Showing 12001 words to 15000 words out of 165901 words

Chapter 5 - SAMARIN SHAHO Completed Book Surayyhms.txt

Advertisement

Surayya   

06 Jun 2024

13861

mu..


Da sarki ya sa aka dan rusuna akayi shiru sautin kuka na kawai ke tashi nan umma na ta daure ta tare numfashin sa ...


'tace ya mai girma Hamma kasani Bani da wani abun cewa anan...
domin kuwa gaskiya kamar hasken rana take idan har ta fito babu wanda ya isa ya sa hannu ya kare ta Allah shi zai isar mana da ni da diyata...


Ina kuma yi muku tuni da Allah bazai barku ba dana fada da ban fada ba zai biye mana haddin mu..kuje da gaskiur ku na rike rashin gaskiya ta da na diyata ayi mana hukunci.


Waje na so ya kaure da sharhi ,sarki yace a dakata masa.


Nan yayi dogon magana mai cike da bacin rai rashin jin dadi da masifa yayi Allah wadar da ni da ummah..


Ya kuma ce zai hukun ta sageer duk dama ba a tabbatar da nashi bane shikan sa kokunto yake.


Anan Aka taru aka bada baba babaji hakuri
Aka bashi baki sosai .aka danne sa kamar da gaske.


Sai sarki ya juya ya kalle mu rai abace yace ke kuma saratu kafin na dawo kanki ki rusuna gaban babanki yanzu anan gaban kowa ki bashi hakuri cin zarafi da bata sunan da kike so kiyi masa.


Jiki na har karkarwa yake yi tsaban kuka da takaici amma haka na shiga yunkurin sabulewa daga jikin ummah zanje gaban baba babaji na bashi hakuri...


Dam dam na ji umma ta riko hannaye ne..


Idanun ta ne suka kuma kafewa Alaman ta bushe zuciyar ta, tace"
Babu wanda zaki bashi hakuri anan saratu..hukunci kawai na roka mana.




mamakin abun da tace yasa aka soma tabe taben baki ana salleme wa.
A umarnin sarkin?
Kai wai me ake jira da gambo ne ba aci uban ta ba..


sarki ya ce adakata...


Gambo?


Umma tace naamm hammayo


"Ki kace bazata ba kowa hakuri ba..


ummah tayi shiru daga bisani tace in har ma kashe mu za'ayi ayi gaggawar yin haka sabida yata dai bazata taba bawa babaji hakuri ba..
kuje da gaskiyar ku Duniya ta ishe kowa riga da wando.


sai tassss umma taji saukar mari afuskan ta daga hannun babban aminin sarki..


yace "Sha shashah kawai ashe baki da hankali gambo?
Allah wadar dake Mu sam bama bukatar irin ku anan garin bakar ashana kawai....


Sarki yace tabbasss , gambo kin nuna mana bamu isa dake ba kuma baza mu iya zama da tsagerun irin ki ba.


Tunda kuwa kin ce sarati bazata bada hakuri ba ai addini ya mana hukunci wanda suka aikata zina sabida haka ranka shi dade tunda saukin da ka musu bai mata ba
Ayi ma yarinyar nan hukuncin ta kawai kowa ya huta


Anan ma aka kusa aka kawo dorina
Aka shimfida ni da karfi da yaji aka kwaso sageer aka mana bulala 100 100 chifff chif


"ni kam Har Sumewa nayi tsaban kuka da azaban da nake ji ajiki na cahn da na kuma farfadowa ummma nagani a kaina tana kukan mai dauke da tashin zuciya...gaba daya ta sauya min kamannin ta kamar ba ita din ba




Worst part awajen in ka dubi fuska kusan kowa babu mai jin tausayin mu sai ma tsana da tirrr dake bayyane a fuskan su karara


Sarki yace toh ke kuma gambo
Daga yau na yanke miki hukuncin barin Garin nan ta kofar yammma, kar na sake ji ko nasake ganin Ki daga nan har yankuna biyar da garin nan
Na haramce ki da kasar nan kiyi nesa damu chan kuje bariki Bakin halin ku shi zai kashe ku..




Guda aka rangada aka shiga tafi ana shewa..


Sarki da mukaraban sa na barin waje aka ma na eeele ni da ummah aka sa mu agaba har hanyar kofar yammma bamu dauki komai namu ba haka muka fice daga garin kurwala.






Ga dare yayi ga bakin ciki ga yunwa ga radadin takaici gashi da kyar ummah ke ja na bulalan da aka min har yanzu na damu na ga danyen ciki ajiki na..


Tafiya kawai muke yi mu biyin mu babu hutawa.
tun muna kukan har muka dena kowa yana ji da abunda ke ransa..


Da kyar muka kai zauren wasu yan uwa fulani..


Matar gidan ita ta taimaka mana da ruwa ganin yadda muka galabaita anan ummah roka mana sarari muka zauna muka huta don kuwa akwai tafiya sosai agaban mu kafin mu kai wani gari....


"sai da na dan huta na dada jin yadda Ciki na ke min ciwo amma bana ma so na ji tsaban yanayin dana tsinci kaina na kuncin rayuwa...


Ummah kam tayi shiru kamar bata tuna komai...
Cahn Tace saratu? Inaga fa zan dan nemi kudi anan yankin saboda kinga yanayin ki baza mu iya jure tafiya da kafa ba gashi bansan ina zamuje ba..


Nace ummah kudi kuma ta yaya zaki samu anan?


Tace "Ke dai bari mana ki gani naga kamar akwai aiki wajen wancan bafulatanin tayi min nuni da shi wani manomi ne sosai ana kan hidiman masa dure a buhuhunan sa ..


Nace to ummah ..nima zan taya ki


Ta girgiza min kai alaman ah a na huta kawai nan ta mike tabisa wajen su..

Cikin hikima da dabara irin nata ta cire kasala da gajiya ta hau aikin ma bafulatnain nan kamar bakar jaka..
shikan sa sai da ya sha mamaki..


Buhuhu na 15 da rabi na sabon gyero umma ta samu ta dura masa kafin nan an aneman goma saura na dare sai layi da haki take idanun ta sunyi jajir dan wahala..




A hakan ma bata daddara ba duk da ma ummah na da saurin sabo amma anan ba wanda ya san meke faruwa da mu tace ma matar gidan insha Allahu washe gari zamu tafi idan aka biya ta..


Anan muka kwana bata mana rowan abinci ba kuwa,muka sauke gajiya cikin daren har da wanka....


Washe gari ban tashi ba tsaban yadda nake ji da tsamin tsamin duka ajiki na ga laulayin ciki da kananun ciwon mara.


Umma kam tuni ta bi layin karbo kudin aiki...
Dubu10 kacal ta samu
A haka ma ji tayi kamar an tsoma ta a Aljanna


Ta zo ta daga ni tace maza ki shirya yanzu zamu tafi kar azo agan mu anan yankin saura mana yanki 2 mubar kurwala....yi da jikin ki saratu..


Nace toh umma na mike adaddafe na shirya ..


Fura mai kyau ummah ta siya dukan mu uka sha harda matan gidan..
Umma ta bata hakura ta bata dari biyar daga kudin aikin ta.
Daga nan muka fece....


Tafiya muke, duk da haka ba Abun hawa
Ciwon ciki na sai dada tsanantawa yake ga waje da nisa gari biyu zamu wuce amma ko rabin daya bamuyi ba ..


Tun ina boye ma ummah abun da nake ji har na soma wash washhh...


Anan ta riko nj niki niki tana mun sannu sannu in mun danyi nisa sai mu zauna bakin inuwa mu huta
Idan naji dama dama sai mu wuce
Har muka fice gari na biyu muka shiga na karshe..


Ido na yayi ja sosai, tsaban azaban danake ji aciki na..umma tace ki daure saratu ba abun hawa ne da sai na daura ki kije tashan mass kki jira ni,
Amma babu kiyi hakuri kinji..?


Anan na dan soma zub da hawaye na sosai..nace babu komai ummah amma cikin nan ne sosai yake murda ni..


Cikin damuwa ummah tace kiyi hakuri saratu nasan dole zaki ji wahala bari muyi sauri mu samu mota sai ki huta...ko zaki ci wani abun ne yanzu?


Na ce mata ah"ah


Nana Ta cigaba da lallabani muka soma tafiya..


tausayin umma ya sanyaya min zuciya ta naga kamar tama mance da kanta a kuncin rayuwa da bakin cikin da aka cusa mata ni kawai take kulawa


Dalilin haka yasa Nima sai na tursasa zuciya na na dage duk da abunda nake ji har muka kai tasha muka shiga motar haya
wanda dama ya rage guda daya ne tall shine na zuwa kano..


Ba yadda muka iya anan din muka tsakuro


akan balance ma na zauna nikam don Ancika makil shine mota a yau din na karshe kuma ba halin jiran wani...


Dadin Abun dai an rage mana ana kudi ne dan adubu 2 da dari 2 aka kaimu har kano


Bamu da isa ba sai wajen karfe 8 saura na dare..


Kowa ya fita a motar amma nikam na ma kasa dago kaina tsaban ciwon Ciki ga dumin jini da yake yawo a cikin jikin na ta ciki ina ji...


Umma ne ta daddafe ta jawo ni a hankali na fito..


Ganin yadda jin ke bina yasa hankalin ta ya tashi sosai....

" a gurguje ta sama min waje ta ajiye ni kar mutane su fara lura da halin da muke ciki ga shi a kanon ma ta baya muke wani local govmnt ta cahn wajen kumbotso bamu ko shigo gari karara ba


Kuka nake yi a hankali ena wayo Allah wayyo Allah ciki na ..zan mutu...ummmah..uhmmm
Mmmm numfashi na ke sama sama , a duk lokacin dana motsa kuma jini ke fita daga jiki na.


Nan Nayi lugwi ina nishi Ban sake ganin umma ba sai da wata yar dattijuwa tace gata nan baiwar Allah wannan ne yata ce"
Ki taimaka min dan Allah bata da lpya ne


Kare min Kallo matar tayi taga inayi kamar mai shirin dauke numfashi na ina wssshhh ita kanta tasan bana jin dadi




A take Matar tace to muje mana..


Umma ta rike ni muka kama hanyar isa gidan matan wanda bai da wani nisa da tasha.


Sunan ta sahura bazaura ce wacce bazata wuce 35-37yrs ba


Anan gidan ta dakuna biyu ne amma babu komai aciki sai tabarma da katifa sai dan ghna na kayan sawa.


Umma ta shimfida ni akasa tana cewa nagode baiwar Allah ko kinsan inda zan hada murhu na sami ruwan zafi?




Wani irin kallo ta mana Tace "Ah a, malama nifa kawai taimaka miki nayi ku sami wajen kwana amma ba ruwa na da wani abun ki..


Umma ta marairaice tace kiyi hakuri nima tambaya kawai nayi yata zan dan kimtsa ki taimake ni..


Batace komai ba Tayi ma umma nuni da wani murhu wanda daga gani ankai kusan Shekaru biyi ba adaura komai akai ba..
nan umma ta je waje ta shiga tattaro karare da duk abunda zata samu ta hada min ruwan zafi wanda ya sa ta
Ta kai 2 hrs sannan ta kammala..


Anan kafin ta zo na sume ya kai sau hudu tsaban azaban lalurin ciwon cikin ...


"Saratu? Saratu... sai naji kamar a mafarki ummah na kira acikin layi na bude idon kamar wance ke sjirin shekewa lahira na amsa da naaamm ummmah..ummah mutuwa zanyi ki taimake ni ummah ciki na ciki na ummah....


Rigijib ummah tayi agaba na duk da bana iya bude idanuna da kyau na tsinkayo bakar tashin hankalin dake tattare da ita "tace sannu saratu, sannu kinji ,bazaki mutu ba ina tare dake bari naje na tsaftace ki ko zaki ji dai dai..


Ta daga ni riki riki mukayi bayi..anan ta sullebeni ta shiga wanke ni tana matse min ruwan aciki na jinin nan kuwa kamar ana zazzago shi ne,


Ummah tuni ta fahimci cikin ne ya lalace amma bata tabbatar ba..


Haka ta min jinya da dabara irin na su na yan kauye tasss na dawo da dan gwabi sai jiri da rashin karfin jiki danake ji


Dan kwalin ta ta bani na daura da shike ya kaini gwiwa sai ta dan yage
mayafin ta tayi min nadi nasa tsakanin cinya na na tare jini..


Fes ta wanke kaya na ta shanya a haka ma bata dawo dakin ba sai da ta fita tayi yawon neman chemist ta siya min maganin ciwon ciki ibrufen da paracetamol ta hado da shayi mai dan yaji yaji hadin kasuwa da bredi daga wajen mai sai dawa ta zo da shi..


Sam na kasa hana kaina kuka sosai nake yi cikin tsumayi da tsananin bakin ciki..


gashi bana jin karfi sam sam ajiki na


Ummah ita kanta sai da tayi shiru ta zuba min ido..
tace "Wato ke saratu magana baya wucewa wajen ki ko? Kina gani dai baki da lpya
Har yaushe zaki cigaba sa damun kan ki akan abunda yanzu ya zama tarihi?
Ki ci abincin nan kawai bana son shashanci


"Nikam ina sai kukan kawai nake yi mai ban tausayi.


Abun ya ishe ta zata sake magana nace
Ummah..."wallhy ke nake tausayawa ke nake tunawa ummah kina shan wahala da hakkin da bana ki ba Allah zai saka miki ummah...


Nan itama ta taro hawayen ta sai yanzu ta gano ashe tausayin ta wai nake ji abun yana damu na...


Nan ma bata lallaba ni ta hau bambani
Ke saratu ni bana son Shasahan ci kici abinci kawai ki rabu da komai ai ya wuce ...
Nikam ai mahaifiyar ki ne duk duniya babu abunda nake takama da shi in ba ke ba raina naki ne saratu akanki zan iya mutuwa ma ba wahala ba


kar kisa aranki wahala muke yi abunda ya kamata nayi miki kwanan nan..
Ko kina da wanda zai miki ne?


Cikin kuka na gyada kai alaman ah'a nan ne ta shiga lallabani har na samu naci abincin...


Ciki na yayi kauri ya dau dumin shayin sai muka kwanta bacciii


Chan dare yayi nisa na farka sakamakon tsanantawa da ciwon ciki na ya dawo


Umma na hange agafe tnaa bacci agajiye har gwarti ke deban ta..


Sai naji bazan iya tashin ta ba kawai na cigaba da dauriya na abu na gaba gaba
Kafin safiya na suma bana ko motsi




Da safen A wargaje ummah na ke tashi na amma shiru har matan gidan wato sahura ta karaso


Ganin halin da umma take ciki na tashin hankali gani a kwance cikin jini bana ko motsi ya sa ta tsorata ta soma mata masifa


Tace nifa ..Kawai ku fita ku bar min gida na ai dama Kwana kuka ce gashi Allah ya kawo mu safiya ...
Maza maza kufice nikam ban isa ba da wannan fitinan ba..


"ummah tace emmm Baiwar Allah dan Allah kiyi hakuri ki dubi girman Allah ki barmu na same mafita ma yata nasan ciwon ta ne kawai ya tashi zan je nan na siyo magani zata farfado.


Tsoro yasa Sahura ta turje sam taji sauraron ummah har sai da ummah ta ce to ta ara mana dakin zata bata kudin na san wani lokaci.


Suka yi bargain akan dubu 7 da kyr ta yadda ta karbi dubu 5 ya rage mana saura dubu 1 dawani abu kacal a hannun mu


Nan Kafin ta kyale mu mukaji sarari ta tausaya bawai bata tausaya ba


Kuma ta lura umma na duk yadda akayi batayi karatun boko ba bare arabi
Ba abunda ta sani anan birni ita dai akwai wayo ne sosai


Ganin yadda umman ke jeka ka dawo daga chemist zuwa kai na ya sa ta je ma ummah..


Tace "Ai na fahimci matsalar yarki wato cikin tane fa ya zube ya kamata ki kaita asibiti a duba ta.


Umma ta ce toh"amma ina ne asibitin naku
Ko zamu iya zuwa adan duba min ita ..


Sahura ta kira wani yaron matashi shi ya kaini ni daa umma har sabitin gwamnati dake tsallekan anguwan..


Bayan wulakanci da muka sha da zagi wajen likitan su akan cewa ba akawo ni akan lokaci ba sai da abu yayi nisa anan aka bani gado aka shiga duba ni..


Bayan wasu lokuta kadan likita ya taho dakan sa ya same umma yaron nan na ne tare da Ita don sahura tace masa mu baki ne


Yace kece mahifiyar ta ko?.umma tace eh likita lpy dai ko?


Yace to lpyar kenan dai amma meyasa kukayi sakaci kuka barta tayi ta zubda jini haka?ba kisan zata iya mutuwa sanadiyar hakan bako?


ummah tace" ayi hakuri likita mu Baki ne agarin a taimaka mana tafada cikin magiya


Likita yace hmmm ku dai yi hankali nan gaba kar kisake irin wannan wasa da rayuwar mutum..


Yanzu dai sai kuyi hakuri ta rasa cikin dake tattare da ita, sannan tana bukatar wanke cikk da karin jini....


Sai ayi sauri a kawo mana ko kije chan ki biya kudin... ya mika mata list bill din dubu 15 har da yan kai...


Umma ta duba
Da kyau ta gani bata ma iya karantawa ba kuma bata ce komai ba ta juya asanyaye zata bar wajen


Likita yace malama"
zakuyi hanzari fa don rayuwar yarki na ciikin hatsari muna bukatar kayan aiki nan da 24hrs idan ba haka komai zai iya faruwa ta riga ta rasa jini da yawa...


Ummah tace to likita na ji za 'a kawo


A lokacin kuka ne ke so ya kufce mata ga
Wani mutsumusan tashin hankali da ke yawo a zuciyan ta na jin halin da ake ce ina ciki


Tace wayyo ni fadima a ina zan samu kudin nan "
Tafada tare da daure a hannu akai cikin tsananin Jimami..


Sosai yaron da ummah tazo da shi ya tausaya mata
Yace ya kamata muje ki duba ta tunda yanzu babu kowa a kanta


Umma tace haka ne muje..
Suka zo dakin da aka ajiye ni har ta zo ban farfado ba an dai samin ruwa ina kwance kamar mutacciya..


Hakan Ya dada karya zuciyan ummah kukan ta zage tayi mai cike da dumbin bakin ciki agaba na..
yaron nan ke bata baki har ya samu Suka fito waje...


Anan ummah ta shige neman mafita...


Tace "Ummm kana ganin ta ina ne zan fi samun aikin gaggawa wanda zai kawo min kudi ko min kankantan sa Zan iya kar kadamu..




Yaron yace "Ah a gaskiya nikam ban sani ba.


anan kuma ai kafin ki samu aiki akwai wahala gaskiya bazan boye miki ba zai yi wuya sai dai kiyi kadan kadan ana baki dai dai gwargwado rayuwan nan birni fa kamar na wani wajen bane..


Ummah tayi ajiyan zuciya bataa dadddara ba tace amma ina dai zan samu ?.


yace Eh insha Allah, kiyi nan hanyar akwai masu siyar da abinci dayawa a bakin hanya kije bazaki rasa abunyi ba ko da 500 kike samu ai arage wani aBun


Ummah tace toh angama
Sai ka rukuta min sunan nan wajen saboda kar na bata kasan da bakunta ..


Yace haka ne nan ya nemo aron takarda ya rubuta ma ummah..


Nan Ta shiga yawo cikin kasuwa neman kudin aiki kafin nan da 24hrs din ya cika..


Acikin kasuwar Tun karfe 9 saura take naman inda zasu taimake ta ma shiru saima korata da ake


wasu ma sam basu yarda da ita ba duba da yanzu ana tsoron maganan Boko haram


Sosai taga wulaknci da cin zarafi..har mari saida ta karba wajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login