Showing 48001 words to 51000 words out of 194085 words
Chapter 17 - KUDI KUNBAR SUSA COMPLETE BOOK By Surayyams.txt
yake mugun debar ta ayayin da kwakwalta yake jiyo mata shi kamar qamshin jikin aliyu..
Can babban falon dake site dinsa ta nufa ta turo door a hankli ta kutso kanta ciki bakin ta dauke da yar sallama"salam alaikum..duka su anty maryam da anty zakiya suka juyo atare suna me zuba mata idanu
..wani shiru ne ya ratsa wajen jud ta tsaya cak tana dan rarrabe idanu tana dan satan kallon su,
Kyawawan mata ne ajin farko dukan su sanye da tsadadun atampa sunsha manyan kyalalluka da hadaddun jakuna na mata yn yara ne agaban su wayanda bazasu wuce shekaru 10 zuwa12 ba..a ladabce jud ta karaso ta rusuna a gaban su tace sannun ku da zuwa ina wuni?anty zakiya ce cikin dauriya ta amsa gaba daya qamshin da ta shigo musu da shi ya gama tafia da su,anty maryam kam shiru tayi tanata kallon irin tsaban kyaun da Allah yy ma jud kaf ta tsaye ta kare mata kallon kurel kamar wacce taga fatalwa,.
Haka nan jud ta musu gaisuwar mutuntaka sudai har yanzu Basu ganeta ba dan haka kowa ya zuba mata idanu yana faman magana shikadai a zuciar sa
waje jud ta nema agefe ta zauna inda ta dada basu aikin kare mata kallo,da har anty zakiya zata tambayeta ita wacece charaf sega sallamar safiya da tray din botle water da viscuits da nau'oin junks ta shigo.Dada gaishe su tayi sannan ta rusuna ta aje komai agaban su,"Ashna ce ta soma kaiwa hannu ta dudduba batace komai ba
..mama ni ba zanci biscuit ba,..Ahmad yaron anty zakiyan dake shine karami ya fada yana make kafada yana mita a dole shi asalin abinci yake so,"..anty zakiya bata kulasa ba duk dama daga long jouney suka taso tasan babu lefin sa in yace hakan dan yau wuni sukayi ahanya kuma duk iriyar abunda suke ci kenan...anty maryam tace safiya wai babu abinci ne agidan nan,safiya tace hjy yanzu zan je na dora ayi hkri daman kimtse kintsen kayan kune ya dan sha min kai
..jud tace anty bari kawai zan dafo musu tunda kina aiki..safiya ta danyi murmushi,jud ta kalle Ahmad da cute smiles tace hi friend me zakaci ne?...da murnan sa yace rice,Ashna kam se kallon jud take kamar lost sheep batace uffan ba Hakama su anty zakiya suke binta da kallo..jud tana ficewa suka saka safiya agaba da son jin wacece wannan?
Nan tagaya musu yar abokin alhaj aliyu ne,amma ayanzu tana zamane da su...
Ko Daga yadda safiya ta musu bayanin jud din sun gamsu da halin ta sosai,kafin wani 40 mints me kyau jud ta tsara fried rice me cike da kayan su karas green beans green prrpr da neatly sliced cow liver ta zuba a warmers,Hade da samosas din da safiya ta karasa mata duk ta hadisu akan faranti tazo ta jera musu akan dinning,ta dawo falon tace musu ta gama.."yaran ne suka fara gaba, aka bar su anty suna ta shan mamakin jud dan sai abun ya musu kamar a mafarki yau gasu nan dai sunzo bulama mansion an karbe su hannu biyu agidan aliyu,koda shike safiya ta gaya musu cewa ramat bata nan..dan haka ne ma suka sake jiki suna aiwatar da ryuwan su hankli kwance,tsaf jud tayi serving dinsu tagama da sauri ta juya zata bar wajen anty xakiyya tace yan mata bismillah mana ina zakije?..,jud tace zanje daki ne anty kuci abincin..Anty maryam tace a'a zauna abunki seta wayance tace baki ko gaya mana sunan ki ba,"whats ur name. ."jud tayi murmushi tace sunana jud Abbakar..atare sukace masha Allah nice name,have a seat..Sit down mana..babu musu taja chair ta zauna itama tayi serving kanta abincin amma kadan kadan take ci sabida kunyar idanun su duba da cewa dukan su manyan mata ne..
Daga yadda kowa kecin abincin za kasan girkin tayi dadi Ahmad har labarin santi yake ma jud duk dama yau ya soma ganin ta arayuwar sa Ashna still tana shiru da alamn tana jin shakkar maganan ne..Hira kadan su anty suke jefowa tsakanin su suna dan yima jud tambyoyi inda itama ta fahimce cewa ashe da sanin aliyun ma suka zo،..
Bayan sun kammala safiya ce da sauran ma'aikatan suka tattara komi jud ta musu sallama ta nufi dakin ta,Washe gari ma da zata wuce schl sanda ta biya ta gaishe su anan taji cewa zasuyi sati guda sannan tun jiyan suke neman aliyu awaya ba asame shi ba..
Su basu wani damu ba dan sunsan yanayin tsabgogin sa amma haka kawai jud abun ya dame ta"she is alwys missing him bata ma san meyas ba amma Allah Allah takeyi aliu ya dawo gida,haka rayuwa ya kasance agidan komai ana musu a mutunce cikin girmawa..ashna da Ahmad kuwa ata wajen ciye ciyen kayan kwamulashe da girke girke suka fara sabawa sosai da jud,Wani bin har kitchen zakagan su tare suna debe ma juna kewa,su anty xakiya kuwa sunsha yin hirar jud abayan idanun ta musamman yanayin qamshin ta da tsaftar ta uwa uba yadda take mutunta su a duk dama bata taba sanin su ba..abu daya ne kawai suka lura bata fiye yi ba kuna shine sakewa ayi hira da ita sosai..
Fannin jud kuwa ita sam bata dau abun datakeyi na kyautata musu sabo ba dama ita hakan aka a tarbiyatan da ita,shiyasa tun da can arayuwanta bata taba raina wani ba se akan ramat data takura mata
Wani bin su anty su kan so suja ta da hirarraki koda na film ne amma jud is always absent minded acikin fantasy world din ta da ta saba na aliyu so ita babu abunda ta sani sosai akan irin wayannan rayuwan..
Duk da haka iya dede kima tana debe musu kewa dan tun Kafin sati ya zago su anty suka sake mata fuska sosai,yauma taje schl ne da alkwarin inta dawo zatayi musu pounded yam da original oha soap...so tun kan ta dawo kowa yake ta zumudin cin girkin tan ...
Fannin abbakr komai yakan tafi masa dede musamman da hamida take dan satan hanya tana dawowa nigeria wajen sa kwana biyu in sun huta se ta sake komawa saudi ..
Ramat kamm ko ajiikin ta dan dama shege yace karta taba yarda ta dawo dawuri dan aljanun sunce inta dawo bata cimma burin ta a saudia ba to tabbas baxata sake komawa lpya ba,..
In hamidan zata zo nigeria ne ramat takan bada aikan ta ma shege so kusan komai a tsare Yake awajen ta for now.
Hamida kuwa bata wani jin dadin rayuwar duba da yadda mugun son kai rin na ramat ya addabe su ga hamshakiya bilkisu ta sako ta agaba.
Koda ta nuna musu cewa mijin ta nada kima arayuwarta bakaramin gulman ta sukeyi ba
Ita de ramat tana mugun son hamidan ta,har yau bata da i kamarta a duniya..har gani take baxata iya tsayawa kan kafarta ba in hamida ta juya mata baya wani abun in na kudi ne tana so tayi ham ham ita kadai amma daga zarar ta tuno hamida seta dan sassauta,hakan na mugun kona ma bilkisu rai tsana marar fasali ta dasa aranta game da hamida..
Kasancewar yau friday ne kimanin kwana 12 kenan da tafiyar aliu kaduna ,tun 11am yau aka tashi su jud a lectures dan haka suka je kasuwa itada da kawarta mariya suka siyo kayan hadin oha soup da sauran abubuwan da babu su agida.
Ba acika barin mariya tana fita ba amma haka ranar jud ta matsa akan tazo mata,so a Tare suka shigo mansion din itada da mariyar safiyace ta sanar mata cewa su anty zakiya dik sunje shoping dake baifi kwana biu ya rage musu su koma ba,nan suka ajiye kayayyakin girkin da suka siyo a kitchen suka nufi daki inda suka bude shafukan hira,..
To Dama mariya takan dan duba site din datayi mata register awaya dan taga how far da kuma yaushe ne karshe da jud ta hau gaba daya,tayi iya dube duben ta kaf sai taga ma kamar jud ta goge abun ne a wayar ta,hakan yasa mariya ta sake baki duk ta dauka ko sauki ne ya samu
Seyau data sha mamaki sosai sakamakon bude system din jud gani tayi cewa jud har yau tana nan ayadda take wajen masturbation but abun ya daure mata kai matuka da ta lura kamar boye mata takeyi kuma..
Batade ce komai ba suka cigaba da hira bayan la'sariya suka ci uban wanka suna wani fidda qamshi na fitina dan yau atare sukayi siracen turare suka tattale ko ina a fuskokin su
dukan su kaya iri daya suka zaba stylish fallazo trosers green nd dark red colour dan dede tsayin su da white long sleev fitted shirt sunyi tucking ta ciki mariya sai tayi rolling da green veil ita kuma jud ta sa deep red dake kwalliyar fuskan ta da red lips da glitter eye shadow tayi..
Dake tayi lining bakin ta da bakin liner se fuskn ta yayi matukar yin kyau a duk sanda ta motsa idanu kyalli kyallin gliters din dake saman idanun ta su suke haskawa.
Straight site din su anty zakiya suka nufa inda suka same su azaxxaune akan gado su Ashna duk sunyi wanka su anty sunata faman shirya wasu kayan da suka siyo a jaka da alaman yanzu suka dan warware anty maryam kam ma ko wankan bata yi ba,da fara'ar su suka tarbe su jud tayi introducing mariya a matsayin kawarta..."anty ta kare masu kallo she was like an fasa mana girkin ne?zuwa ina haka yan mata..jud tayi murmuahi tace ah'a babu inda xamuje..munzo duba ku ne daga nan zamu wuce kitchen,tabe baki ant zakiyy tayi tana murmushi tace da kyau,with all these beautiful dressing ana qamshi za'a shiga kitchen?.. she was like lallai mahaifiyarki ta cancanci yabo..
Jud ta jawo hannun ashna suka wuce gaba Ahmad na gefen mariya yana nuna mata sabon puzzle dinsa suna tadin shirme..
Anty xakiya tace maryam kiyi ki kintsa se muje falon kafin su dawo,wani uban hamma anty maryam ta doka tace toh dan wallah yunwa nakeji..
Anan kitchen su hudun su suka baje kayan girke girken su very neatly mariya tana yayyanka musu kifi da naman kaza in desired shape jud tana faman soya miyarta...jud tana mugun son Ashna dan bakaramin kama da aliyu taso tayi ba duk da yarinyar bata son magana amma haka nan ta sace zuciarta da kwamulashe yanzu adan dole take bin jud kamar jela..
In 15 minutes suka kammala miyan oha wanda yaji kayan hadi ya fito rass kamar kar aci da bakin yunwa tuwon sakwaran be dauke su 10 minutes da kammala hadawa ba dake agidan akwai engine murza sakwaran so sosai tayi laushi tayi danko..
Da taimakon safiya sukayi serving duka abincin a wasu manyan dinner set safiyan tana kimtsawa jud tana fitowa da shi waje tana serving
Itakuma mariya da sauran yara sunje can sama dauko su anty...Sanye da manya manyan leshunna suka fito duk sunyi kyau Wani surutu wajen ya dauka cikin raha "anty maryam take bada su mariya dariya da jokes da nuna zumudin ta wajen azuzuta dadin taste din abincin jud tunma kafin su zazzauna..
Dede sun fito falon a lokacin jud ma ta taho da desert a faranti..safiya ce tayi serving din kowa ta koma kitchen inda kowa ya baje yana gwasar girkin jud
Anty zakiyayya cikin nuna jin dadin ta tayi mata kyautar abun wuya me kyau da dan kunne...ita kuma mariya kudi aka bata dake bata karasa cin abincin ba ta mike tace anzo daukarta zata wuce gida..
Jud tana dawowa daga raka mariya ta samu suna nan akan dinning har iyanzu hirar sukeyi,ganin anty safiya bata fito ba se ta shiga tattare kayan da sukayi dirty a dismisal tray zata wuce da su kitchen,"Ashna tana lashe hannu tana dan murmushi da dan karfi tace anty jud,se jud ta juyo tace yaushe zaki sake mana irin wannan tuwon?zaki mana gobe..?baki bude anty zakiya ta kalle su anty maryam kuwa ta fashe da dariya irin ashe bani kadai bace kwadayayyar cikin kwaiwayar muryan ashna tace yes anty jud yaushe za'a sake mana girkin?..cikin gwalo idanu anty zakiya tace kai kai to baxatayi ba,...duk me son ya lashe hannu yaje kitchen yy girki,jud ai kin gaji ko?...gyara zaman tray din a hannun ta tayi ta dan sunkuyar dakai tana murmushi me sauti..juyowar ta ke da wuya sai kicibis sukaci karo da Aliyu..
Page23
*KUDI..kumbar susa*
_YADDA AKE BIYA,HOW TO SUBSCRIBE,plus payment details_
_FARASHIN SA👇🏿_
#300 naira ne
#450 naira for VIPs
*1- Biya Ta bank acct*
_Use👇🏿_
Account name:
Surayyah muhammad suleh
Acct number 0152983148
Bank: GTB
*Sai ki tura screen shot shedan ki wa 👉🏿08036651119*
*2.MTN RECHARGE CARD OR VTU TRANSFER👇🏿*
*08060712446*
*Sai ki tura screen shot shedan ki wa 👉🏿08036651119*
*3:yan kasashen da ba nigeria ba masu biya ta PAYPAL,OR*
Use👇🏿
Account name:
Surayyah muhammad suleh
Acct number 0152983148
Bank: GTB
Phone Number :07058797141
CITY:bauchi
[7/31, 2:09 PM] SURAYYAHMS: ******tana murda kofar kitchen Safiyance ta gani a tsaye tana bada odern kayan abinci ma mai girkin su dake yanzu duk ma'aikatan gidan sun dawo maxa...
ganin jud a tsakiyar su yasa ta matso kusa da sauri tana me tambayar ta lpya dai ko?jud ta dan makale wuya fuskanta ta adan sake tace..."uhm dama nazo wajen ki ne...Da alaman fargaba safiya tace to bismillah karaso ciki...nan take safiya ta sallami sauran ma'aikatan dake wajen ta sama ma jud arm chair ita kuma se ta dan rusuna a kasa kusa da ita..tace ina sauraranki..wani shiru ne ya dan ratsa sannan ta sauke boyayyen ajiyan zuciya tace dama Alfarma nazo nema wajenki akan dan Allah kina bari ina danyin wasu aiyukan kitchen rashin motsawa na yawan kashe min jiki..seta dan langwame wuya slowly ta furta pls.."cike da mamaki safiya ta dago ta kalle ta tace a'a jud wannan dokar alhaji ne kuma baya son acika saba ma dokokin sa..kiyi hkr kinji?zan miki duk abunda kike so amma banda saka ki aiki..jud tace anty safiya dan Allah ki taimaka min ni..in kina so bazan gaya masa inayin wani abu ba, nidai bana son zaman nan ne..se ayita min kallon kamar bani da lpya bayan ni lpyata lau...
Safiya tayi shiru tana tunanin abun har cikin ranta, tayi mugun yabawa da tunani irin na jud amma kuma har yanzu tana tsoron bada amsa sabida tasan halayen aliu..
In ya sa doka bai cika so ana tsallakewa ba what in wata rana by mistake yaga jud tana goge goge agidan bayan yace kar abarta ta taba komai...safiya ta girgiza tace kiyi hkri kinji..bazan iya ba Alhaj ze yi fada,jud tace to ko inje in gaya masa?da sauri safiya tace a'a tsaya tukun..a ranta tasan in jud taje ta fadi hakan gaban aliu still bazata tsira ba aliyu zai iya tunanin ko basuyo mata abunda take so ne shiyasa tace zatayi dakan ta
Can safiya tace to ya kike so ayi,me zaki na yi?ai kinga kusan komai akwai masu yin su,shara goge goge wanke wanke aika girki..to ke me zakiyi..jud ta dan sauke ajiyan zucia tace "dama wannan satin zan koma schl so inaga zan na girka abincin in na dawo ko in zan tafi..safiya tace to yayi amma fa karki manta alkwarin ki ba ko yaushe zaki na shigowa nan ba kuma karki fa gaya masa....jud tace karki damu na fahimta nagode,da haka suka rabu safiya tana ta mamakin jud aranta,ayaran zamanin yanzun nan waze nemi takurar kansa da aikin gida inba mace me tarbiya ba.."AYanayin kyau da kwalisan jud ta gama daukawa yar kwai ce,yar aci a kwanta dake dama ta lura ba yar son magana bace..
Amma kuma abunda ramat ta fada nata akan yarinyar ya sha bambam da yadda take gani dan har yau bata isa tace ga munin halayyarta ba,beside yau watan ta guda kenan agidan da duk kyauntan nan anma bataji ance maza suna layi a kofar gida ba..ko ta taba shiga dakin ta ta iske ta tana wayace wayace..
Ita de dabiun yarinyar ya mata har cikin ranta aranta sai bata jin kmar zata iya cutar da ita..
Bangaren su aliu kuwa da suka fice tare da abbakar abakin mota suka tsaya suna dinke zantukan su inda aliyu yake dada tabbatar masa dacewa yana da sauran hutu
Ahakan ma da kyar yaci nasaran langwasa ra'ayin abbakar ya hakura ya bar masa biyan kudin makarantar jud da duk wani abun da take bukata.
Abbakar yana da kawaici sosai so aganin sa in yace eh ai dawainiyar zeyi yawa aliyu
Shi kunya yakeji in ya tuna cewa shida matarsa sun bazama neman duniya ne suka daura ma wani nadaban nauyin yarsu..
Shikuwa aliu ko ajikin sa arayuwar sa kwata kwata be damu da wai dan ya kashe ma wani kudin sa ba
..musamman ma abbakar dayake mugun jin dadin hira da shi..haka suka rabu abbakar badan ya so ba ya damka masa komai na karatun jud.
Washe gari ssafe jud ta farka tayi yan kimtse kimtsen ta,kirar farko awayarta na inna ne..a ladabce ta dauka suka fara gaisawa dake yau tun asabuhin fari ta tashi tayi sallah se inna batayi korafin komai ba ta shiga mata tambayoyi akan lpyarta,atafir jud taki cewa komai akai sema nuna ma inna cewa yawan xaman ta babu aikin yi shiyake sata jin kasala amma har ma tayi magana da me aikin gidan..daga jin hakan se hankli inna ya kwanta
bayan nan jud ta fito ta nufi kitchen tadanyi abubuwan da zatayi komai tana yi ne safiya tana kallonta,safiya kuwa tun tana dar dar da lamarin har tazo ta sake jikin ta musamman data lura da yadda jud ta warware tana gazar gaxar kamae ba itaba,anan fargaban harsashen ciwon nata ya gushe aranta itama se ta cigaba da abubuwan dake gaban ta..
To Bayan kwana biu aliyu be nemeta ba bata sani ba ashe yaje babban family house din sune shima yayi kwana biu acan,dan tun kan su rabu da abbakar a ranan hajy binta ta kirashi awaya tace masa gata nan tazo nigeria agurguje kuma tana bukatan ganin sa cikin gaggawa.
Shiyasa Ba shiri yaje din sede tun da suka gaisa suka watsake kewar juna da mahaifiyar san be sake jin kunne ba tsaban korafe korafen abun kunyar da matar sa ramat take aikatawa a saudiya
cikin tsananin damuwa da takaici hjy binta take bayyana masa iya abubuwan da suke zuwa kunnen ta game da harkokin ramata a saudiya
Kusan Komai a kunnen ta akeyi dan babu