Showing 1 words to 3000 words out of 194085 words

Chapter 1 - KUDI KUNBAR SUSA COMPLETE BOOK By Surayyams.txt

01 Sep 2025

1103

 SURAYYAHMS: *KUDI...*
_Kumbar susa!_



_DANDANO!_


_NA SURAYYAHMS_


_Page 1..._


Kasancewa yau rana ce ta farin ciki Daddadan sautin algaita,kakaki,ganga da sauran nau'o in traditonal drums and trumpet su suka cike babban filin.

Da yamma ne da misalin bayan la'asariya,Kusan kowani mahaluki yau ya fito kwansa da kwartan sa duk ana tsaye ana kallon hawan dabar,durbar al'ada ce wanda duk wani jinin sarauta ke cike ta ayayin kasancewar duk wata muhimmin hidima musamman hidiman daya shafi na nadin saraura, aure ko bukukuwan sallah.

Cikin wata kasaitacciyar royal canopy fari kar na hangota ta hakimce cikin burgewa da nitsuwa akan kujera golden colour mai sheki,jikin ta a kawace yake da white french lace wanda aka sakaya shi da transparent golden alkyabba issashe har yana bin kafarta

bold make up din ta ya dada fallasa matukar kyaun datayi،kawayen ta ne a gefe sanye da shudiyar dogayen riguna kowacce dauke da bridal maids palates an rubuta nicknames din su da kyau gwanin ban sha'awa.

A Dayan canopyn kuma mai girma sarkin sokoto ne da hakimai magada arziki da sauran representative din shugaban kasa,some ministers,senators and many other distinguished visitors.

Daga cinkoson mutanen dake tunkarowa a sannu a hankali suka fara darewa suna bada hanya inda a kallo na farko naga wasu yan maza biyu sun bayyana a gaba sanye da green and white garland sun rike babban black and shiny gold royal signboard suna bin sautin kidin suna rausayawa suna nunawa

,"Sr,Ahj Aliyu shettima bulama,
Matawallen sokoto Aka rubuta boldy akan board din..
Wanda Tun kafin na hangosa na jinjina ma kwalisar sa

Sai bashi kara akeyi Da alama shine Angon ranar,dan ko jikin shi ma a kawace take da pure white babban riga,ko inansa a tsare yake da launi daban na expensive golden desgner accessories kama daga kan takalmi agogo kai hatta links dn dake jikin hannun jumfar sa abun nazari ne,kwalliyar sa yayi matukar kyau shima an kuma sakaya shi gaba daya ne da golden and black alkyabba
Akan dokin sa daya sha kwalliyar shiny golden dresses yake tahowa quiet slow
And majestic.

Zagage da yan banga sune a gefe da gefen hannun dama da hagun sa,makada,yan koroso da masu busa algaita da kakaki sune agaba kowannen su sanye yake da irin tasa colourful garlands din.

"Allah yaja zamanin ka matawallen sokoto,dan gaban sultan kuma surukin sarki,Allah ya jikan hussaini da dan fodio..maroka ne ke fadan hakan sau bila'adadin suna kuma maimaitawa da xakin murya sakamakon 1k notes da ake musu yayyafin shi

Isowar dokin sa tsakiyar filin yyi daidai da lokacin da yan bindiga suka shiga sake sautin harbin alburusai domin bada signal din isowar sa,anan har akayi leading dokin sa gaban canopyn da amarya da kawayen ta suke

Beutifully dressed Anties da kawayen amarya su sukayi ma amarya fatima zarah muhammad jagora har gaban dokin mijin ta.

A hankali take takawa dagwas dagwas kuma cikin nitsuwa da haduwa har ta kai ga gaban dokin a lokacin kusan hankalin kowa na kansu

Amarya Fatima tana dan aje kanta kasa cikin jin kunya Wani irin Kirari maroka suke zuba mata ana raha ana bin bayan ta da turare cikin nishadi har ta iso daf gaban sa.

"sautin guda mai shiga rai mata suka sake ayayin da shikuma ya dube ta cikin shauki yace.." Tubarkallah,u look so beautiful fatima.

Gyada kai kawai tayi bata tare da ta dago ba tace thanks
A matukar kunyace

Anan aka bude shafin daukar hotuna kowanni professional photo artist yana deban portrait dinsu ta kowani angle..

Murmushi take zubawa mai taushi tana ji aranta kamar Tun da take bata taba ganin mutane kamar na yau ba,duk da kasancewar ta layin karshe acikin jerin yayan sarkin sokoto
Wanda Allah bai nufa zasu auru da wuri ba amma sosai auren ta yayi albarka.

Fatima zarah yar sultan sarkin skt ce kuma itace mace ta farko ajerin yayan sa mata bayan aysah rukayya,hafsa da ummi da aka aurar.

She is 32,kyakkwa mai ilimi da sanyin hali,quiet unsual da Allah bai bata miji akan lokaci ba amma bata taba daga hankalin ta ba.

Wasa wasa sai jinkirin ya kasance mata alheri wajen samun old time boyfriend din ta tsohon dan siyasa Aliyu shettima wanda dama qaddara ne ya rabasu kuma wani qaddaran ya sake dawowa da su a matsayin ma'aurata.

Daga nan Babu bata lokaci aka cike duk wani gutsiru tsome da rububin biki
Har ma da na al'adun gidan sarauta Karfe 10 na safiyar washe gari akayi rakiyar amarya filin jirgi domin kai ta chan abuja inda gidan mijin nata yake.

Daga isar su abujan Anan ma wani sabon liyafa mai kayatarwa aka bude shafin sa,wanda dangin ango musamman ma mahaifiyar sa hjiya binta bulama ta sa aka kawata shi ya hadu har ya zamto abun kwatance a kasa.

A yadda ake zumudi ana tattalin amarya fatima in kai bako ne bazakayi saurin cewa akan kishiya za'a aje ta.ko da shike da alamar kishiyar nata bata san anayi ba dan ko idanun ta ba a gani a hidimar ba bare kafafuwan ta.

Sosai aka sha hidima,da dare kuma aka yi cuncurudon convoy na motoci zallan kirar benz da mesarati har gaban wata kasaitacciyar mansion a unguwar maitama.

As a mansion as it is,ko ina haske yake yi kamar ba dare ba daura da bakin gate din xaka ga inda aka manna _Bulama JNR_ residence adan karamin gold plate mai shining,shuke shuke da flowers su suka kawata outdoor view na environment din sosai

Daga cikin gidan kuma gini ne mai na dauke da 15 correct bedrooms with bathrums of full sized jacuzzis,sai 7 big and well furnished palours 55 feet long royal dining table da garnished and lush interior decors komi anyi arranging dinsu tsaf.

A wani bangaren gidan akwai sites na fully loaded gym,a classy snooker hall sai manya manyan swimming pools of different designs and shape kowanne a side dinsa, garage ne ta waje da yaji cars tsadaddu na zamani kala kala wasu har an ajiye su waje under shades a haraban gidan.

Daidaikun matan ne suka fito tare da amarya cike da nuna tattali,a lokacin magajiyar matar sarkin skt da ayarin ta ne suka sauya sautin iskan gidan da zazzakar sautin gudan su

Amarya har ila yau sanye take da cotton maroon lace an rufe mata fuska da tsaddaden mayafi mai sheki assorted with expensive swrasvoki stones hannayen ta sunji asalin jan kumshi duk inda suka wulga da ita tana fida wani irin azaban qamshin traditional acent ahaka har sukayi cikin gidan da ita.

Duka duka Lokaci kalilan suka deba suna xaga wajen dukan su yan kawo amarya kowa yana raha ana sam barka,daga nan Har sashin amarya aka bi aka mata ban kwana cike da kewa kowa ya wuce mota domin a maida sa masaukin sa.

Itace a lullube luf zaune a tsakiyar fankacecen king sized italian canopy bed.

"Anty fatima toh zamu tafi...Allah ya bada zaman lpya.

Kanwar ta rukayya dake kusan tafi kowa damuwa da ita ta fadi haka ayayin da magajiya take kokarin rabasu da kyar dan kuwa dukan su hawaye ne akan a fuskan su.

Tun isowar su da safen rukayya ta kasa boye damuwar ta wajen nuna zakewa da tambayar shin ina kishiyar anty fatima take?dake kusan dukan su basu taba ganin ta a fili ba,ita kam ko da sau daya ne tana so ta gan ta da idanun ta

A Jiya Tunda suka zo abuja ba ace musu komi game da ita ba kuma ko yau din ma ance musu tana nan acikin gidan.

Abun ya dame kusan kowa amma dayake anyi bikin babu hayaniya sai ake yawan danne tsegumi

Magajiya dake ita ta manyan ta sosai in taga wani magana ya fara tashi sai tja rukyn gefe cikin ja mata kunne tana cewa"Anyi auren nan lpy rukayya ki iye bakin ki mana,be zama mana lallai sai mun ganta ba,kusan kowa yasan labarin hjya RAMAT,Bakar mutuwa ce wacce rashin ganin ta bashi zai hana fargaban gamo da ita ba.

Ita kuwa rukayya sam bata son jin haka dan har yau da fargaban auren dadan nata take kwana take tashi

Magajiya kuwa takan hakimce ne da yi mata bayani
Sai tace."Yo me aciki dan anyi biki har munzo bata fito ba?rashin fitowar ta ai Alheri ne agaremu

karki manta sarauniya fatimar mu yau ta kada tarihi mai girma a cikin gidan nan,dan kuwa itace mace na farko acikin jerin mata takwas da Alhj aliyu ya aura sumul garau Batare da anyi wani hayaniya da matar san ba Ajiyar zuciya kawai Rukayya ta sake Cike da daurewar kai da yake dada fallasa halin fargaban data ke ciki...

Tace"Magajiya ni fa bawai na matsa bane sai mun ganta,wani bin ne sai ina ganin kamar dan bata sani akan lokaci ba ne yasa tayi shiru,ai naji ance bikin anty faty sai ana daf taji labari kO?...

Mata takwas bata barsu ba sai ace akan anty fati ne xatayi shiru?

Ni dai gaskiya ina so naga reaction din ta,shiru shiru haka nan sam babu dadi,wayanda ma tayi borin akansu basu zauna ba wa yasan metake shiryawa akan anty fatimar,toh Allah kadai yasan me zatayi ma anty fatima in muka tafi..mudai gamu ga Allah,da takurarren tagumi ta karashe.

Magajiya tace "Haba Rukayya..sai ta dafo kafadun ta
Cikin son ta kara mata gwarin gwiwa

Tace tabbas mun dade muna cikin fargaban haka amma Allah ba yadda baya sauya al'marin sa,nikaina nasan a yadda hjya ramat ta shahara wannan shirun nata ba mahanin komi bane...kuma in da tayi niyyar nuna halin ta akan fatima da sai yafi na kowa ma dan anboye mata auran.

"Yawwa magajiya kin fahimce ni ashe
......rukayya ta furta hakan tana sauke ajiyan zuciya,tace mu dai muna rokon Allah ya dada nuna ma na haske akan namu.
A Duk dama ance kishiyon ta basa ko kwana daya agidan nan anma inada yaqinin Insha Allah nan gidan anty fatima ne.

Magajiya tace
"Allah yasa haka.
Allah ya karbi adduar ki rukayya,ya kuma daura mu akan mata mugaye.

Tace ameen magajiya.

Hirar da suke tayi kenan har suka isa gida daga nan aka wuce da su airpot cikin daren suka kama hanyar masarauta..

***
Bangaren angon shima cike da farin ciki da annashuwa ya fito daga sashen mahaifiyar sa Wanda Tsananin farin ciki da annashuwa ke lullube da yanayin ta.

a kusan kowani lokaci makamancin haka hjy binta bulama takan gode ma Allah sosai Albarka take saka ma auren tamkar wacce Bata damu da fargaban dake cinta arai bayan istihara da fadin malamai dake cewa danta Aliyu Shettima bazai zauna da wata ya mace nan kusa ba

itadai tunda anyi auren lpya aganin ta Allah yafi karfin kowanni al'amari

Kara auren alhj aliyu wani Babban Burin ta ne wanda bata wasa da shi,Kai ba itaba bama harma da yan uwa da dukkan dangin sa kowa a matse yake yaga yuwuwar Sabon aure a rayuwar dansu koda ranar mutuwar su ne Kullum adduar su kenan ko da dansu aliyun zaiji sakat a rayuwan sa.

A Tsawon shekarun nan babu irin launin tijara da kalubale da basu fuskan ta ba wajen uwargidan sa hjy ramlat ba,sedai hakan bai sa sun rusuna ba Daga alhj aliyu ya sami mata za ayi maza maza a rufa masa baya akarbe ta hannu bibbiyu adaura auren.

But Sabida iftilain da ya afka masa akan matayen musanman akan mace daya aura na karshe data dawo tsuntsuwa ranar tarewar ta,akan haka Yau kusan shekara shida kenan rabon sa da sake tunanin yin wani aure,Shikan sa alhaji yana maitan son yaga yy auren amma gaba daya sai baya gane kansa bare yawancin tunanin sa.

Ayau,Addua hjy binta take dada masa Tana kuma dada nuna masa jin dadin ta abisa karamci,yarda da girma da sarki sultan muhammad yayi musu.

Duba da yadda duniya take yawo da labarin unsuccesful marriages dnsa Mai martaba Sarki sultan muhammad bai damu ba,domn kuwa shika dai ya yarda ya basu amanar yarsa fatima

Shiyasa Alhj Aliyun Shima ya fahimce mahaifiyar san sosai datake cewa ya rike fatima amana,sosai kuma ya aje girman karamcin sarki har cikin ransa .

Dan Nasiha hjy binta tayi masa sannan ta sa masa albarka ta sallame shi

Bayan nan Shi kadai ya taho gida,dan an manyata so there is less need for all fomalities shiyasa tun da yamma aka sa masu kulawa da tsare tsaren auren suka sallame kawayen amarya da masu komawa agoben da goma na arziki.

Daga shigan sa gidan nasa
"...shashin hjy ramat ya fara kusa kai dan tunda akace mata zai yi aure ranar juma'a magana mai dadi na fatan baki basuyi ba har yanxu..

Dama 3 days to the weding aka gaya mata batun aurenf sai dai ta basu mamaki matuka da bata zagi kowa kuma ba ta hana yuwar komi ba

Yawanci Sai dai ta girgixa kan ta tayi masa tsaki mai sauti

"Xakayi nadaman wulakan tani Bulama,ba Wani xakayi wa kishiya har kana boyewa ba?To Lallai Ka debo ruwan dafa kanka.

Kalaman ramat kenan..kuma kullum azafafe cikin kunan rai take jefa masa

Shidai Baya ce mata uffan dan a koyaushe ya zauna Daga ya tuno ta sai dai yayi murmushi yana mai kada kansa cikin nazari

Aganin sa ko a cikin sahun mata masu nuna tsana ma kishiya a duniya bai taba ganin nau'in balai irin na first wife dinsa ramat ba

Yana saka kafar sa a site dinta kuwa yaji kanshi yayi wani mummunan sarawa,wani dishi dishi yake gani inda ya tsinkayo muryan
Babbar mai aikin ta wato safiya,a ladabce ta rusuna ta gaishe shi tare saf bashi labarin cewa hajiya ramat din ta bada doka akan cewa duk wani mai himman ganin ta ya bari sai da safe bata son ganin kowa.

"Wannan raini ya dame shi matuka,da arzikin shi da mutuncin shi mai aiki ce zata tsare sa
Shida gidan shi tana saka masa dokan inda zai shiga?

Har Ya budi baki zaiyi magana wani irin sarawa kanshi ya dadayi sanda ya dafe goshin sa,daga nan bai gane komi shikansa baisan ya akayi ya sallame ta ya juya yabar wajen ba.

Yana tafiya kuwa safiya ta isar da sakon ta ciki...Har tana batar kalma ta durkusa gaban su...

"Hajiya alhajin ya koma....

Wani wal wal din walkiyar ababen hannu dana wuya ne yake haskawa manyan mata biyu ne zaune cikin shiga ta alfarma

Hjyn ramlan ne a zaune akan kujera na farko ita da babban aminiyar ta hajiya hamida agefe duk sun yi kyam suna faman shan qamshi

tsaban iya kaskntarwa ko kallo bata iya maida ma safiya ba bare ta samu amsar taf

Sai Cahn dataga dama sai ta juyo,Maganan ma takanyi shi ne kasan fatar bakin taf kamar bazatayi ba

" tace ki tashi ki bishi ki tabbata ya shige sashin amaryan na sa bayan yayi mintina goma sai ki dawo ki gayamin

Da barin jiki safiya tace toh cikin ladabi ta mike ta fice after 15 minutes ta dawo tace musu eh yana ciki,na kasa kunne da alaman yanayi ma amaryan san nasiha ne.

Gyada kai kawai ramat tayi suka sallame ta

Tana barin wajen aminiyar ta hajiya hamida ta mike hurjan jan tare da sake mayafin ta cikin azama..tace tashi,ramat muje ki shirya kema

Babu bata lokaci Cikin dakin su suka nufa ba Inda hjyf hamida ta fito da wata bakar jaka daga wardrobe wanda bata tsaya bude shi complet bama ta zaro wasu jajayen yaduna matsu tsantsi ta shiga warware su

agaban ta hjy ramlat ta tube tsindir ta nade ta da kayan tsaf izuwa dunduniyar kafafun ta.

"Durkusa acan,ta mata nuni da tsakiyar fankaccen gadon ta dayaji puref white cotton yard daga gani ba tambaya kasan shima na tsafi ne.

A durkufe hjy ramla tasaka gwiwon ta a tsakiyar gadon inda aminiyar ta hjya hamida ta ciro karamin kwarya ta rufe idanun ta tsam tana tofe tofen harufan sihiri aciki

Bayan minti 2 ta bude idanuwan ta Kwaryan ta aje a tsakar kan hajy ramla,tabi ta rage wutar dakin zuwa dim inda fuskokin su kawai ake iya ganewa

Wasu ayoyin sihiri ta shiga karantowa da daddan sauti

"yah habusa,ya marhuk,alkada adabara majusa..

A hankali take maimaitawa Muryan ta har na rarrabewa,alamu sun nuna kusan dukkan imanin ta tasa take rerawaf fuskn ta dauke da yanayi mai nuna matukar yardan da tayi wa abunda takeyin

Anan Bata tsaya ba har sanda ta kai aya sannan hjya ramla ta shiga maimaita wa itama har sanda kwaryan dake kanta
Dakan shi ya bule dakin da wani irin spritual smoke mai raxanar wa..

Ganin komi ya kammala sai ta dauko karamin karrrawa tana bugawa gyelen gyelen a gefen kunnen ta na hagu da dama

Tace"...habbusa ga ramlat dinka tazo da bukatar ta,sai Ta dawo ta karkada shi a gefen hagu da karfi tace
.
Ya habbusa...ya ubangiji na,ina rokn ka da ka tafiyar da ita kamar ruwa mai tsananin karfi da bai da matsaya sai madakatan karshen rayuwar sa.Ta tafi,ta kurmance kar ta tsaya har abadan abada.

Cikin wani irin sauti mai kuna ta kuma cewa Habbusssa
.. .karrawan ta buga one more time sannan duka suka rufe ido suna mai rike hannun juna

Ko secnd basuyi ba Wani iska mai tsananin zafi ya shiga ratsa su, bat kwaryan ya bace a dakin jim kadan komi ya washe kamar ba ayi komi anan ba.

Cikin sauri hjy ramla ta sauko suka nannade bedsheet din ta mika ma kawarta hjy hamiida

"Nidai baxan fito gobe ba sai ki kaimasa ladan aikin sa ni zan tsaya na fuskan ce kowacce shegiya acikin gidan nan

Hjy hamida tace toh kema ai sai kije ki huta acan dayan dakin amma ba anan ba...Ni ma na tafi,kedai kisan yadda xakiyi nagaya maki bana son asaka mana ido wannan karon kinsan yarinyar yar gidan sarauta ce

Tsaki kawai taja tace hamida bana shayin su..."Ohon musu tunda ni suka so su taba,Allah sa tana fita a karo na farko mota ya buge ta yyi gutsil da namar ta akan kwalta..

Hjya hamida bata ce uffan ba har taja mayafin ta ta kama hanyar bude kofa,tsayuwar scnds tayi.

Tace"To nidai na tafi sai kin jini .

Tun kan ramat ta amsa ta rufe kofar ta fice mai gaba daya agidan....


*KUDI..kumbar susa is starting tomorow insha Allahu*

_YADDA AKE BIYA,HOW TO SUBSCRIBE,plus payment details_

_FARASHIN SA👇🏿_

#300 naira ne
#450 naira for VIPs


*1- Biya Ta bank acct*

_Use👇🏿_

Account name:
Surayyah muhammad suleh
Acct number 0152983148
Bank: GTB

*Sai ki tura screen shot shedan ki wa 👉🏿08036651119*


*2.MTN RECHARGE CARD OR VTU TRANSFER👇🏿*
*08060712446*

*Sai ki tura screen shot shedan ki wa 👉🏿08036651119*

*3:yan kasashen da ba nigeria ba masu biya ta PAYPAL,OR oda WORLD REMITS*
Use👇🏿

Account name:
Surayyah muhammad suleh
Acct number 0152983148
Bank: GTB
Phone

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login