa uwa uba marar tarbiya.
Jiri ne ya soma dauka na sai naji bazan iya daukar maganan ba cikin wani irin hatsalallen fushi da ihu na ce "ku dakata...!!!
Kowa ya dakata....
Tsit waje yayi da mamakin jin haka nasan wasu sun sha ko aljanu ne dani
anan na mike gaban sarki kamar mara hankali
Na tsaya
Cikin kuka Nace" hammma, kai sarki mai adalci ne ka dada dubawa ummah na bata da laifi akan abunda ake tuhumar ta ..
Ni Nasan gaskiyar abunda ya faru in ka bani dama zan fada maka.
Kowa sai yayi shiru
Baba babaji yau a munafukin sa ya fito Sai ya sauya kama ya zauna abokin sa ne ya tashi a zafafe zai kama ni da duka wai nayi rashin kunya da katsalandan a maganan manya anan Aka riko sa.
Sarki yace" kowa ya nitsu ..kar wani ya sake motsowa idan bajaka duk abunda nayi masa shi yaso..yace saratu ina jin ki mai gaskiyar da kika sani akan wannan lamarin.
Anan nayi ajiyan zuciya kukan dake so yaci karfi na ma na tukare shi
Nan na soma zuba labari A- Z yanayin zaman mu da ummah a hannun baba babaji har rakube da nake yi a gidajen mutane na fadi daliili na,
Kukan da nake yi anan yasa ummah na kuka itama
Har cikin ranta bataso na fadi abunda ya faru dani na fyade da cikim shegen ba.
Shiru ne ya ratsa wajen tabbas zuciyan wasu ya girgiza da jin oda side of story na dana umma dana bayar ..
Cikin magiya da kuka nace in har akwai karya acikin abunda na fada Allah ya wulakanta ni a cikin wutar sa...dan Allah ka bi mana hakkin mu bamu da kowa sai Kai sai Allah
Shikan sa sarki zuciyan sa ya girgiza amma sai ya daure ya juya yace ena babaji ?
A dan rude baba babaji yace ranka shi dade gani
Sarki ya dube sa cikin wani irin yanayin damuwa yace ka fadi tsakanin ka da Allah me kasani akan wannnan maganar ?
Nikam tuni ummah ta riko ni tana kuka tana lallabani yanzu kam duk masu bakin zagi sun dan rusuna ana dai kan sauraro
Anan baba babaji yace" uhmm ai daman ni nasan za'ayi haka ranka shi dade shiyasa ma nazo da shaiduna ga su nan.
Yayo nuni da manyan munafukan sa abokan sa aciki naga har da sageer.
Yace ma sarki "wallhy wayannnan da kake gani sunyi nisa wajen makirci da munafurci amma ni bazan yi dogon magana ba gaskiya ta ita ne zata fidda ni.
Ya juya kamar da gaske yace ma ummah wallhy gambo ba dai naji kunya ba sai dai ke kiji kunya yau sai na tona asirin ki.
Umma ta dube sa ta kar kada kai tana shiru .
*WATTPAD VOTE AND FOLLOW @SURAYYAHMS*
*OFFICIALCATTY🐈*
[2/23, 22:43] +234 802 646 5734: *🅱BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™/SUN6th/ 2019🔞
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
🍒🍒
_A TRUE SENSATIONAL STORY_
~_Story written by_~
*SURAYYAHMS*🔥
*OFFICIALCATTY🐈*
*_WATTPAD_ @SURAYYAHMS_*
@ IG:Surriem-sule_
*#Lovestory2018/19*
*#romance#purefiction*
*#Destiny at fault..*
*Any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison All my stories are strickly mine,beware copycats!.*
_this page is For_
_Xinnie nie_
_siyamah ta_
_and_
_hafsat Ay_
_PAGE4_
Shiru wajen ya dauka
Anan baba babaji ya yayi nuni da inna wuro yace baba kinji ai wai nace kin mutu?...
Sai ki tashi kiyi bayani ma sarki yaji da bakin sa ko hakan ne, Kema haka zuwaira sai ki kawo mana wayar naki a duba a gani ko da gaske ke kika kira ni ki kace min inna wuro ta rasu da har ni zan tura gambo taje gaisuwar rasuwa...
Tun kafin ya gama maganar sa Inna wuro ta soma tashi Ta bude ido a hargitse '"tace ni dai ban mutu ba gani da rai na kuma babaji bai taba cewa na mutu ba...nan ta fashe da kukan su na tsoffi, "ni da babaji ya kawo ni nan gari yana kulawa dani ace har shi zai laka min mutuwa? Kai Allah ya isa munafuki baiji dadi ba..halan ma so ake na mutu ake wani nokewa da karyan banza
toh ta Allah banaku ba.
Nan Zuwaira ta cafke da buhun zagi tana tsiwa a dole ranta ya baci tace "wayyoh Allah na shiga uku da sharrin duniya kowa anan dai ya san ban taba rike wayar salula ba tun da aka haife ni,..in banda raini da neman araba ni da miji na sai arasa wanda za a sa acikin zancen karya da makircin da ake so adaura masa sai ni? , tace duk karyan mutum sai an gano sa ai dama mu mun sani mutum bazai yi gudu dansa yayi rarrafe ba,
hmm watoh anje an shirya ma yarinya maganan karya da makirci ta zo tana zuba tana kukan munafurci toh wallhy nikam na fi karfin ku munafukai..
Allah kuma sai ya saka min sharrin da aka min bazan yafe ba
ta fashe da kuka,
Sarki yace ya isa hakan.
Nan baba babaji ya sake cewa toh,sauran maganan cewa na bata ma gambo suna,ranka shi dade ina ganin wannan kazafin ita kadai tasan da su don kai ma shaida nane ba ataba kama ni da wani abu ba bare miyagun kwaya,
hasali ma kai ka bani shugaban comiten zauren lura da zaman takewan matasan garin nan da tarbiyan su ko ba haka bane?
Kowa ya ce haka ne kam.
Yayi shiru kamar wani abu nacin sa arai yace Sai kuma maganan saratu "ya juya ya kalle ni yace saraatu Allah ya tsine miki albarka...
Nan waje ya kaure ana cewa "Ahhh ahhhhh haba wa babaji babaji kar ka tsine mata
Ayi dai hakuri mutane suka shiga bashi baki,
"Anan ya dada borewa Ya hau tafasa ku barni natsine mata dan uban ta"kuka ya fashe da shi yana kumfar bakin ya nuna ransa yayi mummunan baci,yana cigaba da tsine min.
Saratu dan ni ba uban ki bako?toh Amma Allah ya isa tsakani na dake meye ban miki ba a duniya da zaki laka min sharri don ki zubar min da mutunci na,..
A lokacin Ana rirrike sa kamar zai buge ni sarki ya tsime yana duban ikon Allah
Yace"Yar iska kawai duk abunda nake yi akan ki baki gani saida kika tona min asiri kika dauko cikin shegee? Sau nawa ina kama ki ina rufa miki asiri saratu yanzu ni na zamu miki abun tozartawa...
Anan ya shiga kwalla kira "Kai sageeru ena sageer nan waje yayi tsit aka juya ana dubawa ta ina sagirrr zai fito..
Sum sum ya fito gwanin tausayi a Gaban sarki ya hantsala sagir din kamar barawo yace zakayi magana ko sau na ci uban ka...ka fadi kowa yaji...marasa mutunci kawai..
Hankalin kowa ya tashi..ummma ta dada riko hannun na duka muna kukan zuci.
Ban san me naui ma sageer ba amma nasha mamakin Yadda ya hada labarin karya ya bayar akan neman mu.
Baba babaji yace" ka fadi meyake faruwa tsakanin ka da saratu agarin
Sau nawa kuma ena kama ku turmi da ta barya a dakin ka?
Sageer Yayi shiru cahn da dogari suka soma yunkurin zasu daka shi ya dago da kyar yace " ayi hakuri sau dayawa..
wani irin kuka na fashe da shi ina kallon sa cikin razana
"Lahhhh ha ilah ha illahu la hawla wala kuwaata illa billhi
Hau hau hau aka soma tambade de da maganganu ana tabe baki..
wasu suna cewa dama chan sun sani wasu suna cewa tabbass sun sha gani sa tare da ni ashe abunda muke yi kenan?
Sarki ya daga hannu, ya mike tsaye ya ce sagirru " kana nufi kenan cikin jikin saratu naka ne?
Nan ma yayi shiru jikin sa ne ke rawa sosai alaman ba da son ransa yake wannan shariar ba sai da sarki ya daka masa tsawa
Ba bata lokaci ya amsa da i..ina yace"eh kamar nawa ne
Anan ma aka sake kaurewa da salati wato tsabagen iya karuwan cin saratu ba ma da tabbacin waya bata ciki..?
Anan fa Kishiyon ummah na suka soma na su surutun cewa an zubar musu da mutuncin dangin su
Fada ne mummanna ya so ya kaure akayi chaaaaa Ana zagi na ta uwa ta uba sharrin da labarin da ban taba ji ba anan yau sai da aka fade shi kowa sai da tsine min Albarka iya isar ta.
Lokacin ummma ta mike tsaye dani ta bie ni abayan ta daga ni har ita kuka muke yi, babu bakin amsa maganan kowa..
Da kyar sarki yayi controling dattijai da matasa da matan garin da suke wajen
kowa yayi cirko cirko yana nina bacin ransa akan mu.
Musamman ma magana da ya zo da cewa kawai na so ne na bakan ta baba babaji na zubar masa da mutuncin sa.
Aka ce wannan ai cin Zarafi ne dan haka dole adauki mataki mai zafi akan mu ko ayi mana luli zaman garin nan sai ya gagare