Showing 90001 words to 93000 words out of 194085 words
Chapter 31 - KUDI KUNBAR SUSA COMPLETE BOOK By Surayyams.txt
 island zuwa wajen nemo amincewar mahaifiyar sa wajen tarayyar sa da jud.
***
Abangaren su hamida kuwa komai yakan tafi mata dadai amma tsabar son kudi dasa kishin abun da ke faruwa yasa ta kasa kwantar da hanklin ta akan komai yau ana neman cika wata guda rabon ta da saudia arabia,
Kyakkwar zama dan tayi tunanin yarta data ketare kasa bata iyawa,sede in abbakar ya gaji ya nemi aliyun dan kansa shima kuma ba lokacin yake samu ba dan bakaramin albarka aikin nasa takeyi anan ba abbkar ya samu matukar karbuwa a jahar katsina sede har yau yana kan bakar sa na komawa da iyalinsa asalin gidan sa dake abuja
Hamida ta buga ta rawa Kusan kowani busines ta dauko da fara sai taji gaba daya ya fice mata arai,kullum acikin tunanin su ramat take,ko yaya ake ciki,sun same waccan ubar hanyar kudin?..kenan ita haka nata rayuwar zata kare bayan tasan in har ramat ta dawo mammalkiyar rijiyar mai a saudi abun bazai mata da sauki aranta ba? ai tunda taji shiru kwana biyu tasan komai ya tafi dadi ne dan duk rintsi duk tsiya in har da ramat ta shiga damuwa da tuni ta kirawo hamida tana neman taimako
Bata sani ba ashe kusan sabanin hakan ne yake gudana acan,dan  dama deal din ramat da bilkisu na sati biyu ne toh gashi nan dai sun aikata komai kuma har an musu wancan hanyar da suke nema Sede wani baban abun mamaki ne ya afku wanda ya jawo ramat ta kauracewa kowa ta boye kanta gudun karma duniya taji ta shiga uku,"
sati biyu bayan dawowar su daga dubai sau daya suka je gaban sultan da bilkisu daga nan tunda kwanaki ya kifta ramat ta tsinci kanta da samun kananun ciwon mara da yawan yin fitsari,tana gwadawa kuwa ta same kundumemen cikin shege ajikin ta yau kimanin kwanan sa 20,iya kiyasatwa sunyi da bilkisu  yau 22 days da dawowar su daga dubai kuma babu tantama bada cikin kowa ajikin ta sukayi tafiyar ba.
Wanan lamari ya dame ramat sosai sakamakon shaye shayen maganai da allurai da aka dinga zabga mata dan ciki  ya zibe amma haka yaki fir.
Gaba daya ramat acikin fargaba take batada da aikin yi sai kukan kaico da razana tasan dai larabawan can bazasu taba karban wannan cikin ba,shin in ta koma nigeria me zata gaya ma aliyu wani karyan zata masa bayan tasan ta kaurece masa for good 2 month for gashi ciki ma yanzu ne yake kaiwa kwana 20?
Hakan yasa tayi boyuwar neman mafita sai ta kyale hamshakiya bilkis tana me zuwa gaban sultan suna tattunawa hakan ya zame ma ramat tamkar babban asara,dan kuwa akwai makaken bambancin hali nagarta wayewa da iya bi da harkoki tsakanin bilki da hamida
Sau dayawa in bilkisu taje fadar sultan tadawo sai sunyii kaca kaca da ramat zagin uwa ta uba kafun su dawo su shirya
A hakikanin gaskiya Inba danma an masu hanya me karfi bane by now da Bilkisu ta ruguza komai dan bata da manners sannan dakikiyar kwakwalwace da ita
Uwa uba babu wanka dan Karshen wanka in bilkusu ta jajjabo sai dai ka ganta tana tauna cheiwing a acikin rigar leshi bugun legas ta yarbawan asali,duk da zafn neman arzikin tan nan zaiyi wuya ka wulga ta hannun ta baka shako warin hammata ba
Abubuwa duka sun taru sun cunkushe zuciyar ramar tana ji tana ganin samu amma bilkisu tamaida sa rashi
 Gashi babu yadda ramat ta iya sa cikin jikin nata  
Ana saura sati guda thas bayan sati uku cif cif da dawowar su daga dubai,sultan ya yanke hukunci zai mallaka mata rijiya ko da ta duba tagani sai ta lura karami ne sosai aranan ma kusan dambe sukayi da bilkisu amma hakan ba shi ya hana komai wakana ba
Ko da ramat ta nuna rashin amincewar ta sultan sai yace "ya bata maganan shi ta karshe kenan."ko ta samu karamin koko ta same babba amma da sharadin hannun jarin sa 50-50% kan ramat kamar zai kunce tsaban bakin ciki amma dai hakan ta amsa dan tasan inbata amsa ba zata iyajin kan ta agefe. 
Wannnan abunda ya farun bakaramin jefa ramat kewar hamida yayi ba
Gashi Ta rasa yadda zatayi da laulayi gashi irin me nunawar nan ne minti daya ta tsit da yawo,bata son kaza bata so warin kaza
" taso ta kira shege yay mata aiki akan sa amma Tayaya ma zata iya gaya ma hamida tayi cikin shege bayan tasan ta hanata tafiyar ma takiji tun farko?
To tunda wautar bilkisu ya jawo mata asarar deal din komai yazo ya kare abaiibai kawai taji bazata iya ba kawai dolenta ne fa ta gaya ma hamida gaskiya dan ta shawo kanta asan nayi
Bangaren hamidar ma hakan rayuwarta yake tafiya duk kamar an saka musu hannu,bakin kishi da damuwa akan maganan business din saudi ya mugun sakota agaba u can imagine tulin zaman ta anan katsuna babu abunda take tsinanawa sai buruntu
Washe gari da safiyar Allah ta fito raka mijin ta ya fice aiki kenan saiga sallamar wata bakuwar daya sa gaban ta yayi mugun dokuwa da faduwa..
Bakuwar ce ta shigo ta dada kafewa agaban hamida tace sallama dai masu gida,ina tambaye ne ko angane mini yar uwata hamida yar fullo...mace me qamshi..?
Wani ihun balai hamida ta fasa ta rikito a gurguje tace "mena ke gani. hande?hande..  Hande.. karkice dani mafarki nakeyi nuna ta da yatsa tayi a firgixe muryan ta na rawa tace "Hande...sai ta fashe da kuka ayayin da bakowar ta taho a disashe ta rungumeta ajikin ta sosai suna me taya juna.
"Asalin sunan Hande,hamdiya muhammad,..duk da kasancewar hamida na marainiya amma hande kamar yar uwace mata na jini,dan itace suka hada uwa da ita ata wani fannin amma uba kowa da nashi
Ma'ana lokacin da mahafiyar hamida tayi aure hande itace yar agwalar data zo da ita tana zama agaban ta har aka haifo hamidar sukayi tashen kuruciya tare..
Sede banda uwa babu abunda ya hada su,kowa da nasa uban kuma kowa da nasa yaren dan baban hande asalin kanuri ne daga jahare maiduguri,bayan mutuwar iyayen hamida na asali duka ahannun inna kainuwa suka rayu
 dake inna kusan uwace ga marayu
To da hamida zataje karatu  gombe ne mahaifin hande ya zo ya dauke yarsa ya maida ta maiduguri after 20years sai yau Allah ya sakeyin gamowar sa
Waje na musamman suka nema suka zauna yau Sunci kukan kewa da rabuwan bazata da sukayi,labari akan labari game da abubuwan da suka wakana tun ana kuka har aka dawo ana buga shewa ana dariya
"Abu kadan hande zata buga guda tace
Shegiya hamida qamshi ansamu duniya haka kukayi kudi?hamida kuwa sai dai tayi murmushi tana alfaharin d yadda taga yar uwantan
Dan kuwa babu marabar su wajen  wayewa iya daukar wanka da kwalisa
Sede ita hamdiya ba  zallan dirin manyan mata take da shi ba 
Tana da asalin kiba
Da tula tulan maxauna fiye da na hamida
Ita dai hamdiya ba fara bace sosai amma baza ace da ita baka ba kwarariiya ce wajen iya kwalliya da tsara duk wani abun da ya shafi gyaran jiki musamman ma na ya mace..
Takan hada kaya harda kayan mata sannan tsaban ta shahara babu wata jaruma me sana'ar ata yankin sokoto maiduguri niger sudan india da yankin larabawa wanda bata sani ba
Busines din ta kenan kuma Tayi kudi da harkan bana wasa ba,ayanzu haka ta dawo neman yar uwan ta ne sabida mutuwar mahaifin ta wanda dama  shi ya mata katangar karfe da hada zumunta da yar cikin mahaifiyarta hamida sannan ya kafe ta ya hanata aure.
Taso ta tsine ma bakar halin sa amma duk cikin halayen hamdiya babu abunda ya fi karfi kamar tausayi da mattukar son neman ilimin addini ta karanta fannin biology education a unimaid amma bazaka wani gane hakan ba sabida ita bokon a ado kawai ta dauke shi
Awajen ta sana'arta ya mata riga da wando,hakan yana daya daga cikin kyakyawar garkuwan da ta samo har Allah ya kawo ta wannan lokacin
Daga yadda suke hirar au zaka san lallai sunyi matukar shakuwa  dan babu abunda suke boye ma juna,kaf labarin arzikin hamdiya ta bada hamida hakama hamidar ta shiga zayyana mata dukan abunda ke faruwa da ita game da neman kudi da abunda ya lifta tsakanin ta da kawarta kuma aminiyarta ramat wanda hamdiyar bata taba sani ba sai yau,ita takan ce ma tafi kowa sanin hamida akan maitar son kudi
So xata iya amincewa da Komai daya futo daga bakin hamidar
Sai dai maganan ramat shiyaso ya bata musu komai
Dan Fada hande ta shiga mata tana nuna sam hanlkin ta bai kwance akan ramat din nan ba,tacw ace mace ce da mugun zuciya har haka?tace kedai hamida baki sauya ba inba shegen son kudi ba inake ina hada hanya da muguwar iri
Irin wannan?wanan fa ba kawa bace irin su ne ake cewa da haihuwar su gwara barin su,me zata tsinana maki?zakici aminta ne yanzu keda bakinki kike gaya min yadda kuka rabu a saudi,to in zaki shafama kanki sa'a ki kunce kawance nan
Hamida tace tab a'ha hamdiya,bazaki gane bane,wallahy bazan iya haka nan kawai ba,kin manta nace miki ramat tana auran asalin attajiri ne?wallhy in har ta sami harkan man nan sai nasan yadda zanyi in yanke rabo na haka kawai in kyale kifi inbi gwado?tab
Hamdiya tace hm yi saffa saffa dai nidai na gargade ki
Tace waima kina zagawa wajen inna kuwa?
Hamida tace turrr wata innar datake juya min kan miji da yata?
Hamdiya tace wayyo Allah anyi uwar banza kince min ki haihu da abbakar dan Allah ina yata jud,jud ko?ita take?ke kya rasa suna sai jud?sekace wanda akayi mana gorin baki da ja.
 Dariya hamida ta fashe da shi
Jud yar gatan maman ta ina kike kizo kiga asalin mamanki,ina kike farar wata sha kallo
Ta kalle hamidan tace Hamida anya ta gado kyaun mama kuwa?ko de dangin inna ta debo
Hamida ta yanke dariyar tace ai sai kiyi,yata kam ta girma sosai kuma ma dake tayi kama
Allah ya kiyaye ta debo gadon mabarata 
Murmushi kawai hamdiya tayi ta cigaba da zaga falon tana nema  ganin jud,dan tariga tasan yar tsaman dake tsakanin hamida da inna tun suna kanana wannan tara yaran bara da simple life irin na inna shi sama hamida taki jini sam arayuwarta
Haka suka karashe shirmen su sukayi dakin hamida ta gaya mata ai jud bata nan taje india,nan ma wani sabuwar hirar aka bude,kafin yamma har sun cancnda azabar wanka sun sha kwalliya gidan shikansa ya gumame kamar zai yi magana dan qamshin turare
Dake hamdiyar tace zatayi oder sinadaran kayan hadi kayan mata anan katsina,se hamida tasa aka share mata wani babban site agidan na musamman abun gwanin ban sha'awa yarda suke matukar kaunar juna.
 
Koda abbakr ya dawo bai same matsala da hande ba,dan ba marabar ta da hamida saidai ita babu wannan tsinannen son kudi aranta kamar na hamida kuma ita tana da sanin ya kamata kodan Albarkacin harkallar cinikayya da gogayya da mata datakeyi awajaje daban daban..
Hakan suka yi zaman suna dan fita,hande tana dawowa karfe hudu na yamma ne inda ta dinga saka hamida agaba tana cusa ta akan hanya musaman rufe idon datayi akan kudin ramat da ceqa kawau tafara tada nata a Kwana biyu kacal hamdiya ta hana hamida zaman sakat
Dadin samun gwarin giwar hamida yazo ne a lokacin da hamdiya tace itama a abuja  zata siya gida kuma takafa kamfanin ta
Tasan kenan koba komai dai bazasu sake rabuwa ba dan bakaramin son yar uwantan take ba
Sede tsaban son kudin hamida takejin bazafa ta kyale ramat ba,yau kamar yadda hande ta taso mata da tambayayo akan rayuwan yarta jud haka itama ta bijiro ma zuciyarta tsaban tunanin ramat dan tana da yaqinin awannan satin zasu dawo...
hande ba mace me daukar dumi bace amma sam bata ji dadin yadda hamida ta babbata amsa akan rayuwar jud ba
Da kyar ma ta amince sukayi video call ta waya,Allah ya so jud din ma ita daya ne nan hamida ta hada su da hande
Suka jima suna gaisawa dan hande har hawayen dadi se datayi data kalli jud kuma sukayi magana,tace ma jud nice asalin mamarki karki damu xaki dawo ina nan injiranki ko auta?jud sede tayi murmushi dan ta lura sabuwar antyn ta bata da matsalar saurin sabawa da mutum
To bayan nan kusan kowani rana tana tura mata sakon yaya take?tun abun nama jud wani iri harta zo ta saba tana amsa anty hamdiyar,ita kuwa intaga hakan dadi takeji aranta dan bata tsammanin yar sun ta girma tayi hankali har haka ba
Kuma gani take sune kawai famylin ta na asali a duniyar nan
hakan yasa yau dataje office din ta ta kira inna suka sha hirar dn tuni ta karbe numberta wajen abbakar inna yau harda kuka
Hamdiya tace mudiin suka kammala komai zasu dawo abuja me gaba dayan su
A kiyastawarta baifi nan da kwana 10 zuwa kwanaki sha biyu ba
Hamida ta dawo ita daya by 4 zata shiga gida babban wayarta ne ya hau ruri tana dagawa kuwa taci karo da sunan shakikiyarta wato ramat. 
_KKSPls inbaka biya ba karka karanta game bukatar sayan littafin ya turo katin mtn ta 300 ko 450vip ma 08060712446,ko ta acct 0152983148 surayyah muhammad suleh gtb.kuji tsoron Allah kubar masu shi_[7/8, 12:00 AM] SURAYYAHMS: 42..
_KKSPls inbaka biya ba karka karanta game bukatar sayan littafin ya turo katin mtn ta 300 ko 450vip ma 08060712446,ko ta acct 0152983148 surayyah muhammad suleh gtb.kuji tsoron Allah kubar masu shi_
Saida hamida taja aji cikin sake saken me zata tarar sannan ta aza wayar a kunne,tace hello?tunkan ta kara wata kalma wani sautin dirin kuka ya sauka a kunnen ta,"wani muguwar buguwar zuciya ya tsaida da hamida atsorece tace meye,wai meye haka zaki kirani kinamin ihu akunne?kinje kinyi kisan kaine?ko yan damfara suka hau kanki,cikin kuka ramat tace hamida na shiga uku,ashe har xaki iya yin watsi dani hamida? meyayi zafi da zaki ki kira na yau har ana neman cika wata guda?hamida ashe akwai abar duniya da zata raba mu?cikin dakewa
Hamida tace butan wa dama akan wannan maganan ne kike neman tsinka min zuciya..ehm dakata min,..akwai mana ramla... tsaf abar duniya zata rabamu...aikin ban mamaki har wata kidahumar ce xata zuga ki akaina?anyways i dont have time to talk about it,ince de anyi business anci riba mu ambarmu da tsiyarmu?juyn mulki ne dama ya taho da sauyin matsayi
Cikin kuka ramat tace hamida ki pls kiyi hakri dan Allah saurare ni, ni wallahy banda wacce tafiye min ke a duniya,ko uwata bata kawo mun ke amfani ba. 
Hamida ta yatsina
"uwarki fa kikace ramat"tace eh ita din fa jumare david...,hamida tace ohh cut the crab ramla bana son wani dadin baki kifada min matsalar ki kawai dan nasan matsalace yasa kika nemo ni,"tace hamida naci bakar azaba da kika barni,i seruiosly regret hada harkata da bilkisu she ruined me ta bata min komai,cike da mamaki hamida tace kamar yaya me kike nufi,?wai duk uwar karuwancin da kika biye mata kuka jefa kanku baki samu rijyar man ba?
Cikin kukan takaici Tace nasamu mana.
Hamida dake fama da bakin cikin  jin haka cikin sake zazzakar tsaki da bacin rai tace and "so what?meye ne to kika kirani kinamin kuka?bukatar ki be biya ba?ramat ta dada fashewa da kukan soundin helpless can tace ina kuwa zai biya bayan bilkisu tana kusa,hamida can you imagine mu  dawo saudia banda lpya dan na turata ta gaban sultan tay closing deal,cikin shessheka tayi stressing maganan
"closing deal fa kawai shikenan komai ya lalace na rassa rijiya yanzu haka "share" kawai aka bani 50-50 dani da sultan,hamida tace innalihhi wa inna ahi rajiun,wani irin dan kutumar uban ciwo ne da zai aje ki haka ramat,kinada hanklu kuwa inake ina dora waccan jakar akan babban sana'a,u knw how things are with sultan,u only get one chance take it or leave ita,dada fashewa da kuka ramat tayi tace hamida wannan ciwon ya fi karfina ne,wallhy am feeling terible wil you please help me?nasan ke kadaice a duniya zaki rufa min asiri,yau in aliyu ya ji wannan maganar wallhy na shiga uku.
Im dead,ko shege ba kira ba wallhy am just confused
Wani bugu kirji  hamida yay karayi tace meye ne?wai nikam kanjamau kika debo ne kome?
Tace wannan ai yafi shi,don wallhy in bakiyi min wani abu akai ba nasan zan iya rasa martaba ta zan rasa aliyu har abada..
Hamida tace speak out,wani ciwo ne wannan?
Tace ciki,hamida ciki sukamin a dubai kuma wallahy bansan waya min ba kuma duk iya abnda kika sani nayi amma cikin nan yaki ya zube,nasake baki shege yace bazan haihu ba amma likitoci sunce min suma haka sukagansa ajikina 
Wayyyo na shiga na i just cant tek anymore risk da shawarwarin bilkisu dan Allah hamida kitaimaka kiyi wa Allahn daya halicce ki yamki rai kizo min gobe,..i really need ur help kawata hamida please do sumting...kuka takeyi sosai harbakin ta na rawa 
hamida ta katse wayar bata ce uffan ba illa tsabar kaduwa da daurewar kai daya hanata motsi
Tace Ciki?cikin shege da auren wani?innalillahi Kinga abun danake jiye mata kenan ko
God forbid,Wani alkwarin banza shegen ma ai bai isa ja da ikon Allah ba,Allahumma ajirni fi musabati.
Da jimamin haka ta nufi cikin gidan sanda tayi wanka ta nitsu sannan ta rubuta ma ramat din sako ta hanyar email,tana me sanar mata zata zo a goben amma se abbakar ya amince.
So bayan abbakar ya dawo duka suna zaune a falo da anty hamdiya,hirar inna sukeyi sai ga hamida tana dan sa musu baki abun ya matukar basu mamaki amma ba wanda ya tanka saida hamde tayi musu sallama sannan ta kawo masa zance...Tace "ramat tana asibiti tana matukar bukatar taimako
kuma nakira aliyu ance ya bar kasa ko kaji labarin sa?Yace subhanallah banji ba meyasameta?tayi kamar abun bai wani dame ta ta jingina kai a kan kujera"..tace zazzafan zazzabi ne tun jiya ta kira tana min kuka wai sede inzo,..but i dont knw if i can,abbakar yace hmm yau kuma?ke dai in kinada lokaci sai ki kirata kiji imma yayane seki kirani inji me kuka yanke,tace to daga hakan suka rabu bayan yaje daki ta tura ma ramat tex akan ta kira shi yanzun ta yi pretending dan bata so ta nuna zataje din ko hamde tayi korafi,hakan kuwa akayi washe gari abbakar dakan sa ya









