Showing 51001 words to 54000 words out of 268365 words

Chapter 18 - Tana Tare da ni complete book document .txt

29 Aug 2024

44751

Hannu Anas yasa cikin gashinsa yana hargitsawa “ohhh! Kacallah I’m not in a good mood yau please go I’m sorry.” Nan yagama signing wa Kacallah ya fice. Fannah kam mamaki Anas yake bata wai mutum ata had’asa da Allah amman baiji da sauri ta kawar da kanta daga kansa kafin ya koreta. Ana cikin haka wayarsa ya soma ringing nan Fannah ta d’ago kai tana kallonsa bayan ya duba yaga wa ke kira yaja tsaki ba tare da ya d’aga ba. Call d’in na tsinkewa aka sake bugawa a fusace ya d’aga wayar yasoma magana a tsawace “Aleeya please karki sake kira na, wace erin super glue ce ke? nace miki banasan ki I don’t love you ki hak’ura mana! Don’t ever call me again ni na fad’a miki.” Karap ya katse wayar.

Baki wangalau Fannah ta bud’e tana kallon Anas dukda cewar batasan meya had’asa da budurwar tasa ba setaji ta tausaya mata aiko ma me tayi bekamata yamata haka ba, yayi hurting feelings nata yayi yawa haba mana.


“Lafiya?” Ya tambayeta tare da dawo da ita daga duniyar tunanin data fad’a. “Eh..ehh lafiya” ta fad’i a rikice.
“Then stop starring at me, kidena kallo na haka please!” Ya daka mata tsawa. Kuka ta soma take tasa hijabinta ta rufe fuskar ta dashi. Ita dama ya sallameta taje gida tagaji da zama nan. Bayan kamar minti goma akayi knocking bakin k’ofar office na Anas a lokacin kuwa yana kan waya nuni yayi da ido kan Fannah taje ta bud’e. Hawayenta ta gama sharewa sannan ta mik’e taje ta bud’e wani ne bata tab’a ganinsa ba.
Bayan Anas ya kammala wayan ya d’ago blue eyes nasa ya aza kan yaron “yes Haruna wani abu ne?”


“Boss yanzu wani ya kawo wannan flowers wai daga Aleeya kan kayi hak’uri ga letter nan manne a jiki.” Nan ya matso kusa da table na Anas da nufin ajiyewa.
“Ka kuskura ka ajiye wannan gabbage (bola) a gabana you’ll be fired.” Ai tsam Haruna ya rungume flawan a jikinsa. “Boss dan Allah kayi hak’uri.”
“Ka fita dashi bana san ganinshi cikin office d’ina.”
“Yes Boss. Dama kitchen ne ya d’an kama da gobara amman an samu an kashe da wuri, b’arna kad’an yayi wanda ya kamata a kira me giara da wuri.” Ya fad’a yana b’ari dan ya karanci yau Anas is not in a good mood.
“Meya jawo gobaran?”
“Chef (me girki) Zainab ce ta manta tabar cylinder a bud’e se gas yayi flowing amman bada sanin ta bane.”
“Kaje kayi firing nata now wannan ganganci ne, kace mata inji ni ta tattara kanta tabar min building.”
“Yy.. Yes Boss” take ya juya ya fita. Fannah kallon Anas take cike da mamaki mesa zuciyarsa take da tauri haka?

“Kinada abin cewa ne?” Ya tambayi Fannah ba tare da ya kalleta ba. “A’a” ta amsa a takaice. Tun k’arfe 2:00PM Anas ya tattara kayakinsa yasoma shirin tafiya gida. Coffee cikin flask yasa Fannah ta had’a masa takuma kai masa har cikin mota sannan ya fice koda ya isa gida Amal kawai ya kula ya wuce d’akinsa. Ba komai ne yasa Anas acting haka ba kuwa a ranan se dan mafarkin Ummimi dayayi.


Fannah kuwa isarta gida duk su Mami suka soma jero mata tambayiyi ya sabon aikinta, k’arya tayi tace musu great, alhamdulillah.


_Washegari..._


Tun k’arfe 7:00AM Fannah ta gama shirinta dukda kuwa Anas be kirata ba amman dan gudun kar tayi latti. Se 7:30AM ya kirata. Tana d’agawa kafin ta gaishe sa yace, “ina jiranki by 8:00AM in kika k’ara koda minti d’aya a bakin aikinki.” Kafin tace, “okay” ya katse wayar. Daman tagama shirinta kud’in transport kawai ta d’auko ta fice daidai 7:55AM ta isa office kasancewar hold ups. A gigice tashiga ciki ta yi elevator daidai 7:58AM tayi knocking bakin k’ofar office na Anas shiru taji ba amsa tayi knocking kusan sau uku ba response wayarta taciro ta duba agogonta taga har 8:00AM yayi daidai nan personal elevator’n Anas ya bud’u tare da bayyano da Anas. Sanye yake da black suit farin shirt da red necktie sosai yayi kyau.


Bayan ya k’ariso ta gaishesa ba tare da ya amsa ba yasa card nasa ya bud’e ko’far tana a bayansa suka shiga office d’in. Jakarsa ya ajiye kan table sannan ya juyo tare da crossing hannayensa kan k’irjinsa yana kallon Fannah dake sanye da jan hijabi da torches na black tanajin idanunsa kanta ta sada kanta k’asa tana wasa da yatsun ta.
“Kin karya min doka.” Ya fad’a ba tare da yanuna damuwa ba.
A razane ta d’ago kai “Sir wani doka?”
“Kinzo nan before time which means kin karya min doka 8:00AM nace kizo nan ba kafin 8:00AM ba. Take not banasan shisshigi next time.”
Kai ta giad’a a hankali “okay sir.”
“Good make me coffee.” Jakarta ta ajiye kan kujera ta nufa fridge d’in ta bud’e tare da ciro abubuwan da zata buk’ata within 2 minutes ta had’a masa taje ajiyewa kan table d’in amman hannunta se b’ari yake garin haka coffeen ya zube saura a jikinta saura jikin Anas saura kuma kan wasu papers.


Tsawa ya daka “WHAT IS WRONG WITH YOU? Meke damunki? Bakida ido ne. Mschww” harara ya watsa mata “you’re so clumsy.”
Hawaye take sosai “Mr. Fauzi I’m so sorry dan Allah kayi hak’uri.”
Ba tare da ya tanka ta ba ya mik’e a fusace ya shige d’aki tare da bankad’o kofar wanda ya sake razanar da Fannah. Kamar tasan yau ma seya sata kuka ta taho da handkerchief nata danko jiya ta b‘ata farin hijabinta da kwalli. Hawayenta ta share tarasa dame zata goge kan table d’in dan tasan sarai ya dawo ya iske wajen haka ze k’ara mata wata masifan. D’an kwalinta kawai ta cire ta goge wajen. Bayan ‘yan mintuna Anas yafito dawata farar T shirt da ¾ wando wanda ya mugun amsar sa, koda yafito kuwa be tambayeta dame ta goge wajen ba zama yayi kan kujerar.

“Me kuma kike jira baki had’a min wani coffeen ba miss clumsy?”
“I’m sorry” ta fad’a tare da d’aukan cup d’in se b’ari take ta juya kenan hijabinta yakama kujera take ya sunb’uce daga kanta daman wuyan ya mata yawa. A garin haka ribbon nata data kama kanta sakwa sakwa dashi shima ya fad’i gashinta me uban waya ya bayyana. Take ta tsuguna ta d’au ribbon d’in tana k’ok’arin miyarwa amman dan yadda ta rikice dakuma yadda takejin idan Anas kanta yasa tama kasa kama kan se fad’i k’asa ribbon d’in yake ta mayar da hijabin kuma be zo hankalinta ba.


Tunda Anas yake be tab’a ganin gashi kamar na Fannah ba duk zaman da yayi cikin turawa be tab’a ganin erin gashin nan ba ko gashin Ummimi da Amal ma bekai wannan ba. Shi bama tsayin ba uban cikan ne sekace aljanah. Ganin ta kasa kamawa shikuwa ba taimaka mata zeyi ba ya d’au wayarsa ya kira wata. Bayan minti d’aya akayi knocking “come in” Anas yace. Nan wata ‘yar budurwa ta shigo.
“Yes Boss.” Da yatsa ya nuna Fannah “help her ku kama mata kanta” cike da mamaki Fannah ta d’ago kai tana kallonsa. Ta rasa gane wani erin hali ne da Anas sometimes seyayi mutunci. “Okay Boss” cewar ‘yar budurwan. Ita kanta gashin Fannah ya bata mamaki sanda ta yi dagaske ta kama mata. “Nagode” Fannah tace mata, murmushi tama Fannah sannan ta dawo da kallonta kan Anas dake d’an rubuce rubuce. “Is that all sir?”
Kai ya giad’a mata. “Ungo wannan papers kikai wa Salees ki ce masa ya sake printing yanzu wannan yarinyan ta zubar da coffee kai.”
“Okay Boss.” Amsa tayi ta fice.
“Thank you” Fannah tace masa.
“For?” Ya tambayeta ba tare da ya kalleta ba.
“Da ka kirata ta tayani kama kaina.”
“Ni bana buk’atar godiyan ki kuma bawai na kirata bane dan ta taimaka miki, ganin gashin kinne banaso.” Har cikin zuciyarta ta ji zafi wannan munanan kalamu amman ya ta iya? Dama shi neman kud’i haka yake.


Mik’ewa tayi taje ta had’o masa coffeen wannan karan bata zubar ba. Bayan ya shanye tace, “Mr. Fauzi inasan in d’an fita.”
Ba tare da ya kalleta ba yace, “ni ba hana ki fita nayi ba just kisani in na kiraki baki zo a dadai lokacin ba kawai ki tattara kanki kibar min building.” Tasan sarai Anas ze aikata abinda ya fad’i ya korata kamar yadda ya kora wata me girki jiya. Zaman kawai ta cigaba da yi. Kai ya d’ago yana kallonta da blue eyes nasa “well? Kin fasa fitan ne? ”
“Eh zan zauna.”
“Better” yace ya cigaba da abinda yakeyi. Bada jimawa ba wayarsa ya soma ringing yana ganin Angel ke kira ya d’aga take “Hello my Angel” ya ce. Baki wangalau Fannah ta saki tana kallonsa cike da mamaki. Anas d’in ke kiran wata mace da Angel? Lallai kam koma wacece ita she must be lucky. “Yau ziyara zaki kawo min?... Okay ina jiranki... Oh! Har kin shigo? Toh ina jiranki.” Bada jimawa ba k’ofar office d’in ya bud’u Fannah ta zuba ido tana jiran taga wata babbar budurwa kawai taga d’iyar da k’anwarta ma tafita komi. Da gudu tayi kansa tana masa oyoyo! Zama tayi kan cinyarsa “Ya Anas shine yau ka taho office baka tadani munyi breakfast ba.”
“Haba! Angel bacci kikeyi sesa banso tada ke ba.”
“Toh ya Anas karka sake kaji? Nifa har yanzu banyi breakfast ba kuma barin yi ba.”
“Haba my Angel yi hak’uri. Tare kuka taho da Shettima ba? Kice masa ya kaiki duk eatery’n da kikeso kiyi breakfast in na dawo zamu fita tare.”
“Yeyy! Ya Anas” tayi hugging nasa “I love you.”
“I love you too Angel.”

Fannah harda d’igan miyau dan mamaki wai Anas ke dariya yau haka? Bama murmushi ba? Kuma ba k’aramin kyau dariya ke masa ba ga dimple ga fararen hak’wara. Kallonsu ta tsaya yi yadda suke kama nema yasake burgeta.




*© miemiebee*


beeenovels.mywapblog.com
[12:48, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫


❣🎀❣🎀❣


*_written by miemiebee👄_*


2⃣3⃣








“Ya Anas wace wannan tamin kyau.” Cewar Amal da suka had’a ido hud’u da Fannah dake ta kallonsu.
“Wannan?” Ya nuna Fannah. Kai ta giad’a “ai kin fi wannan kyau Angel.” Fannah dake murmushi take yanayinta ya soya jin abinda Anas yace. “Dagake Ya Anas?”
“Sosai ma Angel wannan ai bata da kyau.”
“To Ya Anas wace ita? Metakeyi anan?”
“Nima bansanta ba tana aiki anan ne.”
“Nikam tamin kyau Ya Anas.” Nan ta mik’e daga kan cinyarsa ta nufo wajen Fannah. “Hi” tace da ita. Fannah na murmushi tace, “hello beautiful.”
Amal ta murmusa sosai “dagaske ina da kyau kamar yadda Ya Anas yake fad’i?”
“Sosai Ya Anas naki beyi k’arya ba.”
“Toh me sunanki?”
“Fannah kekuma fah?”
“Amal amman Ya Anas na kira na da Angel.”
“Nice name Amal.”
“Amal kije kiyi breakfast kinji? Karki biyeta da surutu kinji Angel d’ina?”
“Okah Ya Anas, Fannah ba-bye.”
“Ba-bye” Fannah tamata sannan ta fice. Ita ina ma yadda halin Amal ke haka halin Anas yake dataji dad’i, kawai se tana murmushi wa kanta.


“Kuma murmushin me kike?”
Babu ta amsa sa a takaice. Kallo ya watsa mata sannan yaci gaba da abinda yakeyi. Coffee sau uku ta had'a masa a ranan sannan da yazo tafiya ta had’a masa cikin flask kamar jiya.


****


Fannah da Afrah ne zaune tsakar sede kallo d’aya Afrah tamata tagano Fannah ta wula duniyar tunani.
“Wai Ya Fannah tunanin me kike haka?”
“Aww ni!” Ta fad’i a birkice. “Ba komai.”
“Oh common kidena min k’arya dan Allah. Bade kema kin kamu da san Mr. Fauzi ba?”
“Ya Salam!!! Afrah wai giya kike sha ne?”
“Toh fad’a min tunanin me kike?”
Numfashi Fannah taja, “kinsan wani abu ne Afrah?” Kai Afrah ta kad’a Fannah ta cigaba; “ni al’amarin Mr. Fauzi mamaki yake bani kinsan ban tab’a ganinsa yana dariya ba ke ko murmushi bayya yi kullum cikin masifa da tsawace mutane yake, amman yau da wata k’anwarsa tazo bakiga yadda yake dariya ba wallahi-”
Afrah ta katse ta “sekuma ya miki kyau kikaji dama kema yana miki dariyan koh?”
“Ke Afrah anyi mutum wallahi.” “Nama fasa baki labarin.” cewar Fannah.
“A’a yi hak’uri Ya Fannah please.”
Fannah ta cigaba, “kinsan wani biggest secret nasa kuma?” Kai Afrah ta kad’a mata.
“Dan Allah karki fad’awa kowa, Mr. Fauzi yana shaye shaye.”
“Iyye!” Afrah ta zaro idanu waje. “Yana mene? Shaye shaye fa kikace?”
“Ke da Allah kiyi a hankali kar a jiyo mu. Yana shaye shaye amman kuma danayi tambaya se akacemin wai yanada horrible past, akoi abinda ya tab’a faruwa a rayuwarsa can baya wanda yasa yake duk wani abinda yakeyi yau kuma kinsan the most interesting part of it? Duk tsiyar Mr. Fauzi wallahi when it comes to family yanada kirki sosai kiga yadda yabani bandir na N200 mana.”


“Gaskiya ne amman Ya Fannah wallahi tausaya miki nake, shaye shaye fa in randa ya bugu ya miki wani abun fah? Ki nemi wani aiki please banasan abu ya tab’a ki.”
“Karki damu Afrah in shaa Allah ba abinda ze min, ni so nake naji me tarihin sa mesa yake shaye shaye. No offense amman Mr. Fauzi kyakkyawan namiji ne da duk macen data gansa (musamman ‘yan matan miemie bee novels group LOL) zataji tana sonsa kotaji ya burgeta ga kyau ga kud’i ga class ba abinda ya rasa mesa zena shaye shaye? Dole da akoi k’wararren reason and I must find out wayasani ko in giara masa rayuwa.”


Cike da mamaki Afrah ke kallon Fannah, yaushe rayuwar mutane ya soma damun Fannah’n da bata shiga cikin jama’a. Ahhh! gaskia Mr. Fauzi ya k’ure ta fannin had’ewa. “Toh kekuma tanan kika b’ullo yau? Ai bari ya cigaba da saki kuka ni ba ruwa na. Ina ruwanki da shaye shayensa yaga dama ya dawwama dashi mana. Nikam gaskia ina ji miki tsoro.”
“Worry not Afrah.”

Washegari ma tun 7:00AM Fannah tagama shirinta se jiran call daga Anas take amman shiru 7:30AM nayi kawai ta tsari napep ta k’arisa office nasa koda datayi knocking bakin k’ofar kuwa ba response ta gwada bud’ewa ma a rufe waje ta nema ta zauna daga gefe tana jiran dawowansa.


8:00AM on the dot k’ofan elevator ya bud’u Anas ya bayyana daga bayansa. Cike da mamaki Fannah ke kallon Anas dake sanye da suit as always. Wai shi jira yake ne se takwas d’in daidai ya cika ya shigo a’a kokuwa kawai perfect timer ne? Binsa da kallo take tana wannan nazari har ya iso bakin k’ofar bata sani ba.
“Incase kina mamakin ko tsayawa nake se daidai 8:00AM yayi nake iso nan toh you are mistaking kuma wai ban hanaki kallo na haka ba?”
“I’m sorry” ta fad’a a kunyace.
“Ba abinda na tambaya ba kenan.”
“Ka hana...” Ta fad’i kanta a k’asa.
“Then kidena, saboda ke barin fara sa niqaf ba. Mschww!” nan ya bud’e k’ofar office d’in yashiga, Fannah na biye a bayansa. Bayan ya ajiye jakansa ya juyo tare da crossing arms nasa a chest nasa yana kallonta.


“Waye ya gayyace ki nan?” Sam bata fahimce sa ba. Hijbanta me hula ta sake ja tare da rufe mata kusan rabin fuskarta, ta tsani taji wannan blue eyes nasa kansa.
“So kike na sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login