Showing 252001 words to 255000 words out of 268365 words
Chapter 85 - Tana Tare da ni complete book document .txt
ni har Amal bame yafe miki sede ko Abuu da Shettima kina iya hak’uri in maganganun dana fad’a miki are a bit harsh to your ears, hakan na nuni da tsantsan tsanan da nake miki ne Ummimi dukda cewa kina mahaifiyata.”
“Anas enough!” Ummie ta daka masa tsawa “kai bakasan wannan mahaifiyarka bace kake gasa mata bak’k’en kalamu haka iya son ranka? Ya Ibraheem kamishi fad’a.”
“Anas yayi laifi Nafeesa, amman kuma in kika lura Aysha itace sila da ace bata aikata abinda tayi 15 years back ba da Anas bare tab’a gaya mata munanan kalamu haka ba, I’m not saying Anas is right what am saying is he has a point mukad’ai muka san kalan hell da mukayi witnessing da wannan marar imanin ta tafi ta barmu. Aysha me muka tab’a miki? Talaucin da kika tafi kika barmu danshi kisani bamu muka d’aura wa kanmu ba, gashi nan kinzo kin gani da idanunki Allah ya yaye mana shi saboda haka me kika zo min a gida?”
“Tabbas ba k’arya ko kuskure a magananka Ya Ibraheem Allah shike azritawa aduk sanda yaga dama, inda zan iya bayyana muku how sorry I am da nayi, inda kunsan kalan tashin hankalin dana shiga bayan barinku danayi, wallahi tun a duniya anan naga sakayyan butulcin dana muku shiyasa nake barar gafararku Ya Ibraheem inhar baku yafemin ba bansan a’ina zan sa kaina ba bansan ya zaman kabari ze zame min ba ku agaza please. Ya Ibraheem inhar kai baka yafemin ba ba yadda yaran nan zasu yafemin please ka taimaka, Ummie dan Allah kisa baki ko zejeki.”
“Ya Ibraheem kayi magana please godiya yakamata muyi tunda har Aysha tagano kuskurenta kuma tayi repenting se ku kuma kuyi hak’uri ku tausaya ku yafe mata, Aysha ko zaki bamu labarin ya rayuwarki ta kasance cikin wannan shekaru goma shabiyar dasuka shud’e ba tare da kowa yaji ko ya ganki ba? Ko ban tambaya ba nasan kina cikin babban tashin hankali jikinki kad’ai amsa ce game tambaya in shaa Allah, in family’nki sukaji labarinki zuqatansu zasu kariya su yafe miki.”
“Nagode Ummie” tayi maganan tare da komawa kan kujera ta zauna. “LABARI NA bashida dad’in sauraro, ba komai bane aciki banda k’uncin rayuwa wanda ni dakaina na d’aura wa kaina saboda kwad’ayin kayan duniya dana sa a gaba, kwad’ayi ya kasance halin mata dayawa a rayuwarmu na yau. A gaskia duk wacce tad’au kwad’ayi abinyi toh wallahi tana tattare da gwagwarmayar rayuwa saboda kwad’ayi ba abar yi bace. Labari na wanda yasamu asali tun daga ranan dana bar gidan Ya Ibraheem nabi Alhajin Yola shine mafi mumunan labarin da na jima banji ban kuma gani a real life ba sede a labarai.” Taja numfashi sannan ta cigaba...
*© MIEMIEBEE*
beeenovels.blogspot.co.ke
[13:00, 12/18/2016] +234 903 612 6826: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫
❣🎀❣🎀❣
*_written by miemiebee👄_*
In dedication to *Aunty Sis💞*
9⃣5⃣
_“A yinin ranan da nabar gidan Ya Ibraheem nabar yarana abin muradina Anas da Shettima badan komai ba sedan bak’in talaucin daya addabemu sau dayawa muna tashi ba abinchi bayan gashi a waje Alhajin Yola ya nuna yana sona yana kashe min kud’i ba tare da na kawo wani tunani a raina ba na tattara kayakina nabar gidan Ya Ibraheem dukda erin kuka da roqana dasu Anas suka rik’ayi hakan be hanani tafiya ba saboda alokacin kwad’ayi ya riga ya rufemin ido”._
_“Bayan nabi Alhajin Yola yawuce danu Yola a ranan inda muka sauk’a awani had’ad’d’en hotel, seperate d’aki yakama mana acewarsa bamuyi aure ba tukuna be dace mu had’a d’aki ba washegari ya tinkareni ya fad’amin abinda ke zuciyarsa na aurena dayakeson yi dukda nasan haramun ne aure akan aure hakan be hanani amincewa da k’udirinsa ba, achan Yola aka d’aura mana aure acikin sati yamana processing visa inda muka wuce tsarkacacciyar k’asa Saudi yin honey moon sede wani gudu ba hanzari ba tun isar mu chan nake fama da zazzab’i, zuwan mu asibiti aka tabbatar mana juna biyu ne d’auke dani cikin Amal kenan, barin b’oye muku amman a lokacin cewa ma nayi azubar da cikin kasancewar chan gari ne me tsarki basu aikata haramun aka k’i biya min buk’ata koda muka dawo gida hankalina a tashe yake tsoro na kar Alhajin Yola yace ya fasa zama dani tunda na taho masa da cikin wani gidansa, alokacin banida wata burin data fi in kasance dashi saboda yadda yake kashe min kud’i. Shi ya kwantar min da hankali yakuma tabbatar min da cewa in kwantar da hankalina inyi rainon cikin kar na zubar yaso in na haife se na dawo muku da abunku, without a second thought na amince da hakan, haka nata rainon cikin Amal daya bani wuya har fiye da na Anas cikin fari dalilin haka yasa natsani abinda ke cikin ko ante-natal d’ina ba regularly nake zuwa ba fata na Allah rabani da abinda ke cikin nawa lafiya.”_
_“Munyi tsawon watanni 7 a Saudi ba tare da mun samu sab’ani da Alhajlin Yola ba tarerayata yake kamar ‘yar baby abinda nakeso shi yakemin alokaci d’aya na mulmule tunda nafita daga first trimester. A wannan watan ne muka dawo Nigeria inda muka sauk’a a Maiduguri nacigaba da rainon cikina dana tsanesa fiye da mutuwa, kwatsam da daren wata rana nak’uda ya taho min wanda nad’au mutuwa zanyi bayan kusan awa shida danayi a labour room nasamu Amal ko k’are mata kallo banyi ba, in tambayi nurse d’in mace ce ko na miji ma banba saboda jin dad’in da nake na rabani da ita ko shi da Allah yayi, naso barin ta ta kwana a asibiti amman sunka k’i dole na taho da ita gida anan ne na gano mace ce na haifa duk erin kukan da Amal take a lokacin dan yunwa besa na shayar da ita ba yaron dake mana d’an hidima ne yabata ruwa ta rik’a sha kafin garin Allah ya waye Alhajin Yola yasa sa a mota da Amal tare da letter dana rubuta aka kawo muku ita”._ d’ago kai tayi ta kalli Amal dake ta kuka jikin Anas kamar ba gobe taji ta k’ara tsanan kanta na wulaqanta wannan kyauta da Allah yayi mata.
_“Se a wannan lokaci nakai Alhajin Yola gun iyayena basu ko damu taya nayi auren ba tambayar da suka min d’aya ne shin yanada kud’i? siyayyan da Alhajin Yola ya musu ne yazame masu amsa, k’arya namusu nace ka saken ne Ya Ibraheem shiyasa na sake aure, please kayi hak’uri ka yafemin na sharrin dana maka”..._
“Ko kad’an baki min sharri ba Aysha saboda aranan da kikayi stepping foot kika bar gidana a ranan na miki saki d’aya saboda nasan duk inda zakije aure zakiyi nikuma ina sonki barin iya jure fushin Allah akanki ba shiyasa na sauwak’e miki kinga ko bakiyi aure akan aure ba.” wani sabon kukan ya sake rufe Ummimi she can’t ever forgive herself.
“Tabbas babu kaman ka acikin mazaje Ya Ibraheem nagode k’warai Allah yima sakayya. _“Daga nan muka wuce New York kamar yadda yamin alk’awari, rayuwa bata tab’amin dad’i kamar a wannan lokaci ba sede abin mamaki koda na tambayi Alhajin Yola wani aiki yake seyace min he is self employed niko da dama kud’insa ne ya damen ban kawo wani abu a raina ba haka muka d’au tsawon shekara muna soyayya dashi ba tare da mun samu wani matsala ba iyayena kuwa kullum yana cikin musu alkhairi daban daban a shekara na biyu da aurenmu ne nasamu cikin Barrah da Basmah wanda suka kasance twins kyawawa wane Amal shekarunsu uku nasamu Yusuf wanda yake sak Anas shi kuma, harta blue eyes nasu iri d’aya”_ ta d’ago kai tana kallon Anas da take ya kawar da kallonsa daga gareta, hawayen ta ta share sannan ta cigaba;
_“Alhajin Yola ya kasance yana matuqar son ‘ya‘yansa becika tsawata masu ba koda sunyi laifi ne, haka rayuwa ta cigaba da kasance mana cikin jin dad’i alokaci kad’an ne nake tunawa dasu Anas da Shettima amman kuwa in na tuna da talaucin daya fitini gidan Ya Ibraheem sema inji na tsanesu tun daga kan Yusuf haihuwa ya tsaya min. Su Barrah suna da 12 years aduniya nasoma fuskantan chanji daga mahaifinsu mutumin da baida magana baida masifa yamiyar da masifa abinyi abu kad’an kayi seya tsigale ka, akwai lokacinda har mari na yayi saboda yana ma Yusuf fad’a nashiga toh tun daga wannan lokaci ban sake gane kan mahaifinsu ba, yadena sonmu kullum cikin k’untata mana yake school fees na makaranta ma seya ga dama yake biya musu nayi nayi ya gayamin inhar laifi na masa ya fad’a mani in basa hak’uri amman ina inya watsa min wani mugun kallo ni dakaina nake tashi masa agun a 13th birthday’n su Barrah yayi suprising namu duka, birthday cakes biyu ya siyo musu mukayi celebrating birthday nasu washegari yasa duka yaran cikin mota cewa ze kaisu park su shaqata yatambayeni ko zani nace mai a’a bansani ba ashe wannan rana shine rana na k’arshe da zan sake sa yara na a idanu na ba_. Kuka ne yafi k’arfinta hankalin kowa ya tashi wajen banda Anas, duk sun k’osa suji meya faru, Ummie da Fannah ne ke bata hak’uri.
Picture’n taciro ta miqa ma Ummie “yau watanni bakwai kenan da rasuwansu.”
Salati kukeji a d’akin bayan Ummie tagani ta miqa wa Abuu se Shettima lastly Amal then back to Ummimi again, anan duk sukayi mata ta’aziya shima Anas badan yanaso ba yayi mata.
_“Tun safe ya fita min da yara har La’asr basu dawo ba kodana kira wayansa kuwa har ta tsinke be d’aga ba wayoyin su Barrah kuwa switched off yake cemin, anan fa hankalina ya tashi daman tun tafiyarsu nake ji ajikina something bad will happen to them nakasa zama gu d’aya fatana Allah dawo min dasu lafiya se bayan Isha’i naji k’aran bud’ewan gate a guje na fita waje bayan yayi parking na tsaya gun ina jiran fitowan farin cikina yara na, sede basu ba alamansu, mahaifinsu kad’ai nagani cike da tashin hankali na tambayesa ina yaran suke kallo na yayi a raunane sannan yace min wai an sacesu, bansan a lokacin dana sume wajen ba next abinda nasani shine gani na danayi kwance akan gadon asibiti se a washegari muka dawo gida ba kalan tambayan duniyan da banma Alhaji Isma’il ba ya fad’amin ina ‘ya‘yana, amsar nasa d’aya ne an sacesu jiya a park cike da tashin hankali na d’ago mayafina zan kai report station ganin haka munafikin ya dakatar dani yamin qaryan wai tun jiya yakai report yanzu haka police sunakan investigation haka har wani sati ya zagayo ba labarin yarana, ban sake sanin meke min dad’i ba akullum ina sa ran za’a samu su Barrah amman inaa adaren wata rana na fito daga d’akina zan wuce dining space dan shan ruwa naji Alhaji Isma’il akan waya har na wuce se wani abu ya dawo dani baya nakasa kunne ina sauraron meyake fad’i a wayan. Hankalina ya matuqar tashi jin da bakinsa yake fad’in “ran yara na uku dana baku be isheku ba yanzu na mata ta kukeso?” Innalillahi wa’ina ilaihi raji’un”_
_“Mutuwan tsaye nayi a wajen totally speechless ban hankara ba naga Alhaji tsaye a gabana fuska nakad’ai ya zame masa amsa ga tambayan daya s min. Ina kuka na mai maganar, “Alhaji? Dagaske ne?” Na tambayesa. Kame kame yasoma bansan a lokacin dana fara kai masa bugi ba, ba kalan zagin da ban masa ba a daren nace zan kai k’aransa station nan ya kukkule duka k’ofofin gidan da dambe da fad’a yakaini wani d’aki ya rufeni, ina jinsa yayi waya da d’aya daga cikin ‘yan k’ungiyan nasu yana cemai ya yarda ze sihar dani nima acewarsa tunda nasan sirrinsa yanzu ba amfani na again, ba waya akusani dani koda akwai ma bansan wa zan kira ba kwana nayi ina Sallah Allah ya kub’utar dani daga sharrin sa, washegari nasome neman abinda ze taimaka min in b’alla lock na k’ofan, da cokalin da nasamu na b’ab’alle screws d’in k’ofan na fito a lokacin bayi gida yafita, kayaki kad’an na d’auko da sauran essential things da zan buk’ata, na nemi wayana sama da k’asa na rasa, a gurguje nabar gidan nakai report police station ko ya akayi maganan yaje kunnensa oho next abinda naji shine wai yagudu yabar k’asan kwata kwata tun daga wannan rana ban sake sa shi a idanu na ba 3 months ago na ganshi awani super market tundaga wannan lokaci na shiga b’uya saboda nasan aduk lokacin da ya ganni tabbas nima siyar danayi zeyi, aiki na samu awani restaurant as a cleaner dashi na dogara har izuwa lokacin dana had’u da Anas da Fannah, kunji takaicaccen labari na.”_
Tausayinta ne yakama kowa a d’akin harta Anas, seda Ummie ta zubar da hawaye.
“A gaskia kinsha gwagwarmaya a rayuwanki Aysha ba abinda zamuce se Allah ya kare aukuwan na gaba ya tsaremu daga sharrin mutane da aljanu gabad’aya...” dadda’d’un kalamu Ummie tariga gaya wa Ummimi shi kansa Abuu ya mugun tausaya mata yasani alhak’in sune yakama ta tunda har a duniya taga sakayya yaci ace sun yafe mata suma.
“Aysha ni na yafe miki na yafe miki har abada abinda ya faru dake kuma Allah takaita” cewar Abuu.
“Ya Ibraheem nagode, Allah ya saka da alkhairi, Shettima, Shettima dan Allah ka yafemin abinda na maka.” Shiru yayi bece komai ba ba irin rok’an da bata mai ba seya bud’e baki zece ya yafe mata seya kasa haka ta dawo kan Amal ma duk ba wanda ya iya ya yafe mata Anas kam ba magana Abuu be sa baki ba saboda yasan ba’a shiga tsakanin uwa da yara yasani with time duk zasu yafe mata.
***
Abuu ne tsaye da Ummie a dining ayayinda Ummimi ke zaune da Fannah a parlour su kad’ai Anas da qannensa duka sunyi d’aki.
“Ya Ibraheem yanzu ya zakayi da Aysha?”
“Ni kaina bansani ba Nafeesa, bansan me zanyi da ita ba.”
“Agani na mubarta ta zauna damu anan tunda ba inda zata iya zuwa batada kowa banda mu.”
“Me kike nufi Nafeesa?”
“Ina nufin ka dawo da ita d’akinta ai akwai aure a tsakaninku.”
“Barin iya dawowa da Aysha ba ina sonta amman barin iya dawo da ita ba.”
“Zaka iya Ya Ibraheem kayi hak’uri mukoma parlon.” Bayan sun dawo suka zauna Ummie tayi gyaran murya “Aysha kinje kinga iyayenki kuwa?”
“Banje ba tukuna bansani ko iyayen nawa ma suna raye ba.”
“Kinada masauk’i yanzu?”
“Banida Nafeesa.”
“Toh yanzu wani mataki kika d’aukar?”
“Ba abinda nakeso kaman in kasance da ‘ya‘yana Ya Ibraheem dan Allah kayi hak’uri ka dawo dani d’aki na badan halina ba dan Allah.”
“Aysha na soki kuma zan cigaba da sonki amman ban tsammanin zan iya dawo dake.”
“Ya Ibraheem please karka min haka dan Allah karka hanani daman kasancewa da yarana again nayi kuskure amman wallahi na tuba barin sake aikata abinda nayi da a baya ba, ka taimaka please”
“Aysha kiyi hak’uri amman barin iya dawo dake ba” yana kaiwa nan ya miqe. Hak’uri sosai su Fannah suka rik’a bata. Da k’yar Ummie ta samu tayi convincing Abuu ya yarda aka bawa Ummimi d’aki d’aya a gidan Anas najin haka yasa Amal ta had’a akwatinta suka koma gida tare yasan muddin Amal tacigaba da zama da Ummimi toh eventually Amal zata yafe mata abinda baiso kenan.
****
Tun isar su Fannah gida bata ma Anas magana ba a d’akinta Amal ta sauqa daidai da Azahar Anas yatura Amal dataje ta kira Fannah suyi Sallah a d’akin Hanan ta tarar da ita bayan tayi sallama tace, “Ya Fannah wai kifio muyi Sallah inji Ya Anas.”
“Kice masa yajaku ku biyu zanyi nawa da kaina” da “toh” Amal taje ta isar wa Anas da saqon Fannah, daman yau yasan da akwai drama shida kansa ya miqe yaje yasamu Fannar, agefenta ya zauna “Flower tashi muje muyi Sallah.”
“Bakaji meh Amal tace maka bane? Nace kajaku zanyi nawa ni kad’ai.”
“Mesa toh?” kafin yakai hannunsa kan cikinta taja da baya.
“Mara na namin ciwo se anjima zanyi.”
“Toh zamu jiraki.”
“Ni ina ma ace yadda kakemin haka kake ma Ummimi wallahi Habeebi ko kad’an banji dad’in abinda kama Ummimi ba yau, uwa uwa ce fa you are not being just inhar kai baraka yafe mata ba then don’t drag Amal into it, I know ba tsakani da Allah kasa Amal had’a akwati ta biyomu ba gudun kar ka barta achan eventually tayi forgiving Ummimi ne koba haka ba?”
“Ke kikaji wajen zaki tashi muyi Sallah ne kokuwa?”
“Bansani ba nima” tana kaiwa nan tabar masa d’akin binta