Showing 24001 words to 27000 words out of 165901 words
Chapter 9 - SAMARIN SHAHO Completed Book Surayyhms.txt
saba da anty sahurah sosai..
duk da yanayin rayuwar mu ita bata nuna mana gadara da kaskanci boro boro
Sati biyu mukayi anan gidan alhj sai da na matsa ma ummah suka shirya da anty sahura suka fahimci juna.
Sai dai ummah tace bazamu koma gidan ta ba tukun a tunanin ta ko idan anga kwazon ta wajen aikin ta zai sa a dan bata dama itama tayi aikin permanent da su
Alhj sabo shine mai kudi a duk yankin anguwar mu
Haka muka zauna muna aiki da shike aikin gida ne sai nake taya ummah na ,aika da sauran su.
A kwana a tashi zaman mu anan ba abunda muke fuskanta sai kaskanci amma bai dame mu,sai a cikin kwanan mu na ashirin da hudu a ranar da daddare
Muna bacci wasu mutane suka shigo gidan alhj.
kowa ya tsora ta musamman ma ni da ummah da muka tabbatar cewa barayi ne fa suka shiga cikin gidan sata,
Bayan shigar su da kamar minti 10 sai gashi ana buga namu kofar,
Kamar zan shide dan tsoro na rike kafar ummah sosai muna rawan dari..
haka aka fito damu tsomo tsomo aka hada mu da su alhaj da hajiya akasa tsakar gida.
Jaka ne a hannun su alaman sun karbe abunda suka zo daukewa daga ciki.
fuskan su duk arufe yake,
ogan su ya fara cewa mu bashi kudi ko ya kashe mu,...
Da kyar ummah ta bude baki cikin tsoro ta ce musu mu masu aikin gida ne bamu da ko sisi sai abunda za'a bamu..
ban san ko wannan maganan bane ya bata ma hajiya da alhaji rai.
ko zallan tsoron bindigogin dake kanmu ne oho
"Har ya sa suna ji babba daga cikin barayin nan
Ya ke jayayya akan idan har ummah bata da kudi zasuyi raping dina..
Hankalin ummah in akwai karshe wajen tashi
Ya kai nan..har ta mance bindiga ne akanta wajen roko da magiyan da sunan Allah akan su rufa mata asiri amma ba imani ko kadan aran su
Ji nake kamar sun kashe masu gadin gidan ma don babu motsin kowa..
Nan in banda kuka babu abunda nake yi..
haka suka damke ni zasi kwantar dani agaban su ummah Tazo da gudu cikin kuka tafada akai na tana dada rokon su su kyale ni cikin kuka mai ban tausayi da tashin hankali..
duk wanda yake da imanin wajen sai da ya sauke mana hawaye amma ko ajikin su..
Na rude sosai ina cikin tashin hankali har sai da na budi baki nace ma ummah,in har za'a min fyade toh lalllai zan iya mutuwa a yau ta yafe ni....
Kamar na dada taurara mata rai ta dada rufe ni ta kankame ni tace sai dai akashe ta amma kam bazata bari a cutar dani ba..
Dariya barayin nan suka shiga mana
Yace ma ummah shi ba zai kashe ta ba amma zai koya mata darasin da bazata taba mantawa ba
A bisa bata masa lokacin da tayi yanzun..
"Innnalilhi wa inna ilahi rajiun inaji ina gani yasa aka kai masa ummah na cikin dakin mu...
Ya bita ciki saura na kanmu sa bindiga
Ba abun da nake ji sai motsi da kukan ummah wajen minti 14 sai gashi ya fito yana gyaran wandon sa...
A wannan lokacin karamin bugawa zuciya ta tayi ina ta kokarin kare kaina daga tabewar hankali..
Dai dai da shigowar wani a wargaje yana cewa ogah is time..muje kawai babu lokaci
Duk sun fahimci kansu sai suka hanzarta suka bar mu anan...
Da uban gudu na mike na shige dakin
Ummah ne a takune agefe ta rufe jikin ta da kunceccen zanin ta tana wani irin kukan dake taba min kokon zuciya na...
agaban ta na zube ina bari duk na kasa sake muryan na domin kuwa kukan dake damuna ya harde min magwaro tamkar idan na bude shi zai harde ne in mutu.
kuka kawai muka rungume juna munayi ba wanda ya iya magana mai tsayi..
Har Allhj da hajiya suka shigo suka bamu baki kamar da gaske..
A daren da bamuyi bacci ba tsaban kunci.
amma sai dai kuncin bai kai wanda muka fuskan ta ba bayan an gama bincike game da barayin
duk fushin asarar da su alhaji da hajiya sukayi kaf suka sauke shi akan kowa musamman ma mu maikatan gidan..
Karshe ma ta sa aka bincike ummah a caji ofis cewar ta hala samarukan ta ne ta hade baki da su don su cuce su.alhhj ma ya goya mata baya wai ai ba ataba zuwa musu sata ba sai da ummah ta fara aiki da su.
Da kyar anty sahura ta taimaka aka gano gaskiyar lamarin aka kyale ummah
haka suka kora mu ni da ummahn,wajen masifar ba amana adalci ba har ummah ta kona kafar ta da ruwan zafi tsaban bacin rai da takaici..
Alhj har da ce ma ummah na ai dai dai kenan
A ganin sa dama wacce bata da miji kam ai watsasiya ce..
abun yamin zafi sosai
Bayan haka Gidan anty sahuran muka sake komawa ta tausaya mana sosai...
Yanzu hakan anty sahura da ni ke sa ma ummah magani a kafarta daya kumbura sosai yana fid da ruwa da kyar take dingisawa take fita gwanin tausayi...
babu wanda yake tausaya mata abubuwa sai chagude mana sukeyi,
wata rana ma sahura ke ciyar da mu rana da yamma da dare..
Tunani sosai ya sata agaba damuwa da sacewar imani sai ya soma shigan ta sosai..
Dadin karawa da taga yan maza sun fara gane akwai budurwa anan har an soma kawo hari ..
Hankalin ummah sai ya tashi yaKi kwanciya,sai ma ta yanke fita neman abincin kwana biyu tana zaune tana sakewa da warwarewa tana kuma bada hankali sosai wajen jinyar kafar ta don har ya bushe yana rufewa..
Yau cikin watan mu biyu har da sati guda Bayan rabuwar mu da rayuwar mu a kurwala .
A daren yau ne ummah ta yanke makan ta daukar shawaran sahura
Zata je kamar bazata je ba, amma ta riga ta yi tunnanin ta ta hada calculation din ta alamun kuma sun fi tasiri a zuciyan ta..
Hakan ta je ta samu sahuran suka sake kulla fahimtar juna
Suka warware niyyar su akan saving rayuwar da zasu bada karfi akai da cimma burin su na rayuwa..
Sannan ummah ta ce" duk abunda zatayi zatayi ne sabida na tashi na tsaya na da kafa na a duniya,
Tana samun hakan har abada ta bar hanyar....
Sai abunda rayuwa kuma tayi...
Sahura ta dada karfafa mata gwiwa tare da bata tabbacin kwanan nan burin su zai cika
Kuna zasu zama mutane kamar yarda suke muradi
Komai zai daidaita..
Duk sunyi hakan ne tare da alkwarin boye min Komai...
Sirri ne tsakanin su wanda sukadai suka shirya shi
Ina gidan sai kawai nake ganin wani sabon sHakuwa ya shiga tsakanin ummah da anty sahura...
Sai naga ummah yanzu ta watsar da neman kudi
Anty sahura ke bamu abinci mun dada dawowa tamkar gida daya jini daya..
Abun da yafi bani mamaki shine yadda suka sa kai akan wasu abubuwan,kamar wanka kwalliya, sa sutura koyan magana da dan tawalidu na yan birni naga duk umma na koya wajen anty
..na dauka ko duk strategy ne na neman wani aikin tunda ga wahalan data ke sha awajen har da rainin wayon yan birni.
Wani wata gudan suka dauka suna shiri..
Da shike sun sa abun arai lokaci kalilan ummah ta iya sa suturan da anty sahura ke bata
Ta kuma iya sa powder da jan baki ga wani sabon Wayo da ta karo ma kanta don yanzu na ji da salon suna ummah ake kiran ta wato fadima...
Abu kamar wasa, suka shirya tsaf ranar asabar da yamma suka kama hanyar Adress din SSA danjuma..
Gida ne mai kyau mai tsari,amma daga bakin kofar gate aka dakatar da su.
Mai gadi yace kuka ce wajen oga kuka zo...ummah tace eh..shiya bani wannnan ta yi masa nuni da confidential
Card...yace miye sunan ku...
Duka suka fada sahura da fadima
Baice komai ba ya juya ta shiga dan dakin su ya buga masa waya...
Suka yii magana
Yace abada ummah wayar..
Ta na cewa hello,
Ya dago muryan ta amma mamakin ya hana sa boye dan takaitaccen dariyar da ke damun sa arai...
Yace kin zo da mutaner ki su kamani ko?..
Ta gyada kai kamar wacce take gaban sa tace kawai nazo wajen ka ne....
Yace fadimatul fauziyyat. I like that da wuri kika shiga hankalin ki..i said it Ure a smart girl dama na sani...
Ita dai tana shiru
Yace'..Yanzu kin san me?
Ki jira ni anan inda kuke zan bada mota yanzu akai ku quest house dina ku jira ni ina zuwa tace toh..ta mika waye ma mai gadi..
Nan ta sanar da sahura yadda sukayi ko minti 5 basu kara ba aka zo aka fito da mota kirar jeep aka dauke su zuwa guest house din ssa danjuma..
*WATTPAD VOTE AND FOLLOW @SURAYYAHMS*
*OFFICIALCATTY🐈*
[2/23, 23:24] +234 802 646 5734: *🅱BRILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*
_YA HAYYU YA QAYYUM_
_PAGE8_
Bayan isar su ummah da minti 20 sai ga shi ya shigo da yan mata biyu wanda akallah bazasu fi shekaru 22 zuwa 23 ba...
Kowacce ta rike sa sai wasan banzan su suke, anan ummah ta dauke kai tana Allah ya sawwake ta ga yarta saratu a wannan irin rayuwar,tunanin haka ya sa bata wani dago ta kalle su ba har ya sallame su ya zo ya zauna suka gaisa da ummah da anty sahura..
Tunanin sa ko anty sahurah yar uwan ummah ne amma haka fir suka ki gaya masa asalin relationshp din su.
Chan ya sa aka kawo musu abinci da sauran su,suna ci yana tanbayar ummah abun da ke tafe da ita,
Ba bata lokaci tace "ranar kace idan ina bukatar taimako zaka taimaka min,
Dama aiki Muke nema ta wajen ka.tayi nuni ita da anty sahura..
"yayi shiru domin kuwa dama Ya sha mamakin zuwan tan sosai amma bai kai mamakin da ya sha ba yanzu data furta aikin take nema kuma tawajen sa.. .
kenan fadima zata iya kwana da namiji? Ko dai wani abu ne ya same ta?..yana rayawa aransa yana kallon ta...
Cahn yayi murmushi yace fadima kenan,ai ni dama na baki a farko sabida nasan baki gane ni waye ba ko?
a hankali ta gyada ka
Yace, aiki kam bazaki rasa shi ba ko dan abun da ya faru tsakani na dake zan duba na gani
Sai dai akwai sharadi,ta dago ta dube sa yace "kin tabbata kin shirya ma aikin da kika kawo kanki?
Ummah tayi shiru, wani bugun zuciya ne take famar danne shi amma sai tayi yake,tace na shirya Zanyi...
Sai dai fa kasan damuwa ta baifi na sami abun da zan tallafa rayuwata ba ne,so acire maganan jin dadin rayuwa da rudin duniya aiki kawai zanyi...
yadda tayi maganan yasan kunci da takaici ya sata furtawa Sai yayi karamar murmushi yace toh ai shikenan,
Ki rike alkwarin aikin ki nima zan rike miki naki alkwarin deal?..
Ta dan gyada kai ta dube sahura..
Nan ya cire kudi kimanin 5ok da kati mai dauke da adress ya ajiye kan table yace ga wannan ku saka kaya ku zo nan anjima da misalin karfe 9.
ummah ta dauka ta bada sahura ta duba,strip club ne amma na manyan mutane...
sahura tace mungode sir,yayi murmushi yace idan dokan aiki tafara ba gudu ba ja da baya...
ni ne shugaban ku.
ummah ta mike da cewa mun maka alkwari yace to sai na ganku...nan suka fice suka koma gida..
zuciyar ummah cike yake da damuwa amma haka take bunnewa suka siyo kayan da zasu sa da dan abinci da sauran abunda zasu bukata na kansu da sabon sana'ar su
ummah cemin tayi ta same aiki amma zata fara gwadawa domin aikin dare ne, kuma yana da kyau sosai za a bata kudi dayawa.
ganin ita da anty sahura ne zasu tafi yasa na kwantar da hankali na ban yi mata musu ba..
Misalin karfe 9 suka isa gida ne madaidaici daga bakin kofar duka bada kati aka barsu suka shiga motici ne manyan manya wanda akalla sunkere masu tsayi kuma basu da yawa sosai.
Dim Blue and red light ne gaba daya daga compound din har ciki inda ba agane fuskan mutum da kyau..
haka suka shige suka isa gaban ssa danjuma,
sahura ce ta san wasan su su a cewar ta manyan manyan mutane ne anan suna hutuwa ,wasu na shaye shaye wasu hira kawai suke yi yan mata suna rawa hapf naked agaban su suna nishadi...wasu kuma asalin karuwan su suke tare da su..
sai dai da shike is highly confidential tamkar club suka maida shi kamar kungiya haka suke gudanar da harkokin su,
Anan aka kasa su ummah a kasuwa,
Inda aka zabe ummah a matsayin wacce zata nayin club special strip dance a kowanne karshen dare arabian title sabida kyaun jikin ta da surar fuskan ta.
and then ta dan manyan ta sun san wannan bazai mata wahala ba tunda zata sa kaya wadatacce.
Bakamar yan mata ba,
Ita kuma anty sahura sai aka yi rashin sa'a ,wani ne yace zai dauke ta as personal mistress dinsa gashi shi bai cika zuwa nan ba so dole tana binsa duk inda yake..
a haka aka basu tsarin aiki, duk damaa ummah taji dadin bazata kwana da kowa ba amma it dosnt make any differnce to her,
haka suka rarrashe zuciyan su aka musu 3days training ana basu rabin kudin aikin su,
har suka saba sosai,
A kullum Ita da anty sahura Zasu fito daga gida tun 8pm,sai kowa tayi hanyar ta
Wani bin ummah kadai take dawowa gida don duk rintsi itakam agida take kwana..
Wani abun mamaki shine
A duk aikin da tayi a duniya da fadi tashin,da wahala, babu inda farin jinin ta da sa'ar ta yake haskawa kamar wannan rawar larabawar datake yi agaban maza
Sati biyu tayi amma ta fara dawowa evrybodys favourite.
Doguwar riga ake bata baki kirin wanda ya dan kame round and sexy bodyn ta, da shike ma gaban kayan akwai dan tsagu kadan ta kafar ta yana bada balance wajen rawar ta da rausayawar ta
Kuma ana daura musu alragaya wanda ke rufe kansu da gwalagwalai agaban kamar mayafi irin na masu rawar karuwan larabawan da chan zamanin manzanni..
Sosai ta kulle zuciyan ta ta nitsu waje daya tana abunda ya kawo ta,
Gashi ba hayaniya babu wanda ya taba ci mata mutunci sai ma yabo da tarairaya datake samu daga clients,wasu ma suna daga zaune har manni suke mata bayan makudan kudin da take karba bayan kowani dare..
Bayan tayi complete 1months tana zuwa akai kai kullum.
Har Aka dawo da ita a sati sau uku take rawa,
Shikan sa ssa danjuma sai da ya yaba da hasken tauroron ta,ta jawo masa arziki da mutanen arziki bana kadan ba..
Sai ya kasance a kowani rana cikin kwana uku akalla zata tafi da 250 to 300k..
sabanin 30 40 50k da dachan take karba...
Ummah Ta wanku ta dada karo wayo da sanin me duniya ke ciki sai dai har yau bata mance da kuncin dake zuciyar ta ba.
Wata biyu da fara wannan aikin suka tara kudi na ban mamaki da shike ma idan ba abinci da sutura ba ba sa sayan komai na jin dadin rayuwa ..
Anty sahura ta koma zama da saurayin ta,
Ummah sai ta kama mana haya 3 bedroom flat mai dauke da komai aciki,ta siya min kayan sawa sosai da dan karamar wayan android mai kyau..
Daki na daban nata daban sabida yanzun bata son nasan wasu abubuwan da take yi,
ni dai nayi mamaki nayi godiya har na rasa me zance ma Allah da naga lokaci guda rayuwar mu ya sauya..
sai dai har ila yau idan nace ma ummah nima ta nema min aikin ina taya ta, sai tace min ah a, ai yanzu ta sami wajen mai kyau ana biyan ta sosai so babu amfanin nima nayi wani aikin..
A cewar ta ma tana tara kudi ne zata saka ni a makaranta mai shegen kyau...sosai nake cikin Nishadi da ta fadi hakan ..kullum sai na mata adduar sa'a da fatan alkhairi
ita kuma kullum sai ta sa na mata alkwarin bazan fita waje koda nan da nan ba,bare na kula wani na miji
Hakan na dauka kullum ina gida ina kallo ko karatun littafin hausa dana turanci a online ..
Lokaci na dan tafiya,abubuwan suna dada kamawa yadda yakamata ma ummah,sai ta soma daura buri mai tsauri akaina,ta tara kudi amma tana so ta tara wanda zai kaini babban makarantan sai wane da wane a lissafin ta idan tayi wasa da damar ta wata rana baza ta kai labari ba.
anan club kuwa ssa ya soma daura nashi dogon buriin akanta, daf tana cikin nema min makarantar daya dace ta sani ya zo mata da maganan ko ta sauya saka kayar rawa zuwa mini gown ko ya sauya ta da wata clients..
hakan ya jawo sa'insa sosai tsakanin su, har ummah tayi fushi ta dena zuwa aikin na kwana biyun.
Ita tana nan ta damu gashi tana so tafara aikin sani a makarnta bata so kudi ya yanke mata a hanya..
shima acahn ya damu
Clients sun taslkura sai dai a nemo musu ita,
Dan dolen sa yayi hakuri ya kira ta aamma da sharadin dole zata yi tunanin nan da kwana hudu idan ba haka ba sai dai ta shiga layin bin maza kamar anty sahura..
Sam hankalin ta bai kwanta ba, amma haka take cigaba da rawan ta..
Batare da ta yanke hukuncin ko zatayi yadda yake so ko bazata yi ba
A ranar da kwana hudun ya cika ta zo adaddafe cike da shakkun makoman ta sai ta ta riske baya nan abun ya bata mamaki sosai,
Domin Babu abunda yake hana shi zuwa nan sai ciwo ko mutuwa.
Tayi tambaya aka ce mata bai fito ba yau
sai tayi aikin ta normal zata karbe kudin ta aka ce sai taje ta same shi,
Ba laifi ta shiga motar haya ta je inda akace mata yana nan,
A wani palou aka mata jagora tana jira...
chan wajen minti 30 sai ga surutun su daga ciki shida wasu mutane su biyu..
ummah ta mike tsaye tana binsu da kallo kamar yadda suma suka bita da shi,a ladabce ta gaishe su suka amsa..
Ssa danjuma yace kiyi hakuri ga aikan ki ya zaro envelop dauke da kudin aikin ta ya bata,
Tunda ta karba tayi godiya bata sake kallon kowa ba anan ta juya tafice.
Tasan dole wayannan mutanen akwai su da muhimmanci wajen ssa shiyasa