Showing 138001 words to 141000 words out of 165901 words

Chapter 47 - SAMARIN SHAHO Completed Book Surayyhms.txt

Advertisement

Surayya   

06 Jun 2024

13916

sarah ne, gani take bata isa ta hana ta zama da wanda take kauna ba besides ahe ready to do anything don ta mallake mahfud da familyn sa.


Anan bayan ta kammala plan din ta sai ta fito yammah ne dab lokacin dawowar sa....


Daga saman bene dake hango parking space sarah ta hango sa ya sauko a mota,.. farin ciki ne ya mamaye ta sai tayi sauri ta dauko foam ballon rod dake wajen wanda take wasa da shi bayan ta kammala bitan ta,wato abun kumfa ne da ake hurowa sai yayi manyan balls yana sauka da kansa zuwa kasa kamar snow ball ko kumfar omo..


Tana tahowa ta tsaya daff inda zai bi daga sama ta huro su da yawa sukayi manya da kananan balls masu kyau
Cike da so da kauna Ta hure wajen sa
Tun daga saman suka yi flying all over the place bai hankara ba har gefen kuncin sa.


Dama yana taba abu zai fashe cike da mamaki ya dan shafe gefen cheek dinsa ya daga kai sai ya hango ta...


suna hade ido da abun a hannun ta take waving dinsa tana murmushi mai sace zuciya gaba daya balls din suka dada saukowa akansa beautifully...


" kallon ta yake cikin yanayin kauna Lokaci guda ta sake sace komai na shi,ji yake a duniya don shi kawai akayi ta.


Dan karamin murmushi yayi ya mata alaman i love you in 143 da yatsun sa da kuma shape din heart,itama tayi d same bata hankara ba sai taga yayi blowing kiss a iska tayi dan dariya ta cafke lokaci guda kuma ta boye fuskan sa ta juya masa baya tana dariya..


Abun yayi masa dadi He wass so in love and happy da sauri ya shigo don ya hauro ya same ta..


Shabnam da ke zaman jiran sa ganin bayan sa kawai tayi yana haurawA chan saman benen ta steps


Cikin mamaki Sai ta taho itama ta shiga bin bayan sa..


Itako sarah tana kan leken sa she tot da ta juya masa bayan yana nan wajen ne.
Har zata juyo sai suka ci karo da shi...
Mamakin ta ta ke boyewa da dan karamar Dariya ta danyi ta sunkuyar da kanta "yace ina abun yake nima abani na rama..


Cike da jin kunyar sa tace babu, ni ka je ka huta karatu zanyi...


Abun na burge sa yau sarah bata so ta hade ido da shi sai sunkuyar da kai ta ke..


Haka ta rabe jikin sa ta zauna kan chair dake wajen ta jawo qur'anin ta tana dubawa shiru amma ta kasa yi inda zai ji...haka kawai taji kunya ya kamata ..


Sai ya dawo ya zauna gaban ta cike da tsokana yace sarah bazaki kalle ni bane, nima karatun zanyi? Tace ah a, kaje ka huta baka da lpya..


Yana matukar son shwagabm nata sai ya marairace yace i har ana so na tafi to ayi karatun nan naji...


Bata so ba amma haka ta daure ta nuna masa zata iya " ya dawo daf da chair din datake zaune...a hankali ta soma karanta suratul Qalam...aya daya zuwa biyu sai ya sa nashi qira'ar suna yi tare,tun tana jin nauyin sweet and melting voice din nasa har ta sake suka bada rthym daya suna yi...


bayan sun kai atop ya dube ta cike da shaukin so yace,i cant wait to live uptill the rest of my life with you... i love you very much sarah ure my life..


Nan suka tsaya kallon juna


Shab na daga nan bakin door kusa da sun lura da kyuw ma da zasu ganta amma gaba daya hankalin su na wajen juna..


Hawayen ta ta share ta juya tana tahowa tace babu amfanin na fada ma mahfud abunda ke raina..
Amma dole ne na fada inda za abi min hakki na.
I love him so much and is not my foult...cike da wannan zuciyar ta wuce part din granny.


Nan kuma sarah ta rako sa har shashen sa suna dan hirar soyayya kadan kafin tayi excusing dinsa ta fito..


granny na zaune tana shirya kayan qamshi sai ga shabnam..


Yadda ta zauna a sanyaye ya sanar ma granny ba lpya ba amma sai ta share ta da cewa my princess sai yanzu kiga dama zuwan waje na ko marmarin zaki tafi ki barni ne haka"


Tana shiru tunani suke cunkushe mata rai...tana jin granyn na teasing din mata akan tafiyar gobe


Chan kawai sai ta sa mata kuka cikin bori...tace ni ba inda zanje granny i wanna stay here forever....


Grnny ta juyo tace what?Duk abunda take yi ta bari ta zo ta zauna daf da ita tace shabnam?meke damun ki ne pls talk to me kwana biyu ina lura dake meke damun ki....


fargaba ya sa ta dago zatayo magana granny tace uhm uhmm dont tell me akan maganna tafiyar ki ne kike kuka, ba shi bane i want you to tell me whats bothering you..ko ance miki ban gane ki ba ne..


Jin haka ya sa ta yi tunanin fada kawai ta huta tinda grannyn ma ta dan sani,tace granny bana so na tafin ne.and theres is also somthing i want to tell you
grnny bata amsa ba amam tayi mata kallon go ahead


Tace Emmmm emm granny..kina ganin mahfud zai aure ni?ta marairaice gwanin tausayi


Waje granny ta zaro ido ta kalle ta Duk dama ta sani amma sai taji mamaki..how bad it is ?
Yanzu kam Tasan son mahfud ya rike zuciyan shabnam..


Sai tace ban fahimce ki ba? Dama kuna ...


tayi saurin tsare granyn da cewa no babu wannan" he dint know anything yet sai dai idan ta reaction dina ya gane..


sai ta langwame wuya cike da yarinta tace ina son shi granny tun ba yanzu ba i swear i wanna be his wife...pls help me grannny


i really love mahfud ta riko hannun ta dam dam ta sakalce mata fuska ..


Cike da damuwa granny ta kalle ta hannun ta sa tana shafe gefen fuskan ta don ta danji sauki sauki...ta lura sam bata cikin right senses din ta..
Gaba daya ta sa damuwar abu aranta sosai


A nitse granny tace if i understand you,shine dama kina son mahfud amma shi mahfud bai sani ba And you want marriage now shabnam?


Ta dago tare da gyada kanta seriously..yace yess granny


Sauke ajiyan zuciya granny tayi tace"look child, is not a crime to love somone... amma ai da tun da kika fara da kin sanar da shi ko ni zan iya gaya masa....


but right now shab mahfud has brot somene to us and he loved her..tun kafin granny ta karashe ta fashe da kuka tana girgiza kai alaman bata so taji


Cikin shesheka take cewa granny shikenan bazaki taimaka min ba..pls help me granny wallhy ina son shi,i wanna be with him for life...pls granny....please..kunnen ta ta rufe da hannayen ta
She just dont wanna think about sarah,ita dai kanta kawai ta sani....

"A hankali granny ta jawo ta jikin ta ta shiga rarrashin ta cike da tausayi batare da tace komai ba...


Kuka ta shekewa ita kam ba ji tana rokin granny ta taimaka mata ta auri mahfud ita lallai shi take so


haka granny tayi calming din ta ta zaunar da ita anan din na dan wani lokaci kafin sai ta tashi ta fice don ta samu daman tunani akan lamarin don sosai tausayin shabnam ya kama ranta.


This girl thats alwys happy and giggling yau ita ce ta birkice gaba daya cikin radadin so...?


She knew she have to do something dole nema ta samu ganawa da mahfud akan shabnam..
#surayyahms






*#FARGABA*






#wapdsurayyahms
*Official cat*
[2/16, 19:24] SURAYYAHMS🐈: *🅱RILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*


_Shafin naku ne_
Siyama ibraheem
Swrht teemah tj
Ummu haidayr
Barister fatimah
Hauwa baba
And maman xarah.

I so much miss you tawajena malama maryama saeed maman areef Allah sa kina cikin koshin lpya ameen.




_44_




Ba bacci take yi ba amma sam sai bataji shigowar grannyn ba har ta zo ta zauna anan gefen ta


A hankali ta dube ta cikin tausayawa don kallo daya zaka mata kasan tana cikin zulumi


Hannu granny ta sa ta yaye duvet din da ta rufu dashi half adan firgice ta taso suka hade ido ba shiri ta yo kasa ta dan rusina gaban ta jiki asanyaye..


Tun kafin granny ta yi kyakwan motsi ta soma sauke mata hawaye cikin magiya da shagwaba tace "in nayi miki laifi dan Allah ki yi hakuri bazan sake ba...
Granny pls have mercy on me kar ki raba ni da shi kinji granny? I swear,bazan taba sa shi ya ki jin maganan ki ba i promise you...dan Allah kar ki raba ni da shi pls..ta karashe cikin shessheka.


Shiru granny tayi tana kallon ta gwanin tausayi, she just wonder what came over her amma gaba dayan su tausayin su take ji..


Sai ta dan matse tare da sauke ajiyan zuciya ta dago ta tana cewa ya isa haka taso ki zauna..


Cikin kula da kauna ta shiga share mata hawayen ta tana cewa"to zauna.. yi shiru abun ki saratu, ni ba ki min laifin komai ba


Zama na dake agidan nan sai dai ma ce ni zan nemi gafarar ki nasan wani lokacii zakiga kamar bana kaunar ki.. but no dear,i just want the best for you..


And am so pleased with you..a kowani fanni kin birge ni musamman da yau kika gwada min kuskure na wajen kulawa da yar uwan ki shabnam.


To be honest, tausayin ta na ji sosai i was not even thinking about her future
Amma kinga ke kin yi kokari wajen cire son kai kin zama mana zabin gaskiya ..am soo proud of you my dear.. mahfud has just made the best choice
So Wipe all this tears kar ki sake sauke su sai don farin ciki cos we cannot wait anymore"


Grannyn ta karashe da murmushi mai kayatarwa
Sai yanzu sarahn ke gane kan maganan sai ta sunkuyar da kai cike da jin kunya,farinciki da godiyan Allah ta soma mata godiya..


Haka suka dan dauki lokaci granny tana mata nasiha,
Sai yanzu take ganewa ashe duk abunda grnny take yi tana sane


Aranta tace to lallai sun mata halarcin da ba abunda zata saka musu da shi face ta so dan su so na har abada..


Washe gari da safe sai 11 ta fito ahakan ma da kyar ta tashi sabida baccin dake damun ta
Don a daren nafilfili tayi cike da neman taimakon Allah a dikkan al'amuran ta


Anan site din anty warda ba abunda bata fara shiryawa ba tuni har ta yo guzuri na gyaran amarya


tun safiyar yau din ta bata wasu,wasu kuma ta sa ta soma amfani da su akai akai


Anan daga gefe kuma suna kan shirin auren da mahaifin sa.


Bayan kwana biyu Mahfud da mahaifinsa suka shirya zasu je wajen ummah don ayi maganan a tsaida rana.


amma haka granny taki sam sai da aka dauki wani sati guda ana shirya komai a cewar ta suna zuwa wajen ummahn baza su dawo ba sai an daura auren mai gaba daya.


haka kuwa aka yi tsaban zumudin granny ya sa saran ta ke sanin komai


Duk dama tana ninnike da damuwar tunanin mahaifiyan ta


Tunda aka fara shirin auren ta soma mafarki da zazzabin ummahn ta amma ba wanda ya lura..


anty warda gani take ko dan abubuwan datake bata yake sa ta shiga moody.. amma ita kadai tasan yanayin yadda tunanin ummahn ta yake nakasa ta kowani rana.


A bangaren yazeed kuwa ya kashe kudi sosai wajen samum hadin kan gagaruman jounalist wanda zasu taya sa sa program din yayi muhimmmaci..


Ciki sa'a aka fara komai aka yi presenting
Dinsa imda aka samu kyakyawar debate daga media houses


Anan aka goge kuskuren sarah


sai aka fi bada karfin cewa sarahn ma ita tafi cancanta da tayi aikin ta
Sabida ita tasan zafin rayuwar dan adam da sadaukar war sa.


Sannan aka sa karfi wajen son awayar da kan jama'a akan dukan wanda ya tsinci kansa a halin da sarah da ummah suka tsinta kar suyi kasa agwuwa suma su tada rayuwar su su taimake mutane kamar yadda sarahn tayi.


A Lokaci kalilin sai gashi har kananun kungiya da discpline clubs and socities sun fara rally ana so lallai adawo da martaban faundation din sarah da ya mutu


abun nan ya matukar bada safeenah da su hjy asma haushi don haka suka aika ma yazeed katin gayyata wajen auren safeenah da faisal.


Da dai kamar abun bai dame sa ba musamman ma dayaji da aminin san ne faisal.


amma da shike akwai sakayyar Allah sai gashi yaji zafin kishin betrayal sosai aransa..


duk dama yanzu babu space din kowa sai na sarahn.
Yanzu shi burinsa bai wuce WHAR su sake apology letter da call off ma sarah ta dawo kam matsayin ta ba


yasan hakan shine hanya guda da zai dawo masa da ita..


this time haushin abunda su safeenahn suka masa
Ya qudira aransa muddin sarah ta fito sai ya nuna ma kowa banbancin sa da da yanzu

A ganinsa duk tsiya duk rintsi shi zai sake daga sarah har ta yafe masa suyi aure...so next mission dinsa baifi ya takura su safeenah da mrs ruth a sake letterr neman sarah ba


A ranar da su granny da su mahfud suka je saudi arabia wajen ummah
Washe gari aka daura auren mahfud da sarah a babban masallacin riyadh ya ci albarkacin dumbin muslmai dake zagaye da safiyar jumma'an ranar.


Sadakin ta dai dai da na matar larabawa don haka a tsade aka bada ita in euros aka biya.. a kudin nigerian mu is equal to huge amount of money worth millions.


Anan germany anty ke fama da jikin sarahn dake tsanan tawa a hankali sabida tunanin ummahn yanzu tasa agaba ba sauki Catherine ce kawai ta taho shine ta samu ta barsu tare tana luka da ita


Bayan daurin aure da granny da mahfud da su ummahn suka dawo germanyn sai dai shigowar dare sukayi a duk yadda ta so taga yarta haka granny ke danne ta har washe gari da safe.


Anan ma zazzabi ne mai zafi ya hana sarahn sakat amma ta daure


A hakan ake shirya ta cikin kasaitatun dresses sea green daga Wani shaharareen designer a QATAR..
Tasha make up da jeweries masu dauke numfashi ga suman kanta har na wani rinewa idanu tsaban yadda yayi baki ya kwanta sai sheki yake yaji kasaitaccen gyara..


Anan ummah da granny suka shirya duk yadda abubuwan zasu kasance


Da safen aka yi walima wanda bai kunshi kowa ba sai neigbors dinsu wato su shabnam da iyayen ta..


Dumbin tsarin wajen da abubuwan kyautatawa da kyaututukan da akayi duk ma masu bukata aka tara aka ciyar..


Auren sirrin ce aka gama shi tsaf daga su kansu da cath, familyn shab da kuma friends din mahfud wanda tun awajen daurin auren ma suka rabu.


An saka tsaro mai girma Don haka ko media basu sanda komai daga zancen auren sarah da mahfud ba duk dama yaci sunan sa one in town komai anyi sa ne kamar anayi na karshe.




Ummah taso ta bayyana kanta ma sarah tun a wajen waliya kamar yadda suka shirya da granny amma yadda ta ganta ayau din sai da taji ta karaya..


Daga gefe tayi kuka sosai ganin yadda yarta ta dawo,wani bin sai tayi blaming kanta na fita arayuwar saratun


amma idan ta sake duba yadda ta dawo na daban a hannun wasu suka sake shaping din ta sai ta sauke godiyan ta ma Allah


Haka ta buya basu ga juna ba har ka akare taron.


Har dare bayan su cath kowa da kowa ya watse
Anan aka taro a falou full house
Sarahn ne kawai a daki..


An sake sauya mata dresing da kwalliya lzuwa masu shegun pure white wedding dress riga da skirt mai bajewa da tsawo


Tana zaune agaban mirror ba abunda take tunowa sai yadda ummahn ta dataji ayau data na kusa da ita..
tun tana fada azuciya hd ta shiga furtawa afili


Cewar ta 'yau na auro wanda kike so ummah gashi ban śaba daga tarbiyan da kika bani ko daya ba...
Wai yaushe zaki zo min ne ummah? Ina kewar ki sosai... nan hawayen ta ya sauko ta dan jingina kai tana kiran ummah cikin nunfashin jimamin ta.


Daga nan kuma tuni ummahn ta taho zuwa dakin don ta samu ta gana da yarta tayi mata nasiha ita dakan ta ta mika ta wa dangin mijin ta...


Ta iso tuntuni amma bata motsa ba don daga bakin kofar take jin yadda sarahn take ciki..


Cike da jimami sarah ta sake furta ummah...anan ta ji an dafa ta...tare da furta saratu?


Wani mau taji akunnen ta bugun zuciyarta ne yasa ta farga ta firgita
Ta dago fuskan ta suka hade idanun su.


jiki na rawa ta mike tsaye tare da sake salatin da ya taho da wasu irin mahaukatan hawaye


A birkice Ta furta ummah kece wannan ko mafarki nake yi...
Hawayen ummahn tare da murmushi suke zuwa don sosai sarahn nata ta dada sauyawa sai tayi mata kyau sosai tana jin kamar ba ita ta haife ta ba.

da wani irin muryan jimami mai shiga zuciya da karya gabobin jiki ta jawo yarta tana kiran sunan ta tana cewa nice saratu ummahn kine..gani nan ban je ko ina ba.. ina tare da ke yata"


Kuka sarah ta fashe da shi suka kankame juna tamkar jinjirar da tayi watanni bata sha nonon mahaifiyar ta ba..


a hankali take rarrashin ta sai da sika samu nitsuwa take gaya ma duk abunda ya faru aranar..


Wasu mugaye ne, da suka ji abunda ya faru da su ranar da labarin su na karya da aka yada ya bazu šabanin yadda komai ya faru.


Sai suka so suyi amfani da wannan daman don su kashe ta a wutar gobarar da aka kuna a gidan gonan ta da gangan


Don a kwashe gadon arzikin ta sai ace ma sarah ai mahaifiyarta ta mutu saboda abun kunyar da suka aikata


Amma sai Allah ya sa sectaryn ta yana da rikon amana shiyayi saurin ceto rayuwarta daga nan ya tseretar daita kasar saudia


tana isa ciwo mai tsanani ya tarke ta rai a hannun Allah ...


Tace ko da na tashi na nemi ki saratu sai aka ce min baki nan shine na kira mahfud a ranar don nasan bazai taba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login