Showing 3001 words to 6000 words out of 165901 words

Chapter 2 - SAMARIN SHAHO Completed Book Surayyhms.txt

Advertisement

Surayya   

06 Jun 2024

13856

iyalan kai gulma waje ko..yanzun
Me kika zo yi anan


"tsut ta kame bakin ta dake bari tana jimami "Uhmmm uhmmm baba ,dama na zo gayan aika ne.


"eh ..ehh baba kayi hakuri aika ta zo


Yace "Aika? wajen wa kenan.


Ya juya ya tsula mana razanananun idanun sa


Tace" Dama goggo rabi ne tace addayo ta zo ta debe kwanukan ummah..


Nasha mamakin karyan da aziza ta yi yanzun sai na sake baki ena kallon ta
na kasa cewa komai


"kuka ta fashe da shi tana bashi hakuri..daga bisani yace wuce ki bani waje


da gudu ta fincike tayi waje. sai binta da ido nake bayan ko sake kallo na batayi ba..


harara ya watsa min sannan ya shiga ciki


bance uffan ba sabida komai ajere na bari daga abun da nasan zai ce yana bukata na miko masa .


tsaki ya ja bayan ya ga hakan.


kenan baida dalilin da zaisa nayi masa wani kwakkaran aiki bare ya sake samun daman gaya min maganganun batsa dana cin zarafi kamar yadda ya saba.


Ina ganin ya zauna yana waya na sabule nayi waje din nasan zama ni da shi inuwa daya ba alheri bane tunda aziza tayi min hanya sai na bari akan shine makara ta


Fita na ke da wuya Ashe ranshi yayi mugun baci dana fuce din ,a ganin sa ya samu wani damar baza min halin sa tunda umma bata dawo ba tukun.


Ko cin abinci baiyi ba ya rufe ya biyo baya na


Cikin rashin sa'a kuwa
Ina fita na ci karo da sageer a bakin kofar gida
tsayawa nayi ena rokon sa ya tafi don kirjina har bugu yake min kar baba babaji ya fito ya riske ni da shi a tsaye.


Mun kai kusan minti 10 muna sa'in san magana amma da kyar sageer ya amince ya tafi a dole wai shi da gaske yake zai aure ni..


Bayan tafiyar sa Juyawa da zanyi sai cahraf muka hada ido da baba babaji gani nayi yana leko bayan sageer daya kusa lumewa daga lungun gidan mu..
na sunkuyar da kai na kirji na na bugu wani irin mugun kallo yamin ya kada kai ya wuce abunsa


ni kuwa ganin baice komai ba ya sa na bari a hala baiga komai bane sai na sullebe na shiga gida.


Akan hanyar sa Dariyar mugun ta yayi sosai har cikin ransa yace " yarinya kenan,ai dama yaro yaro ne,ni babaji bazan taba rainon dan damisa na bar ma na dawa ba wannan karya ne..


Dama chan ena ta farautar sarahtu Amma daga yau ena ga komai ya kare


Wannan ai Sageer ne dan gidan halliru mai nama hmm"dan gidan wanda nake bi bashin filin gona ta daya gina gidan sa ya kasa biya na dan jaraban talauci..kayyah!!!
...ya karashe da wani shu'umin murmushi


Nikuwa Hankali na kwance na zauna a daki,
Sai wajen 8 saura suka kuma shigowa da umma na


A ladabce na sake gaida su
Na kimtsa ma ummah kayan sana'ar ta don dama masa take siyar wa a babban kasuwar kan tudu itake da babban rumfa don ummah na akwai azama da hikima irin na matar karkara.


Hiran su suke yi irin wanda na tsana don sosai kawu babaji yake soka ma umma maganan banza kuma bata isa ta rama ba..


wani bin har yakan ce mata yar bariki goyon farar hula wato karuwa kenan


Umma na bata da hayaniya sabida bata da ilimin komai amma a ladabce take mayar masa da suka in abun ya ishe ta....


abu daya ke bani haushi yadda yake saurin wasa da hankalin ta ta wajen juya magana..


in har yace abu kaza ne bata isa tayi musu da shi ba yafi so ma tabi bayan sa ko kuma tayi shiru kawai


Duk randa ta haura ko akan gaskiyar ta ne sai ya soma dukan ta yana zagin ta ta uwa ta uba,umma na kuwa tunda akayi hakan sau biyu sai ta dena bashi daman haka kwata kwata duk abunda yace yanzu sai dai ta hau kai itama ta dada zuga shi ba don son ranta ba.


Ni kaina nan na sha deban jibga a hannun sa akan samarin dake biyo ni kofar gida


a hakan ma wata rana na san karya yake min amma ban isa na tanka ba haka zasu min lisss
sai dai daga baya umma tabani hakuri


Suna na zaune Wayar sa yayi kara ya dauka


Yace"Wai yaya ne kam zulai?
dan shiru yayi daga bisani ya kwaroro salati
Yace"Hmmmm duniya kenan tabbas anyi mana rashi kai kai kai bari to zan neme ki kawai...


Ai Wannnan maganan ma ku barshi haka zan zo da kaina ma gobe
Yana kaiwa nan ya katse wayar yana jimami,.


Ummah tace "Me gida lpya kuwa...?


bari kawai gambo..ya ya mutsa fuskan kalar jimami yace"ai zama bata kama ki ba Gobe zaki je chan dindima inna wuro ne ta rasu yau din nan da dare.


"Innalihhi wa inna ilaihi rajiun,. Allah ya ji kan innna.. Allah ya sa ta huta amma babaji ciwo tayi ne haka?Sai naga kamar jiya jiyan nan yafendo ta gaya min inna wuro garau take tana ma filin roron gyada.


Ni dai ina daga gefe ta bakin kofa Ina shiru uffan bance ba


"nan baba ya hatsala"Ke da Allah rufe mun baki gambo,da
Cahn mutuwar sai ya zaba wanda zai dauka ne? bana son shashanci da neman tsugudidi fa"




Ummah ta tabe baki tace "ahhhhh toh Allah ya baka hakuri
Mai gida Nace ba?
Goben da su zulai kenan Za muje ko?


"ban sani ba ..ya mike a fusace kamar zai mare ta
wanda hakan ya sani sulalewa chan nesa da bakin kofar kadan na rakube.


Ke kadai nace zaki je, da daban aure ki ba ai su nake turawa..wai nikam rashin kunya zakimin ne gambo?


Uhmm uhmmm..umma tace kamar bata damu ba


Tace Allah ya kaimu goben..daga nan taja bakin ta tayi shiru


Shiru ne ya ratsa wajen ban sake jin motsin su ba..
nima bacci ne yayi nasaran dauka na a gefen bakin kofar ban sani ba


gurnani da sambaton baba babaji ya sa na firgita. cikin sanda da tsananin kunya na mike na kama hanyar soro ba wanda ya sani kamar kullum naje na kwanta kan dakali.




Bayan sallah asubah
Wanke wanke na ke yi ayayin da dai dai kun mutanen gidan mu ke fitowa .


Yanzu kam babu wanda yake kulani sosai a gidan..
su yayu na ma kamar tsine min sukayi ..ai idan mace takai haka a gidan uban ta ba aure to karuwa ce"().


"'yawwwa Gambo ya kamata ki fa hanzarta ki kama hanya maza maza ayi wankan inna dake.
cewar baba babaji.


"toh me gida ummah ta amsa..Nan ta shiga shirin ta tsaf.


Bayan na kammala dumame na rusuna na gaida su" tsaban kallon da baba babaji yake aika min a sace ya sa na kasa cewa komai na daure fuska.


umma duk tana lura da yanayi na amma sam na kasa gaya mata tafiyar tan ne bana so kwata kwata sam hankali na ni bai kwanta ba.


Gashi ya sa ma na ido ko tari umma tayi sai ya amsa"


hakan mukayi rabuwa da kaikayin magana a zucin mu umma ta kama hanyar dindima.


Tun tafiyar ta komai ya sauya Acikin nishadi baba babaji yake, don sosai fuskan sa ya nuna hakan duk dama yana yi yana fuskewa yana shan qamshi..


tunda umma ta tafi ko hutawa banyi ba don tamkar baiwa haka ya maida ni
Yau da safen har wanke masa aswaki da kasar takalmi sai da nayi


"karfe 11 saura ne,sai na dan jinguna kadan ena jiran lokacin makarantar rana yayi,nan naji an kwalla min kira...




gani baba,na shigo na rusuna gaban sa.


je ki bakin kasuwa wajen mai shayi zai baki aika ki kawo min..


Nace toh azuciya naa ina tunani"Tabbb yanzu fa ya ci dumame jibgi guda ko mai zaiyi da aikan mai shayi oho"


Nan na mike ina kokarin ficewa .


Ya dada hade rai Yace saura kuma nazo na kama ki a inda kika saba lafewa kina iskan ci da yan iskan nan marasa tarbiya irin ki,..


madallah ma kinsan yanzu nine aka bar min ke agidan na ko?to ki kiyaye kan ki da ni saratu.


A ladabce nace to ,sai ya juya kansa ya ce
Kuma layin mai goro zakii bi kar ki sake kibi bakin titi kinji na gaya miki kenan.


Gyada kai kawai nayi
Bance uffan ba na sabule nayi waje na kama hanyar kasuwa...




Ina fita Ihu ya sake ya soma rawa yana kirari makan sa adakin shi kadai
" Kiriiiiiii baram bam bam bam bam kaii kai,..sai ni babaji dan gidan goggoji sara dai a hankali.... dawa sai maza,, .. duk wanda yayi jiran tasha dani da shi zamuyi kwanan mota.


Yiiihuhu sai ni babajii dan goggoji yau ango kake tartil babu hafsin.


Kikiki ya fashe da dariyar kuruciyan zuci Mai shake da jahilci da tsananin mugun ta.


hahahaha yarinya yau naki taka kare kwanan ki sai agadon babaji dama chan nagaji da cin durin uwaki...


Ya koma kan gado ya kwanta galala cikin tunani yace"Ga nan rabi bazaura na jira na alayi kwana nan zan yaga ku na auri ta na huta.. Na gaji.


Haba,itama tabi duk ta hanani sakat babu dama nace zan ci nata durin agaban gambo dan nasan munafurcin mata sarai.


Cikin shakekken nishadi yake maganan sa'yanzu duk sai sun gane kuran su.


Ya koma ya dada juyi cikin maganan zuci wanda zai tabbatar maka da ya kullace ummahn ya ke cewa"hnmmmmm Kina wasa dani ne gambo,yo ni me zanyi da saiwar jikin ki da yaya bukar ya gama shanye wa?dama chan dan kuruciyar ki na gani.


dukan ku ai akan tarko na kuke lokacin ku ne yayi,kinga kafin ki dawo daga gaisuwan mutuwar karyan dana miki.


Lokacin har wannan shashashar yar nakin ta san ni waye,


itama da sannu zata haura kan qayar dana daura mata shi yanzu....


kai bari ma na fita saboda naji dadin ganin komai ya tafi min dai dai idan kuwa sageer yamin kuskure nasu ya kare agarin nan.




dariya ce akan fuskan sa ya dau hular sa ya fice hanyar kasuwa.












_FIRST CHAPTER REVIEWS I NEED SOME MOTIVATION_ 🙄🙄, _yana ji na gaji ne_ 🥺


























*Follow Wattpad@ SURAYYAHMS*
[2/23, 22:35] ‪+234 802 646 5734‬: .*🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }






™/SAT5/ 2019🔞
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
🍒🍒






_A TRUE SENSATIONAL STORY_




~_Story written by_~
*SURAYYAHMS*🔥
*OFFICIALCATTY🐈*






*_WATTPAD_ @SURAYYAHMS_*
@ IG:Surriem-sule_






*#Lovestory2018/19*
*#romance#purefiction*
*#Destiny at fault..*
*Any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison All my stories are strickly mine,beware copycats!.*






*hmm It seems like the universe has given me soo many special maryams THIS PAGE IS also for this exceptionaly special maryam watoh"MARYAM SANEE(mamuhgee)GOD will bless you for me#ride or die with us#die hard is uz🥰*




*SURATUL HUJURAT*


*2."Wa La Yagtab":* Do not backbite each other. Its a major sin equivalent to eating your dead brother's flesh






_PAGE2_










Umma na da kafa take takowa zuwa tasha don haka ta dau Lokaci sosai don sai wajen karfe 10 na safe ma ta kai kan titi.


anan ma zaman diris tayi tana jiran motan haya koda kuwa akori kura ne ya kaita cikin yankin su inna wuro amma shiru babu wanda ya wulga...




"nikuwa tun da na foce a gidan Tafiya nake sanye da hijabin uniform dina bana kallon kowa.


Gashi dama hankali na ba a kwance yake ba sabida yanayin lungun da baba babaji yace na bi.


wajen shiruuu ne babu mutane sosai,ni kaina Allah Allah nake na samu na fice..


Sai da na kai Daf da bakin gargada naji wani kara kamar an fasa tayar mota sai da na dan razana ,ko samun daman juyi banyi ba naji an shakuro ni ta baya an matse min baki da karfi...


Firgici na shigayi cikin tsainnanen tashin hankali da tsoro ganin sageerr ne a kaina yana faman kokuwa da ni...


Ka sake ni..ka sake ni nace..nan na shiga tsala ihu neman ceto.


Shikam Baice uffan ba ya jawo ni da karfin mallaka yayi wani hanya dani daga nan ban sake sanin meyafaru ba..




Daga bangaren ummah kuwa har yanzu bata yi dacen mota ba, har tagaji da bata lokacin da zaman jira, chan da azahar sai ta tashi ta soma daukar niyyar takawa da kafa kadan kadan zuwa kauyen su inna wuron.


Akwai nisa ba laifi.
ummah tana tafiya ne kamar bata yi,
in tayi ta gaji ta samu dan inuwa ta kan tsaya jira ko wani zai bi nan ta sami wanda zai amince ya kaita ciki amma kusan duk wanda suka shige ba wanda ya amince ya taimaka mata har da fuskan sani.




Ummah ta ga abun mamaki sosai
yau dai gashi da kudin ta take rokon abun hawa amma duk suka turje sam baza su dauke ta ba.


Gashi Ba halin komawa gida ga wahalan tafiya kuma tasan halin baba babaji bazai taba amincewa da hakan ba.


A haka ta daure tana tafiyan ta har magribh ya rufa ana neman ishai lokacin tana dab da shiga babban kasuwar yankin su inna wuron.




Nikuwa sai Wajen karfe 8 saura na bude ido kan wani benchi na tsinci kaina ba abunda ya same ni amma dai an cire min hijabi


,...kuka na fashe da shi tare da mikewa zaune ena duba dan iskan nan wato sageerr"ashe haka maza suke? Ashe duk kalaman bakin sageer karya ne macuci ne dan iska?.meyasa zai kawo ni dakin sa ya ijiye ni?


To wallhy sai na masa rashin mutunci, anan mutuwa ko ni ko shi na fada a zuciye hankali na yayi mummunan tashi.




Cikin wannan bambamin naji ana kokarin bude kofar, kuuuuu ciki na ya tsure jin hayaniyar mutune " muryan baba babaji na soma ji..don shi yafi na kowa kauri.




"hannu na daura aka.."Wayyo Allah na,na shiga uku,ohhhh ni saratu
"handi mmbani"
Shikenan rayuwa ta ta kare yau..


"Munafuki ,ai yau karyan ku ta kare bude min kofa maza ....na ji babban aminin baba babaji na cewa daga waje


Sageer kuwa sai bada hakuri yake


A tsaye na mike na daura hannu aka zuciya na na duff dufff kamar zai leko waje
Sai gwaff aka turo kofar..
A tsorace na firgita hawaye ne suka biyo bayan rawar da jiki na yake yi


La haila ha illa lahu muhammadar rasullillahi sallahu alaihi wa salam SARATU!!!!


Eh lallai kam saratu yau kinji kunya,toh yau sai na kashe ki agarin nan...baba babaji ya soma bari yana kumfar baki.


Ihu na so na tsala duk gaba daya naji rudani na neman zautar dani,a tsorace na shiga bashi labarin iya abunda na sani "baba wallhy wallhy
"


Ni ban san me yafaru ba
Ka tanbaye sageer wallhy bani da masaniya akan komai shiya kawo ni nan
Allah ka tambaye shi .na kara sautin kuka ina rantsuwa.
Masifa abokin sa ya shiga mana baji daya kamar kisan kai muka aikata..suka tsorata mu sosai
Barin ni da na kasa gane komai a wajen sai rantsuwa nake ina maimaita abu daya.


Amma Kamar baiji ni ba yace "Ke Kinci ubanki, zancen banza zancen wofi yo ke din ne ban sani ba ko shi sageer din ?


Ohhh mani zaki kawo ma shahshanci "wato har kina da bakin magana ko,?


Na girgiza kai cikin kuka alaman a'a,cikin shessheka nace wallhy gaskiya nake fada maka baba,


Nan Ya dada hatsala. "inayi ki nayi,? saratu ...saratu..ya daka tsalle a fusace zai jawo ni abokin sa ne ya damko sa yana basa hakuri..


Sam nakasa gane meke faruwa, meyasa komai ya juya kamar ni na kawo kaina dakin sageer me suke nufi da ni?wai meyasa baba yaki daukar magana na wallhy ban san komai ba.Hasali ma haushin sageer din nake ji da ya kawo ni nan tun tuni ya ajiye ni..


Ya na bangaje sagerr daya yi tsomo tsomo agefe ya damko hannu na yayi waje dani bayan ashariya da bakaken maganganun daya gaya masa shima ya barsa nan da aminin sa,
dani da shi muka tafi....


Sam bana jin dadin zuciya ta kuka kawai nake yi ena tafiya madel madel agaban sa badon dare yayi ba nasan da sosai jama'a zasu gane halin da muke ciki duk dama ya min kashe din nayi masa shiru sai munje gida.


Ummah ne zaune tana dan hutawa sabida yunwa ya mata illah gashi saura kiris ta shiga masaukin ta sai nishi take tana kama kwankwaso..
Gambo? Lahhh da gaske gambon ce


Ummah ta dago,Ahh larai? Kice anan da dare nan?


Ai ke zan tanbaya, ena kika fito haka a wannnan hanyar bakar jeji da aljanu gambo? Ko dai maganan dan goggoji gaskiya ne amma me ya hada yar niger da hanyar dindima, ai kamata yayi ki dubi gabas ba kudu ba.


Dariya umma tayi tace,toh? Karai sarkin maganan jyaji da shi dai.


Wallhy tafiya zanyi zuwa dindima amma bansamu dacen mota ba tun safe nake nema.
Inna wuro ne Allah ya mata rasuwa babaji yace na je na bi mana baki...


"cikin mamaki oarai ta dago ta dubi ummah "Shiruuuu tayi na dan wani lokaci sannnan tace tabbbbb ikon Allah...


Kai duniya abun tsoro ne Ba shakka sai da na kawo cewa akwai makarkashiya a zancen nan dama ni chan ban taba amincewa da dan gogojji ba ..makaryacin banza almunafuki.


"ummah tace, Kamar ya fa larai?wannann wani irin magana ne haka? meya faru kuma..ke kinga tun tuni kike mini magana cikin bita da kulle ki futo kawai ki gaya min meke faruwa.


"larai ta juya ta kalle ummah tare da cewa,"Ai dole ne ma nagaya miki gambo sabida in ban fada bama zaki je chan ki tarar da gaskiya.


Hankalin umma ya tashi
Duk Ta sa ido da kunne tabawa larai tana sauraran ta.


"To bari kiji ingaya maki, mijin ki yabi gari ya yada cewa tun sahe kika fita yace wai kin gudu a dakin ki kin barshi da yarki yana bi gari yana neman ki...


cewa yayi dama ance masa sana'arki na siyar da masa ba haka kawai yake bunkasa ba akwai abunda kikeyi na daban wanda shi kansa bai sani ba. Naji fa kamar yace kina bin maza,..


Kirjin ummah ya dada bugawa'a ranta tace karuwan ci kuma? har ta budi baki zatayi magana larai ta kuma cewa"


Yama bada cikiyan duk inda aka ganki a yankin nan a tsare masa ke kar abari ki bar garin nan har sai ya samo ki dakan sa
mutuwa kuma da kike fada na inna wuro 'to inna wuro na can kurwala tana hutu gidan babaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login