Showing 21001 words to 24000 words out of 165901 words

Chapter 8 - SAMARIN SHAHO Completed Book Surayyhms.txt

Advertisement

Surayya   

06 Jun 2024

13860

tashi ganin zan mutu a hannun sa ba sai da Allah ya bani ciki,miji na yayii bakin ciki sosai da na gaya maza, kuma nasha duka wajen sa har sai da na kasa tashi..


fitar sa yaje ya karbo min maganin zubda ciki ban ma san da ga ina ya samo ba kina gani kinsan ba mai kyau bane..ya jika a ruwa yace maza na shanye tasss a gaban sa ko ya kashe ni...
Wallhy baida imani gambo, haka na sha nayi ta ruwan jini anan kasa a daki na tsawon lokaci sai dai ya zo ya wuce ya barni rai na a hannun Allah,gashi matan sa basu isa su zo kusa dani ba ya hana kowa motsawa..


Washe gari Ban tashi ganin kaina ba sai akan gadon Asibiti kawata ce aminiya ta ita batayi aure ba ma itace ta kaini asibitin anan na kwana ana duba ni ..


"dana farfado da danyen jiki na na lallaba na taso na wuce gidan mu,Ko da naje da maganan nan mijina ya gama kulle nashi,kuma bayan sa suka bi sosai suka kuma tsane ni.


Ko magana ba abari nayi ba aka shiga min fada babu wanda yake so ya saurare ni ,kawu na har da min dan banzan duka cewar sa na tona musu asiri...


Duk na lura da su kowa na fadan ne da son zuciyan sa,su baba su kawu duk dan abunda suke ci ne a karkashin miji na na arziki basu so ya rabu da ni


Dana tabbatar da hakan Nima sai nayi zuciya nace bana son aure na tada bori na haukace har sai da na tunzira miji na ya sake ni a gaban kowa da kowa


Su ummah da su baba Haka Suka taru akaina suka ce na bada hakuri a sasan ta nace sam sam na kuma turje nayi zuciyan maza..


..wannan kuskukern ya sa uwata da ubana suka yi Allah ya tsine dani ..


Nayi nadama gambo amma raina ne ya baci ina ji ina gani da kuruciya ta amma zuciya ta ta soma kangare wa da rashin imani...


nasan idan na koma aure na miji na kashe ni zaiyi kuma bazai dame su ba don ba su san wani hali nake ciki ba.


tun daga ranar kowa ni abu marar kyau ya same shi sai ya laka min alhaki


Bakar Tsangwama da mummunan tsana daga iyaye da dangi ya sa na bi shawaran zuciya na na fito duniya har kika ganni anan...


Yau shekara na kusan 15 kenan Da barin gida kuma nasan ba mai sake karba na ko da na koma




Wani bin nakan nemi labarin su amma su ban taba ji ance sun nemi ni ba, ta cigaba ba kukan tana cewa to me zanyi gambo?a duk lokacin da na tuno da ni wacece sai na ji na shiga wani hali, dole na soma shan wayannan abubuwan don su sani bacci kar wata rana na mutu da bugun zuciya..




Ummah Itama Tun tuni ta ke sharben hawaye, tabbas wasu iyayeen haka suke ba ruwan su da halin da yarsu zata shiga ciki ko take ciki musamman idan miji ya zo yana musu sallah sallah ace yana da kudi kuma yana dan kyautata wa
To fah yar su bata da baki kuma ko wani laifi ko ganganci na ta ne ita kadai.




Hakuri ummah ta shiga bata da dada dan kalamai kamar wanda ta san wani abu game da addini sosai..
lafazi take na masu imani tana tausasa zuciyan sahura har ta dena kuka


Ta kuma duban ummah tace"yau zan tambaye ki tambaya na karshe gambo,
Dukkan mu bayara bane shiyasa bazan sake takura ki ki gaya min labarin ku ba,


amma na roke ki ki saukaka ma kanki da yarki ku nemi duk wani hanyar da zai taimake ki ko ma ya take don zaman birni ya sha bambam da duk kauyen da kuka fito...


Ummah tace haka ne ai na gani da kaina..sai dai labari nan ne babu dadin ji sahura kuma tsoro nake ji.

Anan itama ta baje ta bada sahura labarin mu kaf ko tunanin sahura zata iya mata karya batayi ba tsakani da Allah ta gaya mata har ranta duk abunda muka fuskan ta..


Da ita ma abunda ta furkan ta na wulakanci da tozarci awajen mutane wanda basu sani ba..


Sai dai har ila yau babu abunda yafi shiga ran ummah kamar fyaden da ssa danjuma yayi mata akan kudin jinya na..she feels really miserable about it.


"jikin sahura yayi sanyi Sosai da sosai ta ke hawaye suka sauko mata har muryan ta nakin fitowa yau ta soma jin ina ma da ba haka ta karbe mu ba tun farko,


Suka taru sukayi ta jimami da kuka suka kuma rarrashi kansu, don da ita da umma kusan sao'in juna ne shekarun su bazai wuce 35 -37 ba..


Anan ummah tace,ni fa da kike gani na sahura yanzu babu abunda yake raina illah na sami abun yi na taimaka ma kaina da yata saratu, ina burin saratu tayi makaranta ta taimaka ma rayuwan ta ko da bana raye bana burin saratu ta kare a hakan jikin jahilci rashin wayewa da wahala, kuma in Allah ya yarda sai na cimma wannan burin nawa..


Sahura tace ni kuma zan baki dukkan goyon baya gambo,


Kar ki damu da wanda zai cuce ki ko ya kece miki mutuncin ki rayuwar nan dama cude ni in cude ka ne ,saboda babu wadda zaki iya masa ...
Ummah tace haka ne




Tace"gambo Idan kika tsaya zaki yi na mutunci da gaskiya har duniya ta nade bazaki kai inda kike so ba kuma zaki wahala sosai sai dai ma ince wani wahalan shi zai kashe ki...


Ummah ta kuma cewa haka ne kuwa aini na gane ma idanu na sahura akwana biyun nan da zan gaya muku bakar wulakancin da nake sha da bazaku sake bari na na fita neman kudi ba


Sahura ta dan jinjina,
Tace yawwa gambo na fara wani tunani amma bansan ko ya zaki dauek sa ba,


ummah tace ina jinki...


ta dube ummah tace Tun da kince wannan ma cucin marar imani ya baki lambar sa yakamata mu san abun yi akan sa.. Ni inaga ma Ta kan sa zamu fara


Ummah tace Allah ko sahura?"tunanin ta ko su ma din wani abun zasu masa ko zata dan ji ta huce kadan daga raunin da ya dasa ma ranta ..


Sahura tace
Eh,
ai yanzu bamu da lokacin sanya ko jinkiri, rayuwar mu da rayuwar saratu zamu sa karfi da karfe mu daga sa duk wanda ya cuce mu sai mun cude shi shima,
Ke dai ki gaya min gaskiya kin shirya zaki iya sadaukar da komai dan kii cmma burin ki dana saratu?
Ummah ta dube sahura da karfin gwiwa tace ashirye nake sahura.
Tace kin tabbata gambo? Ummah tace wh na tabbata
Shiru ne ya ratsa wajen sahura na kan hada tunanin ta chan tace
Yanzu kinga dare yayi sosai ki kwanta gobe ma karasa magana


insha Allahu mafita ta kam ta samu ke kanki zaki fi gane ma rayuwar ki yanzu..


Ummah tace ko? toh shikenan, sai da safe sahura..a haka sukayi sallama




Tun shigewar ummah daki sahura ke tunani anyabkuwa ummah zata amince da shawarar data yanke musu?


Ta kuma kawowa wahalhalun da ummahn ta sha sai take ganin kamar ko dan su ma kawai sai sai ummah saukin amince mata..


SSa danjuma?
Ko acikin yan siyasan da ake kaisu musu aiki suna basu kudi bata tabajin sunan ba,


daga bisani tace dole na bincike shi ita kuma gambo dole zata tayi abunda bama so din. Idan ba haka ba bamu da wani mafita


Ta dade Cikin wannnan tunani bacci ya dauke ta..































*WATTPAD VOTE AND FOLLOW @SURAYYAHMS*


_OFFICIAL CATTY_
[2/23, 23:11] ‪+234 802 646 5734‬: *🅱BRILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*


_Asma'u adilili gaisuwa ta gare ki_


_PAGE7_


Da sassafe sahura ta shigo dakin mu duka muna bacci, jakar ummah ta daga ta bin ciko ta dauki compliment card din ssa danjuma tayi waje cikin sauri..




da muka tashi ranar tamkar an dan washe ma ummah wani nauyi ne a kan kirji ta, sosai take jin dama dama da dan karfin gwiwa sanadiyar samun tataunawar da sukayi da sahura ajiyan..


Ni kam bansan komai ba,..
sai na share ko ina na kammala dan kimtse kimtse na.


Gidan da ummah takanje tayi musu wanke wanke safe su bamu abun karyawa ummah ta je


Haka itama anty sahuran dana tashi yau ban ganta ba..


Zaune nake akan tabarma ina jiran shigowar su, dan kuwa a halin da muke Ciki bana damuwa da komai sai halin da mahaifiya ta ke ciki..


a kullm tunani na meyasa ummah bazata bari na taimaka mata ba, abun na matukar damu na..


Salam alaikum,naji dadaddan muryan ta mai dauke da sakewar zuciya..


sai naji dadi haka kawai ya ziyar ce ni na mike tsaye cikin fara a na amsa ta


Kwanun da ke hannun ta sauke kasa tace fatan baki galabaita ba ko saratu ga abinci nan xoki ci"


Na dan yi murmushi Nace"toh umma bari na kawo mana ruwa na shige daki...


Anan kan dakali muka zauna tare muna cin abincin ,dan shinkafa ne da wake a hannu a hannu,ina lura da yadda ummah take kakamewa saboda ta bar min wanda zai kai min magwogoro...


Cikin raina hakan na mugun damu na sabida nasan ita kanta yunwa take ji ga aikin da zata fita yi..


Yanzu nan ni kaina nasan wahala take sha ga ummah da kokari da azama wajen neman na kai..
Wannan wani irin rayuwa ne da mu? Ina ci ina tunani.


Ban ko dade ba sai na ga ta tsame hannun ta tana lashewa daga bisani ta dau buta ta wanke ta mike tare da cewa kinga bari na fita na zaga ko yauu ma zan dan samu wani abu..


A lokacin ni kadai nake jin zafin da raina ke min Kamar zanyi kuka nace toh ummah Allah y baki sa'a , tana lura dani amma sai ta dauke Kai tana cewa
naga kamar sahuran ma
Bata nan idan ta dawo kice mata na fita...


Na kuma cewa toh sai kin dawo..


akan kafan ta ta sake zaran mayafin ta tayi waje har ta mule ina binta da kallon tausaya wa ..


Ummah Tana kaiwa bakin layi suka yi kichibis da sahuran ta sha gayu kuwa sai sauri take"suka matso gefe tace gambo? Har kin futo kenan..


Tace ai naga baki nan da safen nan har kin wuce? Fatan dai lapya ko?


Sahura tace bar wannan maganan, ai dazu na zo dakin ki kuna barci.
Zo nan mu koma daga gefe dama akwai maganan da zamuyi dake mai muhimmanci..


Ummah ta bada hankali sosai suka tsaya daga gefe.


Sahura tace, dama bincike naje yi da safen nan akan wannnan mutumin da ya yayi miki fyade ranar,


Ummah ta gwalo ido waje tace habawa?


"Hmmm, bari kiji ingaya miki gambo ashe fa babban mutum ne sosai yana da kudi bana wasa ba,nan ta dan gaya ma ummah tarihin sa kadan bisa yadda ta binciko,


duk dama ba ilimi ne da ummahn ba amma ta gane ana nufin shi din tamkar bature yake tunda ance rayuwar turawa yake yi kuma cahn ya tara arzikin sa ..


Tace bazan bata lokacin gaya miki shawaran dana yanke ba gambo, tunda har shi dakan sa ya baki katin neman sa ..so nake kije ki same shi kema kina masa service yana baki kudin da zaki fara taimaka wa kanki da ryuwar yarki asiri arufe....


Samun irinsu akwai wahala sosai, tunda kina da shi a hannu tamkar baki da matsala ne gambo.


Ummah ta dan yi shiru,cahn ta dago tace ban gane mi keke fada ba fa Sahura..wai meye shi sabis"service' din?


Tace, ohhh Allah na gambo, to bari na miki dallah dalla..so nake kije ki same shi ki na masa aiki yana biyan ki..


Wani irin aiki kenan?..ummah tafada a dan birkice..
ai wannan mutumin baida wani aikin da zai bani sai da ya lashe jiki na sahura,ko duk abun da aka gaya miki kennan wajwn binciken naki?,,toh wallhy karya ake miki.
nima da fari ai cewa yayi xai bani aiki amma ya je ya keta min haddi..tirrrrr wallhy ah a.


Sahura da ke lura da ummahn tace,sai kuma yaya?,me ya ragu ajikin ki yanzu waya san haka ya faru in ba niba?yanzu ke da kike maganan ki in ba don shi ba ai da saratu sai dai muce Allah ya jikan ta?


...look gambo,yakama ta ki daura kanki akan tunanin sauki da nake hango miki da yarki. Lokaci yayi da zaki buga dutse da hannun ki ruwa ya fito.


Tuni ummah ta juya mata baya hankali atashe ta ce, tirrrrr kina nufin naje nayi karuwanci kenan?
Gaskiya badai nayi karuwan ci ba sahura zanje dai na nemi aikin kawai wahalar ta kashe ni..


"Sahura,tace iyeeh ta tabe baki tace haka kika ce gambo?
Ummah tace eh kiyi hakuri bazan iya ba.


Sahura bata ji dadi ba amma ta daure ta juyo da ummah suna fuskan tar juna, tace mutuncin ki da kike gudun kar ya tabu ya riga ya tabu gambo,yanzu wahalar da kanki kawai kike yi , gambo ki duba fa ki sa ma kanki nitsuwa kiyi abu guda daya da zai
Taimake ki


idan ma tsoro ko kunya kike ji anan ba wanda zai sa miki ido musamman ma da babu wanda ya san ku,


sannan bawai nace ki dawwa ma bane karuwanvi ba abu mai kyau bane.


Hikimata shine Idan kin dan samu abunda zaki samu kun taimaki kanki da yarki sai ki bari ki yi rayuwar ki yadda kike so ke da yita kin gane me nake nufi kuwa?. .


Ummah ta dan girgiza kai alaman bazata taba ganewa ba bare ta amince ..


Cikin zaquwa Sahura tace"nima fa zan tayaki gambo,duk halin da kike tunanin zaki shiga ena tare da ke..


Ko kina tunanin akwai hanyar da yafi mana wannann ne? Lokacin ki na tafiya ke kanki kinsan kwanan nan saratu zata dada girma irin girman da ke kanki bazaki so ba,
Maza ne ko ina ke kan ki kinsan bzamu dawwama muna boye ta ba masu b


Da ni dake bazamu iya kare ta ba, ba gwara mu saida ran mu tun yanzu ba kafin abubuwan suzo sufi karfin mu..


Ummah Ta dago ta kalle sahura tare da sauke karamin hawaye tace....gaskiya bazan iya karuwan ci ba sam sam sam sam bazan iya ba ..
Wannan ba tarbiya ta bace sahura.


Ni dai zanje na cigaba da aikin wahalan a haka bazan iya ba kiyi hakuri kinji?
A rude ummahn ke maganan har jikin ta na bari tayi kuma saurin dakale hannun sahura ta bar wajen tana kuka..


Wani irin yanayi sahura ta shiga ciki na rashin jin dadi amma sai ta daure ta bi ta tana jawo ta tana fincikewa


Tace ke gambo kar ki tara makanki jama'a ki tsaya muyi magana...


A zafafe ummah ta juyo tace nagode da dukkan
Taiimakon ki da kulawar ki sahura amma wallhy na gwammaci na mutu dana sake kai kaina ma wannan Tsinannen shegen...
ki sake ni naje sahura ki sake ni naje neman halak dina kawai shiyafi min..


" ba yadda ta iyah da ummah sai tace To
Kije!


Kije ki kashe kanki daga nan har mahdi ya bayyana naga ko zaki tabuka wani abu.


Ni dama Sauki nake nema miki gambo da kamar kinsan abunda ke miki ciwo a duniyan nan zaki gane hakan amma kin butulce makan ki...
To wallhy ki daina zubda hawayen banzan da kike yi na cewa kina son rayuwa ma saratu babu abunda kike so mata illa bakar azaba irin namu...


Ummah ta girgiza kai batare da tace komai ba ta fincike hnnun ta jikin sahura ta wuce tayi gaba..


Da kyar ta rarrashi kanta ta waske ta tafi neman aikin amma sosai zuciyan ta ke mata nauyi da tunani kala kala..


Itama sahuran haka ta kai kanta cikin gida ta yi kwanciyar ta, tunanin ta itama take yi dama ta san dole sai an sha fama kafin ummah ta gane abunda ta ke gane mata..
Amma gani take hakan shine masu mafita mai inganci.


Ita gani take kawai a matsayin su na marasa gata da galihu, tsinnanu,marasa ilimi babu wani abunda zai yi kargo arayuwan su dole su rufe ido suyi wanda basu so din..


Ita ma bata son haka amma ko da ta zo birnin itama a dole da shi ta dogara take tallafa wa kanta sai dai babu wanda ya sani don ita kanta ba son rayuwar take ba..


Bangaren umma kuwa Tun daga ranar da hakan ya faru tsakanin su da sahura abubuwa suka dada tsanan ta mata


Duk dama sahuran tayi kokarin wajen shawo kanta amma fafur ummah ta turje..


Tun daga nan itama sai bata sake dago maganan ba kuma bata nuna tayi fushi akan ra'ayin ummahn ba ita dai ido ta zuba mata,,




Sai dai yanzu idan ta fita kasuwar su dake kusa neman aiki da shike bayan gari ne, toh daga mai bata aiki agidan giya sai mai ce mata ta zama mai musu aikiin danna a Restaurant.


Abubuwan rashin mutunci ba wanda bata gani ba


Ta haka sahurah ke shigo mata da maganan cikin salo tana nuna mata dalili


Gashi dai boro boro maganan sahurah na cewa ummahn wahalar dakan ta zatayi kawai a rayuwa ya nuna afili amma ummah sam ta ki ta bada kai ma karuwanci.


duk suna yi ne ban sani ba,


Rana guda da sahurah da ummah suka samu wani mummunan tsabani akan shigowar da wani dan harkan ta yayi bazata har bayan gida ya iske ummah tsirara tana wanka .


Duk dama anty sahurah tayi rantsuwar cewa bata san da zuwan sa ba


amma ummah sai take ganin kamar kawai sahurah ta nace ne sai ta gurbata mata tunanin akan tarbiyan ta da wayo..


hakan ya sa ummah ta roka mana temporary work na aikin gida a nan gidan alhaji buba, inda da take wanke wanke da safe ana bata abinci..da shike ma mai aikin nasu na asali ta haihu taje gida


sai aka bamu daki guda daya muna zama agidan.


Gidan ba laifi amma sai dai matar gidan na da mugun kyankyami, ga son girma da nuna isa akan gidan don haka ne ma sam sam bata son kuskure.


Tsakanin ummah da anty sahurah sam banji dadin ‘zaman su ba sabida na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login