Showing 96001 words to 99000 words out of 194085 words

Chapter 33 - KUDI KUNBAR SUSA COMPLETE BOOK By Surayyams.txt

01 Sep 2025

1131

ba da dubara na ba,ya ubngiji na,"cikin sarkafewar murya ta rusuna kasa,da cikakken ihsni tamkar agaban sa take,tace ka sa wannan neman aure ya bambanta da kowanne samun aure arayuwan dana aliyu,ka dabbaka alherin dake ciki ka kore sharrin dake ciki,Allah,kasa yarinyar nan ta xamto sanadiyyar dabbaka zuria dayyaba arayuwar dana.

Hakan ta cigabafa adua cikin yaqini dan tun bayan mutuwar fatima ta cire abun aranta shuyasa all this while bata masa maganan kowa ba,amma tunda yau shiyaje ya kyallaro yace gashi,gani take me hana yuwar auren nan se lillahi dakansa,ko in ita yarinyar tace bata so! ..

Tuno da hakan yasa ta fada cikin tunanin yadda zata gane gaskiyar maganan ta fannin jud,dan ta lura yarinyar akwai kunya,gata dai yar zamani cas cas amma she daubt ko in taje nata da maganan auren nasu zata ita bata cikakkun amsa

Duk da tunanin hakan datayi bata fasa ba,sede ba atake taje ba sanda ta nitsu ta dada yin tunani sannan bayan awa uku ta futo direct ta nufi dakin jud.

Tayi sallama sau uku ba a ansa ba,a hankli ta turo kofar tana leke,wanda yayi dede da budewar kofar bayi ta ciki,jud din ne ta fito daga wanka bata ma lura da mutum abakin kofa ba sanda ta yakice head wrap din ta da alamar zata bushar da gashi,wani ruff suka sulale suka zube agadon bayan ta,inda aka bar hjy binta da dada kare ma halittar jikin ta kallo,ko inan ta nads haske da kyaun gani har wani shegen kyalli fatar kafarta keyi yan dede ne yatsun ta dogaye kuma tsirara ajere bisa layi kamar ita dakan ta ta zana su,abu daya ne suka
Rasa kuma shine lalle,hjy tuni ta mule duniyar tunani dan har wani gani amarya amarya take yi ma jud,jud tana shirin gyara daurin towel zata kunne handrier sai taji uhmmmmm uhmmm abayan taa
A mugun firgice ta waigo,wani instant hade ido sukayi tayi saurin maida nata kasa cikin jin kunya

Hjy tayi murmushi
Har yanzu bata dena sama kyaun ta albarka axciyarta ba,kamar wata balaribiya haka nan jikakken suman sukayi da fuskan ta
Hjy ta matso bayabo ba fallasa tanacewa ashe wanka kike?ai nata sallama banjiki ba,jud ta sauke ido kasa Tace eh,bata san ya akayi ba taji hannun hjy akafadunta,"no need to be shy of me dear
Zauna anan in tayaki,ba musu jud ta zauna akan stool,da mamakin ta taga hjya ta yalyali suman kayin ta ta kunne hair dryr tana busar mata da shi,time to time tana mata oiling da deep moisturers,kuma
A hanlki take bi da ita kamat yar kwai tanayi suna dan hira kadan kadan,tun jud taba matsewa har ta dan sake jiki
tsaban dadin gentle touches din har wani lummushe idanu take tana jin layi

Can bayan ta gyara tayi mata parking tsaf tace me zakiy?
Tace kayana zansa in shirya,hjy tace ok sai ta kyketa ta futa,

Turaren dumama jikin ta ta bula tana meyi makanta sirace aftrr some minutes ta shirya Sai a Wajen cin lunch suka hadu tana zama ba a wani dade ba aliyu ya basu waje kuma dama tunda ta zauna kallon shi take yi asace har ya mike ta bi bayan shi da leke hjya nata kallon ta tana murmushi,"juice me sanyi ta zuba a cup ta kurba cikin gyaran muryan ta da saida jud ta waigo suka hade ido,faffadan murmushi ta sakar mata ayayin da jikin ta ke amsar sakonnin data keso ta isar,gaban ta ne ya fadi ras ta rasa nayi sai juya fork take tana rau rau da idanu,"cikin dada so ta bayyana mata cewa ta sani hjya tace ci abincinki mana aliyu kam yaci nashi..karki damu da shi,jud ta danyi murmushi Dan Shiru ne y gifta kafin hjya tace gobe zaku tfi ko!tace eh mumy,aje fork din dake hannun ta tyi ta kalle jud din tace ok,yau she ne hutun schl zai kare?Tace kwana biyar masu zuwa zamu koma..
Naji ance iyayen ki ma zasu dwo abuja ko?tun kan jud ta amsa tace my dear u see i wll like to meet ur parent ina dai zasu bani ke?jud ta bata shiru. Tace nima nan da satikai biyu zanzo jud tayi shiru bata ce komai ba can tace Allah ya kawo ki lpy mumy,jin hannun hjy tayi akan nata tana me wani irin tsare ta da sigar kallo wanda ya furta thousands words but yet its silence,kallo ne na nuna so,nuna yarda, da gode mata da amincewa da su tayi,kallo ne na she is welcome to thy family wanda ya saka jud jin ta kara birkicewa da frgaba a hankli ta sulale hannun ta kamar wacce zata tashi ta bar wajen,gently speaking hjy tace yata?cikin sanyin murya Jud tace naam,akwai maganan da nake so muyi dake ba a matsayin komai ba sede a matsayin mu na yaya mata,..so do sit down ki bani hankln ki
Ba musu jud ta gyara zaman ta cikin bada nitsuwar ta me gaba daya hjy tace toh Alhamdullh ala kulli haalin duk dama Zama cikin zuriar bulama ba aba bace me sauki ba amma ki dauka inkin same ni kamar kina magana da yawun kowa ne a family na,duk wani hukunci da zan yanke shi zasu yanke, hakama duk wani abun karuwa da zan kawo babu shakka awajen su duk nasu ne..ko kin fahimceni?jud tyi shiru cikin rudani hjy tce,...ok Aliyu ne yazo min da magana akanki dazu..maganan aure...kina sane ko?
Jud ta dada sunkuyar da kai mayafin abayar ta take dan wasa da shi batace komai ba...,"ajiyan zciya hjy tayi tace in har kina son shi babu me hanaku aure yata,ni dama damuwata kece,bana so kiyi abunda baki da tabbacin su,nasan aliyu ya gaya miki yana da mata ko?ai kinsan ta ma naji ance sunayi da mahaifiyar ki...

Ahnkli Jud tace eh

Hj tace,to karki sa komai aranki addua zaki tayi Allah ya tabbatar, nikuma namiki alkwarin Muddin da yardanki aciki To kisa aranki ni me baki goyon baya ne nothing to fear kinji?.

Jud ta dada dauke idanun ta kasa cikin tsananin jin kunya

Ina so kiyi tunani ne sosai sabida ke yarinyace kuma har yanzu baki san me duniyar take ciki ba..daga yau Ki dauke ni kamar uwa,kuma zanso ace na samu hakan awajenki har karshen rayuwar mu...be free with me karki damu duk matsalarki d damuwar ki ni me dauka ce,u just need to calm urself nd trust us ko jud?jud bata san sanda ta gyada kai ba,Allah ya miki albarka..tace ameen cikin jin kunya ta tashi ta bar wajen
Dakin ta tanufa ta fada kan gado wani dadi da karfin gwiwa na mamaye ta,tunda maman sa ta nuna ta karbeta hannu biyu wani karin son shi ya shiga huruwa a zuciyarta

Haka ranan suka dinga wasan boye har dare yayi inda suka shiga shirin tafiyar su,nan ma aliyu ne yace ta tabbata tayi godiya ma mama in sunje sallama bcos she packed alot of suprises for her sai sunje gida zai bata.

Aikuwa hakan akayi dan bakaramun godiya jud tayi ma mumyn aliyu ba,tasha albarka da kalamai masu karo karfin gwiwa jirgin 8am ya tashi da su zuwa UK dan anan zaifi musu saukin zuwa direct har nigeria....😍
I wll wait nd see in har ba a fitar da wannan ba zan cigaba in aka fitar i wll love to take necessary caution
[7/9, 5:32 PM] SURAYYAHMS: 44.
_KKS38Pls inbaka biya ba karka karanta game bukatar sayan littafin ya turo katin mtn ta 300 ko 450vip ma 08060712446,ko ta acct 0152983148 surayyah muhammad suleh gtb.kuji tsoron Allah kubar masu shi_

Can cikin dare suka isa uk dan haka aliyu yace su kwana anan sabida ya lura kamar jud din ta gaji sosai,daki me kyau aka basu inda ta shara baccin ta kusa da shi,can cikin dare ta farka haka kawai takejin sha'awar kirar anty hamdiya,ringing biyu aka dauke tace salam helo anty?

Da muryn bacci anty Tace jud?kece da dare haka lpya tace anty dare ne wajen ku nan fa baifi saura awa biyu safiya yayi ba?
Hamdiya oihh to ya akayi ne?yaya kuke nata kiranki baya shiga tace eh anty a jirgi nake zamu dawo nigeria yau shine nace bari na sanar dake..

Umma na fa?harta dawo ko har yanzu?
Tace bata dawoba kinsan kawartan batta lpya jud tace ohh,anty tace kinsan ya zaa'yi bacci yamin yawa in kun tashi ki rubuta min sako kuma daga zarar kin shigo abuja ki sanar dani zan kiraki tace ok to anty Ki kula min dakanki kinji?tace ok sleep tite sai suka katse wayar,runtse idanun ta tayi tana jin wani sanyi sanyi aranta its feel difrnt azuciyan ta dan bayan abban ta da inna raban taji wani nata y damu da ta haka ta dade,haka kawai takejin ta aminta da halayen anty hamdiya.

Juyawa tayi ta dayan gefen ta ga aliyu na baccin sa hanklli kwance,matsowa tayi daf tana me kare ma fuskar sa kallo,tun daga kan goshin sa dake kyalli Zuwa zarara xaran gashin idanun sa,doguwar hancin sa dayayi marging da kyararren sajen sa wanda sukayi kyau a masaukin gemun sa yan dede gwanin ban sha'awa kasar habar sa,ga lips dinsa tayi wani irin fressh kamar an shafa masa jan baki Tsadadden Murmushin ta kawai tayi ta sake ajiyan zuciya ta sauko akan gadon tana ta tunanin sa can ta nufi bathrum domin yi wanka


Fannin su ramat kuwa ba karamin azaba tasha da zubar jini ba dan da kyar yazo ya dena kuma ta sane sarai bazai wuce mahaifarta ne ke da matsalar da hakan ba but how comes ita da shege yace bazata dau ciki ba?

ayaune da sukaje asibitin likita ke tabbatar musu da cewa ta rabu da cikin amma setayi jinya sosai ko dan ta samu karfin jikin ta.

Gashi Har yanzu Suna hotel din a boye don har yanzu ramat bata iya tsinana komai sai kwanciya da yawan cin abinci ko da ta kira bilkisu awaya taki sam ta gaya mata inda take bare ta gaya mata suna tare da hamida ne kuma anyi nasara ciki ya zuba,to kamar yadda likuta ya basu shawara haka ma boka shege ya basu shawara cewa yayi ramat ta lura da lpyarta ta warke sosai kafin ta dawo nigeria dan kuwa akwai yaki me karfi dake shirin tunkarota wanda bai bayyana masa ba,aganin ramat wani yaki ne wannan inba yaki tsakanin ta da uwar aliyu ba ai jiya taji a news ance zata dawo zatayi running wani "peace nd conflict resolution programe a hilton abuja,kenan zata xo ta dame ta

Hamida kuwa bata nan take ba,ita dai ta nace akan shege saiya gaya musu menene rikicin amma ramat sam taki bada kai bare ta sa kaimi shege kuwa ko ajikin sa yakan dabbaka kalaman sa masu dadi ne a kunnen ramat ta hanyar nuna mata ko acikin faduwartan ma akwai nasara alhali shikan sa yasan ba hakan bane kawai dai kudi yake so

yana matukar so ayi da shi sosai acikin kudin man fetur din nan,dan dama yana so ya mallaki wani gida dake cikin ministers qtrs Abuja dan ya maida sa gidan karban bakin sa manya wanda baya so suzo jejin da yake kuma gidan har milliyan 200 ne
Baya so kuma ya karar da arzikin sa kaf wajen siya.

Kwana biyu na musamman yake kira ya musu hirarraki ramat gani take aida hamida ta zo ne ya manne musu yayi yawa haka.

Shiya dada bada shawaran cewa ramat tayi babban partyn samun nasarar ta datake shiryawa anan saudi basai ta dawo nigeria kamar yadda suka tsara yi a abuja ba

Matsala daya ne da
Hamida taki bada amincewar ta akai

musamman da ramat din ta nuna tana so ta cusa mata cewa lallai tazauna ta jirata ciwon ta ya warke suna shirin hidiman tare in yaso in anyi sai su dawo nigeria

Hamida tace atafur ita gida zata dan akarkashin miji take,kuma bazata iya kara sati uku akan wanda tayi ba,kuma ma inba a abuja zaayi hidmar ba ita bazata zo ba sabida tana da abubuwan yi agaban ta,kuma tace mata karshen wannan satin zasu koma abuja

Tun abun na wasa wasa har ran ramat ya so ya baci

Tace hamida na lura yanzu bani da muhimmanci arayuwanki wancan wawar mijin naki yafi miki ni yafimiki komai arayuwanki

Hamida tace wawar miji? hararata tayi a sigar mata marasa hakri,sede ubanki ne wawa amma ba miji na ba, ke ramat ki iye bakin ki taja ta nuna ta da yar yatsa

Ramat Tace eh naji,amma ai gaskiya ne,kina bashi dama dayawa haka fa bilkusu ta kawo babban harka na samun kudi amma sabida shi kika tsallake kika gudu

Hamida tace eh kedin da kikaje meya sameki?dan ke baki san darajar aure ba akace miki nima bansani ba?
Ki dube ni nan asalin bafulatana ce
Ni gaba daya ba,ramla bazan zauna anan ba bayan kekanki kinsan da wayo ma na barsa dan nazo na share kazantar ki
In bilkisun wata abace ai da sai ki nemo ta ku xauna iskanci kawai

Ramat tace iyyye Hamida meya kawo gori?dan kawai banda lpya na nimi taimakon ki

Tace dakata min bawani gori anan.. magana daya ne
Ure sick zan zauna anan harki warke amma batun program wallhy babu ni aciki dan mijina abbakar bazai taba yadda ba
Inde kinaso in kasance dake ramla kawai mukuma gida tare ayi komai acan

Tace hamida bazan iyaba,kinsan abun da nakeji kuwa?toh wallhy ina zuwa aliyu ze iya cewa in bashi ladan auren sa,kuma in ya tabani ahaka sede kizo kiyi zaman makoki na,what if wani abu ya faru ma ya gane na zubda ciki...i migh even colapse u knw,kuma kinsan shi u knw how he is baya wasa wajen abun nan..ta dafe goshi cikin gajiya tana kkuni "Wayasan ma abunda shege ya hango min kenan yaketa kwana kwana Pls hamida stay by my side kwana dayane fa abun nan

Hamida Tace hmmmm Gaskiya nafada miki jinya kawai zan miki in abun ba dole bane kawai muje gida in yaso mwayi daga baya.

Haka sukayi ta musu amma basu cimma matsaya ba
Washe gari suka shirya da zimman komawa estate
,kawai sega shi estate ko ina a kargame an kulle har bakin gate da manyan gwaduna, ramat tana cikin mota bata sauko ba dan sosai hanklin ta ya tashi,ta dau wayarta ta hau kire kire hamida ta tambaye maigadi waya kulle musu gida?mai gadi yace jami:ai ne sukaxo suka kulle

Tana juyowa tace ramat kinji ko?
Tsaki ramat tayi ta kife kanta da gwiwa kamar zata fashe da kuka"
Tace Hamida Mukoma hotel aliyu ne yasa aka kulle masa abarsa..
Yanzu na kiira care taker wai angaya masa na tara mata barayi yan iska

..cikin gwalo ido hamida tace wht?lallai gulma akwaita da nisan kiwo hmmm lallai tabb,Allah ya sawwaka yanxu haka Bazai wuce akan wayannan kawayenkin bane.

Tace bilkisu?

Hamida tace itafa
Tace bilkisu ta dena sata karma adaura mata kawai aliyu ya tsane ni ne kuma baki so afadi lefin sa,baida wani aiki se aikin to zartani,ai yasan ina nan meyasa zaisa a kulle gida banda walakanci?msweee

Hamida tace abeg shut up kwananki nawa baki nan wayasan metake aikatawa anan din?aike ma baki son laifin kawarki,ramat tana shiru,Nan suka lallaba suka koma hotel din bayan kwana biyu ta jawo bilkisu cikin su

****Karfe 5 na yamma aliyu da jud suka sauka inda wata katuwar black jeep tinted black tazo debar su,waya yake tayi ayayin da jud ta lafe agefen jikin sa kanta na aje akan kafadarsa tanajin duk abunda yake fada shikuma hannun ta daya ya kama yana wasa da su acikin nashi

Jikn ta ne yayi sanyi sosai jin abunda yake fadan,.."haka kawai taji babu dadi aranta,tace yanzu fa muka dawo kasar ko hutawa baiyi ba zaace ana nemar sa wani wajen?
..shikenan mutum ba hutu arayuwar sa kenan

Fuskan ta ba asake ba har suka iso gida inda su safiya da sauran ma'aikatan suka nuna murnan dawowartan suka gaggaisa tayi hanyar dakin ta

Wanka ta fada ta sauya kaya ta fito kafin nn har angama shirya musu abinci sunaci yake tambayarta gajiyar hanya cikin nuna kulawar sa itako cikin shagwaba da sangarta take amsashi,anan ne ya ke mata bayanin dan tafiyar da zaiyin zuwa lagos acewar sa in yaje can tare da maman sa zasu dawo abuja dan ata can zata sauka se azo ayi maganan su me gaba daya agaban iyaye.

Taji dadin hakan shiyasa Bata wani bayyana masa rashin jin dadin tafiyar da zaiyin sosai ba musanman ma data lura kamar ya saba da abun har baya damun sa,"

Da yamma ya aiko mata da pakackage na gifts suprise din da mahaifiyar sa ta bayar, abata"tana budewa taci karo da wani tsadadden sarkan wuya dan kunne da awarwaron daham mai makale da agogon sa agefe sunyi matukar kyau suna sheki,dayan kuma turarruka ne daban daban masu matukar tsada jud kamar zata fashe da kuka dan all this meant alot to her tasan inda kudinsu aka bata bazata iya karban su matsayin kyauta ba,agaban aliyun ta kira hjy bintar sukayi magana sosai tana me gode mata hankalin sa ne yake dada kwanciya in yana kallon yadda kauna da soyayyar uwa yake neman ninkuwa tsakanin su,ji yake kamar baida wani abunda ya rage masa face ya gode ma Allahn sa

Saura kwana biyu a koma schl Shiryawa jud takeyi ayayin da aliyu ya sa aka gama mata komai kamar kullum yanata jan lokaci ne dan ya zauna tare da ita dan,yaga kamar bata son tfiyar sa amma take boyewa
Aynzu Inta zauna kullum bata da wani aiki se de suyi waya da anty hamdiya time to time take kiran su anty zakiyya wanda already har hjy binta ta sanar da su mke faruwa kuma sunyi matukar farinciki bana wasaba,su suka kara bada hjy binta tabbacin halayen jud wanda ya dada hura wutar kaunar ta axuciyar ta,tun da suka barta take zumudin auren

Haka kawai taji ta matsu ta damu komai tana yi ne agurguje dan next week yazo ta dawo nigeria ta fuskace iyayen jud a daura auren nan maza maza..

Tun tafiyar su da kwana daya ta bada aikin istikhara yanzu haka zaman jiran amsar ta take dan gaba daya ta saka ranta akan jud,tanajin this time aliyu ya kure ta wannan karon ya kawo na gida,gata bafulatna me jin yare da kiyaye al'ada.

Kan kace kobo jud tafaraa ganin kulawa ta ko wani fannin dangin sa dan haka itama ta dada jin abun ya matukar shigarta har Bata wani damu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login